daga dakin.
Dakinshi ta tunkara sha biyu ta gota, kofar a bude
take tana ta6a handle din ta bude.
Bai samu ya yi bacci ba a lokacin yana dauke da iPad
suna magana da wani abokinsa ta social network daga
kasar Saudiyya.
Kwatsam! Yaga ta shigo masa, abin ya ba shi
48
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
mamaki matuka, yarinyar da ta tsane shi ko kallonsa ba
ta yi, to me ya kawo ta dakinsa a wannan lokacin?
Daga shi sai shortniker ba ko singileti. Ya yi saurin
mikewa yana cewa, "Subhanallah! Mabaruka lafiyarki
ki ka shigo min daki babu sallama?" Ya jawo
jallabiyarsa ya saka don kare mutuncinsa.
Ya ci gaba "Ba kya tunanin a ya za ki same ni wanda
ba zia miki dadi ba?"
Ta zumburo baki daga in da take tsaye jikin kofa ta
ce, "Ni ina ruwana, wannan ba shi ne gabana ba."
Ya yi murmushi ya ce, "Ok! Naji to meye gabanki?"
Tayi mai banza tana turo baki. Ya sake cewa, "Mabaruka
menene?" cikin kulawa.
Ta ce tana kumburi "Magana nake so muyi." Ya ce,
"Da ni kuma?" Ta yi masa banza. Ya sake cewa "Ni
makiyin naki?" Yana murmushinsa mai kyau.
Ta ce cikin fada, "To in ba da kai ba da wa zan yi?
Dakin wa ka ga na shigo?" Ya ce, "Kiyi hakuri to dakina
ne, naga ko muryata ba kya son ji bare ki ce kina son
49
WAYE ANGON?
magana da ni."
Maryam Ja'afar
Ta ce cikin kufula ba tare da ta kalle shi ba. "Ni ba
nazo nan don in ja magana ba da surutai marar ma'ana
ba, kawai nazo ne na taimake ka."
Ya kalleta da kyau ya ce, "Ok, bismillah zo ki zauna
ga kujera."Ya nuna mata kujerar da ke facing din shi. Ta
juyo tana harararsa ta ce, "Ba zama ya kawo ni ba, ka
daina tunanin zan iya zama dakinka."
Ya yi murmushi ya ce, "Maganar ba ta da
muhimmanci kenan tunda a tsaye za a iya yin ta. A
zatona tana da girman da za a girmamata." Yana rufe
baki ta dauka.
"Na gaya maka ban zo nan ba don surutai marar
ma'ana ba, ka saurare ni kawai."
Ya nisa ya ce, "Ok, kin ce ni za ki taimaka, to na gode
kije kawai idan har ba za ki iya zama ba, ba zan iya
saurararki ba kin atsaye ina zaune, kin gane ko?"
Ta harare shi cikin tsananin jin haushinsa har ita zai
wa barazana, don haka ta kulu kawai ta juya fuuu ta fice
50
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
tana cewa "Kai ka sani ba damuwata ba ce." Ta buga
masa kofar ta fice.
Ya bita da kallo cikin tsananin kaunarta, hakan da
tayi burge shi tayi, ya kasa dauke kansa daga kofar
kamar tana gani. Can ya yi ajiyar zuciya ya ce a
bayyane.
"Ya Allah idan har Mabaruka ba alkhairi ba ce gare
ni, in kuma ba za ta taba sona ba kamar yanda nake sonta
na damu da ita, nake tausayinta. Ya Allah ka cire min
sonta kada ka bar aurannan ya yiwu tsakaninmu, ka
zaba min mafi alkhairi ga rayuwata, ita kuma ka bata
wanda take so ya zamo alkairi gare ta."
Ya koma ya jingina jikin gadon ya yi lamo yana jin
zafin sonta na kara zafafa a zuciyarsa, yana kara
yaduwa.
Koda ta shiga dakin ta shige toilet tayi zaune kan
abin kashi ta dinga rizgar kuka, wai me yasa zuciyarta
take mata zafi har haka? Wallahi ba ta sonshi ko kadan,
tsanarsa ce dankare a ranta. Me yasa ba zai kyaleta da
51
1
WAYE ANGON?
Sulaiman dinta ba?
Maryam Ja'afar
Taci kukanta son ranta sai kuma ta koma yi wa kanta
fada, to kukan me ki ke don me ba ki fada masa abin da
ya kai ki ba? Ke fa za ki cutu, ki sauke girman kanki ki
danne tsanar tasa ki roke shi, me yiwuwa ya fahimce ki,
shi kenan ki huta da kuda.
Amman in ba haka ba ki kai wasa aka daura aurenki
da shi.za ki mutu da bakin ciki, kullum za ki dawwama
da kuka kina ganinsa kina kara tsanarsa da takaicin
zama da shi, wai a matsayinshi na mijinki.
Ai kuwa tazo wuya, ba za ta taba yarda tayi rayuwa
da makiyinta ba ya nakasa mata rayuwa ba. Lokacinta
na kurewa, daga yau ba wata damar, gwanda taje kawai
ta ceci rayuwarta.
Don haka ta nutsu da hakan ta mike ta kara ficewa ta
tunkari dakinshi. Har za ta tura ta shiga sai kuma ta tuna
yanda ta tarar da shi dazun.
Don haka sai ta fara knocking har ya kwanta amman
bacci bai dauke shi ba, ya ji ana bugawa. Ya tambaya
52
د
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
"Waye?" don sam ranshi bai kawo za ta dawo ba, yasan
halinta. Ta yi shiru kamar ba da ita yake ba.
Ya kara tambaya. Cikin masifa ta ce, "Ka zo ka bude
sai ka gani." Jin ita ce yasa ya mike ya nufo kofar, ya
murza key ya bude.
Ya ce, ,"Menene kuma?" Tayi masa banza tana
kumburi, ganin ba ta da niyyar ba shi amsa kuma ta ki
shigowa yasa ya ce, "To shigo." Ta shigo din ta jingina
da bango har da harde hannuwa a kirji.
Ya bar kofar bude ya tsaya gabanta ya ce, "Menene
wai?" Ta ce a kufule, "Na ce zan yi magana da kai." Ya
nuna mata kujerar again, ya ce "Toje ki zauna."
Ta dago ta harare shi ta kuma kauda kai don bata iya
jurar kallonsa saboda kiyayyarsa, tsawon dakiku.
Ya ce, "Mabaruka!" Tayi shiru, ya kuma cewa "Wai
me ke damunki ba ki jin magana ko?" Ta zumburo baki
tana gunguni. Ya ce, "Na ce kije ki zauna muyi maganar,
ina son na kwanta dare yana yi fa."
Ta ce, "Ni ba zan zauna ba." Ya ce, "Ok, to zo ki tafi
53
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
mun yi maganar gobe." Taki tafiyar. Ya dubeta da kyau
ya ce, "Mabaruka!" Ta amsa cikin makoshi. Ya ce, "Ме
ke damunki?" Tayi shiru, ya ce "Kije ki zauna muyi
maganar to."Ta ki ko da motsawa.
Ganin za ta bata masa lokaci yasa ya janyo hannunta
har gaban kujerar ya zaunar da ita. Tana zama ta mike
tsaye, ya kara zaunar da ita ta sake mikewa tana turo
baki.
Ya dubeta cikin ido ya ce, “Kin iya kafiya ko?" Tayi
masa banza. Ya saki hannunta ya ce, "Ok, mike din
tunda kin raina ni ba ki jin magana."Ya koma ya zauna
kan gadon ya yi shiru, ransa ya 6ace amman babu
alamar yaji haushi.
Ba tun-yau take tare da shi ba, ta san shi sosai tasan
halinsa lokacinta da yake mutuminta abokinta kan ya ce
yana sonta ya zama makiyinta.
Ransa zai 6ace a zuciyarsa amma saboda hakurinsa
ba za ka gani ba a fuskarsa. Sai in ya kai iyaka za ka gani
a idonsa su sauya launi zuwaja.
54
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Don haka ta fahimci ya yi fushi ne, don haka a
sanyaye ta koma ta zauna din. Bai ce komai ba dai ya yi
shiru.
Ganin hakanne yasa ta ce, "Daman um daman..." ta
kasa fada.
Ya dubeta cikin kulawa ya ce, "Fadi mana, kar kiji
komai zna suarare ki na kuma yi miki kyakkyawar
".fahimta י,
Don haka ta ce a marairaice, idanunta sun kada, ta ce
"Wallahi ban taßa sonka ba, ba na sonka, kai ne namijin
da nafi tsana a rayuwata..."
Kai maganganun sun masa zafi da nauyi a rai, tamkar
ta fesa masa wuta ya ji, duk da ba yau ta fara fada masa
ba amman duk sanda zata nanata sai ya ji yafi sanda ta
fada a baya zafi.
Murmushi ya yi a fili ya dubeta ya ce, "Na sani
Mabaruka." Taci gaba "To me yasa ka nace sai ka aure ni
bayan ka san ba na sonka ko ka aure ni haka zan
dawwama za ka cutar da ni ka tauye ni? Kaima ba za ka
55
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
yi farin ciki da aurena ba, bare ka samu nutsuwar da
ango yake smau in ya yi aure.
Kaga da ni da kai zamu yi rayuwa cikin kunci da
hakuri da juna tun da kuruciyarmu mu gagara moreta.
Amma idan kayi hakuri da ni sai Allah ya sauya
maka, ya baka wacce ta fini, wacce za ku yi rayuwa ta
farin ciki da ita, ni ma in auri wanda nake so in yi
walwalata da nishadina da shi a kan mu kasance da juna
ba cikin farin ciki da walwala ba, mu rasa samun
nutsuwar da ma'aurata ke samu.
Auren tursasawa ba shi da dadi Imran, sai bacin rai
da takaici." Ta saurara tana sauraron me zai ce.
Ya numfasa ya ce, "Mabaruka kenan, maganarki
gaskiya ne tabbas! Amman abin da nake son ki.sani,
wannan-son da ki ka ga ina miki ba ni na sa ma kaina ba,
Allah ne ya sa min shi, da zan iya cire shi wallahi da tuni
ya dade da fita a raina, tun kan lokacin nan don na sami
sauki kema na barki ki huta..."
Ta katse shi cikin fada. "Kaso hakanne, tun yaushe
56
WAYE ANGON?
za ka cire shi in ka sa wa ranka?"
Maryam Ja'afar
Shi ma ya ce "To naji, ke me yasa ba ki cire tsanar
tawa ba ki ka sa son nawa in har ni zan iya cire sonki?"
Tayi shiru tana harararsa.
Ya ci gaba “Wannan ba shi ne abin da yasa na nace da
auranki ba, illa dalilina daya. Tabbas! Ina sonki amma ni
ma ta wani 6angaren zai iya zama tursasawa daga
mahaifina kamar yanda mahaifiyarki ta tursasa ki.
Da zan fada miki yanda muka yi da shi me yiwuwa
da kin fahimce ni, amman akwai abu daya da zan miki,
Momy ita ta haife ki nasan za ta fahimce ki, kije ki same
ta ki fada mata ra'ayinki a kaina, ki ce ma ni na turo ki.
Idan ta amince ta janye aurenmu to wallahi nayi miki
alkawarin na janye na hakura, gwanda na mutu da sonki, nayi miki wannan alkawarin."
Ta marairaice kamar zata yi kuka ta ce, "Wallahi na
gwada haka amman ta ki yarda, nayi mata kuka na
roketa, na nuna mata amman ta ki fahimtata, tayi
rantsuwa sai na aureka, tunda naje ni kai sai ka gwada
57
WAYE ANGON?
mu gani."
Maryam Ja'afar
Ya kalleta ya yi murmushi ya ce, "Ba zan iya ba
Mabaruka, hakan yana daga cikin alkawarin da nayi wa
mahaifina, ba zan iya karyawa ba."
Ba juyin duniyar da bata yi da shi ba amman ya nace
a kan alkawarinsa, har biyu na dare suna abu daya, tayi
masa kuka ta durkusa gabansa tana rokonsa.
Hankalinsa ya tashi, ya tada ta shi ma ya bata hakuri
ba zai iya ba, amman taje ta gayawa Allah shi ma zai yi
addu'ar ya zaba musu abin da zai fi zama alkairi kafin
jibi.
Mikewa tayi a fusace ta harare shi son ranta, sannan
ta wuce. Har taje bakin kofa ta juyo tana kallonsa.
Ta ce, "Shawarar da zan ba ka, kada ka yarda a hada
wannan partyn da za ku yi, don ba zan je ba wallahi. Idan
kuma a ka tursasa ni naje, na rantse za ka sha kunya
gaban mutanenka da abokanka, sai kayi kuka wallahi!"
Daga haka ta doka masa kofa ta fice a fusace.
Yaja ajiyar zuciya ya ce, "Na bar maka komai a
58
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
hannunka Ya Allah, ka kawo min agaji da mafita." Daga
haka ya mike ya shiga bandaki ya dauro alwala ya zo ya
shimfida darduma yana kai kukansa ga Allah.
IMRAN KENAN.
Yayin da ita kuma ta koma dakinta tana tafe tana
bala'i, "Wallahi za ka gani, ba ka san wacece ni ba, za ka
sha mamaki in halinka kafiya."
Bacci dai ba ta yi ba a ranar, haka ta kwana tana juyejuye tana doka tsaki, tsanarsa tana kara ruruwa a ranta.
Yayin da shi tunda ya gayawa Allah ya sami
nutsuwa, nan da nan bacci ya kama idonsa, a nan ya
6ingire har asuba.
Washegari ana gobe daurin aure a gidan su Sulaiman
tunda safe karfe bakwai ya fito ya shiga dakin Inna
(mahaifiyarsa) tana zaune tsakiyar daki tana daura suga
a leda na sayarwarta.
Ya tsugunna yana gaisheta, ta bishi da kallo ta ce,
"Sulaimanu ina za ka haka tun da safe?"
59
1
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ya ce yana mikewa, "Wallahi ina da uzururruka yau
kasancewar gobe daurin aure, shi ne nake ta sauri naje
na aiwatar kar ranar ta min kadan."
Ta tabe baki ta ce, "Um, sai ka ce kanka aka fara aure,
sai rawar jiki ka ke na rasa dalilin rawar kafar nan da ka
ke wa yarinyar nan, kai ba auren farko ba bare ka ce ba
ka taba yi ba."
Ya yi murmushi yana sosa keya a kagarce yake ya
fice kar ta hana shi fita, duk yanda yake kokarin boye
dokinsa sai da ta gano.
Ta ce, "Ko kokon ba za ka tsaya ka sha ba? Ga shi can
Sameera ta dama." Ya ce, "Inna sauri fa nake kin.." ta
katse shi "Yau naji ikon Allah! Yau aure zai hanaka shan
koko Sulaimanu? Wai wannan wace yarinya ce za ka
auro mana?"
Ya yi shiru tamkar saman kaya yake, a tsorace ta ce,
"To zauna sai ka sha sannan ka tafi, so ka ke kaje ka
fadi?" Ya sani ba shi da ikon cewa uffan a kan abin da ta
zartar.
60
WAYE ANGON? 1Maryam Ja'afar
Ya ji kamar ya yi kuka şaboda takaicin tsare shi da
tayi, da tuni ya yi nisa da tafiya. Kuma bai isa ya tafi ba
ba tare da ta sani ba, dole sai ya ce zai fita.
Ta ce, "Za ka zauna ko sai na mike nima?" Ba shiri ya
koma ya zauna, sam ba yunwa yake ji ba, dokin da yake
ma bai bar shi ya ji yunwar ba.
Ta kwalawa Samira kira, budurwa ce kanwarsa ta
shigo tana gyara daura zani, kanta ba dankwali sai gashi
da ya tashi buzuzu, ta ce "Gani Inna." Ta ce, "Zubo
mishi kokon da dumamen.” Ta се, "То." Тa fice tana
kwalkwalar tasona.
Shan koko da cin fumame dole ne farilla sai ya ci shi
sannan ya tafi duk in da za shi, duk da yana da mata bata
yarda yaci na matar ba sai dai nata.
Sai dai ya ci wancan a 6oye, sannan ka'idarta ba a
mata sauran abinci in ta zubo maka dole sai ka cinye shi.
Ta dawo dauke da kofi na roba cike da kokon, sai
kwanon dumamen tuwo miyar kuka shar sai kwandalakwandalan waken da ka ke hangowa, da ganin shi bai
61
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
dahu ba, guda-gudanshi yake. Ta ajiye a gabansa ta fice.
Haka ya ci gaba da karyo tuwonnan yana ci saboda
dan banzan taurinsa kamar ya fasa ihu. Sai da ya tura
tuwonnan duka tumbinsa, ya wanko hannu ya dawo
yana cewa, "Nina tafi."
Ta ce, "Ina kayi kenan?" Yayi jim! Sannan ya ce,
“Akwai wasu abokaina da zamu hadu da su to can nayi."
Ta ce, "To jeka Allah ya tsare." Ya ce, "Amin." Har yana
hardewa wajen sa takalmi, kar ta kara tsayar da shi.
Har ya wuce ta kira shi ya ji kamar ya runtuma kar ya
dawo, ya dai daure ya dawo din. Ta ce, "In ka fita ka ce
wa Saddiku mai shago in yaga yara da kwanon siyen
יי koko ya turo su."
Ya ce, "Koko kuma Inna? Ana bikin ba za ki hakura
ba?" Ta dago da bala'inta ta ce, "Ka ji min dan iskan
yaro, auranka din banza zai hana ni neman kudi, za ka
ba ni ne?"
Ya yi saurin cewa, "A'a yi hakuri.” Daga haka ya
juya. Ta ce, “Kai zo nan.” Ya juyo ta ce, "To in gaya
62
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
maka ko ranar da aka kawota sai nayi ba fashi ka ji ko?"
to."
Ya ce, Naji sosai Allah ba da sa'a." Ta ce, "Amin, jeka
Ya juya har ya kai zaure ta kara kwala masa kira. Ya
dafe kai "Oh ni Sulaiman! Na shiga uku." Ta kara dago
murya, "Sulaimanu kana jina kayi shiru ko nasan ba ka
isa ficewa ba."
Ya juyo dole yana kumburi. Ta dube shi da kyau ta
ce, "Wai saurin me ka ke ne, in fa kayi wasa wallahi za a
daga bikinnan." Ya zaro ido "Dagawa kuma Inna?"
Ta ce, "Eh! Ko ban isa ba? Sai a fasa ma gabadaya."
Ya yi saurin cewa "Kin isa mana sosai, ayi hakuri." Tayi
kwafa ta ce, "Jeka to Allah ya tsare, ka duba in mai
kosan nan ta fito."
Ya ce, "To." Da sauri ya wuce. Ta dago murya "Kar
ka yi dare fa." Shi ma ya dago "To an gama Inna." Da
gudu ya karasa fita. Ya saki ajiyar zuciya da dafe kirji.
“Wai, Allah ya fito da ni! Inna jaraba." Bai saurari ya
duba mai kosan ba, don ba dawowa zai yi ya gaya mata
63
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar.
ba abin da ya gani. Ya tare mashin ya bar unguwar zuwa
hidimominsa.
Koda suka tashi ita da Rafi'a, tun sannan mai gyaran
jikin da aka dauko ta fara aikinta, in da ta hau darzar
mata jiki tana yi tana zo6ara baki da musu.
Idan mai gyaran ta ce tayi haka ta ce a'a, ita ga yanda
za ta yi. Abin ya kai matar bango ta ce, "Shin ke wace
irin yarinya ce da kafiyar tsiya? Na ce haka kin ce haka,
a gyara ki ne ba kya so ba ki ga kuďaden da Mamanki ta
kashe ba a kan gyarannan?”
Ta turo baki ta ce, "Yo ina ruwana." Rafi'atu ta ce,
יי
"Don Allah kiyi hakuri kar ki ga laifinta."
Ta dube ta ta ce, "In tambaye ki don Allah?" Ta се,
"Ina jin ki."Ta ce, "Amman auren dole za a yi mata ko?"
Ta kasa bata amsa, sai dai Mabarukan ta ce "Kwarai
kuwa, auren dole auren maza biyu kuma."
Mai gyara ta kasa fahimta. Rafi'ar ita ta mata bayani,
abin ya bata mamaki matuka, ta dubi Mabarukar ta ce,
f
64.
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
"Eh lallai kam dole kyayi kumbure-kumbure, Allah ya
sawake."
A dakin da suke kusa da na Imran ne, ya shiryo tsaf
cikin dogayen kaya farare sol yasha hula da farin glass,
ya zauna a saman dogon hancinsa.
Haka kuma ya yi wa kyakkyawar fuskarsa kyau, mai
haske. Dakin bude yake suka yi ido biyu da ita lokacin
da yake tsaye a falo suna magana da Momy.
Tayi masa kyau sosai, ya saki fuska yana mata
murmushi, ya yi mata alama da "kin yi kyau" daga can ta
gallo masa harara tasa kafa ta banko kofar ta rufe.
Ya yi dariya abinsa ya wuce. Motarsa tayi ready
wanke an goge, ya shiga ya zauna ya turo mata text.
an
Kin yi kyau my light, you will receive millions kiss
from me, Insha'Allah.
Urs husband,
Imran Umar.
Ya yi dariya yaja motarsa, Maigadi ya bude masa
Gate ya fice.
65
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Lokacin da taji shigowar text a wayarta ta jawo ta
duba ta karanta, ta ce "Allah ya isa, mugu!" Idanunta
suka ciko da kwalla.
Suka juyo suna kallonta ita da Rafi'a, ta ce "Menene?
Ke da wa?" Hararar Rafi'ar tayi. Suka gaji suka kyaleta.
Karfe hudu tuni an gama gyarata, tayi wani irin
kyau. Daman ga ta fara ta kara rikidewa kamar ba ita ba,
jikinta har santsi yake, ga lallan da aka zuba mata ya yi
wa farar kafarta kyau a kai mata kwalliya.
A ka bata kayan da Imran din ya aiko mata bayan
fitarsa, wanda zata sa suyi anko a nan aka dinga rigima
da ita ta ce wallahi ba za ta sa ba, har Momy tazo.
Ta ce, "Ba za ki sa kayan ba saboda me?" Kai tsaye ta
ce, "Ba zan je ba ne." ta ce, "Saboda wane dalilin
kenan?"ta ce, "Don ba na sonsa, ba na son abin da zai
hada ni da shi."
Ran Momy ya baci, ta fidda hannu ta mareta ta ci
gaba da fada.
"Uban wa ya haife ki? Ke ki ka haifi kanki da ki ke
66
د
WAYE ANGON? na fada kina fada? Kina gaya Milvaaga
son ranki? Wa yake da alhalin zaba miki miji?
Cutarki a kai aka hada ki da dan iska bare ki min
rashin kunya? Kin fi ni hankali ne?" Ta saurara.
Yayin da ita kuma take cizgar kuka kamar ranta zai
fita. Momy ta ci gaba.
"To don ubanki kar ki sa kar kuma kije, idan naji
labarin kinje sai na taka miki wuya, kici gaba da mishi
rashin kunya." Daga haka ta fice mutane na ta ba ta
hakuri.
Ita kuma ta ci gaba da kuka kamar ba za ta daina ba.
Rafi'atu ita ke rarrashinta, amman ta ki sauraron kowa
bare ta bari sai don kanta, idanunta suka yi ja sun
kumbura sannan ta bari, ciwon kai ya dameta.
Rafi'atu ta ce, "Kinga ran Momy ya baci har ta kai ga
taba ki, kin fiye kafiya Mabaruka, ki mata abin da take
so zuwa party ba zuwa gidan Imran ba ne, kije awa daya
ya yi yawa ki dawo sai ki samu sauki daga fushi.
Don wallahi tayi fushi sosai, ga mutane suna taruwa
67
WAYE ANGON?
WA
Ċ
S
Maryam Ja'afar
ana kallon kuna sa'insa da mahaifiyarki kina gaya mata
magana son ranki, wanda ba tarbiyya ba ce sai a tafi ana
yi da ke.
Kiyi hakuri don Allah Mabaruka kar ki bata kunya,
kar a daura miki aure tana fushi da ke, kiyi kokari ku
rabu lafiya tana sa miki albarka."
Ta ci gaba da share mata hawayen, da kanta ta dauko
kayan tasa tana yi tana turo baki a ka sake mata kwalliya.
Masha Allah kowa yake cewa, tayi kyau fiye da
tunanin mai tunani, tamkar ba ita ba, kayan sun mata
cas! Kamar an gwadata.
Less ne hadin fari da pink riga fara sikyat pink sai
gwaggwaro pink tayi cas! Sai walainiya take cikinsu an
zubo da gashin gefe guda ga sarka wacce ta dace da
kayan, agogo zuwa 'yan hannu.
Aka dinga daukarta hoto duk da ba fara'a a fuskar sai
zumbura baki da harare-harare, ji take kamar tasa kaya
jikinta saboda amfani da tayi da kayan makiyinta.
Tasan kudinshi yasa ya siyo tabbas hannunsa sun
68
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
taba kayan. Zuciyarta ta dinga tashi ta dinga yatsineyatsine tana tara miyau.
Abin mamaki kawayansu suka ga suna ta tururuwar
zuwa sun cika dakinta kowaccensu tasha kwalliya,
akwai masu shirin kwana ma kowa in tazo da tsegumi
wai a ce ba a gayyace ta ba.
Rafi'ar ke cewa da ba za a yi komai ba suma sai yau
suka sani, haka dai kawaye suka yi dandazo, wasu har
kan gado.
Kowa sai da suka yi hoto da ita daga wayoyinsu, still
dai fuskarta ba walwala. Sai suke tsokanarta ta fara
kukan aure ne?
Ba a sami tafiya ba sai bayan sallar Magriba, sannan
a ka zo aka dinga daukar kawaye da wasu iyayen zuwa
tsararren hotel din da a ka tsara aka yi kwalliya da kalar
kayan ango da amarya,
Duhu ya fara sanda za a dauke ta aka tsayar da motar
gabanta har wani walainiya motar take da ganinta
sabuwa ce dal.
69
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Aka ce ta shiga, to da duhu ba ta san akwai wani ciki
ba, da shigarta ta ji ta ta fada jikin wani abu mai laushi,
zata yi ihuya yi saurin sa hannu ya dode mata baki, dole
tayi shiru tà kasa kwatar kanta.
Ya kunna hasken wayarshi ta haske mishi fuska,
kawai taga Imran ne. Ta fiddo idanu tana kallonsa cikin
tsananin haushi da takaici, ta ci gaba da harararsa.
Yayin da shi yake dariya ya yi kyau cikin irin
kayanta, kamshinsa yana dokar mata hanci, ta yunkura
zata kwace kanta ya riketa gam!
Ta harare shi ta ce, "Sake ni."Ya ki, ta kakalo miyau
(yawu) ta tofa masa a fuska, tare da cewa "Allah ya isa."
Ba shiri ya sake ta, yasa hannu ya shafo miyan. Ya yi
murmushi ya kalleta da take harararsa ya ce, "See."
Kawai taga ya lashe shi ya kara gogo wani ya lashe shi.
Sannan ya ciro handkchief daga aljihunsa ya goge
fuskarsa. Yasa a hancinsa ya shake shi har da lumshe
idanuwa. Ya bude yana kallonta ita ma duk tana
kallonsa.
70
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ya ce, "I will keep it, ba zan taba wanke shi ba nayi
miki alkawari, don in dinga shakar kamshinsa ina jin
dadithanks." Ya maida aljihu. Ta kauda kanta tare da jan
tsaki.
Rafi'a ta shiga gaba direban daya daga cikin
abokansa yaja motar suka yi gaba.
Ta koma jikin kofa ta rabe, bata son jikinsa ya hadu
da nata, gefe kuma tana jin wani takaicin yanda jikinsu
ya gogu har ya ta6a ta, ta ci gaba da yin Allah ya isa a
ranta har suka isa.
Suka fiffito, suka tsaya aka sa kawayanta gaba don
suyi mata rakiya zuwa wajen zamansu, wasu kuma
bayansu aka saka su tsakiya ita da shi.
Sunyi kyau matuka, in ka gansu zaka ce wallahi babu
masoyan da suka dace da juna irinsu, abin ya burge
mutane sosai, aka ci gaba da daukar su hotuna zuwa
bidiyo.
Aka ce su kamo hannun juna su shigo hall din. Ta
juyo ta harare shi ta ce, "Wallahi ka kuskura ka taba ni
a
71
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
sai ranka ya 6aci." Ya yi murmushi ya ce, "Ni ma ba zan
fara ba."
Bayan sun zazzauna aka fara abin da ya tara su.
Abubuwa sun yi kyau matuka, kowa yana yabawa, duk
'da ita amaryartana yin nesa-nesa da angon.
Kamshin turaransu daddada mai tsada dan waje, shi
ya zamar mata kamar tana shakar kwan da kaza ta fara
kwancinsa ya fashe, haka take ji ta koma tana dode
hanci har zuwa lokacin fuskarta babu annuri.
Wasu sun fahimci wani abu, yayin da wasu ba su lura
ba. Amman da mamaki amarya ranar partynta bata fara'a
sai gumtse-gumtse da 'yan harare-harare.
Idan abokansa sun zo suna gaisheta sai taja tsaki ta
kauda kanta, ba wanda take amsawa. Wannan shi ne
kadai abin da tayi ya 6ata masa rai, amman hakuri irin
nasa sai ya share kawai.
Jikin abokansa ya yi sanyi, duk sun fahimci wani abu
game da amaryar tasa.
Lokacin da suka dawo ana tsayawa zata fice ya yi
saurin tsayar da ita ya ce, "Ba za ki min sallama ba?"
72
$
S
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Harararsa ta yi kawai ta fice tana cewa, "Don Allah ka
sakar min mara nayi fitsari, na dai yi abin da ka ke so ko,
to ka kyale ni."Ta fice tare da turo kofar.
Ganin yanda ta fito ne yasa Rafi'atu ta biyo ta.
Da shigarta ta fara yakice kayan tana wurgarwa,
"Tir! Da kayannan, ba zan iya ci gaba da zama da ku
jikina ba."
Rafi'ar ta shigo ta tsaya tana kallonta, daga ita sai
under wear tayi sama da shi, ta ce "Wannan wane irin
hauka ki ke? Ai suma na jikinki din