ya koma.
Sai bayan shekaru uku sannan na sami 'ya mace,
muna ce mata Salaha. Watanta hudu Allah ya amshi
abinshi. Muna nan muna nan dai kamar ba za a kuma ba
can sai ga wata haihuwar, a nan muka samu haihuwar
Mabaruka, to Allah ya rataya Alhamdulillah wannan shi
ne a takaice."
Alkali ya kira Mahaifiyarta ta tsaya a dayan gurin ya
ce, "A takaice ko za ki fada wa kotu tarihinki?"
Ta ce, "Eh! Sunana Halima Bello, 'yar nan garin ce
ni, mahaifina shi ne Mallam Bello, gidanmu duk mata
ne ni ce mace ta farko 'ya a gidanmu.
Ina da kanne biyar, nayi aure tare da Mal. Yusufa
kamar yanda ya ce, Allah ya bamu 'ya'ya hudu tare da
shi amman Allah bai sa sun tsaya ba sai Mabaruka."
Alkali ya ce, "Meye rayuwar aurenku da shi?"
"Eh, lallai kam an sha fadi-tashi na rayuwa tsakanina
100
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
da shi, dangane da wuyar rayuwa na talauci. Mun yi
yawon haya gida-gida a lokacin kudin hayar ma
gagararmu yake sai dai mu biya rabi kan ya kare zamu
harhada da 'yan kasuwancin da muke ni da shi mu biya.
Tun bayan barin wajen aikinsa inda yake wankin
hula. Kwatsam sai ga wani sabon kamfani an bude ana
neman ma'aikata.
Don haka bai yi wasa ba yaje cikin sa'a aka dauke shi
aikin. Ba laifi albashin da albarka, na daya na biyu ana
uku ya harhada ya sai fili.
Muna nan dai rayuwa ta fara sauki shi kanshi ginin
yana yin shi gutsin-gutsin in an samu ayi, yanayin dai
ginin talaka bai gama ginin ba aka samu matsala
kamfani a ka kulle, don haka sai dai ya koma sana'ar
wankin hularsa.
a
Haka dai rayuwar ta ci gaba da gangara mana ganin
mun kusa gama ginin mahaifiyarmu ta rasu, to gadona
da shi nayi amfani na sayar da dan abin da ke gare ni
daga kayan daki da 'yan canjina na tattara na ba shi ya
101
WAYE ANGON?
Karasa ginin,
Maryam Ja'afar
Daki biyu ne shi daya ni daya, muka tare hankalinmu
kwance, lokacin Mabaruka na yayeta.
Ban fasa sana'a ba ina yi mu kanci abinci da kyau shi
ma ya kawo abin da ya samu, don haka sai rayuwa tai
mana sauki, ga shi ba yawon haya a gidanmu ne ga
sana'a muna yi ni da shi.
Wata rana, ranar Asabar ina zaune ina yankewa
Mabaruka farce ya shigo da kaya niki-niki a hannunsa,
na bishi da kallo ina cewa.
"Malam daga ina haka afujajan da kaya?"
Ya zauna tare da mike kafa yana cewa, "Ke dai bari,
daga kasuwa nake." Na ce, "Kasuwa kuma?" Ya ce,
"Eh! Na bude na gani.
Atamfofi na gani har guda uku, sai leshi daya da
hijabi da takalma sai 'yan kayan shafa. Na dago ina
kallonsa na ce, "Wadannan kayan fa?"
Ya ce, "Kanwarki taja min sayensu, haki ne." Na ce,
"Ban fahimta ba, wace kawar?" Ya ce, "Ku fa mata
102
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
akwai ku da basarwa, wace kanwa ki ke tunanin zan
kawo miki? Abokiyar zama mana wacce Mabaruka zata
sami 'yan kanne." Ya fada yana jan kafar Mabarukar
yana mata wasa.
Idanuwana suka fito na ce, "Aure ka ke nufin za ka
yi?" Yayi dariya ya ce, "Yawwa 'yar gari ashe kin gane,
aure fa. Jibi take tarewa."
Matuka raina ya 6aci, saboda ganin ya raina min
wayau, yana kallon wuyar da muka sha na rayuwa duka
yaushe muka fara samun sauki, amman ko shekara ba
mu kulla ba ya fara zancan aure.
Wai har jibi zata tare, kenan an daura aure tunda har
ana maganar tarewa? Na dai daure na ce "An daura
kenan?"
Kai tsaye ya ce, "Wallahi yau mako daya kenan,
anjima masu yin farar kasa za su zo su dan shafa mata a
29 dakin, in ya yi ragowa kya samu.
Na ce, "Allah sa alkairi, na gode da fenti ita dai da
yake sabuwa ce a mata tafi bukata." Ya ce, "Ah to ba
103
WAYE ANGON?
laifi bana tunanin ma zai isa."
Maryam Ja'afar
Na kara cewa, "Amman kana ganin adalci ka min har
a daura maka aure ba ka sanar da ni ba sai ana jibi ba ni
da wannan kimar da zaka sanar min?"
Ya ce, "Kiyi hakuri bana son ki tayar da hankalinki
ne, amman yanzu tunda an riga an yi damuwarki da
sauki."Daga haka ya mike yasa takalma ya fice.
Koda amarya ta tare nasha mamakinsa matuka, kirikiri ya canza baya jin komai gabana yake rawar jikin
matarsa kamar bai taba aure ba.
Hatta cefane ya fara canzawa idan ranar girkina ne
sai ya dauko Naira dari ya bani ya ce ba shi da lokacin
zuwa kasuwa in sai abin da zan siya ayi maneji.
Idan kuma ranar girkinta ne haka zai shigo da ledoji
fal da kayan miya, kaji da cefane ko kifi tayi girki gajegaje ta juye musu a ledar da naman ni ta bar min saura a
tukunya.
Duk idan nayi magana ya hau fada, ai ba ni da hakuri
shi ma ba daga shi ba ne kawai dai abin da ya sani ita ta
104
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
shigo da kafar dama shi yasa duk ranar girkinta
aljihunsa yake jinsa da nauyi.
Wata ranar girkina zai fita da safe ya miko min Naira
dari ya'ce "Ga shi nan in sai kayan miya yana sauri ne.
Naki karba na ce "Ka ba yaro ya siyo ai ba a rasa mai
siyowa ba, ba lallai sai ni naje na siyo ba."
Ya ce, "Wane yaron nake da shi zai siyo?" Ya jefo
min ya wuce yana cewa, "In kin ji yunwa kin siyo." Ya
ficewarsa.
Dole tunda ina jin yunwar da rana tayi na dauka naje
na siyo wake gwangwnai dayan da dan barkono da
manja na dawo na girka.
Abincin nan da na gama na ba Binta matarsa ko
kallonsa bata yi ba bare taci, ni dai naci haka zalika shi
ma da ya dawo na kawo masa ya ce a koshe yake.
To a ranar ta karßi girki tun da ya shige dakinta ban
kara jin motsinsa ba.
Washegari tunda safe ya fice, ashe kasuwa yaje sai
gashi da kaya dam a hannunsa, ya wuce dakinta ya kai
105
WAYE ANGON?
mata.
_ Maryam Ja'afar
Ta fito tana gyarawa, kayan miya ne da kifi lodi
guda, duk ina kallo ban ce komai ba, sai da ya fito muka
gaisa na ce.
"Amman abin da ka ke ya kamata kenan? Yau ka
sami lokaci kuma aljihunka da nauyi a kullum in dai ni
ce da girki ba ka da kudi sai ranarta? Malam kar fa ka
manta baya ka nutsu ka gyara kuskurenka."
Ya 6ata rai “Ni matsalata da ke kenan bakin ciki,
kina bakin ciki ana kawo mata ni ba daga ni ba ne kuma
abincin nan in an dafa ana baki kin fi ma kowa ci amman
kullum kina bakin ciki da haka."
Raina ya 6aci, na ce "Kai kasan ban taba maka bakin
ciki ba da samuwarka ba, ina son dai ka gyara
kuskuranka don ka zamo mai adalci, ka tashi gobe
kiyama babu alamar rashin adalci a tare da kai."
Ya ce, "To ba zan yi ba, ki dauki mataki. Daga haka
ya fice.
Abin kullum gaba yake karawa, musamman da ta
106
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
samu ciki abin da yake nema kenan, don haka rawar
jikinsa ta karu na koma bora a cikin gidansa, ba ni da
matsayi a idonsa ko kadan sai dai ita ke juyinta son
ranta.
Kullum ita ke yin daidai amman ni ko ya nayi
kuskure duk makota sai sun ji saboda fadansa.
Zaman ya koma min na hakuri, ko kadan bana jin
dadinsa, ko yana dakina babu wata mu'amula
tsakaninmu idan ni na neme shi sai ya ce shi ya gaji, don
Allah na kyale shi ya huta sai yai ta sharar bacci ya banni
zaune cikin tsananin bukata.
A kullum haka muke, ta kai ga na fara masa kuka
amman ko sau daya bai taba saurarata ba.
Kamar wata rana mun yi haka da shi da dare, da safe
yana tashi ya'ce in je gida na huta zai neme ni, na
tambaye shi dalili sai ya ce naje dai kurum.
Haka nan ba da son raina ba saboda bukatuwar
mijina na tafi gida, koda mahaifina ya tambaye ni dalilin
zuwana, na ce shi ya ce na taho gida.
107
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ya dube ni da kyau ya ce, "Halima." Na ce, "Na'am
Baba!" Ya ce, "Kin tabbata ba ki masa komai ba ya turo
ki?" Na ce, “Wallahi ban masa komai ba, kai ma ka sani
Baba a tsawon zamana da shi ban taba zuwa ko yaji ba,
ban taba karo maka kararsa ba, lafiya muke zaune da shi
ban taba jin ya yi min korafi nayi masa wani abu ba.
Ya yijim cikin gamsuwa sannan ya ce "Amman abin
da mamaki Halima, a ce haka nan miji ya turo mata gida
wai ta zo ta huta?"
Nayi shiru dai. Ya ce, "Amma zan neme shi yazo in ji
me ke faruwa?" Na ce, "A'a Baba kada ka neme shi
tukunna ka bari muga me yake nufi kenan? Idan abin
nasa ya wuce misali sai a tuntube shi."
Ya ce, "Haka ne kuma, shi kenan Allah ya tabbatar
mana da alkhairi."
Haka na zauna gidanmu tun ina jiran zuwansa mu
tafi har dai na mike kafafuwa, idanuwana kullum a
kofa, duk sanda Babanmu ya shigo ina bin bakinsa da
kallo ko zan ji ya ce "Ga mijinki yazo ku tafi."
e
108
☑
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Amman shiru nake ji ba shi ba alamarsa, ga jarabar
son mijina da yake damuna, kullum mafarki nake na
koma gidan har dai mahaifina ya fahimce ni.
Wata rana ya kirawo ni dakina. Bayan na zauna ya ce
"Kiyi hakuri Halima, nasan kina son komawa gidanki,
amman kin ga har zuwa yanzu bai zo ba, bare ya bukaci
hakan. Amman na yanke shawarar zan neme shi sai naji
dalili.
Idan laifi ki ka yi masa ki ba shi hakuri ki koma, idan
kuma dai wani dalili ne duk zamu ji."
Na gamsu da hakan, don abin da nake nema kenan
fada ne dai ban yi ba.
Don haka kwana biyu da maganarmu, kwatsam na
tsinkayo maganarsa zaure tare da Babanmu, farin ciki
ya bayyana gare ni, ba tare da naji ya suka yi ba, na hada
kayana inajiran a kira ni.
Ba wani dalili ba ne nashi illa kame-kame, wai na
fiye kishi, tunda naga ya yi auren nan nake kishi da
matarsa na takura mata da sa mata ido duk abin da take
109
WAYE ANGON? Maryam a'afar
idona na kai bare da ta samu ciki wai na dinga jin haıshi
ina mata mugun baki, wai dan ai ba zama zai yi ba, nima
haka nayi.
Maganganu dai ga su nan da ji kasan tsara su acai,
koda mahaifina ya ji bai yarda da zan yi hakan ba,
amman dai ya ce "To ya yi hakuri zai min fada ba zan
kuma ba insha Allah."
Ni kaina nasan ya fada ne amman ba haka ba ne, nayi
hakuri kawai na bar shi eh a kan hakan ne, muka tattara
ya wuce da ni.
Koda na shigo gidan kallon banza ta min, tare dajan
tsaki. Cikinta ya turo sosai, plate din farfesu a gabanta
tana sha. Ta harare ni ta ce, su karya dai an ji haushi ba
zuciya an dawo dai to kizo ki zauna ba za ki samu kima
da daraja ta matar gidan na ba za ki ga wane matsayi za
ki zauna.
Raina ya 6aci zan yi magana ya daga min hannu, "Ba
na son rashin hakuri da Allah wuce kawai."
Ba na son mu fara daga dawowata hakan yasa na
110
WAYE ANGON?
dauki jakata na shige dakin.
Maryam Ja'afar
In da tsari ake bi tunda na kwana da yawa ba na gidan
to yau ni ke da miji, amman ina ganinshi ya shige
dakinta. Na kyale shi ayi kwana biyu kamar yanda
muke yi, don haka na share.
Akai kwana biyu duk yana dakinta a zatona zai dawo
dakina, amman naga yana kokarin shiga dakinta, na
dakatar da shi na ce.
"Ka manta ne yau a dakina ka ke?"Ya juyo ya harare
ni tare da jan tsaki ya bude labule ya shige, na kara daga
murya na ce baka ji ni bane yau fa a nan kake kwananka
biyu a dakinta.
Ji nayi an turo daki bam! A wannan ranar nashi kuka
iya karfina na tabbatarwa kaina lallai a yanzu ba ni da
kima a gidansa, ba ma da son ransa ya dawo da ni ba mai
yiwuwa saboda mahaifina ne.
Sai da na gaji sannan na bari na fito nayo alwala ina
jiyo dararrakunsu daga daki na goge kwallar dake son
taruwa a idona na shige dakina.
111
Π
WAYE ANGON? Maryam la'afar
Tun daga sannan na daina kasancewa da mjina
dawowata wata biyu kenan, yana gidan amman ya
manta dani ya ma daina maganar girkina, kullum ita ke
yi kayan abinci suna dakinta in ta gama ta yafo min a
plate ta shige musu da saurah dakinta.
In ya dawo ina masa magana ya ji tsoron Allah sai dai
ya wuce ya bar ni tsaye sa shige daki har da banko kofa.
Lubabatu kanwata ce ita ke bina wata rana tazo min
ziyara. Wuni guda ta gama fahimtar me ke faruwa,
musamman da taga an turo min plate daya na abinci ta
shige daki ta rufe.
Ta kare dubana yanda na rame nayi baki kashi har a
fuska, ta ce Yaya! Na kalleta ta ce, "Fada min me ke
faruwa?"
Abu daman yana cina a raina kamar jin nake kun san
in kana cikin damuwa idan ka fadawa wani ko ya ya ne
zaka samu sauki, ban yi niyyar fada mata halin da nake
na fada mata.
Hankalinta ya tashi ta dinga kuka, tayi bakin cikin
112
WAYE ANGON?
kasancewata a wannan halin ta dinga fada.
Maryam Ja'afar
Ai ba kallonsu za ki dinga yi ba Yaya, gidanki ne fa
nan tazo ta same ki taje tayi 'yan abubuwanta ta anshe
miki miji sai ki sa ido kina kallonsu.
Na ce, "To me zan yi Luba?" Ta ce, "Nuna mata za ki
ita karamar 'yar iska ce, ba tare da kinje gun boka ba ko
Mallam, nasan kina addu'a amman dabaru hikima za ki
janye hankalin mijin na ce to ba sai in ina ganin mijin ba
ma.
Та се, "Кo yana dakinta ne banka ki shiga ki zare
mata ido ki nuna mata ke ma 'yar bariki ce, ba a fiki
wayau ba, don ma tana ganinki laka-laka shi yasa.
amman in irina ce ai ba inda zataje wallahi.
Na ce, "Ba mai maganin abin nan sai addu'a, Luba
wani rashin kunya duk ba mafita ba ce, ke dai ki taya ni
da addu'a kurum."
Haka dai Luba ta tafi tana ta fada akan zata dawo
kwana biyu taga ya abin ya sauya, lallai dai in yi abin da
ta ce.
113
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Har nayi bacci kamar daga sama naji saukar bulala a
jikina na mike ba shiri bai saurara da dukana ba sai da ya
min liga-liga sannan ya kyale ni yana huci wai na fara
zama 'yar iska, wato an zo an zuga ki kun hadu ke da ita
ku ka dinga ci mata zarafi zagi ba wanda ba kuyi mata
ba, har da duka.
Na kalle shi cikin mamaki na ce "Ni aka ce maka?"
Ya ce, "Ko zata yi miki karya? Yanzu gata can
kwance bata da lafiya, sakamakon dukan da ku ka yi
mata har ya shafi cikinta.
Na dube shi hawaye na zuba na ce "Wallahi-wallahi
ba abin da ya shiga tsakaninmu, ko magana bare zagi har
ya kai ga duka na rantse me yasa zan dakar maka mata in
kuma kallon halin da take ciki."
Ya ce, "Za ki iya ai, sau nawa kina nuna adawarki
saboda kin kasa ki haifa su zauna gatanan shekararmu
nawa da ke, me naci riba da ke sai wannan wai 'ya mace
guda daya tal? To meye ma amfaninki?
Ni ba farin ciki nake da ita ba wallahi. Ina son magaji
namiji, wannan shi ne musababbin aurena, kuma gashi
114
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
nan da alama zan samu, yarinya mai albarka tana
kyautata min fiye da ke, ina jin dadinta amman kina
kokarin nakasa min ita."
Na ce, "Komai na Allah ne, ba ka fi ni son na haihu ba
su zauna, ba daga ni ba ne ko ita ma hakan yana iya
faruwa da ita don Allah ya nuna maka ikonsa."
Fadin wannan magana yasa ya kara hassala yaci
gaba da duk na sonr anshi sai da yaga bana motsi sannan
ya kyale ni ya fice yana maida numfashi.
Darennan ban iya ci gaba da bacci ba, na ci kuka har
na gaji hawaye suka kafe sai a sannan na fara nadamar
dawowata gidansa bayan tunda na dawo har zuwa yau
ban kasance tare da shi ba.
Haka naci gaba da zama gidansa ba wanda yasan
halin da nake çiki sai Luba, tana yawan kawo min ziyara
duk sanda tazo sai mun sha kuka ni da ita, ta so ta yi wani
kokari a kaina amman na hanata, ni nasan komai lokaci
ne, ba abin da ke dauwama.
Na cutu a gidan Baban Mabaruka nayi kuka nasha
115
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
duka na wulakanta a idonsa na koma shara me aiki tafi
ni daraja.
Allah cikin ikonsa, matarsa ta sauke a ranar da ta
haihu a ranar dan ya koma, wannan shi ne dalilin
rabuwata da shi.
Saboda hakan na faruwa ya ce ni ce na kashe masa da
don na yi masa baki cewar ita ma dan ba zai zauna ba,
don haka a ranar yai min kora ta wulakanci gaban
iyayenta da 'yan unguwa, yasa bakin wuta ya dinga
dukana gaban jama'ar ina kuka ina rokonsa har ya tillo
ni waje bai fasa dukana ba rigata ta yage zani na
kwance amman ya kasa saurara min.
a
Da kyar 'yan unguwa suka kwace ni ta hanyar rike
shi. Wani mutum ya cire babbar rigarsa ganin tsiraicina
ga mutane dankare, don haka ya rufe ni da ita a nan ya
min saki uku gabadaya.
Wata makociyata ta fito ta ja ni gidanta, ta ba ni
suturarta nasa har zuwa lokacin ban fasa kuka ba, cike
da takaicin wulakanci da tozarcin da ya min gaban maz
116
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
da mata yara da Kanana, ta dinga lallashina da ban
hakuri, ta ba ni waya na kira Luba.
Lokacin da tazo taji me ya faru ta harzuka matuka ta
nufi gidansa taci masa mutunci ni na hanata.
Tun daga wannan ranar mahaifin Mabaruka ya fice
min a rai, ina masa matsananciyar tsana babu wanda ba
na son jin ko maganarsa, irinsa bare na gan shi muka yi
rabuwa ta har abada.
Dole ina ji ina gani ya kwace Mabaruka ta ci gaba da
zama gun matar Babanta wacce ba kalar wuyar da bata
sha ba gunta.
Na dawo gidanmu da zama tare da matan Babana
zamanmu lafiya har hankalina ya kwanta damuwata ta
wuce, mahaifina yaci gaba da min addu'ar samun miji na
gari.
Haka Allah ya hada ni da Alh. Umar mahaifin Imran
kenan, tun ban amince da shi ba har na yarda muka yi
aure.
Ban taba tunanin ana samun namijin da ke nunawa
117
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
matarsa so da kulawa ba irinshi. Ya damu da ni da
matsalata, ya zame min tsani, rayuwata ta canza tayi
kyau farin ciki ya zauna tare da ni zamana lafiya da
mijina cikin tattali da kulawa.
Alh. Umar Allah ya azurta shi da tarin dukiya yanda
da kasuwanci kasashe-kasashe da gida Najeriya shi
kanshi bai san adadin dukiyarshi.
- Mutumin kirki ne me fara'a da son dariya, yana bada
taimako ga talakawa koda yaushe ya ware wani abu
daga dukiyarsa da yake rabawa mabukata a kullum.
Matarsa ta rasu da dadewa, Imran da Sharifat sune
kadai ta haifa, Balarabiya ce a wajan kasuwancinsa ya
hadu da ita a kasar Saudiyya, mai kamala da addini, 'yar
babban Malami ce a can akwai tarbiyya da nutsuwa tare
da ita.
Ta ba su Imran tarbiyya da ladabi daidai gwargwado,
sun fita daban, ko bayan zuwana sun dauke ni tamkar
mahaifiyarsu ban taba fuskantar wulakanci ba, ko
rashin kunya ba gurinsu.
118
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Imran ya yi karatunsa a (England) na Pilot har ya
kammala yanzu haka yana aiki a nan gida Najeriya.
Sharifa kuma ta bukaci tayi karatunta a Saudiyya a
kan Arabic, hakan yasa ta koma hannun dangin
Mamanta taci gaba da karatunta sai ta samu hutu take
zuwa gida Najeriya.
Ban taba ganin 'yan uwa masu son juna ba irin su
Imran da Sharifat mai sunan mahaifiyarsu. Imran ya
damu da Kanwarsa da damuwarta haka zalika ita ma
koda yaushe Yayanta.
Ta zauna tare da su Imran tamkar 'yan uwanta,
shakuwar da ke tsakaninta da Imran ya wuce misali, ya
dauke ta jininsa kanwarsa, zai fitga da ita yawo wuriwuri. Ita ma tana jin dadin kasancewarta da shi, sai su
wuni tare suna wasa.
Ta dubi Alkali "Wannan shi ne takaitaccen tarihin
rayuwata."
Alkali ya yi 'yan rubuce-rubuce sannan ya ce yana
119
WAYE ANGON?
kallon Baban Mabarukar.
Maryam Ja'afar
"Ka ji abin da ta ce, da gaske haka ne ko ka musa?"
Ya sunkuyar da kai sannan ya ce, "Eh haka ne."
Mabaruka ranta ya 6aci, hawaye suka dinga zuba ta
dinga kallon mahaifinta mugu azzalumi wanda ya
wulakanta mata uwa, ya tozartata. Ashe ma ba ya murna
da ita a samuwanta 'yarsa?
Haba shi yasa a kullum take yawan tambayar
mahaifiyarta me ya raba ta da Babanta? Ashe ba komai
ba ne a labarin sai wulakanci da tozartarwa, tabbas tasan
zata tsani mahaifinta, shi yasa taki fada mata.
Haushinsa ya darsu a ranta, ta dinga masa kallon
mugu.
Alkali ya sake cewa.
"Waye Sulaiman? Meye dangantakarka da shi?
Sannan me yasa ka hadata aure da shi?"
Ya ce, "Sulaiman kamar kani ne a gurina, don kanin
matata ne Binta, ubansu daya da ita. Ya kasance yana
zuwa gidana, idan ya zo kanshi tsaye yake shigowa
120
WAYE ANGON?
saboda tamkar gidansu ne.
Maryam Ja'afar
Yana yawan tsokanar Mabaruka a duk sanda yazo ita
ma takan biye mishi.
Tsawon lokaci suna tare da juna tun daga zolayar da
suke wa juna har suka fara soyayya tsakaninsu, hakan ta
bayyana shi da kanshị Sulaiman din ya min maganarta,
ya kuma bukaci da na ba shi aurenta a shirye yake ya
aureta.
Nayi farin ciki da haka, don nasan waye shi. Yana da
hankali da ilimi, matata ta kara karfafa min gwiwa. Na
kira Mabaruka na tambayeta ko tana sonshi zata iya
aurensa?
Ta ce, Sosai ma Baba na gamsu da Sulaiman na lura
da shi yana da hankali da ilimi, wannan yasa na yarda da
shi.
Na ce, Shi kenan kije na amince da aurenku har
bayan raina, ko da na mutu ki aure shi, ni ma na yarda da
nutsuwarsa.
Hakan yasa na shaidawa Sulaiman ya turo
121
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
magabatansa na ba shi auren Mabaruka, bai yi wasa ba
ya turo su muka yi magana.
Wannan shi ne musabbabin da na aura mata
Sulaiman."
Alkali ya gamsu, yasa aka kira Sulaiman. ed
Ya ce, "A takaice wanene kai?" Ya ce, "Sunana
Sulaiman Garba, mahaifina ya dade da rasuwa, na taso
karkashin kulawar mahaifiyata, ni da kanwata Samira,
nayi aure har sau uku ina da 'ya'ya biyu, amman yanzu
ina da mata daya ne sai Mabaruka!" sn ssdM LI
Aikali ya ce, "Ka ba da sadakinta kuma?" sanoi
Ya ce, "Sosai na ba da sadakinta da duk wani abu na
aure, kuma Kanin Babanta shi ya daura mana aure da
ita."
A kakira Baba Hamza. s
Alkali ya dube shi ya ce, "Kai ne kanin Mahaifinta?""
Ya ce, "Eh ni ne uwa daya uba daya muke, kumani na
karbi sadakinta kuma na daura auren tare da cikakkun
122
WAYE ANGON?
L
shaidu da waliyyai.
7Maryam Ja'afar
Alkali ya ce, "Ya a ka yi ka daura aurenta bayan ka
san an daura mata aure da wani?"
Ya ce, "Ban sani ba, nasan dai suna rigimar auren shi
da mahaifiyarta." Ya kara da cewa, "Kuma lallai na
daura kafin su su daura, hakan yasa ban yi was aba na
daura din."
Alkali ya gamsu, ya dubi Momy ya ce, "Ya a ka yi a
matsayinki na mace ki ka daurawa 'yarki aure da wani
bayan kin san Babanta ya daura mata aure da wani?"
Ta ce, "Ni ba ni na daura mata aure ba, kanin
Babanta shi ya daura mata aure, bayan yaga iyayen
יי
angon sun ba shi sadakin aure.'
Alkali ya ce, "Meye dangantarki da angon? Ya kuma
aka yi ki ka hada auren?"
Та се, "Kamar yanda na ce Imran dan mijina ne, na
dade da yabawa da dabi'unsa, nasan idan har Mabaruka
ta aure shi zata yi farin ciki ba gidan da zata ji dadi irin BD TDIN SUE
gidansa. ВРАве ua'nd idanrm snjswinlsa sua enui an
123
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Saboda yanda yake sonta da kuma ingantaccen
ilimin addini da ya samu, kuma yana aiki da shi. Imran
yaro ne mai nutsuwa da hankali, yana da tausayi
matuka.
Idan suna wasa in ta yanke ko ta fadi ina ganin yanda
yake damuwa da ita, duk yanayinsa ya sauya duk da
lokacin yana shekara sha takwas tana da shekara
takwas.
Ya taso da sonta da tausayinta, duk in yaje ya dawo
zai nemeta, sannan yana da matukar saukin kai da
hakuri, zan iya cewa ba wanda yasan Mabaruka da
yanda zai tafi da ita sai shi.
In ranta ya baci yasan yanda yake lallashinta, ita
kanta tana kasancewa cikin farin ciki tare da shi, har ta
girma ta kammala Sakandire.
Na barwa kaina suna son junansu ne kamar yanda shi
ma Baban Imran yake zato, wata rana ya gansu tare.
Yanda yaga suna nishadi da walwala fuskokinsu a kan
na juna suna sakarwa juna murmushi, ba su san da kowa
124
WAYE ANGON?
gabansu ba.
Maryam Ja'afar
Ina kicin ya shigo ya same ni fuskarsa da farin ciki ya
ce, "Kin san me?" Na ce, "A'a." Ina kallonsa.
Ya ce, "Wani abu nake gani a gidánnan, ban sani ba
ko ni kadai na gani." Na ce, "Me kenan?" Hannuna ya
jawo ya kai ni inda suke ya ce, "Kalli ki gani."
A lokacin sun koma suna hoto tare, da ka gansu zaka
fahimci akwai wani abu tare da su, na juyo ina dariya na
ce da shi.
"Ai in wannan ne ni na ma saba da gani kullum, kai
ne dai ba ka gani tunda ba zama ka ke ba."
Ya ce, "Ki ce haka suke amman ba ki taba sanar da ni
ba da gaggawa."Ya ce, "Ba ki fahimci komai ba ne?" Na
ce, "A'a shakuwa ce tsakaninsu."
Ya kara da cewa, "Da soyayya kuma." Na zaro ido
ina kallonsa, na ce "Iye!" Yayi dariya ya wuce, ya zauna
yana cewa "Yes."
Ni ma na zauna ina farin ciki, na ce "Amman ya aka
yi haka?" Ya yi dariya ya ce, "Ikon Allah mana, amma fa
125
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
zan fi kowa farin