nashi ne sai ki maida
hankali ki cire su."
Kan ta gama'rufe baki ta yayumi tawul ta wuce bayi
tana cewa "Har wanka sai nayi don na tsarkake jikina
daga kayanshi." Ta banko kofar.
Ta zaune bakin gado tana cewa Allah ya shirya ki
Mabaruka. Ta canja kaya da riga da zani ta kawo hijab
tasa, Rafi'ar ta bi ta da kallo ta ce "Ba ki sallah ba ne?"
Ta ce, "Tafiya zamu yi." Ta wuce tana duba drower ta
ce "Tafiya! ina zamu?" Ta ce, "Gidan Babanmu." Та се
73
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
"Ke ba inda za ni yanzu kin san karfe nawa?" ta се
lokacin da take dagowa.
"Na sani mana, ina son ganin Babanmu yau dinnan
ba sai gobe ba."
Duk naçin Rafi'a sia da ta jata suka tafi.
Baban ya dinga yi mata fada a kan me za ta bar gida
daidai bikinta, ta marairaice fuska ta ce, "Kun sa ni a
tsaka Baba, kai ka ce kaza ita ma can ta ce kaza, wai ya
ku ke so nayi?"
Nan anje an yi jere an karbi sadaki, ita ma can ta
karba. Wai ba kwa tunanin ya abin nan zai kasance
fisabilillah, kar fa ku jawa zuri'arku abin kunya. Ta ya ya
za a daura min aure da maza biyu Baba?"
Ya ce, "Ke ban san maganar banza, ni dai ni ne
ubanki, to don haka ban san wani miji naki ba sai wanda
aka ba ni sadakinki, ban taba ganin inda mace ta daura
wa 'yarta aure ba sai mahaukaciyar uwarki, ko ta daura a
iska ne don ba waliyyinki.
Don haka Sulaiman shi ne mijinki na halaliya, ki bar
دو
zancan Innarki, aurenta ba aure ba ne."
74
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ta ce, "Amman Baba, Baba Haruna shi ne wanda ta
wakilta kuma kaninka ne uba daya uwa daya. Ko a
Musulunci ya daura min aure, aure ya dauru sadakina
tuni yana hannunsa."
Ya dubeta da kyau ya yi shiru, sannan ya ce, "Za mu
riga daura namu kafin nasu, kije kawai ki kwantar da
hankalinki ba ki da miji sai Sulaiman."
Sam bata nutsu ba, jiki a sanyaye ta wuce cikin gida
suka karasa ita da Rafí'a, sai da taji daman ba ta zo ba
saboda cinkoso in da za su kwanta, babu wasu ma sai a
zaure za su kwana an cika dakuna biyun daman a
kuntace suke ba su da girma, haka nan an cika tşakar
gida yara da manya, gidan har wani huci yake fitarwa.
Ta tuno dakinta na gidan Momy za a haďe dakunan
da kucicin tsakar gidan wanda mutum bakwai ba za su
kwanta ba, a hada da zauran shi ne girman dakinta, ga
toilet ciki ga iska mai dadin kamshi na fesowa daga
na'ura.
Ga kuma nau'ikan abincin da sai ta zaßa taci. Ta dafe
kai ta dubi Rafi'a ta ce, "Da na sani ban zo ba, gurin
75
WA WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
1c
b
kwana ma ba mu da shi alhalin ga dakina can ba kowa
cikinsa."
Harararta tayi ta ce, "Ba abin da zan ce, Allah ya
Кara."
Baba Haruna da Baba Hamza duk kannan Babanta
ne, gidansu a jere suke, Baba Haruna shi ne madaurin
aurenta 6angaren Momynta.
Baba Hamza kuma shi ne madaurin aurenta
6angaren Babanta. Don haka taja hannun Rafi'atu zuwa
gidan Baba Hamza.
Shi ma dai gidan akwai jama'a 'yan biki, amman duk
da haka ba su rasan gurin kwana ba, sauro da zafi ya
hanata bacci, duk da ba wai bata jinsa ba ne a'a na yau ya
linka na kullum.
RANARDAURINAURE
Tun da safe Momy ta kira ta ta ce "Kina ina ne?" Ta
ce, "Ina nan gidan Baba Hamza." Ta ce, "Ok, to ki zauna
a nan kar kije ko'ina, da an daura za a dauke ki, kin ji na
gaya miki ko?"
76
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ta turo baki can ciki ta ce "Eh." Ta ce, "In ji kin bar
gidan kuma." Ta kashe.wayar.
Idanunta suka cicciko da kwalla, ta dubi Rafi'a ta cе
"Na shiga uku, da gaske da Imran za a daura min aure,
ba fa na sonshi wallahi ba na sonshi. Ina jin daci a
zuciyata."
Ras ame zata ce tayi, sai dai kallonta kurum da take.
Baba yasa aka kirata, ya bita da kallo "Ina ki ka
kwana ne?" Ta ce, "Gidan Baba Hamza." Ya ce, "Da
66 kyau, to ki koma can ki zauna kada kiyi nisa daga nan.
Ta ce, "To."Kawai.
Tayi wanka da kwalliya ta kawo kayanta ta sa wanda
da kanta ta dinka su don fitar biki, tayi kyau sosai,
sunanta na amarya ya fito.
A nan suka yi zamansu suna cike da zullumi, yayin
da gabanta ke faman dukan tara-tara a kagarce take
ranar nan tayi ta wuce, damuwarta ma ta wuce tasan
matsayinta.
Ranar tayi mata tsawo matuka, ko ya taji motsi sai
77
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
gabanta ya yanke ya fadi, shin wanene ANGON?
** ****
Bangaren Sulaiman kamar kullum, bayan ya gama
shan kokonsa na ka'ida da dumamen tuwon sama-sama,
ya yi bankwana da Inna ta ce, "Ho! Sulaimanu kai dai da
rawar jiki ka ke, na rantse in ba ka rage yawan
zumudinnan ba yau ba in da za ka je."
Ya tsorata ainun, ya ce, "Na bari, na bari Inna." Ta се,
"Ka ci gaba ma." Ya tsugunna gabanta yana jiran
umarninta ya tafi. Kamar kan kaya yake jinsa.
Sai can ta ce, "Tashi ka tafi." Ya rankwafa "Godiya
nake Inna, Allah bar girma." Ba ta ce amin ba ya wuce.
Dakin Nafisa matarsa ya shiga, tana kwance
hannunta rike da waya ya shigo, ta bi shi da kallo tana
murmushi ta ce "Ango-ango kai ne har yanzu ba ka fita
ba, na sha ma ka dade da tafiya."
Ya ce, "Ina fa na tafi, Inna ta rike ni." Ta сe, "To kayi
ka wuce kar ta jiyo ka nan, wallahi na kagara kanwar
78
WAYE ANGON?
nan tazo."
Maryam Ja'afar
Ya dube ta tsaf ya ce, "Wai ke ba kya ma ko kishin
nan irin na sauran mata ki tada hankalinki sai nayi ta
lallashi amman ke ki ke ba da kwarin gwiwa."
Tayi murmushi ta ce, "Yaya kenan, in kaga abin da
ya fito da bera daga rami ya fada wuta ya fi wutar zafi,
don haka ina sonka wallahi sosai, amma yin auranka zai
sani farin ciki.
Wani 6angaren 'yar uwa za a kawo min wacce zamu
hadu mu share hawayen juna, don haka ina murna."
Ya ce, "Da tsiyar da za ku shirya min kenan, kin
sanni kin san waye ni, ki taka sannu."
Tayi dariya ta ce, "Sosai ni na sani, Allah dai ya ba
mu zaman lafiya, ya kawo ta lafiya."Ya ce, "Amin 'yar
Nafisata." Suka yi dariya.
Sameera tazo wucewa taji dariyarsu ta window, da
gudu ta shiga dakin Inna har tana harba takalma, sai dai
ta ganta gabanta.
Ta ce, "Sameera a hankali ki ke wa ya koro ki?" Tana
79
1
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
haki ta ce, "Kina nan sake da baki ya ce miki ya tafi, to
ga shi can dakin matarsa ina jiyo 'yan dararrakinsu,
kin..."
Ai kafin ta karasa ta mike har zani na faduwa ta fice
tana cewa, Dauko min bakin wüta ki gani." Da gudu ta
dauko ta mika mata.
Sai dai kawai suka ganta gabansu, ba jira ta ci gaba
da zuba mishi, ba shiri ya fice ta ci gaba da bala'i.
"Niza ka rainawa wayau, ka ce ka tafi ashe nan ka
laba6o don ka raina ni, me ka ke a nan din?"
Ina! Tuni ya dafe keya, ta dubi Nafeesar ta ce, "Ke
kuma za ki sani munafuka, kin san dadin miji, kin
murkuso shi daki. Sai na ka rya miki kafa." Ta wuce
tana kumfar baki, ta bar dakin.
In da sabo ta saba, ta yi murmushi iya fuska ta ce,
"Lokacinki ya yi za a kawo wacce zata yi maganinki,
insha'Allahu za ki gani." Ta koma tayi kwanciyarta
abinta, hankalinta kwance.
Shin wai waye ma Sulaiman?
80
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Wacce Inna? Meye matsalarta, duk ku min afuwa za
ku ji nan gaba kadan.
Bangaren Imran kuwa Ango, tun safe yake tare da
abokansa su shiga nan su fita, yayin da wasu 'yan
uwansa suka zo daga kasar Saudiyya, wasu kuma daga
England.
Har ya shiga wanka wayarsa ta dinga kuka, ya share
ya ci gaba da wankansa, ganin kiran ya yi yawa ne yasa
ya fito jikinsa da kumfa, ya dauki wayar.
'My little Sharifat' ya gani, ba shiri ya kai kunne yana
dariya.
"Oh sorry my dear, ina wanka ne fa. Yanzu haka
akwai kumfa jikina." Daga can ta bata rai cikin
shagwabar da ta saba yi mishi ta ce, "Ni ban yarda ba tun
yaushe na sauka ina nan airport amman ka share ni ba ka
murna da zuwana ko?"
Ya yi dariya har taji sautinta me dadi ta lumshe
idanuwa saboda jin dadin kasancewa tare da shi.
Ya ce, "Na miki alkawari minti goma ba zan kara ba
81
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
A
zan zo na dauke ki." Tayi dariya "Kada ka damu ka
shirya a nutse yau rana ce mai girma da muhimmanci
gare ka, ba a bukatar gaggawarka.
Kayi kwalliya mai kyau wacce zata rikita mutane,
don ranarka ce kayi kwalliyar da baka taba yi ba, zan jira
ka har lokacin da zaka zo."
Ya ce "Thank my dear, I miss youuu!" Tayi dariya
daga can ta ce, "Me too my dear, I love you." Ta sakar
masa kiss.
Shi ma yạ mayar mata, "Am coming bye!" suka
kashe wayar, wanke kumfar kawai ya yi ya zura
jallabiyajikinsa har rawa yake ya dauki keyn motarsa ya
fice zuwa airport.
Da gudu ta taho da ta hango shi, shi ma cikin doki ya
nufota da zuwa ta fada jikinsa. Shi ma ya rungumeta tare
da yi mata kiss ya dagota yana farin ciki, ya ce "You are
welcome."Tayi dariya bakinta ya kasa rufuwa.
Suka wuce yaja 'yar jakarta zuwa mota, suna tafe
suna hirarsu mai dadi na yaushe gamo da tsananin
3
82
WAYE ANGON?
kewar junansu har suka iso gida.
Maryam Ja'afar
Da gudu ta fito daga motar tayi ciki tana kwalawa
Momy kira.
"Momy! Momy!!" Ita ma daga can ta jiyo muryarta
ta fito cike da murnar ganinta, tana zuwa ta fada jikinta
tana cewa, "Nayi missing naki Momy."
Tayi dariya ta ce, "Ita ma Momynki tayi missing
dinki." Tana rawar jiki take cewa "Ina Anti Amarya
matar yayana?" Ta ce, "Ba ta nan kuwa tana gidan
Babanta." Tayi sukut tare da cewa "Kai Momy, me yasa
ba ki fada mata zan zo ba?"
Ta ce, "Kiyi hakuri yanzu sai Yayanki ya kai ki can
ba abin damuwa ba ne."
Suka zauna tana cewa, "Momy ya hidimar duk kin
fada, mutane ko?" Ta ce, "Ke dai bari Sharifa, sai a
hankali. Hidima ba abu na wasa ba ne."
Ta ce, "Ayya Momy, sorry za ki warware big bro ya
wahalar mana da ke.Daddyna fa?"
Ta ce, "Yana hanya, yanzu zai suaka." Ta ce, "Daga
83
1
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
ina?" Ta ce, "America." Ta ce, "Oh Daddy dai tafiyetafiye yake ana bikin big bro ma?"
"To ya za a yi, shi ma bai so ba dole ce tasa yaje din."
In ji Momy. Sharifat ta ce, "Allah Sarki Daddy, Allah
sauke ka lafiya."
Tun karfe daya da rabi 'yan daurin aure suka fara
taruwa ta kowane 6angare, gidan Baba Haruna makil da
Jama'a, hatta angwaye sun zo.
Turawa da Larabawa da 'yan Najeriya waje babu
masaka tsinke, Maroka sai kewaye-kewaye suke da
Mabusa, suna ta kara yayada "Za a daura auren Imrana
Umar yare da Amaryarsa Mabaruka Yusufa, a kan
Sadaki Naira dubu dari lakadan."
'Yan cikin Mabarukar suka juya, zufa ta karyo mata
tamkar an watsa mata bokiti na ruwa, jikinta ya hau
rawa. Ta rike Rafi'a gam tana mata wani tsorataccen
kallo.
Ta ce, "Na shiga uku! Rafi'a za a daura ba da
Sulaiman dina ba, ya haka? Me yasa za a riga daura
6
84
도
WAYE ANGON?
wannan auren? Biyu saura fa yanzu?"
Maryam Ja'afar
Rafi'ar ta kasa cewa komai, hankalinta ita ma ya
kada matuka.
Ganin taruwar mutanen dandazo guda, duk an
halarta ba wanda ake jira sai kawai aka bada sanarwar a
daura kawai tunda kowa yazo, saboda haka aka fara
addu'a.
Runtumawa tayi a guje zata fice, Rafi'atu da sauran
kawayenta suka rukota, cewa take "Na shiga uku! Na
shiga uku!! Za a daura za su daura min aure da
makiyina, ku bar ni naje na hana su kar suyi."
Ta dinga fizge-fizge kamar sabuwar hauka. In ta
kwace ta bige wannan sai wannan ya rikota, duk ta bi
birkice, gashi ya tashi buzuzu ta dinga ihu kamar zata
shide.
Baba yana Masallaci sallar azahar, yayin da Jama'ar
Sulaiman sun fara taruwa ango yana kan hanya da
waliyyansa.
Abu kamar wasa Limamai suka daure Mabaruka a
85
1
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Karkashin kafar Imran, ci sha sutura wajen zama ya
koma wuyan sa, sai da amincewarsa zata fita komai in
zata yi sai ya amince, ta zama halaliyarsa ta zama tashi.
Kamar daga sama taji ana cewa "An daura auren
Imrana da Mabaruka a kan Sadaki dubu dari lakadan ba
ajalan ba, ya biya."
Da taha wani dogon numfashi kan ta sauke sai dai ta
fadi nan sumammiya.
Koda waliyyan Sulaiman suka zo ba 6ata lokaci suka
daura aurenshi shima tare da Mabaruka.
A takaice dai an daura auren a tare lokaci daya, nan
fa abu ya zama surutu, hayaniya tayi yawa, mutane
sukai dandanzo al'ajabi da mamaki da tir da wannan
zuri'a ake yaushe ake haka?
Shin Musulmai ne kuwa? Nan fa aka yi yuu kowa na
tsegumi aka dinga tururuwar ganin Baban amaryar da
angwayen.
Nan da nan 'yan Jarida suka bayyana, masu dauka
suka ci gaba da yi. Sun yi nasarar ganin Babanta, sun zo
86
க
WAYE ANGON?
suji ta bakinsa inda suke cewa.
Maryam Ja'afar
"Baba ya aka yi wannan abu ya kasance ka daura
auren'yarka ga maza biyu?"
Ya ce, "Ni ne mahaifin Mabaruka, kuma ni sadakin
mutum daya na karba, shi ne Sulaiman kuma da shi na
daura mata aure a matsayina na ubanta.
Ban san wani ba can. Wannan shi ne abin da zan iya
cewa kawai." Suka koma 6angaren Ango.
"Ya sunanka Malam?"
Ya ce yana gyara malum-malum (babbar riga)
"Sunana Sulaiman."
Syuka ce, "Shin ko ka san ku biyu a ka daurawa aure
da matar da ka aura?"
Ya ce, "Eh na sani." Suka ce "To me za ka ce?" Ya ce,
"Abin da na sani ni ne angon ban san wani ba, kuma zan
dauki amaryata nan ba da jimawa ba, saboda Babanta
shi ne ya daura min aure da ita, shi na ba sadakina kawai
nasan ni ne angon."
Suka koma 6angaren Imran.
87
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
"Alhaji Imran me za ka ce game da wannan auren, ko
ka san ku biyu ku ka auri matar da aka daura aure?"
Ya yi murmushi tare da gyara tsayuwa ya ce, "Yes, na
sani." Suka će "To me za ka ce?" Ya ce, "Nothing to say,
ni dai nasan ni ne Angon." Sun yi-sun yi da shi ya kara
cęwa-wani abu amman ya nace a kan hakan.
Kun san 'yan Jarida da shige-shige, sai da suka
kwakulo gidan Mamanta shi ma cike yake dam da
mutane, hankula ya tashi lokacin da suke tambayarta ya
akai haka ta kasance?
Ta ce, "Ni Imran shi na san na ba 'yata kuma na karbi
sadakinta, Babanta kanin mahaifinta shi ne ya daura
mata auren, sadakinta na hannunshi."
Suka ce, "To amman kun san hakan babban sabo ne
da abin tir da tozarci gare ku?"
Ta ce, "Ni ban san wani ba, Imran shi ne mijin 'yata
da shi a ka daura." Abin da ta iya cewa kenan.
Sun so suga Amarya amman amarya na can a birkice
sai ihu take tana tirje-tirje, bayan farfadowarta. Don
88
WAYE ANGON?
haka ba su sami ganinta ba.
Maryam Ja'afar
Rafi'atu ta ce, "Wai Mabaruka ba za ki nutsu ba,
wannan haukan shi ne mafita gare ki?"
Tana kukan ta ce, "Ai gashi nan abin da nake fada
miki da gaske suke sun daura min aure da maza biyu,
kina kallon dandazon mutane ana zuwa kallo da 'yan
Jaridu, duk duniya sai taji, shi kenan ni sun tozarta
rayuwata sun wulakanta ni."Ta ci gaba da kukan.
Mutane yawansu kamar ana arfa a wannan layin har
dare ana abu daya, a ka zo daukar amarya, 'yan biko
suka zo daga gidan su Sulaiman.
Baban da kansa ya shigo inda Mabarukan take har ta
gaji da kukan, sai ajiyar zuciya. Ya riko hannunta har
bakin mota, ya dubeta da kyau ya ce, "Mabaruka!"
Ta ce, "Na'am Baba!" Ya ce, "Ni waye gare ki?" Ta
ce, "Mahaifina." Ya ce "To na aura miki Sulaiman, kije
gidanshi kiyi zaman aure, kin ji ko?"
Та се, "Тo Baba."Ya ce, "Allah yai miki albarka."Ta
ce, "Amin Baba." Ya sata motar angwayen, kawayen
89
ل
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
amarya da 'yan biko duk suka shisshiga suka wuce.
Suna fita kan layin sai ga su Imran da abokanansa
'yan daukar amarya, aka ce musu ai an zo an dauki
amarya. Da gudu suka yi ribas suka take musu baya, ba
su sami cimma su ba har sai da suka isa kofar gidan
Sulaiman din, wato gidan Inna.
Suka fiffito aka fito da amarya, Imran din da kansa
ya tare wadanda suka riko amaryar ya dube su ya ce,
"Ina za ku kai min mata, bayan ni ne Angon amaryata
ce?"
Suka bibbishi da kallo, yasa hannu ya jawo ta, ya ce
“Ni ne Angon ba gidan da zata je sai gidana." Sulaiman
ya hango abin da ke faruwa.
Da gudu ya iso ranshi a 6ace ya ce, "Mallam lafiya za
ka rike min mata? Ni ne Angon ta." Yasa hannu ya riko
ta shi ma.
Ran Imran din ya baci matuka, kishi ya turnike shi.A
kan me zai rike mishi mata? Idanunsa suka kada jajir ya
90
WAYE ANGON?
ce, "Sakar min mata ni ne Angon.”
Maryam Ja'afar
Shi ma Sulaiman din yana rike da ita ya ce cikin
tsawa, har jijiyar wuya na fitowa, ya ce "Karya ka ke ni
ne Angon." Suka fara janta wannan yaja wannan yaja,
kamar za su cira ta.
Yayin da ita ke kuka wannan ya jata wannan yajata
mutane suka taru suka rasa me za suyi, kowa dai kan
gaskiyarsa yake.
Tsawon mintoci suna haka, kowa ya nace shi ba zai
sake ta ba tashi ce. 'Yan bikon Imran iyayansa, daga ciki
har da Sharifat ganin abin ba zai kare ba tazo ta dube shi
ta ce, "Sakar mana mata, kowa yasan mu muka aure ta
ba kai ba."
Haushi ya turnike Sulaiman din yazo iya wuya, ya
daddage iya karfinsa ya kai mata naushi a baki.
Idanuwan Imran ya fito ya dubeta da ta duke baki fashe
jini na zuba idanunta sun kadajajir, ai shi ma sai ya nade
hannun riga ya kai masa naushin a baki.
Kan kace me tuni dambe ya kaure tsakaninsu, ji ka ke
91
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
tim! tim! suka dinga nausar junansu, nan da nan jini ya
bayyanajikinsu.
Ganin sun kaure da fada yasa 'yan bikon Sulaiman
suka jata za su shige da ita gida, 'yan bikon Imran suka
gani suka yo kansu. Nan ma abu ya rincabe tsakaninsu,
wannan ta daki wannan wannan ta daki wannan.
Sai ga jini suma yayin da abokan ango suma tsakanin
na Sulaiman da Imran suka kaure, ji ka ke tim-tim sai su
kuma mata dum-dum dudum!
Ma su dundu kenan da ma su cizo, su kuma
angwayen tuni sun buda fili dambe suke ba ji ba gani.
'Yan uwa suka yo kansu, yawan mutanen ya gagara a
raba su saboda sun fi 'yan rabon yawa nesa ba kusa ba.
Amarya ko ta koma gefe tana rusar kuka, ta rasa me
zata yi. Sai dai ta kalli wancan group din sai ta kalli
wadancan. Sharifa ta hango ta, don haka da gudu tayo
kanta zata turata mota, habawa ita ma ta dafe keya ta
shige gidan Inna.
Jin hayaniya kofar gida yasa Inna ta dauko 'yar
6
92
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
fitilarta tana haskawa tayo wajen don taga me ke
faruwa? A zaure suka ci karo da ita, habawa tuni sai ga
Inna wanwar a kasa, fitila a tarwatse.
Suka yi cikin gida ba su saurara ba, bare su san me ya
faru. Jikin Inna ya hau rawa ta kasa mikewa sai dai ta
shige da rarrafe cikin gida a tsorace, cewa take "Yaki a
ke."Ta shige daki fitsari tararara yana binta.
Suma sauran matan suka yo cikin gidan aka ci gaba
da dauki-ba-dadi. Inna tayi mutuwar zaune ta kasa
kwakkwaran motsi, idanuwa waje ta garkame daki har
zuwa lokacin bata fahimci me ake ba.
Bata kawo wa ranta 'yan kawo amarya ba don bata
san ya akai auran ba, tunaninta yaki ake ko tashin
kiyama ne yazo.
Fitsari tayi shi anan zaune yafi a kirga, 'yan cikinta
sai hautsinawa suke, suna kokowa da zawo yana son
kawo tashi ziyarar, irin bugawar da gabanta yake zai iya
shafar zuciyarta ta buga.
Ko ya taji tim sai ta zabura, Samira bata nan. Yayin
93
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
da su kuma suka ci gaba da fashe-fashen duk abin da
yazo musu gaba daga kayan Inna an yi tatar kokon gobe
aka dauke shi aka juye wa amarya jikinta wajen zubawa
wata. Ruwa kuma tun daga na girke har kan na butoci sai
da suka karar da su, tukwananta na kasa duk aka fashe
su da bokitai.
Amarya ta dinga kuka tana yarfe jikinta da kullin
koko, tayi nan tayi nan, ita kanta Rafi'atu taci duka duk
da ba da ita ake ba.
Can mazan ma suka shigo, Sulaiman jikinsa faceface da jini, ya shigo cewa yake "Kan ubannan, gidan
namu ne ku ka birkita haka? Ina uwata?"
Ya dinga daga murya "Inna! Inna!! Kina ina?"
Habawa su Inna ana can idanuwa sun yo waje sai da taji
muryar Sulaiman din sannan murya can kasa kamar
wacce ke gadon asibiti tana jin jiki ta ce, "Sulaiman gani
nan a daki."
Ya tura dakin, warin zawo da zarnin fitsari suka dake
94
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
shi a hanci, ya dode da sauri yana cewa "Meye haka?"
Ba ta saurare shi ba ta ce, "An gama yakin?" Ya ce,
"Wane yaki?" Ta ce, "Rigimar me ake?"
Ransa a baсе уа се, "Kokari suke su kwace mini
mata, bayan ni ne Angon." Daga haka ya fice yana cewa
"Ki zauna nan kar ki fito."Ya rufo kofar.
Gabadaya gidan sun birkice shi sun yi fatsa-fatsa da
komai, danin amarya da uwargidansa Nafisa kuwa jini
na fitowa dagajikinta.
Koda Samira ta dawo taga gidansu haka ta ce "Kam
bala'in nan, ku su waye ku ka mana haka?" Daga cikin
masu bikon Imran daya ta ce "Mu 'yan gidan ubanki
ne.
Habawa, nan ma sabon fada ya kara hardewa, suka
ci gaba da kicimilli, mota guda ta 'yan sanda tazo saboda
kai mata rahoto da aka yi, sai zuwan 'yan sandan sannan
aka saurara, kowa jiki yayi laushi likis, ba bata lokaci
aka tattara su a mota sai ofishin 'yan sanda.
A wannan ranar duk aofishin 'yan sanda suka kwana.
95
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Inna lokacin da ta fito taga abin da aka mata, ta dinga
fada in da take shiga ba ta nan take fita ba, bala'i take har
zani na faduwa.
"Iskancin da aka min kenan kan wata amarya can! To
wallahi ba zan yarda ba, duk abin da aka lalata min sai an
biya ni, amaryar banza. To za ka zo ka same ni, kaje ka
auro. 'yar mahaukata ba da ni ba wannan abin kunyar,
kazo ka sakar musu 'ya wallahi an zo an tarwatsa min
gida an lalata shi, to ban yarda ba."
Sai da safe sannan D.P.O yake jin abin da ya faru, ya
tambayi kowa. Abin ya daurewa 'yan sandan kai,
wadanda ke gun.
D.P.O ya ce, "Wannan abin yafi karfina, sai dai a tura
ku kotu, ita ce zata yanke muku hukunci aba mai mata
matarsa ko kuma kowannanku ya hakura."
Har dare ba su dawo ba, daga bisani ne aka sallami
kowa don ba mai laifi, babu mai laifi a nan sai iyayan
Mabarukan, don haka su kotu zata kama da laifi su za'a
tuhuma, meye dalilinsu na yin hakan?
96
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Sai dare can sannan suka komo gida, kowa ya kama
gabansa.
Gidan su Rafi'atu ta wuce, don ba za ta iya zama daya
daga gidan iyayenta ba, don su suka jefata wannan
masifar.
Duk amarya ana mata aure a kaita gidanta a ranar
tana farin ciki amman ban da ita, tazo iya wuya matuka,
bakinta ya kulle bata da abin cewa.
Ta sha maganin ciwon jiki ita da Rafi'ar bayan
Maman Rafi'a ta matsa mata tasha ruwan lipton don kar
maganin ya dame ta, rabonta da cin abinci har ta manta.
Ta kwanta lamo ita ba bacci ba ita ba tunani ba, sai
dai hawaye dake zarya, ta rasa me ke damunta ta dora
kanta saman cinyar Rafi'atu, a hankali take shafa mata
kai kmo ta samu bacci, amman idonta kamas babu
alamarsa.
Daga angwayen nata guda biyu Sulaiman da Imran
zuwa iyayenta ba wanda bai isheta da kira ba amman ba
13i97
a
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
kiran wanda ta dauka, daga karshe ma ta kashe wayar
gabadaya ta wullar da ita can gefe.
Ranar da suka fara zama kotun Musulunci, Alkali ya
bukaci ganin Babanta, Mamanta, Baba Haruna, Baba
Hamza, Imran, Sulaiman tare da Mabarukan.
Duk suka fito gaban kotu suka tsaya, sannan Alkali
ya ce su koma su zauna. Bayan sun zauna ne sannan ya
bukaci ganin Baban.
Ya fito ya tsaya inda ake tsayawa, akwai Lauyoyi
masu kare 6angaren Imran da ya dauka jin an kai
maganar kotu, shi ma Sulaiman baisa wasa ba ya dauki
Lauya.
Alkali ya bukaci sanin meye sunansa.
Ya gyara tsayuwa ya ce, "Sunana Yusufu Ali Daura."
Alkali ya kara cewa, "Wane addini ka ke bi?" Ya ce,
"Musulunci."
Ya kara cewa "Daga baya ka Musulunta ko ko da shi
ka taso?"
"Da shi na taso, ba tsinci iyaye da Kakanni suna yin
98
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
shi, ni ma da na gan su sai na ci gaba da bin shi har zuwa
yanzu."
Alkali ya ce, "A takaice ko za ka iya fadawa kotu
tarihinka, waye kai?"
Ya ce, "Eh, ba laifi zan iya. Kamar dai yanda nace
sunana Yusufa, asalina dan garin Katsina ne cikin garin
Daura, iyayena da Kakanni duk a can suke, nazo
wannan garinne tun ina saurayi neman kudi da ilimin
Muhammadiyya.
Alhamdulillah na samu ilimin, sana'a kuma ba
wacce bana yi in ta samu, naji dadin zama garin nan,
saboda ci gabansa da yanda ake samun ilimi.
Na ci gaba da zama a gidan Malaminmu tare da
abokaina, Allah cikin ikonsa har nayi aure na samu
hayar daki daya na tare da matata.
A lokacin ina sana'ar wankin hula kuma
Alhamdulillah ina samu, Allah yasa min albarka а
cikinta har zuwa yanzu kuma da ita nake cin abinci.
Bayan aurena da shekara uku na samu karuwar
99
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
haihuwa ta da namiji, a nan take ya koma. Bayan
shekara na kara samun haihuwar shima sati biyu da
taron sunansa