tayi zata wuce, dan gaba d'aya kallon Zafreen d'in yasa ta jin jikinta yayi wani iri har tsigar jikinta na tashi. Wajen ta wuce kuma kawai kafad'arsu ta gogi juna, zata fita a wurin Zafreen ta cabko hannunta ta dawo da ita baya, cike da wulak'anci da jin izza 脿 yarenta na slovaque tace "Wacece ke da har zaki rab'ani ki wuce?"
Gyara tsayuwa Ayam tayi a hankali tasa hannunta ta b'amb'are na Zafreen dake jikinta, a tausashe kuma a ladabce itama 脿 harshen slovaque tace "Ni ba kowa bace, amma d'aliba ce nima a makarantar nan, kamar dai ke."
Ta k'arashe tana nuna Zafreen, cikin jin haushi Zafreen ta nuna kanta tace "Kinsan wacece ni kuwa?"
Wani dogon tsaki Ayam taja tare da fad'in "Shirme kawai, amsar tambayar nan fa na baki yanzun nan, akan me zan tsaya b'ata lokaci na a kan ki?"
Yatsina fuska tayi cike da wata irin gadara da izza ta sake niyyar fita a k'ofar, tare gabanta Zafreen tayi tana fad'in "Ke kin isa ki fad'a min magana sannan ki wuce, k'arya kike."
Kallon k'awayenta tayi dake gefe suna kallonsu tace "Ku fad'a mata wacece ni, ku fad'a mata ni ke da gaba d'aya k'asar nan da kewayenta, idan har na so yanzun nan zata bar makarantar nan."
D'aga gira Ayam tayi ta turo d'an bakinta k'arami ta juya ta kalli k'awayen ita ma, wata doguwa a cikinsu ce tayi saurin fad'in" Ke kinsan wacece Zafreen kuwa? To ita ce gimbiyar Khazira, 'ya d'aya a gurin sarkinmu Musail."
Babu alamar damuwa ko wata shakka Ayam ta tab'e baki tace" Da gaske? To ni kuma sunana Ayam,' ya ga... "
Mai kula da shiga da ficen d'aliban ne ya katsesu ta hanyar fad'in" Kai ku fita a nan, kunsan minti goma na baku ku shiga ku ga k'awar ta ku."
Da sauri k'awayen suka ce" Gimbiya zo muje, ki rabu da ita zamu had'u wani lokacin."
Ido cikin ido suka kalli juna amma a take Zafreen tayi k'asa da na ta tana kallon fararen takalmi k'afa ciki masu kamar soso kuma kamar roba dake k'afar Ayam d'in, cike da shak'iyanci Ayam tace" Ki kula malama, wannan fa makarantar gwamnati ce, kuma shekara ta dubu biyu da ashirin muke, babu k'arancin 'yancin a zamanin nan, bugu da k'ari ni d'in haifaffar Larhjadin ce, esxuze moi."
Baki bud'e suka bita da kallo har ta tsaya kusan mutumin dake zaune cikin case d'in shi, magana ta mishi hakan yasa shi mik'o mata wayar tafi-da gidanka ta shiga danna lambar gidan na su, dan ba kowane lokaci ake basu damar anfani da wayoyinsu ba.
Rai b'ace kamar zata mutu ta juya suka fita tana fad'in "Na fasa ganin shi d'in ma."
Da sauri suka rufa mata baya d'ayar na fad'in "Gimbiyarmu, kar ranki ya b'ace kinji, k'aramar alhaki ce wannan, zaki iya sa wa 脿 koreta ai."
Cak ta tsaya sai kuma ta kalli wacce tayi maganar, ita kuma sunkuyar da kan ta tayi k'asa da tunanin ta fad'i ba daidai ba.
Murmushi ta saki tace "Kin kawo shawara mai kyau *Laika"*, ban wayata?" Ta fad'a tana tara mata hannu, mik'a mata tayi ta karb'a ta shiga danna wasu lambobi sannan tayi gaba suka nufi na su b'angaren tana amsa waya.
*Ayam* kam na ta buga wayar amma shiru ba'a d'aga ba, d'an tsakin rashin jin dad'i tayi tace" Watak'ila Momma na mak'ota."
Aje wayar tayi ta kalli mai kula da k'ofar tace" Shin-shiy (nagode)."
Da kallo mamaki ya bita 脿 zuciyarshi yana fad'in" Me yasa take son raina min hankali yarinyar nan, kullum da kalar yaren da take min."
Zata shiga cikin sauri shi ma zai shiga a hanzarce, kafad'unsu ne suka had'u, amma Ayam dake wata pigigiya ce saida ta nemi fad'uwa a k'asa, cikin takaici da rashin sanin yaren da ita kanta tayi tace" Tirr! Yau jakuna nake ta had'uwa da su."
Gyara jakarta tayi sai a lokacin ta d'aga kai ta kalli dogon mutumin, mummunan fad'uwa gabanta yayi sakamakon tsoron daya bata, ba wai hallitarsa ke da ban tsoron ba, had'add'iyar fuskar shi da babu annuri a cikinta, fararen idonshi k'anana daya zazzaro ya k'ura mata, girarenshi duka biyun daya bala'in d'agesu sukayi sama daga k'arshensu, ga kuma matsatsen bak'ar rigar dake jikinshi data fito da k'irarshi.
D'an bakinta ta bud'e har hak'oranta suka fito ta shiga zazzare ido, gyara tsayuwarta tayi tare da sunkuyar da kanta, ko Momma da Papanta bata tab'a had'a ido dasu ba haka, duk yanda take son su kalleta itama kuma ta kalli cikin idonsu abun ya gagara, da sun had'a ido suke d'auke na su, haka ma daga k'awayen abokai da sauran mutane, hakan ya dameta har wata rana ta tambayi Deeyam me yasa bata had'a ido na tsayin sakan uku da ita? Sa茂 tace mata "Ji nake kamar ina kallon babban teku, hakan ya sa naji kamar zan fad'a ciki."
Sake d'aga kanta tayi ta kalleshi, tar-tar suka sake had'a ido da shi yana mata mugun kallon nan kamar zai taka wuyanta ya yankata, mitsitsika idonta tayi ta motsa bakinta ta aro jarumta cike da tsiwa da tijara tace" Malam baka gani ne? Ina kake kallo da zaka kawo min hari haka?"
Yanda yake kallonta babu rusunawa da kuma sak'onnin dake cikin kallon yasa ta juyawa da gudun tsiya ta shige ciki tana k'yalk'yala dariya kuma tana fad'in" Sai ka ce wani dorinar ruwa wacce kullum fuskarta a murtuke."
Da kallo ya bi bayanta, yanda take gudu tana dariya hannayenta rik'e da jakarta, kayan makarantar ne jikinta, riga mai hannaye iya damtse mai ratsin shud'i, sa茂 farin wando shi ma da ratsin shud'i amma iya gwiwa yake, rigar ma tsayinta ya sauko kan cinyoyi kuma botira gareta a gaba har k'asa, sai hula fara dake kanta wacce a saninshi dai yasan ba doka bace sakawa.
Takaici mai sunan takaici, haushi iya haushi had'e da jin d'aci a mak'oshinshi, ga kuma azababbiyar tsanar yarinyar da yaji har zuciyarshi, ba dan komai ba sai yaren da tayi magana dashi na Italy, shekararsa shida a garin yana karatunsa, dan haka babu abinda za'a fad'a ya gaza ganewa.
Wata zazzafar iska ya huro ya shiga d'aga k'afar sa wanda kana gani zaka san ranshi a b'ace yake zuciyarshi kuma tafasa take, cikin ranshi ban da tsaki da k'wafa babu abinda yake, cikin jin haushi da masifa yake ayyana "Busassar banza, kafin na gama abinda ya kawoni sai na tabbatar ba kya iya banbance tsakanin ruwa da yawu, banza mai idon mayu."
Kai tsaye ofishin babban jami'in ya shiga ya gabatar masa da kan shi, tarba ya samu kafin ya had'a shi da k'aramin mataimakinshi ya rakashi zuwa masaukin malaman ga masu buk'ata.
*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:30 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._
_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._
_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._
Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.
_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._
_Bismillahir rahamanir rahim_
*4*
Bayan fitar Umad aka kira wayarshi, ganin mai kiran yasa hankalinshi ya tashi da sauri ya d'aga kiran yana fad'in "Hello yallab'ai."
Daga can b'angaren wazirin sarki Musail yace "Yallab'ai Jacob, ya aiki?"
"Lafiya lau yallab'ai."
Wazirin ne yace "Kaga na kiraka ko?"
Amsawa yayi da fad'in "E yallab'ai, fatan dai lafiya?"
Wani d'an murmushi yayi yace "Lafiya lau, gimbiya ce ta kirani yanzu take fad'a min sun samu matsala da wata 'yar talakawa, ta fad'a min yarinyar ta ci mutumcinta sosai."
Mik'ewa yayi tsaye yace "A nan makarantar? Wacece wannan?"
A gadarance yace "Sunanta Ayam."
Zaro ido yayi dan har jikinshi saida ya amsa sunan, ba kasancewarta wacce gwamnati ta tsaya ma ba, shi kawai yarinyar tsoro take bashi, shiyasa ko kallon fuskarta baya son yi, yarinyar da zata maka yare kuma ta nuna bata son wane yare tayi ba. A ladabce yace "Yallab'ai ya kake so a yi yanzu?"
Kai tsaye ya furta "A koreta ko da kuwa k'arshen shekararta ce wannan, hakan zai zama izina ga yan baya."
Da sauri ya cire hular kansa yace "Me?"
Da mamaki waziri yace "E, ko da matsala ne?"
A gigice yace "Yallab'ai *Khatar* akwai babbar matsala ma, dan yarinyar nan da kuke gani gwamnati ce ke d'aukar nauyin karatunta, yallab'ai Ayam bana jin ko a k'asar England za'a iya korarta a makaranta bare 脿 nan k'asar."
Cike da tsiwa waziri Khatar yace "To shine me? Waye ubanta a k'asar nan?"
Girgiza kai yayi cike da tausayin kanshi dan har wata zufa ke tsatsafo masa yace "Yallab'ai Khatar ba 'yar kowa bace, hasalima mahaifinta ba wani hamshak'i bane, amma kuma tasirin yarinyar yafi na democrad'iya."
Wawan tsaki ya ja tare da fad'in "Kenan yanzu babu abinda zaka iya yi?"
A sanyaye yace "Gaskiya yallab'ai akan yarinyar nan zan iya rasa aikina had'e da tukuicin shiga babbar matsala, dan kad'an daga cikin ikon da gwamnati ta ba wa yarinyar nan, akwai lamunce mata ta ziyarci iyayenta duk sanda ta so, dan ma yarinyar na da lissafi ne take daidaita kanta da sauran d'aliban."
A tsawace Khatar yace" Shiru malam, ni ba wannan na tambayeka ba."
Cikin rarrashi yace" Kayi hak'uri yallab'ai, na maka alk'awarin zan ja mata kunne ta fita harkar gimbiya Zafreen."
K'it! Ya kashe wayar hakan ya ba colonel d'in damar sauke numfashi mai nauyin gaske shi ma ya aje wayar.
K'aramin Sajan (sergent) d'inshi ya kira yace" Kira min Ayam *Utais*, izuwa yanzu suna aji tare da malam *Pedro*."
Sara masa yayi ya amsa da" To yallab'ai." Sannan ya fice.
Mintuna k'alilan suka shigo tare da ita, fita yayi bayan ya mata iso ta samu wuri ta zauna tana kallon major d'in, saida ya rufe musu k'ofar kafin ya kalli fuskarta saidai ba cikin idonta ba yana wani inda-inda yace "Am... Ayam Utais, dama nasa...a kirani ne naji dalilin samun sab'aninki da gimbiya Zafreen?"
K'uri ta masa da idonta hakan yasa shi mik'ewa tsaye yana dariyar rashin gaskiya kamar wacce tace kwab'e kayanka na zaneka, cikin duburburcewa ya ke fad'in "A'a, kin gane ko? Ba komai ma ba sa茂 kin fad'a ba, abinda nake so dake kawai ki rabu da ita, karki sake shiga sabgarta dan ke karatu ne ya kawoki nan, kin kusa kammala zangonki dan haka ki maida hankali kinji."
Turo baki tayi gaba kawai ta jinjina kai alamar gamsuwa tare da mik'ewa zata fita, da sauri yace" Kina ji Ayam."
Tsayawa tayi ta juyo tana saurarenshi, d'orawa yayi da fad'in" Gobe mai horar daku malam Pedro zai koma k'asarshi, dan haka gobe da safe zaku ci gaba daga inda kuka tsaya tare da sabon mai horarswa."
A sanyaye ta maimaita" Sabon mai horaswa?"
"E." Ya fad'a yana komawa ya zauna, jinjina kai tayi ta fita a ofishin tana tab'e baki da maimaita sabon mai horaswa? Waye shi? Kuma da wane salo zai zo shi kuma? Ko shi ma irinsu malam *Elinio* ne da ya gama latse 'yan mata kafin ya koma k'asarsa Brazil?
*Suna* zazzaune wajen cin abinci da dare Ayam ta kalli k'awayen na ta su uku tace "Kunsan me? D'azu colonel yake fad'a min wai gobe za'a kawo mana sabon mai horaswa."
Duk k'ura mata ido sukayi sai Deeyam da tace "Sabon mai horaswa kuma? Gobe gobe kuma? To me ya samu Pedro d'in?"
Saida ta zura cokalin robar a bakinta tace "Yana nan, babu abinda ya sameshi, da alama wani aiki ya samu daya fi wannan."
Jinjina kai sukayi kafin Ayam ta sake fad'in "Kunsan ni me nake so, ina tsoron kar a kawo mana irin malam Elinio, yana mana darasi yana tsaremu da ido yana kallar mana d'uwawu."
Dariya Deeyam tayi tace "To ya zamuyi idan ma irinsa ne? Mu dai na mu bijire masa ne kawai."
Kallon Deeyam d'in tayi tace "Ni kuma ba haka nake so ba, kunsan me zamuyi?"
Girgiza kai sukayi inda d'aya a cikinsu tace "Sai kin fad'a."
Cikin rad'a tace "Mu kai ziyara b'angaren malaman, ta haka zamu san wane iri ne shi dan mu d'auki matakin kare kanmu."
Zaro ido sukayi sai Deeyam da tace "Ta ya ya haka zai faru? Ko kin manta ba'a barin d'alibai zuwa b'angaren da malamai suke, haka su ma malaman basa zuwa inda d'alibai suke?"
Waina idonta tayi sannan ta k'urawa Deeyam su tana kallonta, kawar da kanta tayi murya k'asa k'asa tace "Ki daina kallona haka Ayam, na rantse miki saida gabana ya fad'i."
Tab'e baki Ayam tayi ta d'auke idonta tace "To na d'auke, ni dai yanzu ku bar min komai a hannuna kawai, ku dai ku shirya zan tasheku a tsakiyar dare."
Tana gama fad'a ta mik'e tare da juyawa ta bar wurin, da kallo suka bita da fari kafin d'aya 脿 cikinsu tace "Kamar kullum, yau ma mu zamu d'auke mata farantin abincinta."
Deeyam dake cin abinci ce tace "Tunda kinsan da haka, me ye na bitar shi kuma?"
Wata a ciki ma murmushi tayi tace "Lokuta da dama Ayam tayi abu sai ka d'auka wata sarauniya ce."
Dariya suka yi gaba d'ayansu haka har suka kammala suka mik'e suma da farantan a hannayensu suna ajewa wurin da aka keb'e dan ajesu kamar sauran d'alibai.
*01:43*
Tana daddab'a Deeyam ta bud'a ido tace mata "Tashi mu tafi."
Tashi tayi zaune tana murza ido tace "Ayam, ina kuma zamu je?"
Cikin rad'a tace "Tashi mu tafi kedai."
Sake bud'a idonta tayi ta kalli saura k'awayen dake bayan Ayam dukansu cikin kayan baccinsu, a hankali ta sulala ta sauka akan gadon.
Cikin sand'a suka dinga fita a d'akin har sukayi sa'ar haurawa ta wani corridor ba tare da tsoron su fad'i ba, ai kuwa a sauk'ake sai gasu a b'angaren malam kamar wasu b'arayi, jerawa sukayi suka dinga hawa matakalar har suka iso wajen d'akunan, kallon juna sukayi Deeyam tace "Ina d'akin?"
Nuna musu Ayam tayi tace "Wannan d'akin ne ai babu kowa."
K'arasawa sukayi suka sake tsayawa cirko cirko, kallon su Ayam tayi tace "Yanzu Sabrine ke ki fara shiga."
Waro ido tayi tace "Me yasa ni zan shiga."
Cikin rad'a Ayam tace "To ai kin fi mu kyau da dirin halitta mai kyau."
Harara ta wurga mata tace "Na k'i to, babu ruwana ni."
Juyawa Ayam tayi ta kalli Deeyam tace "To ke ki shiga, tunda kina da abubuwan d'aukar hankali."
Cikin fad'a Deeyam tace "To wai ke da kika jagorancemu me zai hana ki shiga?"
Wata dariya tayi ta kalli kanta tace "Haba dai, dubeni fa, aini bana da fasalin d'aukar hankalin namiji, ba kowane namiji nake birgewa ba saboda nayi rama dayawa."
Tab'e baki Sabrine tayi tace "To saidai mu koma kam, amma babu inda zanje."
Deeyam ma had'e hannaye tayi tace "Ni ma haka."
D'ayar ce ta kallesu tace "To mu koma kunji, bana son wani ya ganmu za'a hukuntamu."
Cikin rad'a Ayam tace "Yanzu ku d'an aikin nan ne zai gagaremu? Kun manta irin tijarar da muka zuba a baya ne?"
Deeyam ce tace "Bamu manta ba, amma dai yau kam ni dai babu ruwana, inda matsalar take shine rashin sanin waye malamin, ni bansan me yasa kika damu da son sanin wane iri ne shi."
Gyara tsayuwa Ayam tayi da kyau ta kallesu tace "Ku fad'a min zaku shiga ko a'a?"
"A'a." Sabrine ta fad'a tana juya baya, jinjina kai tayi tace "Shikenan, ni zan shiga ciki, amma ku jirani a nan."
Murmushi Deeyam tayi tace "Fatan nasara."
Harara Ayam ta jefa mata tana gyara hularta tace "Matsalarku ce."
Kallon k'ofar d'akin tayi tana sauke numfashi, wani yanayi na tsoro da fad'uwar gaba take ji wanda bata tab'a ji ba, hatta da jinin jikinta ji take ya k'ara gudun tafiyarshi.
Cije leb'enta tayi na k'asa sannan ta kai hannu ta k'wank'wasa k'ofar d'akin, amma sai ta ji shiru babu ko alamar motsi, sake kwank'wasawa tayi nan ma shiru, a karo na uku ta sake kwank'wasawa tana jan gajeran tsaki.
Deeyam ce tace "Ayam, tunda kika ji shiru ki zo mu je kawai, watak'ila baya nan."
Sabrine ce ta karb'e da fad'in "Ko kuma ma bai zo ba."
Juyowa tayi ta kalli Sabrine da tayi maganar tace "Hakane?"
D'aga mata gira tayi alamar e, jinjina kai tayi tace "Bari mu gani to."
Cikin sand'a ta kama hannun k'ofar ta murd'a a hankali, jin ta bud'e yasa suka kalli juna, maida kallonta tayi ga k'ofar ta tura a hankali tana shiga cikin d'akin.
Tattausan k'amshin turaren 112 ne ya fara mata maraba, sai kuma siririn hasken daya gauraye d'akin, komai na d'akin a gyare kuma a killace yake sannan a tsaftace, babu alamun da suka nuna akwai mutum a d'akin, hakan yasa ta bayan k'arewa d'akin kallo ta jawo k'ofar da niyyar rufewa.
Cak! Ta dakata sakamakon tsikayar wani k'aramin hoto a gefen gadon ajiye, sakin hannun k'ofar tayi ta k'arasa da sauri ta d'auki hoton, k'urawa dattijuwar matar ido tayi mai cikar kamala da haiba, tana cikin shiga ta alfarma kamar wata sarauniya. Samun kanta tayi da sakin murmushi sanadiyar k'aunar matar data ji, a hankali a asalin harshenta na slovaque tace "Watak'ila ya manta da hoton ne?"
Sai kuma ta tambayi kan ta "To amma wa ya zauna a d'akin?"
Rashin sanin amsar yasa kawai ta d'aga kafad'a alamar ko oho, juyawa tayi ta fara tafiya hannunta rik'e da hoton.
Tana daf da hita aka bud'e k'ofar k'aramar ban d'akin dake cikin d'akin, da sauri kuma a mugun tsorace ta kalli inda ta ji k'arar, a wani bala'in tsoracen wanda bata san sanda ya ziyarceta ba ta saki hoton wanda ke lullub'e da kwalba ya fad'i k'asa.
K'arar glass d'in da kuma ihunta a tare suka gudana, sai kuma tayi saurin yin gum da bakinta kamar wacce aka tusawa k'wallon goriba a bakin.
Idonta masu abun al'ajabi ta zuba masa tana kallo ba tare da rusunawa ko jin d'ar a yanda ta ganshi ba, a hankali take yi tana k'yabta idonta tana kuma sauke numfashi kamar wacce aka b'atawa rai, a zahirinta kamar jira take yace kul tace cas, amma a bad'ini kuma gabanta ci gaba yake da fad'uwa, ganinshi d'aure da towel d'in nan kalar shud'i ba k'aramin gigita mata lissafi yayi ba, dogo ne sosai mai k'ira da zubin jarumai, duk da ba wata murd'add'iyar sura ce da shi mai jan hankali ba, amma dai yana da fasali mai kyau wanda zai iya juyar da k'irarshi a duk ta yanda ya so.
Duk da bak'i ne amma kuma bak'inshi mai kyau ne da k'yalli kamar na macen dake samun gyara a kai a kai.
A hankali cikin b'acin rai da mamakin abinda ya kawota d'akinshi ya tsura mata ido, yana d'ora ido 脿 kan ta saida launin idonshi suka canza tsabar haushi da takaici, sai yake bala'in jin kamar ya k'urma ihu dan ya samu sassaucin abinda ya tokare masa zuciya.
Ba ma wannan ba, wai a kan wane dalili ne shi kam yake had'uwa da wannan mai zubin aljanun ruwan, ga ta dai 脿 cikin kayan bacci wando iya gwiwa da riga mai k'ananan hannu, gaba d'ayanta fa ba zata gagareshi ya dunk'uleta a hannu d'aya ya jefata a hudar hancinshi sannan ya fyatota.
Kallon hoton dake k'asa yayi, da sauri ya tako ya tsaya gabanta tare da durk'usawa yana kallon hoton, a mugun fusace ganin yanda hton ya fashe ya sa ya d'ago ya k'ura mata ido.
Ayam da tunda ya fara takowar nan da sauri gabanta ya shiga dakan uku, kasa motsawa tayi sai bakinta data warwareshi daga kumburewar da ta mishi, hannayenta ta d'ora kan mararta ta dafe tana fatan kar fitsari ya taho mata.
Umad kam cikin fitar hayyaci ya d'aga hannunshi ya wanketa da mari, a k'ufule ba tare daya bata damar gama fahimtar rad'ad'in ba ya nuna mata k'ofa da yatsa cikin hard'add'iya kuma nagartacciyar muryarshi da harshenshi da ya fi k'warewa a yaren Gallois yace "Fita a nan, kuma karki bari mu sake had'uwa, *b'arauniya* kawai."
Da sauri ta d'aga idonta dake kallon k'asa ta kalleshi jin sunan daya bata. Shi ma sai lokacin ya fahimci wani abu a tare da ita, ya mareta marin da yake da tabbacin ya ratsata sosai, to amma" Me yasa bata yi ihu ba? Kuma bata fad'i ba duk da rashin nauyinta." Abinda ya tambayi kanshi kenan, sam kamar ma ba ita ya mara ba a fuska.
A gaggauce ya kawar da tunanin ya maida hankalinshi ga Ayam data rumgume hannaye a k'irji cike da izza, salo da kuma gadara tana kallon k'wayar idonshi ita ma cikin harshen Gallois da bata tab'a sanin ta iya ba tace "...
*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:31 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._
_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._
_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._
Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.
_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._
_Bismillahir rahamanir rahim_
*5*
Ayam data rumgume hannaye a k'irji cike da izza, salo da kuma gadara tana kallon k'wayar idonshi ita ma cikin harshen Gallois da bata tab'a sanin ta iya ba tace "Af Allan, ond byddwch yn mynd ar ol ar fy ol (zan fita, amma ka koreni a mutumce)."
Baisan sanda mamaki ya sake bayyana a fuskarshi ba, gyara tsayuwa yayi da kyau dan ya Fahim I shekarar da zaiyi kisan kan shi ce ta kama, nuna ta ya sake yi a dake yace" Ke, ke mahaukaciyar ina ce?"
Ba tare data rusuna idonta ba ta sake muskutawa ita m'a sannan tace" Sanin mahaukaciyar ina ce ni ba zai anfaneka da