hudashi zuwa wuya, wani huci ya shiga saukewa ya mik'awa Adah wuk'ar yana fad'in "Duk wanda ya yi k'ok'arin hanani kasheta to shi ma kasheshi zan yi, sarkin yak'i."
Da sauri Adah ya amsa yana rusunawa, juya baya yayi yace "Ka d'ebi wasu daga cikin mayak'anka ku nufi Tankara, idan tana nan ku taho da ita, idan kuma hakan ya gagara ku sanar da ni, ni zan je har inda take sannan na kasheta da hannu na."
Amsawa yayi da "Angama Ranka shi dad'e." Kafin ya kama hannayen gawar nan ya jashi k'iiiii har ya fice da shi a falon.
*Larhjadin*
Ba wani yammaci bane sosai, amma dake makarantar akwai wadatar shuke shuke sai tayi luf sai iska mai sanyi dake kad'awa, duka d'aliban mata suna tsatsaye bakin mota inda dreban ke jiransu, suna cikin shiga ta kakin ma'aikatan gandun daji, riga da wando kalar shud'i da babu kwalliya, saidai daga yanayin d'inkin da wasu ado da akayi ga rigar zai shaida maka masu tsaron k'asarsu ne, bak'ak'en huluna ne a kan su sun daidaita musu zama cikin k'warewa, ga kuma takalminsu bak'ak'e k'afa ciki sai k'yalli suke sun d'auresu tamau da d'amara.
Gyara tsayuwarta tayi tana murgud'a baki tace "Wai malamin nan bai san lokutan karatu dana hutu bane? Ya zai shanya mu a nan?"
Sergent d'in colonel ne ya tsaya gabansu cikin d'aga murya yace "Ayam Utais, yallab'ai canal (colonel) na san ganinki yanzu a ofishinshi."
Waina idonta tayi ta kalli Deeyam da ita ma ke kallonta tace "Wai ni sai yaushe ne canal d'in nan zai barni na huta?"
Murmushi Deeyam tayi tana rik'e d'amarar k'ugunta a hannu tace "Ranar da ke ma kika barshi ya huta, ba ke kullum 'yar masifa ba ce."
Turo baki tayi gaba alamar rashin jin dad'i sannan ta nufi hanyar tafiya tana fad'in "Sai na je kuma yayi ta sadda kai k'asa kamar ya ga gyatumarshi."
Yanda aka mata d'inkin daidai da zubin hallitarta yasa kayan suka karb'eta da kyau, duk da bata da wasu mazaunai na a zo a gani, amma dake ta d'aure da zanzaro sai hakan ya basu damar juyawa.
Motocin data gani da suka amsa sunansu masu bala'in kyau da kuma shek'i yasa ta k'ura musu ido a ranta ta ayyana "Ko dai bak'i a ka yi?"
Suna kai wa bakin ofishin ya ja ya tsaya ya nuna matata shiga, kallon shi tayi t tab'e baki sannan ta kama hannun k'ofar ta murd'a, k'afa d'aya ta fara zurawa ta shiga a matuk'ar nutsuwa da kuma wani irin kwarjini da izza, tana k'arasa shiga kamar dai mutanen ciki ita ma sai ta zuba idonta tana k'are musu kallo.
Canal dake kujerarshi ya had'e hannaye wuri d'aya sai rarraba ido yake, amma tana shigowa ya mayar da hannayenshi k'asan teburin ya koma kallon takardun gabanshi kamar wanda ya ga aljana. Waziri Khatar kuma na kujerar dake fuskantar ta canal d'in fuskarshi a matuk'ar had'e yanda zta gigita mai kallonta, ga shigar da yayi ta alfarma ita kad'ai zata sa ka rusuna mishi ka d'auka sarkin ne da kanshi.
Sai Zafreen dake tsaye bayan wazirin ta rumgume hannayenta ta k'urawa Aya d'in ido. Sai kuma wanda zata iya cewa shi bata san me ya kawoshi nan ba, dan in wannan yana zaune ne saboda marin da ta wa Zafreen, to shi kuma fa? Yallab'ai Umad kenan, gashi dai cikin kakinshi a shirye tsaf, amma kuma ya barsu suna jiranshi har yanzu gashi za'a zo a nemi b'ata mata rai.
Yanda ta tsaya gaban tebur d'in yasa canal d'aga kai ya kalleta, suna had'a ido kawai sai ya ga kamar hararanshi ma take, da sauri ya mayar da kanshi ga d'aya daga cikin fadawa biyun da Khatar ya shigo da su yace "Rufe k'ofa."
A ladabce bafaden ya rufe k'ofar a lokacin ta juya ta kallesu sannan kuma tasan da zamansu, maida kallonta tayi ga canal d'in tace "Yallab'ai ka ce kana son gani na."
D'aga kai yayi ya kalli fuskarta, amma abinda Umad dake zaune yana tsare kowa da ido ya lura da shi shine yanda yake ta yawo da idon na shi ya kasa tsayar dasu a kan fuskarta bare ya kalli idonta, hakan yasa shi dasa alamar tambaya aka wannan lamari.
Cikin taushin murya yace "Ayam, me ye dalilin da yasa kika mari gimbiya Zafreen? Shin ban fad'a miki ki fita a sabgarta ba?"
Gyara tsayuwarta tayi ta juya ta kalli Zafreen d'in, sai kuma ta kalli waziri daya cika fam yana jiran fashewa, tab'e baki tayi ta kalli canal tace "Tun ranar ai na fita a harkarta, ita ce ta sake shiga hurumi na."
Wata irin tsawa ya daka mata tare da buga tebur din ya mik'e tsaye yana fad'in "Ke d'in banza, wacece ke da zaki ja da ita? Kinsan matsayinta a makarantar nan kuwa? To ko yanzu ta so z..."
A hassale ta kalleshi gaba da gaba ta zazzaro idon ta wanda launin shud'i yayi wani kore-kore ga mai kallonsu, cikin tsiwa da fad'a tace "Waye kai da zaka min tsawa? Uba na ne kai ? Na sanka ne? Ka zo d'aukar mata fansa ne? To ina jira kayi yanda zakayi da ni."
Sake k'ura masa ido tayi ta nunashi da yatsa manuniya tace "Malam murya k'asa, ni ba kowa bace amma haka kawai nake jin na tsani a d'aga min murya, kuma a jinina nake jin kamar ina da izzar da zan hukunta duk wanda ya min hakan cikin d'anyan kai."
Juyawa tayi ga canal, tuni ya gyara zamanshi yana ta k'yak'yabta ido, tabbas da yana da addinin musulunci a lokacin daya shiga karanto addu'ar tsari da shed'anu, sam bai yarda da Ayam dan lamarinta tsoro yake bashi, shi fa babu kamar ma yanda jikinshi ke d'aukar b'ari idan ya hangeta kawai, har ya kan tambayi kan shi k'awayenta da sauran mutane basa jin hakane ? Sai kuma ya ba kanshi amsa watak'ila dan sun saba da ita ne shiyasa, dan sun fad'a mishi tun suna yara suke tare tun a makarantar *Ansawwd* (ma'ana *inganci*).
A sanyaye kamar ba ita ba tayi kalar tausayi tace "Canal yarinyar nan fa marin k'awata tayi, kuma ka sani kai ma bana son a tab'a min k'awayena, to me yasa zan k'yaleta?"
Cikin sub'utar baki yace "Gaskiya ne, na sani Ayam, yanzu kiyi hak'uri ki je na jiranki zaku tafi jeji."
Wani k'ayataccen murmushi ta saki tace "Shukran."
Sakin baki yayi a ranshi yace "Yau ma wani yaren?"
Juyawa tayi cikin takon k'arfi da salo ta fita a ofishin babu wanda yayi yunk'urin hanata, Umad dake zaune mik'ewa yayi ya sarawa canal d'in sannan yace "Yallab'ai da izininka zan tafi."
Da hannu ya nuna masa k'ofa alamar ya tafi d'aya hannunshi kuma na share gumi da yayi, saida Umad ya fita Zafreen ta girgiza kan ta ta dawo hayyacinta, rarako idonta tayi tace "Kutumar can, wacece ita?"
Khatar daya kasa anfanuwa tunda ta shiga kora masa bayani ko k'yabtawa bai yi sai yanzu, cikin fitar hayyaci da rashin sanin me ya fad'a yace "Ta musamman."
"Me?" Zafreen ta fad'a a tsiwace, kamar mari ta gaura masa haka ya zabura ya juya ya kalli canal, cikin masifa ya shiga fad'in "Dama haka kake mata kashedin? Wai wannan wace yarinya c da kai kan ka ke tsoron had'a ido da ita? Me ta taka a k'asar? Dan gwamnati ta d'auki nauyin karatun ta ba shi ke nufin zata taka kowa ba, ka fad'a min wacece ita?"
Tsura masa ido canal yayi yace "Wacece ita?"
"E, wacece ita?" Ya fad'a a zafafe, numfashi ya sauke sannan yace " *Abinda idonka ya nuna maka*, ita d'in ita ce, bayan haka bansan komai ba."
Tsaki Khatar ya ja tare da juyawa ya kalli Zafreen yace "Zo muje gimbiya."
Da sauri suka fice a ofishin canal na kallonsu, saida suka fita har da bayinsu shi ma ya ja tsakin yace "Aikin banza, naga ma kai ka fini firgita da lamarinta tunda suman tsaye ka yi, can kuje ku k'arata da matsalarku da ita ni ku daina sakani, tunaninta kad'ai hawan jini yake tayar min."
*Ayam* kam na fitowa ta kawo daf da motocin da Khatar ya zo ta tsinkayi muryar Umad yace" Ke."
Yi tayi kamar bata ji ba ta ci gaba da tafiya, sake fad'in yayi" Ke."
Nan ma ko waiwaye bare hasa ran zata tsaya, saida ya bushi iska ya daddage yayi ta maza yace" Ayam."
Cak ta tsaya tare da juyowa tana murmushi tace" Na'am yallab'ai."
Gyara tsayuwarta tayi saida ya k'araso yana d'an cije leb'e da mamakin kenan ta ji banza ne ta masa? Tsareta yayi da ido kamar mai son gano wani abu a fuskarta sannan yace" Me yasa kika wa babban mutum fitsara? Dama rashin kunyarki ta kai haka? Sannan me yasa kika mareta?"
Ajiyar zuciya ta sauke irin ka dameni d'in nan sannan ita ma ta zuba idonta a na shi a yaren Italy tace"...
*Saura k'iris a rufe free page, hanzarta ki biya na ki, farashin mai sauk'i ne.*
*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:32 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._
_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._
_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._
Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.
_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._
_Bismillahir rahamanir rahim_
*8*
Cikin yaren Italy tace "E tu? Il figlio verde o uno dei loro cortigiani (kai kuma fa? D'an korensu ko d'aya daga cikin fadawansu?"
Zaro ido yayi a tsawace cikin b'acin rai yace "Silenzio! Omicidio cosa ci dirai, pazzo (shiru ! Ki dinga sanin me zaki fad'a mana, mahaukaciya)."
Cike da shak'ihanci ta gyra tsayuwa tace "Kai ma ka dinga sanin sunan da zaki dinga kirana dashi malam."
Girgiza kai yayi irin na takaicin nan yace "Nonsense (shashanci)."
Murmushi tayi tace "I'm not talking about nonsense, I'm telling you so i can do what you don't expect (ba ina magana bane akan shashashanci, ina fada ne dan zan iya yin abinda baka tsammani)."
Da mad'aukakin mamaki yace "How do you change language like this? Who are you (ta ya kike iya canza yare haka? Wacece ke)?"
Sunkuyar da kan ta tayi tana murmushi tace "Tu me prend juste comme tu me vois, je ne sais m锚me pas, c'est juste moi (Ka d'auke ni a yanda ka ganni kawai, ni kai na ban sani ba, ni ce kawai)."
Juyawa tayi a sanyaye zata tafi ya bita da kallo, gyara tsayuwa yayi har ga Allah jiri yake ji na son kwasarshi ya jefar a k'asa, yarinya kamar aljana ko wata matsafiya, da sauri ya girgiza kan shi ya kawar da abinda zuciyarshi ke sak'a mishi a kan ta, takawa ya shiga yi da k'arfi k'arfi har ya isa garesu inda suke tsatsaye.
Ganinshi ya taho yasa d'aliban duk suka dinga shiga cikin motar wasu ta k'ofar gaba wasu ta baya, Ayam ma na daf da shiga ta ji an ce "Gimbiya ta."
Da farin ciki ta kalli inda ta ji sautin kuma ta gane sautin waye, da gudu ta sauko a matakalar ta nufeshi tana fad'in "Pah."
Tana zuwa ta bud'e hannaye zata fad'a jikinshi kawai ya rusuna kamar yayi ruku'i, hakan ya k'ara saka Umad ghara tsayuwarshi yana kallonsu.
Marairaicewa tayi ta turo baki tace "Pahhh? Me yasa?"
D'agowa yayi yana dariya yace "Tuba nake, ai ba laifi nayi ba dan na kira gimbiya ta da gimbiya."
K'arasawa tayi ta bud'e hannayenta ta rumgume shi tsam tana sauke ajiyar zuciya, bai yarda ya rik'e jikinta ba, dan wanda tayi ma suna d'aukan hakan wata alfarma ce garesu, su suka raini yarinyar tun tana k'arama, sun sha al'ajabi da mamaki a game da abinda ya shafeta, har wasu lokuta sukan shiga yanayi na tsoro da fargaban ko dai ba mutum bace, lallai sun yarda rashinta a msarautar nan shi ne yafi alkairi.
Hannunshi dake b'oye a bayanshi ya fito da shi cikin murmushi yace "Gimbiya ga kyautar ki."
D'agowa tayi ta kalleshi tasa hannu biyu ta karb'a tana dariya tace "Amma Pah ai gobe ne ranar, me yasa ka kawo min kyauta yau?"
Da fara'a a fuskarshi yace "Maman ki ta fad'a min kin je bana nan, kuma kin kira kika tambaye ni, shiyasa na kawo kai na kafin ki sake nema na."
Fad'ad'a murmushinta tayita sake rumgume shi tace "Thank you Pah, I'm so proud of you."
Kallonta yayi a ladabce yace "Na sha fad'a miki bana gane kowane yare bayan na slovaque da azharbaijan, ban fahimci me kika fad'a ba."
Had'e murmushinta tayi tace "Pah, dama ina so na tambaye ka, wai me yasa sai na dinga yin yaren da ni kaina ban sani ba? Na lura hakan ya fara tsorata mutane game da ni."
Girgiza kai yayi yace " Ban sani ba, bansan komai akan haka ba, ina ga baiwarki ce haka."
Cike da gamsuwa ta saki fuskarta tace" Pah, ce wa nayi nagode sosai, kuma ina matuk'ar alfahari da kai."
Kan shi ya rusuna dake nuna ya ji dad'in abinda ta fad'a a matsayinta na shugabarshi, kamar katari sai kuwa ya had'a ido da Umad dake tsaye yana kallonsu idonshi cikin bak'in glass, duk da basa kallon juna ido cikin ido, amma sai Utais ya k'ureshida ido, lura da inda yake kallo yasa Ayam juyawa, da sauri ta kalli Utais tace "Pah, ni zan tafi, zamu fita ana jira na."
Hannu ta d'ora a kafad'arshi ta sumbaci kumcinshi tace "Pah zan kiraka, kar fa kayi nisa da gida."
Bai kula da abinda ta fad'a ba dan hankalinshi ya tafi kan Umad, saida ta juya zata tafi yace "Waye shi?"
Juyowa tayi ta kalleshi ta kuma juyawa ta kalli Umad, gimtse fuska tayi tana jin haushin yanda ya tsaya musu haka kamar mai son ganin me zasuyi, kallon Utais tayi tace "Sabon mai horar da mu ne Pah, kar ka damu ka je kawai."
Jinjina kai yayi ya gyara tsayuwarshi ya bita da kallo, saida ta shiga motar rik'e da kwalin kyautarta sannan Umad ya shiga ta d'aya k'ofar, tayar da motar akayi hakan yasa Utais ya shiga d'aga mata hannu ita ma daga ciki tana d'aga masa hannu kamar zasu rabu, saida sukayi nisa sosai har sun kusa fita a makarantar ya daina d'aga musu hannun, numfashi ya sauke a hankali ya furta "Wanene shi? Ya aka yi ya min kama da wanda na sani da jimawa?"
D'aga kafad'a yayi ya shiga takawa shi ma dan dama idan ka zo ganin wani baka shiga da abun hawanka idan ba kai d'in wani bane, bare kuma shi da bus ya hau ya zo nan d'in kuma ita zata sake maida shi inda ya fito.
Tunda motar ta fita a harabar makarantar d'aliban suka kwashi rera wak'ar da suka saba yi a irin wannan lokacin, amma Ayam hankalinta ya karkata kan mahaifinta, zuwan nan da yayi ya sata jin wani abu daban, bai tab'a zuwa a irin wannan lokacin ba, yanda ya sunkuya mata ga da ga kuma ya jadadda mata da dan ya kira gimbiyarsa da gimbiya me ye a ciki ?
Ajiyar zuciya ta sauke ta sake k'amk'ame kwalin kyautar daya bata, Umad na zaune a kujerarshi a baya yana k'arewa yanayinta kallo daga cikin glass, wata zuciyar ce tace masa "Akan me zaka mayar da hankalinka kan wannan yarinyar? Ka duk'ufa neman abinda ya kawoka mana."
D'auke kan shi yayi haka har suka isa jejin mai abun al'ajabi da tsoratarwa, fitowa sukayi suka kama layi a jere, gabansu ya tsaya hannayenshi goye a bayanshi cikin d'aga sauti yace" Shin a cikinku akwai mai sha'awar ganin wata dabba ne a zahiri?"
Bakwai a ciki ne suka amsa da" E yallab'ai."
Hannun damansa ya kalla ta farkon ya tambaya da" Me kike son gani?"
Cikin d'aga murya ba tare da idonta ko gangar jikinta ya motsa ba tace" Alfadari yallab'ai."
Kallonta yayi yace" Me yasa?"
Tana yanda take tace" Ina so na tabbatarwa kai na lallai ana samar da shi ne ta hanyar had'a jaki da kuma doki suyi barbara."
Jinjina kai yayi alamar gamsuwa ya kalli ta gaba ita ma ya tambaye ta, da haka duk suka fad'i kalar dabbar da suke son gani a rayuwarsu har aka zo kan Sabrine dake kusan Ayam tace" Dorina yallab'ai."
Kallonta yayi ita ma yace" Me yasa?"
Tana kallon gabanta tace" Saboda jiya ka fad'a mana tana da kakkausar fata, ina so na tab'a na ji." 馃槀
Takawa yayi a hankali ya tsaya gaban Ayam, haka kawai ya ji zuciyarshi na kakkarwa da jin d'ar d'in tambayarta, dan bai san me zata fad'a ba ita, karta fad'a musu abinda zai kashesu ma, k'wayar idonta yake kallo daga cikin gilashin nan sannan yace" Ke fa?"
Kamar sauran ita ma muryarta a sama tace" Zaki yallab'ai."
Tsamm! Ya ji tsigar jikinsa ta tashi wani yam yam yam, sauran kam duk kallonta sukayi baki bud'e, dreba kan shi dake cikin mota zaune saida ya lek'o ta taga, jinjina kai yayi a ranshi yace" Na sani dama ita ce, me ma yasa na lek'o? Aljana kawai."
Sake had'e rai yayi yace" Me yasa?"
Ba alamar wasa ita ma tace" Haka kawai yallab'ai, burina ne tun ina k'arama."
A hankali ya janye gilashin daga idanunshi ya kalleta ido da ido ko hakan zai bata damar canza ra'ayi, d'an sakin fuskarsa yayi sannan yace" Zakin gaske kike son gani ? Ko kuma na teddy?"
A lokacin kallon fuskarshi tayi ta saki murmushi tace" Na gasken yallab'ai."
Muskutawa yayi yana kallonta ta k'asan ido yace" Me yake birgeki a game da zaki?"
Sakin hannayenta tayi tare da gyara tsayuwarta ta shiga kallonshi tana dariya tace" Ka gane yallab'ai, wannan tafiyar tashi ta k'asaita, wannan yalwataccen gashin daya masa k'awanya, idonsa masu d'aukar hankali, ni kawai ina so na ganshi a zahiri sannan na shafa bayansa, sannan ina so na ga faffad'ar k'afarsa wacce ke iya illata sauran dabbobin da duk ta daka sau d'aya."
Wani basaraken murmushi ta saki ta tafa hannayenta tace" Kai gaskiya zaki yayi, ina son ganinshi a zahiri idan da yiwuwa ma mu zama abokai."
Mayar da gilashinshi yayi a d'an hassale yace" Ina wasa da ke ne da zaki zauna yi min wannan bayanin?"
Cike da fara'a tace" A'a yallab'ai, amma ai a wajen aji ne."
Da mamaki yace" Kamar ya?"
Kallonshi cike da yanayin yarinta tace" Yallab'ai ai jiya kai ka fad'a a aji ne muke d'alibi da malami, amma a wajen aji ka ce zamu zama kamar abokai."
D'aga girarsa yayi ya juya zai shiga cikin jejin yana fad'in" To to d'alibai a motsa..."
Ayam ce tace" Yallab'ai."
Juyowa yayi ya kalleta, kamar wata sakara ta saki baki tace" Dama ka tambaye mu ne ba dan ka cika mana burin mu ba?"
Fuskantarta yayi yana sake cire gilashin yace" Me kike nufi? Zakin kin d'auka abun wasa ne?"
Turo baki tayi gaba tace" Na sani yallab'ai."
"Dan haka ki manta da son ganinshi kawai." Ya fad'a yana juyawa zai bar wurin, a sanyaye tace "Ba zan iya ba, zan had'u da shi ko ta halin yaya."
A gadarance ya juyo yace "Kin tabbatar?"
Jinjina kai tayi tace "Na tabbata."
Wani shak'iyin murmushi yayi yace "Shikenan zan nuna miki zaki, amma ki sani idan kika firgita ko kika suma a wurin nan, to tabbas ke zan mik'a mishi a matsayin abinda zai yi kumallo da shi, kin yarda?"
Murmushi tayi ita ma tace "Na yarda yallab'ai, amma fa idan ban tsorata ba?"
Zuba mata ido yayi yana kallo kamar ba zai ce komai ba kafin ya gyara tsayuwarshi yace "Zan miki kyautar da zata baki mamaki da zaran na tabbatar da gaskiya a kan ki."
Shiru tayi ta k'ura masa ido kamar zata yi tunanin maganar sa, shi ma abinda ya fahimta kenan kamar zatayi tunani kawai yayi saurin fad'in "Jira ni."
Waya ya ciro daga ajihunshi suna kallo yayi nesa da su yana amsa waya, bai fi minti uku zuwa hud'u ba ya dawo garesu ya tsaya, cikin karsashi ya shiga nuna musu yana fad'in "D'alibai, ku nutsu sosai sannan ku kula, bindigogin dake jikin d'amararku ba sa d'auke da alburusai na kisa sai na kashe jikin kowace irin dabba, shi ma zaku harba ne idan kun shiga had'ari, sannan ina so ku maida hankalinku kan bishiyoyin wajen, sannan ku yi taka tsantsan d kuma lura da inda zaku saka k'afarku, dan a jejin nan an fara samun b'ata garin dake shigowa wasu suna kashe dabbobi masu wuyar samu, wasu kuma suna karya itace suna shiga da su cikin gari, dan haka ku kula sosai ku tuna da shekararku ce ta k'arshe wannan."
Sara masa sukayi da buga k'afafunsu suka amsa da" To yallab'ai."
Da k'arfi sosai yace" Kun gane?"
" E yallab'ai." Suka sake fad'i a tare, jinjina kai yayi yace" Ku yi gaba zan zo a bayanku, zan fara nunawa shed'aniyar nan abinda ta nema, kuma bana son saka rayuwar d'aya a cikinku had'ari."
Da k'arfi ya sake fad'in" Kun gane."
"E yallab'ai." Suka amsa da shi, sake jinjina kai yayi yace "To to ku motsa, kuyi aiki cikin had'in kai."
Rarrabuwa suka fara yi suna gudu wasu su biyu wasu uku duk suka famtsama zuwa cikin jeji, juyowar da zaiyi ya ga ashe shi take kallo, kallo mai ma'anar "Ina jin kunyar ka fa malam."
Yatsina fuska tayi tace "Na fad'a maka ka kiyaye kirana da kowane suna."
Cire giashin yayi yana murtuke fuska yace "An fad'a, me zakiyi ? Wai ma ke ya akayi kika raina ni?"
Kawar da kan ta tayi tana wuwulasu tace "Ni ba mace ba ce, kawai ina ga fa so na kake shiyasa kake tunanin haka."
Wani irin yatsina fuska yayi ya ja baya yace "Ke? Me? So? Da ke kuma?"
Girgiza kai yayi yana ci gaba da yatsina fuskar nan yace "Allah ya sawak'e min wahala."
Da sauri ta kalleshi da mamaki a fuskarta tace "Allah ka ce? Waye shi?"
Ba alamar damuwa da tambayar data masa ya gyara tsayuwarshi yana d'auke kan shi daga kan ta yace "Allah shi ne wanda ya hallice ni, ya hallice ki kuma y..."
Da sauri ta katseshi da fad'in "Shi ya hallici sama d k'asa? Da duk wannan tsirren dake cikin jejin nan? Shi ne ya k'agi tekunan da suke ambaliya a doron k'asa?"
Da mamakin tambayarta yace "E hakane."
Gyad'a kai tayi ta tafa hannunta tace "Dama na ce, na sani akwai wani dake juya duniyar nan wanda buwaya da izzarshi ta fi gaban wasa, amma ba wani banzan abun bauta Ghira ba wanda ko jini babu a jikinshi bare ya anfani wani."
Kallon Umad tayi irin kallon tsanake ta sauke numfashi tace "Wane addini ne wannan? Ya ake a shiga? Ina so ni ma na zama d'aya daga cikin mabiyansa, na fi son ubangijin da zan bautawa ya zama mai jin buk'atuna, zan so ubangijin da zan bautawa ya zama shi ne ya samar da ni ba wai wanda kakanninmu suka samar ba, zan so ubangiji na ya kasance a tare da ni a ko yaushe ba wai sai na sha wahalar d'aukarsa a cikin jakata ba, kuma ina so ubangiji ya zama mai amsa rok'ona a