Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels HNL WAYE ANGON 1 WAYE ANGON Maryam Jafar Kaduna DORDID DDINAN G00O1I0D WAYE ANGON?1 Na Maryam Ja'afar Kaduna Mrs: Khabeer Abdullahi WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Humaira khalil Adam marubuciyar INA SIRRIN YAKE? ALKALAMAWA (gidan fasaha) Ban cire kowa ba gaisuwa ta musamman da jinjina gareku marubutanmu bisa kokarinku na dabbaka harshen hausa da gyaran zamantakewa. Allah yaja nisan kwana ya daukaka alkalummanku Ameen "YAN UWA DA DANGI Ga gaisuwata gareku na miko da fatan alkhairi jerin sunayenku bazai jeru ba ana idan ko harnace sai haka to tabbas zan cika littafin wani mabai samu shigaba ga adduar zumunci nan soyayya da kaunar juna Allah ya karo mana ya hade kawunanmu ya dorar da zumunci me dorewa Allahumma Ameen. 2 : WAYE ANGON? Maryam Ja'afar WAYE ANGON? afi'atu ta shigo dakin hannunta rike da plate din RaLabinci, hannu daya kuma zobo ne a robar ruwa da ake durawa guda biyu sun dauki sanyi karara. Tabi inda Mabaruka take kwance da ido ta zauna tare da aje plate din ta ce "Mabaruka!" Shiru bata amsa ba. Ta kara kiranta "Nasan idonki biyu ki tashi." Ta tashi a zaune a kasalance, kalľo daya za kai mata ka gano bata cikin walwala, ta dauko dankwalin da ya cire a kanta ta yafa ta dubi Rafi'atun ta ce "Menene?" Kallonta take tsaf! don son gano wani abu, sannan ta ce "Wai meye haka Mabaruka? Kina son damuwa tai miki yawa ko?" tayi mata shiru. Ta ci gaba "Ki saukakawa kanki don cuta bata da wuyar shiga jikin mutum wallahi." Ta yatsina fuska tanakallonta, ta ce "To me nayi kuma?" Ta ce cikin kulawa, "Ba ki komai ba, amman kwanciyar da ki kai ba bacci ki ke ba illa tunani da kuka, tun da na fita na bar ki a haka na kuma taras da ke a haka. 3 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Ta sunkuyar da kai ba tare da ta ce komai ba. Rafi'an ta ce "Don Allah ki daure kawata ki barwa Allah komai, ke dai kici gaba da addu'a kurum." Ta dago da tsumammun idanunta kamar zata yi kuka ta ce "To me ki ke so nayi? Kwana biyu fa ya rage?"Tayi jim sannan ta nisa ta ce "Na sani Mabaruka, amman Allah na ce fa ki bar masa komai ki gane lokacinki bai Kure ba." Ta ce, "Ke kadai ki ka zama matsalata Rafi'a, wallahi da tuni nayi nisa da garinnan, inda zan sami yanana da nutsuwa." Ta ce, "Na gaji da jin haka Mabaruka,kin fada yafi a kirga, na ce miki babu inda za kije wallahi." Ta buda baki zata yi Magana a kasalance ta yi saurin katseta. "Ya isa! Matso ga abinci muci muyi sallah, sannan mu tafi."Ta kalleta t ace, "Ina kenan?" Tana juya abincin ta ce, "Kasuwa mana, daga nan mu sauka wajen Anti Farida muyi saloon din. Tun safe nake fada miki haka amman kin kasa rikewa." Ta dubeta da kyau ta ce, "Nima tun safen nake fada miki ba zan je ba, kin kasa rikewa."Itama ta kalleta ta ce 4 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar "Wallahi ba ki isa ba, ya zama dole ki matso ma ki gani. Muna da abubuwa fad a yawa Mabaruka?" Ganin bata da shirin matsowan yasa ta haye saman katifar da abincinta mika mata cokali ta ce, "Karbi muci mu wuce, yana hucewa galokacin sallah yana tafiya." Ta makale hannu ta ki karba. Hakan yasa Rafi'ar ta daga murya ta kwalawa Mamakira. "Mama!" Daga can tsakar gida Maman ta ce, "Ya aka yi ne?" Ta ce, "Mabaruka ce mana.' Jin haka yasa ta taso ta nufo dakin. Ta dubi Mabarukan ta ce, "Ya aka yi ne?" Ta dago da jajayen idanunta tana kallon Maman ta kasa cewa komai. Ta dubi Rafi'atun ta ce, "Ya aka yi ne?" Ta ce "Abinci taki taci." Maman ta karasa wajen Mabarukan ta zauna gefen katifar ta ce "Ya aka yi ne Mabaruka don me ba za ki ci abinci ba?" Ta ce a sanyaye "Bana jin yunwa ne. Ta ce, "To me yasa ko na safe fa banga kin ci wani abun kirki ba, zama da yünwa illa ne, daurewa za ki kada damuwarki ta shafi cikinki. 5 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Damuwa dai akwaita rashin cin abincin ba zai yaye damuwar ba, illa ma ya kara damuwa. Amman in kika ci za ki samu karfin jikinki kuma damuwarki tayi sauki." Mama ta saurara. Mabarukan ta ce, "Zan ci Mama ko zuwa anjima."Ta ce, "A'a ban yarda ba, yanzu nake son kici. Kinga zaku je saloon ya kamata zuwa yau kin yi saloon din da lalle, ga maganinki can a kan wuta anjima za a kawo 'yan shilar." Ta kalleta zata yi kuka ta ce, "Duk meye amfaninsu Mama? Ni fa ba na farin ciki, don Allah ku kyale ni da wadannan abubuwan." Mama tayi murmushi nasu na manya ta ce, "Mabaruka kenan! Ita Amarya an santa da gyara da kwalliya don angonta da mutanen da za su zo mata murna su ganta fes! Gwanin sha'awa kowa ya yaba ya gamsu lallai Amarya се. Amman idan ki ka tsaya a haka waye zai zo ya ce ke amarya ce? Kwalliya ya żama dole kiyi Mabaruka, kiyi 6 2 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar hakuri." Zata yi magana Maman ta katseta "Ya isa! Dauki ki ci abincin.” Ta jawo mata abincin a gabanta tare da cewa "Oya maida hankali in ga kin ci da yawa." Yawan musun ba shi da amfani bare ga babbar mata wacce take ganin girmanta da kima, uwa ce gare ta. Don haka ba don tana da bukatarsa ba ta fara tsikararsa ranta cunkushe ba ya mata dadi sam! Ji take kamar ta fasa ihu ko ta samu sauki. Maman ta mike tana cewa, "Yauwa Mabaruka! Hakuri za ki ki ci abincin ku tafi kar kuyo dare." A can makoshi ta ce, "To." Bayan fitar Maman Rafi'a ta ce "Kin ji ko? Don Allah ki saki ranki ko nima kin karfafa min gwiwa, kowa da yanda Allah yake tsara masa rayuwa da jarabarshi. Taki kenan a haka tazo miki, kar kiyi fushi ko ki ja da ikonAllah." Ta dubeta ta ce, "Ke tunda ki ke kin taba ganin irin haka tsakaninki da Allah?" Ta ce, "A'a ban taba gani ba." Ta ce, "To da wane suna zan kira nawa auren? Ni ba 7 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar auren dole ba ko a garin mahaukata ba a haka, bare a Musulunci wanda hakan babban laifi ne da hukunci mai girma ga duk wanda ya aikata haka, duk saboda kafiya irin ta iyayena da jahilcinsu kowa son ransa yake so. Ta ce, "Ya isa haka nan. Ki bar kiransu da haka, dole dai akwai mafita a al'amarin nan, kuma za ki gani." Та се, "Тo amman meye amfanin yin kwalliyar Rafi'a? ban san wane matsayi nake ba, ban san wane angon zan wa kwalliyar ba?" Ta ce, "Da duk wanda aka riga aka daura shi ne ki kaiwa kwalliyar."Ta numfasa ta ce, "Tir! Da halin iyayena, da yanzu na dade da kai יי kararsu kotu, amman aka hana ni." Ta ce, "Ya isa haka Mabaruka! Mu ci muyi sallar sai mu wuce." Bayan sun gama sunyi sallah sannan suka fice. Karfin shiga kasuwar daman za su kara tsintsinto wasu abubuwan da ba a karasa saye ba, ba don son Mabaruka ba. Duk abin da Rafi'ar ta gani sai ta dauka, suka yi shatar me Adaidaita ta cika dam. 3 이 8 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Fitowa tayi daga shagon ta fito ta tsaya bakin motar, sam! Ba abin da yake burgeta, ba abinda ta zabo don ra'ayinta duk zaben Rafi'ar ne tamkar ita ce amaryar. Ta fito ta sameta ta dubeta da kyau ta ce, "Shi ne ki ka fito ki ka bar ni da zaben ki ka dawo nan ki ka tsaya?" Mabaruka ta yatsina fuska tana kallon wani wurin daban. Ta ce, "Meye amfanin sayen kayan to, alhalin ban san gidan wane angon za a kai ba, Sulaiman ko Imran?" Rafi'ar ta ce, "Ko ma wanene kin san dai dole gidan daya za a kai ki, ko Imran din ko Sulaiman, don haka ki zage kawai ki dauki abinda ki ke so." Shigewa motar tayi ta zauna tana cewa, "In kin gama ina nan ina jiranki, rana na dukana." Sakin baki tayi tana kallonta, sannan ta kada kai ta koma shagon tana cewa, "Allah ya shiryaki Mabaruka." Sai da ta gama daukar abinda zata dauka sannan ta dawo motar suka shiga. A shagon saloon din Anti Farida suka tsaya, ta ce wa Mabarukan ta shiga ta jirata ta kai 9 WAYE ANGON? kayan ta dawo. Maryam Ja'afar Mabaruka ta shiga shagon da sallama jiki a mace tana jan kafa. Anti Farida ta bi ta da kallo har ta zauna, ta ce "A'a amarya ya dai na ganki haka ba kuzari, ko an fasa kukan amarcin?" Mabaruka ta zumburo baki taki cewa komai. Anti Farida ta ci gaba da fadin "Yanzu nake shirin ruifewa in je in ji lafiya har yau ba ku zo ba, ina Rafi'atun?" Ta ce ciki-ciki "Ta wuce gida ta dawo." Ta kalle ta tsaf! Sannan ta dawo kusa da ita ta zauna tare da dafa kafadarta, ta ce "Menene Mabaruka?" Mabarukan ta kalleta idanunta sunyi kwalkwal. Hankalin Anti Farida ya kara tashi ta ce. "Fada min mana, ko an fasa auren?"Mabaruka ta ce, "Da hakan yafi min dadi da kwanciyar hankali." Anti Farida ta ce cikin rashin fahimta. "Kamar ya?" Та се a marairaice zata yi kuka "Maza biyu fa ake kokarin aurar da ni gare su." Cikin sauri Anti Farida ta zazzaro idanuwa ta ce, 10 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar "Me? Maza biyu? Ban fahimta ba?" Ta rausayar da kai "To ya zan miki ma bayanin? Kawai dai maza biyu a ke kokarin aurar, da ni gare su, saboda kafiya da naci da taurin kan iyayena biyu, Mamana da Babana. Kowa yana ji ya isa da ni, hakan yasa kowa ya nace lallai wanda yake so shi zan aura, bayan ni din ni cе kadai ba cira ni za ayi ba." Ta fada hawaye na zubowa daga cikin idanuwanta. Anti Farida ta ce, "Oh God! Amman ya haka? Wane irin addini ku ke bi ne?" Ta ce tana kallonta “Musulunci mana." Ta kara cewa, "Amman daman an taba yin haka?" Ta ce, "A iya rayuwata ban taßa gani ko jin labarin ga inda aka yi cikin sani su fa sun sani kowa ya dage sai dai daya ya hakura ba me janyewa. Ji suke kowannensu shi ya haife ni, yana da iko da ni." Ta ce, "To ina iyayensu?" Ta ce, "Babu daya daga cikinsu dake a raye. Ta kara cewa, "Danginsu fa?" Mabaruka ta ce, "Duk kannansu ne babu me iko da su. Hakan ya ba su damar 11 WAYE ANGON? bìn son ransu." Maryam Ja'afar Tausayin Mabaruka ya bayyana a idonta, ta dafata tare da cewa, "Kiyi hakuri Mabaruka, amman ya za a yi wannan al'amarin ba kiyi wani kokari ba?" Ta kalleta a sanyaye ta ce, "Nayi iya bakin kokarina na nuna musu amman ba wanda ya saurare ni. Karshe na yanke shawarar kai su kara kotun Musulunci. Da Rafi'a naso muje amman tayi kutun-kutun ta hana ta dinga zagina ba ni da hankali zan kai karar iyayena kotu na tona musu asiri a duniya wannan sirrinmu ne ita dai دو tasan dole daya zan aura.' Ta ce, "To ke waye ki ke so a cikinsu?" Mabaruka ta ce, "Sulaiman mana! Kuma shi ne zabin mahaifina, kowa yasan yanda muke da Sulaiman, tare muka taso da shi, ina sonsa tuni shima haka duk da kasancewar yana da mata. Na dade da yin kaura daga gidanmu naki zama gun Babana, haka naki zama gidan Mamana duk don su tsorata su hakura su bar min zabina, na dawo gidan su 12 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Rafi'atu na kashe wayoyina amman Maman Rafi'a taje ta same su ta fada musu ina wajenta kar hankalinsu ya tashi su dai su kara nazari da tunani kar son zuciyarsu ya halakar da su su jefa 'yarsu a masifa, amman ba su ji ta ba. Ganin hakanne yasa ba tare da sanin Rafi'atu ba na sulale zan gudu, a kan hanya naci karo da ita dole na dawo. Yanzu haka a gidansu nake, ta kasa ta tsare ni." Anti Farida ta ce, "Kada ki damu akwai Allah, dole daya za ki aura you will see." Ta langabar da kai ta ce, "Zan ga yanda za a yi kuwa." Daidai shigowar Rafi'atun, ta gansu jigum! Ta bisu da kallo tare da jan kujera ta zauna, sannan ta dubi Anti Farida ta ce, "Tana nan tana ba ki labari ko?" Ta nisa ta ce, "Ina ji amman Rafi'a ya ki ke ganin haka zai yiwu? Anya ba ki kuskure ba da ki ka hanata aiwatar da kokarinta? Akwai sabo faa kan hakan." Rafi'atu ta dubeta da kyau ta ce, "Duk abinda nake ina sane Anti. Ni dai nasan duk taje ta komo miji daya 13 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar zata aura, duk wanda a ka riga aka daura da shi shi kenan magana ta kare. Amman batun ta kai iyayenta kotu bai taso ba, bare ta gudu bata san hannun da zata fada ba. Me yiwuwa ta се gwanda masifar nan. Ita 'ya mace ce, me mutunci dole ne ta zauna gaban iyayenta. Don haka ban goyi bayan hakan ba, kuma ba zan taimaka mata ba, illa iyaka na ce mu ci gaba da gayawa Allah." A nan Mabaruka ta ce cikin fushi "Kwana biyu fa ya rage Anti, me zamu yi lokaci fa ya kure? Zuwa yanzu ya kamata a ce na gama yanke hukunci amman har zuwa yanzun ban san wane matsayi nake ba, ban san me zan yi ba. Wallahi ina cikin tashin hankali." Ta dafe kai... Anti Farida ta ce, "Abinda Rafi'atu ta ce haka ne kam! Zamanki a nan shine mafi kwanciyar hankalinki da darajarki. Dole dai gidan daya za a kai ki. Kiyi addu'ar kawai Mabaruka." Ta dube su ta ce, "Ni yanzu ba ma ta in auri wanda nake so ba nake, a'a wannan abin kunyar da suke son 14 ע WAYE ANGON? Maryam Ja'afar jawo min ne ya dame ni, duk duniya sai ta sani har tsufana. Duk in da nabi sai an nuna ni, haka yarana za su taso. Gefe kuma ga babban sa6on Ubangiji da a ka yi. Ni ban ma san meye hukuncin haka ba." Rafi'atu ta ce, "Ko ma menene ki sa ido ki gani za a yi komai ya wuce, ki sa haka a ranki. Ba wani abu na kyama da zai dame ki." Haka dai suka kasance a shagon Anti Farida uwar dakinsu, tana musu suna kara zanta zancen. ** ** Sulaiman Ango ba zama, ya shiga ya fita tuni ya gama raba katinshi na gayyatar daurin aure ranar Asabar mai zuwa, da misalin karfe biyu daidai na rana. Zuciyarsa fal da murnar samun amaryarsa. Babanta ya kirata, ta jawo wayar tana dubawa. Sam! Babu annuri a fuskarta ba kuma son yin magana da daya 15 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar daga cikinsu take yi ba. Haka nan dai cikin sanyin jiki ta danne tare da kaiwa kunne tana sallama. Daga can ya ce, "Kina ina ne ba, ba mun yi da ke yau za ki dawo gida ba?" Ta yatsina fuska tace, "Ni gaskiya na fasa ba abinda zan yi a gidan." Ransa ya baci, "Zan ci mutuncinki fa Mabaruka! Kin maida ni abokin wasanki ko? Tun yaushe mu kai maganar nan da ke? To ki maida hankali wallahi ki taho yanzunnan ga Jama'a nan sun fara taruwa ana tambayarki, na fada miki." Daga haka ya datse layin. Zuciyarta ta cunkushe tayi shiru ta rasa me zata yi. Rafi'a ta ce, "Ya kuka yi da shi?" Ta fada mata komai. Ta ce, "Ai ba damuwa sai mu wuce tunda an kusa gamawa. Ni na ma manta da yau ne wa'azin, duk damuwarki ta rikita ni." Sai da suka gama sannan suka fito. A kan hanyarsu ne a ka sake kiranta. Wayar na hannun Rafi'atun ta duba taga Mama (Maman Mabarukan), don haka da sauri ta miko mata tana cewa "Karbi Mabaruka, Mama ce." Harararta tayi ta kara yin gaba, har wayar ta yanke ba 16 E 3 Σ WAYE ANGON? Maryam Ja'afar su dauka ba. Sai a karo na biyu ganin Mabarukar ta ki karba yasa ita ta dauka. Suka gaisa da Maman ta ce, "Ina Mabarukan ne?"ta ce, "Gata nan wai taki karba ranta ya 6aci."Maman ta ce, "Ki bata wayar."Ta ce, "To." Ta mikawa Mabarukan ta amsa tana zobara baki. Daga can ta ce, "Zan ci ubanki fa Mabaruka, wacce irin kafaffiyar yarinya ce ke wai? Kina son ki bani kunya ko? Jibi daurin aure amman ba kya gida, wacce tsiyar ki ke yi a waje?" Mabaruka ta ci gaba da turo bakin ba tare da ta ce komai ba. Maman ta ci gaba da cewa, "Wallahi kiyi marmaza ki taho yanzunnan, tun kafin ranki ya baci. Zan turo Imrana yazo ya dauke ki, kina gidan su Rafi'ar?" Cikin gunguni ta ce, "A'a muna saloon." Ta се, "То zai kira ki ki fada masa inda ki ke." Daga haka ta yanke layin. Haushi, takaici da bakiń ciki suka tokare ta. Sakin wayar tayi tayi gaba abinta cikin tsananin fushi. Rafi'ar 17 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar ta tsugunna ta tattara wayar ba tare da ta ce komai ba, sannan ta biyo bayanta. Tafiya kawai suke ba me magana har suka iso. A kofar gida suka gamu da Baban, ya fito da butoci za suyi alwalar sallar Magriba tare da mutanansa. Ya kirata taje tana 6ata rai, ya dubeta a tsanake ya ce, "Menene naga ranki a bace?" Bata jin akwai amsar da zataiya ba shi. Ya kara nanatawa. Ta ce "Ba komai, kaina ne yake ciwo." Ya kalleta tsaf! Ya fahimci ko menene, amman ya ce, "Ciwon kai kuma a wannan lokacin bai kamata ya dame ki ba. Ke da ke kokarin zuwa gidan masoyinki?" Ta kalle shi kallon bai san me yake ba. Shi a tunaninsa har wani farin ciki ząta yi? Da babu wata harkalla a daura auren da shi ne zata yi farin ciki, amman wannan auren da cikinsa yake da fitintinu..? Ya katseta "To ki je ki sha magani. Tun dazu a ke jiranki har an gama taron amman akwai sauran Jama'a cikin gida ki isa kwa gaisa." Bai gama rufe bakinsa ba ta 3 E 18 WAYE ANGON? juya ta wuce don ta gaji da maganarsa. Maryam Ja'afar Gidan ya fara daukar harama da 'yan biki, 'yan Kauyensu duk cikin mutanen babu dangin Mamanta ko daya, daga nashi sai na Inna matar Babanta, su ke ta hidimarsu. Da shigarta ma su tsokanarta nayi ma su janta nayi, babu wanda ta saurara suka shige dakinsu ita da Rafi'a. Ta fadi zaune jagwab tare da dafe kai ta ce, "Na shiga uku ni Mabaruka, da gaske dai ne?" Idanunta suka yi rau-rau zata yi kuka. Kafin Rafi'atu tayi magana wayarta ta hau kuka ta duba, Imran ne. Ta kai kunne tare da cewa "Hello!" Daga can ya amsa suka gaisa yana tambayarta "Mabaruka fa? "Ta ce, "Gata nan kusa." Ya ce, "Ok! Ki ce mata gani nan kan hanya ina zan sameta?" Та се, "Muna nan gidan Babanta." Ya ce, "Ok, ga ni nan na kusa." Tа се, "To." Tare da kashe wayoyinsu, ta dube ta ta ce, "Ga Imran nan kan hanya ya kusa." Ta dube ta da rinannun idanunta ta ce, 19 WAYE ANGON? "Wai ya zan yi ne Rafi'a? ina zan sa kaina?" Maryam Ja'afar Tayi shiru tana kallonta cike da tausayinta, ta ci gaba "Shi ya kira ni lallai in taho nan ita ma ta kira ni lallai in tafi can, har ta turo shi ya tafı dani wai ya ake son nayi? So suke su birkita min kwakwalwa don Allah?" Ta cè, "A'a wannan duk mai sauki ne, tunda mun zo nan din ya gan ki sai ita ma muje can din tunda ita uwa ce mace, me yiwuwa akwai wasu abubuwan da zata ba ki daman abin da ya kamata kenan daidai wannan lokacin kina tare da ita, don yi miki shiri mai kyau wanda shi Baban ba zai yi ba, ko kin zauna a nan ba abin da zai miki, to gwanda ma ki tafi can din kawai." Ta jingina da bango tare da cewa, "Oh! Ya Allah ka kawo min dauki cikin gaggawa, kai kaďai ka san me kenan, kai kadai ka san abin da zai faru. Ya Allah ka kawo min komai da sauki." Gidan a cunkushe yake da Jama'a, daman ga shi a kuntace. Dakuna biyu ne ko kitchen babu. Girkin a 20 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar tsakar gida aka fora shi, don haka gidan ya dauki zafi rau babu in da iska ke shigowa, ga hayaniyar Jama'a ga zafin wutar girki, don haka koda Imran din ya zo bata yi musu ba suka sudade suka tafi ko don su sami saukin cunkuson nan. Suna tafe tana gaba gefensa duk ta hade rai babu alamar fara'a a fuskarta, tana yin komai ne don an fi karfinta, yayin da shi kuma jefi-jefi yake kallonta zuciyarsa tana masa dadi saboda kusan mallakarta da ya yi nan da kwana biyu. Shi kadai ya san yanda yake jin ta a ransa, sai Allah. Zuciyarsa har zafi take. Babban burinsa da farin cikinsa ya samu Mabaruka a matsayin matarsa da a komai ya gama nema ba shi da sauran damuwa a ransa. Ya fi kowa dace a rayuwarsa saboda samunta, bai san ya zai misalta irin son da yake mata ba, komai nata burge shi yake, ko me tayi duk da ba son shi take ba. Idan yana tare da ita ya kan manta damuwarsa, ya kan ji shi cikin sabuwar duniya me dadi. Idan ko ya 21 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar same ta akwai alkawurra da ya yi wa kansa tsakaninsa da Allah, gefe kuma da sadakin da zai bayar. Ita kanta akwai alkawarin da ya mata a bayan aurensu, ko lefen da ya hado mata abin kallo ne, akwati set shida kowane dankare da kaya kamar a mafarki. Ga gwala-gwalai da manyan less-less da atamfofi (supers), takalmi, jakunkuna, kayan make up (shafeshafe) har wanda ba a taba ganin irinsu ba sai a kayanta. In da aka zubo su a dalleliyar motarta sabuwa dal duk cikin lefen take. Mota ce mai matukar tsada da kyau sabuwar shigowa, wannan lefen ya dauki hankulan mutane haka aka dinga daukarshi a wayoyi ana yada shi cikin gari. Sannan kerarran gidan da za a kaita ba zai kwatantu ba, girmansa da tsaruwarsa ya wuce misali, ita kadai sai tarin ma'aikata ma su kula da ita. Kowa a kagarce yake zuwa wannan ranar. A takaice Allah yajarabce shi da sonta kamar me a rayuwarsa. Yana yi yana dan tsokanarta da hira amman tamkar 4 22 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar ba ta motar, a kagarce take so take su isa ko ta sauka daga motarsa. Ya yi dariya ya ce wa Rafi'a, "Ban san me ya sami kawar taki ba take fushi da angon nata." Daga bayan motar ta ce, "Kun fi kusa ai Imran. Tambayeta za ta fada maka, tsakaninku ne." Ya yi murmushi daidai karya kwanarsa in da suka shiga layin gidan. Ya ce, "Allah ya tabbatar mani da wannan kusancin tsakaninmu." Ba ta iya ce masa amin ba. Yayin da Mabarukan da ta juyo ta mai wata muguwar harara, ji take kamar ta shake shi ya mutu gabadaya shi kenan wutar ta mutu ta samu kwanciyar hankali su ma iyayenta su jitu. Tayi kwafa kawai ta kauda kanta tana kallon window. A sanyaye ya ce, yana kallonta "Kiyi hakuri." Ba ta ce komai ba, tun kan ya gama parking ta fito har sai da ta kusan faduwa, amman bata damu ba tana tadewa da mayafinta ta wuce da gudu-gudu, sauri-sauri. 23 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Ya bita da kallo yana jin wani irin sonta na fizgarshi. Rafi'atu ta fito ta dube shi ta ce, "Kayi hakuri Imran, za ta bari idan har kai ne mijinta." Daga haka ta wuce ya bita da kallo sam maganarta ba tayi masa dadi ba, bai iya fitowa ba

Chapter 1 of 9