Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
ce in zo, tun daga lokacin sai da aka koya min tukin mota karama da baba, Bus da ta kwasar kasa......, ya zamo babu motar da ba zan iya ja ba, ina fitowa suka dauke Ni aiki da albashin da na zarce manyan ma'aikata............" Imtee kallon sa take yi kawai, sosai ya dage yana sanar mata alkhairan ahalin da ta girma da tsoron su da jin akasin abinda yake fada a bakin yan anguwa..... To ko gidajen da suke siyewa cewa aka yi fa zuwarwa mutane suke da bindiga su baka zabi ranka ko gidan ka, a dole ka siyar musu gidan ka tafi ka bar musu filin....... Su ne kaΙ—ai suka gagare su, ehe! Ajiyar zuciya kawai ta sauke a lokacin da ya gama ya sake fuskantar ta a tausashe ya ce" Ba zata cutar da ke ba, taimaka maki zata yi, ba zan so su dakatar da ke daga zuwa makarantar nan ba, ki tausayawa iyayenki irin kudin da suke zuba Miki, ki yi kokari ki jajirce ki zamo cikin zakarun da gobe zaki samu damar tafiya musabaka har Saudiya, ke ba zaki fi kowa jin dadin ace kin tafi da mamanki da babanki Saudiya ba? Baki da burin kai su dakin Allah ne????" Da sauri ta zuba masa ido, a tausashe ta ce" Zan iya kai baban mu dakin Allah da maman yara????, Ni????" Kai ya gyada mata cike da gamsarwa ya ce" Kwarai kuwa, idan kika dage da karatun nan har kika samu kika zama zakwakiya a cikin sauran, tabbas za'a ba iyayenki kujerar maka , wace zasu maki rakiya har su yi ibada kafin ku dawo cikin aminci a karkashin kulawar makarantar nan....." A saman lebenta ta furta" Ya Allah ....., yaya ka ga maman yara a Saudiya, ace Ni ce na kai ta.....???" Sam bai iya jin me tace ba, sai sake cewa ya yi" Kin yarda zaki koma????" A hankali ta gyada kanta, sannan kasa kasa ta ce" Ama ba yau ba, sai gobe idan na dawo in sha Allah " Kai ya gyada yana murmushi ya ce" Madallah, ya batun soyayyar mu????" Sai da ta zarro ido tana dubansa kafin ta dauke kanta ...., dan ita abin har kunya yake bata, wai ashe zata girma itama ta fara soyayya? Cabdijan Juyawa yayi baya ya dauko ledar da ya zo mata da ita ya bude ya ciro waya kirar Samsung ya miko mata yana fadin" Wai Fa'iza ke batun baki da waya, shine na je na siyo maki ita yau harda layi da komai na saka maki, duba ki gani????" Da dan tsoro take duban wayar, a hankali ta miko masa ta ce" Yaya zan yi da waya Ni? Ta yaya zan iya rike waya a gidan mu? A'a ai da ba'a bamu ba har yanzu babanmu ne yace sai mun girma" Murmushi yayi yana kallon kwayar idannuwanta ya ce" Girma? Bayan wannan? Ai kin gama girma baby, kuma wayar nan da kika gani kina iya amfani da ita har ta tsufa in sake maki sabuwa ba tare da an sani ba a gidan ku, duba fa ki gani irin yadda yan mata ke fantsamawa da waya, kin ga fa sai da na lodo maki film ne, wakokin soyayya ne da sauransu, dubi ki gani....." Ya kuwa ringa nuno mata abubuwan da sai dai su dauki rediyon maman yara su buya su saurara, Bama kamar yan wakokin nan na soyayya ....gasu Ζ™arara a gabanta tana kallo A tausashe ya ce" Ki yi hakuri ki amsa, zan so in riinga kiran ki da dare muna firar soyayya kin ji? Please dear......." Kasa cewa komai ta yi sai sada dubanta, dan kuwa zuciyarta ta kasu kashi kashi da tunani daban daban......., kamar ta amsa kamar idan ta yi haka ta ci amanar mahaifinta ne?????????, to Ama ai mamanta ta sanar mata ba wani laifi a haka ko? Sai ma da ya ciro kudade ya saka a ledar ya hade ya daure mata ya ce" Wannan kuwa ki sha ice cream kafin ki bani dama na zo zance sai in zo maki da shi mai yawa.....shin kin taba shan ice cream kuwa???????" Gaba daya zuciyar Imtee sai ta ringa kasuwa kashi kashi......, karshe ma sai ta kasa yankewa kanta hukuncin abinda ya dace sai shine ya yanke mata ta hanyar daukan hanyar gidansu da ita, ya sauke ta daf da gidan sannan ya mata Salama ta shige gidan da sakon ta jikin ta na rawa Kicibus ta yi sakamakon ganin auntyn yara na shanya a filin gidan, kuma tsayuwar motar ta sa ta dan dakata dan tunanin waye zai zo nan a mota kuwa?, hakan ya sa ta dan zubawa kofar ido tana kallo, har Imtee ta shigo bata daina kallon kofar ba da jiran jin an shigo, sai da motar ta tashi ta yi gaba sannan ta dawo da dubanta kan imteen da tunanin ko kawai wani ne ya zo wucewa ya dan bi ta kusan gidan nasu, bata taΙ“a kawowa kanta cewar IMTEE zata iya shiga motar saurayi ba harma a kawota kofar gidan su ba, sai dai tsayawar da ta yi jikinta na nunin alamun rashin gaskiya, da abinda ke hannunta, da kuma gannin ita daya ce ya sa itama zuba mata ido tana son ganin shigowar A'isha, da kuma jin IMTEE ta mata Salama irin na yaya masu tarbiyya idan sun zo gidajen su, dan takan yi Salamar, tana yin Salama sosai, Ama yanzu sai bata yi ba......ko menene dalili........??????????????????? A tausashe ta budi baki ta ce..........πŸ’…πŸ’…πŸ’…πŸ’…πŸ’…πŸ’…πŸ’…πŸ’…πŸ’…πŸ’… An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9