Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ita. 'wataƙila ga in da addu'oinki suke yi miki amfani, amma ki ke garaje da ɓacin rai' wata zuciyar ta tunatar da ita, a take ta yi ta istigfari. Sosai Baba ya ɗauki maganar Saleh da muhimmanci, Nana kuma ta na ta kai kukanta ga Allah, duk da neman lafiya da take roƙa ya rinjayi duk sauran adduo'in da take yi. Gashi duk da shirun da take yi wa Saleh idan ya zo, ba ya zuciya sai ya kuma dawowa, dan babban abin da yake saka shi zuwa ba yau ba gobe, bai wuce tozali da ƙirar jikin Nana ba, da yake jin kamar zai ɗimauce, idan bai kai hannunsa jikinta ba. Ta kan ƙare masa kallo, tana mamakin yadda Baba ya rintse ido, daga ganin aibun Saleh, kama daga kan askin banzar da yake kansa, zuwa suturar da yake sakawa da sunan gayu. Kodayake dama gayu idan ya haɗu da jahilci hauka ne tuburan, duk soki burutsun da zai yi mata babu maganar Allah a ciki sai shirmensa. Gefe guda ga kewar malam Auwal da ta dameta, tabbas ba dan mutunci da kamewarta, na ɗiya mace ba da babu abin da zai hanata zuwa gidansu ta tuntuɓi ko lafiyarsa ƙalau. Sai dai duk da haka sai da ta tambayi abokinsa malam Nura, ya tabbatar mata da lafiyarsa ƙalau ayyuka ne su ka yi masa yawa kawai. Kimanin makwanni biyu kenan, ba ta ga malam Auwal ba, zuciyarta na raya mata, karɓar lambarsa a wurin malam Nura, ta ari waya ta kira shi, amma ta kasa. Kwatsam su na cikin karatu a aji, ta jiyo muryarsa a waje. Ta kasa riƙe kanta, ta tashi ta fita. Kafin ta isa, har ya shiga cikin ofishinsa, yana cikin tattara litattafansa, kawai ya waiwayo ya ga Nana. "Yaya Auwal meyasa ka ke guduna? Ina ta son mu haɗu na yi maka bayani, amma ka daina zuwa ma gaba ɗaya" "Babu malami a ajinku ne?" "Eh, tilawa muke yi" "Ki koma aji" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba. Ta marairaice ta ce "Amma Yaya Auwal, magana nake son mu yi, dan Allah ka fahimce ni ba abin da ka gani, ba abin da ka ke tunani ba ne... "Ki tafi aji na ce Nana, ba sai kin yi mini bayanin komai ba" yayi maganar cikin tsawa. Tsayawa ta yi tana kallonsa, bayan tayi nasara sun haɗa ido. A hankali ta sauke ajiyar zuciya, ba ta tafi ba kuma ba ta ce komai ba, sai dai idonta ya cika da hawaye. Sai ya tausasa murya ya ce "Ki je aji Nana, ba na son gardama" Ta girgiza kai ta ce "Koma me ka ke ɓoye mini ka gaya mini. Kai malamina ne, kuma abin koyi na, ka karantar da ni nagartattun halayen fiyayyen halitta Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Wanda ya haɗa da gaskiya, da kuma haƙuri. Ka gaya mini ko ma mene ne a ranka dan Allah" Jiki a sanyaye ya ɗan sunkuyar da kansa, sannan ya kalle ta ya ce "Nana kin san komai nufi ne na Allah, maganar aure tsakanina da ke, ba zai yiwu ba yanzu haka Qatar zan tafi da wani ɗan ƙanƙanin lokaci" Murmushi ta yi, duk da hawayen da ya cika mata ido, ta ce "Ko kai fa, ka ga yanzu da ka gaya mini gaskiya zan fi samun nutsuwa sosai da sosai. Ina yi maka fatan alkhairi amma dan Allah ka ci gaba da yi mini addu'a, na san larurata ce ta saka ka fasa aurena, ka yi mini addu'a Allah ya bani wanda zai iya aurena da larurata a haka" "A'a Nana, idan baki manta ba, tausayinki da halin da ki ke ciki, ya sanya na ce zan aure ki, ban ƙi auren ki saboda larurar ki ba" Ta share hawayenta ta ce "Eh, da fari tausayina, daga baya ka koma so na, dama na san zaka rabu da ni, dama na fi so na ji daga bakin ka ne, tun lokacin da aka ce ba zaka iya riƙe aure ba, na ga komai a bacci, har rabuwar nan tamu na yi mafarki na gani, ba zaka aure ni ba. Hakan ba ya nufin zan manta tarin alkhairin ka a gare ni, Ubangiji Allah ya baka mace ta gari lafiyayyiya" Zai yi magana ta girgiza kai, ta fice daga ofishin, zuciyarta na zafi hawayen da take ƙoƙarin dannewa, su ka ƙi dannuwa. Auwal bai taɓa tunanin yana son Nana har haka ba, sai da Umma ta hana shi aurenta, kuma abin bai tsaya a nan ba, sai da Umma suka tura shi Qatar. Nana ta tafi rijiya, ta ɗebi ruwa ta wanke fuskarta, sannan ta koma ajinsu aka ci gaba da tilawa da ita. Sosai rabuwa da Auwal ya shigi Nana, duk da ta yi mafarkin hakan, amma ba ta bari ta gasgata hakan ba. Har aka tashi daga makaranta, hankalinta ba ya kan abin da aka ƙara musu sam. Da daddare, bacci ya gagari idanun Nana, sai tunani da zancen zuci, ya din ga ziyartar zuciyarta, har ta rasa wane tunani ya kamata ta yi. Jamila ce ta zo da abinci daga gidan maman khairat, ta cewa Nana ta tashi ta ci, amma ta ƙi. Sai da ta takura mata, sannan ta ci kaɗan, ta sha lemon ta kwanta, sai dai abincin ya tsaya mata yaƙi wucewa. Tana daga kwance, tiryan-tiryan, yadda aka fasa aurenta na farko ya dawo mata, yadda take samari, su na tafiya, duk da galibi mutanen banza ne suke bibiyarta. Amma Suleiman ya zo da gaske zai aure ta. Sai dai Baba ya din ga zubar mata da mutunci a idonsa, ta hanyar roƙe-roƙen kuɗi, kuma wani abin mama ce take ziga shi yake yi, har ita ma wasu lokutan sai ta tura ta ce ya bata kuɗi, sun wuni ba su ci abinci ba. Tun yana bayarwa da marmari, har ya gaji ya fara mita. Ya san da Nana ba ta da cikakkiyar lafiya, duk da a lokacin abin ya lafa, amma mama ta zaunar da shi, ta din ga karanta masa Nana aljanu har sun fara haukata ta. Matarsa ta zo har gida ta ci mutuncin Nana, har da an gaya musu babarta ce take biye-biyen bokaye, abin ya koma kanta take fama da aljanu. Duk da dama Mama ta saba faɗar wannan maganar, idan ta so cin mutuncinta, amma abin yayi mata zafi ya mata ciwo. Wuni ta yi tana kuka, Suleiman da kansa ya je gida ya ba wa Nana haƙuri, bayan ya samu labarin abin da matarsa ta zo ta yi mata, sai dai tun da matar ta koma gida, ya aka rasa gane kanta, ta kwanta rashin lafiya. Ta din ga fama da matsanancin ciwon kai, idan ta fara sai ta fita hayyacinta ko gani ba ta iya yi, suka je asibiti ba a ga komai ba. Ya koma gidansu Nana, ya ce idan ta san wani abu ta yi wa matarsa, ta bari uwar 'ya'yansa ce, ba zai so lafiyarta ta taɓu ba, tun da ai ya zo ya bata haƙuri. Nana ta din ga rantse-rantsen ita babu abin da ta yi mata, ƙarshe dai matar kamar za ta haukace, ya zo ya ce a dawo masa da kayan aurensa, tun a waje Nana ta cutar da iyalinsa, ina ga idan ya aureta, dama kuma an ce masa mahaifiyarta na biye-biye. Duk yadda Nana take son ta yi aure, ko dan saboda tarin ƙalubalen da take fuskanta, amma fasa aurenta da Suleiman bai wani dame ta ba, domin tana fargaba mussaman yadda aka gama zubar mata da mutunci a wurinsa. Ajiyar zuciya ta sauke da ta zo nan a tunaninta, sai da kanta ya sara, ta sauke ajiyar zuciya. Ga abubuwa da dama su na cin zuciyarta, tana buƙatar abokin shawara da tattaunawa, amma rashin yardarta bai sanya ta bawa wani damar, hakan a rayuwarta ba. Mutanen da suka cancanci hakan a rayuwarta duk ba ta ita suke yi ba. Babbar damuwarta a yanzu, bai wuce yadda ta san ko ba ta so, Baba sai ya ƙaƙaba mata Saleh ba, dan ta fuskanci zamanta ne kawai ba a so cikin gidan, duk ga su Suwaiba da Jamila, su babu wanda yake takura musu a kan aure sai ita. Sosai take jin zafin rashin Auwal, ko ba komai mutum ne ma'abocin Alqur'ani da kuma riƙo da addini, ta san abu ne mawuyaci a iya cutar da shi, ta sanya ran idan tana tare da shi, za ta samu sauƙin wasu abubuwan. "Ke baiwar Allah" ta ji an kirata. Ta ɗaga kai, ta hangi wata mata bararoji a tsaye, ta yi kwalliya da tarin tsummokara, da wasu irin tarin sarƙoƙi na zare a wuyanta, da ƙullin kaya a hannunta, ta burtso da gashin ta gaban goshin ta. Nana ta ɗaga kai ta ganta a wani wuri, da ba ta san ina ne ba. Matar ta ce "Zo na baki magani" Nana ta ce "magani kuma, na me?" Matar ta sauke mayafin da ta rufe fuskarta, ko ina tsagu ne a fuskarta, har baka iya tantance kamaninta, saboda azabar billayen da ke fuskarta. Matar ta ciro wani magani a cikin, ƙullin kayanta ta ce "Ki zuba a tafin hannunki, ki lashe" Nana ta ce "To ai ba ki gaya mini na mene ne ba?" "Idan ka sha, ba zaki ganin Ƙaisar ba, zai daina bibiyar ki yana takura wa rayuwarki, zai rabu da ke har gaban abada. Dukkanin damuwar ki za ta kau, babu wanda zai sake zuwa auren ki, yayi nasarar korarsa ko ya saka miki wani ciwo. Dan yan daf da fara kashe mutane, domin wata ƙungiyar asiri ce suke nemansa ido rufe yayi musu aiki. Idan suka sadaukar masa da jini, zai fara kisan mutane ne, kuma zai fara da mutane mafi soyuwa a gare ki" Jiki na rawa Nana ta miƙa mata hannu, domin karɓar maganin. Matar ta yi murmushi, haƙoranta suka bayyana baƙaƙe ƙirin da su, ta kama tafin hannun Nana, ta zuba mata maganin, da yawa. Tana kama hannunta, Nana, ta ji tamkar an zare mata lakar jikinta, jikinta yayi wani irin sanyi, da ta kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi. Ta kai garin maganin bakinta ta fara sha... Ayshercool 08081012143 https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807 BUZU AISHA ADAM AYSHERCOOL YOTA/002 P9 Ko da Nana ta sake lasar maganin, sai ta ga fuskar matar tana komawa baƙa ƙirin, tana ta fito da dogon harshe, tamkar na macijiya, wani abu mara kyan gani na futa daga bakin nata. Iya ƙarfinta Nana take son ta yi addu'a, idan mafarki take ta farka, amma ta ji tamkar an saka dutse an tokare maƙogwaronta zuwa huhunta. Babu tsammani, ta ga wata irin guguwa ta haɗu, Ƙaisar ya bayyana a tsakaninsu yayi wani irin mugun cilli da matar a gefe. Yayo kan Nana, ya zubar da sauran maganin hannunta, ya shaƙe mata wuya. Wani irin kakari ta din ga yi, ta na amai dunƙunlen jini yana fitowa ta hancinta da bakinta. Ji ta yi numfashinta na neman ɗaukewa. Ita ma Nanan, ya yi jifa da ita gefe, ta riƙe wuyanta tana numfashi da ƙyar. Ya kalle ta a zafafe ya ce "Idan ki ka ci gaba da irin wannan gangancin, za a kashe ki a haka, babu wani mahaluki da zai iya raba ni da ke. Guba ta baki za ta kai jininki ayi tsafi da ke saboda tasirin taurarinki. babu wanda zai iya baki wani magani ya raba ki da ni, idan ki ka ci gaba da yinƙurin rabuwa da ni, za ki kashe kan ki da kan ki" yana maganar tartsatsin wuta na fitowa daga jikinsa, yana ƙona Nana. A hankali ta buɗe idonta, ta ganta a kan shimfiɗarta, ta takure jikinta yana ta rawa, numfashinta yana fita da kyar. Wuyanta sai raɗaɗi yake yi mata, haka ma jikinta. Ta kai hannu ta ɗauki fitilarta ta kunna, tana haska ɗakin, ba kowa a ɗakin sai ita kaɗai. Jikinta ya ba ta wani abin tayi, su Jamila suka gudu suka bar ta a ɗakin. Ta yinƙura da azama ta tashi tsaye, amma jikinta sai raɗaɗi yake mata, kafaɗunta kamar ba a jikinta suke ba. Ayatul kursiyyu ta din ga karantawa, ta fita ta ɗauki buta, ta shiga banɗaki. Tana fara fitsari ta ji ƙarnin jini, tana dubawa ta ga fitsarin jawur, jini a maimakon fitsari. Gashi ko kwana bakwai ba ta yi da gama al'ada ba. Ta wanke jikinta tayi alwala, ta koma ɗaki, gaba ɗaya ta kasa yadda har yanzu ba a cikin mafarki take ba. Da safe ta fito ta yi aikace-aikace da za ta yi, Jamila ta ce "Nana me ya same ki haka?" "A ina?" "Jiya da daddare ki na ta kakarin amai, ki na kuka a bacci, yanzu kuma kalli jikinki, kamar an zane ki da bulala" Baba da ya fito daga banɗaki, shi ma ya kalli Nana. Jikinta duk kwanciyar bulala, gashi ta ɗashe ta yi haske, kamar mara jini a jiki. Nana ta kalli jikinta, ta ɗan taɓe baki ba ta ce komai ba, ta ɗebi ruwa ta shiga banɗaki domin yin wanka. Sai dai wannan karon ma, fitsarinta jini ne kawai yake zuba. Kawai ta jingina da jikin banɗakin, ta fashe da kuka, sai da ta yi mai isarta sannan ta ta fara yin wankan. Sai dai tana zuba ruwan a jikinta, ta ji kamar fatarta za ta zazzago, jikinta ya hau kyarma. Duk da a cikin banɗaki ta yi, haka ta furta a'uzubillah, ta cigaba da zuba ruwan a jikinta tana wanka, har ta kammala ta fito. Ta yi alwala, ta shiga ɗaki ta shirya, tana kallon Baba yana kallonta, amma ba ta gaishe shi ba, haka kurum ta tashi da matsanancin ɓacin rai, ko ganin Baban ba ta son yi. Ba ta kula kowa ba, ta fice ta tafi makaranta. Gaba ɗaya jikinta ciwo yake yi mata, ga jiri tana fama, dan haka a cikin aji ta yi zamanta, ta kifa kanta a kan tebur, tana ta kewar rashin Auwal. ***** "Safiyya" "Na'am Hajjaju" "Yaya kin yi magana da Jamila kuwa?" "A'a yanzu dai nake saka ran zuwanta" "Dan Allah, ki ɗan bugi cikinta ki ji, yarinyar nan ta sha lemon kuwa?" Maman khairat ta ce "In sha Allah, zan bugi cikinta zamu yi magana da ita" "Amma ina fatan, ba ki gaya mata ko na mene ne ba" "A'a haba Hajiya, ya ma za ayi na gaya mata, ai kin ce ko wani ma ya ci ba komai, ita ɗin dai ake so ta ci, zan tambaye ta idan ta zo" "To shikenan, na gode sai na ji ki" ***** Ƙamshin turare ne ya cika wa Nana hanci, sai dai ba ta motsa ba ko ta buɗe idanunta ba. Teburin da take kai, ya ɗan bubbuga, sai a lokacin ta buɗe idonta a hankali. Dishi-dishi ta fara gani. A hankali idonta ya washe, ta ɗaga kai ta kalle shi. Yayi murmushi ya ce "Anty ya dai ki ke bacci, ko babu lafiya ne?" A hankali ta tashi zaune, ta kalli agogon ajin nata ƙarfe biyu. Tunani ta hau yi, tun da ta shigo da safe take wannan baccin, ko kuwa? Maganar Muhsin ce ta dawo da ita hankalinta ya ce "Anty kin ga na gama" yayi maganar yana nuna mata littafin sa, da ya cika page guda da A. "Afuwan Anty Nana, direbansu ya yi tafiya ne, mahaifiyarsa babu lafiya, ni kuma ba ni da isasshen lokaci, na shiga wani meeting ne, shi yasa na daɗe ban zo ɗaukarsa ba, ki yi haƙuri na ɓata miki lokaci". Jinjina kai kawai ta yi ta tashi, ya ce "Mu je sai mu sauke ki a hanya" sai dai haryanzu ba ta yi magana ba, ta bi shi su ka tafi. Jamila na zaune, tana ta zaman kashe wando a gidan maman khairat, kamar yadda ta mayar da hakan ibada, tana tayata aiki su na hira. "Ni kuwa jiya kin ci abincin jiya Jamcy?" Jamila ta ce "Lallai ma Anty Safiyya, me zai hana ni ci, na yi abincin kuma na kasa ci?" "Wallahi ni gaba ɗaya kasa cin abincin na yi, na ce da na sani, na ce ki tafi da shi duka" Jamila ta ce "Subhnallah, ko dai Khairat za a yi wa ƙani" Tayi murmushi ta ce "Rufa mini asiri, wallahi sai da ki ka tafi na ga kamar abincin ba zai ishe ku ba, kuma har su Nana duk sun samu sun ci?" Sai da Jamila ta yi mamakin tambayar, amma ta ce "Eh mana, Nana ce ma babu lafiya, ba wani ci ta yi ba, kin san 'yar ƙi faɗi ce, sai na je da abu sau shurin masaƙi amma babu lallai ta ci" "Eyya, to ai ba komai, mun riga mun zama ɗaya Allah ya ba ta lafiya, ta sha lemon ma?" "Eh amma ba da yawa ba" Safiyya ta jinjina kai ta ce "Dan Allah ki yi mata sannu" Jamila ta ɗan taɓe baki ta ce "To, za ta ji, kin san ita kullum cikin ciwo take ne, abin nata ba na ƙare bane ba" Suka ci gaba da hira, ƙasan zuciyar Safiyya, cike da farin ciki ***** Ƙarfe huɗu da rabi na yammaci, sannu a hankali yake ƙarewa garin kallo, duk ya kwana biyu baya garin, amma ba wani abu ne ya canza ba, amma har cikin zuciyarsa yake jin kewar Kanon dabon. Tun daga can babban titi ya sauka, ya saɓo hanya, domin ya samu isashshiyar damar ƙarewa garin kallo, yadda yake so. Dandazon mutane ya hango a wani wuri, mutane na ta surutu da hayaniya. Har ya yi gaba, kawai ya dawo da baya domin ganewa idanunsa abin da ya tara wannan cincirindon al'ummar. Ya din ga kutsawa, yana ture mutane. Kawai ya tarar da wata matashiyar budurwa a kwance a wurin, sai dai ta juyar da fuskarta ba a iya ganin fuskarta. Ya taɓa wani mutum ya ce "Malam lafiya, me ya faru don Allah?" Mutumin ya ce "Wallahi tun azahar, muka ganta a kwance a wurin nan, an zata ma ko ba ta da hankali, ko kuma ba ta da lafiya, amma jikinta fes babu datti ba alamar hauka a tare da ita. An yi anyi ta tashi ko motsi ba ta yi, kuma tana da rai. An duba jakarta babu waya sai maka da kuɗi, yanzu ma dai an kirawo 'yan sanda". Bai ce uffan ba, cikin azama ya nufi kanta, mutane na ƙoƙarin hana shi, amma bai saurari kowa ya je kanta ya ɗago ta. Idanunta a rufe, sai dai hawaye da yake ta fita ta gefen idonta, ga jikinta zafi tamkar wuta. A sanyaye ya ce "Nana" shiru ba ta amsa ba. Miƙewa yayi yana ƙoƙarin ɗaukarta, wani ya ce "Malam lafiya, ina zaka kaita?" "Ƙanwata ce" ya faɗa a taƙaice, ya fita ya taro adaidaita sahu. Bai sake tsayawa yi wa kowa bayani ba, ya saɓa Nana ya shiga adaidaita sahu, ya tafi da ita. Mama na tsakar gida tana tankaɗen tuwo, sai ganinsa tayi a tsakiyar tsakar gida. Suwaiba da take jan ruwa ya kalla ya ce, "Shimfiɗa mini tabarma a tsakar gida" Ta ajiye gugan, ta ɗaukko tabarma, ya kwantar da Nana a kai. Ya ɗebo ruwa a kofi, ya zo ya zauna a kusa da ita, yana ƙare mata kallo, gaba ɗaya ta rame sosai da sosai. Cirko-cirko mutanen gidan suka yi, su na bin sa da kallo, kowa da magana a bakinsa, amma babu damar furtawa. Ya tofa ayatul kursiyyu, da falaqi da nasi, kowacce da bismillah, ya shafa mata ruwan a fuskarta, da tafukan hannayenta. A hankali yake bin jikint da kallo, yana mamakin shaidar duka ce, ko ta ƙonuwa a jikinta. "Nana" ya kira sunanta. Cikin sa'a sai ta buɗe idonta a hankali, ta sauke a kan fuskarsa. Shiru ta yi tana kallon sa, kamar ba ta taɓa ganin sa ba, zuciyarta na raya mata kawai tarkacen mafarkin da take yi ne. Ta yi shiru, ta tuna ta shiga motar baban Muhsin, su na tafe a hanya, a kunnenta ta ji ana ce mata, ga Auwal can a marrraba, nan da mintuna goma tirela za ta taka shi. Babu shiri ta tsayar da baban Muhsin, bai gama parking ba, ta buɗe motar ta fita daga nan kuma, sai ta ɗimauce ta rasa gane gaba da baya. Mayar da idanunta tayi ta sake lunshewa. "Ma'u" ya kuma kiranta yana matsa hannunta. Ta sake kallonsa a hankali ta ce "Wai da gaske kai ne?" "To da waye? Dama haryanzu ba ki warke ba, ki na wannan ciwon Nana? Kuma uban waye ya dake ki duk jikin ki ya tashi haka?" Ta yinƙura ta tashi zaune, kawai ta fashe da kuka. "To kukan uban me ki ke yi kuma? Na ce uban wa ya dake ki?" "Ba dukana aka yi ba" ta bashi amsa tana share hawayenta. "To me ya kai ki yin bacci a titi, maza sun baibaye ki, kamar ƙudaje sun ga mangwaron Binta suga" Ba ta bashi amsa ba, ta ci gaba da kuka. Ya tsuke fuska ya ce "Dalla yi mini shiru, ina yi miki magana ki na wani kukan banza" "Me yasa ka tafi ka bar ni?" Ta yi magana cikin kuka. Guntun tsaki yayi, ya ce "To dai ba ga ni na dawo ba? Uban me ake tsinana mini a gidan idan na zauna, yanzun ma tunaninki ne ya addabe ni, nake ta mafarkinki shiyasa na taho, kuma ina zuwa na tarar da dandazon mutane, ina dubawa na ga ke ce. Allah dai ya tsinewa wannan matsiyatan aljanun naki banzaye marasa imani" Za ta yi magana, Baba yayi sallama suka amsa, sai dai ya ja tunga ya tsaya, ganin wanda bai taɓa zato ba a gidan. "Kai imrana, uban me ka ke yi mini a gida? Me ya kawo ka gidana?" Tsuke fuska ya yi ya ce "Kamar yaya? Ya ka ke magana kamar wani shege ba kai ka haife ni ba? Gidan ubana na zo, kuma wurin 'yar uwata na zo" "Ban yi maka iyaka da gidana ba? Ki na me ki ka bari ya shigo mini gida?" Yayi maganar yana kallon mama. A ƙufule ta ce "Au to kokawa ka ke so na yi da shi? Ko saɓa shi zan yi na jefa waje, tun da kai ka dawo sai ka fita da shi ai" Ya sake kallon imrana ya ce "Ba magana nake yi maka ba? Ban hanaka zuwar mini gida ba?" Cikin rashin ɗa'a Imaran ya ce "Sai ka ce wani gidan kirki, to ka mayar da ni in da na fito, cikin uwata ta mayar maka da ni" Nana ta ce "Imarana Baba ne fa" "Shi ɗin, shekaru uku ba ka ga ɗanka ba, da haka yakamata ya karɓe ni komai girman laifin da na yi masa? Ba azabtarwa da ake yi mana ne ya tilasta mini barin gidan nan ba" Gaddafi ne ya shigo, bayan dawowarsa ya jiyo hayaniya daga cikin gidan ya shigo, domin duba abin da yake faruwa. Shi kansa mamaki ne ya kama shi, ganin Imran a gidan. Baba kamar ya fashe da kuka ya ce "Imrana ni ka ke gaya wa haka? Ka tashi ka fita ka bar mini gida na ce maka" "Idan na bar gidan shege nake, wallahi sai na gama kwanakin da zan yi. Ke Nana ga jakata nan zan je na dawo. Nana ta tashi ta ɗauki jakar, ta nufi ɗakinsu da ita, Baba ya daka mata tsawa ya ce "Bashi jakarsa ya bar mini gida" Cikin kuka Nana ta marairaice ta ce "Dan Allah Baba ka yi haƙuri, tun da ya ce idan ya gama kwanakinsa tafiya zai yi. Shekara uku ban ganshi ba, dan Allah ka yi haƙuri" "Au Nana kin fi son ɗan uwanki da ni ko? Amma yana sane da mu, ya kama gabansa ya tafi gantalinsa har shekaru uku, yana gararamba bai waiwayo gida ba, sai yanzu saboda ya mayar da ni ɗan iska zai dawo mini gida?" Imaran ya nufi Nana, ya karɓi jakarsa, ya kaita wani ɗan lungu ya ajiye, ya fice ya bar gidan. Shi kansa Gaddafi kasa magana ya yi, saboda tsagwaron zunzurutun tsageranci kawai yake iya ganowa a cikin idon Imran ɗin. ***** "Hajiya Sa'a aiki ya lalace fa" "Ban gane ba, kamar yaya?" "Akwai wani hatsabibin shaiɗani a tattare da yarinyar nan, ya lalata mana aiki gaba ɗaya. Ba a samu adadin jinin da ake buƙata a jikinta ba" Dafe kai Hajiya Sa'a tayi, ta ce "Yanzu mene ne abin yi, ka ce akwai sa'a a tattare da yarinyar yanzu babu wata dabarar kuma? Yarinyar ce wata irin majanuniya, har kaya na bayar a kai mata, babu yadda ban yi a sake kawo mini ita gidan yarinyat Safiyya ba, dama a can na ganta wai ta ƙi yarda. Ni kuma na abin na je gidansu ba, ba na son zargi da saka ido" "Aikuwa neman mafita ya ganki, domin wani baƙin sheɗani ne a tattare da ita, babu lallai ya bari wani ya raɓe ta, saboda wasu dalilansa, 'yar aiken tamu ma ya ƙona ta. Yanzu dole ki san yadda za ki yi, a sake ba ta maganin zamu sake tura

Chapter 7 of 13