Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 10
lamunce masa ya karanta maka me takardar tak'unsa, daga sarkin Giobarh fa sak'on ya zo." Ita ma banza ya mata sai ma 'yar wak'ar daya shiga rerawa yana fad'in "Lu'u lu'u ki dawo gareni, lu'u lu'u ki dawo gareni, idan babu ke a rayuwata, ji nake kamar ma na mutu." A mugum hassale matar ta mik'e tana daka tsawa da fad'in "Ina! Ba zai yiwu ba, Bukhatir ka fara wuce gona da iri fa, wannan wace irin rayuwa ce ? Me kake neman ka mayar da kan ka ne ? Lu'u lu'un banza da..." Tassssss! Ya d'auke fuskarta da mari, tuni bafaden dake tsaye ya rintse ido dan yasan dama haka zai faru, shi yasan yanda Bukhatir ke masifar son wannan lu'u lu'u, dan haka shi ma yake kaffa-kaffa indai abinda ya shafeta ne. Tunda ta sunkuya ta dafe kunci kasa d'agowa tayi, a nutse kuma a ikonce tsabar yana ji da kansa da burin mallakar masarautar Egypt ya nunata da yatsa ya mata alamar ta fita a nan, d'auke hannunta tayi daga kunci ta kalleshi da ido sun mata jajir, cikin shashek'a tace "Ni ka mara saboda na zagi wata ban..." Tauuuuu! Ya sake d'auketa da wani marin kuma, yanzu kam a hassale kuma a gigice cikin d'aga murya yace "Ki b'ace min da gani *Zeyfi*, kuma kar ki sake gigin tab'a kimar lu'u lu'uta, idan kuma kika sake to a bakin aurenki." Zaro ido tayi baki bud'e, ai da gudu ta fita a d'akin rigarta na jan k'asa, saida ya ga ficewarta yaja wawan tsaki, kallon bafaden yayi yace" Me ye? Me yace? " Jiki na kakkarwa ya shiga warware takardar, saida ya bud'e ya fara karantawa kamar haka _" Mai girma Bukhatir, wannan takardar d'amba ce ta neman sulhu tsakanina da kai, bisa tabbatarwa da mukayi mu da kai abu d'aya muke nema, zai fi idan muka had'a k'arfi da k'arfe wajen cimma burinmu, dukanmu manufa d'aya garemu a kanta, manufar kuwa ita ce *d'aukar fansa* ga sarki Musail, zanyi farin ciki idan ka had'a hannu da ni, hakan kuma zai zama k'aruwarka, idan ka amince da buk'atata ka turo min da sak'on gayyata zuwa fadarka, sak'o daga sarki Wudar."_ Zaune yayi ya tsunduma tunani, ya d'an jima haka kafin ya kalli bafaden yace "Me kake tunani game da hakan?" Cikin ladabi yace "Shugaba, a gani na wannan wata dama ce ta cimma abinda muka jima muna nema, duk da abu d'aya muke nema da su, amma ba kamar yanda sarki Wudar yake tunanin manufar d'aya bace." Jinjina kai Bukhatir yayi yace "Gaskiya ne, idan har muka had'a hannu da shi muka sameta, a dalilinta zan hau k'aragar mulkin kakan Zafeera ma'ana mahaifin mahaifiyarta Juman, idan haka ta kasance kuwa zan zama mai sa'a a doron duniya." Jinjina kai bafaden yayi tare da fd'in "Hakane shugaba na." Wani k'ataccen murmushi ya saki ya gyara zamanshi k'afa d'aya kan d'aya yana wasa da yatsunshi yace "Tun ina k'arami nake son hawa kujerar mulkin nan, saidai sarautar a hannun yayan mahaifina take, hakan yasa shi ke mulkar gaba d'aya k'asar nan, hatta da mahaifina da suka fito ciki d'aya shi ma duk'ar da kai yake a gabansa, sannu sannu sai na fara karkata hankali na kan 'yarsa k'waya d'aya tak, murmushin da take min na d'auka na so, ashe ita tana can tana soyayyarta da wani ba ni ba, hummmm! To me ya kamata na yi? Sai na zauna na zama d'an kallo kenan?" Wani malalacin murmushi yayi tare da girgiza kan shi sannan ya mik'e ha shige uwar d'aka yana fad'in" Ka tura masa da takardar gayyata." Sunkuyawa yayi alamar amsawa sannan ya fice zuciyarshi cike da farin ciki dan bai yi tsammanin zai amince ba. *Masarautar Khazira* Zaune suke akan babban teburin cin abinci kamar na bak'i, suna had'a ido ya sakar mata murmushi yace" Sarauniyata." Had'e fuska tayi ta kawar da kan ta, murmushin gefen labb'a yayi yana kallon farantin gabanshi da babu komai a ciki yace" Kina hushi dani saboda na fad'a miki ni na kashe mijin da da zai aureki, to me yasa kike tunanin zan k'yaleshi? Ba rabonsa bace ke, ki manta kawai." Girgiza kai tayi cike da takaici tace" Baka da tausayi Musail, bayan shi mutane nawa ka kashe? Yanzu ma gashi saboda son zuciyarka 'yata data rage min ina kallo ina jin dad'i, ka turata neman wata wacce ba zata tab'a samunta ba har abada." Cikin d'aga murya tace" Idan ta mutu ita ma sai na yi me kenan?" D'aga kai yayi ya kalleta a sanyaye yace" To sai me? Ni ba mijinki bane? Ai zan iya sake baki wasu 'ya'yan idan kina so." A hassale ta mik'e tsaye tace" Tirrr! Har abada ba zan bari ka sake rab'ar jikina ba, kuma ka sani burinka akan y'ata ba zai tab'a cika ba." Da mamaki ya kalleta yace" Me kike nufi Juman?" Cike da gadara tace" Ina nufin yata da kuka yi yunk'urin kashewa kai da Dhurani, na san komai da kuka shirya a kan ta, ba zaku tab'a nasara ba ka ji da kyau." Tsaye ya mik'e yana mata wani kallo yace" Juman, ko dai ke kika tseratar da yarki?" Ba tare da tsoro ba tace" K'warai, ni na kub'utar da ita, ka samota mana idan ka isa." Juyawa tayi zata bar gurin ya daka mata wata irin tsawa yace" Jumaaaaaaann." Dakatawa tayi ta juyo tana kallonshi, a sukwane ya nufota da babbar rigarshi, kallonshi ta dinga yi har saida ya zo kan ta, bai tsaya komai ba ya gaura mata mari, kafin ta ankara ya shak'i wuyanta da hannu d'aya, duk da shi ya shak'eta amma kuma idonshi sun bala'in yin jajir dasu duk sun fito tsabar takaici da b'acin rai, cikin fitar hayyaci ba tare da duba yanda take d'aukar numfashi ba kamar zata mutu yace "Sai na kasheki, sai na kashe ki Juman, ba zaki tab'a zama silar gurguncewar rayuwata ba kuma na k'yaleki." Hadimai biyun da suka taho da kwanukan abinci ne suka tsorata ganin wannan lamari, juyawa sukayi zasu fita inda babban bafaden sarki Musail *Adah* yayo kansu da gudu, hannayen sarkin ya rik'e yana bashi baki da yayi hak'uri ya sakeg'ta zata mutu. Hadiman da suka fita ne suka had'e da waziri Khatar zai shigo ciki shi ma, ai a tare suka sake dawowa da hanzari bayan sun fad'a masa, yana zuwa shi ma kamawa yayi suka shiga k'ok'arin b'amb'areta, da k'yar sukayi nasarar k'watarta a hannunshi duk ta galabaita dan k'iris ya rage ta suma, cikin hargagi sarki Musail yake nunata da hannu yana fad'in "Ba soyayyar da kika tabbatar ina miki fiye da komai bace ta sa kika min haka ? Ai dai tak'amarki ina sonki dan haka babu abinda zai faru ko? To ki ji da kyau Juman sai na hukuntaki, ke baki san waye ni ba shiyasa, amma da sannu zaki sani tunda kika tab'oni, kuma bak'ar 'yarki zan kamota abisa taimakawar bayina, a gaban idonki zan yanka wuyanta, dan ba zan bari yar dana haifa ba ta kasheni sannan ta rabani da mulkina ba." Adah ya kalla yace" Kai Adah, ka mata jagora zuwa kurkukun k'asa na *Sabah*." Maida kallonshi yayi gareta har yanzu da numfashinta take fafutuka yace" Zaki d'and'ani uk'ubata Juman." Gefenta sarkin yak'i Adah ya tsaya hakan yasa ta kallonshi sannan ta kalli sarki Musail tayi dariyar mugunta tace" Uk'ubarka wacce ce ban sha ba ? Kai dabba ne ba d'an adam ba, kuma 'yata tafi k'arfinka banza kawai." Kan ta ya sake yi da azama waziri dake ta rarraba ido tsakaninsu yana son fahimtar inda suka dosa ya shiga tsakaninsu, cikin d'aga murya sarki Musail yace" Ka fitar min da ita a nan, kuma na tsawon kwana uku ban yarda a d'iga mata ko da tafi d'aya na ruwa ba bare abinci, wannan umarni na ne." Fashewa tayi da dariya tace" K'arshenka ya zo Musail, na ga hakan nan ba da jimawa ba, ka tabbatar min da mafarkina zai zama gaskiya dalilin uk'ubar nan da kake neman sakani a ciki, tabbas 'yata zata zo a dalilin haka, wannan shi ne ma'anar hannun da take mik'a min a cikin kowane mafarkina." Cikin ladabi Adah ya mata nuni da k'ofa, juyawa tayi da sauri ta shiga takawa tana fad'in" Ku zuba ido ku gani, da sannu sabon tsari zai zo a k'asar Khazira, 'yata zata canza komai ko da hakan na nufin ta cire kawunanku ne, mak'ask'anta kawai." A dakonce waziri ya kalli sarki Musail da mamaki yace" Sarki na ka tabbata hukuncin nan ne ya kamaceta?" A hassale yace" To da me ya kamata nayi?" Dogon tsaki yayi ya nufi hanyar fita yana fad'in" Ka nemo min babban malami a duk inda yake." Sunkuyawa yayi yace" Angama shugaba na." Saida ya shige sannan ya d'aga kan shi, jiki a mace yana ta tunanin abinda ya faru yanzun ya fita isar da sak'on sarkin. *Wannan littafi na kud'i ne, ku garzayo ku biya na ku dan jin yanda zata kaya, dan an kusa rufe free page, dan neman k'arin bayani tuntub'i lambar dake sama, zan ga masoyan k'warai da masoyan baka馃槀.* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:32 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *7* Ta b'angaren wurin kwanan hadimai da bayin gidan suka bi suka wuce, yanda hadiman suka yi tsuru suna kallo cikin jimami ana wucewa da sarauniyarsu yasa duk suka ji ba dad'i, a sanyaye take wucewa har saida suka kusa shiga ta wata kusurwa, d'aga kanta tayi dake k'asa ta kalli wani d'aya daga cikin fadawan gidan, wani k'ayataccen murmushi ta sakar masa ta juya harshenta zuwa larabcin parsi tace "Ko ta halin yaya kayi k'okari ku had'u da ita, ka sanar mata ta fad'a musu su ninka kulawarsu da saka ido a kan ta, dan komai ya kusa fitowa fili." Sake fad'ad'a murmushi tayi ta d'ora hannunta akan shi kasancewar matashi ne tace "Ka kula da kan ka." Duk da hawayen dake taho mishi saida ya rusuna mata yana jinjina kai alamar karb'ar sak'onta, wucewa sukayi haka hadiman wasu ke kuka wasu kuma jimamin ne kawai a fuskarsu, a haka aka shiga da ita wata hanya dake sadar da mutum zuwa k'asa, tafiya sukayi mai nisa a cikin wurin da zaka rantse a wata duniyar kake ko kuma wani ramin b'era ne, banda jan fitilun da suka haska gurin da zai kasance mai duhun gaske. A hankali suka fara isowa kurkukun inda d'akunan suke a laye kowane mutum d'aya ne a ciki, k'ofofin bak'in k'arfe ne da manyan kwad'on da ake datse k'ofar, daga sama kawai ake k'aramar tagar da iya fuska zata iya lek'awa ta ga na ciki. A b'angaren dama ya bud'e mata wani d'aki ta shiga sannan ya mayar ya rufe, babu komai a d'akin banda shafaffen simiti, baya ga haka babu komai a d'akin dan ko wuta babu kuma ba wata taga bayan wacce ke jikin k'ofar, ko haske iya na fitilun dake corridor wurin ne ke d'an haskaka sauran d'akunan. A hankali ta sulale ta zauna a wurin tana fashewa da kuka, kukan ba wai na canjin daya risketa bane a take, na yanda 'yarta da kuma marik'anta zasu kasance, tasan dole su sake jajdadda nemanta, suna samunta kuma kasheta zasuyi, wannan tunanin yasa ta yin kuka kamar zata shid'e. *Giobarh* Suna had'uwa da mutumin ya mik'o masa k'aramar farar takarda a nad'e, karb'a Haman yayi ya bud'a takardar ya karanta sannan ya kalleshi yace "Ka tabbata?" Jinjina kai yayi yace "Na tabbata yallab'ai." Shi ma jinjina kan yayi ya fito da dunk'ulen kud'i ya bashi yace "Nagode." Da sauri ya karb'a yana fad'in "Ni ma nagode yallab'ai, idan buk'atar wani abun ta taso ka nemeni kawai." Jinjina kai Haman yayi amma bai ce komai ba, lafiyayyar motarshi ya shiga cikin salo da k'warewa ya tayar ya bar gurin, tafiya yayi mai nisan gaske kafin ya isa ga lambun da aka bashi kwatancen. Fitowa yayi a motar ya tunkari shiga ciki, k'ofar da akayi da siraren k'arafu na ya tura ya shiga yana ta kalle kalle da son hango mutum, saida ya kai tsakiyar lambun ya ji motsi ta gefensa, waiwayawa yayi hakan yasa shi ganin mutum tsaye ya d'ana bindigarsa a kan shi yayi shirin kare kansa. Gyara tsayuwa Haman yayi ya fuskanci mutumin ya d'aga hannayenshi sama yace "Kwantar da hankalinki, ban zo nan dan na cutar da kai ba, ni ba mugu bane." Saida ya sake saitashi da bakin bindigar yace "Ta ya zan yarda da kai? Waye kai ? Kuma me ya kawoka sansani na?" Hannu d'aya Haman yasa aljihu ya fito da bajon shi ya nuna masa yace "Ni sunana Haman Bahar, jami'in bincike ne na farin kaya, na rok'eka ka tsaya muyi magana." Kallon tuhuma ya masa yzce "Na kasa yarda ba cutar da ni za ka yi ba." Cikin ankarewa Haman ya zura hannunshi bayan rigarshi a k'ugunshi ya ciro bindigarshi mai lasisi ya jefa a k'asa kusan k'afafun mutumin yace "Wannan shi ne, na rok'eka ka saurare ni, na zo ne muyi magana akan b'atan yar sarki Musail, an tabbatar mana da kai ne bafaden da kasan jakadiyar sarauniya Juman, dan ku ne masu gadin bakin k'ofar shiga masarautar kai da mijin ta mai sunan Utais." Sak'e yayi tare da sauke bindigar yayi k'asa da ita, ba tare daya daina tsareshi da ido ba yace" Me kake son sani daga gareni?" Gyara tsayuwa ya sake yi yana sakin numfashi yace" Kai ne mutumin da ka san mutanen nan guda biyu, sannan daga majiya mai k'arfi kai ma nemanka akayi aka rasa shekara d'aya da b'atan gimbiya Zafeera, dalilin b'acewarka nale son sani, da kuma inda zan samu Habbee da Utais." Wani d'an murmushi yayi tare da juyawa yana tafiya yace" Tambayarka ta d'aya kam zan amsa, amma ta biyun ka manta da ita." Da sauri ya bi bayanshi tare da sunkuyawa ya d'auki bindigarshi ya mayar a mazauninta yana fad'in" Me yasa ka ce haka?" Bai amsa mishi ba har saida suka shiga wani falo, wuri ya nunawa Haman ya zauna yana k'arewa d'akin kallo, tsaye yayi a kan shi yace" Shayi zan kawo maka ko ruwa?" Girgiza kai yayi yace" Ko d'aya, nagode." D'aga kafad'a yayi irin oho d'in nan sannan ya zauna kujerar dake fuskantar Haman d'in, k'urawa juna ido sukayi kafin yace" Ina jinka." Gyara zama Haman yayi yace" Me yasa ka bar masarautar Khazira?" Cikin sakin fuska yace" Dalili ne mai k'arfi, umarta ta akayi da na bar k'asar, ba ni ne bari dan ina so ba." Da mamaki yace" Waye ya umarceka?" Ba tare da kwalo kwalo ba yace" Sarauniya Juman ce." Wani sabon mamakin ne ya kama shi yace" Sarauniya Juman kuma? Amma me yasa?" Gyara zama yayi ya sauke ajiyar zuciya yace" A duk masarautar ni kad'ai na iya yaren k'asar Azarbhaijan, hakan yasa ni da su Habbee muke hira a tsakaninmu dan su 'yan k'asar ne." Da matsanancin mamaki Haman yace" Akan haka ta umarceka kayi nesa da masarauta?" Jinjina kai yayi alamar e, ba tare daya shanye mamakin ba yace" In hakane kuwa kar ka ce min sarauniya na da hannu a b'atan yarta?" Wata yar dariya yayi sannan yace "Ka canka daidai." Girgiza kai Haman yayi yace "Amma ta ya ta iya jurewa haka? Me yasa ma tayi hakan?" Cikin rashin sani yace "Wannan ne kuma ban sani ba, abinda na sani kawai shi ne ta kub'utar da 'yarta." Jinjina kai Haman yayi yace "Na ji wannan, yanzu zaka taimaka min ka fad'a min inda zan samu su Habbee?" Girgiza kai yayi yace "Kamar yanda na fad'a maka ka manta da tambayar nan, dan ni ma ban sani ba." Murmushi Haman yayi yace "Kaga, ka daure ka fad'a min, idan ma wani abu kake so ni ka fad'a min zan baka, binciken nan yana da mahimlanci a gareni." Mik'ewa yayi tsaye yace "Na fad'a maka ni ban san inda suke ba, sak'o kawai nake isar wa da sarauniya." Shi ma tashi yayi tsaye yana sauke numfashi yace "Amma ta ya kake isar mata da sak'on?" Ajiyar zuciya mutumin ya sauke kafin yace "Kana neman k'ureni ka sa na karya alk'awarin dana d'auka." Cikin rarrashi Haman yace "Kai kanka nasan za kayi farin ciki a ce yau farin cikin sarauniyarka ya dawo ta dalilinka, gimbiya Zafeera yarinya ce da muka fuskanci girman lamarinta, dalilin hakan rayuwarta ta shiga cikin had'ari mai girman gaske, muna son sani wani abu a kan ta dan bata kariya ne daga masu son cutar da ita." Jim yayi yana kallon Haman na tsawon dak'ik'u, muskutawa yayi yace" Na yarda da kai yallab'ai, ba dan komai ba sai dan abinda ka fad'a gaskiya ne cewa rayuwar gimbiya Zafeera na cikin had'ari." Numfashi ya sauke kafin yace" Zaka samu cikakkun bayanai inda suke a wajen wata tsohuwa dake k'auyen Larhjadin. " Cike da zumudi Haman yace" Me ye sunan tsohuwar? A wane gari ne?" A nutse yace" Ruman, k'auyen *Tankara*." (Mai Dambu ta mu ina godiya da wannan kyautar, Allah bar zumunci) Hannu ya mik'a masa cike da jin dad'i yace "Nagode sosai,na ji dad'in had'uwa da kai." Jinjina kai yayi shi ma yace "Ni ma haka, fatan nasara." Murmushi yayi sannan suka saki hannun juna ya fita a lambun gaba d'aya, a hanyarshi ta zuwa k'auyen Tankara ya kira lambar Umad, dan yayi niyya yau zuwa gobe sai ya samo bakin zaren nan, dan sun jima suna doguwar tafiya saboda yarinyar nan, abinda ya fi basu wahala kuwa shi ne kafin su samu wanda zai iya basu bayanai a kan ta, da k'yar suka samu wata baiwa da sarki Musail ya ma ciki, amma saiya koreta saboda a lokacin yana cikin tashin hankalin neman Zafeera, ita kuma haushin yanda ya koreta bai sakata a layin k'wark'wararsa ba ma bare ta zama matarsa yasa ta fad'a musu bafaden da taji suna wani yare da su Habbee. *Umad* na tsaka da jinjina k'arfin halin Ayam na marin da ta wa Zafreen ya ji k'arar wayarsa, da sauri ya d'aga ya d'ora a kunne amma bai ce komai ba, Haman da yasan komai ne ya fara fad'in "Kana ji?" "Umm." Ya fad'a a k'asan mak'oshi, d'orawa da "Na samu mutumin nan Umad, ya ban adreshin d'aya mutumin kuma na sameshi." A zabure ya tashi tsaye yace "To ya kukayi? Me ya ce?" A tsanake yace "Ya fad'a min komai, yanzu haka zan je k'auyen Tankara ne." Da mamaki Umad yace "Tankara kuma?" "E." Ya fad'a kai tsaye, da alamar tambaya yace "To amma me yasa?" Kamar yan1 gabanshi ya shiga girgiza kai yana fad'in "Umad lamarin nan fa ya wuce yanda kake tunaninshi, wai ma kasan da sarauniya Juman ita ce ta sa aka d'auke yarinyar dan ta kub'utar da ita?" Da mad'aukakin mamaki Umad ya shiga zagayen d'akin hannunshi akan k'ugunshi yace "Idan na fahimceka sarauniya Juman ita ta umarci jakadiyarta Habbee da mijinta da su gudu da yarinyar, haka kake nufi?" Jinjina kai yayi yace "Tabbas kuwa hakane." Wani shak'iyin murmushi Umad yayi sannan yace "Hummm! Sannu sannu dai, komai ya kusa fitowa fili." Zura hannunshi yayi aljihu yana takawa a hankali yace "Shikenan Haman, ka ci gaba da bincika mana komai a tsanake, Allah ya kiyaye ka." Murmushi yayi yace "Nagode, sai na kiraka." Lumshe matsakaitan idonshi yayi alamar to kamar suna kallon juna. *Khazira* Hankali tashe babban malamin ya iso fada, sai ga sarki Musail na ta kewayar d'akin ya cire babbar rigarshi ya aje sai zufa yake, cikin tsawa da hargagi ya kalli malamin yace "Babban malami ta ci amanata, Juman ta ha'ince ni, shin soyayyar dana nuna mata ce ta gagara? Ko kuma butulci ne irin na mace?" Jim ya d'anyi kamar zai ba wani damar fad'an wani abu, sai kuma yay saurin fad'in "Yanzu me ye abun yi baban malami? Ya zanyi na samota ta dawo gareni? Ina so na kamata da hannaye na, Dhurani bana so na mutu yanzu." Ya k'arashe maganar yana d'aga murya, cikin rarraba ido Dhurani yace "Sarki na, wannan ai abu ne mai sauk'i, mu takura gimbiyar mu har sai ta fad'a mana." Khatar ne yayi saurin fad'in "Da zata fad'a ai da ta fad'a, shekaru ashrin fa muka d'auka muna bilinbituwar nemanta, a gaban idonta muke yi da me ta tab'a taimaka mana?" Sarkin yak'i Adah ne ya d'an jinjina kai duk da ba'a buk'ace shi ba yace "Gaskiya ne, amma ko bata fad'a da bakinta ba mu zamu nemota." Kallonshi sarki Musail yayi yace "Adah bana son wasa, wane irin nema ne baku mata ba ? Tun kana da k'ruciya kake yawon nemanta, sai yanzu ne zaka ganta?" Sunkuyar da kai yayi yace "Sarki na, sa'ilin da zamu kai sarauniya kurkukun sabah sun yi wani yare ita da d'aya daga cikin bayinka, bana tamtama cewa maganar da sukayi ta shafi gimbiya Zafeera." Da saurin bala'i sarki Musail ya tunkareshi yace "Wanene shi? Me suka tattauna?" Girgiza kai yayi yace "Ban sani ba ya shugabana, dan kafin ta masa magana saida ta canza harshe." A bala'in tsawace yace "Waye shi a gidan nan, je ka kawo min shi nan." Sunkuyawa yayi alamar amsawa sannan ya juya cikin takon k'arfi yaf fita a falon, bai d'auki lokaci ba ya dawo waccen bafaden na bayanshi, gefe sarki yak'i Adah ya tsaya shi kuma ya zube har k'asa yana gaishesu, saidai a zahirinshi da bad'ini hankalinsa a tashe yake, ba ka da abun zargi ma ka ji tsoron amsa kiran sarki Musail bare kuma shi da yake ji a jikinshi asirinsa ne ya tonu. Cikin daka tsawa sarkin yak'i Adah yace "Kai k'ask'antaccen bawa, sarki yana so ya ji abinda kuka tattauna tsakaninka da sarauniya Juman?" D'aga kai yayi ya kali sarkin yak'i jikinshi na makyarkyata, kame-kame ya fara ya rasa me zai ce da shi, a sukwane sarki Musail yayi kan shi, kafin ka ce me ya saka k'afa ya hankad'ashi ya fadi kwance, kafin ya tashi yasa k'afar ya take masa k'irji, cikin k'araji yana zazzaro ido yace "Zaka fad'a min ko sai na kasheka a banza? Ka sani duk wanda yace zai shiga tsakani na da cikar burina kamar wanda zai taimakawa mak'iyana kyautar takobi ne dan yak'ata, dan haka ba zan bar shi a raye ba, yanzu fad'a min me ta fad'a maka?" Cikin tashin hankali da tsananin tsoro yace" Sarki na, shugaba na ka min rai karka kasheni, ta ce ko ta halin yaya na isar da sak'onta, na fad'a mata ta ninka saka ido akan gimbiya." A tsawace ya sake fad'in" Wacece? Kuma a ina take?" Cikin rawar jiki yace" Wata tsohuwa ce, a k'auyen Tankara." "Me sunanta?" Dhurani ya tambaya daga gefenshi, cikin rawar leb'e yace "Ruman, Ruman ne." K'atuwar takobin dake k'ugun sarkin yak'i Adah ya jawo, kafin kowa ya ankara kawai ya sokawa bafaden nan ita a tsakiyar ak'ogwaronsa ta

Chapter 5 of 10