babu wani a gurin nan, kuma ga wanda ya kawo ƙarar ana nemansa ruwa a jallo"
Baba ya ce "Ai bayan tafiyar ku ta dawo"
Gaddafi ya ce "Ta dawo kuma? Ni fa har gurin da muka ajiye mota muka shiga, bamu ga gidan nan ba"
"Wallahi ta dawo, tana cikin gidan nan"
Sai da aka tafi tare da Nana har police station, aka yi rubuce-rubuce sannan aka saki Gaddafi suka taho gida. Tana jin yadda Gaddafi yake rantsuwa shi da sake shiga duk abin da ya shafe ta har gaban abada.
Kwanaki biyu suka shuɗe, Nana ko rintsawa ba ta iya yi, sai da ta gwammace dama a gidan sarkin baka ta yi zamanta.
Mama kuma ba su fasa faɗa da Baba a kan lallai ya nemi in da Nana zata zauna ba. Dama normally ma ba abinci ake ba ta ba sai an ga dama, yanzu kuwa tun da ta dawo Baba ne ma ya kan bayar a sayo mata kunu ko awarar naira ɗari, shi ma ba iya ci take yi ba, balle kuma yanzu.
Dama ba su fiye shiri da Suwaiba ba, sun fi shiri da Jamila, sai dai a wannan karon tun da ta dawo, babu wanda yake shiga sabgarta, hatta ɗakin da take ba sa shigowa. Tana jin yadda idan aka yi baƙi, ko aka zo duba Nana mama take muzanta ta, tana cewa aljanunta ne suka halaka Auwal, wanda ya fasa aurenta kuma suke ƙoƙarin kashe Suwaiba.
Nana tana ganin yadda wasu daga hudar jikin Nana suka fara warkewa, sai dai wasu ba su fasa zubar da jini ba.
Turaren da Jamila ta kawo mata ta gani a kan tagar su, an feshe fiye da rabi. Ita dai ta san turaren nata ne, amma ta kasa tuna yadda aka yi ta same shi.
Cikin dare ta kasa bacci, ta tashi zaune ta haɗe gwiwoyinta ta kifa kanta, har yanzu gani take kamar za ta farka daga bacci, ace mata Auwal bai mutu ba.
Kwanakin nan da aka ɗauka kuma, ta gazagata da gaske malam Auwal ya rasu. Tana so ta je ta yi wa mahaifiyarsa ta'aziyya amma ba ta sani ba ko ta santa, ga kuma surutun da ake ta yi a kanta.
"Ya Allah ka yafe mini rashin tawakalli da na yi, na bari ɗimuwa ta sanya ni yin abin da bai kamata mai imani ya yi su ba. Ya Allah Auwal bawan ka ne, mai kwaɗaitar da al'umma bin ka da manzonka, mai hidima ga addini, mai ƙaunar Manzon Allah ma'abocin Alqur'ani ya Allah ka yafe masa ka yi masa rahama" ta yi maganar kuka yana ƙwace mata.
Dariyar da ta ji ne, ya sanya ta ɗaga kanta. Ta ganta a zaune jikin wata bishiyar tsamiya, ita kaɗai ƙwal a daji rana tsaka.
"Iska na wahalar da mai kayan kara, yanzu duk saboda soyayyar ki ka koma haka? Kamar gaske mutumin nan ya riga ya mutu, kuma ba fa wai son shi ki ke yi ba, shaƙuwa da tausayi ne a tsakanin ku" tashi ta yi tsaye a fusace tana waiwayen in da za ta ga ƙaisar. Domin kuwa sai a lokacin ta tuna ya nuna mata mutuwar malam Auwal, kuma ya taɓa alwashin kashe Auwal ɗin, amma da ta tashi daga baccin, a wancan lokacin sai ta manta da komai.
"Kai ne ka kashe shi ko?"
"Idan zan kashe shin ne zan soka masa wuƙa? Kwanansa ne ya ƙare ba zan iya kashe shi ba ai, ni ba na kisan kai sai an dame ni, kamar yadda Sarkin baka ya taɓo ni, nima na taɓa shi wataƙila na karya alkadsrinsa wannan maitar wataƙila ita ce ajalinsa"
Cikin matsananciyar damuwa Nana ta ce "Kenan kashe shi za ka yi? Wai kai wani irin halitta ne azzalumi mara imani? Duk wanda na mu'malanta sai ka cuce shi?"
Ƙaisar ya ce "A'a ni ba na taɓa kowa sai ya taɓa ni. Ba ya fara lallaɓa ki ki sadaukar masa da ni ba? Ba ki yi tunanin ta wace hanya zai yi amfani da ni ba, kawai saboda ki rabu da ni, ki ka amsa masa kuma ke ba ki san ya ake sadaukarwar ba, ki ka amsa. Tabbas ya shiga gona ta ni kuma na shata masa layi" yayi maganar yana bayyana a gabanta.
Cikin kuka Nana take faɗin "Allah ya yi mini maganin ka ya saka mini, idan ka fi ƙarfina ba ka fi ƙarfin Allah ba ai. Kuma kana kallo aka kashe malam Auwal ba ka yi komai a kai ba, banda zalunta ta da azabtar da ni ba abin da ka ke yi"
Ya yi murmushi ya ce "Zuwa islamiyyar ta ki ba shi da amfani ashe, ai idan abin da ya fi haka za ayi masa ba ruwana, azabar da ya din ga saka ki na bani, na yi farin ciki da mutuwarsa sosai, ki roƙa masa Allah gafara, dan wasu lokutan idan damuwa da gajiya ta yi masa yawa, yana shan ƙwayoyin gusar da hankali ya yi bacci mai tsawo. Sannan akwai tarin hotunan 'yan mata a wayarsa, ke har ma hirar tsakar dare a dandalin sadar da zumunta yana yi na rage zafi da 'yan mata..
"Ƙarya ka ke yi, wallahi ƙarya ne ba dai malam Auwal ba... Nana ta katse shi cikin ƙarji.
Ƙaisar ya ce "Ai dama ban ce ki yarda ba, ku bil adama ma akwai wanda ya kai ku ƙarya ne. Sarkin baka kuma zan kasa zan tsare sai na ƙarasa shi, saboda ba neman sadaukar masa da ni ne kawai ya sanya na yi masa wannan hukuncin ba, wani gagarumin laifi ya tafka mini da sai na ga bayansa"
"Dan Allah kar ka kashe shi, mutumin kirki ne, kuma mutane wasu sun yi imani da maganinsa, marasa ƙarfin da ba za su iya jelen Asibiti ba, yana taimaka su babu ko kwabonsu"
A hankali ya fara zagaya Nana ya ce "Gaba ɗaya halayyarki ba ta da saiti, ke gaba ɗaya ba a gane inda ki ka dosa, kin gama kushe abin da yake yi, yanzu kuma kin ce a ƙyale shi, mutane na amfana. Idan ya mutu sai ki je ki gaje shi, tun da dama ya kai ki ya nuna miki magunguna. Kwanta ki yi bacci kafin ƙwaƙwalwarki ta samu matsala, ki shirya tarar sabuwar matsalar da take tunkarar mu daga ni har a dalilin zuwan ki gidan wannan mutumin.
Za ta yi magana kawai ta daina ganin komai, sai juyi da ta yi a ɗakin da take, cikin magagin bacci. Ƙoƙarin yinƙurwa take yi ta tashi, amma wani irin bacci mai kama da fita daga hayyaci ya yi awon gaba da ita.
Bayan kwanaki uku, jami'an tsaro ba su fasa zarya a gidan su Nana ba, a kan neman Imran. Ga fitina da mama take yi a kan zaman Nana, abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, sai da maƙwabta har da mai unguwa su ka shiga lamarin, aka din ga rarrashinta, aka din ga janyo mata ayoyi da hadisai, a kan tauhidi da ɗayanta al'amura. Nauyin manyan mutanen da suka haɗu, ya sanya ta ce ta haƙura Nana ta zauna, zuwa lokacin da za a ɗaura mata aure.
Nana gaba ɗaya lamarin da yake faruwa a gidan na su baya gabanta, har da batun ɗaurin aurenta da ake yi, sati biyu masu zuwa. Rashin samun Abincin nan da ba ta yi, ya fara damunta dan sannu a hankali mutuwar malam Auwal ta fara sakinta, sai dai duk lokacin da ta tuna shi sai ta yi masa addu'a.
Tana zaune a tsakar gida da yamma, Suwaiba na tsakar gida tana ta jin kaɗe-kaɗe a wayarta, kanta ko ɗan kwali babu.
Bararojin nan ce a zaune a kusa da Suwaiba, jikinta duk ya ciko ta warke, ta zura kanta kusa da Suwaiba tana leƙa wayar ita ma.
Nana ta yi shiru tana kallon Suwaiba, tana son ta yi magana, amma tana tsoron abin da ka iya biyo baya.
"Ke Suwaiba, tashi ki shiga ɗaki, dan jaraba kalli yadda ta zura miki idanu, kar ta ƙarasa tanɗe ki" Mama ta yi maganar cikin haɗe rai.
Suwaiba ta kashe wayar, ta yinƙura ta tashi, aikuwa bararojin ta haɗe rai, kafin Suwaiba ta kai ɗaki, ta hankaɗeta ta faɗi ƙasa.
"Kin gani ko? Abin da nake faɗa ko? Dama na ce ba zan zauna da yarinyar nan ba, gashi dai sai ta kashe mini 'ya hankalinta zai kwanta"
Kawar da kai Nana ta yi gefe, ta ci gaba da zancen zucinta, dan ba hatsaniyar gidan ce a gabanta ba yanzu.
Da daddare Nana ta tsaya tana ƙarewa jakar da ta zo da ita daga gidan sarkin baka kallo, tun da ta zo da ita, ba ta buɗe ta ga abin da yake cikin jakar ba.
Yau ma kwanan ihu Suwaiba ta yi, cikin ikon Allah Nana kuma, tun da ta dawo ba ta ihun nan da take yi da daddare sai Suwaiba.
Washegari Monday, Nana ta shirya domin jarraba zuwa makaranta, duk da ta san za ta sha bala'i gurin director, na rashin zuwanta tsawon lokaci, amma ta tafi cike da fatan Allah ya sassauta zuciyarsa ya sanya ya karɓe ta, ya biya ta Albashinta, kuma ta ci gaba da aikinta.
Sai dai ta tarar da saɓanin abin da take ta fata, domin kuwa ta tas director ya yi mata, ya ci zarafinta ya ba ta takardar kora. Jiki a sanyaye ta karɓi takardar ba tare da ta buɗe ba ta ce "To sir salaryana ka taimaka ka bani na last month"
"Ba za a bayar ba, shi ma last month ɗin wani zuwan kirki ki ka yi, kullum ba ki da lafiya"
Nana ta sake marairaicewa ta ce "Dan Allah ko rabi ne, ka taimake ni"
"Ba zan bayar ba, asarar da ki ka janyo mana, na wahalar neman wata malamar a kuɗinki" Nana ta ji zafin korar da aka yi mata, duk da ta san laifinta ne, amma dai yakamata a bata hakkinta.
Ko sallama ba ta yi da sauran malaman ba, dama ba cikinsu take shiga ba, saboda yadda suke yi mata kallon Nanny kawai.
Dama da ƙafa ta zo makarantar, dan haka yanzu ma ba ta da kuɗin abin hawa, da ƙafarta ta miƙi hanya.
Horn ɗin da aka ishe ta da shi ne, ya sanya ta tsaya, ta waiwaya. Motar baban Muhsin ta gani. Ya ƙaraso gurin da take ya ce "Anty kwana biyu lafiya kuwa? Muhsin na ta rikici ba kya zuwa makaranta shi ba zai zo school ba"
"Wallahi na ɗan yi rashin lafiya ne"
Cikin tausayawa ya ce "Eyya Allah ya sauwwaƙe, mun yi magana da director ya ce sallamarki zai yi, ba yadda ban yi ba, amma ya ƙi yarda ya haƙura" Nana ta yi guntun murmushi da iyakarsa laɓɓanta ta ce "Ba wani abu, rabona ne ya ƙare a gurin kawai".
"Eyya babu daɗi, to hawo na sauke ki a gida"
Ta girgiza kai ta ce "a'a ba komai na kusa ƙarasawa ai"
"A'a da saura ai na sani, hau dan Allah" ya yi maganar yana buɗe mata ƙofar gaban motar" ta yi bismillah ta hau.
"Wallahi ban ji daɗin sallamar ki da director ya yi ba, ki na da ƙoƙari matuƙa gaya." A wannan karon ma murmushin dai ta yi tana wasa da yatsun hannunta.
"Ki bani takardun ki, na nema miki admission a school of legal studies, ko koma makaranta mana"
Ta girgiza kai ta ce "A'a na gode sosai"
"Me yasa? Karatun ne ba kya so? Nana ba zan cutar da ke ba. Ba na wasa da duk abin da ya shafi yarana, yanzu haka Muhsin ne ƙarami, amma duk lokacin da nake gari ni nake kai shi makaranta, saboda yana son hakan. Da ɗa da dukiya ba ayi musu mugunta ba ka san wa zai amfane su ba. Amma ki yi tunani idan kin amince zan samar miki admission ba, ko ba duka ba zan ɗauki ɗawainiyar karatun naki."
Cikin girmamawa ta ce "Ka na cikin mutanen da ba zan manta da su ba a rayuwata, ba zan so ka ɓata kuɗin ka ba, ina ga nan da wani ɗan lokaci za a ɗaura mini aure, kuma garin zan bari gaba ɗaya"
"Allah sarki, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya. Bani wayar ki na saka miki lambata, idan lokacin bikin ya yi ki sanar da ni, zan halarci ɗaurin aure in sha Allah"
Nana ta girgiza kai ta ce "Ba ni da waya ai, ka yi mini addu'a na gode sosai da sosai. Sannan a cewa Muhsin ya yi karatu da kyau, Allah ya yi masa albarka" jiki a sanyaye yake kallon Nana, haka kurum take ba shi tausayi gaba ɗaya yanayinta ya nuna akwai labari mai ban tausayi a tattare da ita.
Ya yi parking daidai gurin da take sauka, tana kiciniyar buɗe ƙofar motar, ya miƙa mata kuɗi, ya ce "Ga wannan ba yawa, Allah ya baki wani abin yin." Za ta yi magana ya girgiza mata kai. Ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode sosai da sosai" ya daɗe yana kallon yadda take tafiya da ƙyar ta shige cikin layuka.
*****
Malamin Hajiya Sa'a yana zaune, ya duba wurin da yake gabansa, ya kalle ta ya ce "Hajiya a wannan karon ma babu sa'a fa, 'yan aikenmu sun makara, domin fafur sarkin baka ya hana yarinyar nan, ƙarshe ma ya mayar da ita gida, ya ce mu je can mu ɗauke ta, yanzu haka tana can"
"Kai wannan wace irin masifa ce? Ni an taɓa bani aiki mai wahalar wannan ma kuwa?"
Ya yi dariya ya ce "Ai na gaya miki hatsabibin aljani ne a tare da ita, kuma mutane irinmu, mu na burin mallakar aljani irinsa, domin kaf jinsin babu aljani mai tsananin juriya da kasada kamar sa, tun da sarkin baka ya mayar da ita ba tare da ya mallaki aljanin ba, na san akwai matsala. Yanzu ki bar wannan mu jingine ta zuwa wani lokaci kaɗan. Yanzu ga wani aiki mai ɗan sauƙi, 'yar aikenmu na kan waccan yarinyar da ta yi amfani da turare kuma ta warke ma. Ki duba dangi wanda yake jininki ki samo yaro da bai wuce shekara biyar ba, a sadaukar mata da shi, domin ta ƙara samun kuzari zan sanya ta yi miki wani aiki"
Hajiya sa'a ta ɗan yi shiru ta ce "Akwai ɗan wa na, ba zai gagara ba"
"To shikkenan, tashi ki je, Sa'a na tare da ke Hajiya Sa'a tun da ki na bibiya ga duk abin da aka saka ki. Ki je za a sanar da ke lokacin da ake buƙata" tashi ta yi tana jin daɗin yabon da ya yi mata.
*****
Nana da ta koma gida, ta tarar an kai Suwaiba asibiti, daga gurin masu magani, wai jikinta babu jini an riƙe ta a asibiti.
Sam Nana ba ta yi gigin bin su ba, ta dai yi wa Suwaiba Addu'a. Ta duba kuɗin da baban Muhsin ya bata dubu goma cif. Addu'a ta din ga kwarara masa da shi da zuriyarsa, saboda ta ji daɗin kuɗin nesa ba kusa ba.
Da yamma Ummi ta zo gidan, ta tarar da Nana a gida.
"Nana ke ba ki je asibiti duba Suwaiba ba?"
"Hmm kin san da yadda ta yarda nake zaune a gidan nan ne ma? Su na cewa ina ƙoƙarin kashe Suwaiba, wai ina sha mata jini.. sauran maganar ya kakare mata saboda kukan da ya kufce mata mai taɓa zuciya.
Jiki a sanyaye Ummi ta ce "Yanzun ma da na je, su na ta maganganu amma dan Allah ki manta da su. Ke dai Allah ya baki lafiya. Na zo ne a kan batun shirin bikinki, Baba ya ce ba za ayi taro ba. Amma ko ba za ayi taro ba ai kya fara gyaran jiki dai ko?"
"Me zan gyara? Ni dan Allah ki rabu da ni"
Ummi ta ce "Kamar yaya na rabu da ke? Aure fa za ki yi."
"Auren jeka na yi ka ba? Ai kun san ba so nake yi ba, amma babu yadda na iya ne, shi ne sauran mafitar da ya rage mini"
"Au Nana ba za ki daina maganar ba kya so ɗin nan ba ko? Ke ba kya tausayin kanki da wannan wahalar da ki ke ciki ko? Ki je ki ki yi ta yi, sai mutum ya tausaya miki, idan ki ka tafka wani rashin mutuncin zai gane ke ba abar tausayi ba ce. Ki je ki yi abin da ki ka ga dama, ni na cire hannuna a kan ki"
"Allah yana tare da ni, na san shi ba zai cire hannu daga kaina ba" Nana ta yi maganar hawaye na gangarowa daga idanunta.
Ayshercool
08081012143
Alhamdilillah free pages sun kammala, masu buƙatar ci gaba su na iya tuntuɓata a kan lambar wayata.
1k ne a telegram
Via 0069685771
Aisha Adam stanbic ibtc sai shaidar biya ta 08081012143
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 13