ciki da abin nan." Na ce, "Ban da ni
ko?"
Ya ce, "Ke ce ta farko, ban taba ganin wadanda suka
dace dajuna ba sai su."
Na jinjina kai alamar gamsuwa, na ce "Wallahi zan
yi farin ciki Alhaji." Ya ce, "Kinga yanzu ya rage namu
دو kenan." Na ce, "Tabbas haka ne.
Koda muka tara su muka yi musu maganar, da farin
ciki Imran ya ce "Tabbas haka ne, na dade da son
Mabaruka amman ban taba sanar mata ba. Ko don ina
ganin itama haka ne a ranta."
Da sauri ta kalle shi yanayinta ya sauya.
A takaice dai Mabaruka ta nuna mana ita bata sonshi,
kawai dai Allah ne yasa shakuwa tsakaninsu, amman ita
Sulaiman take so.
Yanayin da Imran ya shiga hankalinmu ya tashi, duk
ya sukurkuce, shi kanshi mahaifinsa bai ji dadin hakan
ba.
Hakan yasa na tursasa mata lallai sai ta aure shi, don
ina ganin kuruciya a tare da ita, kamar ma bata san meye
126
WAYE ANGON?
son ba, zata je ta cuci kanta.
Maryam Ja'afar
Musamman da ta min maganar wai Sulaiman take
so, kanin Binta. Na tsorata ainun don nasan sharrinta.
Tamkar uwa ce a gidan su Sulaiman din, ita ce mai bada
shawara kuma suna jin maganarta.
Hakan yasa na tsani aurenta da shi, kar ta shiga halin
da na shiga a baya sanadiyyar mahaifinta BUISIS
Hakan yasa na kara tsanar auren, saboda żabin
Babanta ne kuma ga shi ban gamsuba! ог л
Don haka na nace lallai ba za ta aure shi ba sai Imran,
don nasan tana sonshi kuruciya ce kurum ba za ta gane
ba. Amman in sun yi auren za ta fahimta, hankalinta zai
fi kwanciya a kan Sulaiman din. av idawen sys2
Hakan shi ne yasa na sami kanin Babanta na fada
masa abin da nake tsoro, shi ne Baba Haruna, shi ma
yaga gaskiyata ya ce na turo Imran din yake suka yaje
suka gaisa ya gamsu da shi da halayensa ya yaba sosai,
don haka ya shige min gaba har ya daura aurensu. Bgnib
Ta dubi Alkali ta ce, "Wannan shi ne dalilin daura
127
WAYE ANGON?
aurenta da Imran."
Maryam Ja'afar
Nan fa kotu ta hargitse akan wannan hardadden
auren, wasu cewa suke shin me kotu zata yanke? Wa ke
da mata kenan? Wasu su ce Sulaiman wasu su ce Imran.
To ku a ganinku WAYE ANGON a cikinsu?
Ita kanta kotu kanta ya dauki zafi a kan wannan
al'ama rin, don haka ta daga zaman sai bayan sayi daya.
A haka dai aka tashi zaman, 'yan Jarida suka dinga
tururuwar son yin magana da su amman ba su samu
dama ba. Ana tashi Imran da Sharifa da Momy suka
shige motarsu, Imran ya jawo hannun Mabaruka zai
saka ta mótar...
Saukar naushi ya ji ta bayanshi, bai san sanda ya
duke ba kansa inda ya dake shi yai mai nauyi ya
durkushe nan yana kokowa da numfashinsa, karshe dai
ya sume a nan.
Sharifa ta rugo da gudu tayo kanshi tana kuka ta
dinga girgiza shi, amman ina! Momy ma hankalinta ya
tashi.
128
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Shi kanshi Sulaiman din hankalinshi ya tashi, kowa
ya yi cak! Yana kallon me zai faru? Dagowar Sharifat sai
dai ya ji saukar wani gigitaccen mari.
Ya dago yana kallonta abin ya ba shi mamaki,
wannan yarinyar ce ta mare shi? Don haka ya fidda
hannu ya kai mata wani marin shima kan ka ce me fada
ya hargitse tsakaninsu.
A ka shiga raba su, su kansu 'yan rabon suka kama
dambe tsakanin 'yan adawa, ji ka ke sautin duka na
fitowa tif! tif!n kau! Waje fa ya hargitse, Allah yasa 'yan
sanda suna kusa suka rufar musu.
A ka kwashi Imran sai asibiti da gaggawa, Sharifa
tana biye da su tana kuka, duk sawun yatsunshi a
fuskarta. Ita kanta wacce ake fadan kanta hankalinta ya
tashi ganin Imran kwance ba numfashi, ba ta yi kasa a
gwiwa ba suka bisu asibitin ita da Rafi'atu da magoya
bayansu.
Yayin da 'yan sanda suka damke Sulaiman, magoya
bayanshi suka nufi ofishin 'yan sandan suma.
129
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
A asibiti an ba Imran gado an kuma yi nasarar
farfadowarshi, duka ne ya ji shi har da ya dawo jin kansa
yake gingiringin wani dum!
An dai masa duk abin da ya kamata, su Momy da
Daddyn Imran din suna gewaye kanshi, yayin da
Sharifa ke saman gadon da yake tana dan jajja masa
yatsu.
Mabarukan tana gefe tana kallonsu tamkar bakuwa
tazo ganin marar lafiya, su kadai ke nan nan da shi.
Rafi'a ma na gefenta.
Hankalinshi ba ya ko ina sai kan matarsa Mabaruka,
so yake su hada ido amman ta ki yarda su hadan. Ta
turbune fuska kanta na kan window, ya lumshe ido tare
da ajiyar zuciya.
Gajiya tayi da tsayuwar, tambayar kanta take to me
ma nake a nan? In tafiyata mana. Don haka ta dubi
Rafi'atu ta ce, "Zo mu tafi."
Rafi'atu ta kalleta da kyau ta ce, "Maba ruka ba ki da
hankali ko? Kina kallon ba shi da lafiya kowa bai bar
130
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
gurin nan ba sai ke? Me za ki je kiyi a gidan to?"
Ta ce, "Ni fa ba zan iya zama ba, don ba abin da zan
masa, ai dai nazo yafi ace ban zo ba." Daga haka taja
hannunta za su wuce.
Ta dubi Sharifa ta ce, "Za mu tafi, Allah yа
sawwake." Ba ta amsa mata ba sai dai harara saboda duk
saboda ita ne za a kashe mata dan uwa, bata damu ba ta
juya abinta.
A bakin kofa suka ci karo da Momy da ta fita raka
Daddy. Wata irin harara tayi mata ta ce, "Ina za ki?" Ta
turo baki ta ce, "Gida, na gaji."
Momy ta wuto cikin dakin tana cewa, "Ba in da za ki,
in kin tafi waye zai kular miki da shi? Duk cikinmu wa
yake da alhakin jinyarshi in ba ke ba, shi ne za ki sa kafa
ki fice?"
Tayi shiru tana fushi, ita bata tafi ba ita bata dawo ba,
ganin hakan yasa Rafi'ar ta sakar mata hannu ta dawo ta
zauna don daman bata gamsu ba.
Ta sake cewa, "Za ki dawo ko sai nazo na karya miki
131
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
kafafuwa, daidai ki ke da da ne? ba ki da damar da za ki
je wani guri ba tare da izininsa ba."
Fadin wannan maganar ya kara harzukata, dole ta
dawo tana cika tana batsewa kamar zata fashe.
Tayi zaune kasa saman tayils din ba tare da ta ce wa
kowa komai ba, suma suka shareta kamar ba ta dakin.
Ya lura da inda take zaune, sam bai ji dadi ba, akwai
illa zamanta kasa kuma a asibiti, ya buda baki ya ce,
"Mabaruka!"
Tana jin sa amman tayi kamar ba da shi take ba, kanta
na gefe. Sharifa ta juyo ta kalleta.
"Wai wannan zata dinga wulakanta mata dan uwa?
Wacece ita da take jiń kanta, hartana jin ita isassa ce?"
Tayi kwafa tare da harararta ta dauke kai. Ya sake
kiranta. Nan ma ba ta amsa ba. Sharifar ta ce tana
kallonsa "Menene Yaya? Me za a yi maka?"
Ya ce, "Da Mabaruka nake. Ta tashi daga kasan can
akwai matsala zamanta a kasa." Haushi ya turniketa,
kan me zai damu da ita alhalin ita bata damu da shi ba?
132
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
'Sannu' ba ta hada ta da shi ba, tunda abin ya faru sai
shi zai damu kanshi da ita? Ta fada bata sonsa kuma ta
bayyana a zahiri, don haka babu dalilin nace mata,
gwanda kawai ya barwa Sulaiman din can su karata.
Momy ta ce, "Rabu da ita Imran, tayi ta zama ai ta
san akwai illa baka da lafiya kana bukatar hutu."
Zai yi magana ta dakatar da shi "Ya isa haka, koma
ka kwanta." Baya son musu, don haka dole ya kyale ya
yi lamo idanunsa a rufe amman ba abin da yake gani a
idonsa sai Mabarukar.
Bai san me yasa ba, daga sanda aka daura aurannan
wani sonta ke kara ruruwa a ransa matsananci, wanda
bai taba jin irinsa ba, a yanda yake ji zai iya komai don
kwatar matarsa, zai kuma jure komai ba zai yarda ba a
kwace masa mata ba alhalin kowa yasan shi ne
ANGON.
Rafi'atu tazo kusa da ita ta dubeta ta ce, "Mabaruka!"
Ta dago tana kallonta, ta ce "Ba kya jin magana ko?"
Tayi shiru tana gimtse baki ta ce, "Mijinki ya yi miki
133
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
magana ki masa banza, ki ki yin abin da ya ce.
Wani kallo da tayi mata jin ta ce wai mijinta, tamkar
ta fasa mata baki. Ta ci gaba da cewa, "To in shi ya yi
miki laifi don ya ce yana sonki, ita Momy me ta miki don
ta hada aurenku alhalin tana sonki?"
Tayi dai shirun taci gaba "To ai kin tashi saboda
darajar haihuwarki da tayi, kada ki bata kanki Mabaruka
kan son zuciyarki, ki zama marar da'a da rashin kunya,
Allah zai yi fushi da ke saboda rashin yiwa mahaifiyarki
biyayya kina 6ata mata rai gefe kuma ga na mijinki."
Ba ta da alamar tankawa bare ta tashi din.
"Ba za ki ji abin da nake gaya miki ba, wallahi ni ma
zan nesanta da ke, zan kyale ki kije kiyi abin da ki ke so,
ba zan iya tafiya da wacce bata da da'a ba."Daga haka ta
yunkura zata fita.
Da sauri ta tashi ta koma kan kujera ta zauna, sannan
ta dawo.
Yayi murmushi ya kalli Rafi'ar a hankali bakinsa ya
furta "Thanks."
134
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Kasancewar yanda suke da kusanci da Sharifat da
Mabarukar duk sanda tazo hutu tamkar tagwaye, su
kwana tare su wuni tare, su fice yawo wurare-wurare,
hatta kayansu wani lokaci iri daya, kan ta dawo zata
dinka musu ko kuma ita tan taho mata da su na irin
Kasarsu.
Tamkar tafi kowa murna da aurenta da yayanta,
amman tunda ta fahimci bata kaunar dan uwanta har a
ka zo aka yi wannan rikicin, har ta kai yau tayi
sanadiyyar kusan rasa ransa, amma ko a jikinta, bata
daina nuna masa kiyayya ba, ba ta ko jin kunyar
mahaifinsu da ita take nunawa bata son nasu.
Don haka ta sire mata a halin yanzu ba wacce ta tsana
sai ita, kuma tayi alkawarin ba za ta taba barin wannan
auren ya yiwu ba.
Tasan Yayanta mutum ne mai hakuri da sanyin rai,
cutarsa zata dinga yi ta hanyar cuzguna masa ta dinga
nuna masa tsantsar tsana, shi kuma ba zai dauki wani
mataki ba zai kyaleta ne tayi mai isarta koda shi zai cutu.
135
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Don haka ba za ta yarda da cutar dan uwanta ba, in ita
ba ta sonshi su suna sonshi, fiye da kowa ma, sun fi son
rayuwarsa a kan tasu.
Tasan ita 'yar lelensa ce abin da take so yake yi, in har
ta bata rai ta ce bata son abu bare yaga hawayenta to
tabbas zai rikice hankalinsa ya tashi, shi ma wannan
abin zai siri masa ya yi mata abin da ta keso.
To wannan karon tayi alwashin sai tayi fiye da hakan
don ya hakura da auranta.
Haka dai suka kasance a wannan ranar har dare,
Daddy ya dubi Momy ya ce, "Sai mu wuce gida ko, dare
ya yi sosai."
Ta ce, "To wa zai zauna tare da shi kenan?" Ya yi
murmushi tare da nuna mata Mabaruka da ido. Tayi jim
tana gane hikimarsa, eh tabbas haka ne don haka ta ce
shi kenan.
Suka harhada flask-flask din ta dubi Sharifa ta ce,
"Muje ko." Ta kalleta ta ce, "Ba a nan zan kwana ba? In
na tafi wa zai zauna da shi?" Daddy yaja hannunta yana
cewa "Zo kiji." Suka fice.
136
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Momy ta dubi Rafi'atu ta ce, "Taso muje Rafí'a, ki
bar kawar taki sai gobe mun dawo."
Ita kanta Rafi'ar hakan ya mata dadi, ta mike da sauri
yayin da Mabarukan idanuwanta suka fito. Ta dubi
Momy a marairaice ta ce, "Kada ki min haka Momy,
wallahi zan cutu. Ku bar Sharifa tare da shi."
Ta harareta ta ce, "Idan kun tare da shi sannan ne za
ki cutu, amman daga yau kullum tare da shi za ki dinga
kwana, ga shi nan mun bar miki amanarshi, marar lafiya
ne duk abin da yake bukata ki masa tun kan ya nema, na
fada miki."
Ta riko Momyn tana kuka, "Wallahi ko numfashi ba
zan iya maidawa ba in dai daga ni sai shi a dakinnan
zuciyata daci take min, don son Annabi kar ku bar ni a
nan. Inaji na tamkar a kungurmin daji nake..."
Wani irin mari tayi mata wanda yasa ta saki hannunta
ba shiri, ta dafe kunci ta ci gaba da harararta.
"Wawiya wacce ba ta san me take ba." Daga haka ta
fice. Rafi'a ta ci gaba da kallonta cikin bacin rai ta ce,
137
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
"Kinga ni ko karo na biyu kenan tana dukanki saboda
lafiyarki, har kina fadin baki iya maida numfashi. To mu
dawo gobe mu tarar kin sankare shi ne za ki nuna mana
tsantsar kiyayyarsa."Ta juya.
Da sauri ta riko hannunta tana kuka, ta ce "Kema
haka za ki ce ba ki ga cutar da aka min ba?" Ta harareta
tare da fizge hannunta ta ce, "Tabbas iyaye na cutar
'ya'yansu wajen zabar musu mijin da ya dace da su don
farin cikinsu ba don musgunawa ba, kije kiyi abin da ki
ke so Mabaruka, kar ki kasance da shi ki bar dakin."
Daga haka ta fizge hannunta ta fice a fusace.
Ta daki bango tare da fashewa da kuka ta duke a nan,
zuciyarta tayi mata nauyi da daci, bata jin akwai abin da
ke mata dadi.
Shi kuwa Imran yan akwance bacci ya dauke shi bai
san ma me ake yi ba.
Lokacin da Daddy yaja Sharifat zuwa bakin motar
tana masa kuka ta ce, "Me yasa żamu bar shi da ita
alhalin bata sonsa? Wallahi zata cutar mana da shi
138
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Daddy, kar mu bar shi daga shi sai ita, me yiwuwa ya
bukaci wani abun ta hana shi."
Yas ata motar ya dube ta ya ce, "Kada ki damu,
Yayanki zai kasance cikin farin ciki a yau, ba abin da zai
dame shi, za ki gani. Sannan kada ki manta akwai aure
tsakaninsu, wata rana za su yi zaman aure na har abada,
ke dai ki masa addu'a."
Ta ce, "Ba na son aurennan Dady, akwai cutarwa."
Ya yi murmushi ya ce, "Mu muna so shi ma yana so,
za ki kuma gani. Me yiwuwa ki samu mai sunan
Umminku a samù Sharifat ko kuma ku samu Daddy, ko
ba kya son mai sunana?"
Ta dan yi murmushi ta ce, "Ina so."Ya ce, "Yawwa to
ki musu addu'a." Ta ce, "Amman kana da hakikanin shi
ne mai matar?" Ya ce, "Yes, Imran shi ne mai matar, shi
kotu zata ba Mabarukar don shi ne Angon a zatona.
Ta rausayar da kai ita dai ba haka taso ba.
Su Momy suka fito suka shiga suka wuce a motar
tafe suke suna farin ciki a kan wannan tsarin, tabbas
139
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
haka za su ci gaba da yi da alama komai zai yi daidai.
Rafi'a ta ce a sauke ta kan layinsu zata wuce gida,
gobe tazo asibitin da Mamanta, don haka suka sauketa ta
wuce gida.
** **
Su Sulaiman kuwa ana can ofishin 'yan sanda an
garkame shi, ba za su sake shi ba har sai an ga tashin
Imran.
Inna ta dinga cizgar fada, haka nan yaje ya dauko
musu jangwamgwam! An zo an garkame shi kan wata
yarinya can, to ahir dinka ba kai ba yarinyar nan.
Ya ce, cikin jin haushi "To matata ce fa, don me za ki
ce haka?"Tayo masa dakuwa.
"Uwaka nace, ja'iri mato ba mata ba don ubanka, kar
na sake jinta a bakinka ga matarka can a gida ka bar
musu can su karata, ai ban san haka auran yake ba,
munafuki ka 6oye min ka san ba zan yarda da wannan
mahaukacin auren ba, wanda ko a Musulunci haram ne
140
WAYE ANGON?
babba.
Maryam Ja'afar
Babban laifi, kai kanka mahaukaci ne sakarai har ka
yarda aka aura maka ita alhalin an daura da wani."
Ya ce, "Ni fa bań san wani ba, Babanta shi ya aura
min ita, shi kuma wancan uwarta ce ta daura kuma kin
san mace bata faura aure, don haka ni ne mai matar, ni
koto za ta ba."
Ta ce, "Idan ba kai min shiru ba sai na kwade maka
baki, tunda nake ban ta6a zuwa gaban Alkali ba amman
sanadinka sai gani a kotu.
Yau kuma ga ni a wajan 'yan sanda, kai kanka ba a
taba saka a wannan gurin ba, sai dalilin mahaukatan
iyayen yarinyar, to ka kyale musu 'ya ba kai ba kara
zuwa kotun bare ni, shi kenan magana ta kare."
Da ba uwarsa ba ce da sai ya naushe mata baki, shi
haushinsa ma da takaici da yanzu bai san ina matarsa
tayi ba, kar dai ace tana wajanshi?
Kishi ya taso masa, idanunsa suka kada jajir har huci
yake idonsa sun rufe tamkar ya 6alle karafan yake ji.
141
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ta dube shi ta ce, "Au! Dukana zaka yi ka ke huci?"
Sam idonsa ba kanta yake ba, karfi na kara zuwar masa
יי ya ce "Ki bar gun nan.
Ta ce, "In bar gun nan?" Ya nanata cikin tsawa "Ki
bar gunnan na ce."" Ya daki karfen. Ta tsorata ainun, da
gudu ta bar gun tana waiwaye, sam bata taba ganinshi
haka ba ya bata tsoro.
Ya dinga dukan karfen da bango yana ihu, "Wallahi
idan ya taba min mata sai na kashe shi, matata ce ni ne
Angon." Haka ya dinga kururuwa kamar zai fasa gurin
ya fito.
Har dare sai da sukai mai allura sannan ya nutsu ya
kwanta.
Mabaruka kuwa tana nan tana ci gaba da kukan har
karfinta ya kare, tayi zaune dabas bakin kofa tana ajiyar
zuciya.
Taiwa kanta alkawari ko motsi ba za ta yi ba daga
wurin haka za su dawo goben su tarar da ita bakin kofa
bare ta juya taga makiyinta, ta dinga ayyanawa a ranta
142
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
dama ya mutu kan goben sai dai a zo a dauki gawarsa,
wallahi da tayi farin ciki, a duniya damuwarta ta kare.
Bacci ya yi mai nauyi, wani ikon Allah ko da ya farka
ya ji kansa wasai, nauyin da yake ji babu shi tamkar ba
abin da ya same shi, shi kanshi bacci magani ne.
Ya mike zaune yana waige-waige a dakin bai ga
kowa ba, ya yi mamaki da bai ga su Momy ba, tafiya
suka yi kenan!
A haka idanunsa suka sauka kanta, a durkushe ta
juya baya abin ya ba shi mamaki matuka. Mabaruka
kuma me take a nan? Da ita aka bar shi kenan? Abin ya
daure mai kai, ya a ka yi ta yarda ta tsaya.
Ya yi shiru ko ba komai dai ya ji dadin kasancewarta
a gurinshi, ina ma za ta yarda da shi?
Gani ya yi ta taso ta tunkaro shi fuskarta dauke da
murmushi, yanayin yanda take tafiyar ya daukar maşa
hankali. Ta kara masa kyau a fuska matuka, amman
anya Mabaruka ce? Ko dai ta canza ra'ayinta ne?
Da zuwa ta sunkuya daidai fuskarshi har suna jin
143
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
numfashin juna ta ce a hankali cikin salon jan hankali.
"Ka tashi?"Wani kamshi ya fito daga bakinta wanda har
sai da ya lumshe ido don dadinsa.
Ya kasa buda bakinsa ya yi magana sai dai ya daga
kai "Eh."
Ta ce, "Ya ka ke jin jikin yanzu?" Ya ce, "Na warke."
Tayi dariya tare da cewa "Gabadaya ma?" Ya daga kai ta
kara cewa "Me yasa?"
Ya ce, "Saboda kasancewarki a nan tare da ni, gani
nake kamar a mafarki wai ke ce haka ki ke min dariya,
kin yarda da ni kenan a matsayin mijinki?" Tayi
murmushi tare da shafar fuskarsa ta ce da shi.
"Sosai ma kuwa, kai din ba na yarwa ba ne, a ganina
idan har nayi ganganci ka rabu da ni na tabbata gauliya,
kai din mai tsada ne, karya nake na ce bana sonka,
wallahi ina sonka Imran."Ta fada a marairaice.
دو
Ya ce, "Amman me yasa da ki ke cewa ba kya so.
Tayi murmushi ta ce, "Ba haka ba ne, gaskiyar amman
gaskiyar ina Kaunarka."
144
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Zakin maganar bai san ya zai misalta ta ba, har cikin
kwakwalwarsa ya ce, "Dan sake fada Please." Та се,
"Ina sonka." Ya ce, "Kara." Ta ce, "Ina sonka." Dan
kara." Ta ce, "Nima ina sonka." Yayin da take kara
kusantowa gare shi, har ta hada kawai ta farka ta ganta
kusa da shi.
Ya yi murmushi ya ce, "Nima ban san ya za mu kare
da ke ba Mabaruka." Ya kara jawo ta jikinsa ya rungume
kam yana jin wani nishadi a ransa.
Ya godewa su Momy da suka bar masa Mabaruka
yau kawai ya tabbatar zai sami ingantacciyar nutsuwa
da farin ciki, ya ce "Ya Allah ka nuna min ranar da zan
ganni da wannan baiwar taka a gidana, tana mai
amincewa da ni da sona."
Ta gyara kwanciyarta tare da kara lemewa a saman
kirjinsa duk a cikin bacci, ya yi murmushi yasa hannu ya
rungumo kayansa. Daga haka suka ci gaba da baccinsu
mai dadi sansanyar numfashinsu na haduwa da junansu
shi dai bai san wane irin annuri yake ji ba, kasancewarsa
145
WAYE ANGON?
da ita.
Maryam Ja'afar
Yayin da ita baccinta take hani'an ba ta san inda zata
ce take ba, karfe uku Nurse ta turo kofar ta shigo don
duba patient dinta, yanda ta gansu ne abin ya bata
mamaki, gefe kuma ya bata dariya, ta fita ta kirawo 'yar
uwarta ta ce "Zo ki ga wani abu marar lafiya ya warke."
Suka yi dariya daya ta ce, "Ikon Allah! Soyayya
dadi."Sukaja musu kofar suka fice suna dariya.
Nannauyan baccin da ya dauke ta bai saketa ba sai da
sanyin asuba ya fara kadata, sannan ta juya don ta jawo
bargo ta lulluba kamar yanda ta saba yi da zaran ta ji
sanyi irin wannan lokacin zata ja bargonta.
Jinta tayi an matseta ta duba da kyau, kawai ta ganta
jikinsa kwance. Wata irin kara ta saki tayo tsalle ta diro
daga kan gadon tana maida numfashi.
Ya farka a firgice shi ma, ġaninta ya yi tsaye tana
binsa da kallo cikin tsananin mamaki, gefe kuma wani
takaici da haushinsa ya lullubeta, ta ci gaba da kallonsa
tana harara, kana kallon tsantsar tsanarsa a idonta.
Ya tashi zaune ya dubeta ya ce, "Lafiya? Me ya
146
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
faru?" Tayi shiru tana harararsa din. Ya mike tsaye ya
tunkarota yana cewa, "Mabaruka lafiya kuwa?"
Da sauri taja baya tana cewa, "Kada ka kuskura ka
matso ni, in ba haka ba wallahi sai na rotsa ma kai,
mugu, dan iska azzalumi." Daidai zubowar hawayen da
bata san da zuwansu ba, saboda tsabar takaicin
kasancewarta da shi.
Ya tsaya cak yana kallonta, ya ce "Me nayi miki na
muguntar? Me na kuskure miki?"
Ta kasa cewa komai sai dai hawayen da ke zirarowa
daga cikin gurbin idanuwanta.
Ta dauke kanta daga gare shi ta dubi jikinta har kasa
ta maida kanta saman gadon don son gano wani abu,
bata fahimci komai ba ta dago tana sake kallonsa.
Har yanzu idanuwanta da hawaye, ta ce "Ka fada
min gaskiya me ka yi min?" Sam bai fahimce ta ba, ya
ce, "Kamar ya?" Ta harzuka ainun ta fada cikin tsawa,
idanunta suka yo waje.
Та се, "Ка fada min gaskiya me ya shiga tsakanina
da kai a darannan?" Sai a sannan ya fahimce ta.
Ya bita da kallo, ya koma ya yi zamansa yana cewa,
"Oho, tambayo kanki me yiwuwa shaukin hakan ya
mantar da ke."
147
۲
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Fadin wannan maganar yasa hankalinta ya kara
tashi, ta harzuka wasu hawayen suka zubo mata, ta nufo
shi ta čakumo shi tana cewa.
"Wallahi idan har na tabbatar ka min wani abu na
cutarwa sai na kai kararka gurin Allah, mugu, dan iska,
macuci wanda bai san darajar soyayya ba, sai ka fada
min me ka min."
Ta ci gaba dajijjiga shi tana kuka.
Ko motsi ya kasa yi bare ya bata amsa, illa dai
kallonta da yake. Ita kuma ba ta fasa ba, har ta koma
dukansa a kan kirjinsa hannu bibbiyu tana kuka.
Cak ya rike hannunta yana kallonta da jajayen
idanunsa, itama shi take kallo, suka ci gaba da kallonkallo, kowa da ma'anar kallonsa ga dan'uwansa.
Shi ya fara magana cikin sanyinsa da saukin kansa
ya ce, "Menene haka Mabaruka? Me ke damunki? Nine
Angonki fa, ni mijinki ne idan har wani abu ya shiga
tsakanina da ke wanda ki ke zargi har za ki yi bakin ciki
kiyi kuka hankalinki ya tashi har haka, ba fa fyade na
miki ba, ni mijinki ne ina da hakki a kanki. Laifi ne don
miji ya kwanta gado daya da matarsa?"
Ta harare shi ta ce, "Ni ba matarka ba ce wallahi, kar
ka sake kirana da matarka, har abada ba ni da miji irinka
148
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
haka kai ma kaje can ka nemi matarka, wacce tayi daidai
da kai amma ba Mabaruka ba."
Ya ce, "Ba zai yiwu ba, tunda har kina matsayin
matata dole ne na kira ki matata, amaryata don ni
mijinki ne duniya ta shaida, ni ke da ke ke tawa ce,
hakkina mallakata. Kuma dole ne duk sanda na bukace
ki in same ki ba tare da kin tuhume ni don me ba, got it?"
Ji take kamar ta shake shi don haushi, idanunta sun
kasa barin nasa, kallon banza tsantsar tsanarsa take ji a
ranta da kiyayya.
Ta tofar da yawu gefe ta ce, "Tir da na kasance
matarka, Allah ya sauwake, wallahi kyamarka nake ba
don kai kazami ba ne illa sai don yanda nake jin tsana
rka a raina tana tukata."
Ta kwace hannunta daga jikin nasa ta kara cewa
"Kuma sai Allah ya saka min da ka kwanta kusa dani ba
da son raina ba, sai don yaudararka da cin amana. Allah
ya isa wallahi." Hawaye suka zubo mata.
Ya ce, "Ki daina wahalar da kanki, kina guje wa
auran da aka riga aka daura, Mabaruka ni fa mijinki ne
ba yanda ki ka iya. Kiyi hakuri ki saki ranki ki barwa
Allah komai.
149
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ni kuma nayi miki alkawari da kaina zan koya miki
sona, zan kuma ririta ki tamkar kwai a hannuna, duk
wani abu na jin dadin rayuwa zan ba ki shi ko da ni zan
cutù.
Har ya karashe maganar babu abin da take ji a ranta
sai tukuki, babu magana daya da ta burgeta cikin
maganganunsa sai ma kara mata tsanarsa da suka yi.
Ta durkushe a nan tana jajantawa kanta wannan
alakakan, da gaske kenan ya riga ya santa a 'ya