bai yi magana ba, Suwaiba ta ci gaba da kakari "Baba ku taimake ni, Nana za ta kashe ni, jinina take lasa tana sha, dan zatin Allah ku hanata jikina zafi yake yi mini"
Imran ya ce "Wace Nanan? Nanan da bata gidan nan?"
Mama ta ce "Amma dai a yanayin da take ba za ta yi wa Nana ƙarya ba"
Imran ya ce "To Nana dai ba mayya ba ce, abin da ku ke zunɗenta ne Allah ya jarrabe ku. Ni dai dan Allah Baba ka gaya mini in da ku ka kai Nana, ni fa hankalina ba zai kwanta ba ina nan tana wata uwa duniya da ban sani ba"
A fusace Baba ya ce "Ban sani ba, ba zaka iya rayuwa tana wani guri ba, da ka tafi gantalinka shekara nawa tana nan ka na can gantalinka?"
Cike da ƙwarin gwiwa Imran ya ce "Amma ai na san tana gida a gabanka, ni gaskiya ban ji na gamsu da wannan tsarin ba"
Ga dai Nana ba ta gida, amma yadda suka ga rana haka suka ga dare, Suwaiba na ihun Nana na sha mata jini.
****
A hankali Nana ta ja jikinta ta zauna, duhu kawai take gani ba ta iya gane komai, ko tafin hannunta ba ta gani. Ta shafa bayanta ta ji alamun bango, ta ja jikinta ta jingina da bangon tana sauke ajiyar zuciya.
Cikin damuwa ta haɗa kanta da gwiwa, zuciyarta sam babu daɗi yau kuma nan Allah ya kawo ta.
Jin ƙarar buɗe ƙofa, ya sanyata ɗago kanta. Wasu mata ne biyu sanye da uniform su ka shigo ɗakin. Suka bubbuɗe tagogi sai ga haske ya ratso ɗakin. Duk da yanayin hasken ya nuna rana na daf da faɗuwa.
Ɗaya daga cikin matan ta ce "Ta ce taso" babu musu Nana ta tashi, ta bi su suka fita, sai ta ga kamar ba gidan da aka kawota ba.
"Za ki yi salla ne?" Ɗaya daga cikin matan ta tambayeta.
Da sauri ta jinjina kai alamar eh.
Aka janyo mata ruwa a rijiya, aka nuna mata banɗaki. Ta yi alwala ta fito aka mayar da ita ɗakin nan ta yi salla. Su na tsaye su na jiranta kamar wata fursina, wata matar ce daban, ta shigo ta kawo wa Nana abinci da ruwa pure water.
Nana ta kalli Abincin gasashsen nama ne, amma ta kawar da kai.
"Ki ci abinci mana" matar ta yi magana cikin kulawa.
"Na ƙoshi" ta faɗa a taƙaice. Babu yadda ba su yi da ita ba, amma ta ƙi ci.
Har sai da ran ɗaya ya ɓaci, ta fice ta tafi gurin mai maganin.
"Sarkin baka, yarinyar nan fa taƙi cik abinci"
"Ahh haba dai? Ta tashi kenan?"
"Eh tun ɗazu har ta yi salla ma"
"Na fa gaya muku yarinyar nan ku lallaɓa mini ita, ba na buƙatar a takura mata, ko ɓata mata rai. A nemo Salamatu ta tura 'yar aike cikin gari, a samo mata wani abincin" rai a ɓace matar ta amsa da to ta fita.
Nana tana zaune tana tunani, sai ga wata matar daban ta shigo da kayan saƙi shuɗaye a jikinta.
Sallamar da ta yi Nana ta amsa tana bin ta da kallo.
Cikin sakin fuska matar ta ce "Barka da yammaci baƙuwar sarki" Nana ta bi ta da kallo ba ta amsa ba.
Ta ajiye wa Nana kwanuka, ta ce "Ga abinci an saka a canza miki"
"Ina su Baba?"
Salamatu ta ce "Sun tafi, sai nan da makonni biyu za su dawo"
"Me yasa za su tafi su bar ni a nan? Ni gaskiya gida zan tafi"
"To shikkenan, amma fara cin abincin tukuna" Da ƙyar Salamatu ta lallaɓa Nana ta ci abinci, shi ma don tana jin yunwa ne sosai shi ya sa ta ci."
Nana ta riƙe alwalarta, a nan ɗakin ta gabatar da sallar magariba, sai dai tsoro ya fara kama ta, ganin ɗakin ya yi duhu babu haske kuma ita kaɗai a ciki.
Ba a jin amon kiran salla, sai dai ta kintaci lokaci kawai.
Ta tura kanta tsakanin cinyoyinta, ta rintse idanunta tana ta adduo'in da suka zo bakinta.
Tana ji ana sallama, amma ta kasa ɗagowa, sai da aka taɓa ta sannan ta ɗago a razane tana sauke numfashi.
Salamatu ce ta shigo da fitila, da kuma kayan abinci.
Ta ce "Yi haƙuri, na tsorata ki ko? Ga abinci ki ci, ga kuma fitila idan ki na buƙatar mai taya ki kwana kuma sai mu kwana tare"
Cikin damuwa Nana ta ce "Ni ba na buƙatar komai, gida nake so na tafi"
"Haba Nana, ba kya so ki samu lafiya ki rabu da abin da yake damunki ne? Magani za ayi miki, babu wanda zai cutar da ke" ta daɗe tana rarrashin Nana, tana kwantar mata da hankali. Ta ɗan ci abincin sannan ta kwanta, tana ta adduo'i.
Ji ta yi sanyi ya dame ta, ta dunƙule guri ɗaya, amma ba ta daina jin sanyin ba har cikin ƙasusuwanta, ta juya domin ta gyara kwanciyarta kawai ta ganta a cikin Sahara itakaɗai.
Ga dare, sai dai farin wata ya haske saharar, sai wani irin sauti da kunnuwanta ke ji, kamar na tasowar guguwa amma ba ta san daga ina sautin yake ba.
A tsaye ta ganshi a cikin saharar, a wannan karon ma fuskarsa a rufe a cikin rawani, sai dai a wannan karon dogo ne sosai fiye da kima. A hankali gurin ya ƙara haske duhun ya ƙara raguwa. Sai kuma ta ga tsayin yana raguwa har ya dawo na daidai mutane, ya saka hannu ya warware rawaninsa.
Ƙaisar ta gani a tsaye, duk ba ta iya ƙare masa kallo, amma yadda yake bayyanar mata a mafarki cikin suffar mutane shi ta gani.
Ta buɗe baki za ta yi magana, ya fara rikiɗewa ya zama tsoho tukuf, tun da Nana take a doron duniya ba ta taɓa ganin tufa kamar wannan ba, gashin kansa yana jan ƙasa fari ƙwal da shi, ga wasu irin kaya masu kama da yanar gizo gizo a jikinsa saboda tsabar tsufa.
Nana ta fara ja da baya a hankali, zuciyarta na hakaito mata addu'a, amma ta kasa furtawa. Ya sake girgiza ya koma wani baƙin raƙumi mai muni, ya buɗe bakinsa ya fara feso mata wuta.
Da wani irin gudu Nana ta juya, tana ihu, ma'aikatan gidan suka rirriƙeta.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Baba ka yi mini addu'a, wayyo Babana, baba Imaran, Jamila dan Allah ku yi mini addu'a na kasa yi"
Cikin damuwa Salmatu da ke riƙe da Nana ta kalli mutumin da ke tsaye a kan Nana yana kallonta ta ce "Sarki ka yi wani abu a kan lamarin nan, kar fa ƙwaƙwalwarta ta taɓu"
Ya durƙuso yana haska fuskar Nana ya numfasa ya ce "Ni na san za a rina. Salamatu"
Ta amsa da "Na'am sarki"
"Idan kin ji ana zaki bari, damisa bari faɗanku na manya wa yake shiga, sai wawa sai mahaukaci, to wannan rigimar ce. Wannan yarinyar da ki ke gani ban san ta ina zan fara yi miki bayani a kanta ba. Dole jikinta ya ƙara rikicewa saboda haɗuwarta da buzayen nan. Da ba su riga sun tafi ba, da ƙarshenta a cikin su ɗaya ya samu waraka ɗaya kuma ya mutu a haka tsakanin ita da Buzun"
"Sarki ka ƙara rufe mini kai na, ban gane me ka ke nufi ba"
Ya yi murmushi ya ce "Da ina buƙatar ki gane, ai gwari gwari zan yi miki salameme. Ya saka yatsunsa biyu a goshin Nana, take ta yi shiru bacci ya kwashe ta.
****
Sosai Imran yake nema ya hana kowa zaman lafiya a gidan, saboda rashin Nana, ya kaɗa ya raya Baba ya ƙi gaya masa gurin mai maganin da aka kai Nana.
Ɓangaren Suwaiba ma abin nata gaba yake yi, sai ana zaune lafiya, sai ta yanke jiki ta faɗi tana kururwar Nana na sha mata jini.
Babu shiri Mama ta ce dole ta fita nema wa Suwaiba magani, kafin Nana ta kashe ta. Baba ya ce ta bari a kai ta gurin da aka kai Nana, amma fafur ta ƙi yarda.
Washegari, bayan Nana ta idar da sallar asuba, Salamatu ta zo.
A duk lokacin da ta zo gurin Nana, cikin sakin fuska da fara'a take yi wa Nana magana, hakan ya saka Nana ta ɗan fara sakin jiki da ita kaɗan, duk da ba magana take yi mata ba.
"Nana taso mu je ko" babu musu ta tashi ta bi Salamatu.
Suna fita daga ɗakin, ta tuna mafarkin da ta yi, sai da ta ji gabanta ya faɗi, ta fara karanto addu'oin da Malam Auwal yake bata. A take ya faɗo mata a rai, har yanzu tana jin kewarsa sai dai a wannan karon, jikinta ne yayi matuƙar sanyi.
Salamatu na gaba tana biye da ita, sai da suka ɗan yi doguwar tafiya, sannan ta fuskanci a cikin gidan da aka kawo ta neman magani suke.
Ta ga yadda ake jere masu taɓin hankali, wasu a cikin mari aka ba su abincin safe, lafiyayyen kunu da ƙosai. Gaba ɗaya suka zuro wa Nana ido. Masu ɗan sauran hankalinsu, su na ta gaida Salamatu tana amsa musu cikin sakin fuska.
Masu rashin ji a cikinsu, su ƙi cin abinci, su na ganinta suka kama kwanukan abincinsu. A gaba kaɗan kuma ɓangaren ƙananan yara ne, masu larurar ƙwaƙwalwa, da ake iƙrarin aljanu ne su ka sanya musu. Wasu ɗauke ciwukan da a turance ake cewa (Down syndrome, autism, poliomyelitis) da sauran su wato masu shan inna, galhanga da sauran su.
Suka ƙara yin gaba, suka ɓullo gurin da ake Sakiya, kamar yadda ta hango jiya da suka zo. Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, ta rintse idanunta yau ma kibiya ake sakawa a cikin magani, sai a ciro ta a saka a cikin wuta, ta yi jawur, aka ciro ana sokawa a cikin wani mutum da cikin ya kumbura tamkar zai fashe. An tara wata tasa wani irin koren ruwa yana kwararowa daga cikin nasa mai azabar wari.
Mutumin yana zaune, tamkar ba cikinsa ake hudawa ba.
Salamatu ta ce "Tsoro ki ke ji har haka? Sun je Asibiti aka ce hantarsa ta lalace, sai dai ayi masa dashen wata, su kuma iyalansa ba su da hali, aka kwatanta musu nan. Lokacin da aka kawo shi, ko tafiya ba ya iya yi, yau satinsa guda a nan yana iya takawa"
Cikin damuwa, a kuma karon farko Nana ta yi mata magana kai tsaye ta ce "Ba ya jin zafi kuma? Da me zai ji? Zafin wuta ko ciwon, ko kuma huda shin da ake yi, idan ya mutu fa?"
Salamatu ta yi murmushi ta ce "Ai ba da ka muke aikin ba, kamar yadda asibiti suke da anesthesia, magunguna da alluran kashe zafi, mu ma mu na da su, irin namu na gargajiya, ba ya jin komai. Ilimi ne ya bawa likitoci damar sanin cuta da magani mu ma kuma haka"
Nana dai ba ta gamsu ba, ta ji ne amma ba ta yarda ba.
Sai yanzu take jinjina girman gidan, su shiga nan su ɓulla can, ko ina ɗaki-ɗaki ne na marasa lafiya a gidan.
Wata ƙaramar ƙofa su ka shiga, amma ta ga sun fito wani katafaren ɗaki ƙato, ba wai kayan alatun zamani ne a ɗakin ba, kawai dai an tsara shi ne.
Ta kalli ƙasan ɗakin, an rufe shi da fatar dabbobi daban-daban, wata ta gane ta wace dabbar ce, wata kuma ba ta gane wacce ce ba.
Hatta jikin bangon ɗakin, an yi masa ado da fatar dabbobi, ta damisa kawai ta iya ganewa da kura, su ma dan tana gani a tv ne wasu lokutan.
Ga kuma ƙahunhunan dabbobi su ma, an ƙawata ɗakin da su, sai kuma jakunkunan fata suma duk an rarrataye su a ɗakin. Ga curin layoyi su ma duk an yi musu guri a ɗakin.
Yana zaune a kan wata karaga, mai ɗauke da ƙwarangwal ɗin kawunan zaki, bayan karagar kuma an yi mata ado da kawunan macizai.
Nana ta yi tsuru, tana tunanin anya ma a zahiri take, ko dai kawai tarkacen mafarkin da ta saba yi ne.
Tasowa yayi jikinsa sanye da kayan fatar giwa, yana faɗaɗa murmushinsa ya ce "Barka da zuwa baƙuwa ta mussaman, lale da ke" Nana ta yi shiru tana kallonsa, duk da ta gane shi, lokacin da aka kawota ta ganshi, amma ba a wannan ɗakin ba, kuma yau baƙinsa ya ragu.
Salamatu ta ce "Sarki ga ta na kawo ta, ta tashi lafiya ƙalau"
Ya ce "Alhamdilillah Allah abin godiya, Nana Asma'u na san kin gane ni, amma ba ki sanni ba, ni ne Garba mai tagwayen baiwa, Sarkin bakar ƙasar hausa, kuma ana yi mini take da Garba ga baka ga aska. Salamatu ba ta abin zama".
Salamatu ta zura hannu a wata 'yar ƙaramar jakar fata, ta janyo wani abu da Nana ba ta gane ko mene ne ba, shi ba kujerar tsuguno ta mata ba, shi dai ga shi nan. Tana tsaka da kallon abin ta ga yana motsi, ta ƙura ido kawai ta ga kan kunkuru ya leƙo ashe kunkuru aka ba ta a matsayin abin zama.
Babu shiri ta doka tsalle ta ja gefe tana kallon kunkurun.
Sarkin baka ya bushe da dariya, ya ce "Tuba muke, mu je ki ga yadda muke gudanar da ayyukan gidan, ko kya saki jiki ayi abin da yakamata"
Wata mata ce ta faɗo ɗakin babu ko sallama, bafulatana doguwa mai tsayi fiye da kima. Tana shigowa Nana ta ji zuciyarta ta yi wani irin gigitaccen bugu, da sai da ta zata mutuwa za ta yi. Matar ba ta ce komai ba, ta shirya ƙorran da ta shigo da su a wata ragaya.
Sarkin baka ya ce "Idan kin gama, ga saƙonki can" bafulatanar ba ta ce komai, ta buɗe wata randa ta ɗebo wani baƙin abu ta sha, ta zo za ta wuce Nana ta fita, Nana ta sunkuyar da kanta ƙasa ta fice daga ɗakin.
"Asma'u kin ga matar da ta shigo ne?" Nana ta jinjina masa kai jikinta yana rawa.
"Me ki ka gani a tare da ita?"
Da ƙyar Nana ta ce "Ba ta da ƙafafuwa, a kan iska take tafiya" tayi maganar bakinta yana rawa.
Ya ɗan yi shiru, Salamatu ta ce "Ya buɗe mata ido kenan tana ganin komai"
Sarkin baka ya jinjina kai, ya ce "Taho muje" ya tashi ya yi gaba su ka bi shi a baya.
Wani guri suka nufa, sai da suka je daf da wata ƙofa, ta fara jiyo ihu mara daɗin ji. Ya buɗe ƙofar ya shiga, sai dai Nana ta kasa shiga.
Salamatu ta ja hannun Nana da ƙarfi, su ka shiga, sai gurin ya rikiɗewa Nana tamkar a film, mahaukata ne a ɗaki-ɗaki, tamkar a prison, su na ta kurma ihu sai ta ga ashe waɗanda ta gani da farko ba hauka suke yi ba, wannan ne masu yin hauka na gaske. Tamkar shirin fina-finan zombie, haka suke ihu su na ziro hannayen su. Nana tsigar jikinta ta din ga tashi, tana jin tamkar ita ma ta fasa ihu saboda rawar da jikinta yake yi, da wani irin azabar ciwo da kanta yake yi.
Hatta haƙoranta da laɓɓanta rawa suke yi, ya yin da sautin ihu da kururwar mahaukatan, ya ci gaba da amsa kuwwa a cikin kunnuwanta, ta rintse idanunta tana sauraron bugun zuciyarta a cikin kunnuwanta dummm dummm da ƙarfin gaske.
Tsawa Nana ta yi hakan ya sanya gaba ɗaya su ka yi shiru, su na kallonta, tamkar an yi ruwa an ɗauke, a hankali ta buɗe idanunta domin ta ga tsawar da ta yi ce ta sanya su yin shiru, ko kuwa?.
Sai dai ta ga tabbas ita ɗin ce ba wani ba.
Sarkin baka ya kalleta tare da sakin wani irin ƙasaitaccen murmushi da shikaɗai ya san ma'anarsa.
Wannan littafin 1k ne a telegram, ta wannan account ɗin 0069685771
Aisha Adam stanbic ibtc bank
Sai shaidar biya ta 08081012143
Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807
BUZU
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
YOTA 002
P13
Ya sake duban Nana ya ce "Manya gatan wasa, uban duƙusa uban haɗari, ai shikenan tun da haka zamu yi da kai"
Ya yi gaba yana ci gaba da murmushi, ya din ga bayar da umarnin abin da za a yi wa marasa lafiya, tare da yi wa Nana bayanin aljanun da kowanne yake ɗauke da shi, da dalilin da yasa ya kama mutum.
Nana ta sha mamaki, wasu a dalilin harkar bokanci, da ta'amalli da aljanun ya sanya suka haukace, wasu kuma sun yi ƙoƙarin amfani da aljanun ne dan su yi kuɗi, su ma suka haukata su. Wasu kuma sharuɗɗan da aljanun suka saka musu, suka gaza cikawa ya sanya suka haukata su.
Ya nuna mata wasu hamashaƙan 'yan kasuwa ne, da masu kuɗi a ka yi musu sihiri da aljanun da suka haukata su.
Babban abin da ya bawa Nana tausayi, har da wata matashiyar budurwa, da ta zubowa Nana ido, tamkar ta haɗiye ta. A hankali Nana ta taka ta nufe ta. Ta zuro hannunta ta tsakanin ƙofar ɗakin, tana miƙowa Nana.
Nana ta miƙa mata nata, ta din ga shafa hannun Nana sannan ta ce "Kin san tazarar da ke tsakanin ƙasa da iya gejin da jirgi yake zuwa a sama? Nigeria mu na da tarin karatu, goyon bayan ƙasar mu kawai muke buƙata, mu je in da zato bai taɓa zato ba. Ina da burin ina raye kafin na mutu, na kasance cikin waɗanda za su ƙera wa Nigeria jirgin sama nata na kanta. Dan Allah ki saka baki na je ƙaro karatun nan, na warke fa ki ce ya sake ni" ta yi maganar tana kuka.
Sarkin baka ya ce "Kubra Yusuf, in sha Allah burin nan naki zai cika da zarar kin warke"
Cikin kuka ta ce "Ai na warke dan Allah ka kira Daddy a mayar da ni gida na tafi karatun nan, kar na yi missing Flight"
Cikin damuwa Nana ta ce "Dan Allah a fito da ita daga ɗakin nan, kamar ta warke fa"
Sarkin baka ya kalli Nana ya ce "Ai ba da baki ake gane wanda ya warke ba, yanzu ana buɗe ta, sai ta kusa hallaka ki a gurin nan. Ainihin ta 'yar makaranta ce, degree ne da ita a engineering, kuma ita ce overaller a department ɗin su. Ta fita da makin da ba a taɓa samu ba a tarihin department ɗin su. Gwamnatin tarayya ta biya musu kuɗi su je su ƙaro karatu a kan fsahar ƙere-ƙere su biyar, ita kaɗai ce mace daga arewa. Shi ne aka yi mata asiri da wani baƙin aljani, aka ba shi jinin mutum, ta taso daga makaranta ta ba shi sadaka, shi yake ta azabtar da ita, a hakan ma zamanta a gidan nan, an rage ƙarfin tasirinsa.
Cikin tausayawa Nana ta din ga kallon yadda ta koma gefe, ta zauna tana ta kuka da ƙarfinta. Haka suka wuce ta.
Bayan sun baro gurin, suka tafi wani guri, shi kuma jarirai ake kawo wa sabuwar haihuwa, domin yi musu aski, kaciya da cire beli.
Idan sarkin baka ya dunƙule hannunsa, yana buɗewa sai ka ga aska, ya yi siddabarunsa ya shafa kan yaro da askar, sai ka ga ya cika hannunsa da gashin yaro.
Idan ya shafa aska a wuyan jariri, sai dai ya zira hannu a bakin yaro, ya ciro wata tsoka har ya cire belin.
Haka kaciya, sai dai da gashin jariran, da belin, duk a cikin jakar zabirarsa yake zubawa.
Sannan ya kan kama hannun yaran, ya ɗaura musu laya, ko ya sanya musu tagulla.
Ya kalli wata mata ya ce "Ahh hajjaju an sauka ashe?"
Ta washe baki ta ce "Wallahi sarki, gobe ma suna"
Ya kalli yaron, da fatarsa duk ta yamutse ya ce "Ke ya aka yi ki ka bari mayya ta kama miki ɗa? Tun yana ciki matar da ta aiko miki da kunu, ki ka sha ta kama miki ɗa"
Cikin damuwa matar ta ce "Innalillahi wa innalillahi raziƙuna, wallahi sarki ka ga ba ya gaba yaron nan, kullum cikin kuka ba ruwan nono na rasa yacca zan yi ohh ni Sakina, amma Allah ya isa wallahi"
Daga yadda matar ta faɗi Innalillahi, Nana ta ƙara tabattar da jahilci a gurin matar, yadda suke ba wa maganganun sarkin baka ammana ba tare da musu ba har mamaki yake bata. Ya faɗi maganin da za a bata suka yi gaba.
Wani guri suka shiga, shi kuma masu ciwon suga ne, ya yi musu ya jiki suka amsa. Bayan sun gama gaisawa ya kalli masu kula da su, ya ce "Yauwwa, kar a kuskura a karya dokokin da na saka, da sassafe kafin su ci komai a ba su magani, a basu zuma cokali biyu da garin habbatussauda, sai su karya kumallo da ruwan dahuwar yaɗiya mai ɗumi, sannan su ci ganyenta. Da rana a basu faten dankalin turawa da alayyahu, a sake basu zuma da habbatussauda, sai da daddare a ba su gurji da kwaɗon rama, sai a sake ba su magani. Yau maganin cikin ɓawon gyaɗa bibbiyu za a zuba musu a ruwa su sha. Shi ne jadawalin abincin da za a ba su yau" ma'aikatan suka amsa masa da to. Nana kuwa rasa bakin magana ta yi, sai kallon ikon Allah, tamkar likita a asibiti da marasa lafiyar sa.
Sun zagaya sosai da sosai a cikin gidan, sannan suka koma wancan ɗakin da suka tarar da shi da farko.
Bayan sun shiga, ya zura hannu a cikin zabirarsa ya din ga zaro gashin jariran nan, da belin da ya din ga cire musu, yana tarawa a cikin wata tasa, sai da ya cikata taf. Ya dubi Salamatu ya ce "Salameme zuba wa Fulani a randarta" Salmatu ta karɓa, ta je ta buɗe randar da bafulatanar nan ta ɗqzu sha wannan baƙin abun ta juye a ciki.
Ya kalli Nana ya ce "Za ki iya tuna daga wani lokaci, ki ka fara ganin uban duƙusa a bacci?"
"Waye hakan?" Nana ta tambaya cikin rashin fahimta.
"Aljanin da yake zuwar miki"
"Wai ƙaisar?"
Ya yi murmushi ya ce "Shi"
"Ba zan iya tunawa ba" ta bashi amsa.
"Ina kallonsa a tare da ke ɗazu, shi ya yi wannan tsawar mahaukatan nan suka yi shiru, so nake ya bayyana a jikinki mu yi magana da shi, amma yaƙi. Masu ihun nan da ki ka gani, duk masu baƙaƙen aljanu ne masu taurin kai, wanda ko an ba su magani, suke lafawa su dawo daga baya. Nan gurin ɗaure su na yi, nake hukunta su da azaba kala-kala, a matsayin gargaɗi da kashedi. Akwai hayaƙin da ake yi musu safe da yamma an gama hayaƙin muka je, amma ƙaisar ya ƙi bayyana. A duniya aljanun da suke irin sa ba su da yawa". Nana ta yi tsuru tana kallonsa da saurarensa, tare da kallon maganganun sa a matsayin soki burutsu.
"Amma ke me yasa ba zaki yadda ki karɓi abin da yake gadonku ba, ki ka gwammace ya yi ta azabtar da ke?"
Take Nana ta tsuke fuska, ta tsani ta ji an danganta ta harkar bori da gadonsu, kamar wani abin arziki.
"Ni ba zan yi shirka ba"
Sarkin baka ya ce "Ba shirka ba ce ba, bayar da magani, idan bayar da magani shurka ne, Asibiti ma shirka suke yi. Ki amince sai mu haɗu mu ci gaba da gudanar da taimakon al'umma"
Ta girgiza kai ta ce "Ni ba zan yi ba ba na so"
"Anya? Ki yi tunani kar ki zo nan gana kina nema ido rufe fa" tayi shiru ba ta yi magana ba.
"Salamatu mayar da ita ɗakinta, a bata abinci, idan tana buƙatar wani abin a bata"
Salamatu ta jinjina kai, daga nan ta jagoranci Nana suka bar ɗakin.
****
Zaune take a katafaren falonta, ta hakimce a kan kujera tana amsa waya "Hajiya Sa'a, ya mu ka ji da iftila'in nan da ya tinkaro mu, coustom sun riƙe mana kaya a Abuja?"
"Aikam, mu na nan muna ta up and down, Allah ya sa su sakar mana a kan lokaci"
"Amin ya rabb, wallahi hankalina duk a tashe yake, na haɗa kuɗin mutane da jarina duk na zuba na sayo kayan nan, ni dai fatana Allah ya sa kar su yi condeming ɗin kayan nan wallahi ban san in da zan saka raina ba, ga mutane sun fara ƙorafi"
Hajiya Sa'a ta ce "Ahha haba Sadiya, babu abin da zai faru fa, ki kwantar da hankalinki ki yi addu'a"
"To shikkenan Hajiya, na gode sosai da sosai" bayan sun yi sallama, Hajiya Sa'a ta yi murmushi ta kalli maman khairat ta ce "Safiyya mutuniyarki ce fa, Sadiya"
"Ohh Allah sarki"
"Duk hankalinta a tashe yake, batun kayan da coustom suka riƙe, ni ba ta son ko kaɗan kayan nan ba a gabana suke ba"
Safiyya ta yi dariya ta ce "Haryanzu ita kanta a tukunya yake kenan, ba ta san dawar garin ba?"
"Ina fa ta sani, a zatonta business yake tara mini
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 13