ja, mijinki ne fa!"
Juyowa ta yi tana galla mata harara, ganin tana mata
dariya yasa ta dauke kanta cikin kuluwa.
Ita kuma ta ci gaba da kular da ita, "Wata rana tare z
aku'shiga wankan har yasa sabulu ya wanke ki tas!"
Wani tukuki taji a ranta da daci, ta tofar da yawu tare
da cewa "Tir! Allah ya sawwake."
172
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Tayi dariya ta ce, "Kema ki masa." Ta juyo cikin
facin rai ta ce, "Rafi'atu don Allah ki min shiru kar ki
harzuka ni fa in miki abin da har ki mutu ba za ki manta
ba."
"Maida hankali don Allah, don kawai na ce haka? To
bari kiji ma ba wanka ba, gado daya za ku dinga
kwanciya bargo daya, sannan ki fara haifa masa 'ya'ya."
Cikin zafin rai ta mike idanunta suka sauya ja ta ce,
"Idan ki ka sake furta magana daya a kansa Allah ya
23
1sa.
Tayi dariya ta ce, "Iye! Matar Imran din ba!"
Ba za ta iya jure maganganunta ba, idanunta suka
rufe ta fice daga dakin a fusace bata ko gani.
Tana bude kofa taci karo da wani abu, sai dai taji ta
fada. Bude idon da zata yi ta ganta kwance jikin
makiyin nata, yasa hannu ya tallafeta kanta saman
Kirjinsa sun fadi kasa.
Ya sakar mata murmushi tare da cewa "How are
you?"
Zuciyarta ta dinga harbawa, ranta ya baci matuka,
173
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
idanunta suka kara canja launi, kallonsa take kamar ta
shake shi tasan da niyya ya yi haka dan iska kawai.
Ta dube shi da kyau ta ce, “Sakar ni Mallam ba na son
iskanci."Ya ce, "Ni ban rike ki ba duba da kyau."
Ta duba itan ce kwance jikinsa, yayin da hannunsa
suke a sake, ta yunkura zata mike a fusace.
Sarkar wuyanta ta riko rigarsa, ta kara fusata ta fara
kiciniyar warwarewa amman ta kasa, gata dai kwance a
jikinsa. Shi kuma ganin bata bukata bai cire ba yasa ya
kyaleta, musamman da yake jin farin ciki kasancewarta
a tare da shi.
Duk kokarinta ta kasa, dole ta sauke girman kan don
ta rabu da jikinsa da take jin kamar a saman wuta take
kwance, fuska turfune ta ce "Ka kwance."
Ya yi dariya yana kallonta, ta kauda kai tana dode
hanci saboda warin turaransa da take ji.
Shima ya kasa warwarewa saboda shi ne a kwance,
ya dubeta ya ce, "Na kasa, sai dai ke ki dawo yanda nake
ni kuma in koma yanda ki ke sai na iya cirewa, amman a
2
174
WAYE ANGON?
haka ba zan iya ba."
Maryam Ja'afar
Ta dalla masa harara ta ki yinyanda yake nufi.
Ya ce, "To shi kenan kar kiyi ni ban da matsala mu
kwana a haka, idan su Momy suka zo sun gane me hakan
ke nufi."
Fadin haka ne yasa da sauri ta birkice ta koma kasan
shi, shi kuma yana samanta.
Ta runtse ido tana jin wani irin tsanarsa da takaicin
kasancewarta a jikinsa.
Ya yi dariya a ransa yana jin daman bata juya din ba,
don ya ci gaba da kasancewa tare da ita, amman ba
komai akwai ranar da hakan zai kasance.
Cikin fushi ta ce, "Malam kai nake jira fa." Ya yi
dariya yana kokarin cirewa.
Yana cirewa ta tashi da sauri bayan ta ture shi, tayi
gaba tana tofar da yawu. Ya ce, "Amman ai kin tsaya ki
min godiya in ba ki ba ni hakuri ba."
Ta jishi sarai amman bata da niyyar dawowa.
Duk a idon Rafi'a komai ya faru, tayi dariya tare da
175
WAYE ANGON?
komawa daki.
Maryam Ja'afar
Koda ta fita a harabar gidan ta hadu da Daddy, ta
wuce gunsa tana turo baki.
Ya dubeta ya ce, "Me kuma ya faru?"
Ta ce, "Ina son naje gun Babana, amman Momy ta
hana ni."
Ya ce, "Shi ne kadai matsalarki?" Ta daga kai.
Ya ce, "Ok, zan fita nima. Zagaya ki shiga mota in aje
ki sai na wuce, hakan ya yi miki ko?"Ya karashe yana
dariya.
Ta daga kai kurum tare da wucewa ta lalubo lambar
Rafi'a bayan ta shiga ta ce, "Ki zo muje ga Dáddy nan zai
kai ni." Ta ce, "Ba zan je ba, ki tafiyarki gida zan wuce
yanzunnan."Ta ce, "To."Tare da kashe wayar.
A daidai kofar gidan ya tsaya da motar, inda Baban
Mabarukar yake tsaye shi da mutanensa. Ta fito daga
motar, shi ma Daddyn ya fito ya zagayo.
Ganin Babanta ne yasa ya karasa gunsa cikin fara'a
ya mimmika wa mutanen hannu suka yi musabaha. Ya
mikawa Babanta amman kememe ya rike hannu ya ki
176
ง
WAYE ANGON?
mika masa, kallonsa ma ba ya yi.
Maryam Ja'afar
Ganin hakan ne yasa ya yi murmushi ya се, "То
barka da yamma." "Lafiysi." Kawai ya ce har zuwa
lokacin ba ya kallonsa.
Ba yau ya saba ganin hakan ba, don haka bai damu
ba. Ya yi bankwana da sauran mutanen ya wuce, ya dubi
Mabarukar da ke gefe ya ce, "In ba ki wani abu ko ki dan
rike?"
Ta yatsina fuska tare da cewa, "A'a bana bukatar
komai Daddy, na gode." Ya kalleta da kyau ya ce, “A'a
na san ki Mabaruka kina da kashe kudi."
Akwai dalilin kin karbar, amman duk da haka ya ciro
kudi daga aljihu dumus ya mika mata yana fara'a.
Ta ce, "Wallahi ba ni da bukatarsu Daddy." Ya сe,
"Eh na sani rike dai." Ta karba tare da godiya kamar
dole.
Ya ce, "Shi kenan in tafi ko?" Tayi murmushi
iyakarsa fuska, ta ce "Eh."Ya shige motarsa yana cewa,
"Sai yaushe za ki dawo kenan?" Ta sosa kai tare da
177
WAYE ANGON?
cewa, "Sai dai na dawo din."
Maryam Ja'afar
Ya ce, "Ok." Ya tada motar ya wuce, duk tana tsaye
har ya bace sannan ta nufo gida.
Baban ya kirata ta karasa.
Ya harareta ya ce, "Wannan wane irin iskancin banza
ne?" Ta dube shi ta ce, "Me nayi Baba?"Ya ce, "Ban sani
ba. Salon tarbiyya ce haka zai dinga ba ki kudi har haka?
Me za ki yi da su?"
Ta turo baki "Ni ma fa sai da na ce bana so amman ya
bani..."Ya katseta "Na kwade ki, fitsararra! Me yasa ki
ka karba, ko dole ne?" Ta matsa baya tana turbuna
fuska.
Ya kauda kai kurum tare dajan tsaki.
Ta wuce cikin gida fuuu!
Koda ta shiga Inna na zaune tsakar gida tana kasawa
yara alalan talla, taga shigowarta sallama kawai tayi ta
shige dakinta.
Ta fada kan katifa tare da cillar da kudin. Kuka ya
taho mata ta dode baki kar aji ta, ta sani sarai iskancin da
take a can gidan nan ba ta yin shi, tasan Babanta ba a
178
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
1
masa wasa, ba bakonta ba ne sai ya shigo da bulala ya
mata dukan da zata yi mai dalili.
Inna ta shigo ta bita da kallo ta ce, "Ke Mabaruka me
ya faru kin shigo haka a firgice?"
Ta goge hawayen sannan ta dago ta ce, "Ba komai,
kaina ke ciwo kurum." Ta ce, "Kai kuma?" Ta daga kai
kurum.
Ta ce, "To kin sha magani?" Ta ce, "Eh." Kawai.
Idonta ya sauka kan kudin da ta watsar, ta matso tana
cewa "Mabaruka wadancan kudin fa?" Ta dago ta
kalleta cikin fushi ta kuma kalli kudin ta kauda ido.
Ta ce a can kasa-kasa "Daddy ya ba ni." Ta washe
baki "Hala ba ki so ki ka wurgar?" Tai mata banza.
Ta zauna tana cewa, "Kinga ko manjan alale bai isa
ba daman ina jiran Babanku yazo ya biya ni Naira talatin
dita ta shekaran jiyada ya ci min alala sai a karo min, kin
ga sai ki biya mishi kawai, nima a dan gutsura min." Ta
karashe tana dariya.
Ganin zata isheta da surutunta na maula yasa ta ce
"Dauki ki sai manjan don Allah kaina na min ciwo."
179
Π
WAYE ANGON?
Ta bude hakora "Nawa zan dauka?"
'Yan dubu-dubu ne, ta ce "Dauki uku."
Maryam Ja'afar
Ta wangale baki tana dariya ta ce, "Ho Mabaruka
'yar Baba, akwai kyauta in kinga dama." Ta zari kudin
tana cewa "Allah miki albarka 'yar Mabaru."
Ta bita da kallo ganin yanda take rawar jiki har ta
fice. Taja tsaki sam ba su ne gabanta ba, masifar da ke
saman kanta tafi kudin nan ita ke ta kudi.
Da dare Baban ya shigo har zuwa lokacin tana daki a
kule, musamman kasancewar tana hutun sallah, hakan
yasa tunda ta shiga bata fito ba.
Yana kwasar tuwo ya dubi Inna dake gefe tana kirgar
kudi, ya ce "Dan aro min hamsin nan kafin gobe."
Ta dago tana kallonsa bayan ta tsaya da kirgar ta се,
"Kafin gobe ka ji cika baki, sai ka ce su ke gare ka. Irin
ba canjinnan ko?" Bai saurareta ba ya ci gaba da silbar
tuwonsa."
Ta ce, "Nawa na ara maka? In za a kirga sun kai
saba'in, bana damunka ne don naga nan tsiya ta ganka ta
180
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
barka, amman shi ne har ka ke da kwarin gwiwar
tambayata wasu. To naki na bayar."
Ya ce, "Goro fa kawai zan siya ba wani abun zan yi
da su ba." Ta taso "Eh goron mana, in kawai ne ka siyo
da kudinka yanzu gobe karin safe duk kaina zai kare, in
an samu ka kokarta ka bada wazobiya na koko, ni sai na
Kukuta na samu na sikari."
Mabaruka da ke daki taja tsaki tare da tashi zaune. In
dai tana gidannan bata hutawa da sauraron abubuwan.
takaici daga Inna da Baba.
Kullum cin bashi yake, yayin da ita kuma cikin
goranta masa take. Sam babu abin burgewa a zamansu.
Kan Naira ishirin sai su dinga tashin hankali, duk
makota sai an jiyo su, shi yasa ta gwammace gwanda
tayi zamanta gidan Momy hankalinta kwance.
Jin za su kaure da bala'insu yasa ta mike a kasalance
ta jawo jiki bayan ta daura gyalanta a kai ta fito taja ta
tsaya. Sai sannan ya tuna da ita.
Ya bita da kallo yana cewa "Me ki ke a daki tun dazu
har na manta da ke?"
181
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ta zauna kan daya daga cikin jarkar ruwan da ke
ajiye tana cewa "Bacci nake." Ya ce, "Bacci?" Ta daga
kai:
Ya ce, "Da kyau Sarauniya! Kin yi bacci mana
hankalinki a kwance." Ba ta ce komai ba illa fushi da
take, daga haka ta mike ta shige bandaki don kama
ruwa.
Daidai fitowarta daidai fitarsa, ta tsinkayi Inna na
bala'i.
"Allah ya isa wallahi, shine ka fakaici idona ka dauki
ishirin, to wallahi a kudin kokonka."
Ba ta iya cewa komai ba don wani abun in ya kai
intaha yafi karfin magana. Tayi alwala kamar yanda ta
saba in zata kwanta.
Ta dubeta ta ce, "Tuwo fa, ba za ki ci ba za ki kwanta
haka?" Can kasan makoshi ta ce "Na koshi." Tare da
shigewarta daki.
Inna ta ce, "Um! Nima ba na gajiya, nasan ba cin
tuwonmu ki ke ba amman nake tambayarki."
183
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Akilu yaro dan shekara takwas ya shige dakin hade
da tabarmar kwanciyarsa shi da Halliru duk kannata ne.
Suka kama kiciniyar kwanciya, ta bisu da kallo tana
jin wnai takaici. A kullum idan zata kwana a gidannan
sai ta zama bakuwa, kamar ba ta taba kwanansa ba,
saboda matsaloli da take cin karo da su.
Duk gidan daki biyu ne, matsattsu, daya na Inna
faya nata to a natanne ake cakudata da kannanta duk
maza ne su shida ne hudu na kwana tare d aita daya
yayayye yana gun Inna sai mai shan nono.
Don haka a nan suke kwanciya. Idan dare ya yi dare
suka tsula fitsari su hade da junansu daki ya dauki zarni
hade da tusarsu, kafin dare sun yi sau saba'in, kuma irin
mai kumbura ciki da gagara maida numfashi.
Ta bude window don shan iska,, amman ba wani
sauki. A haka dai take wannan wahalallen baccin, ta
kagara gari ya waye. A cikin daren sai taji kamar tayi
tsuntsuwa ta tafi gidan Momy tayi kwanciyarta a
rantsattsen gadonta, inda daddadan iska da kamshi ke
fesowa, bacci mai dadi da sa kwanciyar hankali.
184
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Hakan yasa ba ta jera kwana uku a gidan Baban tana
kwana, in tayi kokari kwana biyu ne shi ma a daddafe.
Don haka suka gama shimfidarsu suka kwanta, ta
dafe kai tare da salati.
"Oh ni Mabaruka! Yau na shiga uku, da rana ban huta
ba sai tashin hankali, yanzu ma ba zan huta ba, kafin
dare cikina ya kumbura suntum."
Ga kabdagaggen tsoro na intaha da ke gareta, sam
bata kwanciya daki ita kadai saboda tsoro, dole sai tana
jin motsin mutum kusa da ita.
Ko gidan Momy takan kwana da masu aiki tunda
take ma bata taba kwana ita kadai ba, a kullum Momy na
cewa idan ki ka yi aure Mabaruka ban san ya za kiyi ba.
Idan ta ce haka hankalinta na tashi ta shiga zullumi to
da zata iya da waje zata dinga fitowa tana kwanciyarta
saboda gidan ko ana sanyi shi zafi yake saboda yanda
.yake a kuntace ga girki da ake a tsakar gida gaf da
dakunan, don haka wajen ba zai yi sanyi ba sosai.
Ta koma ta kwanta lamo tana zullumin yanda daran
185
WAYE ANGON?
nata zai kasance.
Sulaiman ya kirata ta dauka a gajiye.
Maryam Ja'afar
Ya ce, "Kina ina?" Ta ce, "Ina nan gidan Baba."
Ya ce, "To bari in zo.."Тa сe, “Ayya ba za ka samu
ganina ba, agajiye nake har na kwanta kayi hakuri."
Bai so haka ba amman ba yanda ya iya dole ya
hakura suka dan taba hira sannan suka kashe waya, ta
koma ta kwanta luum!
Imran ya shiga waige-waigen ina ta shiga har sai da
ya tambaya, Rafi'a ce lokacin da take kokarin tafiya tace
"Tana gidan Baba tun dazu baka sani ba?"
Jikinsa ya mutu murus ba kuzari, jin haka ya ce
"A'a." a gajarce, daga haka ya juya ya shige dakinsa, ya
fada gado yana tunano tauraruwarsa.
Bai so tafiyarta ba, ina ma zai kara kasancewa da ita
kamar jiya, ko ma dai wayarsa ne da zata dauka da ya ji
dadi, ya sani in zai kirata sau dubu ba za ta dauka ba, zai
wahala ne kawai gwara ya hakura akwai lokacin da zai
kasance da ita har abada.
186
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Amman duk da haka zai jaraba, don haka ya janyo
waya ya fara jera mata kira yafi a kirga.
Bacci har ya fara daukarta ta dinga jiyo kiransa ta
jawo ta duba wani dogon tsaki taja tare da hararar wayar
tamkar yana gurin, ta tillar da wayar tare da canja kafada
tayi kwanciyarta tana turo baki.
Shi kuma bai fasə ba da ya tsaya sai ya ji bari ya kara
kira me yiwuwa yanzu ta dauka, don haka ya dage ba ji
ba gani, ganin ba za ta dauka ba yasa ya fara jera mata
ruwan tasa-tasai.
Karar shigowar sakonni a wayar ya isheta, ta jawo
wayar gabadaya ta tillar tana cewa, "Fitinannen banza
mai shegen naci marar zuciya mugu! Ta koma ta kwanta
tana kara jin tsanarsa na karuwa.
Da ya kira ya kira ya ji ta a kashe jikinsa yayi sanyi,
tausayin kansa ya kama shi ya aje waya a salube ya yi
jugum, shi kadai yasan yanda yake jin radadin sonta har
zafi yake ji a ransa, wai da me ya gaza burgeta har yau
bata sonsa, meye aibunsa wai?
Da ire-iren wadannan maganganun bacci na tunanin
187
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
3
Mabarukarsa matarsa ya dauke shi me cike da
mafarkinta.
Darennan ta farka yafi a kirga saboda yanda dakin ya
suntume da wari ga zarni zafi kuma ya dameta, ga sauro
in ta rufe zafi ta kasa maida numfashi.
Haka in ta bude sauro ya yanyameta, ko ya ta motsa
sai taja tsaki daga tsakar gida ta jiyo ana kashe sauro da
hannu tare da jin tarin Baban.
Ta mike ta fito, ganinsa tayi kwance kan 'yar
tabarmarsa da 'yar fitila a noke. Sanyi ya ziyarce ta
ganin wani a tsakar gidan, gwanda ta fito nan ta kwanta
ya fiye mata kwanciya a akurkin dakinnan.
Don haka ta shiga ta yayumo tabarma tazo tana
kokarin shimfidawa, jin motsi ne yasa ya jawo
touchlight ya hasko tare da cewa "Waye a nan?" Ta ce
"Ni ce Baba."
"Me ki ke yi a nan kuma?" Ta ce, "Zafi dakin, ga su
Halliru sunyi fitsari sai zarni suna ta burkice dakin da
tusa, shi yasa na fito nan na kwanta."
Ya mike zaune “A ina za ki kwanta nan 'yar gulma?
188
WAYE ANGON?
Kin ga na fito shi ne kema ki ka fito?"
Maryam Ja'afar
Ta ce, "A'a Baba." Ya ce, "Karya ki ke, to ba za mu
jera ba a nan, ni nasa tawa tabarmar kema ki sa ta ki." Ta
ci gaba da kallonsa cikin mamaki, ta ce "Kamar ya ya
Baba?"
Ya harzuko "Kamar ubanki, za ki koma ciki ko sai na
taso miki cikin tsohon daren nan?"
Ta turo baki ta ce "Dan kwanciyan da zan yi kawai."
Mikewa ya yi zai yo kanta da gudu ta yayimi.tabarmar ta
shige daki taci karo da kofar langa-langar, kusa ta
farketa a hannu tare da ja mata riga ta yage.
Ta fadi zaune jagwafkuka na son fitowa.
A daren ya dinga sirfa mata zagi yana cizgar fada.
Haushi ya tokare ta dama dukanta yazo ya yi yafiye
mata fadannan da yake mata cikin dare ko ta ina zaginta
yake ita da Mamanta.
Taci gaba da turo baki tana guna-guni har ya gaji ya
koma bayan ya rufo kofar ya datse ta gam.
Kwalla ta ciko mata a ido, me ma ya kawota nan da
tayi zamanta gidan Momy tayi kwanciyarta a
189
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
A
2
tamfatsetsen gadonta, iskar (AC) na kadota da
kamshinsa.
Ta dafe kai ta ce, "Wallahi ba ka sona, duk abin da ka
יי ke tun ina yarinya ba ka sona."
Ta ci gaba da matse kwalla da cizon yatsa, me ya
kawota? Sam bata yi bacci ba, daren nan tayi zaune tana
dode hanci tare da kashe sauro duk wanda ya cijeta, duk
tabi ta soshe jikinta tana cewa tir me ake da talauci?
Sai da asuba sannan su Akilun suka tashi suka
kwashe kayan fitsarinsu saboda zuwa Makarantar
asuba.
Ta bude window tare da kofa ta dage labule ta dawo
tsakiyar dakin kan siminti tasa filo nan da nan bacci ya
kwasheta mai nauyi na ramuwa.
** **
A gidan su Suiaiman kuwa, koda gari ya yi shaa, Inna
ta fito daga daki, dakin matar Sulaiman a datse da kofa
ta nufi dakin tana cewa "Wato ba ka fito ba har yanzu?"
Ta shiga dukan kofar tana kiran "Sulaiman!
Sulaiman!!" Ya fito yana mika tare da doguwar hamma,
190
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
ta bishi sama da kasa tan tabe baki ta ce "Meye haka ka
ke wata doguwar mika, kana nufin baccin da ka kwasa
tun jiya har yau bai isheka ba ko ko so ka ke ka nuna min
kana da mata?"
Ya kalleta yana 6a66ata rai, ya ce "To jiyan karfe
nawa na kwanta sha daya fa ta wuce."
Та се, "Тo fada min na hanaka bacci don ubanka!
Rana tayi gadau ace ba ka tashi ba? Me ka ke tsinanawa
a dakin?"
Ya ce, "To ya isa ai gani na fito me zan miki?"
Ta harare shi tare da nuna masa hanya "Muje."
Ba yanda ya iya, yasan kwanan zancan. Ya shuri
takalmi ya wuce zuwa dakin Innar, yana tangadin rashin
isasshen bacci.
Ta daga labulen ta dubi Nafisa matarsa tana tabe
baki.
"To dadi miji, jin dadin ya kare a jira wani daren."
Daga haka ta juya ta wuce.
Nafisar tayi murmushin takaici tare da cewa "Na
barwa Allah, kema kina da lokacinki za ki yi ki bari." Ta
191
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
mike ta tura kafarta ta koma tayi kwanciyarta abinta.
Koda ya shiga yaja tabarmar da ya saba kwanciya
duk sanda tayo masa irin wannan tashin, ya yi
kwanciyarsa nan da nan yaci gaba da baccinsa.
Ita kuma ta koma ta zauna tana daura sugarin
kokonta hankalinta kwance.
Ka'idarta kenan tunda safe irin shidar nan zata taso
shi daga dakin matarsa. Sai dai ya dawo nan ya kwanta a
dakinta duk don kar ya kasance da matarsa.
Saboda wani tunaninta can marar ma'ana, haka
zalika ba zai kwanta ba sai wajen sha biyu na dare
sannan zata ce yaje ya kwanta.
SHIN WACECE MA INNA?
Lokacin da taci zamaninta da mijinta Baban su
Sulaiman din kafin ya rasu yana da mata ta same shi
amman zuwanta duk ta fatattake su da shegen
makircinta da neme-neme, tayi nasara kam ita ke da
gida ta hana shi aure sam.
Duk in da yaje neman aure tsoron ba shi ake
192
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
saboda halinta, ko ta nakasa mutum bayan ta raba shi
da gidan, don haka take cin karanta ba babbaka, tayi
budurinta son ranta har yazo ya bar mata duniyar
gabadaya.
Su Sulaiman kadai ta haifa, don haka suka ci
gadon gidan da suke zaune sai Inna matar Baban
Mabaruka, don haka ita ma tayo kwas na makirci da
fidda matar da duk ya auro ta kuma hana shi wani auren.
Har sarakkuwarta bata bari ba, tasha cusa mata bakin
ciki ta rabata da danta ko keyarshi ba ta gani.
Hakan yasa take tsoron kar a mata abinda tayi ma
wata, ta kwace mata Sulaiman din ta hana mata shi. Sam
bata barinsa ya kebe da matarsa isasshen lokaci, da ta ji
su shiru zata koro shi.
Daidai da abinci bata barin yaci na matarsa a
tunaninta kar a sa masa magani ya ci a rabata da shi, dole
a gunta zai ci ta hada masa ruwan wanka da kanta, daidai
da kayansa a dakinta suke.
Ya taba aure 'ya'yansa biyu da matar, ba arziki ta
gudu saboda takurar Inna da wahalarta, ta kuma hana ya
193
WAYE ANGON?
karbi'ya'yan.
Maryam Ja'afar
Daga nan ya dawo yana rakice-rakicen aure, duk
wacce ya aura da taji wuya zata gudu.
Har kawo yanzu Nafisa tana da hakuri da maida
lamari ga Allah, marainiya ce gidan da ta baro ba
dadinsa taji ba, gidansu kenan don haka ta gwammace
zamanta a nan din ta barwa Allah ya kawo mata agaji.
Haka nan ma sai ta ce su fito waje su kwanta ita ma
tazo ta kwanta anan idonta a kansu.
To bare kuma su fita unguwa tare, ko irin ya kaita
unguwa bata bari.
Kayan abinci a dakinta suke, ko kudin cefane ita
yake ba haka nan ita zata debo yawan abincin da za a
dafa wai bata yarda da almubazzaranci ba, Nafisa zata
dafa tasa kujera ta kafa ta ta tsare har sai angama a kawo
mata tukunyar gabadaya bata barinsa ya kasance da
matarsa, har zuwa yanzu bai sake haihuwa ba.
Muje dai zuwa labarin zai kara bayyana mana halin
Inna.
Koda ya tashi Sharifa ce ke dawainiya dashi
194
承
WAYE ANGON?
6angaren abincin da zai ci.
Maryam Ja'afar
Sam ba shi da kuzari haka nan ya tashi sukuku
zuciyarsa fal take da mararin son ganin Mabaruka, ina
ma zata yarda da yazo inda take don kawai ya samu
nutsuwa.
Ya fito daga wanka yana tsane ruwan jikinsa,
fuskarsa ba annuri, Sharifa dake gefe tana fito masa da
kayan da zai sa ta ce cikin damuwa "Big Bro wai
menene?"
Ya dubeta yana cewa, "Me ki ka gani ne?' Tа се а
marairaice, duk yanayinta ya sauya ba annuri "Me ke
damunka?"
⚫ Ya yi murmushin da zai kwantar mata da hankali ya
matso inda take yana kallonta, ya сe "Ba komai
kanwata, kawai nasan don safiya ne amman tunda na
dan yi wanka zan ji karfi."Ta ce, "Shi kenan Big bros."
Ta hado masa tea hade da madara.
Ya yatsine fuska ya ce, "Ba zan sha madarar nan ba,
kawo min lipton kawai." Ta kalle shi cikin kulawa ta ce,
"Saboda me lafiya ka ke kuwa?"
195
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ya ce yana kallonta "Lafiya mana, na fada miki kada
ki damu."Ta juya ta fita jiki a sanyaye.
Cikin baccinta me dadi ta dinga juyo hayaniya tsakar
gida tsakanin Inna da Baba, ta saurara da kyau.
Inna tana cewa, "Ai daman na fada maka wallahi
kudin kokonka, don haka yau ba ka da kofin koko na
talatin za a siyo ishirin kuma kudina jiya da ka dauka."
a
Ya ce, "Na fada miki rance nayi zan dawo miki
dasu."
Ta ce, "Wallahi sai kai ta yi."
Ta tashi zaune tana jan tsaki, wannan fitinar tasu ta
isheta, duk fadansu a kan kudi ne in dai za ka ji
harshensu to kudi ne mahadinsu.
Ganin abin nasu ya ki karewa kan Naira ishirin yasa
ta mike ta ciro dubu daya daga kudinta ta daura
dankwali ta fice cikin fushi.
A tsakar gida suke ta dubi Baban ta ce, "Ga shi ka
biyata kudinta don Allah."
Yabi kudin da kallo, miyansa ya guda matuka, yasa
196
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
☆
hannu ya karba yana washe baki, ya dubi Innar ya ce
"Kin ga ni ko na wuce wulakanci tunda na haifa."
Ai fa ta taso da bala'i "Yau kasan ka haifa a da me ka
ke cewa? Me 'ya mace zata maka? An ga kudi yau har an
manta ko ita wacecе."
Jin fadan kuma zai koma ta nan yasa tayi saurin
dauko wata dubun ta mikawa Inna tana cewa, "Ga shi
kin sayi kokon na kwana biyu, kiyi hakuri."
Ba kunya kuma tasa hannu ta karba baki bude.
Dukkansu sai suka yi mukwi ba bakin wanda ka sake
ji kudi sun rufe musu bakin.
A nan ya fice ya bar su yayin da ita kuma Innar ta ci
gaba da aikinta. Taja kafa ta shige daki cike da takaicin
wannan dabi'a tasu.
Sai da rana tayi sanna ta tafi gidan su Rafi'atu, a can
tayi zamanta ta kashe wayoyinta.
Kwana daya ya rage a koma kotu, don haka a nan ta
kwana daga nan suka wuce kotun ita da Maman Rafi'ar
sai Rafi'atun.
197
WAYE ANGON?
TIRKASHI!
Lallai za a yi ta kenan!
Maryam Ja'afar
To ku dai biyo ni cikin kashi na biyo don mu ma muji
mu kuma gani,. WAYE ANGON? IMRAN ne ko
SULAIMAN?
Taku;
Maryam Ja'afar 08033406612
198
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau