sanda na rok'eshi, kuma wanda ba ya gajiya da amsa buk'ata ta bare ya min gori wata rana, wannan ubangijin nake da buk'ata, shiyasa ban tab'a bautawa kowa ba."
Gyara tsayuwa Umad yayi sai ma ya rasa bakin magana, kallonta kawai yake ita kuma tana ganin haka ta kyab'e baki tace" Haka dayawa ke ta fad'a, wai ina tsoratasu, wasu ma sun daina kulani saboda launin ido na da kuma wasu abubuwan, kai ma idan ka tsorata zan saka a layin ragwayen maza."
A karon farko da murmushi ya sub'uce masa a gabanta, sosai yayi murmushi har hak'oransa na bayyana a fili, ganin haka sai ita ma ta saki murmushin tace" Karka damu malam, ba zan yarda kowa ya ji major Umad matsoraci bane."
Iskan daya fara kad'awa mai k'arfi had'e da k'ura da kuma k'arar jirgi a sama yasa Umad d'aga kan shi, ita ma d'aga kan tayi sama suna kallon jirgin helicopter d'in, da kai ya mata alama yace" Muje."
Zaro ido tayi tace" Kai ka kira jirgi? Ina zamu je?"
Kallon shegantaka ya mata yace" Ba zaki kike son gani ba?"
Jinjina kai tayi alamar e, saka gilashin shi yayi a ido hakan ha k'ara fito masa da kyawusa, hannun hagu ya mik'a mata yace" Muje to."
A hankali ta d'aga siririn hannunta na dama ta d'ora akan tafin hannun Umad, da k'arfi ya jimk'e hannuta sakamakon shock d'in da ya ji irin na ranar, sai ya bar hakan a matsayin dan bai cika tab'a jikin mace ba tunda ai ita bata ji komai ba a ganinshi.
Fuskarta ya kalla da kyau yana sake nanato kalaman malaminshi akan yarinyar daya fito nema, musamman inda yake fad'in _"Akwai b'oyayyar jarumta a tare da ita, abinda ya cancanci ya bata tsoro ba shi ke tsorata ta ba, wanda kuma kai zai iya kayar maka da gaba, sai ka ga ita abin ado ne a gareta..._"
Tabbas ya fara jin wani abu a kan yarinyar nan, inba haka ba ta ya zata amince da shi haka a sauk'ak'e, lallai da ita xe wacce yake nema sai yace mata "Jarumtarki ta ban haushi, amma kuma raunin da kika nuna na yarda da ni ya birgeni."
Jan ta yayi suka nufi inda jirgin ya tsaya, suna isa k'ofar dama a bud'e take, taimaka mata yayi ta fara shiga sannan ya shiga shi ma, d'amara suka d'aura a k'ugunsu, tashin jirgin aka fara su kuma suka fara k'ok'arin saka abun sauraron magana a kunnayensu saboda basj damar jin maganar juna ba tare da k'arar iskan ta kawo cikas ba.
Zura kan ta tayi ta d'aya k'ofar tana hangen k'asa ta taga, murmushi ta shiga saki ita kad'ai musamman yanda ta ga bishiyu na kad'awa su kuma suna k'ara haurawa sama.
Kafad'arta ya daddab'a tana juyowa yace "Kin tab'a shiga jirgi ne?"
Girgiza kai tayi tace "Ban tab'a tsayawa gani ga shi ba sai yau."
Girarshi d'aya ya d'aga sama da mamakin kuma shi ne babu tsoro a tare da ita? Tafiya suka yi mai nisa saidai duk a cikin dajin suke, saida suka kai inda aka saka allon sanarwa dan daga nan zuwa inda mutum zai k'ara a cikin had'ari zai yi shi, dan dabbobi ne iri iri masu cutarwa a wurin.
Jami'in tuk'in jirgin ne yace wa Umad "Yallab'ai a shirya sauka mun iso."
Kallonta Umad yayi yace "Kin shirya?"
"E yallab'ai." Ta fad'a da karsashinta, jinjina kai yayi sannan ya ba matuk'in umarnin sauka, saida ya tabbatar sun tsaya sannan ta ga ya zura hannu a k'asan kujerar da yake zaune ya d'auko bindiga, wacce ke k'ugunshi ta aiki ya aje ya duba alburansan waccen ya d'auka, d'anata yayi ya saita mata komai tana kallonshi baki sake, yanda yake wasa da bindigar sai ta ji ya birgeta, kallonta yayi yana shirin fita yace "Mu je."
Shi ne ya fara fita, za ta diro shi kuma daidai ya juya tare da rik'o k'ugunta da duka hannayenshi bayan ya soka bindigarshi a k'ugu, cak ta ji ya d'agata ya sauko da ita, kunya ce ta rufeta dan hakan bai tab'a faruwa da ita ba, kaa had'a ido tayi da shi haka shi ma sai ya ji kamar yayi gaggawa a lamarin.
Bindigar ya ciro sannan ya kalleta da kulawa ya shiga mata kurmanci wanda dama dole suke koya saboda irin haka, dan wata dabbar sauti zata ji ta farmake ka wata kuwa sautin tafiyarka ma, jinjina kai Ayam tayi dan ta fahimci abinda ya fad'a mata wato ta biyoshi a baya a hankali sannan ta kula.
Cikin sand'a suke tafiya Umad na gaba tana binshi a baya sai kalle kalle suke, k'wari da k'ananan dabbobi kam suna ta had'uwa dasu wanda ba sa cutarwa, suna cikin tafiyarsu a hankali cikin ciyayi koraye ya mata alama da hannu cewa ta tsaya. Tsayawa kam ta yi tana lek'awa ta ga me ya gani, a wuyanta ta ji motsi daf da hular kan ta, da sauri ta zura hannu da niyyar d'an sosawa, tudun abun da ta ji mai tabbatar mata da k'waro ne yasa bata ankara ba kuma bata shirya ba ta kwamtsa k'ara iya k'arfinta.
*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:33 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._
_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._
_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._
Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.
_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._
_Bismillahir rahamanir rahim_
*9*
Da fari kam zabura Umad yayi dan abun bai yi tsammaninshi ba, bugu da k'ari kuma k'arar a cikin kunnenshi na hagu ta sauka, amma yana ankara a cikin salo da k'warewa yayi azamar had'ata da bangon da suke tsaye kusanshi, hannu d'aya yasa ya rufe mata baki d'aya hannun dake rik'e da bindiga kuma ya zagaye k'ugunta da shi, duk da idonshi cikin gilashi suke amma yanda tayi shiru dole suka k'urawa juna ido, d'an motsa wuyanta tayi tana lumshe ido, a hankali ya d'auke hannunshi daga bakinta ya mayar kan wuyanta, yana jin ya tab'a abu yayi k'ok'arin cireshi a jikinta, gam ya ji alamar k'waron mai kakkausan k'afafu ne da tsini hakan yasa ya mak'ale mata a dogon wuyanta.
Yatsu biyu yasa still idonshi cikin na ta duk da ita ba wani ganin na shi take sosai ba, tana dai hangen kamar ita yake kallo kuma kamar ba ita yake kallo ba, cire k'waron yayi tamkar fara ce ta lak'e mata a jiki.
Wani numfashi ta sauke a take idonta suka kawo ruwa dan koma dai menene tabbas ya cijeta, lumshe ido tayi ta sauke kan ta k'asa, k'waron ya nuna mata cikin masifa yace "Dubi, k'waron da zai iya wucewa ta hudar hncinki, shi ne fa ya hau jikinki kika shaidawa duka jejin nan cewa mun shigo, amma a haka kike cika mana baki ke zaki kike son gani."
Kallon k'waron tayi bak'i wulik da shi kamar suffar gizo kuma kamar hankaka, marairaiccewa tayi tace" Sorry."
A tsawace yace"Shet up, kika sake min maganar zaki wallahi sai na fasa bakinki da hannun bindigar nan."
Turo baki tayi gaba alamar rashin jin dad'i, kafin ta shirya yin wani abun Umad ya fizgi hannunta da k'arfi suka juya dan komawa inda suka fito yana fad'in" Dole muyi gaggawar barin nan, dan hankalin kowace dabba yanzu ya tashi da tunanin an shigo farautarsu, dan haka su ma zasuyi k'ok'arin farautar rayuwarmu, ni kuma ban shirya rasa raina tare da ke ba."
Bin shi take kamar zata fad'i k'asa dan sosai yake jan ta, ba tace komai ba face biyarsa da take kawai, sunyi kusa da inda allon sanarwar nan yake na a kula akwai had'ari a nan daga cikin ciyayin suka ji motsi, cak ya tsaya tare da sakin hannunta, d'ora hannunshi yayi a kan k'irjinta da niyyar mayar da ita baya, dan ya fi ta tsayi sosai a iya d'agawar da ya ma hannunshi dole kan k'irjin zai sauka.
Da k'arfin tsiya ta buge hannunshi tare da saka hannayenta ta rufe nonuwanta tana fad'in "Me ye haka?"
Kan shi kawai ya juyo ya kalleta ya kuma kalli k'irjin, dan shi sam bai ma san me ya tab'a ba bare ka tabbatar da niyyarshi, juya kanshi yayi ya sakar mata tsaki yana girgiza kai yace "Allah tsare ni, b'erayen?"
Cike da masifa ta shiga gatsina baki tana fad'in "B'erayen, amma a hka suka birgekahar kake k'ok'arin yi min..."
Kallon daya mata yasa tayi shiru tana sinne kai, matsowa yayi daf da ita yace "Nake k'ok'arin yi miki me?"
Yanda ta sake soke kai k'asa yasa shi sakin murmushi a ran shi yana jin kanshi na huruwa sama na farin cikin ya tsorata ta ta k'i fad'an abinda tayi niyya, juyawa yayi yana sake maida hankalinshi kan sautin nan da yake ji, a bazata ya ji muryarta tace" Zaka min rashin d'a'a mana."
Lumshe ido yayi tare da juyowa, da yatsu biyu ya mata kurmanci ya nuna mata" Ki maida hankali, akwai abinda ke tahowa ta nan."
Jinjina kai tayi fuskarta fal tsoron abinda ya fad'a d'in, yanda yake sand'a ita ma haka take yi tare da ciro bindigarta ta kashe jiki ta rik'e da kyau, sautin k'ara kusanto su yake, kamar numfashi had'e da gurnani, abinda ya sani kawai shi ne idan ma dabba ce to babba ce daga yanda k'ananan tsirrai ke motsawa, duk da ba'a jin sautin tafiya, amma sai dukansu jikinsu ya basu lallai fa kamar ana sauke takon k'akk'arfar k'afa a zuk'atansu.
Kamar almara ko a mafarki sai ga k'osasshen zaki ya b'ullo daga sark'ak'iyar itacen da duwarwatsu, tuni Umad ya zaro ido dan wallahi a take ji yayi wannan zakin shi ne wanda aljanar nan ta fasalta, dan ba k'arami bane wajen girma haka ma a shekaru, dan fuskarsa ta nuna haka, lalubo hannun Ayam yayi da ta lek'a ta kafad'arshi, tana ganin zaki ta saki fara'a cikin jin dad'i tace "Oh my God, lion."
Da azama ya juya ya fuskanceta ya d'ora yatsarshi a labb'anshi yace "Shiiiiiii."
Juyawa yayi ya kalli zakik dake tafe a tak'ama da gadara, ga dukkan alamu ihunta ne ya fargar da shi cewa an shigo komarshi, ko kuma dai shawagi ne ya ke amma ba farauta ba.
Had'e yawu yayi ya laluba a hankali ya cire gilashinshi ya soka a gaban rigarshi mai mab'allai, sake damk'o hannunta yayi da niyyar su ratsa ta b'angaren hagunsu su zagaye zakin su fita dan su tsira da ransu, sai dai suna fara takawa kamar sunanshi ne suka kira sai kuwa ya juyo ta bangaren da suke.
K'amewa Umad yayi ya rintse ido yana furta "Hasbunallah wani'imal wakil."
Haba wa? Ai sai zakin nan yayi wata kukan kura, gudu cikin k'arfi da salo ya yo kan su, Umad na ganin haka ya ja hannun Ayam da gudu, tsaf ta kubce hannunta daga na shi ta tsaya tare da juyowa ta fuskanci zakin.
Umad dya tsaya ya ga me ya tsayar da ita yana ganin zakin nan ya nufo kan ta cikin gurnani bakinshi a bud'e, bai san me ya aikata haka ba, a kan wani dalili ya ji zai iya fansar rayuwarta, shi dai ji yayi kawai ba zai iya bari komai ya sameta ba, dan haka yayi gaggawar tureta gefe ya tsaya inda take, bindigarshi ya saitawa zakin ya rik'e da kyau yana jiran ya ga me zai faru.
Zakin nan na zuwa bai b'ata lokaci ba wajen nuna izzarshi, wani irin tsalle ya daka sama sai kuwa a jikin Umad bayan ya saki duka faratunshi, tare suka fad'i inda bindigar ma tayi ta kan ta, wata irin mirginawa zakin yayi y ske mik'ewa tsaye, Umad ma duk da bala'in dukan nan da yaji bai hanashi jarumtar tashi ba.
Sake shirin kai farmaki yayi a karo na biyu, saidai ina gaba da gabanta, tuni Ayam ta shiga tsakanin Umad da zakin nan kan gwiwarta tana d'aga masa hannaye alamar sun yi saranda sun mik'a wuya, ai Umad yanda kasan idonshi zasu fad'o k'asa haka yayi dan al'ajabi, kallon zakin yake irin yanda ya tsaya cak suna kallon juna ita da shi.
Juyawa yayi ya hangi bindigarshi, gyara zamanshi yayi zai rarrafa ya d'auka Ayam tayi saurin juyawa ta kalleshi, da hannu ta masa alama a hankali tace "Shiiiiiii!"
Da mamaki bakinsa a sake yace "Kuuuutt! Ni d'in?"
K'uro idonta tayi sosai ta d'ora yatsa a labb'anta cikin rad'a tace "Kayi shiru mana, na maka alk'awari ba zan fad'awa kowa kana tsoronshi ba."
Juyawa tayi ta kalli zakin, a hankali ya dinga takowa har saida ya tsaya gabanta, lumshe ido tayi dan ita kan ga zuciyarta rawa take tana jin me ye a jikinta da yasa zakin ya daina hargagin son halakasu? Me ma yasa tayi tunanin shiga tsakaninshi da Umad ne?
Gashin da ta ji na tab'a jikinta yasa ta bud'a ido, cike da d'ard'ar da tsoro ta kai hannunta na hagu ta shafa gashin nan, sai kuwa zakin nan ya sake kwantar da kan shi a jikinshi, dariya ce ta sub'uce mata ta juya ta kalli Umad tana fad'in "Yallab'ai ka gani, na tab'a shi yau, burina ya cika."
Sake juyawa tayi ga zakin ta ci gaba da shafa shi har zuwa bayanshi, kallon idon juna suke ita da zakin. Umad kam mik'ewa yayi tsaye ya d'auki bindigarshi, zai saka a k'ugunshi ya ji Ayam tace "Sunana Ayam, kai fa?"
K'ura mata ido yayi har ta kalleshi ta nunawa zakin tace "Malami na ne, sunan Umad."
Da sauri Umad ya k'arasa ya gareta ya finciko hannunta yana fadin "Tashi muje na maida ke inda na d'auko ki, rayuwa cikin mutane bata kamace k..."
Wata zaburowa zakin yayi ganin yanda ya finciki Ayam, tuni suka ankara Ayam ta dakatar da shi da hannu Umad kuma ya k'urawa zakin ido, sake durk'usawa tayi kan gwiwanta ta marairaice tace" Zan tafi ka ji, abokina ne shi kar ka cutar da shi, zan dawo wani lokacin."
Mik'ewa tayi bayan ta sake shafa gashin nan na shi ta bi bayan Umad, sauri take kamar yanda shi ma yake yi hankalinsa a matuk'ar bala'in tashe, idan kai na bindiga ya fashe to tabbas na shi zaiyi kowane lokaci, gashi wata zuciyar na ta fad'a masa ita ce, amma sai ya kawar da zancen saboda tunanin ta ya zai sameta a b'agas haka? Sannan yanda aka suffanta kyawunta wannan ko kama k'afarta ba tayi ba, da ma dai kyawunta ya kai na Zafreen zai iya yarda.
To amma kuma wasu halaye da d'abi'unta abun tsoro yake son fara bashi, sai kuma yanzu ya fara gasgata canal Jacob da yaga ko fuskarta baya kalla.
Sautin dariyarta da yaji ne yasa shi juyowa a hankali, wani k'arami kuma mai kalar shud'i da yellow d'in tsuntsu ne ya gani a tafin hannunta tana wasa da shi kamar tana masa cakulkuli, da azama ya dawo gareta ya d'auki tsuntsun ya d'aga hannunshi sama ya tashi, a karan farko daya tab'a ta da niyya kenan, hannayeshi biyu ya sa ya tallabi fuskarta suka kalli juna.
Muryarsa na rawa kamar wanda ya kid'ime yace "Ke! Kalle ni da kyau, ki wa Allahn daya hallice ki karki haukata ni, ki fad'a min gaskiya Ayam, who the hel are you?"
Yanda ya matse kumatunta yasa bakinta kumburowa, cikin shagwab'a ta kalli idonshi ita ma tace "Ni ce, Ayam... Utais."
Cikin jin haushi ya saketa ya juya yace "Merde."
Murmushi tayi ta bi bayanshi saboda ya ci gaba da tafiyarshi, k'asa ta shiga kallo tana tafe tana rausayarta, tsautsayi yasa idonta sauka akan wata k'atuwar wahainiya kore shar da ita, bud'e hannayenta tayi ta sunkuya kamar zata rumgumeta tace "Wow! Wahainiya."
Da sauri ya juyo ai kuwa da gudu ya arta ya damk'ota dan tayi niyyar bin bayan wahainiyar, yana nasarar cabkar k'ugunta ya cirata sama ya labta a wuyanshi, cikin takon k'arfi da sassarfa ya shiga takawa har saida ya isa gaban helicopter dake tsaye yana jiransu, yana k'arasawa matuk'in ya fito yana tambayarsa lafiya? Dan ya d'auka ko ta samu rauni ne, da hannu ya masa alamar ya tashi jirgin kawai, yana zuwa jefata yayi ciki shi ma ya shiga ya zauna.
Jingina yayi a kujerar ya lumshe ido, a sanyaye ya shiga sauke numfashi wani bayan wani, saida suka daidaita a sama sun fara nisa ya bud'e idonshi, d'an juyawa yayi ya kalleta jin shiru, gabanshi ne ya fad'i sakamakon had'a idon da sukayi, ta masa k'uri da ido ta fito da 'yan hak'oranta kawai tana kallonshi.
D'auke kan shi yayi a kan ta ya d'ora hannunshi kan cikinshi, a hankali ya fara b'alle mab'allen rigarshi saida ya ciresu tas, singlet d' in shi kuma jini ne ya fara b'ata ta sakamakon faratun zakin nan da suka tab'a shi.
Tana ganin haka ta sake zaro ido tace "Wayyo Allah, jini kake zubarwa."
A tsawace yace "Shiru dallah."
Gum ta ja bakinta ba ta sake cewa uffan ba, amma kuma idonta akan shi suke, duk wani motsinshi biye take da shi, yana k'ok'arin cire rigarshi ta kakin shi suka sake had'a ido, cike da takaici yace "Wai malama mi ye na k'ura min ido? Ki kalli gabanki mana."
Ba tare data d'auke idonta a kan shi ba tace "Tambayoyi gareni, ina tunanin ko ba zaka iya amsa min su bane."
A hassale yace "To kuma da kika san haka me yasa zaki zuba min wannan idanun na ki masu kama da *dutsen lu'u lu'u*."
Wata kyakyawar dariya tayi tare da cire hular kan ta gajeran gashinta daya fara tsirowa ya bayyana tace "Da gaske?"
Girgiza mata kai yayi ya k'arasa cire rigarshi, zaro ido tayi tana kallon k'wanjinshi, da gayya ya sake juyawa ya kalleta, cike da gatsali yace "Daina kallo na, ko na birgeki ne?"
Da sauri ta kau da kan ta tace "God forbid, me zan ci da kai ni kuma?"
Kallonta yayi galala yace "Amma wace gulma ta kai ki d'akina daren jiya?"
K'yak'yabta ido tayi tace "Kawai na je tantancewa ne."
K'ala bai ce mata ba sai ma mayar da rigarsa da yayi, haka har saida suka sauka inda suka rabu da sauran d'aliban, tuni sun samesu a wurin duk suna jiransu, tuni su Deeyam suka kewayeta suna tambayar ta ko ta ga zaki ? Da farin ciki ta shiga labarta musu har suka shiga mota dan komawa su ma suna fad'a masa abinda ya faru ta b'angarensu.
*Tankara*
A sauk'ak'e Haman yayi nasarar samun gidan Ruman, bayan sun gaisa kuma ya fad'a mata shi jami'i ne, cikin rashin fahimta da tsoro tace "To amma yallab'ai me kake nema daga gareni? Me na yi?"
A ladabce yace "Baba ina neman wata mata da miji ne, kuma an tabbatar min da kina da alak'a da su."
Da mamaki tace "Su wa kenan? Kuma wa ya fad'a maka haka?"
Murmushi yayi yace "Habbee da Utais."
A take jikinta ya d'auki kyarma tsabar tsoro da fargaba, neman sunkuyewa tayi daga tsayen da take, cikin in'ina da tashin hankali tace "Kai kuwa wa ya fad'a maka na san su? Su waye ma su d'in?"
Dariya yayi wacce ta fitoda kyanshi ya mik'e tsaye, cike da isa yace "Baba gashi kin fara d'orani a mizani, tambayarki ta farko ita ta nuna lallai kin san su, tambayarki ta biyu kuma ta nuna ba gaskiya kika fad'a ba."
Gyara tsayuwa yayi yace "Shin Baba zaki iya fad'a min inda zan same su? Ko kuma sai na..."
Bindigar k'ugunshi ya fito da ita yana shafawa, hakan ya k'ara rud'ar da ita sai ta rikice ta fashe da kuka, durk'ushewa tayi k'asa tana rok'onshi "Ka yi hak'uri zan fad'a maka, amma ka min alk'awarin ba zaka cutar da 'yata ba."
Da tsananin mamaki yace "Wacece' yar ta ki? Habbee?"
Jinjina kai tayi alamar e, jinjina kai yayi yana murmushin mugunta a fan shi yace "Lallai gimbiya Juman, wato kafin ta b'atar da 'yarta saida ta bi ta goge duk wani sawu da za'a bi dan kamata."
Kallonta yayi yace "Ina jinki fad'a min? Babu abinda zai same ta."
Mik'ewa tayi tana share hawaye tace "Larhjadin, bayan kasuwar *Buffar*, gida mai lamba 115."
Dad'in daya kama shi ne yasa shi rumgume tsohuwar ya sumbaci kuncinta, ko ba komai zai samu hutu da nutsuwa idan ya kammala aikin nan, sakinta yayi ya juya cikin sauri ya fita yana fad'in "Nagode Baba."
Wayarshi ya ciro a aljihu ya kira lambar Umad, sai dai bai sameshi ba dan lokacin suna jeji, duk da haka bai hak'ura saida yayi ta jarabawa, a k'arshe dai wani masauki ya samu mai kyau ya kama d'aki dan ya jira wayewar garin gobe tunda har magriba ta wuce.
*Larhjadin*
Keb'entacciyar asibitin makarantar Umad ya kai kan shi sakamakon yakushin da zakin nan ya masa, cikin k'warewa da nagartattun kayan aiki aka dubashi tare da yi masa allurar kashe duk wani dafi, kuma dama sam baya jin ciwon yakushin kamar yanda yake jin bala'in ciwo a jikinshi inda zakin nan ya daka masa k'afafunshi, lallai ya yarda k'afafun zaki zasu iya kashe mutum ma.
*09:30* Ayam ta shigo d'akin da aka kwantar da shi, dan bata san me ke faruwa ba saida Sabrine suka fad'a mata, su ma dan sun tafi karb'an magani ne na zazzab'i, kayan bacci ne a jikinta amma ta d'ora rigar sanyi a kai wacce zaka d'auka ta mata yawa ne, amma haka tsari da zubin rigar yake.
Saida ta je ta tsaya gaban gadon kdonshi rufe alamar bacci yake, rumgume hannayenta tayi tana kallonshi, ta jima tsaye tana k'are masa kallo tana doka murmushi, daga bisani kuma hannunta ta d'ora akan hannunshi dake kan k'irjinshi.
Kamar wacce ta daddab'ashi a take yaji wani yanayi a cikin baccinshi, tsam ya bud'e idonshi ya sauke akan fuskarta, da sauri ta d'auke hannunta tace "Am.. Sannu, ya jikinka?"
Muskutawa yayi ya tashi zaune da kyau yana kallon fuskarta, ba tare da yanayin wasa ba yace da ita "Me ya kawoki nan?"
Kamar marar gaskiya tace "Na zo duba jikinka."
Kallon tuhuma ya mata yace "Kin zo duba jikina ne amma kuma kike shafani haka?"
Baki bud'e tace "Lahhh! Ni fa kawai dubaka na zo na yi."
"Saboda kinsan dalilinki nake kwance a nan kenan?" Ya fad'a yana tsareta da ido.
Kawar da kan ta tayi ta turo baki a ran ta tace "Masifaffe."
Wani irin kallo ya mata kamar ya karanta me ta fad'a a fuskarta yace "Me kika fad'a?"
Da sauri ta kalleshi tace "Yallab'ai na ce ba, ni kam me yasa ka cika masifa dayawa ne? Ko sau d'aya ka jaraba yin wuni d'aya tak ba tare da b'acin rai ko had'e fuska ba mana, murmushi zai maka kyau sosai."
A hankali ya juyar da kan shi kan d'an teburin masu jinya inda ya d'ora bindigarsa, d'ora hannunsa yayi a kan bindigar ya kalleta cike da gadara yace" Zaki