ma menene, kar ku cutar da ita."
Cikin kuka Habbee tace "A'a ka barsu, na yarda su kashe ni indai akan alk'awarin da muka d'aukawa sarauniya ne."
A tsawace yace mata "Shiru, kina da buk'atar kasancewa a raye, ko kin manta kina da mahaifiyar da rayuwarta ta dogara a ta ki ne? Ita kan ta gimbiya ta fi buk'atarki fiye da ni."
A hassale mutumin ya daka musu tsawa ya saka yatsarshi zai danna kunamar bindigar a kan Habbee yana fad'in" Ku mana shir..."
Bai gama fad'a ba alburushi ya tashi kan shi sai fad'uwarshi kawai suka gani da kua sautin alburushin, k'ara Habbee tayi a take Utais ya jawota jikinshi suka duk'e, d'ayan kam da wani irin sauri ya kalli inda harbin ya fito, saidai tuni Umad ya kawo daf da shi, bai ankara ba kawai ya buga mi shi hannun bindigar a hanci ya b'arke da jini, a take kuma ya rik'e hannunshi mai bindigar ya karya wuyan hannun hakan yasa shi sakin k'ara, su Habbee na kallon ikon Allah sai gani sukayi ya kama wuyansa gaba d'aya ya murd'e ba tare daya barsu sun shaida wanda yayi ajalinsu ba ya turasu kiyama.
A matuk'ar tsorace suka shiga kallonshi sai Utais da yayi k'arfin halin tashi tsaye yana kallonsa, nunashi yayi da yatsa jikinshi har b'ari b'ari yake yace "Kai ne? Me ka ke yi anan?"
Gyara tsayuwarshi yayi tare da soka bindigarshi a mazauninta ya kalli Habbee yace "Mahma, ki gafarce ni kar ki fahimce ni ba daidai ba."
A tare kuma ya kallesu yace "Kun ga, ya zamar muku dole ku fad'i sirrin da kuke b'oyewa tsawon shekara ashirin, ko ku fad'a ko kar ku fad'a kun sani da dole zata zama shugaba, dan haka ban ga anfanin b'oyewar ba har yanzu."
Jiki a d'arare Habbee tace "Waye kai? Ya akayi kasan da maganar nan? Ko dai kai ma kana cikin masu nemanta?"
Fuskarshi a d'aure yace "Sanin waye ni ba shi ne a yanzu ba, ina so na san wacece gimbiya Zafeera?"
Girgiza kai Habbee tayi sai Utais da yace "Kai kuma a cikin wace tawagar masarautar ka ke?"
Wani kallo ya musu ya zura hannu ya fito da bindigar yana sake saisaita ta, wani shak'iyin murmushi yayi yace "Kar ku d'auka na taimake ku daga hannunsu ne, gani na yi basa buk'atarta tunda har zasu juri jin jayayya a kan ta, shiyasa na k'ara musu gudu."
Tsakiyar goshin Utais ua d'ora bindigar dan yasan mace ta fi rauni sannan ya kalli Habbee fuska a tamke ba alamar wasa yace" Zaki fad'a ko sai kin ga gawar mijinki?"
D'aga hannaye tayi tana girgiza kai tace" A'a, a'a na rok'eka kar ka kashe shi zan fad'a, zan fad'a maka."
" A'a Habbee, kar ki..."
Dungura masa bindigar yayi yace" Zan fasa kanka na sake jin bakinka."
Jiki na rawa Habbee ta nufi inda Umad ya b'uya d'azun a bayan labule, bud'a labulen tayi ta wareshi gaba d'aya, Umad na kallonta ya ga ta tura wurin ka rantse bango ne, amma sai gani yayi wurin yayi baya alamar dai mashiga ce, juyowa tayi ta kalleshi tace "Zo ta nan."
Kallon Utais yayi ya sake kallonta, nuna Utais yayi alamar ya fara wucewa, gaba Utais yayi sannan ya bishi baya ba tare daya d'auke bindigar ba, saida suka shiga dakin Habbee ta kunna hasken daya gauraye wurin.
Dauuuu! Hotonta da hasken d'akin suka daki idonshi a tare, zazzago idonshi yayi kamar zasu fad'o k'asa yana sake k'urawa sosai, gab d'aya jikinshi ya ji ya d'auki wata irin tafiyar tsutsa yayam yayam, sauke bindigar yayi daga kan Utais ba tare daya sani ba, baki da hanci da ido duk bud'e yana kallonta.
Ganin kamar baya hayyacinshi yasa Utais kallonshi yace "E ita ce, nasan abinda kake tunani kenan, ni ma ko da na ganka jiya na ji ban yarda da kai ba, sannan ina ji kamar na san fuskarka, sai dai na rasa inda na sanka."
A hankali Umad ya taka ya k'arasa gaban tabkeken hoton da aka manna a bango na takarda, rigar sanyi ne jikinta kalar bleue mai haske da dogon wando, gashinta mai yawan gaske da yasha gyara kalar maroon ya kwanta a gadon bayanta, d'aya hannunta a mik'e har yana gugar cinyarta d'ayan kuma ta rik'e damtsenta da shi ta kalli hoton.
Ba wai kyau ta yi a hoton ba da yasa ya k'ura mata ido, kawai mamaki da al'ajabin yanda dai ta kasance ita, *Ayam*, ita ce zab'abb'iyar nan? Ita ce lu'u lu'un da ake ta haurigiyar nema?
"Waye kai?" Habbee ta fad'a daga bayanshi, ajiyar zuciya ya sauke ba tare daya d'auke ido a kan ta ba yace "Tun ina shekara ashirin nake neman hanyar da zan bi na d'auki fansa a kan sarki Musail."
Juyowa yayi ya kallesu yace "Yau kuma gashi Allah ya kawo ranar, burina a kan Ayam mai girma ne, da kua nasan ita ce na fara had'uwa da ita ranata ta farko dana fara zuwa makarantar nan da nayi awon gaba da ita, ina tabbatar muku da saidai ku samu labarin b'atanta a karo na biyu."
Zaro ido sukayi da sauri Habbee ta durk'ushe k'asa tana kuka tace" Mun rok'eka dan soyayyarka da iyayenka kar ka kasheta, bata san komai ba ita bta da laifi, me yasa zaka d'auki fansa a kan ta madadin mahaifinta daya cutar da kai?"
Da sauri ya kalleta yace" Kasheta kuma? Na fad'a muku zan kasheta ne? Ai na nemeta ne dan na fi kowa bata kulawar data dace, rad'ad'in rashinta kawai nake so mahaifinta ya ji."
Gyara tsayuwa yayi yace" Kunga babu lokacin b'atawa a nan, ko ba komai mak'otan nan sun ji hatsaniyar data faru, a kowane lokaci yan sanda zasu iya zuwa nan."
Dafe k'ugu yayi da hannaye biyu yace" Aurenta zaku bani yanzu ni kuma na karb'a, idan kuma kun fi so mu bi ta d'aya hanyar shikenen, sai na koma makaranta na sameta."
Kallon kallo suka shiga yi wa junansu, mamakin lamarin shi da kula abinda ya zo musu da shi yasa suka kasa aiwatar da komai, d'aga kafad'a yayi yace" Shikenan tunda baku son ceto rayuwarta, amma ku sani a halin da ake ciki yanzu mahaifinta ya rufe sarauniya Juman a kurkukun Sabah, sannan sarki Wudar na garin Giobarh ma ya baza dakarunsa dan nemo masa ita, wad'annan ma biyu ne daga cikin su, haka ma mai Bukhatir wanda yake kamar d'a ga sarkin Misra shi ma nemanta yake ido bud'e yana son aurenta, kuma wannan a shirye yake ya kashe iyayensa ma saboda ita."
Rab'asu yayi zai wuce da sauri Utais ya rik'e hannunshi yace" Mun amince, amma a bisa sharad'i d'aya."
Kallonshi yayi ya jefa masa tambayar me ye sharad'in? Cike da kalar tausayi yace" Ka bamu tabbacin ba cutar da ita zakayi ba, ka rantse da abinda kake bautawa babu abinda zaka mata."
Murmushin gefen labb'a yayi yace" Na fad'a muku ba zan bari wani ba ma ya cutar da ita bare kuma ni, kawai ina so ne ta wa sarki Musail nisa yana ji yana gani har k'addarar mutuwarsa ta gilma ta hannunta kamar yanda ake farfagandan fad'a."
Jinjina kai Utais yayi yace" Shikenan mun amince, yanzu ya za'ayi ta zo nan dan mu shawo kan ta?"
Yar dariya yayi yace" Ni musulmi ne, kula zan aureta ne kamar yanda addini ne ya shar'anta min, zaka zama waliyinta yayin da zan wakilci kai na."
Kallon juna suka yi da Habbee sannan suka jinjina kai, zaune yayi akan shafafffen tiles d'in dake d'akin da babu komai ya nuna musu su zauna su ma, laluba aljijunsa yayi sai kuma ya kallesu yace" Kuyi hak'uri fa babu kud'i hannu na, makullin motar da ya zo asalin masaukinshi ya d'auka ya aje gabansu yace "Wannan makullin motata ce Ferrari, na bata ita a matsayin sadaki."
D'aukar makullin Utais yayi yana tsura masa ido, da sauri Umad yace "Karka damu fa, da zaran na d'auketa daga nan zan bata har da takardun motar, yanzu ka damk'a min amanarta ni kua na karb'a."
Kamar wasa Utais ya mik'awa Umad auren Ayam daga nan wurin da taimakawarshi, suna gamawa Umad ya kalleshi yace "Cin ta, shan ta, suturarta, kula da lafiyarta, addininta, zamar mata abokin hira, iliminta, duk nayi alk'awarin kiyayewa iya k'arfina, haka ma sauke nauyin saduwa."
Mik'ewa yayi yana fad'in "Insha'Allah ni zan zama uban jikan sarki Musail."
Mik'ewa sukayi su ma Habbee ta sake fad'in "Wai waye kai?"
Wani siririn murmushi ya saki ya juya ya kallesu yace "Umad, d'a ga sarki *Wudar*, *yariman Giobarh*."
Gaba d'aya cikinsu ya yamutsa suka shiga k'arewa kansu kallo, ganin babu wanda ya ce wani abu ciki alamar girgizar daya basu yasa shi cewa "Hankalinku ba zai d'auka ba dama, gaskiya ne mahaifina ma nemanta yake, amma manufar shi daban a kan ta, tawa ma manufar daban a kan ta, mace mai daraja Musail ya d'auke mana bayan ya rabani da d'an uwana da na fi so a duniya, shiyasa ni ma na d'auke masa 'yarsa mai daraja, abun farin ciki kuma shi ne daya yarda ita ce zata zama silar mutuwarshi, hakan zai bani damar jijjiga rayuwarshi na yi wasa da ita kamar biri da mai wasa da shi."
D'aga musu hannu yayi har ya kai k'ofa zai fita sai kuma ya juyo ya tarawa Utais hannu yace" Ara min makullin nan na mayar da kai na makaranta wajen amaryata."
Baki wangale jiki a sake Utais ya mik'a masa makullin sun rasa ta cewa, fita yayi daga d'akin yana fad'in" Ku gaggauta barin nan garin kafin yan sand su nemeku da tuhumar kashe mutanen nan biyu."
Daga haka ya fice a gidan mutane kam har sun fara taruwa a na hangen benen na su, suna dawowa daga doguwar sumar nan suka zabura suna kallon junansu, a gigice Habbee ta shiga fad'in" Me ka aikata haka? Me yasa ka amince masa? Yanzu idan fa ya kasheta?"
Rik'ota yayi yace" Kinga ki nutsu, da fari mu bar nan kamar yanda ya fad'a, idan ba haka ba kuma za'a kama mu."
Da sauri suka fita a d'akin suka nufi d'akin baccinsu dan d'aukar abubuwansu masu mahimmanci.
*To yar uwa kin dai gani, ga Umad zai koma makaranta da auren Ayam a kan shi, shin zai sameta a makarantar kuwa? Ya akayi ma mutanen nan suka zo daidai da zuwan Umad? Wa ya sanar da su har suka yi kok'arin riganshi zuwa? Ya Ayam zata yi idan ta ji wai Umad ya aureta? Ya ma zasu rayu tukuna a cikin abokan gaban nan? Idan kika biya na ki ne kawai zaki samu damar sanin wad'annan abubuwan, ki hanzarta ki biya na ki.*
*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:34 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._
_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._
_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._
Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.
_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._
_Bismillahir rahamanir rahim_
*12*
*Ayam* na komawa b'angarensu d'akin baccinsu ta shiga, kayanta ya cire tz d'aura towel ta shiga wanka, sa'ilin da ruwan ke sauka kan ta ta samu damar rufe ido, a lokacin tunanin mafarkinta ya dawo mata wanda su Deeyam su ka katse mata shi a daren jiya, haka kuma ta had'e abun ta ba tare data yarda kowa ya ji ba, d'an gashinta daya had'e da juna ta shiga murzawa tana mayar da shi bayanta tana gumtsar ruwa a bakinta tana tofowa, idonta a rufe suke k'am ta shiga fad'a a ran ta "Me mafarkin ke nufi? Ko dai mafarki ne kamar kowane? To amma me yasa matar ba tayi kama da wanda na tab'a sani ba?"
Da sauri ta bud'a idonta sakamakon jin motsi a d'akin, amma sai ta share ta ci gaba da wankanta kawai, dan tunaninta su Deeyam ne.
A tsanake ta k'arasa wankanta ta d'auro towel, hannun k'ofar ban d'akin ta kama dan bud'ewa, tana zuro k'afa d'aya ta fito ta k'arasa fito da k'afar d'aya tana fad'in "Ke! Me ya kawoki n..."
Wani duka aka mata a kai ba tare da imani ko tausayawa ba, ko shurawa ba tayi ba ta fad'i gure a sume inda kan ta ya b'alle da jini a k'eyarta, cike da jin dad'i da farin cikin zata cika burinta a kan ga Zafreen ta kece da dariya ta mik'e tsaye tana kallon k'akk'arfan matashin da suka saka ya musu wannan aikin, wanda saida suka jadadda mishi ya mata dukan da zata suma.
Tafa mi shi tayi da murna tace "Aikinka na kyau, nagode sosai."
Laika dake gefenta ne tace "Gaskiya ne, ni ma ki min godiya."
A wulak'ance ta kalleta tace "A kan wane dalili?"
Shiru Laika tayi saida Zafreen ta juya bayanta ta maida hankali ga Ayam dake yashe kwance, bata ankara ba Laika ta d'auki hoton dake aje gefen gadon Sabrine na ita da danginta, sai kuwa ta fasawa Zafreen shi a kai har saida madubin ya mutu a kan ta, take ita ma ta zube bayan ta dafe kanta tana k'ok'arin juyawa ta kalli Laika.
Kallon juna sukayi Laika ta ciro wata k'aramar waya a cikin rigar mamanta ta danna wasu lambobi ta d'ora a kunne, a tak'aice tace "Angama."
Tana aje wayar sai kuwa wata irin kara ta gauraye makarantar an danna na'urar dake nuni da idan wani had'ari ya samu musamman ma gobara, ai kuwa tuni hatsaniya ta kaure a makarantar dan kuwa sauran munafukan da ke tare da su Laika ne sukayi nasarar tashin zanga zanga a ciki, sai gashi sun fara farfasa abubuwa har da motocin malamai da ofisoshinsu.
Makaranta ta hautsine, duk jami'an sun yi iya k'ok'arinsu amma abun da gaske fin k'arfinsu aka yi, ana cikin hatsaniyar nan aka fitar da Ay da Zafreen ta bayan makaranta inda jirgi ya d'aukesu, Laika ma da tawagarta sulalewa sukayi suka bar makarantar, inda suka bar wanda basu ji basu gani ba a hannun jami'an makarantar suna son hukuntasu da laifin tayar da tarzoma.
Tunda ya doso ya ga wannan hayaniya da tashin hankali jikinshi ya bashi babu lafiya, yana fitowa daga dalleliyar ferrarin nan da gudu ya nufi inda yake tunanin samunta, bai damu da kowa ba da kuma abinda kowa zai fad'a.
Yana zuwa b'angarensu yayi sa'ar kicib'is da su Sabrine sun fito da gudu zasu fita, hannun Deeyam ya rik'o da sauri yace "Tana ina?"
Girgiza kai tayi tace "Mu ma ita muke nema, mun shiga d'aki amma bamu sameta ba."
"Shiiit!" Ya fad'a yana sake zubawa a guje ya juyo ya sake tambayar "Ina d'akin?"
Nuna masa tayi da hannu, bai jira komai ba ya bangaji k'ofar ta bud'e ya shige, turus ya tsaya kallon d'akin, da gudu ya k'arasa gaban tagar daya gani bud'e ya lek'a, tabbas ko ma su wanene ta nan suka fita da ita, ga alamu nan ya nuna har da sawayen takalmi.
Dafe gaban goshinshi yayi yace "Ya Allah! Su waye kuma yanzu?"
Wayarshi ya ciro da sauri ya shiga daddanawa ya d'ora a kunne, jim kad'an Haman ya d'aga, cikin tashin hankali ya nufi hanyar fita a d'akin yana fad'in "Haman kana ina? Akwai matsala fa."
Shi ma hankali tashe yace "Matsala kuma? Me ya faru?"
Da azama yace "Kai dai ka fad'a min inda ka ke zan zo na sameka."
Da sauri shi ma yace "Ina nan masauki na dana fad'a maka."
K'itt! Ya yanke kiran ya shiga takawa da sauri har ya k'arasa ga motarshi ya shiga ya sake barin harabar makarantar.
*Egypt*
Babban masaukin daya tanada dan wannan ranar yasa aka sauke mishi su, ya kashe kud'i masu azababben yawa dan kawai ya k'awata mata wannan gida, Zafreen ce ta fara bud'a idonta a hankali da suka mata nauyi har suka d'an fara kumbura, a hankali ta zura hannunta ta dafe k'eyarta saboda tuna abinda ya faru, a sanyaye ta furta "Wash!"
Muskutawa tayi ta tashi zaune sai kuma ta zabura da k'arfi saboda ganin Ayam kusanta kwance ita ma, juyawa tayi dan son ganin ko akwai wani kusansu, sai kawai ta ga kan ta a madubin drower da Bukhatir ya shak'ewa Ayam kaya da ita, saboda a bazata ta ga kanta sai ta saki yar k'arar data saka Ayam motsawa ita ma, tana bud'a ido ta sauke akan kwalliyar rufin d'akin wacce aka yi kamar da gwal aka yi ta.
Ganin Zafreen yasa ta yunk'ura da sauri ta tashi zaune, za ta yi magana sai kuma ta dafe kan ta da ta ji yana mata ciwo sosai, d'an kallon kanta tayi sai ta ga daga ita har Zafreen an nad'e musu kai da bandeji fari, kallon Zafreen tayi tace "Ina ne kika kawo ni nan? Ke ba fa na son iskanci kin ji ko, ki fita a harkata kafin na sake b'ata miki rai."
K'wafa tayi ta mik'e tsaye tana k'arewa kanta kallo ta madubin, towel d'in jikinta shi ne dai har yanzu, Zafreen ma mik'ewa tayi tace "Ke kinsan wacece ni? To ni ma ina son sanin inda nake."
Tsaki Ayam tayi ta nufi inda ta ga k'ofa da niyyar fita, kafin ta isa bakin k'ofar aka bud'o aka shigo, kallon kallo suka shiga yi da k' akk'arfan matashin dake cikin shiga ta alfarma, had'e fuska Ayam tayi ta dafe k'ugu tace" Wannan wane irin rashin mutumci ne? Ina ne nan kuka kawomu?"
Wani sanyayyar murmushi ya saki ya bud'e hannayenshi zai
rumgume ta, da sauri ta ja baya tace" A'a, kai mahaukaci ina ne? Waye kai?"
Ba tare daya d'auke murmushin dake kan fuskarshi ba yace" *Pr茅cieux*, embrasse moi, tu sais combien da temps je passe a attendre ce jour (mai daraja, rumgume ni mana, kinsan lokacin dana d'auka ina jiran wannan ranar)?"
Nunashi tayi da yatsa tace" Zan wanka maka mari idan ka kuskura ka tab'a ni."
Murmushi ya kuma saki ya juya ya kalli wasu matasa guda biyu dake gefenshi ya nuna musu Zafreen yace" Ku d'auke wannan daga nan ku kai ta b'angaren bak'i, wannan b'angaren na gimbiya ta Zafeera ne."
A wani yatsine ta kalleshi inda Zafreen tace" Ni kuma me yasa kuka kawoni nan? Waye kai ma?"
Gyara tsayuwarshi yayi yace" Sunana Bukhatir, mai jiran gado a Egypt."
Zafreen ce ta d'ora da" To ni kuma me na ke a nan? Ku maida ni makaranta mana, kasan ka mu su waye?"
A wulak'ance ya kalli Zafreen yace" Na sani, kuma a dalilin yawan fad'a da kike yi ne ya kawoki nan?"
Hanya ya nuna mata hanya yayi ba yanda ta iya dole ta shige gaba suka bi bayanta, kallon Ayam yayi yace" Ma pr茅cieux, zan turo hadiman da zasu kula min da ke yanzu, wannan shigar bata dace ki ba."
Juyawa yayi zai fita Ayam tayi kukan kura ta shak'o rigarshi dam a hannayenta tana kallon fuskarshi tace" Babu inda zaka je sai ka mayar dani inda ka d'auke ni."
Cikin matsanancin shauk'inta ya lumshe ido ya fara zura hannunshi akan cinyarta yana neman zurawa a cikin towel d'in, ido lumshe yace" Gashi kin kawo min kan ki, Zaf... Eera."
Da sauri ta ske shi ta ja baya tana hararenshi, wani shakiyin murmushi yayi ya juya ya fita, da sauri ta kama k'ofar zata bud'e sai ta ji a rufe take gam, tsaki tayi ta shiga zagaya d'akin tana sln sanin a ina take? Me ta zo yi a nan? Su waye kuma take tare da su?
Bud'e k'ofar da aka yi yasa ta saurin juyawa, matasan mata ne su biyu da kayansu iri d'aya a jiki, da girmamawa suka rusuna suna gaisheta, cikin fad'a ta nufesu tana musu yarensu tace "Wai ku su waye? A ina nake nan ne?"
Nuna musu k'ofa tayi tace "Maza ku bud'e min k'ofar nan."
Rusunawa sukayi a ladabce cike da tsoron kar su mata ba daidai ba ransu ne zai b'ace daga gurin mai gidan na su, d'aya daga ciki ce jikinta na rawa tace "Ranki shi dad'e yallab'ai ne ya umarcemu da mu tayaki shirya kan ki."
A tsawace Ayam tace "Ranki shi dad'en banza, wane banzan shiri ne zaku tayani? Mu saka ce ni aka fad'a muku? Ko dama can fil azal ku kuke min wanka ne? Mtsssss!"
Rikicewa sukayi suka rasa yanda zasuyi, cikin hushi ta nufi k'ofar ta sake kamawa zata bud'e, amma sai ta ji ta gam ta k'i bud'ewa, a tsawace ta kallesu tace" Zaku bud'e min ne wai ko sai na bajeku a nan?"
Da sauri suka fara riga rigan bud'e mata k'ofar, d'aya a ciki ce ta d'ora hannu a k'ofar tare da danne wani mab'alli dake k'asan hannun k'ofar, bud'ewa tayi ta kauce mata a hanyar, ai kam ficewa tayi da sauri tana k'arewa tabkeken falon kallo, tsaye tayi ta shiga bin ko ina da kallo dan gaskiya d'akin ya birgeta sosai, tab'e baki tayi ta ci gaba da tafiyarta ta nufi inda take ganin nan ne mafitar.
Zata bud'e k'ofar kenan aka bud'e daga waje, cak ta tsaya ta zubawa mai shigowa ido, saidai sab'anin d'azu da fuskarshi ke d'auke da fara'a da annashuwa, yanzu kam fuskar a had'e take tam, yanda ta lura yana ta kallon bayanta ne yasa ta d'an juyawa, matasan matan nan ta gani duk sun zube k'asa kawunansu sadde jikinsu sai b'ari yake.
Juyawa tayi ta kalleshi sai kawai ta ja tsaki ta kula juyawa ta kallesu tace "Ku mik'e tsaye kunji, me ye na wani rusunawa har k'asa gaban mutum d'an uwanku."
D'aya a ciki ce tayi k'arfin halin d'aga kan ta ta kalketa sai kula ta sunkuyar, muryar Bukhatir ce ta sa ta juyo sanda yake fad'in "Me na fad'a muku a kan ta?"
Jiki na kyarma d'ayar tace "Yallab'ai mun yi iya k'ok'arinmu amma ta k'i..."
Kashe fuskarta yayi da marin daya sakaya girgiza kamar zata fad'i kwance, a mugun hassale ya nunasu da yatsa yace "Ba k'ok'ari ba, abinda yasa na d'auko ku shi ne dan..."
Gauuuu! Ayam ma ta d'auke fuskar Bukhatir da mari, a wani irin razane matan da kuma dattijon ne dake bayansu suka kalleta, dan su kam yanda suke girmama Bukhatir ko sarkin Egypt basa girmamawa haka, idonshi da suka kad'a sukayi jajajir ya d'aga ya kalleta, ido cikin ido suka kalli juna babu mai alamar rusunawa.
Tunanin hanyar da zai fara hukunta ta yake, tunanin kalar muguntar da zai mata yake, hasaso hukuncin da zai mata yake wanda zaiyi sanadiyar ta fara kakkarwa sanda ta ji sautin muryarshi, amma ikon Allah sai ya ji ya kasa aiwatar da komai, sai ya ji wani tausayinta a zuciyarshi ya malayeshi sanda suka had'a ido, sai kawai ya d'auke hannunshi daga kuncin yana murmushin takaici, dan ko iyayenshi ba zai tuna ranar da suka tab'a marinshi ba, ba dan kar ya zama mak'aryaci ba sai yace tun na k'uruciya wanda bai san anyi ba ma.
Sake kallon fuskarta yayi yana lashe leb'enshi kafin yace "Idan har kina son barin nan sai ki fara bin duk wani umarnin da zan gindaya miki."
A zabure tace "Kai a wa da zan bi umarnin ka?"
Sunkuyar da kai yayi k'asa yana murmushi kafin ya kalleta yace