mace! Da
sauri ta mike ta shige toilet.
A iya bincikenta bata ga alamar hakan ba, amman
duk da haka ta kasa fitowa, taci gaba da kukan tana
watsa wa fuskarta ruwa.
Jinta shiru ne yasa ya dinga kwankwasa mata kofar
ta fito bata jin zata iya amsawa bare tayi abin da yake so.
Tayi banza da shi, iya dukan kofar ya yi amman ta ki
budewa.
Har gari ya waye tar bata fito ba, taci kukanta har ta
gaji tayi zaune jagwam hannu biyu a fuska ta rafka
tagumi.
Tunda safe su Momy suka zo hade da breakfast,
koda taji motsinsu bata yi alamar fitowar ba, zamanta
tayi abinta.
150
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Momy ta dube shi ta ce, "Ina Mabaruka?" Ya yi
murmushi ya ce, "Tana bandaki." Ta kalle shi da kyau
"Bandaki kuma, a can ta kwana?" Ya ce yana dariya,
"A'a a nan ta kwana, yanzunnan dai ta shiga."
Sai can ta fito tana kumbura baki, fuskarta tayi jajir
idanuwan kuma sun kumburo da ka gani kasan tasha
kuka.
Momy ta bita da kallo har ta zauna can ciki ta ce "Ina
kwana?" "Lafiya." Kawai ta ce ta kara da cewa "Me ki
ke a bandaki tun dazu?" Ta sosa wuya kanta na kasa ta
ce, "Abu nake."Ta kura mata ido kawai.
Sharifat ko kallonta bata yi ba bare su gaisa, haka ita
ma ta share ta a halin yanzun duk abin da ya shafe shi ba
sonshi take ba, ba ya burgeta bare ya tsaya gabanta.
Tana kallon yanda suke nan-nan da shi ko ya ya
motsa sai sun ji menene, me yake so? Shi kuwa idonshi
na kanta duk ya ta motsa yana jin matsanancin sonta na
fizgarshi.
Fushin ma da take burge shi take. Aka tila masa
abinci kala-kala ya ci ya gagara kai loma daya bakinsa.
Tunaninsa ita ba ta ci ba shi ma ba zai iya ba, dama ita
suke tattali ba shi ba da yafi samun kwarin gwiwa da
kuzari, me yiwuwa yaci ganin tana ci, amman a halin
151
WAYE ANGON?
yanzu ba zai iya ci ba.
Maryam Ja'afar
Yasa abincin gaba yayin da yake kallonta ta wutsiyar
ido.
Sharifa ta ce, "Big Bro ka ci abinci mana, yana
hucewa." Ya dago yana kallonta tare da sakar mata
murmushi iyakarsa fuska ya ce, "To." Kawai.
Momy ta ce, "Ko ba shi ka ke so ba?" Ya ce, "A'a ina
so." Ta ce, "To maida hankali ka ci ga magungunanka
me yiwuwa ma Likita ya sallame ka yau, naga jikin ya yi
kyau sabanin jiya."
Ya yi murmushi yana kallon Mabaruka da har
yanzun fuskarta a turbune take. Ya dubi Sharifa ya ce da
ita.
"Dauko plate ki zuba abinci kamar yanda ki ka zuba
دو
wannan.
Ta dube shi tana son sanin me zai yi da shi kuma?
Shima ya dubeta ya ce, "Yi mana."ta wuce tayi kamar
yanda ya ce, ta zuba a plate dinsa ta kawo masa.
Ya nuna mata Mabaruka ya ce, "Kai mata." Ta kalle
shi da sauri zata yi magana, ganin yanda ya hade fuska
yasa ta saurara, amman duk da haka sai da ta ce a
shagwabe.
152
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
"Ni zan zuba mata Yaya, ita bakuwa ce da sai an zuba
mata? In ta ci cikinta ne fa in bata ci ba wa ta yi wa?"
Ya kalleta da kyau sannan ya ce, "Ni taiwa."Ya ki
dauke kansa, ita ma ta kura masa ido.
Ya ce, "Yes kije kiyi abin da na saka ki." Ta zobaro
baki ta wuce. Da zuwa ta dankwafar da shi gábanta ba
tare da ta ce komai ba."
Ta dawo kusa da kafarsa ta zauna tana turo baki, ya yi
murmushi kawai yasan duk abin da take don shi ne, ya
dubeta ya ce, "Na gode kanwata."Ba ta ce komai ba.
Mabarukar ta dubi abincin ta harare shi, sannan ta
dago tana kallon Sharifat din tana hararanta ta ce "Zo ki
dauke abincinku ba na so."
Kan ta gama rufe bakin taji saukar duka a bakinta
kuf! Momyn ta ci gaba da kallonta ta ce "Ba ki da
mutunci daman ko, ita tasa kanta ne meye laifinta don ta
kawo miki abinci? Kar ki ci wa ki kaiwa in ba ki ci ba?"
Ta ci gaba da turo bakin ta ce "To kar kici bar shi don
Allah."
Ya dubi Momy a marairaice ji yake kamar shi ta daka
har sai da ya zabura. Ya ce, "Sorry Mom! Ayi hakuri zata
ci ai ba ki ga yanda ita ta dire shi ba ba ladabi ba da'a,
dole ne tayi fushi ta ce bata ci."
153
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Fadin maganar da ya yi yasa ta dago ta harare shi ta
kauda kai, ya mayar mata da murmushi.
Momy ta ce, "Kai rabu da ita, kar taci." Sam bai so
haka ba, yana lalla6a kayansa sun zo za su hargitsa
mishi ita.
Hannu Momyn tasa ta dauke plate din gaba daya ta
ce "Mu muna so zamu ci wallahi." Ana dauke abincin ta
mike kafafüwa tana turo baki tamkar daman ya tare
mata gurin.
Ya ce, "Ayi hakuri Momy." Ta ce, "Kai kaci
abincinka ka fita bukatar ci." Shi ya sani sam ba zai iya
ci ba in har ita ma ba za ta ci ba.
Ya sauko daga kan gadon, ya dauki abincin zuwa
gabanta, da Momy da Sharifa suka bishi da kallo, me zai
yi?
Ya tsugunna gabanta fuskarsa sake yana jin wani
dadin zuwa da ya yi kusa da ita. Ita ko sai turbune fuska
take bata ko kallonsa.
Ya ce, "Mabaruka!" Tayi shiru kamar bata gun. Ya
sake kiranta a can makoshi ta ce "Na'am." Ya ce,
"Menene wai, me ke damunki?"
Ta dago tana harararsa, ya yi saurin kama
154
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
kunnuwansa ya ce a hankali "Sorry!" Ta dauke kanta ya
ce, "Me yasa ba za ki ci ba, kina son nima kar na ci ko?"
Tayi masa banza. Ya sake cewa "Ko ba kya sonsa nasa a
siyo miki abin da ki ke so?"
Tamkar bata nan bare ta amsa, ya sake cewa
"Mabaruka me ki ke so?" Ta ce can kasan makoshi
ganin yanda Momy ke harararta "Ba komai."
Ya ce, "To za ki ci wannan din?" Kai ta daga kurum
don ya kyaleta, ta gaji da maganarsa musamman yanda
ya tsugunna gabanta gaf har tana jin kamshin turaren
jikinsa me sata tashin zuciya.
Ya cè, "Kin tabbata za ki ci?" Ta ce, "Eh." Ya ce,
"Sosai fa." Ta daga kai. Ya ce "Yawwa Mabaruka, don
Allah kici ba don mu ba, nasan ba mu isa mu sa ki dole
ba kiyi abin da ba ki so, amman don Allah zo ki ci don
nima na ci, wallahi idan ba ki ci ba ni ma ba zan ci ba."
Ta ce a gajiye "Naji zan ci."
Ya yi dariya ya ce, "Na gode." Daga haka ya mike ya
koma ya zauna. Wani kululun bakin ciki ya tokare
Sharifat, mikewa tayi ta bar dakin sam ba za ta iya jurar
ganin haka ba.
Momy kuwa duk yanda take jin haushinta taji dadi
155
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
1
ganin yanda ya yi tasan lallai watarana sai son da yake
mata ya dawo ita ke masa, a dai juri zuwa rafi wataran
tulu zai fashe, Imran ba na yadawa ba ne.
Kan dole yasa ta dinga tuttura abincin tana yi tana
goge kwalla. Wallahi sam bata jin dadin abincin, duk da
yanda aka zauna aka kawata shi tana da tabbacin ba mai
dandana abincin ya bari.
Idan gasa ake wanda ya girka abincin shi ne zai ci,
amman dalilin shi ya dauko shi da hannunsa ya ce taci
kuma shi aka dafo mawa yasa take ji ba wani abinci
marar dadi a duniya da ya kai wannan.
Ko kadan bata jin dadinsa, tamkar tana zuba wuta a
cikinta haka take ji har tana fitar da kwalla saboda
takaicin cin da take.
Shi kuwa ganin tana ci dinne yasa ya samu karfin
gwiwa yaci sosai yana ci yana motsa kunne ga dadi a
ransa na ganin tana ci ga shi ga ita.
Yasan watarana ita zata girka masa suci tare har ma
ta ba shi a baki. Ya ci abincin sosai sai da ya kusa tada shi
sannan ya saurara.
Tura abincin take tamkar ba zata bari ba, tayi
alkawarin duk yawansa sai ta cinye ba za ta bari ba, duk
156
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
da yafı karfinta ko da zata yi amai ne, tunda har aka
matsa mata sai taci.
Don haka ta dinga tura shi tana yunkurin amai, ya
tashi zaune yana kallonta yanda take turawa shi ya sani
ba da son ranta ba, amman ai bai ce ta cinye ba, ko ya taci
ya isa me yasa to take haka?
Gani ya yi Momy ta daddage ta kai mata dundu a
baya cikin tsananin fushi, saukar dundun ya yi daidai da
saukar abincin gaba daya ta amayo shi duk a kan plate din.
Ya miken a zabure yana cewa, "Sannu-sannu
Mabaruka." Hankalinshi ya tashi ganin tana amai, ya
dubi Momy a marairaice.
Ita kuwa ta ce "Ke dai 'yar wulakanci ce Mabaruka,
kin koshi shi ne ki ke turawa wato tunda ya ce kici shi ne
sai kin ci wanda yafi karfinki, ke dai ki bata masa ko? Ya
ji haushi? To kin kyauta.Shi yasa nima na taimake ki ki
ka amayo shi."
Ran Momy fa ya baci, ta dinga fada inda take shiga
ba nan take fita ba, kawai ta suri makullin motarta ta fice
fuuu!
Ita kuwa tana duken ko motsi bata yi ba, tayi face157
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
face da amai idanunta sun sauya jajir saboda bacin rai, a
ganinta an takura mata, yanzun in ban da so ake a mata
fada, don me zata mata dundu don dai ace bata kyauta
ba, kuma duk sanadin Imran..
Ta dago tana kallonsa da jajayen idanunta, kallon na
tsane ka. Ya tsugunna yana cewa "Sannu, sannu
Mabaruka."
Ba abin da ya fito bakinta sai "Na tsaneka! Na
tsaneka! Ba na sonka, ka shiga rayuwata, ka takura min
daga farin ciki ka mayar min ita zuwa bakin ciki.
Sanadiyyarka yau na tsinci kaina mahaifiyata na
dukana tana zagina, ina ganin 6acin rai a idonta, wanda
da ba na fuskantarshi a gunta, ko kallon banza bata taba
yi min ba bare duka ko tayi fushi da ni.
Duk kai ka jawo min, don Allah me yasa ba zan
tsaneka ba? Me yasa ba za ka zamo makiyina ba?
Wallahi ko numfashinka ba na so, ka takura min, ka
takura min!" Ta fada da karaji, jikinta har yana rawa
hawaye na zubowa.
Ya ce, "Me yasa har haka Mabaruka? Wallahi ban yi
miki sanadin har haka ba. Ni kawai na ce ina sonki ne,
don kuma na ce haka bai isa yasa mahaifiyarki ta dinga
miki wadannan abubuwan ba, meye laifina? Ni fa..."
158
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ta katse shi da tsawa "Na..." ba ta karasa ba ta
Kakalo aman ta watso mishi a fuska, tana huci tana
kallonsa.
Ya yi cak yana kallonta, fuskarshi dame-dame da
aman har zuwa rigarsa. Farin ciki ya bayyana fuskarta,
ganin ta bata masa rai.
Kamar a mafarki taga yasa hannu ya gogo aman na
fuskar ya tsotse a baki. Sai da ta rintse ido tsikar jikinta
ta tashi saboda kyankyami, zuciyarta ta tashi.
Wani aman yazo, tayi saurin tare shi da hannu taci
gaba da kallonsa, bai fasa ba sai da ya lashe aman
gabadaya na fuskarsa duk yana kallonta.
Zuciyarta ta sake tasowa matuka, ta dinga yunkurin
zubo da shi, da sauri ya rikota ba shiri taji bakinta cikin
nasa yana tsotso, ba ta san sanda aman ya koma ba.
Duk wanda ya bata ta a baki sai da ya lashe shi tas ya
hade da bakin, ta dinga kokarin kwatar kanta amman
ina! Ta kasa duk kokarinta, sai don karin kansa ya sake
ta.
Ta dinga huci idanunta suka fito tamkar zakanya,
tana harararsa yaci gaba da kallonta ya ce, "Ina sonki, na
fada miki yafi a kirga na kuma nuna miki shi a
159
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
zahirance, ina sonki bar haka a ranki. Ni Imran ina sonki
har abada."Ya fada yana dariya.
Takaici ya hanata magana har tana ina ma ta bari ya
hada bakinta da nashi tir! Ta dinga tofar da yawu tana
goge baki.
Mikewa kawai tayi saboda abin ya kaita karshe ta
kalle shi da kyau hawayen takaici suka zubo ta ce,
"Allah ya isa." Daga haka ta wuce bandaki da gudu,
kuka na son kufcewa.
Ya yi murmushi ya ce, "Na gode." Bai damu ba, ko a
jikinsa da kansa ya kwashe aman ya goge wurin.
Koda ta shiga bandakin kuka ta dinga yi kamar ranta
zai fita, bata taba jin takaici irin na yau ba, duk yanda
take kyamarsa amman ya hada bakinta da nashi yasa
mata miyansa.
Ta dinga wanke baki tana kuka har sabulu tasa ta
dinga dirza, amman sam ta kasa nutsuwa da ta wanke
bakin miyansa ya fita.
Koda Likita yazo yaga jikinsa ya ce yana dariya "My
friend ka warware ko?" shi ma ya yi dariyar ya ce,
“Sosai na ware, ina jina zan iya fada da ko da zaki ne."
Ya yi dariya sosai ya ce, "Yes! Yes, I see, amman har
160
WAYE ANGON?
da taimakon Madam ko?"Ya yi dariya kawai.
Ya sake cewa "Lallai ta kyauta."
Maryam Ja'afar
An ba su sallama a ranar zuwan Rafi'atu kenan, ta
tarar suna hada kayansu. Tana kallon Mabarukar tasan
akwai abin da ya faru.
Suka zauna ta dubeta da kyau ta ce, "Fada min me ya faru? Ko angon yasha dumin amaryarsa jiya?"
Wata harara da ta dalla mata sai da ta tsorata, taja
baya tana dariya. Ta sake cewa "Ah to, naga sai wani
hada rai ki ke nasan wannan ne kadai zai sa kiyi kuka har دو idanunki su nuna.
Tayi kwalkwal zata yi kuka, ta dubeta ta ce, "Kema
ba ki sona Rafi'a tunda har kina hadan ni da wannan dan
iskan ke a tunaninki shi ne Angon?"
Rafi'a ta ce, "Ban sani ba, don ba zan iya warware
wannan hargitsin ba."
Ta ce, "Amman dai kin san Sulaiman shi ne Angon,
saboda shi Babana ya aura min ba Imran ba, kuma kowa
ya sani mace ba ta daura aure, kin ga kenan iska ya
kama.
Don haka ba zan taba yarda da shi ba, bare wannan
abin da ki ke tunani ya faru tsakaninmu, tunda ba mijina
161
WAYE ANGON?
ba ne."
Maryam Ja'afar
Ta ce, "Eh mace bata daura aure amman ke kin san
Baba.shi ya daura muku aure kuma shi ma yana iya
daura miki aure."
Ta ce, "Ko ma dai menene Sulaiman shi ne mijina ba
gidan da zanje idan ba can ba."
Rafi'a ta ce, "Shi kenan naji yanzu ma ki tashi ki tafi
kar ki makara, amma dan fada min me ya miki har ya sa
ki kuka idanunki suka kumbura?"
Tsaki taja tare da kauda kai alamar sai ki tayi.
Su suka haďa kayansu ko hannu bata sa musu ba har
suka gama suka fice, Rafi'atu ta jawo hannunta suka rufa
musu baya.
A ranar aka sallami Sulaiman saboda sallamar da aka
yi wa Imran din, amma yasha duka.
Koda ya koma gida Inna ta zaunar da shi gabanta ta
miko masa biro da takarda ta ce, "Sakar musu 'ya!" Ya
dubeta a tsorace saki Inna? Ni fa ina son matata, ta ya
zan sake ta?"
Та се, "Та yanda ka fara jawo mana fitina don
ubanka so ka ke na kyaleka ka dinga zaryar zuwa kotu
162
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
ana garkame ka a magarkama? To ba zai yiwu ba
wallahi.
Ga matarka can a daki ita ta dace da kai ba wannan
'yar mahaukatan ba."
Ya turo baki "Ni gaskiya ina sonta ba zan sake ta ba,
bayan wahalar da na sha ga kudin da na kashe sai su
tashi a banza?" Yana rufe baki ta dauka.
"Sai a biyaka kayanka, ai ba su ci banza ba, nima ban
goyi bayan ka bar musu ba, ni da kaina ma sai in amso su
ba a bar musu ba.Ko Samira sai ka ba kayan shi kenan.'
Ya ce, "Gaskiya ba zan iya ba, kowa yasan matata ce
ni ne Angon."Ta jawo karan dake kusa da ita.
"Sai in kwade ka wallahi, kai ne Angon banza!
Sakarai fanko, kai kana ganin za a baka ne har zaka iya
ja da shi? Shi fa mai kudi ne karfinku ba daya ba, zai iya
sayenta da kudi ya dankarawa kotu da 'ya'yanta kudi
tuni su ba shi sai dai ka sha kunyar banza.
Don haka tun kan ayi ka rabu da ita ka bar masa
kawai, ba dai karfin ja da su ka ke da shi ba wahala
kawai za ka yi."
Mikewa ya yi tare da shurar takalma yana cewa, "Ba
zan iyan ba, ina son matata ki min addu'a kawai." Daga
haka ya ficе.
163
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ta dago murya "Sulaimanu ina magana ka sa
takalma ka fice ko?" Ina! Bai ji ta ba tuni ya fice.
Ta kulu matuka, "Za ka dawo ka same ni don
ubanka."
Samira dake gefe ta ce, "Kema dai Inna ki kyale shi,
in ya sha wuya zai gane shi ya sani tunda an fada masa
ya kiji."
Ta ce, "Ba zan kyale shi ba, in bar shi ya kare a zuwa
kotu ana sakaya shi tun kan abu ya yi nisa gwanda ya
دو kyale musu mata ba dai tashi ba ce.
**
Tun a mota ta ce ita a sauketa gidan Babanta za
sauka. Kallonta Momy bata yi ba bare ta bata amsa.
ta
Su uku ne a motar da Momyn ita ke tuki, sai ita da
Rafi'a shi kuma suna a motar Sharifa.
Ta dinga turo baki tana fushi har suka iso, ta fito tana
6ata rai duk suka shige amman ita ta ki shiga, taja tayi
tsaye tana kumbure-kumbure.
Rafi'a ta ce, "Wai menene haka Mabaruka? Ke dai ba
kya jin magana ko tun yaushe ake fama da ke kan abu
164
WAYE ANGON?
daya son ranki ki ke bi ko?"
Hararar Rafi'ar tayi tare da kauda kai.
Maryam Ja'afar
Ta ce, "Na gode, na sha fada miki ba zan goya miki
baya a kan rashin kunya ba, tuni zan kama gabana.
Tunda ke ba kyaji ki zo mu wuce ciki."
Kallonta bata yi ba bare ta wuce din, don haka ta
janyo hannunta da karfi, amman ta tirje duk iya
kokarinta ta kasa janta.
Taji haushi matuka, don haka ta sake ta. Ta ce "Shi
kenan kada ki shigo." Daga haka ta shigewarta.
Koda ta shiga duk suna falo, Mommy ta dubeta ta ce,
"Ina Mabarukan?" Ta zauna tana cewa "Ta ki shigowa."
Shiru tayi ta rasa me zata ce. Mabaruka na son fin
karfinta, shin wai ya zata yi da ita?
Daddyn Imran din ya shigo da hancin motarsa, ya
fito. Suka yi ido biyu da ita ya karaso har inda take ya
dubeta ya ce "Ya aka yi ne Mabaruka ki ke a nan?"
Ta ce, "Ba komai nafi son nan din ne."
Ya yi murmushi, shi yasan dalili. Don haka ya jawo
hannunta yana cewa, "A'a yaushe za ki tsaya a nan kowa
na ciki, zo muje."
165
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ta ce, "Ni fa in na shiga takura ni suke har dukana
take."
Ya ce, "Ina nan ba mai taba min ke, zo muje."Yajata.
Don dole ta yarda ta shiga din har lokacin fuskarta ba
ta sauya ba. Ya zauna yana cewa, "Don me za ku matsa
mata har a hanata shiga gida?"
Momy ta ce, "Wa ya hanata? Ita ta hana kanta kan
shegen kafiyarta."
Imran da yake kishingide ya tashi zaune yana
kallonta. Suka hada ido biyu da shi, ta dallo masa harara
tare da kauda kai, yayin da ya yi murmushi ya ci gaba da
kallonta din.
Sharifa ta turbune fuska ta jawo waya tasa earphone
a kunnanta kar ta saurari me ake cewa, duk don
Mabarukar.
Ganin yanda ya matsa mata da kallo yasa ta dubi
Daddyn ta ce, "Zan shiga ciki in kwanta Daddy."
Ya ce, "Ba laifi, jeki ki huta." Ba ta ce komai ba ta
mike tayi wucewarta tana harararsa.
Momy ta bita da kallo har ta shige dakinta, ta juyo da
kallonta gun Daddyn tana cewa, "Sai shegen fadin ran
166
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
tsiya, ban taba ganin yarinya mai kafiya irinta ba."
Ya ce, "Za ta bari alamar nasara kenan, zamu sha
mamakinta." A nan Imran din ya ce "Ku ku ke damuwa
da haka, ku bar ni da ita ni nasan yanda zamu kare."
Momy ta ce, "Allah ya nuna min wannan ranar."
Rafi'atu ta сe, "Kuma Mabaruka saukin kai ne da ita,
abu kadan zai sa ta tsani mutum kuma abu kadan zai sa
ta so mutum.
Idan ina tambayarta me yasa take son Sulaiman? Sai
ta ce min ita har yanzu bata ga dalili ba, ita dai kawai
tasan tana sonshi. Na ce ko wani abu nashi ba ya
burgeta? Ta ce ita bata ga komai ba, na ce to me yasa ba
ta son Imran din? Tayi shiru har saida na taba ta na ce me
yasa ta tsane shi?
Ta dube ni ta ce, "Ban sani ba Rafi'a, ni dai kawai
nasan ba na sonshi na tsane shi, haka nan ko muryarsa
bana son ji."
Na ce, "Ko wani abu da yake miki yasa ki ke jin
haushinsa?'Ta yi shiru, sannan ta ce "Ni dai kawai ba na
sonsa." To a haka yasa na ce kamar bata san ma meye
son ba, meye kiyayyar ba."
Daddy ya yi dariya ya ce, "Zata bambance idan taje
167
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
gidansa." Momy ta ce, "To ta ya ya kenan zata
bambance da kanta har tasan meye son bayan tasawa
kanta tsanar?"
Rafi'a tayi dariya tana kallon Imran, ta ce "Wannan
kuma aikin Imran ne." shima ya yi dariyar yana mikewa
ya ce, "Sosai kuwa."
Momy ta ce, "Ina za ka ne?" Ya ce "Wanka nake so
,, nayi."
Lokacin da Rafi'ar ta shiga dakin Mabarukar tana
waya ta hau gadon ta zauna tana sauraronta, da
Sulaiman ta fahimta suna waya, rabi duk shagwaba take
masa.
"Don Allah Sulaiman kazo ka dauke ni daga nan,
wallahi kokarin raba ni da kai suke, bayan kai ne
Angon."
Daga can ya ce, "Kada ki damu Mabaruka, kowa
yasan ni ne aka daurawa aure da ke saboda Babanki shi
ya daura min aurenki, kowa kuma yasan uba shi ke da
aure ba uwa ba, babu in da uwa ke daura aure, don haka
ni ne Angon babu in da za kije gidana za ki zo."
Ta lumshe ido tanajin damuwa a ranta.
Ta ce, "Allah yasa Sulaiman, ka dage don Allah kar
168
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
kayi wasa a raba mu." Ya ce, "Insha'Allahu ba mai shiga
tsakanin masoya ni da ke."
A haka suka gama wayar, tayi lamo idonta a rufe.
Rafi'atu tasa hannu ta dauke wayar ta dubeta ta ce,
"Mabaruka!" Ta bude idonta tana kallonta tare da cewa
"Na'am!c
Ta ce, "Na kagara ayi ta ta kare a yanke hukunci a ba
mai mata matarsa."
Da sauri ta tashi zaune idanuwanta suka yi rau-rau a
yanayin tsoro take kallonta, ta ce "Ina tsoro Rafi'a,
zuciyata ta dade da karyewa kullum cikin zullumi nake,
wallahi ina tsoron kar kotu ta yanke hukuncin da zai yi
sanadiyyar ajalina."
Ta dubeta da kyau ta ce, "Me ki ke nufi kenan?"
Ta ce, "Idan har kotu ta tabbatar Imran shi ne angona
zan mutu ne da na rayu da shi."
Та се, "Mabaruka kin san me ake nufi da mutuwa
kuwa?" Ta ce, "Na sani Rafi'a, don tafi min ko kadan
bana jin walwala kasancewar da shi ake rigimar nan,
koda muryarsa na tsana bare in gan shi har naje gidansa
a matsayin matarsa.'
Ta ce, "Shi yasa na kagara a yanke hukunci ke
zuciyarki ta huta mu ma mu huta, ki daina daukar
169
WAYE ANGON?
zunubbai."
Maryam Ja'afar
Ta dubeta da kyau ta ce, "Zunubbai kuma, wadanne
kenan?" Ta ce, "Kasancewarki tsakanin daya daga
cikinsu kina magana ko ma suna taba jikinki alhalin ke
matar aure ce matar wani ce ko Imran ko Sulaiman."
Ta ce, "Har kina tunanin in nayi magana da dayansu
ina da zunubi alhalin bani da laifi, ban san waye angon
ba?"
Ta ce, "Ban ce dama kina da laifi ba, amman ki taka
tsan-tsan har zuwa lokacin da za a tantance waye
angon?"
Tayi shiru hawaye na kokarin zubo mata, tsawon
dakiku sannan ta dubi Rafi'ar cikin mutuwar jiki da
kasala bakinta ya yi nauyi kamar zata yi kuka ta ce,
"Dole ne daya daga cikinsu, ko Sulaiman ko Imran dole
daya za a ba ko Rafi'a?"
Ta ce tana kallonta "Sosai, daya ke da mata daya ya
kama iska." Hawayen suka zubo ta ce, "Ya zan yi kenan
idan Imran aka ba?"
"Hakuri mana, ki koya wa kanki sonshi ki hakura da
Sulaiman, don samawa kanki lafiya da neman Aljanna.
In ji Rafi'atu.
170
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
"Ba zan iya ba Rafi'a, ba zan iya rayuwa da shi ba, ko
na awa daya ne."
Ta ce, "Za ki iya Mabaruka, an yi sau dubu kuma sun
zauna lafiya, in kin gan su za ki sha mamakin soyayyar
da suke wajunansu."
Ta ce, "Kin san kuwa me ake kira da tsana da rashin
so Rafi'a? har abada ba zan taba sonsa ba wallahi."
Bakin Rafi'a ya kulle bata da abin cewa, kallonta dai
take cike da mamakinta.
Ta ce, "Insha'Allahu Sulaiman shi ne mijina, da shi
zan yi rayuwata mai kyau da tsafta, farin ciki da
walwala."
Ta ce tana kallonta "Ni kuma ina miki addu'a Allah
yasa Imran shi ne mijinki saboda gujewa da na sani gaba
a rayuwarki, kuma shi ne farin cikinki mai dorewa."
Kallonta take tamkar ta kife ta da mari, amman ganin
ba za ta iya ci mata fuska har haka ba yasa ta mike
gabadaya ta diro daga gadon ba tare da ta ce komai ba.
Ta ce, "Ina za ki je?" Ta ce ba tare da ta juyo ba
"Wanka zan yi." Daga haka ta shige.
Rafi'ar ta taso tazo har bakin toilet din ta ce, "Idan an
ce ke da Imran kun dace da juna sai ki ce a'a, alhalin
171
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
ra'ayinku daya. Yanzu haka shima yana can ya shiga
wankan.
Haka nan ya ji yana son yin wankan, ke ma gashi nan
kin shiga don kiyi kawai don haduwar junanku."
Jin wannan maganar yasa da sauri ta saki sabulun da
ke hannunta, ranta ya baci ta yayumo tawul ta daura ta
fito ta bita da kallo tana cewa.
"Lafiya, me ya faru ki ka fito?"
Ba ta kallonta ranta a 6ace ta ce, "Na fasa." Ta fara
maida kayanta. Rike baki Rafi'a tayi tana kallonta cikin
mamaki ga dariya na cinta.
Ta ce, "Kanki ya fara tabuwa ko tsanarsa har ta kai
haka?" ba ta saurare ta ba ta koma ta zauna bakin gadon
tayi shiru. Ita kuma Rafi'a ta ci gaba da magana.
"Lallai Mabaruka aiki na gabanki