fad'in "Yallab'ai ka min rai, ban da masaniya akan komai ni ma, labari na samu daga d'an lek'en asirinmu dake masarautar Khazira."
Sakinshi yayi da k'arfi yana sake fad'in "To su waye suka d'auke yarinyar dana jima ina jiran zuwanta? Su waye su?"
Girgiza kai yayi yace "Ban sani ba yallab'ai, kuma shi ma ya fad'a mana wasu fadawa biyu ne ake zargi da saceta, saboda su ne aka nema aka rasa a yayin da aka rasa 'yar."
Juyawa yayi da bala'in sauri yayi ciki yana fad'in "Ka samo min masaniya akan su, ba zan tab'a barin *lu'u lu'u* na a juji ba."
Rusunawa yayi yace "To ranka shi dad'e."
Saida ya ga b'acewarsa ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi kafin ya juya ya fita a tank'amemen falon.
*Bayan wasu shekaru*
Sarki Musail ya sake zama mugu a gun jama'arsa, ba za'a ce yana mulkin kama-karya ba, sai dai ko ya ya mu'amula ta had'aku zaka ji ba dad'i, zalinci ne tsagwaro a cikin mulkinsa.
Kamar yanda ya zamar masa jiki yanzu ma barasar shi yake ta d'irka, babban dakarenshi na gefe a tsaye yana kallon irin tanb'elen da yake, da k'arfi aka bud'o k'ofar wanda hakan yasa dogarin saurin d'ora hannunshi akan takobinshi yana sake had'e fuska, ganin Zafreen yasa shi d'auke hannu a takobin tare da d'an rusuna mata, a wulak'ance ta wurga masa harara tare da nufa wajen mahaifinta.
Tana isa kusanshi ta tsaya duk da tana kallon bayanshi ne, cike da rashin kunya da tijara tace "Baa, wai me yasa kake neman lalata sunan masarautar nan ne akan wata b'atacciyar yarinya? Ka manta da ita mana tunda ta mutu."
A sangarce ya juyo ya Kalle ta cikin halin maye, duk da yana namiji kuma dattijo amma kyakyawa, cikin layi yace "Ke...sha-sha-sha ce, kuma..mahaukaciya, ba za...ki gane...ba."
Da mamaki da kuma rashin jin dad'i tace "Baa ni ce mahaukaciya? 脌 kan wannan abar?"
D'an tsaki kawai yayi tare da tureta gefe ya zauna kan kujera mai kyan gaske, a hassale ta bi bayanshi ita ma cikin shigarta ta riga da wando k'anana, sai yalwataccen gashinta data d'aure tamau a kai wanda ya fito da kyakyawar fuskarta, cike da tsiwa ta shiga fad'in "Baa wai me yasa kuke min haka? Kai da Maa gaba d'aya ba kwa kulani, babu ruwanku da damuwata bare matsalata, shin Zafeera ita kad'ai ce kuka haifa?"
D'aga kanshi yayi ya kalleta cikin muryar maye yace "Ba zaki gane ba gimbiya, da namiji ce ke da kin fahimci abinda nake ji."
Da sauri ta matsa kusanshi ta dafa kafad'arshi tace "Baa, ka fad'a min matsalar ka zan fahimta, ni ma kamar namiji ce tunda zan iya yin komai da namiji zaiyi."
Wani malalacin murmushi yayi yace "Ke yarinya ce gimbiya, ki je d'akinki ki kwanta kawai."
Durk'usawa tayi tace "A'a Baa, ka fad'a min ni zan maka maganin matsalar ka, na gaji da ganinku kai da Maa kullum cikin tunanin yarinyar data jima da mutuwa."
Cike da damuwa 脿 fuskarshi yace "Ba zaki iya ba gimbiya Zafreen, ki b'ace min daga nan."
Mik'ewa tayi tsaye cikin sauri ta nufi in da dogarin nan yake, duk girmansa na jiki da kuma shekaru bai hanata saka k'afa ta hanb'areshi ba, sakamakon zuwan abun a bazata sai ya samu kanshi da fad'uwa k'asa, da sauri sarki Musail ya mik'e tsaye cikin layi kamar zai fad'i yace "Ke... Wai !"
Sai kuma yayi shiru saboda wuk'ar dogarin data d'auka a jikinshi ta d'orata a mak'ogwaron dogarin, hankali tashe dogarin ya zare ido dan yasan tsaf Zafreen zata huda wuyanshi, dan kuwa halin mahaifinta babu wanda ta rage bata kwasa ba na mugunta.
Juyowa tayi ta kalli mahaifin na ta tace "Na fad'a ma ka zan iya, ni ma namiji ce kuma zan ma ka anfanin da namiji ba zai maka ba."
D'aga mata hannu yayi ya k'yafato ta alamar ta zo, maida kallon ta tayi ga dogarin ta aje masa wuk'ar sannan ta nufeshi, kafad'arta ya dafa yana kallon fuskarta yace" Kin tabbata zaki iya?"
Jinjina kai tayi tace" Ka fad'i abinda kake so, ni kuma zan maka."
D'auke hannunshi yayi 脿 kafad'arta yace" Zafeera nake son gani a gabana, zaki iya kawo min ita?"
Mamaki ne ya bayyana a fuskarta tace" Mutanen gari suna cewa tun a ranar da aka saceta aka kasheta, ina ji 脿 jikina ta mutu."
Girgiza kai yayi yace" Bata mutu ba, ina jin haka a jikina."
Da wani mamakin tace" To amma tana ina? Na ga babu inda fadawanka basu zagaya ba a birni da k'auyukan k'asar nan, kuma yanzu haka an saka sanarwa ga duk wanda ya kawota zai tafi da arzik'in da har jikokinshi ba zasu k'arar da shi ba."
Gyara tsayuwa tayi tace" Ka na ganin idan har tana raye wani zai kasa kawota ne ko dan kud'in nan."
Wani kallo ya mata sai kuma yayi k'aramin tsaki yace" Zafreen wannan aikin na maza, ki je ki kwanta ki barni zan ci gaba da nemanta da kai na."
Da sauri tace" A'a Baa zanyi, zan je nemanta ni da kai na, zan tafi kaji Baa."
Wani kallo ya mata yace" Ta ina zaki fara?"
Turo k'aramin bakinta tayi tace" Baa na fad'a ma ka ina son aikin d'an sanda, zan je inda dayawa daga cikin abokanai na suke karb'ar horonsu, hakan zai taimaka min sosai wajen samota."
Dafa kanta yayi yana lumshe ido alamun bacci a idonshi sosai sannan yace "Kin tabbatar?"
Waina idonta tayi tace " Baa, ya kake neman nuna kasawata ne tun ban shiga aikin ba?"
D'an murmushin yak'e ya mata kawai ya juya zai shiga kusurwar da zata sadashi da d'akin baccinshi, saida yayi daf da shiga ta bishi da kallo tace "Amma ta ya zan ganeta bayan ko fuskarta ban gani ba da tana jaririya?"
Cak ya tsaya tare da juyawa ya kalleta, 脿 sanyaye yace "Ki samu babban malami Dhurani, zai fad'a miki komai a kan ta."
Nunota yayi da yatsa alamar gargad'i yace "Amma ki tabbatar kinyi nasara, idan kuma kika min wasa da hankali..."
K'wafa yayi ya juya zai shige ta sake fad'in "Baa wai me yasa ka damu da ita haka sosai? Ni baku so na ne?"
Wani murmushi yayi a tausashe wanda ya sake bayyanar da kyawun fuskarshi sannan yace "Idan Zafeera bata shigo hannunmu ba, daga ni har ke mun kad'e, dan babu makawa sai ta ga bayanmu."
Da wani mad'aukakin mamaki ta ci gaba da kallonshi tace "Kuma a haka kake son ganinta? Me zai hana ba zamu kasheta ba kafin ita ta kashemu?"
Da sauri sarki Musail da amintaccen dogarinshi suka zuba mata ido, kamar ba zai daina kallon ta ba sai kawai ya girgiza kai ya shige ciki, dogarin ma da sauri ya k'arasa gaban teburin ya kwashi k'aramar wayar hannun sarkin da kuma kwalbar barasarshi shi ma ya shiga d'akin kai tsaye.
Ita kam 脿 fusace ta fita tana jin lallai in ta had'u da ita kasheta ma zatayi kawai saidai ta kawo mishi gawarta, dan ba zata yarda yarinyar ta rabata da komai nata ba. Sanda cikinta ya bayyana haka gaba d'aya gari ake magana a kan ta, iyayeensu suke nuna mata soyayya fiye da ita, an haifeta ta b'ata amma a ce bata tsira ba? Sam ba zai yiwu ba.
*Washe gari* Zafreen ta gama duk shirinta ta nufi wajen malami Dhurani, bayanan daya bata dai kamar yanda ya fad'awa mahaifiyarta ne a sanda cikinta ya bayyana, dan haka ta dawo rai b'ace na jin cewa akan wane dalili ne k'anwarta ta zama zab'abb'iyar ba ita ba?
Tana d'akin mai cike da tarin tsari da kyau tana had'a kayanta dan tafiya, k'wank'wasa k'ofar d'akin aka yi saidai kafin ta bayar da izini aka shigo, juyawa tayi dan ganin wanene haka? Kyakyawar mahaifiyarta ce ta shigo ita d'aya babu rakiyar bayinta ko sabuwar jakadiyarta, tsurawa juna ido sukayi saida ta tsaya daf da ita, kwalliya da adon dake jikin sarauniyar Khazira wato *Juman* zaka rantse ba ta haifi Zafreen ba, dan irin masu kula da kansu ne fiye da kima.
Cike da nuna damuwa da alhini 脿 fuskar ta cikin tausashiyar murya tace "Gimbiya Zafreen, me kike shirin aikatawa haka? Me yasa zaki biyewa mahaifinki wanda kullum a maye yake? Ina zaki je neman 'yar uwarki...?"
Cikin daka tsawa Zafreen tace "Ba yar uwata ba ce, ita d'in' yarku ce da kuke matuk'ar so, wacce ba kwa kula kowa da komai saboda b'atanta, wato dan ita tana zab'abb'iya ko? To zan nemo muku farin cikinku."
Sake marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace "Zafreen ba haka bane, ke ma fa 'yarmu ce kuma muna sonki."
A hassale tace "K'arya ne, da kuna so na dana gani a zahiri."
Juyawa tayi ta rufe zip d'in jakarta, kallon hadimarta tayi dake tsaye bakin k'ofa ta mata alama da ido, d'aukar jakar tayi ta fita da sauri, ita ma zata wuce sarauniya Juman ta rik'o hannunta tace "Zafreen ki saurareni, ba zan bari ki tafi, yanzu ina zaki je? Ta ina zaki fara? Ba zaki tab'a samun ta ba."
A wulak'ance ta shiga yatsina baki tana fad'in "Makarantar horar da sababbin d'alibai zan nufa, zan karb'i horon zama 'yar sanda sannan na nemi taimakon abokaina, zamu sameta kinji ko."
Fizge hannunta tayi da k'arfi wanda yasa mayafin dake kan sarauniya Juman fad'uwa daga kafad'arta, kallon juna sukayi ido cikin ido sannan ta juya zata fita, cak kuma ta tsaya tare da juyowa a hankali, da mamaki ta dinga kallon wuyan sarauniyar kamar zata had'e ta.
Da sauri ta kai hannunta ta d'aga doguwar sark'ar gwal d'in dake wuyan sarauniyar, 'yar k'aramar sark'ar dake wuyanta mai bak'in zare da wani k'aramin zagaye kamar ziro, cike da al'ajabi Zafreen tace "Maa, wannan sark'ar ai jabu ce, ina ta asalin?"
Wani masifaffen murd'awa cikin sarauniya yayi inda ta zaro idonta kamar zasu fad'o, a take ta tambayi kan ta "Ya akayi ta gane?"
Dan ko sarki Musail bai tab'a lura da hakan ba, duk dai ma yanzu ya zama bugagge kullum a shaye yake. B'oyayyen numfashi ta sauke tana tunanin abinda zata fad'a mata, dan bata so asirinta ya tonu a yanzun, kafin ta ce wani abu Zafreen ta sake fad'in" Maa dake nake magana fa, ina sark'arki mai daraja take?"
Cikin inda inda tace" Am.. Zafreen, waccen sark'ar ta b'ata shekarar da mukayi tafi da mahaifinki wanda aka mana fashi a hanya, kinsan kuma sark'a ce mai darajar gaske, b'atanta 脿 wuyana zai tashi hankalin 'yan k'asar nan, shiyasa da taimakon malami Dhurani aka had'a min wannan d'in."
Marairaicewa tayi kamar zatayi hawaye tace" Na rok'eki 'yata karki bari sarki ko wani ya ji labarin nan, karki fad'awa kowa kinji."
Sam fuskar Zafreen bai nuna alamun gamsuwa da maganar mahaifiyar ta ta ba, sai kawai ta girgiza kai ta juya ta fice 脿 d'akin, da kallo ta bita saida ta ga b'acewarta kad'ai ta sauke ajiyar zuciya.
*Alhamdulillah*
_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._
_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._
_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *87-62-53-02* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._
Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.
_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai *Samira*._
01/01/2022 脿 11:30 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._
_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._
_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._
Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.
_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._
_Bismillahir rahamanir rahim_
*3*
*29/12/2020*
*Larhjadin*
Da gudu ta fito daga motar ta tunkari dattijuwar dake tsaye da alama jiranta take, ihu ta saki tana fad'in "Mommaaaaa."
Da fara'a matar ta tunkareta, amma sarautar Allah kawai sa茂 ta rusuna dake nuna girmamawa ga matashiyar, cak yarinyar ta tsaya ta had'e fuska cikin shagwab'a tace "Momma, ya kike abu haka kamar zaki rusuna min?"
Cikin dubara da wayancewa ta saki murmushi tana mai dafa kafad'arta tace "Haba dai *princezna* (gimbiya), abu ne naji na taka k'afata."
Dariya budurwar tayi ta rumgume maman na ta tana fad'in "Momma na nayi kewarki."
"Ni ma haka." Ta fad'a tana lumshe ido wani dad'i na ratsata sakamakon had'a jikinta da tayi da sanyin idaniyar ta ta, sun jima haka kafin su raba jikinsu, kallonta dattijuwar ta dinga yi daga k'asa har sama.
Dogon wando ne matsatse bak'i sai farar riga mai k'ananan hannu, takalminta flat ne masu d'amara fara, k'aramar jaka ce a kafad'arta bak'a sai hular dake kanta ta sanyi, baya ga haka babu wani abu mai kama da kwalliya ko ado a tare da ita bayan wata siririyar sark'a dake wuyanta mai kalar d'anyan gwal sai wani zagaye kamar ziro.
Kyab'e fuska matar tayi tace "Gimbiya ta, ya naga kin k'ara ramewa? Dubeki fa."
Dariya tayi data bayyanar da 'yan hak'oranta na gaba kamar na b'era tace "Momma kin manta karatu na ne? Ina shekarata ta k'arshe ne, shiyasa na dage nake so na ga na fito a major ta foresti猫re."
Girgiza kai matar tayi tace "K'iriniya irin ta ki sai nema gimbiya."
K'yalk'yakewa tayi da dariya ta dafa kafad'arta tana fad'in "Gimbiya gibimya kullum, wai ni Momma ko dai mijinki sarki ne ban sani ba?"
Yanda tayi maganar cikin zolaya yasa matar yin dariya ita ma sannan tace "Maza ki samesu ku wuce, bana so ki k'ara ja min maganar da zan je bayar da hak'uri."
Turo baki tayi tace "Momma dama kin gaji dani?"
Dogo kuma siririn hancinta ta kama ta ja sosai tare da juyawa da ita suka nufi motar dake tsaye k'ofar gida, cikin kukan sangarta take fad'in "Momma ba zaki barni na ga Papa ba? Please."
Dungure mata kai tayi tace " Ban hanaki yi min yaren da ba namu ba?"
Da yatsunta tayi alamar sakata a bakinta tare da cewa "Nayi shiru, ni na tafi, sai na dawo, ki gaida Papa."
Duk tayi maganar ne tana hawa matakalar motar k'waya uku sannan ta juyo, da mamaki maman tace "Amma ba kin zo ne dan muyi magana ba?"
Dariya tayi tace "Momma zan fad'a miki."
"Yaushe kuma?" Ta fad'a da jimami, dariya ta sake yi tace "Momma zan kiraki idan na koma."
Girgiza kai kawai tayi ba tace komai ba, juyawa tayi zata k'arasa shiga sa茂 kuma ta juyo ta kalli maman na ta, ganin Maman na ta tayi ta sake irin sunkuyawar d'azu tace "Sauka lafiya princezna."
Sam bata yi tunanin komai ba har motar ta su ta fara tafiya, kujerarta dake baya ta wuce ta zauna tare da cire hularta, hakan ya bayyanar da kanta wanda gashi ya fara tohowa, dan dukansu yan matan dake motar kowace kan ta k'wal kwabo ne sakamakon aikin da suke da burin yi.
Wata budurwa ce tace "Hankalinmu zai kwanta yanzu tunda an kawoki gidanku kin ga Momma."
Wani kallo ta watsa mata lokaci d'aya ta d'auke kan ta, tab'e baki budurwar tayi ta d'auke kanta ita ma, tafiya suka yi mai nisan gaske kafin suka isa nesa da garin, wani babban k'ofa wacce aka rubuta sunan makarantar *Skola skoli novych smestnancov* (makarantar horar da sababbin ma'aikata) da yaren slovaque suka tsaya tare da yin oda, jim kad'an aka bud'e musu suka shiga.
Makaranta ce amma kamar gari guda, zaka tabbatar da girmanta ne kawai idan ka ga b'angarorin dake ciki, duk wani mai sha'awar karatun aikin saka kaki to nan yake ziyarta, kuma wanda ke karb'ar horon aikin soja ba zai san da zaman mai karantar horon police ba har sai in k'arshen sati ne da ake basu damar fitowa farfajiya har ma mai buk'ata ya fita waje.
Yanzu ma a b'angaren masu karantar ilimin *eaux et for锚ts* (gandun daji/ruwa da daji) motar ta aje su suka dinga shiga ciki, kowace na ta d'akin ta nufa mai d'auke da gado guda hud'u.
Kan gadonta ta zauna dan tasan yanzu wanka zasu fara dashi, ita kuma ba zata tsaya bin layi ko kuma zaman jira babu kaya a jikinta ba.
D'aya daga cikinsu ce ta shiga wanka sai biyun da suka cire kayansu suka d'aura towel, d'aya daga ciki ne ta kalleta tace " *Ayam*, wai me yasa kullum Mommanki take rusuna miki kamar wata shugabarta? Ko al'adarku ce haka?"
D'aga kai tayi ta kalli *Deeyam* d'in tare da gyara zamanta, saidai ba tace komai ba face k'ura mata ido, a zuciyarta kuma tunani take ita kanta ta fara ankara da haka, sau da dama idan ta lura tayi magana sai Momma ta kawo mata uzirinta.
Ganin ba tayi magana ba kawai yasa Deeyam share zancen tare da kallon gashin Ayam d'in tace "Amma Ayam ba kya tsoron hukumar makaranta ta ganki kin ajiye gashin nan? Za fa su iya korarki dan kin taka musu doka kuma da gangan."
Mik'ewa tayi tsaye tana sauke numfashi, hannu biyu tasa ta tattaro gashin kan na ta ta had'e wuri d'aya sannan ta kalleta tace "Kinga fa jibi ne shagalin k'arin haihuwata, nayi niyya 脿 wannan shekarar ba zan yi bikin k'arin shekarar nan da sulb'eb'en kai ba, dan haka in zaki iya ki je ki fad'a musu na tara gashi."
Dariya Deeyam tayi tace "Amma dai zaki mana babban shagali a wannan shekarar ko?"
Kanne mata ido tayi tace "Dole mana, shekarar mu ta k'arshe ce fa."
*Giobarh*
Kalar fatarshi kawai zata nuna maka lallai shi d'in daga gidan hutu yake, duk da yana da duhun fata amma kuma bak'inshi mai birgewa ne da d'aukar ido, tsiri-tsirin gashin kansa dake ta k'yalli yayi wara-wara alamar ana b'ata lokaci sosai wajen gyarashi.
Leb'enshi na k'asa ya lashe yana kallon abokin na shi da k'ananan idonshi masu zurfi, kyakyawan abokin na shi kam dariya ya saki tare da k'ok'arin gimtseta 脿 harshensu na Gallois yana fad'in "Haba abokina, ka bari a rage maka sumar nan mana, taya kake tunanin zuwa wannan wajen a haka kuma da sunan kai malami ne?"
A mugun hassale ya mik'e daga kujerar yana sake murtuke fuska, kallon mutumin dake tsaye gefensu yayi rik'e da jakar kayan aikinshi, a dak'ile yace masa" Fita a nan."
Da sauri ya sunkuya ya juya zai fita, abokin ne yayi saurin fad'in" Kaga, jirani 脿 waje."
Wata harara ya zabga masa ya nunashi da yatsa yace" *Haman* ka daina min haka bana so."
Shima fuska a had'e yace" Na k'i na daina maka hakan *Umad*, me kake nufi ne wai?"
Kawar da kansa yayi yace" Kai zan tambaya ai me kake?"
A hankali Haman ya matsa kusan Umad d'in murya a sanyaye yace" Umad ka saurare ni, kaga fa gobe ne tafiyarka, kuma in da zaka je da abinda zaka je yi abune mai matuk'ar mahimmanci, to me yasa ba zakayi duk abinda kasan zai kusanta ka da lamarin nan ba?"
Had'e hannaye yayi ya rumgumesu a k'irji ya sake gimtse fuska a dak'ile yace" Me kake nufi?"
Jinjina kai yayi yace" Yawwa! Ka gane ko? Duk da kai d'in malamin bogi ne, amma ai ba kowa ya sani ba, kenan dole kayi kama da malamin horaswa, daga gobe fa kakin babban major na gandun daji zaka fara sakawa a jikinka, to kana ganin ya kamata a ce ka je a haka?"
Shiru d'akin ya fara d'auka na wasu dak'ik'u, a tausashe ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kalli Haman cikin yatsina fuska yace" Na sani Haman, amma ka fahimci wani abu, ni ba zama bane zai kai ni, da na je wurin nan abinda ya kaini kawai zanyi na juyo, ban damu da wata shiga ta ba."
Cike da gamsuwa Haman yace" Na fahimceka, amma ni ina so ka tuna da nagartar aikinka."
D'an k'ura mishi ido yayi na wasu dak'ik'u sai kuma ya jinjina kai alamar gamsuwa, hannu ya mik'a mishi sukayi musabaha tare da d'orawa da fad'in" Ka cika alk'awarinka Haman, duk rintsi babu wanda zai san komai akan aikina da kuma shirina, na rok'eka."
Jinjina kai yayi yana murmushi yace" Baka da matsala da wannan d'an uwa, fatan nasara."
Hararanshi yayi yace" Ka jira har lokacin shiga na jirgi yayi mana."
'Yar dariya yayi yace" To ai kace sammako zakayi, ni kuma ban iya tashin safe ba, kaga kenan saidai muyi waya idan ka sauka."
Dukanshi yayi 脿 kafad'a yace" Baka isa ba ai yaro, kai zaka kaini har filin jirgi, ragon maza kawa."
Shafa yalwatacciyar sumarshi yayi yace" Ni ma zan zama jarumi, da fari na saka rai a lokacin da mai martabanmu ya so auro mana zab'abb'iya, to amma da naga an kasa cimma burin sai kawai ni ma na cire rai tare da sauyawar tsarukan k'asar nan."
Girgiza kai Umad yayi bai ce komai ba ya koma kan kujerar ya zauna, ganin haka ya sa Haman lek'awa ya kira mai askin dan ya rage wa Umad tsirakun daya tara a kai."
*Larhjadin*
Da sauri suke ta fitowa daga ajin suna tunkarar sale a manger (wajen cin abinci) dan minti sha biyar malamin ya basu.
Ayam kam ba abincin ne ya dameta sai son tayi waya da Momma ta, hakan yasa ta nufi hanyar fita daga b'angaren na su, inda a nan ke da mai wannan alhakin. Sauri take sosai tana k'ara gyara zaman jakarta a bayanta, kusa da k'ofar zata fita wasu 'yan matan ma suka shigo, kaucewa tayi suka fara wucewa da d'ai-d'aya, amma Zafreen dake k'arshe sai ta shiga kallon Ayam tana yamutsa fuska tana jin gabanta na fad'uwa.
Ayam ma kallonta ta shiga yi da idonta wanda basu da d'igon bak'i ko d'aya, daga kalar farin data mamaye girman idon, sai k'wayar mai d'auke da launin shud'i mai hasken sararin samaniya, 'yar k'aramar k'wayar kuma wani irin ratsin fari ne mai kama da zaiba, ga shi kuma launin shuud'in har wani tsage-tsage gareshi, daga can cikin k'aramar k'wayar kuma sai ka rantse ruwa ne kake kallo wanda zasu iya tafiya da kai.
Da sauri Zafreen tayi k'asa da idonta tana jan tsaki, a ranta kuma cewa tayi "Mayya kawai."
Ayam kam da sauri take dama rab'ata