ita ma a tsorace ta tashi, saboda mummunan mafarkin da ta yi da Hajiya sa'a tana ƙoƙarin shaƙe ta, ta caka mata wata wuƙa.
Baba ya ce "Wani irin Nana za ta kashe ta kuma? Ba ga Nanan a gefe tana bacci ba?"
Cikin fushi da tsawa ta ce "To ka ƙaraso mana ka ga abin da take yi"
Ya ƙarasa ya ga Suwaiba, ta rirriƙe wuyanta, idanunta duk sun fito waje sai kakari take, da ƙyar take furta Nana za ta kasheta.
Baba ya ce "Suwaiban Baba, buɗe ido ki ganni, Nana bacci take yi me ki ke gani?"
Cikin kuka da kakari Ta ce "Baba wallahi Nana ce, jinina take sha, ka hana ta zan mutu"
Baba ya koma gurin da Nana take, ya kai hannunsa ya juyota, idanunta a buɗe, amma babu baƙar ƙwayar idonta, sai farar kawai. Jikinta kuma sanyi ƙalau kamar gawa.
"Ni wannan wane irin abu ne haka?"
"Ke Jamila, je ki ki taso mini Gaddafi" Jamila ta tashi jiki a sanyaye ta fita ƙofar gida, ta ƙwanƙwasa wa Gaddafi ɗaki.
Tare suka dawo, yana tsaki yana bala'in shi tattarawa zai yi ya koma in da ya fito, ya gaji da wannan bala'in na gidan.
Ɗan tsayawa yayi yana kallon in da Nana take, ga gefe Mama riƙe da Suwaiba tana kuka.
Ya ce "Mutuwa Nanan tayi ne na ganta a haka?"
Cikin kuka Suwaiba take miƙa wa Gaddafi hannu ta ce "Yaya ka taimake ni, Nana za ta kashe ni, jinina take sha" tayi maganar tana kuka.
"Wane irin shan jini kuma?"
Nana kuwa tuni ta lula wata duniyar a yanayin da take ciki.
Domin kuwa Ƙaisar take gani. Ya ce "Kin ga da kin sake kin fesa turaren nan a jikinki, da jininki za a sha ba nata ba. Aike ne na musamman domin ke, da na bari kin fesa turaren nan da sai dai wata ba ke ba"
Nana ta kalle shi ta ce "To ni me za ayi da jinina? Kuma meyasa ba ka hana wannan mummunar matar shan jinin Suwaiba ba?"
Ya tanƙwashe ƙafafuwansa ya kaɗa kai ya ce "Saboda ke ce uwar gijiyata, alhakin kula da ke ne kawai a kaina. Duk da ba jininta suke buƙata ba, amma idan 'yar aiken ta ji daɗin jinin na ta, to fa ta samu wurin zama. Ko da su can jinin bai yi musu amfani ba, to ita za ta ci gaba da amfani da jininta, domin ta warke daga ciwon jikinta, idan ba ayi wasa ba hakan zai yi ajalinta."
Cikin damuwa Nana ta ce "To ka yi wani abu a kai mana"
Yayi murmushi ya ce "Zan iya wani abu a kai tabbas, amma daga lokacin da ki ka fara bani umarni hakan yana nufin kin karɓi gadon gidanku. Kuma zamu yi aiki tare"
Da hanzari ta ce "A'a ni ba zan iya shirka ba na gaya maka. Amma ba zan zuba ido komai ya tafi a haka ba. Idan haka ne anya ba wannan matar Hajiya sa'a da ta kawo turaren babu masaniyarta a kan wannan abun?"
Murmushi ya yi ya shafi gefen fuskar Nana ya ce "Ban sani ba, amma ke ma zan shafe komai daga kanki yanzu wani binciken ba shi da amfani sam. Mussaman ke da ba za ki yi abin da ya dace ba, idan ki na tsananta bincike wataran za ki shiga gurin da ba zan iya ciro ki ba.
Kalli nan ki ga, ta waiwaya domin ganin abin da yake nuna mata.
Ɗakinsu ta gani, Suwaiba ta samu bacci, Jamila kuma ta ce Allah kar ta, ba zata kwana a ɗakin nan ba tsoro take ji.
Mama ta ce su tarkata su koma ɗakinta, su kwana tare da yaranta a bar Nana ta ci kanta.
Baba ya kalli Gaddafi ya ce "Gaddafi, gobe in Allah ya kaimu dole mu yi sammako, mu kai yarinyar nan gurin da ka faɗa ɗin nan. Ni kaina na fara jin tsoron abubuwan nan".
Gaddafi ya ce "Allah ya kaimu"
Nana ta dubi Ƙaisar ta ce "Ni dama gurin mamana ka nuno mini, na ganta ko na ji daɗi"
"Idan na fara karbar umarninki, haka yana nufin kin amince da sharaɗina, ni kuma zan yi miki mubaya'a na zama mai hidima a gare ki"
"A'a bari ba na so" tayi maganar tana girgiza kai.
Ya saka dogwayen yatsunsa yana ci gaba da shafa kumatunta ya ce "Alamu na nuna, sarƙar ƙaddara ta mayen ƙarfe na ƙoƙarin janmu wani wuri, ta yi wani ɗauri mai wahalar kwancewa. Ko na ce sarƙar na ƙoƙarin sarƙe ki. Gobe za a wuce da ke gurin mai magani, 'yar uwakki ta shafa miki mugun tabo, tun da ta ce kina sha mata jini, babarta ba za ta yi shiru ba, za ta yi ta gaya wa mutane ne. Ga yayanki can ya sha ƙwayoyi yana ta bacci, gobe har ku tafi ba zai farka ba, domin na ƙarawa abin da ya sha ƙarfi. A duniya zan ga wanda ya isa ya raba ni da ke. Zan ga mai karambanin mai maganin da zai jarraba hakan".
"Allah ne zai raba ni da kai" ta yi maganar a hasale.
"Da zai rabani da ke, da bamu haɗu ba" ya bata amsa.
Nana ta waro ido ta ce "Kaii zaka yi saɓo, ki ba musulmi ba ne? Ko da yake musulmi ba zai yi abin da ka ke yi ba"
Ƙaisar ya yi dariya ya ce "Kamar ba musulmin ne ke neman jininki su yi tsafi da shi ba"
Ya koma ta bayanta, ya zuro kansa gefen fuskarta, hakan ya ƙara adadin bugun zuciyarta, jikinta yayi sanyi ƙalau kamar wadda aka saka a cikin firinji.
Ya ce "Bari na sake nuna miki wani abu, amma akwai buƙatar na tsaya kusa da ke, idan ba haka ba, wannan 'yar ƙaramar ƙwaƙwalwar ta ki bugawa za ta yi. Kalli can" ya nuna mata wani mudubi. Ta ɗaga kai ta kalla.
Kawai ta ga Auwwal a kwance ana yi masa wankan gawa, gefen cikinsa na ta zubar da jini.
Razana tayi za ta miƙe, amma ya riƙe ta ya ce "Kar ki zarge ni, babu sanya hannuna a cikin wannan abin, ya gama shirinsa gobe zai tafi Abuja, ɗazun nan masu ƙwacen waya suka tare shi, suka karɓi wayar suka caka masa ɗan buda.
Yaran kuma da suka yi, abokan yayanki ne, nan da 'yan kwanaki idan bincike yayi nisa shi ma za a kamo shi".
Wani irin yinƙuri Nana ta yi, domin ta ƙwace daga jikinsa amma ta ji an riƙeta. Ta ɗaga kanta kawai ta ganta a ana kiciniyar shiga taxi da ita, ta waiwaya ta ganta a tare da Yaya Atine da Baba.
Ta ja ta tsaya ta ce "Wai ya na ga haka?"
Baba ya ce "Ba ki da lafiya, gidan mai magani za mu je"
"To Baba ai ban yi sallar asuba ba"
Yaya Atine ta ce "Mu je, idan an je gidan mai magani sai ki yi sallar"
Nana ta kalli sama yadda gari ya fara haske, ta ce "A'a ni a bari na yi salla"
Baba ya ce "Ta dawo hayyacinta, a ƙyale ta tayi sallar"
Nana ta shiga gida Yaya Atine ta bita, ta yi alwala.
Yaya Atine ta ce "Rabi ki bari a tafi da Suwaiba gidan mai maganin nan a duba ta ita ma"
Mam ta ce "Eh ko ba gidan mai magani ba, ta je ta ƙarasa lasheta a hanya ta kashe ta, babu in da za ta je, kuma wallahi kurwar Suwaiba ta fi ƙarfinki" ta yi maganar tana hararar Nana.
Nana dai ta yi alwala, ta gabatar da sallar asuba, aka saka ta a cikin taxi, aka ja aka tafi, ba tare da ta san ina suka dosa ba.
Suwaiba kuwa ba ta tashi daga bacci ba, sai bayan ƙarfe tara na safiya, kuma babu wanda ya tashe ta, domin ta yi salla. Sai a lokacin ta yi salla, ta nemi abin karyawa.
Jin Mama na ta jera mata sannu ya sanya ta ce "Wai mama sannun me ki ke yi mini ne?"
Mama ta ce "A'a abin da ya faru da ke jiya mana, wannan azzalumar tana neman kar ki"
Cikin rashin fahimta Suwaiba ta ce "Wace ce? Ni fa ban gane ba"
"Jiya kururwar da ki ka din ga yi ki na Nana za ta kashe ki, tana miki jini, ba mu yi bacci ba fa" Suwaiba ta zaro ido ta ce "Ni ɗin?"
Jamila ta ce "Eh mana, kasa numfashi ki ka yi fa, kina ta kuka wai Nana tana sha miki jini"
Jikin Suwaiba ya yi sanyi, ta ce "To ai ni tun da na kwanta, ko juyi ba na tunanin na yi, sai yanzu na tashi daga bacci"
Jamila ta ce "Ikon Allah, kin ga kururwar da ki ka din ga yi kuwa, wai Nana na sha miki jini?"
"Ni dan Allah ku daina wannan zancen tsoro ku ke bani wallahi kar na je, aljanun nata ne nima su ka shafe ni"
Muryar Imran ce ya dawo da su kan tsakar gidan, yana ta kwaɗa wa Nana kira.
Nasiru ya ce "Nana fa sun tafi gurin mai magani, bayan sallar asuba"
"Kamar yaya ita da wa?"
"Asubar farko, aka je aka taho da Yaya Atine daga gidanta, a taxi ɗin malam Shehu, gari yana fara haske suka tafi. Jiya ne Suwaiba ta din ga ihu cikin dare wai Nana tana sha mata jini, shi ne suka tafi da sassafe"
"Kuma shi ne ba a gaya mini ba, ina ne garin mai maganin, kar aje a kai ta gurin bokaye"
"Wallahi ban sani ba"
Imran ya ce "Ke Suwaiba, ya aka yi Nanan ta sha miki jini, ita ba mayya ba, kar ki ja a ɓata mata suna, ni ba na son ƙananan maganganu ki bar ta ta ji da halin da take ciki mana"
A fusace Mama ta ɗaga labule ta fito ta ce "Ban gane ba, za ta yi mata ƙarya ne? ko dan kai ba a gidan ka kwana ba, ba ka san a halin da ta kwana ba"
"Eh Alhamdilillah, na ji daɗin hakan ma, ai da gani ku ke yi Nana tana sane, duk abubuwan da yake faruwa da ita, tana sane ita ta yi wa kanta ƙarya take yi. Yanzu idan ma ƙarya take idan ma gaske ne, ai kwa gani, kuma wallahi na ji wata magana a unguwa ta cin zarafin Nana, ko yi mata ƙage wallahi sai na saka an ɗaure mutum igiya ta yi saura"
Jamila ta ce "Mama dan Allah rabu da shi, kar ya yi miki rashin kunya"
***
Nana kuwa rarraba ido kawai take yi a hanya, tana ta ƙoƙarin tuna wasu abubuwa a ƙwaƙwalwarta, amma abu ya gagara. Abin da take iya tunawa, kawai hango Suwaiba tana zubar da jini, amma ta kasa tuna takamaiman yadda aka yi ta ga jini a jikin Suwaiba.
Gaba ɗaya ta nemi kuzarinta ta rasa, jikinta yayi sanyi ƙalau, ko ƙwaƙwƙwaran motsi, sai ta yi da gaske take iya yin sa.
Sannu a hankali, ƙwaƙwalwarta ta fara fassara mata maganganun da ta jiyo Baba yake yi. Wai ana idar da sallar asuba, ya kira Saleh a waya ya ce masa wai idan akwai kuɗi a hannunsa, ya turo wani abu za a nema mata magani. Wani irin takaici ya kama Nana, sam Baba ba ya gudun abin kunya da duk wani abu da zai zubar musu da kima.
"Atine, ai yakamata tun yanzu yaron nan, ya fara ƙoƙartawa shi ma, tun da dai aurenta zai yi, duk wata hidima da za a yi mata, ya saka hannu a yi da shi"
Babu kunya Yaya Atine ta ce "Gaskiya ne, ai kamata yayi ace ya ɗauke maka wasu nauye-nauyen".
Baba ya ce "Sosai fa, kuma kin ga hakan zai ƙara tabattar masa da gaske zan ba shi aurenta. Ai mu na dawowa daga gurin maganin nan kawai iyayensa su zo a wuce gurin"
Nana ta rintse idanunta, tana fatan bacci ya ɗauke ta, ba ta tunanin akwai wani wanda zai aureta ta yi mutunci a idonsa, da irin wannan halin na Baba, na son jinginawa wani ɗawainiyar da shi yakamata ace ya yi abarsa.
Sun sha doguwar tafiya sosai, kafin su isa wani surƙuƙin ƙauye, sai da suka yi nisa sosai da sosai, suka daina ganin gidaje. shige da ficen ababen hawa ne, ya sanya suka tabattar da akwai mutane a gurin, domin kuwa hatta kwalta babu a gurin, sai uwar zangarniya.
Yanayin surƙuƙin gurin, sai parking ɗin motar suka yi a bakin hanya, suka saukko domin takawa su ƙarasa, sai dai ƙafar Nana ta ƙi takuwa sai ma lanƙwashewa da ta yi, kamar mai shan inna.
Sun daɗe a gurin, Nana ta kasa taka ƙafafuwanta, sai da ƙyar ta ɗan saki, ta takawa a hankali.
Tun da suka doshi hanyar da aka nuna musu, aka ce a nan gidan mai maganin yake, Nana take ganin garke garke na Raƙuma su na fitowa daga hanyar, jajaye da farare. Yaya Atine ce ta riƙe ta suke tafe a hankali, saboda da ƙyar take taka ƙafafuwanta.
Nana ta ce "Yaya Atine dama akwai baƙin raƙumi?"
Yaya Atine ta ce "A ina?"
"Ga su nan su na ta wucewa, ba ki gansu ba?"
Yaya Atine ta ja ta tsaya ta ce "Kai Gaddafi, ku na ganin raƙuma ko kuma nima abin nata ne zai shafe ni, nice ba na ganinsu?"
Baba ya ce "Raƙuma kuma a ina?"
"Yo ai ji na yi tana zancen baƙin raƙumi, ni kuma ko kofato ban gani ba balle raƙumi. Kai zo ka riƙe 'yar ka, kar na gano abin da ba shikenan ba"
Nana na jin haka, ta zame hannunta daga na Yaya Atine ta ci gaba da takawa a hankali.
Daga nesa suka hango gidan, mutane na ta shiga su na fita.
Ja da baya Nana tayi da sauri tana kare fuskarta.
Baba ya ce "Me kuma ya faru?"
Cikin damuwa Nana ta ce "Baba wai ba ka gani, baƙin raƙumin nan ne yake feso mini wuta fa"
Cikin takaici Gaddafi ya ce "Dan Allah Baba ku daina biyewa yarinyar nan, ku zo mu ƙarasa."
Su na tunkarar gidan, amma raƙuman na ƙara yawa, Nana ta fahimci ita kaɗai take ganinsu, su ba sa ganinsu.
A haka har suka ƙarasa ƙofar gidan, Ko da su ka shiga gidan, jikin Nana ya hau rawa, sai dai hakan bai hanata gode wa Allah da halin da ga tsinci kanta. Saboda yadda ta ga wasu a cikin mari su na hauka tuburan, ban da masu ciwon galhanga, shan inna da sauransu.
Ɗaki ɗaki ne a gidan, ma'aikatan gidan, duk su na sanye da jajayen kaya, kamar ma'aikatan jinya a asibiti.
Hankalin Nana yayi mugun tashi, da ta ga ana yi wa wasu daga cikin marasa lafiya sakiya. A saka kibiya a cikin magani, sannan a sakata a cikin wuta, sai ta yi ja sannan a soka a gurin da yake da larura.
Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, hankalinta yayi mummunan tashi.
Su na ƙoƙarin shiga ƙofar da za ta sada su, da ainihin gurin da mai maganin yake ganin marasa lafiya, idon Nana ya sauka a cikin na ɗaya daga buzaye ukun da suke ƙoƙarin fitowa daga cikin gurin.
Ji ta yi tamkar an watsa mata wuta a cikin idanunta zuwa jikinta, ƙara ta saki ta dafe kanta ta faɗi a gurin. Taku uku ya yi, ya ja ya tsaya ya waiwaya ya kalli gurin da Nana ta faɗi. Habu ya kama hannunsa suka yi waje.
Ma'aikatan gurin, su ka zo su ka ɗaga Nana, su ka shiga da ita gurin mai magani, su Baba su na biye da su.
Mai maganin ya fito sanye da rigar fatar damisa, sai warki a ƙugunsa idanunsa Jawur tamkar garwashi, baƙi ƙirin da shi.
Da sauri ya ƙarasa kan Nana, tamkar likitan da aka kawowa mara lafiyan da yake buƙatar agajin gaggawa. Ya sunkuya a kanta yana kallonta sai kuma ya ɗago a gigice ya ce "Baushe, maza bi buzayen nan ka dawo da su, wataƙila ga makarin na sa ciwon a nan, maza hanzarta kar su tafi"
Su Baba dai su ka tsaya sororo su na bin sa da kallo.
Nana kuwa tari ta hau yi, tamka ƙirjinta zai buɗe, ganinta ta yi a cikin ƙura, ko tafin hannunta ba ta iya gani saboda yadda ƙurar ta turnuƙe gurin. Bayan wani lokaci ƙurar ta lafa, ta ɗaga kanta ta na kallon gurin, ita kaɗai ƙwal a cikin sahara.
Waige-waige ta hau yi, sai dai babu tsammani ta ga mutum a tsaye a bayanta, sanye da baƙin rawani da shigar fararen kaya na buzaye, hannunsa riƙe da akalar raƙuminsa.
Sai dai duk ƙoƙarin Nana a kan ta gane kamaninsa, abu ya gagara fuskarsa a rufe take da rawani.
Miƙa mata hannunsa yayi, mai ɗauke da dogwayen yatsu. Duk da a tsorace take, ta fara takawa a hankali, har ta ƙarasa gurin da yake, ta miƙa masa nata hannun.
Yana kama hannunta, ta ji an zuba mata ruwa mai matuƙar sanyi a jikinta. Doguwar ajiyar zuciya ta sauke, tare da buɗe idonta.
Su Baba ta gani a zaune tsuuruu, kamar mara gaskiya a hannun hukuma.
"Sannu Nana Asma'u" mai maganin ya yi maganar cikin sakin fuska.
Nana ta tashi zaune, ta koma jikin Baba, tana jin yadda haryanzu jikinta yake a sanyaye.
Mai maganin ya zura mata ido, sannan ya sake murmushi ya ce "Manya gatan wasa, wa ya isa ja da ku, idan ba wawa ba? Tuba nake uban duƙusa" dubawa Nana take ta ga da wa yake.
Ya ci gaba da cewa "Asma'u, ki na ganin wani mutum a mafarki, ku na magana ko?" Nana ta yi shiru ba ta ce komai ba.
"Za ki iya tuna me da me yake ce miki?" Still ta yi shiru ba ta yi magana ba.
Ya sake murmusawa ya ce "Malam, gidanmu wanzamai ne, na kuma yi ƙarfa-ƙarfa a kan farauta, duk da mahaifiyata sun gaji farauta . Na daɗe ina hatsabibanci, har na zo na fara bayar da magani, na daɗe ban ga abin mamaki ba kamar yau. Aljanin da yake ɗawainiya da yarinyarka hadiminta ne, tun zamanin kakaninka ai 'yan bori ne. Kuma tun daga kansu ba a kuma samun haihuwar mai irin tauraronta ba, sai da aka haifeta dan haka dole ya yi mata hidima, ita kuma taƙi yadda shiyasa yake ta azabtar da ita. Duk ba wannan ba yanzun nan aka tafi da wani buzu, shi dama na gaya musu ba ni da maganin larurarsa, sai dai a shigowar ku, na ga wani abin mamaki da na daɗe ban gani ba, ina kyautata zaton wataƙila maganin nasa ciwon na da alaƙa da nata.
Kodayake ba a kan wannan gaɓar muke ba. Yanzu ita Nana Asma'u za ku bar ta a nan, sai bayan kwana goma sha huɗu zaku dawo, aljaninta sai dai ayi sulhu da shi idan aka takura shi, ba ita ba ni kaina zai iya halaka ni."
Kallonsa Nana tayi, gaba ɗaya maganganun mutumin nan ko gaske ne, mushiriki ne shi ma, jira take ta ji me su Baba za su ce, ko me za ayi ba za ta yarda a bar ta a gurin nan ba.
Baba ya ce "Mu tafi mu bar ta har mako biyu kuma, itakaɗai?"
Gaddafi ya ce "Ba magani ake mema ba? Ma samu mu huta kwana biyu mu ma, da wannan tamɓelen da take yi ai gara a batta ɗin, Allah ya kaimu makwanni biyun"
Yanayin Baba ya nuna ba haka ya so ba.
Nana ta buɗe baki za ta yi magana, ta ji kamar an saka dutse a maƙogwaronta, tayi tayi amma magana ta gagara.
Ta dage iya ƙarfinta ta miƙe tsaye, amma jiri ya kwashe ta, tana ji tana gani, masu jajayen kayan nan, suka zo suka ɗauke ta, tana fizge-fizge tana komai aka kaita wani ɗaki aka kulle.
Littafin BUZU 1k ne a telegram.
0069685771
Aisha Adam
Stanbic ibtc
Sai shaidar biya
https://wa.me/2348081012143
Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807
BUZU
AISHA ADAM AYSHERCOOL
YOTA/002
(Bright pens 3rd batch)
P12
Imaran tun yana jiran dawowar su Baba da daɗin rai, har ransa ya gama ɓaci, zuciyar sa ta din ga tafasa.
Mama kuwa tuni ta din ga kiran 'yan uwanta tana gaya musu, abin da ya faru da Suwaiba. Suwaiba kuwa ko a jikinta, sabgoginta kawai take yi. Ƙarshe ma da yamma, ta sha wanka za ta fita zance, ta ga turaren nan a kan kayan Nana, ta ɗauki abin ta ta ƙara fesawa ta fice.
Bayan sallar magariba, Imran yana zaune a waje, sai ga taxi har ƙofar gidansu, su Baba sun dawo.
Bai motsa daga gurin da yake ba, sai da ya ga duk sun fito daga motar, amma babu Nana.
Su na shiga gida, ya tashi ya bi bayansu.
"Wai ina Nanan take? Ya ku ka dawo babu ita?" Daga Baba har Gaddafi babu wanda ya kula shi.
Ransa ya fara ɓaci ya ce "Baba ka yi magana, ina ku kai mini Nana?"
"Tana gidan Atine" ya bashi amsa a gajiye, saboda sun kwaso gajiya.
"To me yasa za a kaita gidan Yaya Atine? Me yasa ba ku dawo da ita gidan nan ba?" Ganin Baba ba zai ba shi cikakken lokacinsa ba, balle ya yi masa bayani, kawai ya fice ya nufi gidan Yaya Atine.
Yaya Atine, ta mimmiƙe tana cin tuwon dare, saboda wahalar da suka sha.
Kamar an jefo Imran ta ji sallamarsa.
Ta amsa masa, ba tare da ya ko gaisheta ba ya ce "Ina Nana?"
Cikin rashin fahimta ta ce "Wace Nanan?"
"Baba ya ce mini tana gidan nan?"
"Kuma saboda rashin ɗa'a, ko gaishe ni ba za ka yi ba, ka zo kana tambayata wata Nana, to mun sayar da ita"
Ya ce "Yi haƙuri, a ruɗe nake ne"
Yaya Atine ta ce "Ba wani haƙuri da zan yi, gidan uban wa ka tafi tsawon shekarun nan?"
Duk da ya fara ƙuluwa ya maze ya ce "Kudu na tafi neman kuɗi, tana ina?"
"Kai ban sani ba, ni ba ta gidan nan, ka koma ka tambayi uban naka"
Imran ya kalle ta ya ce "Kamar yaya? Shi fa ya ce mini tana nan"
"A'a tana gidan mai magani, sai nan da mako biyu za aje a taho da ita"
Ashar Imaran ya yi ya ce "Wane irin magani ne, sai an kai mutum a baro shi, to ai ko asibiti ana barin ɗan jinya, balle wani shashasha da bai shiga aji ba, aje a ajiye masa yarinya shi ba muharamminta ba".
"To ai ubanka za ka je ka yi wa ba ni ba. Kuma ba fin mu hankali da tunani ka yi ba, gurin akwai ma'aikata mata da suke kula da mata marasa lafiya " Imran ji ya yi kamar ya kifa wa yaya Atine mari, wannan ai ganganci ne da rashin hankali.
Takalmansa ya shura, ya fita daga gidan zuciyarsa kamar ya fashe saboda takaici.
Gida ya koma cikin takaici, sai dai ya tarar Baba baya nan.
Labarin mutuwar malam Auwal ya karaɗe ciki da wajen unguwar su Nana, saboda an san shi sosai, saboda ya kan ja salla a masallatai daban-daban.
Ga koyarwar da yake yi a islamiyya, kowa yayi masa shaidar mutumin kirki ne shi. 'yan unguwa suka yi alwashin tsayawa tsayin daka, gurin bibiyar jam'i an tsaro da tabattar da an kama waɗanda suka aikata masa haka.
Cike da jimami Nasir ƙanin su Nana yake ta nanata mutuwar malam Auwal, ya ce "Allah sarki Nana, ko ya za ta ji idan aka ce mata malam Auwal ya mutu an kashe shi?" Duk da Baba yana cike da takaicin wasa da hankali da malam Auwal ya yi masa, na ƙin fitowa ya auri Nana, amma hankalinsa ya tashi bayan dawowarsu daga kai Nana gurin mai magani ya samu labarin mutuwar.
Yana tsaka da jimamin mutuwar, ana tattaunawa a masallaci bayan sallar isha'i, Nasiru ya zo ya kira Baba ya ce ana nemansa a gida.
Ko da ya je gida, ya tarar an daddane Suwaiba, tana ta kurma ihun Nana na sha mata jini.
Cikin kuka mama ta ce "Ka gani ko? Kalli halin da Suwaiba take ciki, wallahi an cuce ni ban yafe ba, kuma wallahi ko ka ɗauki mataki ko ni na ɗauka. Dan baƙin bala'i a gaban saurayi ta faɗi tana wannan kururwar fa"
Cike da damuwa ya ce "Wai Rabi ya ki ke so na yi, ki na gani domin neme wa Nana magani, a can gurin mai magani na baro ta, kuma na ce a tafi da Suwaiban ki ka ƙi yarda"
"Ni wallahi ka san yadda za ka yi, dan ba zan yarda a kashe mini 'ya ba"
Imaran ne yayi sallama, yana watso takalmansa da suka tsinke ya ce "Yauwwa Baba na je gidan Yaya Atine, ta ce Nana ba ta gurinta wai a gidan mai magani aka baro ta. Baba ko fa asibiti ana bar wa mutum ɗan jinya, ya za ayi a kaita gurin da babu idon wani nata da sunan neman magani? Ina ne gurin da aka kaita gaskiya zuwa zan yi na ɗaukkota"
Baba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 13