"Mijin da zai aureki."
Da wani mamaki tace "What!"
Ba tare daya daina murmushin ba yace "Ba zaki gane komai ba a yanzu, ki fara shiga ciki ki shirya dan ki samu ki suturta min jikinki, idan kin fito zamuyi magana dake."
Rumgume hannaye tayi tace "Kafin nan ka fara amsa min wad'annan tambayoyin nawa."
Girgiza kai yayi yace "Zafeera mahimmanci gareki a wajena, idan na mayar dake sarauniyata ko fuskarki bana so kowa ya gani, ta ya zan yarda ki tsaya a haka wasu na kalleki? Kin san wacece ke kuwa? Kin san girma da matsayin darajar da kike da shi? Allah ya karramaki dan haka zan tayaki karrama kan ki."
Cikin jin haushi tace" Tukuna ma wane banzan suna kake kirana da shi ne?"
Murmushi yayi mai kama da dariya ya juya zai fita yana fadin" Ki fara shiryawa sannan, zan amsa duk wata tambayarki."
Da wata matsiyaciyar harara ta bi bayanshi har ya b'acewa ganinta, juyawa tayi a masifance tace wa matan" Sai ku tashi mu tafi ko? Zaku tsaya k'aton gardi na dukanku kamar ubanku, wahe shi ma tukuna?"
Yanda tayi tambayar tana rik'e k'ugu yasa d'aya a ciki tace" Kamar d'a yake ga sarkin k'asar nan."
Yamutsa fuska tayi tace" Kama ne ma yake ba d'an sarkin bane, to wace k'asar ce wannan?"
D'ayar ce ta amsa da" Egypt."
Da mamaki ta kallesu tace" Egypt? Kuna nufin nan a Egypt nake?"
Jinjina kai sukayi hakan yasa ta ita ma ta jinjina kai ta k'arasa bakin kofar d'akin, bud'e mata sukayi ta shige suka bi bayanta.
*Khazira*
A kausashe ya buga teburin yana kallon Adah da kan shi ke k'asa kamar zai fasa d'akin yace "Ta ya ya haka zai faru? Sai da na ce zan je da kai na kuka tabbatar min da zaku iya, yanzu me kuka aikata kenan?"
Cikin girmamawa Adah yace "Ka gafarce ni sarki, mun tarar da hatsaniya ne a makarantar, ga dukkan alama wasu abokan gabar ne suka fara ganota shiyasa suka tayar da zanga zangar, da haka kuma sukayi nasarar d'auke mana gimbiyoyinmu."
Da wani sabon mamakin yace "Me? Gimbiyoyi kuma?"
Cike da d'ar d'ar yace "E shugabana, gimbiya Zafreen da gimbiya Zafeera sun b'ata a cikin tarzomar nan."
Da bala'in k'arfi sarki Musail ya cire kambun dake kan shi na tsantsar gwal daya sa aka k'era masa dan alfahari ya jefar a k'asa, a fusace ya juya b'angaren da Dhurani yake ya kalleshi, sai kuma ya tattare rigarshi dake jan k'asa ya tunkari hanyar fita, rufa masa baya sukayi inda waziri Khatar ke fadin "Sarki na, ka nutsu mu bi komai a hankali, na tabbata sarki Wudar ne ya d'aukesu, dan shi ke da burin son d'aukar fansa a kanmu."
Dakatawa yayi ya juya ya kalli Khatar da yayi maganar, jinjina kai yayi yace "In kuwa hakane sarki Wudar ya jaza ma k'asar sa yak'in duniya na uku, dan babu abinda zai hanani shiga masarautarsa sannan nayi fata-fata da su."
Dhurani ne yace "A'a sarkina, ba da haka zamu fara ba, kafin mu farmake su buna buk'atar samun tabbaci suna hannunshi, daga bisani koma menene sai ya biyo baya."
Adah ne yace "Hakane shugabana, dan na tabbata kamar yanda muke tsananin buk'atar gimbiya Zafeera, haka shi ma sarki Wudar, ba kuma zai kamata bane dan ya kasheta."
Cikin hassala yace "To yanzu ya zamuyi? Me ye mafita? A yanzu na fi buk'atar Zafeera a kan Zafreen d'in."
Adah ne yace "Wannan mai sauk'i ne shugaba na, zanyi magana da d'aya daga cikin masu lek'en asirinmu dake sintiri a cikin fadarsa."
Nunashi yayi da yatsa yace "Ka tabbatar nan da zuwa yammacin yau ka samo min masaniyar komai."
"Angama yallab'ai." Ya fad'a yana rusuna masa, saida suka ga ficewarsa kafin su ma duk suka bar wurin babu wani mai farin ciki da yanayin da yake ciki, dan su kansu sun fi buk'atar a samu Zafeera a kuma k'ara mata gudu zuwa lahira, dan su canjin da aka ce zata kawo shi ne yafi tsaya musu a rai, a ganinsu zata rabasu da addinansu ne, muk'amarsu da martabarsu, hakan kuma ba zasu bari ya faru ba mundun ran su.
Bai zame ko ina ba sai kurkukun sabah, tsabar a rikice yake bafade d'aya ne ya take masa baya zuwa can, hannunshi rik'e da doguwar rigarshi cikin sauri har suka isa can, mai tsaron d'akin da take ne yayi saurin bud'ewa sarki Musail ya shige.
Tana zaune rakub'e a jikin bangon ta had'a kai da gwiwa, idonta a rufe suke ruf dan ko ta bud'e babu abinda take gani face dishi-dishi da jiri, har saida ya isa gabanta ya durk'usa irin tsugunnon maza ya finciki gashin ta sakamakon gyalenta daya sauka a kan kafad'unta, da k'arfi ya d'ago kan ta har saida ta saki yar k'ara saboda zafin da ta ji, da k'yar ta d'aga idonta ta kalleshi.
Cikin gadara da cika baki ya mata murmushi yace "To ya kike sarauniyata?"
Kamar wacce ke cikin maye tayi luuu da idonta ta saki wani murmushi ita ma tace "Yan...da kake, haka na ke."
Tura kanta yayi da k'arfi har saida ta bugu ga bango ya fashe da dariya yace "K'arya kike sarauniyata, ni ina lafiya kuma ina cikin farin ciki."
Cikin layi tace "Kai ma ba gaskiya ka fad'a ba sarkina, hankalinka a tashe yake kamar yanda muryarka ke b'arin tsoro saboda ka fara jiyo k'amshin mutuwarka."
Da sauri ya mik'e tsaye yana lumshe idonshi dan gaskiya ta fad'a kam hankalinshi a tashe yake, cike da k'arfin hali ya kalleta yana nunata da yatsa yace" Ki zuba ido ki gani Juman, gobe warhaka ke da 'yarki duk zaku mutu, wannan alk'awari na ne."
Malalacin murmushi tayi ba tace komai ba har saida ya fita a wurin, a zahirinta kam bata nuna damuwa ko tsoron abinda ya fad'a ba, amma k'asan zuciyarta cike take da tsoro da alhini da zulumin abinda zai iya aikatawa.
*Larhjadin*
Ko da Umad ya isa ya samu Haman a masaukinshi fad'a masa abinda ya faru a makaranta yayi, saidai haka kawai ha k'i yarda ya fad'a masa batun auren nan, dan dama yayi ne saboda yasa hankalinsu Habbee ya kwanta su ji nutsuwar zuci su tabbatar tana hannu na gari, duk da dai yasan ba lallai sun yarda da shi ba musamman da suka san waye, amma dai yanzu a tunaninsu tana tare da shi kuma ba zai bari a cutar da ita ba kamar yanda ya fad'a musu, dan haka a sanin da yake da shi yasan aurenshi da Ayam zai cika k'aida ne idan da amincewar iyayenta mahaifa tunda suna raye, shaidu da kuma sadaki.
Cikin tashin hankali Haman yace "Me? Yanzu kana nufin ta sake b'ata kenan?"
Jinjina kai yayi ya kalleshi yace "Hakan alamu suke nunawa, amma a yanzu zamu iya cewa mun san inda take."
Cike da k'aguwa yace "A ina kenan?"
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Zan koma gida yanzun nan, ta hakane zan san inda take."
Da mamaki Haman yace "Kana nufin zaka koma masarauta kenan?"
Jinjina masa kai yayi alamar e, cikin d'ar d'ar yace "Bana tunanin sarkinmu ya sameta, me zai hana ka fara saka ido akan Bukhatir?"
Da wani mamaki Umad ya kalleshi ya d'aga labb'enshi da k'yar yace "Bamu tab'a maganar Bukhatir da kai ba, ya akayi ka san shi?"
Zaro ido yayi alamar firgici, a take kuma ya had'e komai ya saki murmushi yace "Haba dai, ka manta ka min maganar sa? Daga gareka na ji batunsa ai."
Cike da son waskewa ya d'an zagaya ya matsa daf da shi ya dafa kafad'arshi ganin kamar bai yarda da abinda ya fad'a ba yace "Ka gane ko, ina ga zai fi ka fara ta can d'in, zuwa gobe sai mu koma tare."
Wani arnan kallo Umad ya masa sai kawai ya jinjina kai alamar to sannan yace "Shikenan."
Sallama sukayi inda Umad na d'aukar hanya masaukin daya fara sauka ya k'arasa ya had'a kayanshi, dan yayi niyya yau ba sai gobe ba zai d'ora da neman Ayam, dan sai yake gani kamar Haman ya manta shi ne wajen rashin yarda da kafuwa, duk aminci da yardar dake tsakaninku ba zai saka shi d'auke ido a kan ka ba, bare al'amari na wacce yake da tabbacin za'a iya sadaukar da bilyoyin kud'i don samunta. Yana gama shiryawa saida ya fito ya d'auki hanyar zuwa filin jirgi sannan ya kira canal Jacob dan sanar da shi aikinshi ya k'are, dama hanya aka masa a gwamnatacce dan cika aikinshi, to tunda ya tabbatar da wacce yake nema ai shikenan.
*Bayan awa shida (Giobarh*: yana sauka a k'aton jirgin emirates d'in motoci guda hud'u ne suka zo dan d'aukarsa, sanda suka shiga rusuna masa d'aya daga ciki ya karb'i jakarsa mamaki ya shiga yi na samun tabbacin abinda yake zargi, dan ko mahaifinshi sarki bai fad'a ma zai zo ba, amma ga tarba ta musamman daga masarautarshi.
Limozine d'in da aka bud'e mishi ya shiga ya zauna suka mayar da k'ofar aka rufe suka d'auki hanya, gudu ake sosai dan tafiya ce mai nisan gaske daga filin jirgin zuwa fadar ta su, a d'an lokacin nan kuma tangale hab'arshi yayi yana kallon titi a zahiri a bad'ini kuma tunanin komai daya faru kuma yake faruwa yake, da wannan suka share awa d'aya a hanya kafin motocin su tsaya a k'ofar gidan suna oda.
Masu gadi biyu ne suka shiga jan k'ofar suna bud'eta tsabar girmanta da kuma nauyin da take da shi, danna hancin motocin sukayi a cikin farfajiyar wanda shi kan shi filin gidan wata k'asar ce daban data gaji da kyau da had'uwa.
*K'arshen free page, idan kina da buk'ata garzaya ki biya naki, sai kun zo masoyan asali.*
*Masoya na da suka biya kud'insu dan wannan littafi ina son sanar da ku zaku min alfarma d'aya, zan dinga sakar muku sabon shafi ne sau biyar a rana, saidai bai tsayar da ranakun ba gaskiya, kamar yanda a kowace rana ogana zai iya shigowa gari, hakan kuma na raunana rubutu na na kasa samun kai na, fatan zaku fahimce ni.*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels