yaja motar ya wuce.
A kullum idan tazo gidannan yana burgeta, a iya
tasowarta ba ta taba taka gida mai tsananin kyau da
tsaruwa ba irin gidan nan da Maman Mabaruka ke
rayuwa cikinsa ba.
Duk sanda take cikinsa mantawa take da kasar da
take Najeriya, tsarinsa irin na kasashen waje ne, gida
tamkar tangaram ba ko kurjewa ko kasa, ko'ina kal-kal
ma'aikata suna hidimta masa.
Kamshi kamar kamfanin hada turaruka, ga
sassanyar iska da take kadawa mai dadi da kamshi daga
shuke-shuken gidan, gefe kuma ga nau'ikan abinci masu
dadi da lafiya da ake giggirkawa a cikin gidan da
abubuwan sha masu dadi, wanda duk sanda tazo taci su
S
24
1
WAYE ANGON?
take tafiya da sabbatunsa.
Maryam Ja'afar
Dole ne ma mazaunan gidan fatarsu ta canja tayi
kyau, musamman Mama, Maman Mabarukan bare
Mabarukan, gidan ba bakonta ba ne don haka tasan
hanyar da zata sadata da masu gidan.
Kasancewar jibi biki gidan shima ba laifi baki sun
fara zuwa amman kasancewar gidan masu kudi katon
gidan babu wani takura, falo-falo ne gasu nan da dakuna
ana ta hidima duk da su ba wai girki za su ba, sai dai ayi a
kawo.
Duk dangin Maman sun zazzo wasu sai gobe wasu
ma sai jibin, 6angaren Imran ma nasa duk sun żo, abin
gwanin sha'awa da burgewa.
Lokacin da Mabarukan ta shigo bata saurari kowa ba
da suke tsokanarta da gudu ta wuce dakin Mamyn, da
zuwanta ta fada jikinta tana kuka.
Hankalinta ya tashi, ta rike ta tana cewa "Lafiya
Mabaruka? Menene?" Ta dago fuskarta jike da hawaye,
idanunta sun rikide kana kallon yanda kanta ke 6allawa
25
WAYE ANGON?
saboda ciwo.
Maryam Ja'afar
Tana kukan ta ce, "Don Allah Momy ki tausaya min
ki janye maganar auran nan, wallahi ina cikin tashin
hankali kar ki sa ni cikin masifa, ban taba son Imran ba
ko sau daya a rayuwata.
Shi ne mutum na farko da na fara tsana, wallahi ko
muryarsa ba na son ji bare in gan shi, har ta kai ni kuma
ga auranshi.Wallahi zan cutu Momy, don Allah kijanye
ki bar ni da Sulaiman."
Ranta ya baci, ta ci gaba da harararta, taja tsaki
"Maganar banza kenan, ni so ki ke in yi magana biyu?
Tun yaushe sadakinki ya zo hannu! Ko so ki ke girma da
mutuncin da Babansa yake ganina da shi ya zube?
Tun yaushe muke maganar nan? Na fada miki na
nanata miki, wallahi ba ki da miji sai Imran, shi na zaba
miki, ban ga aibunsa ba, nutşuwa, hankali da tarbiyya ga
ilimi, to me kuma a ke nema?
Ina tabbacin wallahi babu gidan da za ki samu
kwanciyar hankali da nutsuwa sai gidansa. Imran yana
26
WAYE A'NGON? Maryam Ja'afar
sonki, yana tausayinki, ya kuma damu da ke. To don me
za ki ce ke ba kya sonsa? Alhalin an halicci zuciya da son
mai kyautata mata!
Don haka ki sa shi a ranki, ki so shi ki dauka tuni shi
ne mijinki. Ko yau na fadi na mutu wallahi ban yarda ki
auri wani ba sai shi, shi nake so da shi na yaba."
Mabaruka ta zauna rajab! Saman lafiyayyan gadon
mai lallausan zanin gado, ta ce "Ni kuma ba za ki duba
abin da nake so ba, zuciyata take so ba? Taki ki ke
dubawa?
Momy zuciyata zata yi daci, zan dawwama da kunci
karshe ciwo ya kama ni na mutu. Sulaiman shi kadai
nake so, duk abin da ki ka lissafo na Imran, Sulaiman
yana da shi har ya fi shi.
A gidansa ne zan fi samun kwanciyar hankali da jin
dadi, shi ne kadai zai ba ni farin ciki ba Imran ba."
Ta kalle ta da kyau ta ce, "To ni kuma ban amince ba,
idan har ni na haife ki ya zama dole ki bi abin da nake so
kiyi kuma." Та сe, "ТTo shi kuma wanda ya zaba min
27
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Sulaiman waye shi gare ni in ke Mahaifiyata ce?"
Kai tsaye ta ce, "Ubanki mana. Hakan yasa ban
yarda da zabinshi ba nawa nake so."
Ta ce, "Shi mahaifina ne shi na saba mishi kenan ke
na miki abin da ki ke so?"
"Kwarai kuwa, don ni na haife ki nayi renon cikinki,
nasha wuya wajen haihuwarki ko na mutu ko na rayu,
haka na haife ki naci gaba da renonki ko na ci ko ban ci
ba ke sai na ba ki kinci kin sha fa.
Duk bai gabansa, sai ya ci sau goma ke bai ba ki kin
ci sau biyu ba, amman ni bani ci ke ba ki ci ba asalima
nafi son ke kici akan ni naci. Nafi sonki a kanshi, yanda
yake sonki nafi damuwa da ke a kan shi.
Koda wasa ma ba za ki hada uwa da uba ba, Annabi
ya ambaci uwa sau uku sannan ya ambaci uba sau daya,
don haka dole ni za ki wa biyayya kafin shi in har kina
neman albarka, kuma zabina ba aibu ba ne alkhairi ne
gare ki, ba ma ke kadai ba har ga mahaifin naki."
Ta dafe kai ta kara fashewa da kuka har yanzu ta kasa
28
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
fahimtarta, shin ya zata bullo wa al'amarin nan?s ums
Anti Karima ta shigo kanwar Momy ce ta bisu da
"kallo, sannan ta ce "Har yanzu dai maganar nan ba ta
Rare ba Mabarukan ad or sase in ad ad smsdsg of
Ta dago tana kallonta da jajayen idanunta, ta ce
"Yaushe za ta kare Anti, bayan ni kadai nake hango
tashin hankalin da za a jefa niek uk eh uiq nsm ida
Ta zauna tana cewa, "Auran Imran dinne tashin
hankali? Ke ba ki gani kin san kuwa irin jin dadin da-za
ki samu gidansa? Ko kayan da ya hado miki ya isa ki
sauke makamanki uwa uba gidan da iya Rera miki
saboda ke kadai kawai yana sonki yana kyautata miki,
kuyi aurenkuku fita kasashe jin dadinku da hutu.T
Amman duk wannan bakyau hangowal kin
gwammace ki auri wancanarPalakaoMalamin
Makarantar wanda kafin albashinisa yazo ya cinyelsu da
9bashisnsd no2.o2 ssy sturl iss sbai swod ide sb
b To melyacP ya ba ki ya ba abokiyar zamanki? Ga
iiwarsd ga Ranwarsa, to bare mu in mika zo hie zamu
029.
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
samu gidan bushe ke bushe? Duk ba ki duba wannan ko
Mabaruka?"
Ta kalleta kamar ta mare ta, ta ce "Wannan ni ba shi
ne gabana ba, ba shi nake so ba. Ni shi nake so shi kadai,
shi ne farin cikina da kwanciyar hankalina.
Arziki kuma wannan na Allah ne, zai iya azurta mu.
Shi Imran din da ku ke magana ba zai iya min abin da
Sulaiman din zai min ba, ba shi da abin da nake so daga
gare shi.
Gidansa zai zame min tamkar akurki, dukiyarsa bata
taba burge ni ba wallahi, don ba za ta bani farin cikin da
nake so ba."
Ta ce, "Ke yarinya ce sakarya, za ki gane gaba ba ki
da hankali tukunna, wa ke kai kansa ga talauci? Kowa
yana neman tsari dashi.
Domin kuwa Annabi (S.A.W) ma yana neman tsari
da shi, kowa inda zai huta yake so. Son banza shirme
akwai abin da ya kai kudi? Ai so shi ne kudi, in da kudi
komai lafiya daidai ne, kudin su ne za su bada farin ciki
S
30
WAYE ANGON?
da sanyaya rai bare yana sonki.
Maryam Ja'afar
Duk ki manta da rashin sonsa da ki ke yi, za ki so shi a
hankali shi da kanshi zai koya miki sonshi. Amman
Sulaiman din ga talauci ga muni, ko fuskarsa ki ka kalla
ta dinga tayar miki da gaba.
To bare kuma ba abin moruwa a tare da shi. Wallahi
Mabaruka tir! da zabinki, kuruciya na dawainiya da
ke."
Mabaruka ta ce, "Bai kamata kina fadin haka ba
Anti, a tunanina kin yarda da Allah Madaukakin Sarki,
talauci ko arziki duk nasa ne, zai iya ba wanda yaga
dama ba kuma don yafi sonsa ba, sai don ya ga imaninsa.
Haka nan wanda yaba talaucin ba don ba ya sonsa ba
ne, sai don yaga Imaninsa. Sannan shi so Allah ke sa wa
bawa in har kana son mutum komin muninsa da
talaucinsa ba ka gani, sabida shi ka ke so ba arzikinsa ba.
Ba kuma kyawunsa ba, shi ka ke so don Allah, kuma
za ka zuana da shi a kowane hali yake, kuma kayi farin
ciki da walwala da jin dadi ba ka da damuwa don farin
1
a
r
n
la
ni
ya
31
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
cikin yana tare da shi da jin dadi da kwanciyar hankalisb
In Allah yaso kuna tare sai ya azurta shi kuma babu
wanda zai kai ka jin dadinsa, saboda kayi hakuri dả shi
sanda ba shi da shi, kuma kai ne cikakken masoyinsa. 2
Amma in ka bi son zuciyarka ka auri me kudi alhalin
ba ka sonsa, wallahi za ka yi rayuwarka a hakurce don
ba haka ka so ba. Kunci, damuwa da rashin walwala za
su sami gurbi a rayuwarka.
Ke
Ga kudin da akwai amman za ka kasance kó da
yaushe zuciyarka a cunkushe, kudin ma su gagara
nunawa a jikinka, saboda ana cinsu da damuwa ba farin
ciki ba.
dShi kuma duk abin da zai yi ba zai taba burgeka ba,
sai ma haushinsa da ka ke ji. Sai ka fara rama, ciwora
rasa me ke damunka, ga ka dai kana jin dadi amman a
rasa me ke damunka.ire sbidsa insg eled semouatst
Daga nan in ka gaza hakuri zuciyarka ta rinjaye ka,
shaidan ya yi tasiri a gare ka. Sai ka fara neman wancan
masoyin naka koda a waya ne, in abun ya yi nisa sai ku
9
32
S
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
fara mahadеtак сор dibagre el dub,ue sbiorids nia
To duk mai ya jawo haka? Saboda ka bi kudi, kuma
wallahi sai Allah ya kama ka da wannan laifin.l nsbi
Don haka ni Sulaiman nake so, shi ne farin cikina da
shi zan samu nutsuwa ba Imran ba, ku barni na aure shis
ku ku janye naku don Allah don farin cikina da
nutsuwata."Ta hada hannuwa tana rokonsuNB OT
sartAnti ta ce, "Wallahi kina bani mamaki Mabaruka,
kudi ai su ne damuwa, in da akwai su damuwar yayewa
take, wannan lokacin har wani duba haka ake kowa
fatansa kenan ya samu mai kudin ya kurda ya shige shi
ma ya lasa.si eins si eb udnc AшоM
s) Amman ke idonki ya rufe kan wani banza can mai
fama da talauci, so ki ke kema kigbi layin wasu a
zuri'armu duk in da suka shiga ana tausaya musu, sun
kode da su da kayansu sai uban kasusuwa a wuya su da
ya'yansu ba suturar kirki, ko pampas ya gagare su sa wa
ya yannı ilim ekey niq nsnislua sb noe emwl,idst!ew
a Saia dinga kyamar daukar'yalyan, su kansu ba a son
33
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
cin abinci da su, duk fa sanadin talauci, kana ji kana gani
a fidda kai a danginka, har a gidanku ma.
Idan kuwa da kudi, ko ba a sonki an yi da ke, kin yi
kyan gani; da namiji ma har za ka biye ma sonshi in ya
tàshi yo miki tsiya sai ya daga ki sama sannan ya yado ya
yi gaba ya nemi wata.
To gwanda tun wuri ki wa kanki fada, wallahi ki
nutsu Imran dai ba shi da laifi, yanda ki ka shiga ransa
haka za ki wala abinki, ke kadai a gidansa kiyi isarki son
ranki, ki juya ki iskancinki ke kadai ba wata daga ke sai
'ya'yanku, kuma kyan nan ga shi nan masha'Allah."
Momy ta ce, "Ke rabu da ita Karima, ita ta sani. Ni
dai na gama maganata da shirye-shiryena, magana tayi
nisa me ya rage kwana biyu, sadakinki na hannun
Kawunki, jibi daurin aure.
Don haka babu abin da za a fasa, ga ki can a gidan
Imran a hankali za ki gane sai kin zo kina min godiya
wallahi, kuma son da Sulaiman din yake miki na rantse
bai kai na Imran ba, mata nawa ke rawar jikin ya aure su
34
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
sai ke ya ce zai aura amman kin nace duk ba ki ga baiwar
da Allah ya miki-ba sia kin kai kanki mahallaka kan
יי shegen so."
Anti ta ce, "Yo ji fa motar da aka kawo mata, ko ke
Yaya ba ki hawan irinta sai ita ta shiga ta kece raini cikin
kawaye da dangi, gaba ma wata zai canja mata wacce
tafi wannan."
Ta ce, "Duk bana so ku tattara ku rike ku kece rainin,
ni bana so Sulaiman nake so, kuma tare da shi zan sami
duk wadannan ta ce sai kije ki tayi ba ki gaji ba, aure dai
ba fashi na gama magana."
Anti ma ta ce, "Aikuwa ga masu tsara dakuna can na
gyara miki, ina ga ma yanzun sun isa su gama, don yazu
יי nayi waya da su Samira ta ce sun kusa gamawa."
Momy ta ce, "Kai ai ko sun yi sauri. Gwanda ma su
dawo din su zo suje min kasuwa ko store ne."
Ganin sun banzatar da ita yasa ta fice daga dakin
fuuu ta nufi dakinta, idonta ya rufe taf da hawaye tana
zuwa ta fada kan gado ruf da ciki tana kuka.
35
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
NTunda Rafi'ar ta shigo ta jiyo maganarta dakin
Momynta saita wuto dakinta ta zauna tana jirantal'A sb
Ta taso ta tsaya kusa da ita ta dagota ta ce,"Me yasa
ki kuka? Tana shesshekar kukan ta ce, "Wai wane irin
iyaye ne Allah ya bani marassa fahimta sai tsabar son
zuciyarsu da kafiya?sIsv n eden igusb sh eyewel
Ta nisa ta ce, "Ba haka ba ne Mabaruka, ki godewa
Allah wallahi wasu ba su sami wannan gatan da ki ka
samu ba, wasu kuma in kinga iyayen nasu za ki yi tir da
su sam ba su cancanci wannan sunan ba. srinsbew Jub
Ta katseta "Ni ma kusan hakanne, waye ba zai yi tir
da su ba? Ta ceş Bana son" maganganun nan
Mabaruka, iyaye iyaye ne ba ki da kamarsu, ba za kiiya
canza su ba, ki sake wásu ke fa matsalarki a kan aure ce
kawai in ba akan wannan ba ba ki taba samun sabani da
su ba, don haka ki bar cewa hakaojna os ne nib owsb
nilьTasa bayan hannu, ta goge hawayen tare da shan
majina ta ce, "To ya zan yi ne? me zan yi da gaskenfa
kowannensu yake lei ilis sb tur obeg nek sbat si eWIIS
36
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ta zauna tare da dafa kafadarta ta ce, "Mabaruka a
koda yaushe ina ce miki ki gayawa Allah matsalarki da
damuwarki shi ne kadai mai miki maganinta.
Wani kuka da tashe-tashen hankali ba za su taba baki
kwanciyar hankali ba, ko mafita. Kiyi addu'a idan Imran
alkhairi ne gare ki Allah ya tabbatar da shi ya círe miki
tsanar da ki ke masa, ya mayar miki da sonshi ki..."
Ta katseta "Kar ki ce haka Rafi'a, ni nasan Imran ba
zai taba zama alkhairi gare ni ba, saboda ba na sonsa.
Kar ki min wannan addu'ar, idan har mai kaunata ce ke."
Kallonta take ta rasa me zata ce mata, wayar Rafi'ar
ta fara kuka, ta jawo ta tana dubawa ta kalleta ta се,
"Imran ne."tamkar bata gun bare ta amsa mata.
Ta sake cewa, "Ina wayarki, kin rufe ne ya kira bai
same ki ba?" Nan ma tanke bata tanka ba. Lura da ba za
ta yi magana ba yasa ta dauka kar wayar ta yanke.
Ta ce, "Kana son magana da Mabaruka ne?" Ya yi
murmushi daga can ya ce, "A'a da ke nake son magana,
don nasan ba za ta saurare ni ba. Ina kuma tarė da
37
WAYE ANGON?
abokaina."
Maryam Ja'afar
Ya bata tausayi matuka, amman ta ce "Ina jin ka to."
Ya ce, "Maganar partyn nan ne, ban san ya abin zai
kasance ba. Na fada muku friends dina suka shirya,
yanzu ma haka muna tare da su a hotel din suna son
magana da daya daga cikinku."
Ta juyo tana kallon Mabarukar, yanda tayi kicinkicin da rai duk da ba jinsu take ba, amman don taji an ce
shi ya kira. Ta numfasa sannan ta ce "Shi kenan ba
matsala ka ba su muyi maganar."
Ya ce, "Ok! Na gode Rafi'a." Tayi murmushi "Ва
komai."
Tsawon lokaci suna magana ta tsakanin abokanan
ango da babbar kawar amarya, sun tattauna komai
yadda zai kasance, daga bisani suka yi sallama a kan sai
goben.
Ta juyo tana kallon Mabarukan, ta ce "Kin ji yanda
muka yi da Imran, a kan partyn nan. Ni wallahi na manta
da maganar nan, wa muka gayyata da zai zo? kar fa ayi
Σ
38
S
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
abin kunya amarya ba kawaye daga ni sai ke?"
Wani dogon tsaki taja tare da kwanciyarta taci gaba
da kallonta, ta ce "Da ke fa nake kinja tsaki kinjuya min
baya, ni ce Imran din da za ki ji haushina?"
Ta tashi zaune a kufule ta dubeta "Me yasa ki ka
saurare su? Ni nace ki dauka bare kuyi magana? Partyn
banza ina ruwana, kije kuyi ni dai ba in da za ni wallahi."
Ta dube ta cikin mamaki tà ce, "Mabaruka kin san
me ki ke fada kuwa? Kina son ki ba shi kunya ki nunawa
Jama'a ba kya sonsa?
Wai meye laifinsa? Me ya miki? Bawan Allah mai
hakuri da saukin kai tunda ki ke kin taba ganin abokin
fadansa koda a cacar baki ne?
Komai nashi cikin nutsuwa da hankali yake yi,
mutane suna ganin girmansa, me yasa ki ke son
wulakanta shi? Me yasa ki ke son tozarta shi
Mabaruka?"
Ta ce, "Saboda ya shigo rayuwata shi ya fara takura
min yasa aka tursasa ni a kan abin da ba ni da ra'ayi,
39
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
wallahi bana sonsa bana sonsa ko kadan ko muryarsa
naji sai raina ya baci, na rasa me ke min dadi.
Kunci ya baibaye ni, har zuciyata tashi take bare na
ganshi, ko gidannan ya shigo sai naji ni a kuntace, na
rasa walwalata: Na fada muku na fada na kara fada don
me ba za ku fahimta ba?
Idan ku ka yi wasa da shi da ku sai na baku kunya, sai
ya yi kuka da idonsa wallahi."
Zuwa yanzu Mabaruka ta daina bata mamaki, lallai
ta yarda bata sonshi, don taga kiyayyarsa a cikin idonta
karara, amman ta dubeta ta ce mata.
“A'a Mabaruka, karki tsananta kiyayyarsa har haka,
wallahi ba ki fahimce shi ba, Imran ba shi da kuskure, ba
shi da aibu wallahi in ki ka aure shi za ki sami kulawa
fiye da kowanne gidan in ki ka je.
Saboda yafi kowa sonki, duk cikin wadanda suka
nuna suna sonki ban ga me sonki ba kamar Imran. Ba
wai ina duba abin hannunsa ba, ko gidansu, wallahi sai
don kyakkyawan halinsa da kirkinsa.
40
S
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Soyayyar da yake nuna miki tsakani da Allah ne, za
ki fi walawa a gidansa kiyi abin da ki ke so, ba ki da
kokwanto a kanshi. Kuma zan fi farin ciki da nutsuwa
idan ki ka aure shi, nasan ba ki da sauran damuwa ko
matsala a rayuwarki.'
Idanunta suka sauya, kwalla ta taru ta dubeta da kyau
ta ce, "Kin kuwa san kiyayya Rafi'a? kin san zafinta da
dacinta?"
Ta ce, "Na sani, abu ce mai sauki ba mai wahalarwa
ba, idan ki ka fahimceta zuciyarki tana fin karfinki ne, in
ki ka zama ke ke iko da ita wallahi za ki nemi kiyayyarsa
ki rasa, ko kuma ta ragukashi sittin cikin dari.
Ni ina kiyayata a inda ta dace a inda naga illa ko aibu,
amman taki kiyayyar in da ki ke yinta bata da illa, illa
kin sawa ranki hakanne, shi yasa ki ke kara zafafa.
Amman ki dan rage ki gani sai Imran ya zamo shi ne
masoyinki ba Sulaiman da auransa ke da matsaloli
cikinsa dankare ba."
Tasa hannu ta goge hawayen idonta ta ce, "Ya isa
41
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
haka Rafi'atu, ba na son shawararki, na gode ku bar ni da
Sulaiman shi nake so, kar ki kuma min maganar Imran
don Allah.""
Ta jinjina kai alamar gamsuwa ta ce, "Shi kenan zan
miki maganarshi nan gaba idan shi ne mijinki. Na bari,
Allah ya baki hakuri ya zaba miki mafi alkhairi cikinsu
zuwajibin."
Ba ta ce komai ba, ta sauko daga kan gadon ta shige
bandakin da ke cikin dakin.
Karfe takwas na dare, don haka ta shirya don
wucewa gida, lokacin da ta fito ta ganta tsaye tana yafa
gyalanta, ta ce "Ina za ki?"
Ta ce, "Gida, dare yana yi." Ta karaso tana cewa
"Gida kuma? Na sha a nan za ki kwana?" Ta сe, "A'a,
Mama ba ta san hakan ba, sai gobe zan dawo."
Jikinta ya yi sanyi, ta marairaice ta ce, "Kasancewata
tare da ke yasa nake jin sauki da walwala, idan ki ka tafi
wallahi zuciyata zata yi kunci Rafi'a, don Allah ki
tsaya."
42
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ta ce, "Mabaruka Mama fa bata sani ba."Ta ce "Zan
mata waya in sanar mata, nasan Mama ba za ta hana ba,
tasan muna tare.
Ta ce, "A'a Mabaruka, na fada miki wallahi gobe zan
dawo a nan zan kwana, amman yau kin ga ban zo da
יי shirin hakan ba."
Tayi jim! Ta zauna gefen gadon tsawon dakiku ta
kasa cewa komai, sai can ta numfasa ta ce, "Ok, kije
daman ke ce matsalata. Wallahi kina tafiya ni ma zan
kama gabana, sai dai a daura auran da wata." Ta hade
rai.
Da sauri ita ma ta zauna a tsorace ta ce, "Kada ki fara
Mabaruka, don son Annabi ki zauna gaban iyayenki, ki
musu biyayya a kan abin da suke so da ke, ya fi miki
alkairi a kan ki shiga duniya, sai ki ga Allah ya kawo
miki mafita a cikin al'amurranki, ya yaye miki
دو damuwarki,tafiyarki ba alkairi ba ce.
Та се, "То in har ba ki son na tafi sai dai ki zauna tare
da ni har a daura aure." Tayi jim! Sannan ta ce, "Shi
43
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
kenan na amince tayi murmushi ta ce, "Na gode kawata,
ba zan iya biyanki ba."
Ba ta çe komai ba, sai ta canza zancen "Anya ba
muyi kuskure ba da ba mu gayyaci kowa ba bikinnan?"
Ta ce, "Na fada miki bana farin ciki da aurannan bare
a zo a taya ni murna, kowa tayi zamanta gidansu
abokanan taya ni jaje nake nema."
Ta ce, "Har yanzu kin kasa ganewa Mabaruka,
amman Allah kai mu muga ya abin zai kasance."
Haka dai suka kasance.
Sun yi wa Mama waya ta ce, "Ai daman tunda naga
kun yi dare na ce me yiwuwa a can za ku kwana."
A ka shigo musu da nau'ikan abinci kala-kala,
Rafi'atu ta zauna ta take tumbinta, hankalinta kwance
yayin da mutuniyar kallo ma bai isheta ba.
Ganin Rafi'ar ta matsa mata ne yasa ta fita ta hado tea
ta dawo tana shan shi bayan shi bata çi komai ba.
Sun dade suna hira daga baya Sulaiman ya kirata. Ta
dauka ba yabo ba fallasa, ya ce "Me ya same ki naji
muryarki haka?"
44
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ta ce a shagwabe, "Kai ma kasan dole muryata ta
kasance a haka, ina cikin tashin hankali fa. Ban san.
wane matsyain nake ba shin kai ne ANGON ko ko
IMRAN ne?
Gobe kawai ya rage min amman har zuwa yanzu
babu wanda ya janye kudurinsa tsakanin Momyna da
Imran din. Ta karbi sadkai da duk kayan aurensa, hatta
jere anyo a gidansa, shi ma yana shirye-shiryensa gobe a
ke party da abokansa suka shirya.
Me yasa to hankalina ba zai tashi ba? Da gaske suke
sun yi shirinsu, 'yan biki duk sun hallara wasu daga
garuruwa wasu kuma daga wasu kasashen, hankalina
yana kara tashi idan naga shirin da suke."
Ya yi jim! Sannan ya ce, "Aure tsakanina da ke shi ne
tabbas, amman nasa gaibu ne NI NE ANGON, duk abin
da suke zai tashi a banza ne, ni ne kadai mai auranki, don
ba a aure biyu. Sadakinki na bayar yau sun zo sun yi jere,
don haka biki ba fashi."
Hankalinta ya kasa kwanciya, abin da yake fada shi
45
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Imran yake fada, shin cikinsu waye na gaibun waye
tabbas?
Zuciyarta ta cunkushe tai mata nauyi har daci-daci
take ji, madadin kalamansa su sanyaya ranta sai ma suka
Kara ingizata har dai suka gama wayar bata samu wata
nutsuwa ba.
Sha daya da rabi na dare Imran ya dawo, sam mutane
basu bar shi ya huta ba tún yau kenan a gajiye ya shigo
gidan kai tsaye dakinsa ya sauka ya rage kayan jikinsa
ya dan watsa ruwa ya dora jallabiya ya sanyo slipas ya
fito.
A filo suka ci karo da Momy, ta ce "Ka dawo
kenan?" Ya ce yana sosa keya "Eh shigowata kenan
mutane sukarike ni."
Ta ce, "Akwai haka kam, hidimar kenan. Abinci fa?"
Ya ce, “Ban ci ba tukunna, yanzu dai zan ci." Ta се,
"Ok, kaje ga shi can a dining naka kadai na ce a aje can.
Ya ce, "To ya Jama'a sun fara taruwa ko?" Ta ce, "Ai
kuwa an gaji wasu sun kwanta wasu kuma ga.su can
46
WAYE ANGON?
suna hira."
Maryam Ja'afar
Ya yi murmushi ya mike ya nufi dinning din yana
cewa, "Daddy fa bai sauka ba?" Ta ce, "Eh sai gobe,
mun yi magana da shi a waya har ya zo airport kuma ya
koma, amman idan komai yai clear zai taho gobe in
kuma sai jibin to."
Ya zauna yana cewa "Ya kamata dai yana nan aka
daura auran, ban so tafiyar nan America ba ko da ya fada
min sai da gabana ya fadi."
Ta ce, "Ai ko ko shi haka yace bai so ba. Yafi son
yana nan ake hidimar komai, amman ya ce ko bari ne sai
ya yi yazo ranar daurin auren akwai abokanshi da za su
zo wasu ma Turawa ne da Larabawa, yana da kyau kuma
su hadu."
Har ya gama dai suna hirarsu, daga bisani suka yi
bankwana ya shige dakinsa ya kwanta saboda gajiya
bayan ya cire jallabiyarjikinsa.
Dare ya fara, sam! Ta kasa bacci, sai juyi take
47
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
damuwarta ta hanata bacci da bakin ciki, tuni Rafi'atu
tayi baccinta har tana nasari.
Imran shi kadai ya zama matsalarta da babu shi tana
jin bata da damuwa, duk shi ya kunna wannan fitinar, da
bai ce yana sonta ba hankalinta kwance.
Ya zama kadangaren bakin tulu, yanda Momy ke
sonshi da alama ba ta sonta haka, tunda ta zabi farin
cikinsa a kan nata. Yanzu in ban da don ya kona mata rai
meye na wani kirkirar party?
Bayan ba shi da tabbacin shi ne angon. Me yasa bai
hana su ba ya nuna ba ya so? Yana son ta ba shi kunya
kenan?" zuciyarta ta bata shawara, don haka bata yi
tunanin komai ba ta diro daga gadon ta fice