ta samu mahaifiyarta ko a waya, Baba ya datseta, har yana nema ya yi mat baki.
'meye na damuwa ma, matar da ko in da ku ke ba ta zuwa, ta ga halin da ku ke ciki, balle ki gaya mata halin da ki ke ciki, ta saka ki a addu'a, ko kuma t nema miki magani' wata zuciyar tayi mata tunin, abin da ba ta so, domin in dai tana ire-iren waɗannan tunanin, ta na jin zafin mahaifiyarta a ranta.
"Ke Nana, zo ga waya Atine za ta yi magana dake" maganar Baba ta dawo da ita daga duniyar tunani da ta lula.
Gabanta ne ya faɗi, wata sabuwa in ji 'yan caca, ba ta ƙaunar duk abin da zai haɗata da matar nan a rayuwarta.
Ba tare da ta amsa ba, ta tashi ta fita.
Baba ya miƙa mata waya, ta karɓa hannunta na rawa ta saka a kunneta, ta yi shiru.
"Ke ma'u ki na ji na?"
"Eh" ta amsa a cunkushe.
"Dan ubanki sai ki yi mini shiru, ko gaishe ni ba za ki yi ba, har kya yi wa mutane ƙaryar iskancin aljanu, mu da a ka yi gadon bori a gidanmu.
Nana ta yi shiru, tana mamkin yadda jahilci, ya sanya yaya Atine alfahari da harkar shirka, da shi ne musababbin gadar mata da bala'i, kamar yadda mutumin da take mafarki da shi, yake iƙrari.
"Ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni, ranar asabar ki yi kuɗin mota, ki taho gidana, akwai gidan wani mai magani da zan kai ki. A baki maganin aljanu da na farin jini, aure dole ki yi shi babu fashi, ko shi wanda ba kya so ɗin ko wani daban. Ke wannan baƙin jinin kamar an jiƙa hatimin jaɓa an baki, daga nonon babarki ki ka shawo shi. Mu zuriyarmu farin jini ne da su wallahi, babu mai nauyin jini"
"Yaya atine, idan ni a nonon uwata na sha, su suwaiba a naki nonon suka sha? Tun da Uwar tawa ba ta nan, menene na sakota a zancen ki, koma wani bala'in ne ya same ni, ba duk a dalilin shirka da iyayenku suka yi ba ne, da har ki ke alfahari da ita" ita kanta Nana ba ta san yaya aka yi, suke fita daga bakinta ba, saboda yadda ranta ya ɓaci zuciyarta take tafasa fiye da kima.
"Ma'u ni ki ke gaya wa haka?"
Gaddafi ne ya yi kan Nana, amma Baba ya tare shi, ya ce "Rabu da ita, ka na taɓa ta babu lallai, mu yi bacci mai daɗi a gidan nan, wataƙila ma ba ita ba ce ba, ƙyale ta"
Ta ajiye wa Baba wayarsa, ta koma ɗaki.
****
Cike da damuwa Auwwal ya koma gida, 'yar tsarabar da ya yi wa Nana, ya bawa ƙannensa, wani irin kishi ya addabi zuciyarsa, sai dai kuma yanayin kallon da ya ga tana yi wa wanda suke tsayen ne, bai gama gane kansa ba.
"Auwwalu" Umma da ta gama kasa gurasa da naman gabanta.
Ya kalleta ya amsa da "Na'am Umma"
"Magana nake son mu yi da kai ta fahimtar juna. A matsayina na mahaifiyarka".
Ya tattara mata hankalinsa baki ɗaya cike da ladabi.
"Ka zo mini da maganar aure, na ce maka ka dakata, ba yanzu ba tukuna. Karo na farko abin da ba ka taɓa yi mini ba, ka kai ƙarata wurin kawunka ƙanin mahaifinku. Ya zo har gidan nan baka nan, mun yi magana ta fahimta da shi sosai na kuma fahimce shi, har ya gaya mini ka gaya masa sunan yarinyar da gidan mahaifinta. Na ce masa to ya ɗan saurare ni. Na zo da kaina na saka ayi mini bincike, shi ma kawun naka na saka yayi ta nasa ɓangaren. To magana ta domin Allah ba zan yadda ka auri wannan yarinyar ba, ashe ita ce wadda ka ke bani labari mara lafiyar nan. 'yan unguwarsu sun tabattar da ba ta da wata matsala sai wannan iskokai, kuma ana kyautata zaton kakaninta 'yan bori ne, ni kuma gaskiya ba zan yadda a ɓatawa tsatsonmu suna ba, a sa a gada wa zuriya masifa ba. Dan haka mun gama magana da shi, shi ma zai neme ka ya kuma yi maka magana. Ya ce mini ya saka wani abokinsa ya yi naka hanyar tafiya Qatar ko Allah ya sa a dace da kyakyawar sana'a. Idan Allah ya sa ka tsaya da ƙafarka ka samu wata yarinyar mai kyakyawar nasaba da lafiya ka aura. Ba cin mutunci ba amma an ce yaran gidan ma galibi su ne suke ciyar da kansu, uban ba ya sana'ar komai, yarinya budurwa kuwa duk in da aka bari ta ciyar da kanta, ai an samu matsala. Dan haka ka cire ta daga zuciyarka" da ƙyar Auwwal ya haɗiye wani abu mai zafi da ya tsaya masa. Mama tana da gaskiya amma idan aka ce waɗannan abubuwan kacokan za a duba a ɗora mata laifi shikenan ba za a aure ta ba kenan? Nan aka zo neman auren ƙamwarsa aka ce ba za a aureta ba, 'yar mace ce, aka yi ta ɗauki ba daɗi kafin auren ya yiwu, amma Umma ta manta da wannan, ita ma tana hango aibun da ba ya cikin jerin abin da zai iya hana aure a shari'a a yanzu".
"Auwalu ka yi shiru, ko baka yarda ba zaka bujire ne?"
"A'a subhnallah, na amince Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi, amma Umma, da a bar maganar Qatar ɗin nan, idan Nana ce na haƙura amma..
Ta tari numfashinsa ta ce "Ai mun gama yanke hukunci, biyayya ce kawai taka Auwal"
Ya risuna ya ce "Shikenan Allah ya wuce mana gaba" ya tashi jikinsa a sanyaye ya bar ɗakin Umma, ya koma shagonsa.
Washegari da safe, ta je gaida Baba, bayan ta shirya za ta tafi wurin aiki, amma ya ƙi amsawa, ya ma tashi ya bar wurin.
Cikin damuwa ta koma ɗakinsu, ta ɗauki jakarta, ta kalli Jamila, da ke ta danna waya ta ce "Jamila, dan Allah ko kin san laifin da na yi wa Baba, ya ƙi amsa gaisuwata?"
Jamila ta ɗago ta ce "Lallai Nana, jiya da ki ka gaggaya masa magana, da shi da yaya Atine, ko har kin manta?" Shiru Nana ta yi, ta fara jin wata ƙara a cikin kanta, ta jingina da bango ta dafe kanta ta ce "Subhnallah"
Jamila ta tashi zumbur, ta ja da baya ta ce "Ya dai?"
"Wallahi Jamila, ban san ya aka yi hakan ta faru ba, da na tashi daga bacci, tunanin abin nake yi kamar mafarki ba a gaske ya faru ba, gaba ɗaya na kasa gane kan rayuwata, amma shikenan" kawai ta fita daga ɗakin, ta saka takalmanta ta fice.
A ƙofar makarantar, danƙareriyar motar ta yi parking, gilasanta baƙaƙe ne ƙirin, ba a ganin wanda yake cikin motar.
Yaro ne ɗan shekaru uku, ya fito daga cikin motar, ya zura hannunsa ya ɗaukko akwatin abincinsa, bai tsaya rufe motar ba ya nufo wurin da Nana take tsaye, yana washe baki cike da murna.
Sakin fuska ta yi, ta ƙarasa ta ɗauke shi, ta ɗaga shi tana murmushi. Sai dai yayi shiru yana kallonta, ganin alamun damuwa a fuskarta.
Ta shiga da shi cikin makarantar, ta fara tafiya da shi aji, in da take ajiyewa ɗaliban nata, kwanukan abincinsu, ta juyo za ta kama hannunsa su fita, amma ya ƙura mata ido.
Cikin harshen turanci ta ce "Muhsin let's go" (Muhsin mu tafi)
"Anty sorry" (Anty ki yi haƙuri) ya furta cikin damuwa.
Kallon sa tayi ta ce "Meyasa ka ke bani haƙuri?"
"Anty waye ya dake ki, ki ka yi kuka?" Ya faɗa cike da yarinta. Haɗiye hawayen da ke ƙoƙarin zubo mata tayi, ta ce "Atishawa na yi, mu tafi assembly ground"
Ko da suka je wurin assembly, an yi tsit ana addu'a, amma ɗalibanta na ganinta, suka fara tsalle, su na kiran sunanta.
"Anty, ko ki saka 'ya'yanki su yi mana shiru, ko ki ja su ku tafi" vice principal ya gargaɗeta. Cikin hikima ta sanya yaran yin shiru, yaran da take jin ƙaunarsu, har cikin zuciyarta.
Lokacin tashin yaran, duk an zo an ɗauke su, saura muhsin da ta biyewa, take yi masa lilo, kafin a zo ɗaukarsa.
Daga ita sai shi a harabar wurin nishaɗin yara, ta ɗora shi a wannan lilon ta sauke shi a wancan.
"Laa Anty kin ga Daddy" yayi maganar yana nuna bayanta.
Ko da ta waiwaya, mutumin nan ne da suka haɗu a ofishin director, ta sauke muhsin, ya nufi wurin babansa da gudu, ita kuma ta ɗaukko masa jakarsa da lunch box ɗin sa.
Har ƙasa ta risuna ta gaida shi, ya amsa cikin sakin fuska ya ce "Ya yaran naki, ya ƙoƙari?"
Ta amsa da "Alhamdilillah"
"Madalla mu na ta goɗiya, mun yaba da ƙoƙarin da ki ke yi wa yara, Allah ya saka da alkhairi"
"Amin na gode sosai"
Har zai juya su tafi ya ce "Amma yaran naki, sun tashi gaba ɗaya ko?"
Ta ce "Eh, sun tafi dama Muhsin ne ya rage, zan tafi nima"
"To mu je, sai mu sauke ki a hanya mana"
Nana ta ɗan yi turus ta ce "Bakomai na gode, ai babu nisa sosai"
"A'a bakomai, ai ni na ce muje sai mu ajiye ki a hanya" sai ta ji mutumin yayi mata kwarjini, ta ci gaba da jayayya da shi, amma har cikin zuciyarta ba ta so hakan ba sam.
Su na tafe a hanya, yana yi mata tambayoyi, kan matakin karatunta, da makamantansu. Ta din ga bashi amsa sama-sama a tsorace, dan haka kurum ta ji ya takura mata da yawa.
Sai dai ya din ga yaba mata, da ƙoƙarin da take yi da yara. A bakin titi ta ce za ta sauka, ya ɗauki kuɗi dubu biyar ya ba ta, ta ce masa ba zata karɓa ya ce ba zata sauka daga motar ba, sai da ta karɓa, sannan ya buɗe, ta yi masa godiya ta nufi hanyar gida.
A ƙofar gida ta hangi Baba, yana zaune a ƙasan bishiya, sai hamma yake yi, idanunsa jawur.
Ta nufi inda yake, ta je ta durƙusa tana gaishe shi. Da ƙyar ya amsa mata yana kawar da kai gefe. Ta ɗaukko dubu uku a kuɗin nan ta miƙa masa ta ce "Baba ga wannan, yaran da nake kula da su ne, baban wani ya bani" sai ya waiwayo da sauri ya saka hannu ya karɓa.
"Masha Allah, ai yakamata dai dama iyayen yaran nan, su din ga yi miki ihsani, tun da dai yaran nan na su da ki ke yi musu wahala, ba wani biyanki ake yi da kyau ba. Ko suturar jikinki suka kalla ai sun san mabuƙaciya ce ke, ba sai an ce su baki ba"
Nana ta basar da zancen, dan ba ta son ire-iren waɗannan zantukan na Baba, masu cike da son zuciya ta ce "Bari na shiga na shirya, na tafi Islamiyya"
"Zauna nan mu yi magana kafin ki shiga gidan" Nana ta zauna sosai tana sauraren Baba.
"Nana duk abin da ki ka ga ina yi, ƙoƙari nake yi a kanki. Ki daure ranar talata ki je gidan yaya Atinen, a jarraba mai maganin wurinta ko za a dace. Idan bai yi ba sai fa mun dangana da mai maganin da Gaddafi ya bani labari, idan ba haka ba babu lallai ki iya zaman aure ki yi haƙuri shi wancan malamin naku dama ba sonki yake ba, tun da ya gudu bai turo iyayensa ba. Tun daga wannan ba sai ki haƙura ayi da shi ba, nima a rage mini ɗawainiya ba. Yanzu ba a auren soyayya, ko wani zurfafa bincike duk bayi ake ba. Ki tashi ki shiga kar ki makara"
Ba ta ce uffan ba, ta tashi jikinta a sanyaye ta shiga gida, gaba ɗaya kalaman Baba babu na ƙwarara gwiwa sai na kashe jiki da cire wa mutum tsammani.
*****
Gaba ɗaya Auwal ya daina shiga makaranta, wanda hakan ya ɗagawa Nana hankali, ta na ta son su haɗu da shi, ta yi masa bayanin abin da ya gani ranar da ya je gidansu, amma ba ta samu ganinsa ba.
Ita ba waya ba balle ta kira shi, abin duniya duk ya dameta. Ranar asabar da sassafe, Baba da kansa ya tashi Nana, ya sanyata shiryawa, ta tafi gidan yaya Atine.
Babu yadda ta iya Baba, zuciyarta ta din ga raya mata, kar ta je, amma ta tabattar idan ba ta je ba, fushi zai yi da ita.
Tun da Allah ya sa ta je gidan, bayan sun gaisa yaya Atine take masifa, wai ta ƙi tsayawa a nema mata magani ta wahalar mata da ɗan uwa. Nana dai ba ta ce uffan ba, Yaya atine ta yi ta faɗanta.
Ta shirya ta saka Nana a gaba, suka tafi wurin mai magani.
Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807
BUZU
Ayshercool
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA 002)
P8
Kallon farko da Nana ta yi wa mai maganin, takaici ya kama ta duƙun-duƙun da shi kamar wakilin sarkin dauɗa. Yana zaune a cikin wasu tarin shirgi da ta rasa ko na uban mene ne.
Ɗakin sai azabar ƙauri yake yi, da tsamin wasu abubuwa da ta kasa tantance ko na mene ne.
Jikin bangon ɗakin, an zana wasu irin hatimai, kuma an saƙale ƙahunhuna da layoyi. A take zuciyar Nana ta bata wannan mutumin boka ne, ba malami ba, ko kuma malun malun.
Ya ƙare wa Nana kallo, ta kawar da kai ta ƙi kallonsa, Yaya Atine ta gyara zama za ta fara yi masa bayani, ya dakatar da ita, ya ce "Ɗan saurara tukuna Hajiya. Ba ki ga ta kasa haɗa idanu da ni ba? Ai sun zo shegun sun ƙaraso, tare ku ka shigo da su ai, ku na tafe su na biye da ita runduna guda, manya da yara tsofaffi da matasa, yanzu haka kusa da ke ma duk su ne a zazzaune makaran nata, sun cika gurin nan"
Yaya Atine ta zabura ta tattare ƙafafuwanta ta ce "Innalillahi. A nan ɗin malam?"
"Eh fa, yi a hankali kar ki hau kan wani"
Nana kuwa waiwaya ta yi, domin ƙara tabattar da a kan wa yake maganar ne?.
Ya gyara zama, ya juya ya ɗaukko wani ruwa, a wata tasa ruwan duk yayi gansa kuka, baƙi ƙirin da shi, ya ɗebo a hannunsa ya watsowa Nana. Take Nana ta ɗan ja da baya, saboda idan wannan ruwan dauɗar ya zuba a hijjabinta jirwaye zai yi.
Ya ce "Kin gani ko, ga su nan za su yi magana, sun ji ruwan azaba, wane su dan uban su. Waye ya zo kanta za ka yi magana ko kuwa?"
Nana ta ɗago kai baki buɗe tana kallon ikon Allah, tana tsoron ta yi wani abin, ya ce Aljanun ne suka zo, kar ta je ya zane ta. Sai dai ta ga idan ba ta yi da gaske ba, sai ya yi mata wanka da ruwan dattin nan, aikuwa ta tashi tsaye ta ja da baya.
Yaya Atine ta miƙe da sauri, ta yi baya cike da tsoro da fargaba.
"Ba za ku yi magana ba?" Yayi maganar yana zare mata ido, tare da miƙewa.
Nana ta ce "Wai suwaye za su yi maganar ni ce fa"
Ya ce "Da alama wannan makaran nata, su na da azabar taurin kai, sai an yi aiki tuƙuru a kansu. Yanzu zan yi mata wani ƙaramin aiki, somin taɓi idan kuma da kuɗi a hannunki ki bayar da dubu goma sha biyar, za a sayo turarukan da za ayi mata aikin da su.
Ranar Litinin kafin hudowar alfijir, ake yin aikin, za ki kawo mana namijin goro guda bakwai, da zuma farar saƙa, kuma da wuya idan ba sai an yi yanka ba, kin ga sun ƙi magana". Yayi maganar yana ƙarasa sheƙa wa Nana ruwan hannunsa, hakan ya sanya hijjabin Nana, kwanciya a jikinta ya fito da surar da Allah yayi mata.
Takaici ya isheta, tun da suka zo, mutumin nan bai ambaci Allah ba, ko ayar Alqur'ani sai shirme da soki burutsu. Warin ruwan da ya zuba mata duk ya cika mata hanci. Kawai ta nufi hanyar fita ta bar ɗakin. Yayi wuf ya riƙo hijjabinta.
A fusace Nana ta juyo ta ce "Meye haka, ka sakar mini hijjabina ba na son haka"
Mutumin ya dubi Yaya Atine da ke zare ido ya ce "Hajiya za su yi magana yanzu, ba ita ba ce ba" Nana ta saka ƙarfinta za ta fizge hijjabinta, ya saka ƙarfinsa ya hankaɗata take ta faɗa kan shirgin da ke cikin ɗakin, wani azababben wari, kamar na ruɓewar wani abu, ya daki hancin Nana, ga ƙume ƙeya da ta yi, wanda gudun kar ta yi ihu, ya sake fakewa da haka ya yi mata wani abun, ya tilasta ta yin shiru. Tana ƙoƙarin ɗagowa, ya shaƙa mata wani abu a hancinta, ta kawar da kanta ba ta sheƙa da yawa ba, amma ta ji wata irin gigitacciyar azaba ta ratsa hancinta zuwa kanta. Ba ta san lokacin da ta kurma ihu ba, jin azabar ta danne mata hanyar fitar numfashi.
Ya kalli Yaya Atine ya ce "Hajiya jeki waje zan yi aikina"
Yaya Atine ta ce "Ka na ganin ba wani abu na je?"
"Eh mana, idan ma kin tsaya babu abin da za ki iya yi, idan ba haka ba idan suka zo fita su shige jikinki" ai cikin azama ta bar ɗakin. Sai da ya leƙa ya tabattar ta bar wurin, sannan ya dawo kan Nana, da take ta layi a ƙasa.
Kan Nana ya yi, yana ƙoƙarin kai hannayensa ƙirjinta duk biyun, ta yinƙura ta juya tana takaicin yadda Yaya Atine ta iya tafiya ta bar ta, daga ita sai wannan zindiƙin mara tsoron Allah.
Ƙoƙarin juyo da ita yayi, yana laluben yadda zai saka hannu a cikin jikinta, tayi wani kyakyawan yinƙuri, ta fizgo wani ƙaho da ke rataye daf da ita, ta raɗa masa a daidai tsakiyar kansa.
Afujajan ya tashi tsaye, yana zazzaro ido, ya gigice saboda yadda ta yi masa dukan a bazata, dan a zatonsa hankalinta ya gushe.
Ya kasa tsayuwa, ya nemi wuri ya zauna, saboda azabar raɗaɗi.
Ta tashi da ƙyar, tana tangaɗi, ya yinƙura ya yi kanta domin hanata fita, kar ta tona masa asiri. Amma ta sake ɗaukan wata ƙwarya wadda take cike da ruwa, yayi baƙi ƙirin saboda tarkacen da yake ciki, ta sheƙa masa a fuska, sannan ta tattara ɗan kuzarin jikinta, ta yi masa ɓarin makauniya da ƙwaryar a fuska sai da ƙwaryar ta ragargaje.
Ganin Nana ta fito tana tangaɗi, ya sanya Yaya Atine tashi ta nufe ta, mutanen wurin na ta yi mata sannu.
"Ke Nana lafiya, ke ce ko aljanun naki ne? Wani mugun kallo ta yi wa Yaya Atine, ta ɗauki takalmanta a hannu ta riƙe.
Yaya Atine ta koma ɗakin mai maganin, ta tarar da shi hanci na zubar da jini. Cikin tashin hankali ta ce "Malam lafiya kuwa?"
"Artabu muka yi da aljanun nata, ba aljanu ne a kanta ba, baƙaƙen iblisai ne, shaiɗan ne da zuriyar sa" ya yi maganar yana shafo jinin da yake fita daga hancinsa.
Sai hankalinta ya rabu biyu, tana ƙoƙarin ta tambaye shi, abin yi, kuma ga hankalinta a kan Nana. Ta koma in da ta bar Nana a tsaye, wanda suke zaune suka ce mata ai ta fita.
Ta fita da sauri, amma ko alamar Nana ba ta gani ba, ta bi hanya tana salati da fatan ba wani wurin ta yi ba.
Sai da ta ƙarasa titi, ta hangota zaune a gefen hanya, takalmanta a hanunta tana ta layi.
Su na yin ido huɗu, kafin Atine ta tsallaka, Nana ta tashi ta shige wani adaidaita sahu, ya ja sun tafi.
Salallami da salati, Atine ta hau yi, ta tari wani adaidaita sahun, ta tafi gidansu Nana.
Baba na ganinta a rikice ya ce "Atine yaya dai? Lafiya kuwa?"
"Ina fa lafiya Isa, mu na wurin mai magani, sun yi karambatta da aljanun nata, kawai ta fita ta haye adaidaita sahu, ai na za ta nan ta yo"
Gaddafi da yake wanki, ya ja tsaki ya ce "Wallahi lamarin yarinyar nan har da iskanci, kuma da gangan take ƙin yin auren nan, a kaita gidan mutumin nan da na gaya maka Baba, idan ba gaske ne, idan ma ƙarya take yi duk zai faɗa babu wani aljani da ya gagare shi"
"To yanzu a ina za a ganota?"
Baba ya ce "To wa ya sani, kwanaki fa kwananta biyu ba ta nan, sai daga baya suka zo da Ummi, wai kawai ganinta ta yi a gidanta, idan ma da gaske take, idan ma ƙarya suke yi oho musu. Ni wallahi na gaji da sabgar yarinyar nan shi yasa nake Alla-Alla a samu mai so ya aura na huta. Kuma ga wannan ƙanin mijin Ummi ta tsaya tana iyayi"
Babu tsammani, sai ga Nana ta shigo, Jamila ta riƙota tana ta tangaɗi, da takalmanta a hannu.
Gaba ɗaya suka yi kan Jamila da tambaya "A ina ki ka ganta?"
"Gidan maman khairat zan je, kawai na hangota tana ta tangaɗi kamar ma ta kasa gane hanyar gida ne"
Mama da take ɗaki, tana jin su, sai yanzu ta yi but ta fito ta ce "Jamila, ban hana ki naniƙar yarinyar nan ba, sai kin kwashi masifa da bala'i"
Atine ta ce "To 'yar nema, da ki na jin duk abin da ake yi, ki ka ƙule a ɗaki?"
Mama ta ce "Ya shafe ni ne da zan fito, ba zaki cikata ba?"
"Mama faɗuwa za ta yi fa idan na cikata"
"Dan ubanki ki rabu da ita aka ce, duk ranar da ta ji miki rauni, ta sabauta ki ai kya shiga hankalinki" Gaddafi ya yi maganar cikin ɗaga murya.
Duk da abin da mai maganin nan, ya shaƙa wa Nana, bai gama sakinta ba, amma tana jin duk abin da suke faɗa.
Ta zame hannunta daga jikin Jamila, ta dafa bango ta nufi ɗakinsu.
Tana jin Baba yana tambayar ta, dan me ta baro wurin mai magani, tayi masa shiru dan ko buɗe baki, wahala yake yi mata balle doguwar magana.
Tana jin yadda Yaya Atine ta cafe, take yi masa bayanin, bataliyar aljanun da ke kan Nana, har da ƙara abin da ba a yi ba, kamar yadda mai maganin yayi mata bayani.
Tun tana jin su sama, har wani abu mai kama da bacci ya ɗauketa.
Kamar a zahiri ta daina jin komai a duniyar da take ciki, ya zauna a gabanta yana kallonta, kafin ya ƙyaƙyace da dariya wani irin baƙin hayaƙi yana fita daga bakinsa.
Sam dariyar babu daɗin ji, ta saka hannu ta toshe kunnuwanta, amma ba ta fasa jin dariyar ba.
"Igiyar ƙaddara, ta ɗaure ki ta ko ina, kuma kina da damar kwanceta, amma azabar baƙin taurin kanki, ya hana ki saduda ki karɓi ƙaddararki"
Nana ta numfasa ta ce "Shirka ba ta cikin ƙaddarata, komai za ka yi mini, ba zan karɓi abin da ka ke buƙata na yi ba"
Ya ɗago dogwayen yatsunsa, ya kai fuskarta ya lakuto gumin da take ta yi, ya kalli gumin a hannunsa ya ce "Ki daina cika baki, lokaci zai fayyace komai"
Daga haka ya ɓacewa ganin Nana.
Bayan farkawar Nana, ta tashi da wata azababbiyar yunwa, ga sallolin da ake bin ta.
Ta tarar da Ummi ta zo, ta gaisheta amma ta amsa mata sama-sama. Ba a damu ba, ta yi sallolinta ta koma tsakar gida ta ce "Mama akwai abinci kuwa?"
"Babu" ta bata amsa kai tsaye.
Ummi ta ce "Mhmm Nana kenan, ai in dai irin wannan abubuwan ne, yanzu ki ka fara gani, tun da zaman gidan bai ishe ki ba, shi wancan na farkon Allah bai ƙaddara an yi da shi ba. Shi malamin naku an ce ya fito yaƙi, amma duk da larurarki, Saleh ya ce yana sonki amma sai wulaƙanci ki ke yi masa. Ya je ai ya gaya mini duk abin da ki ka yi masa"
Nana ta yi kunnen uwar shegu da Ummi, kamar ba da ita take ba.
"Mun yi magana da Baba, aure babu fashi, ya ce a gaya masa iyayensa su turo"
Nana ta kalli Ummi ta ce "Yanzu za ki so hafsa ta auri mutum irin Saleh? Kin san fa ɗan shaye-shaye ne, kuma a Lagos ɗin kin san ina ne wurin sana'arsa da suwa yake tare? Duk ba kwa duba mini wannan?"
"Nana ke ma fa kina da aibun nan, amma ya runtse ido ya ce ya ji ya gani, ita fa rayuwa yanzu idan ki ka samu mai sonki, duk wani tone-tone ba naki ba ne ba" ba ta sake kula Ummi ba, har ta gama abin da za ta yi ta bar gidan.
Tunanin yadda Allah ya ƙwaceta daga hannun mai maganin ɗazu take yi, da tuni ya cuceta ya cuci rayuwarta, ita kanta ta san Allah ne kawai ya ƙwaceta, amma ya riga ya bugar da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 13