karata
kunena tare da tambayar ko waye? Yauma muryar wata mace
naji. A raina nace wai shi Yaya Auwal bashi da mai yo masa
waya sai mata. Nace "wace ce?" ita tambayar aka maimaitamin
dan kuwa itama tambayata tayi da cewa, "ke wacece?" Nacе
"Kanwar sace".
'Tayi dariya tace, hakika to amma ai ya taba gayamin cewa
bashi da babbar kanwa. Dan Kanwarsa bata fi 'yar aji daya na
sakandireba, wacce take ita ce babbar kanwarsa, amma ke da
jin muryar ki an san kin wuce haka hakika wayanki da
kwarjinin ki, da iya maganarki ya nuna cewa ke kin wuce gejin
wannan ajin ina ga ma in ban yi karya ba zan iya dangantaki da
wayayyiyar budurwa da gejinta ya nuna 'yar jami'ace".
"Turkashi, baki yarda ba kenan kada ki dauka da gangan
nake miki wallahi ni kanwar sace, shi ma yaya Auwal din
mantawa ya yi dani". "To ai shikenąn koma dai mecece ke a
gurinsa kice dashi Asiya ce, shin yana ma ina? "Bacci yake a
tashe shi? Nace da ita. A'a rabu dashi kawai in ya tashi kice ya
nemeni a waya". "To" yayin da ta kashe wayar nima na kashe
na ajje, dan ma kada a kara tasoni.
"To kuma ina zaki?" tambayar da naji Yaya ya min kenan,
a lokacin da yake kokarin mikewa zaune. Yace "Ke kuma wa
yace ki shigomin har cikin dakina? Gabana yayi mugun
faduwa, nace, "ma-ma-Mamace tace in zo in fau waya, kuma
na duba wayar ban ganta a falo ba shine na zo nan na dauka.
72
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
Yar kauye shine kuma har da tambayar wa za'ace masa shin ke
baki san duk wanda ya bugo wayar zaki ga sunansa ajiki ba?"
No ba haka bane, amma ai wani lokacin akan ara a buga
musamman wannan da naga an rubuta A.A. Saida jiki, ta yaya
za'ayi in tababtar da mai sunan.
To ai koni ban fahimtaba yayin da yayi murmushi, ni
kuwa na rasa dalilin da yasa duk jikin yaya san yi. Na sinkuyar
da kaina kasa nace, "tace wai sunanta Aisha" Ya saki wani
wawan tsaki yace, "to" Na ji zan tafi ya kara dakatar dani, tare
da sakarmin wani irin kallo wanda a waccan lokacin ban
fahimceshi daidai ba. Sai daga baya yace Humaira ki jirani
daga falo ina zuwa" Nace "to".
Tun da na zauna a falon na ke jin gabana na faduwa
hakika ban san takamaiman abinda Yaya yake son gayamin ba
lokacin da yaya ya fito sanye da doguwar rigar ya tarar dani a
tsaye, a tsakiyar falon ya kara kallona ya yi murmushi yace,
Malama Humair ake nan da mata suna aikin sojoji ai da sai in
kiraki kwamanda. Dan Allah ki zauna wata magan ana ke son
in tambayeki, koda yake tun tuni na so in yi miki wannan
tambayar to amma a lokacin hakan bai samu ba saboda baki
bada hadin kai ba.
To amma tunda yanzu kina da lokaci shikenan tun da
damani ko da yaushe a shirye na ke. Humaira duk da cew ana
tabbatar da abin a idona to ina san ki kara nanatamin domin in
tababtar da hakan. Humaira na taßa tambayarki cewa kina da
saurayi kika ce dani babu. To amma abin mamaki sai gashi na
gani da idona. Hakika dama na taba jin cewa Nasir kanan
Hajiya Rabi saurayin kine, kuma kina matukar sonshi, to amma
ta nan na karyata domin kuwa na gani da idona to amma wani
hanzari ba gudu ba. Dan Allah ina son ki sanar dani gaskiyar
lamarinki. Dan Allah Humaira wanene masoyinki wanda kika
tsaidashi a zuciyarki? Humaira ina da wani babban dalili da
yasa nake tambayarki hakan da fatan tambayar ba zata takura ki
ba".
Turkashi hakika ni na rasa ta inda zan bullowa Yaya
Auwal ya yarda dani hakika ni har ga Allah ban taba yin wani
saurayin da na ajjeshi a zuciyata ba. In har nace bantaba yin
saurayi ba. Hakika nayi karya, na kuma yaudari kaina. Domin
73
Lubabah!
ba lallai bane kowa ya yarda da hakan. 'To amman zan iya
rantsewa akan cew aban taba tunanin ajje tunanin saurayi a
zuciyata ba. na daga kaina a hankali na kalli Yaya Auwal nace.
"To waini yaya Auwal me zance maka ka yarda dani na
rantse maka da Allah bani da wani gwani yaya hakika in har
nace da kai ban taba yin saurayi ba nayi karya, to amma har
yau Allah bai hadani da wanda ya kwantamin ba kuma ma ni
yaya duk wannan ba shine a gabana ba face karatu".
"To naji, amma in ba zaki damu ba ina fatan nan da wani
dan lokaci za'a bani damar in sanar da ke abinda ni na tanadar
miki, in ga ko Allah yasa a dace. "To Yaya babu damuwa yace,
dan Allah yau in zan fita zan baki mukullin dakina ki
gyaramin". Nayi murmushi nace babu damuwa".
"Tun da kika tafi, daga daukar waya mai ya tsayar dake
haka, cewar Mama. Nace Mama Yaya ne ya tsayar dani yace in
share masa falon, ashe fita yayi shi yasa wayar take ta ruri". "Ai
nayi zatan ficewa kika yi nan mukaci gaba da zamanmu.
Tun daga wannan ranar ni nake yiwa Yaya shara safe da
yamma. Akwai wani yammaci da muke zeune da Mama da
kuma Maryam muna ta hira maryam tace, "Yaya Humaira wai
me yasa in kin shiga dakin Yaya baya dukanki?" Na yi
murmushi nace, "Mary kenan shin ke in kin shiga dukan ki
yake yi?" "E mana mu dukama fada yake mana ke kadaice
baya miki fada".
"To in banda abinki Mary bakya ganin ni shar anake masa,
ai shi yace kullum in ringa share masa dakinsa. "E kuwa na
manta Yaya Humaira. To amma ai ke har wasa yake miki? Kin
tuna rannan?" Na dan bata rai nace rannan me? Mary". "Kin
tuna da Yaya yake tambayar wai waye saurayinki? Har kika ce
babu kowa, a lokacin da zamu gidan Abba.
Tun daga şama har kasa na jiyo wani abu ya tsiromin nayi
saurin dag akaina na kalli Mama, amma sai naga ta kawar da
kanta gefe guda, kamar bata jiba. Ana cikin haka muka ji
sallamar yara. Nan dai aka watsar da maganar wajan yi musu
sannu da zuwa.
'Tun daga lokacin na shiga kunyar Mama, duk da cewa
bata ma nunamin taji abinda muke yi ba muna jibi zamu koma
karanta, na ce zan je in yiwa Abba sallama, Alhaji ya amince
74
71
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
min yacc anına yau zamu fita da Manu sai dai yayan naki in
yaga zai sami lokaci ku tafi tarc. Dan shima naji dazu yana
cewa yana son zuwa ya kara duba hajiya iya. Nace "To ina
fitowa naje na sanar da Yaya, A lokacin yaf ito daga wanka ke
nan sanye da doguwar riga da kuma tawul a hannunsa yana
goge kansa.
Turkashi, waini mai yasa nake sa'ar ganin yaya a cikin ireiren wadannan yanayin? Nayi sauri gaidashi yace, "lafiya kika
shigomin daki tunda sassafe ko sallama babu?" yaya ai nayi
sallama," "To ai ni ban jiba, kuma ko na jima ya kamata ace sai na
amsa na umarceki da ki shigo tukunna. Nace, dama Alhaji ne yace
ka tsaya mu tafi gidan Abban tare shi yas ana zo na sanar dakai
dan karka tafi.
To, bari in shiga in shirya kafin in fito ki hadamin (tea shayi
nace, to ina gama hada masa shayin ya fito. Ya zauna akan kujera
na jawo dan karamin tebiri na daddora masa komai akai na tura
masa gabanshi, ya kalleni gami da murmushi yace "na gode ko?"
Zan fita yace in dan jira ya gama mana, sai mu yi yar hira. Nace
"Yaya ai zuwa zan yi in shirya kafin ka gama yace, "to".
Tun da na shiga cikin gida, Mama ta shiga bina da kallo.
Duk nabi na tsargu ni dai na shiga (ſakinmu ni da Khadija na
gama shirina tsab, kadijama tace za t aje, nace ta shirya mana
sai mu tafi tare cikins auri itama ta gama shirinta, sai da muka
gama shirinmu tsab, sannan na tura mary dan ta sanar dashi.
Ta dawo tace dani yace wai ki fito yana fitowa yanzu.
Yaya Humaira safarsa yake sawa. Allah Yaya Humaira, yau
baki gairin shgiar da yaya Auwal yayi ba wallahi yayi kyau
sosai da sosai. Na harareta nace, "to ni ina ruwana nan dai
muka shiga muka yiwa Mama sallama, tace to mu gaidasu
Maryam tace itama zata, kasancewar dama shirye take sai kawai nace ta dauko takalmanta mu tafi.
Tun a hanyarmu ta fita waje, Khadija take cewa "Ita dai Allah yasa yaya Auwal ya batta" nace, "Haba dai mai zai sa ya hanaki? "Ya lai kuwa muna zuwa bakin motar ya doka mata
harara yace da ita ina zuwa? Nayi tsagal nace dashi yaya rakani zatayi" Yace a'a yan rakiyar sun yi yawa gani ga Maryam ita ta koma wata rana mun je da ita amma ita maryam din t ashigo muka kalli juna hakida duk cikinmu babu wanda yaso hakan.
75
Lubabah!
Tana kwance sai nishi take yi, na shiga nace "Hajiya lya
yauma jikinc?" "A'a a'a gajiya ce kawai, dakin nan ne yayi
datti da yawa shine na shareshi, ke haka ake ki "higo daki ko
sallama babu?" wallahi ni shinki ne ya rudani kai ka rantse
wani katan gardinne ya shakeki, in kina haka ai sai kisa tsoro
ya kamani, in zaci ko mala'ikan daukar rai ne ya zo" "Kai 'yar
nan baki da dama, shegantakarki yawa ne da ita, ni dai tun ina
jin kunya har kinsa na daina ji yanzu wannan da a zamaninmu
ne ai da kin sa 'yan mata sun sani a waka ke dawa kuke tafe?.
Tabdi jan lallai ido sun yi nissan kiwo, wannan sai an
hada da gilashin ido sannan suka gaisa. Tace, "hakika ni dai
yaran nan kuna burgeni, yadda kuka hada kanku Allah dai yayi
muku Albarka, dan Allah dan nan ka yiwa Alhaji Safiyanu
godiya kace mun gode mun gode duk wanda ya rike maka naka
koda kwana daya ne babu bacinr ai babu muzgunawa hakika
mai kaunar kane, balle irin rukon da ya yiwa tamu so nake in ji
sauki ni da kaina na ke san zuwa yi masa godiya kullum ni dai
addu'ata daya ce Allah ya hada kawunanku. Kunga ai sai mu yi
tuwo na maina. Ni dai na baka ita ka ji ko dan nan.
'Tun da ta far amagan aYaya Auwal ya shiga yimin wani
irin kallo yana wani kashe ido gami da yanga sai kace mace. Na
yi dariya nace lallai Hajiya lya, dama haka ake bada kyautar
mutum zikau har kike wani ayi tuwanki manki toshi wannan
tuwon da miya za'a cishi”.
Tace "Ja'ira ana so ana kaiwa kasuwa ai ni zan yi zaman
daki". Na karayin dariya nace ai gara da kika yi magana yaushe
zamu zo rakiyar". "Duk ranar da kika shirya". Wani abin
mamaki duk abin nan Yaya Auwal baice damu komai ba, yayi
shiru in banda tunani babu abin da ya ke yi nan dai muka jima
muna hira daga karshe muka mata sallama muka karasa cikin
gidan mun tarar da Nasir zaune a falo a raina nace matacсe,
kulum yana gidan ya kanan nade kamar gidan Uban shi.
Tana ciki ne?" Na tambayeshi cikin facin rai shi kuwa
Yaya Auwal dama yana ganinshi yayi baya ya nufi falon Abba.
"E tana ciki," Ya fada cikin hanzari gami da washe baki.
"Ammafa sallaht ake. Ni zan tafi yace "ki jira ta mana" "A'a in
ta idar na zo mu gaisa". Ban kara saurarar saba nayi tafiyata
abuna. 76
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
B
falon Abba Yaya Auwal ne ya yi shiru kanshi a
A
sinkuye tamkar wanda yake gaban sirikinsa nima na
durkusa na gaidashi mun jima mun ahira zuwa can
yace dani Humaira bari in turaki nan makotanmu gidan da yake
jikin gidanan in kin gaida mutan gidan kice nine na turoki kuma
ki sanar dasu cewa kece 'yar tawa. Yayin da ya shiga bawa
Yaya Auwal labarinsa yace.
Auwalu wannan makocin nawa shima matsalace dashi
kama rni har gara ni an taba haihuwa shi kuwa bai ma taba
haihuwarba yaya Auwal yace aiyaa. Allah shima ya bashi ni dai
na fita na barsu a nan.
A lokacin da na tashi fita sam ban bi ta hanyar da zan
gamu da Nasir ba, sai nabi ta wani fan korido dake gefen dakin
Abba, wanda zai fiddani har kofar gida. Lokacin da na shiga
gidan, anmin karba ta rashin sani, to amam da na yi bayani sai
naga tamkar an hadiyeni, matar mai gidan yarinya ce, saboda
matarshi ta farko ta rasu mun jima muna hira, har muka zama
kamar kawaye, zuwa can maigidan ya fito shima muka gaisa,
matar shi mai suna Hajiya Saude ce ta sanar dashi ko ni
wacece: Hakika yayi farin ciki da ganina daga karshe ya kawo
kudi dubu uku ya bani.
A yadda na barsu da Yaya Auwal haka na dawo na tarar
dasu, suna ta hira abinsu mun jima muna hira daga karshe muka
yi sallama, lokacin da muka zo tafiya ne na biya na gaida
Hajiya Rabi muka yi mata salama muka-kara biyawa dakin
hajiya lya, saboda Maryam nacan tana bacci, muka dauketa
muka tafi.
A kan hanyarmu ta komawa gida ne muka gamu da Alhaji
Kabir, wato kakana wanda ya haifi Mama na. Gaba daya muka
fito daga motar muka durkus amuka gaidashi, ya tambayemu
daga ina muke? Muka sanar dashi sannan ya dubi yaya Auwal
yace, "Auwal naga dariyar taka gamida fara'ar taka tayi yawa,
karfa kayimin fashin mata". Gabana ya fadi. Na shiga uku wai
77
Lubabah!
mai yasa kowa yake yi mana kallan dacewa nc? Yaya Auwal
yayi murmushi yace, "Alhaji ai tace kayi mata tsufa".
"A'a ina maganar tsufa a nan. Ai ni yanzuma gidanka Yaya Auwal zai kaini, in sami daki daya in tare. In kuma kasan
babu daki, ka sanar dani tun da wuri in tafi da shiri, domin
kuwa sai dai muyi kokawa, kowacce karfinta ya bata dakin
kwanan yau. Gaba daya mukasa dariya yace "Kije mana amma
dai kin san matana sun fiki karfi ko?" "E naji na kuma amince.
To amma fa da sharadi guda daya in ni na fi matanka karfi kada
ka isomin da furfura koda alamun tsufa, nafi son in ganka yaro
sak nan ma dariya aka kwashe da ita gaba daya.
A lokacin da yaya Auwal ya cika motarshi kan kwalta,
abin ya dauremin kai da naga ya saki hanyar gida kait saye MC
BacBanas ya nufa. Sai da na tababtar ya tsaida motar sannan na
cillo shi da tambaya nace dashj "Shin mene ne dalilin zuwanmu
nan Yaya Auwal? Murmushi yayi yace abinci zamuci mana,
Allah ba kijiba yinwar da nake ji ba, na tababta kuma tun da
hajiya tasan muna gidan Abba, ba lallai bane a ajje mana abinci
ba ko za'a ajje bai fi ba a ajje na Maryam.
Amma fa ina da wata magana wato wata alfarma zan gaya
miki, wacce na ke son kiyimin ita" wacce irin alfarma Yaya?
"A'a ai ba zan yi saurin sanar da ke ba har sai naji kin tabatar
min da cewa zaki sanar dani gaskiya tsakani da Allah". In sha
Allahu yaya. To shikenan mu shiga daga ciki tukunna ko? dan
wallahi Allah yinwa nake ji yayin da ya tsaya yana kallona
gami da murmushi yana shafa cikinshi.
A lokacin da muka shiga ciki sam babu mutane sosai. Na
sami guri na zauna yayin da ya karasa ya yo mana odar abinda
zamuci saida mukaci muka koshi, yayin da ita ma Maryam ta
tashi a lokacin itama ta cika cikinta tukunna yaya Auwal ya
umarceta da cewa ta koma wani gurin ta zauna yana son yimin
magana yayi haka ne saboda dan banzan surutu irin nata.
A hankali ya dago kai ya kuramin ido zuwa wani lokaci,
duk yasa kunya ta kamani ya murmusa gami da kashe ido.
Hakika ko baice komai ba ma hakan ya gamsar dani yace,
Humaira, wato maganar da na ke son yi da ke ba wata bace face
in sanar dake wani abu da ya dade yana min yawo a zuciyata,
duk da cew akin san komai amma fadar da zan yi ita zata kara
78
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
min kwarin gwiwa yayin dana fuskanci yadda aka karbi
maganar.
A zahiri Humaira ni mai kaunarki ne, kauna ta hakika. A
takaice dai Humaira ina sonki shin KINA SONA?
A nan ne gabana yayi mugun faduwa duk da cewa tuni an
gane manufar Yaya Auwal saboda alamun da yake nunamin, to
amma hakan bai sa ya hana faduwar gaban ba. Na daga ido a
hankali na kalleshi kina sona? Ya kara ambatawa yayin da ya
kuramin ido gami da rukomin hannu.
A hankali na murmusa alamun na amince idan ta ya ciko
da kwalla, ta dago kai ta kalli Yaya Fahad tace, "A wannan
rana ce na amsa soyayyar da ta zame min bala'i na shiga kangin
da tun da uwata ta haifeni ban ta6a tunanin zan shigetaba. Na
amsawa kaina abin da ya jawomin dana sanin rayuwa wanda
har na zo ina dana sanin amincewa. "Tayi shashshekar kuka ta
shiga rera kukan a hankali, cikin sautin murya mai ratsa zuciya.
A nan ne tausayi mai tsanani ya kama Fahad ya tausaya
mata ganin halin da ta shiga cikin wannan dan lokacin. Son ta
ya kara kama zuciyarshi yace, "Humaira kiyi hakuri, bana son
in ganki kina kuka, ki bari gobe kyaci gaba da bani labarin dan
naga hankalinki ya tashi matuka.
Affa fairan ban so haka ba masu karatu nima kumin afuwa
mu hadu a na biyu.
7-9-
Lubabah!
TALLA A KAIWA MAIS AYE
Y
a shiga gida a gajiye saboda yayi aiyuka da yawa
ga Operation ga marassa lafiya mai gadin gidanshi
ya yi masa sannu da zuwa, ya amsa agajiye, ya shige
cikin gida ya shiga daki ya tube kayan jikinshi ya shiga
wanka domin ya ji dadin jikinshi. Sai me?
Wato Rigar Nono da Pant ne shanye a cikin bandakin.
Gashi an wankeshi fes sai kamshin sabulu yake yi
yayin da abin ya masifar daure masa kai. Shi dai a
saninsa yasan shi kadai ne a cikin gidan, sai kuma maig
adi to mai kuma ya kawo kayan mace gidanshi, shin.
WA CE СЕ?
NA
Habiba El-Mustapha
80
1.- So Shu'umi 1-2-3
2- Ilham 1-2-3
3- Wanda Ya Daka Ta Bado 1-2
4- Malika 1-2-3
5- Yaya Ke Nan 1-2-3
6- Zargi
7- Sila
1-2-3
1-2
8- Wanda Yace Namiji Uba Ne... 1-2
Designed & Printed by: Lubabah Publishers
Phone 665532 Kano.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels