Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta ta ce "Nana" sai dai shiru ba ta amsa ba. Ta kalli ƙafafuwan Nanan, futu-futu, har da jini alamar ta taka abubuwa a hanya. "Subhnallah, kar dai da ƙafa ta taho Nana, Nana tashi mana" sai dai ba ta motsa ba. Cikin basarwa Saleh ya ce "Anty lafiya kuwa? Wace wannan ɗin dama da mutum a gidan nake ta sallama ba a amsa ba?" Yayi maganar yana ƙare mata kallo, dan shi gaba ɗaya ma bai lura da raunin da yake ƙafarta ba. Anty ta ce "Ƙanwata ce wallahi, ba ta da cikakkiyar lafiya ne, ga wayata ta lalace balle in kira gida in ce tana nan, kuma ni Wallahi ban haddace lambar kowa ba, balle na kira na gaya musu" Suka ci gaba da jimantawa, Nana kuwa ta ci gaba da baccinta, mai kama da suma. Baba yayi sintiri zuwa islamiyyar su Nana babu adadi, tun yana yawon neman ta har ya gaji. Suwaiba ta ce "Wataƙila mutanenta ne su ka yi wani wurin da ita" "Ba wasu mutanenta, ayi ta fakewa da sheɗanu tana rashin mutunci, ta taɓa yin irin haka ne? Allah ne kaɗai ya san gidan uban wanda ta tafi" Baba ya ce "A'a ba na tunanin za ta je wani wurin ba mu sani ba, tun da ba ta taɓa yin hakan ba, amma ina Jamila ma?" "Ta na gidan uwa ɗakkinta ɗin nan, maman khairat, tun azahar tana can" Baba ya ce "Kuma haryanzu goma saura na dare, ba ta gida uban me take yi a gidan mutane?" Mama ta ce "A'a yau na ga abin tsiya, to malam ba abincin safe babu na rana, ba dole yarinya ta tafi in da za ta samu ta ci ba? Ai gara ita an san in da take, 'yar ka fa? Shi ya yi nasa wuri, ita ma gashi ta kama gabanta" Baba yayi shiru bai sake cewa komai ba. Shirun sa ke da wuya, Jamila ta yi sallama, suka amsa baki ɗaya, Baba ya ɗaga kai zai yi magana, sai yayi shiru ganinta da babbar leda. "Mama na dawo" "Sannu jamila, ya ki ka barota?" "Lafiya kalau Alhamdilillah, baba sannu da gida" Baba ya ce 'Yauwwa Jamila, amma ina ki ka tafi haka ba kya gida?" Jamila ta taɓe baki ta ce "Baba Allah ya gani na gaji da raragefen shiga banɗaki ne, ga yunwa ina ji shi yasa na tafi gidan maman khairat na wuni a can" Baba ya ce "Ku yi ta haƙuri ku na addu'a, in sha Allah za a gyara katangar nan, kuma a gyara masan, mutanen unguwar nan ne ma, babu haɗin kai da zuciyar taimako, amma yadda iftila'in nan ya afko mini, ai kamata yayi ayi gidauniyar da za a tallafa mini" Mama ta ce "Kai wa ka ke tallafawa idan matsalarsa ta tashi?" "Rabi wai babu damar na yi magana, sai ki nemi tozarta ni a gaban yara" Ta girgiza kai ta ce "Ba wani tozarci gaskiya ce" Bai bi ta kanta ba, ya kalli Jamila ya ce "Jamila, Nana fa ba ta dawo gidan nan ba, tun ɗazu ake neman ta ba a ganta ba" Jamila ta tsaya da juye abincin da take yi ta ce "To ina ta tafi?" "Wallahi ban sani ba, an rasa in da ta shiga " Jamila ta ce "Kuma ita ba waya ba, balle a kira ta kuma dai na ga ba ta taɓa yin irin haka ba" "Wallahi kuwa. Kai Sani ɗaukko kwano a zuba mini abincin nan nima na saka a cikina, dan rabona da abinci tun safe, ashe akwai sauran masu zuciyar taimako a unguwar nan, irin wannan abinci haka Jamila" Haka Baba ya karkace aka lamushe abinci da shi, har ya nemi ya manta batun ɓatan 'yar sa Nana. ***** Misalin ƙarfe tara na safe, Nana ce a zaune, tana kurɓar kunun tsamiya, duk da babu sukari a cikinsa, amma ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, ga dankali da aka take mata kwano da shi, wanda rabonta da ta ci ta ƙoshi haka har ta manta. Ummi ta dube ta ta ce "Nana, wai garin yaya aka yi ki ka taho gidan nan a ƙafa haka? Tun jiya kin ƙi magana" Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ban san ya aka yi ba, ni dai kawai ina islamiyya na ji duniya ta yi mini zafi, kamar zan mutu shikenan ban san meyafaru ba, na dai ji ina bacci, kawai na farka na ganni a nan" Ummi ta ce "Ohh wannan larura taki Allah ya yaye miki Nana, an gode Allah ma da ki ka yo nan ba wani wurin ki ka yi ba, in ƙara miki dankalin ne?" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a na ƙoshi Alhamdilillah" "Nana ina kyautata zaton mutanen nan ne, suka hana miki samun mijin aure har yanzu, ga Habibu, rumi-rumi an fara magana aka fasa, ni a yanzu ma akwai wani a ƙasa kuwa?" Nana ta girgiza kai alamar a'a. "Wallahi Nana ina yi miki fatan ki yi aure, ki bar wannan gidan namu, da ba a iya amfana maka komai, idan ba uwarka ce ta yi maka ba, kin ganni nan duk da yau da daɗi gobe babu, yau mu ci gobe mu yi haƙuri, ga azabar dangin miji, amma ya fiye mini wannan gidan namu, da kamar a cikin sa aka yi wahayin babu, ke kanki a yunwace ki ke, ga Baba ya damu ki yi aure, dan Allah kalli wata breziya a jikinki, dan masifa duk kin ƙuƙƙuleta, wallahi da na shiga banɗaki na tarar da phant ɗinki, na za ta tsumma ne da yarwa zan yi, wannan wace irin rayuwar azaba ce?" Nana ta sunkuyar da kai ta yi shiru, dan duk abin da ummi take faɗa gaskiya ne, amma waye zai aureta da wannan larurar a haka? Malam Auwal na islamiyyar su, na ta nuna mata alamar soyayya amma ta yi burus, dan ta san yau da gobe sai Allah, babban fatanta ta rabu da wannan larurar, duk da tana burin yin auren, dan ita kaɗai ta san masifar da take ciki. "Kin san wani abu Nana, akwai wani mai magani da na ji maƙwabciyata su na magana rannan, zan yi mata magana ta kwatanta mini wurin, anjima mu kama hanya mu je ko Allah ya sanya a dace, daga nan na je na duba idan an gyara mini wayata sai na raka ki gida" To kawai Nana ta iya cewa, ta cigaba da shan kununta a hankali. ***** "Alhajin Allah" "Na'am malam" ya amsa yana tattara nutsuwarsa a kan mutumin da yake zaune, a kan tabarma, gefensa ga carbi mai dubu, ga wani ɗan farantin katako da ƙasa a kai. Yayi shiru ya na nazartar ƙasar da ya yi wa zane-zane a gabansa. "Malam me ka gani ne?" "Eh to, buƙata zata biya Alhaji Zailani, amma gaskiya za a sha gwagwarmaya, ga magauta ko ta ina a tattare da kai, arziki zai ninku fiye da yadda ka ke zato, amma gaskiya zaka sha wahala, ƙila ma ka iya rasa ranka, kuma a gidan huɗu ga wata kujerar siyasa nan ko ta mulki da zaka iya samu, sai dai gidan uku ya nuna shi ma akwai bala'i, da tarin ƙalubale" Alhaji zailani ya yakice gumin da yake tsatsafo masa daga goshinsa ya ce "Yanzu malam menene abin yi, dan ko a yanzu kasuwancina harkokin sun fara ja da baya" Ya sake zazzana ƙasa, ya ɗago ya ce "Eh ga wani ƙulli nan a binne a kusurwa huɗu na mararraba, a kanka, amma warware wannan ba zai yi wahala ba, yanzu mafita ɗaya ce da za a samu mai burujin aƙrabu, ko hutu ko surdanu da zai dace da burujin ka, kuma za su taimaka maka ka kai ga ci, ba tare da ka fuskanci ƙalubale ba" Alhaji Zailani ya tattara hankalinsa, ya gyara zamansa ya ce "Malam Gambo to tayaya zan gane su, kuma a ina za a same su, ko nawa ne zan bayar a samo" "Ba samo su za ayi ba, ka samu mace mai ɗaya daga cikin waɗannan burujan, ka kwanta da ita, zaka samu buɗi ta in da ka zata da in da baka zata ba, taurarinta za su haskaka naka da suke ƙoƙarin disashewa, sannan za ta ɗauke wannan wahalar da zaka sha, kafin ka cimma muradinka" Ya jinjina kai cike da gamsuwa ya ce "In dai mata ne gasu nan kamar jamfa a jos, tayaya zan gane wadda ka ke nufi?" Malam Gambo ya numfasa ya ce "Wadda namiji bai taɓa kusanta ba ake so, kuma idan aka samo ta sai na duba ranar sa'ar burujanku. Kuma ba a fuska za a gane mai irin tauraron da nake faɗa ba. A samo mai suna Nadiya, ko ɗausiyya, ko badariyya" Alhaji zailani ya ce "Ni yanzu malam ina zan samo waɗannan sunayen?" "Bincikawa za ka saka ayi, ko Asma'u ma zai yi, amma shi ma da sharaɗi, idan aka samo ɗin sai na lissafa adadin sunanta da na mahaifiyarta na tabattar da haɗuwar aikin" "Shikenan malam, in sha Allah zan yi iya ƙoƙarina, zan samo in sha Allah, ga wannan ba yawa" yayi maganar yana ajiye masa kuɗi a kan shimfiɗarsa. ***** Ummi ce ta kalli Nana a ɗan fusace ta ce "Wai nuƙu-nuƙun me ki ke yi ne haka Nana?" "Wallahi Anty ummi ba na son zuwa wurin maganin nan ne, idan ki na da niƙab ki bani na saka, kar na je wanda suka sanni su ganni" Sheƙeƙe ummi ta kalli Nana ta ce "Au to sai me, ba neman lafiya ki ka je ba, duk wanda ya ce ya sanki shi uban me ya kai shi? Ki wuce mu tafi dan Allah" Jiki a sanyaye Nana ta bi Ummi, sai dai gaba ɗaya ranta babu daɗi, sai dai ta wani ɓangaren tana ƙarfafar zuciyarta a kan wataƙila ta dace da maganin. Maƙil suka je suka tarar da gidan mai maganin, tamkar ana rabon gafara, mata ne suke ta shiga suna fita. Suka samu wuri suka zauna, wasu a shigo da su a rirriƙe, wasu kuma da ƙafafuwansu. Ga manyan mata masu shigar alfarma da kuma yaku bayi. Wasu na ta tumamin iskokai, wasu na kwancez Nana dai ta raɓe ta yi shiru a gefen ummi, kasancewar Ummi ba halinsu ɗaya da Nana ba, tuni ta saki jiki suna hira da matan wurin, wannan ta ce matsalar yara ce ta kawota, wannan ta ce matsalar miji, wasu kishiya wasu larura, wasu su ce mayu ne suka kama su, wasu kuma matsalar rashin mijin aure ne ya kaisu. Nana ta din ga nazarin matsalolin daki-daki, ita a tunaninta matsalar rashin lafiya ce kawai za ta kai mutum wurin mai magani, wadda suke samun saɓani da miji maganin me za a bata, ban da ta kai wa Allah kukanta? Ummi da wayo da dabara, da iya daɗin baki da hira, ta yi wa matan nan wayo, ta ce Nana zata shigar a gani ba ta da lafiya, kwananta uku ba ta magana, kasancewar tun da suka zo ba ta ce uffan ba. A tsanake yake ƙare masa kallo, yadda ya zauna ya tanƙwashe ƙafafuwansa, yake ta wasa da yatsun hannunsa, yaƙi ɗagowa su haɗa ido. Ya mayar da idanunsa kan Habu, da yayi shiru yana jiran bayani daga bakin mutumin. "Wannan ciwon nasa gaskiya ba zan ɓoye maka ba, idan na matsa ni zan shiga matsala, sai dai ku bincika wani wurin" Cikin damuwa Habu ya ce "Yanzu babu yadda za ayi ace ko sunansa ya tuna? Ya san duk wani abu da ya shafi rayuwar yau da kullum, amma ya manta duk wani abu da ya shafe shi" Mutumin da yake zaune a kan sallaya, "Ka san wa ka kawo mini kuwa? Anya ka san waye?" "Na sani" Habu ya amsa cike da ƙwarin gwiwa, cikin gurɓatacciyar hausar sa" Mutumin yayi murmushi ya ce "Ka san dai abin da ka sani, ka bar shi a haka kawai kar ka matsa sanin abin da yake a ɓoye" jiki a sanyaye habu ya kalle na zaunen ya ce "Tashi mu tafi" ya yinƙura ya tashi, ya tsaya ya kalli malamin ya saki murmushi ta cikin rawaninsa suka fice. Babu tsammani Nana su na tsaye a ƙofar shiga wurin mai magani, wasu mutane suka fito, ƙafafuwansa kawai ta kalla ta ji jikinta ya saki, zuciyarta ta tsinke ta sulale za ta faɗi a wurin, Ummi ta riƙe ta da sauri tana salallami. A hankali Nana ta bi bayansa da kallo kasancewar ya riga ya wuce, zuciyarta ce ta raya mata ta bishi da gudu ta ga waye, daina ganin kowa ta yi sai itakaɗai a cikin sahara, sai kuma shi wannan mutumin da ba ta ga kowaye ba, yana tafe yana jan akalar raƙumi ya yi nesa da ita, tana hango shi a can nesa sai kuma manyan sawayen raƙumin da nasa. "Nana" ta ji muryar ummi a kunnenta, ta buɗe ido ta kalle ta a hankali ta kalleta. "Sannu Nana kin tashi" ba ta amsa ba ta ɗaga kai ta gansu a gidan Ummi. "Anty yaushe muka dawo?" Ummi ta ce "Hmm tun ɗazu, ai tun kafin mu shiga wurin mai maganin, ki ka sume, ya ce manyan dakarun aljanu ne a kewaye da ke, mu na shiga ya gansu" Cikin mamaki Nana ta ce "Ya ga su wa?" "Aljanun mana" ta bata amsa cike da ƙwarin gwiwa. "Dama mutum yana iya ganin aljani a suffarsa?" "Ban sani ba, tambaya dawanau, yanzu ga magunguna nan da hayaƙi kowane zan nuna miki yadda za ki yi amfani da shi, ki ci abinci muje na raka ki gida" Nana ta jinjina mata kai kawai, amma bakinta akwai tarin tambayoyi. Da yamma Ummi, ta taso Nana a gaba domin ta rako ta gida. Ko da suka je gidan, mamaki ne ya cika Nana, ganin an zube kayan aikin gini a ƙofar gidansu, a iya tunaninta Baba ba shi da wata hanyar da zai samu kuɗaɗen da za ayi musu wannan gyaran. "Nana, haka gidan ya koma? Ummi ta yi maganar cikin mamaki. "Eh, sai ma kin shiga, rijiya ta haɗe da masai, amma na ga an kawo kayan aiki ban san a ina aka samo su ba" Da haka suka shiga gidan da salallama, Suwaiba da take wanke-wanke ta ɗago ta kalle su, ta ce "Too yau kuma Allah ya yi miki dawowa daga yawon kenan?" Ummi ce ta ce "Wane irin yawo kuma?" But Mama ta fito daga ɗaki ta ce "To ina ta tafi idan ba yawon ba? Wa ta gaya wa za ta je wani wurin? Kwana biyu babanku ya hana mu sakat, saboda ba a ganta ba, ana ta cigiya a unguwa, dama na gaya masa wani wurin ta yi" Har Ummi ta ɗauki numfashi za ta yi magana, Baba ya yi sallama. Suka amsa masa baki ɗaya, baki sake ya bi Nana da kallo, ya ce "Nana daga ina ki ke? Ina ki ka tafi baki gaya mini ba? Ko wurin uwartaki da ba ta san muhimmancin ki ba ki ka wanke ƙafa ki ka tafi?" Ummi ta girgiza kai ta ce "Haba Baba, dan Allah ka tsaya ka ji mana, ka san halin da take ciki na rashin lafiya, shekaranjiya na je ɗaukko yara daga makaranta, ina komawa gida na tarar da ita, a baje a ɗaki ƙafafuwanta duk jini ko takalmi babu, ba ma ta cikin hayyacinta. Ni kuma wayata ta lalace, babansu kuma ba ya gari, shi yasa ban kira na sanar muku ba. Mama ta yi farat ta ce "Wallahi ƙarya ne, ki na nufin tun daga nan ta tafi gidanki a ƙafa? Ƙarya ki ke yi Ummi, ki faɗi gaskiya idan ma, yawon ta zubar ta tafi ki ke kareta" A fusace Ummi ta ce "Allah ba zai nuna mana mai yawon ta zubar a cikin zuriyarmu ba, baƙin bakinki ya faɗa miki kanki da 'ya'yanki..... "Ke ummi rufe mini baki kafin na kwaɗe ki" Baba ya katse ta cikin fushi. Ya ɗora da cewa "Mara kunya wuce ki tafi gidan ki, Allah ya ba da lada" Nana ji ta yi tamkar ta bi bayan Ummi su koma tare, saboda karɓar da aka yi musu, ko arzikin abin zama ba su samu ba, balle a bawa ko ummin ce ruwa, haka ta kasa magana ta bi bayan ummi da kallo yadda ta fita a fusace. Ayshercool 08081012143 https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807 BUZU Ayshercool YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA/002) BRIGHT PENS 3rd BATCH. P3 Nana ta tsaya jiran abin da Baba zai ce, bayan fitar ummi, amma ba ta ji ya ce komai ba. "Wai haka zaka ƙyale yarinyar nan, ba zaka tuhumi ina ta je ta kwana biyu ba?" Mama ta yi maganar tana tsare Baba da ido. "To rabi ya ki ke so na yi, kin san a cikin larura take, ni wannan larurar ta ta ta ishe ni, Allah ya kyauta kawai" Tun da Baba ya faɗi haka, mama ta dasa mita da bala'in baya ganin laifin Nana. Nana kuwa ɗakinsu ta shiga, tana jin yadda maganganun mama ke ratsa zuciyarta, da sanya mata wani irin raɗaɗi da zafi a cikin zuciyarta. Haka ta wuni sukuku, ba wanda ta kula ta ƙule a ɗaki kamar yadda ta saba. Sai dai wunin ɗakin nan, ya ƙara sanya zuciyar Nana a cikin ƙunci, haka kurum kewa da son ganin mahaifiyarta ya bijiro mata. Sai daf da magariba Jamila ta shigo gidan, ta ya da zango a tsakar gida, da abin da ta zo da shi daga gidan uwar ɗakinta. Ƙamshin abinci har cikin ɗaki in da Nana take, ga yunwa tana ta sakaɗar cikinta, kamar ba ta taɓa cin abinci ba, haka take jin cikinta. A lokacin ta tsinkayi hirarsu, wai ashe mijin maman khairat, uwar ɗakin Jamila, shi ne ya ɗauki gabarar gyara musu gidan. Tun tana fahimtar hirar ta su, har ta faɗa duniyar tunani, ba ta iya jin me suke cewa. "Laa Nana yaushe ki ka dawo ke kuwa?" Firgigit Nana ta kalli Jamila, ta yi murmushin ƙarfin hali ta ce "Tun ɗazu, Anty Ummi ce ta rako ni" "Kuma na zo da abinci amma ki na ƙule a ɗaki, kuma na ga alamar yau gidan ba harka, bari Nasiru ya zo ya sayo miki gurasa" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a a ƙoshe nake, na ci abinci a gidan ummi" Jamila ta ce "Gidanta ki ka gudu kenan? Kin taimaki kanki, kya rage wata kafar, wannan gida namu da kullum cikin indararon talauci ake, ni ma tun da Allah ya sa na samu wurin fakewa, na riƙe wuta" Murmushin nan na ta da ta saba, shi kawai ta yi wa Jamila. Ta ɗan numfasa ta ce "Dan Allah Jamila idan wayarki da kuɗi, ara mini zan yi kira. Jamila ta miƙa mata wayar ta fice, wata lamba Nana ta danna, ta din ga kira, a ƙalla sau biyar amma ba a ɗaga ba, jiki a sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta, tare da zuba wa wayar ido, ko za a biyo amma shiru, har aka fara kiraye-kirayen sallar magariba. Sai da ta fita yin alwala, ta tuna babu damar shiga banɗaki, sai dai ta raɓa ta kama ruwa, haka nan ta shiga banɗakin da dabara, ta kama ruwa ta fito ta yi alwala ta shiga ɗaki ta tayar da salla. Tana jiyo yadda yaran gidan, suka tattara a tsakar gida, tare da mahaifiyarsu, sai ɓaɓɓaka dariya suke yi suna hira, ita kuwa tana ɗakinsu a zaune tsuuruu, 'yar fitilar ma da ta kunna, babu batir ta disashe babu haske, ga uban sauro da yake ta yi mata majalisi a ka. Tana nan zaune aka yi kiran sallar isha'i, ta tashi ta gabatar da sallar, ta idar ta fara tasbihi, ita dai ta san ta fara tasbihi, amma ba ta gane kan lissafin abin da take faɗa, ta tafi wasu tunane-tunanen daban. Wuri ɗaya ta tsurawa ido, yadda inuwar wani ƙwaro, yake ta shawagi a ɗan iya in da hasken fitilar da ta kunna yake. Sai dai sannu a hankali, inuwar ta din ga rikiɗewa zuwa wasu halittun daban. Tsoro ya mamayeta, amma a zahiri ta kasa motsi, duk iya ƙoƙarinta, na tuna wasu daga cikin adduo'in da ta iya domin ta yi, abu ya gagara. "Ke Nana!" Suwaiba ta kira sunanta cikin tsawa. A wahale cikin sauke numfashi, Nana ta amsa tana zare ido. "Dan wulaƙanci ana ta yi miki magana, kin yi wa mutane banza, kuma ki na ji, ki je wai ana sallama da ke a waje" Nana ta waro ido ta ce "Ni ɗin kuma?" "Ban sani ba" Suwaiba ta ba ta amsa, tare da ficewa ta bar ɗakin. Ɗan shiru Nana ta yi, tana mamakin waye wannan ya zo wurinta, dan rabonta da wani ya biyo ta ya ce yana so, kusan shekara ta biyu kenan, tun da aka fasa aurenta da Suleiman. Jin abin take kamar a mafarki, haka ta tashi jiki a sanyaye ta fito. Tana jin maganganun Mama sama-sama, amma ba ta iya fahimtar me take faɗa, dan haka kawai ta saka kai ta fita. Duk da babu haske sosai, amma daga yanayin tsayuwarsa, ta gane waye, cikin azama da ladabi, ta durƙusa har ƙasa ta ce "Ya sayyadi ina wuni?" "Lafiya ƙalau Nana, tashi" yayi maganar yana mata alama da hannunsa, ta miƙe tana sunkuyar da kai cikin jin nauyi. Cikin kulawa ya ce "Nana ina ki ka tafi aka yi ta faman neman ki, ba a san in da ki ka je ba? Hankalin kowa ya tashi, daga fita na bar ku a aji, na dawo aka ce mini wai kin fita, sai ɗazu ƙaninki ya ce mini a gan ki" Gaba ɗaya jikin Nana yayi sanyi, ta san ba kowa za ta gaya wa abin da ya faru, ya yadda ba, amma ba ta sare ba ta ce "Wallahi ya sayyadi ni ban san ya aka yi ba, kawai ganina na yi a gidan yayata Ummi, ita ta riƙe ni a gidanta kwana biyu, amma daga nan ba in da na je wallahi" tayi maganar muryarta na rawa cike da karayar, shi ma babu lallai ya gazgata abin da take gaya masa. Cikin tausayawa malam Auwal ya ce "Ba wani abu, kar ki yi kuka, Ubangiji Allah ya yaye miki Nana, ya kawo miki mafita, amma ki na yin dukkanin azkar ɗin da yakamata?" Ta jinjina kai ta ce "Ina yi" "Yauwwa to ki ci gaba, sannan ki yawaita zama da alawala, kamar yadda nake yawan gaya miki, ki riƙe Alqur'ani Nana, Alqur'ani waraka ne" Cikin sheshsheƙar kuka ta ce "Ko hadda ba na iyawa ko na yi mantawa nake yi" Cikin tausasawa ya ce "Ki yi haƙuri, jarrabawa ce, ki ci gaba da gaya wa Allah, kuma kar ki daina ƙoƙarin yin haddar. Ayatu shifa'a ɗin nan da na gaya miki, ki din ga karanta su a ruwa ki na sha" ta jinjina masa kai tana share hawayenta. Baba ne ya tinkaro gidan, dan haka suka yi shiru, ya ƙaraso, Nana tana yi masa sannu da zuwa, malam Auwal na ƙoƙarin gaishe shi. Baba ya amsa sannan ya ɗora da cewa "Ina fatan ta gaya maka, ni ba a zuwa gidan nan yin dogon zance? In dai da gaske ka ke ka turo magabatanka, ni ba na buƙatar komai da wani ƙaƙale, ku kawo kuɗin aure, a ɗaura aure ba sai ka yi lefe ba, ka yi mata kayan ɗaki dan ni ba ni da halin yi mata kayan ɗaki" Take ran Nana ya ɓaci, wannan soki burutsun da Baba yake yi, duk na mene ne? Idan ma da gaske saurayin nata ne, haka zai yarfata, ta yinƙura za ta yi magana, malam auwal ya riga ta ya ce "To Baba in sha Allah duk ba zai gagara ba, zan yi magana da magabatan nawa in sha Allah" Baba ya ce "Yauwwa Allah ya yi albarka" yayi maganar yana shigewa cikin gida, Nana tamkar ta kasa da gudu ta bi bayan baba saboda matsananciyar kunya. Malam Auwal ya ce "Bari na tafi gida, tun da Baba ya dawo, ki shiga gida ki ci gaba da addu'a " cikin girmamawa ta risuna ta ce "Na gode sosai ya sayyadi". Cikin tausayawa ya ce "Allah yayi miki albarka ya baki lafiya Nana" Ta amsa da "Amin ya Allah" ta nufi hanyar shiga gida. A tsakar gida ta tarar da Baba yana tambayar Mama, dama akwai wanda yake zuwa wurin Nana ba a gaya masa ba. "Babu fa wani wanda yake zuwa wurinta, ni rabon da ace an zo wurinta, tun da aka fasa wancan auren nata, kamar an buga mata hatumin jaɓa, malaminsu ne na islamiyya ba wani ba, kuma Auwwalun gidan mai koko ne ba wani ba, malaminsu ne na islamiyya" Bab ya ce "Oho ko ma ɗan gidan mai ƙosai ne, na ce ya yi wa iyayensa magana, su zo ayi maganar aure" "To ce maka yayi yana sonta?" Baba ya ce "Koma ba sonta yake yi ba,

Chapter 2 of 13