ikon Allah Hajiya yana zuwa gaban
mahaifin nata sai yayi masa kwarjini, duk abinda Uban yace,
sai yace to suka ringa juyashi kamar aikin asirida ga karshe ma
sai aka ce an bashi ita, kadama ya matsawa kansa, an ya fe mas
akomai, amma sai yace dasu shi dai ya gode amma zai yi iya
kokarinsa wallahi hajiya daga kayan lefe sai sadaki kawai ya yi
shi kansa lefen ba wani na azo a gani ba yayi sai sadaki da ya
bayar dubu goma, da dubu biyar ma zai bayar da kyar muka
lallashe shi ya bada dubu goman. Ya karayin dariya yace, to
dan Allah Hajiya kowa ya ji yadda auren ya kasance ai yasan
daddarace kawai wadda ta riga fata. Ita kanta in banda gata ga
yadda take, muni kamar biri wallahi babu yadda za a yi tace
zata auri Sulaiman dan yadda take da shegen dogon buri a
zuciyarta wallahi hajiya yawanci irinsu sai dai kawai a yi
sha'ani, wai mutumin birni ya ga na kauye.
41
Lubabah!
Ya juyo da sauri ya kalli lumaira, a lokacin da ta mike
tsaye da niyar zata fice daga dakin yace, ke kuma ina zaki ana
Zaune ana hira mai makon kema ki kawo mana labarin dakika
sani na auren kaddara da ya faru a Kano.
Yama sata dariya, ita a ganinta, ba komai bane ya sa ta dariyar face yadda taga ya zauna, sai zuba yake, ya kanyar rani,
badan komai ba sai dan ya sami shiga a gurinta, tabbas da yasan
yadda dawan garin yake da bai so shirya soyayya da ita ba.
Hakika da ya ji labarinta da ya yi wani tunanin, to amam shi
mutum in yaga abin da ya ke so idan shi rufewa ya ke, sam sai
ya ji shi komai ma ya yi masa dai-dai, shi yasa bahaushe ma ya
ke cewa so hana ganin laifi, ba mamaki ko ta bashi labarin nata
shi yaga hakan ba komai ba ne a gurinshi.
Ya dubeta yana murmushi yace, "tunanin me kike yi? Ко
an tuno miki da kanawa, hankalinki ya yi can. Allah ni dai ki
shirya dan gobe-goben nan rake son jin labarinki tun daga
farko har karshe dan haka ki kiyaye banda ragi, kin ji ko. Dan
in kika rage abu daya ko kika boyemin, zai iya ruguza ginin
zuciyata guda goma.
Yaran banza, yaran wofi ya ji ya doki dodon kunansa, da
muryar mahaifiyarsa. Hajiya taci gaba da cewa "Kai yanzu sai
ka zo cikinmu ka zauna ka kama surutai na babu gaira babu
dalili. Da kake cewa sai ta sanar da kai labarinta, ji nake nice na
gargadeku da kada ku takura mata akan ta baku labarinta. Na ce
ku bari, in ta kara sakewa ita da kanta, dan kantama zata so ta
bada labarin nata. Amma ni na rasa irin wannan naci naku dan
Allah tashi ka fita kabawa mutane guri.
Ya dago kai ya kalli Humaira yayi murmushi yace Hajiya
in na koma gida dawa zan yi hirar, dama Hajiya ina son in bawa
Shafa'atu mukullin gidan taje ta share min shi dan sun barmin
shi kaca-kaca", "Ka bayar gobe sai su tafi tun da sassafe, ita da
Humairar" "To Hajiya yayin daya kara dago kai ya kali
Humaira, ya kashe mata ido gami da tsareta dasu.
Ya dubi Hajiya yace, "Hajiya wallahi bana son yawan
yawo, a wannan lokacin kada 'yan tsegumi su ganni su tafi su
kaiwa Khadija labari, duk subi su ishi mutane da magiya, ni
kuwa lajiya wallahi na sayar akai kasuwa.
42
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
"Ya Rasulillahiw ai dan Allah dan nan mai yasa baka da kunya ne, ni kake yiwa irin wadannan surutan kamar an kwence
maka takunkumi ko kuwa hirar taka daban? In Humairar ka ke
so kabawa labari, ka jata can mana ka bata, ka zo ka cika
mutane da shegen surutu, kace wannan kace wancen. Ni dan
Allah ku tashi ku bani guri har Humairar, itama dan taga Shafar
bata nan ne shi yasa ta shigomin".
Ya sunkuyar da kai cike da matsananciyar kunya. Hakika
babu tantama Hajiya ta dago shi shin shi kuwa wane irin abu ya
ke yi haka, har Hajiya tayi saurin gano shi. Hakika shi so ba'a
sa masa shamaki, ya tuna yadda da yake tsananin kunyar ya
zauna yana zuba haka, kasancewarsa na fari agurinta, amma sai
gashi yau ya zauna yana ta zuba ya kurnar rani maganganu
barkatai da wanda ya dace dama wanda bai dace ba. Kuma
hakika shi kansa yasan saboda Humaira yake irin wannan
surutan, nan dai ya tashi a sanyaye yabi bayan Humaira, wacce
tuni ta fice cike da matsananciyar kunya.
Ya sameta kwance a dakin su ta daga kanta sama tana
tunani. Ba komait ake tunawa ba face rayiwarta da tsohon
mijinta an ya kuwa duk maza ba mayaudara banc. 'T'a tuna irin
gigin da mijinta ya ringa yi mata amma tashi daya haka ta
kasance tsakaninsu wanda take ganin sam Fahad bai kama
kafar-kafar irin son da mijinta ya nuna mata ba.
Ya yi gyaran murya, yayin da ya yi mata sallama bata ji ba
yace Malama Humaira tunanin me ake ne ko kanawa`ne suka
murdo kanbunsu. Ni dai ina rokon mutan Kano da su rufamin
asiri, su barni in cika burina.
Ya kamata ace tun yau kin fara bani labarin ki kinga gobe
sai ki karamin. Dan na lura da wannan cikin tabas akwai
maganganu masu yawa da suke kunshe a birnin zuciyarki. Gara
a daure, a amayar min dasu ko an samaw abayin Allah matsugunni.
Ya Salam ta fada cikin siririyar muryarta, da takan yawan rikitashi, hakika ko rankane ya baci da zarar kaji wannan mu.yar, ta wadatar dakai, ka ji bacin ran ya gushe, ko da ba'a lallasheka ba yaci gaba da tunani aransa yayinda taci gaba da magana tana cewa, "Wai mai yasa ka damu da kasan labarina. To amma tunda ni na maka Alkawari, zan fara gutsuro maka 43
Lubabah!
labarina. Amma kada abin ya baka mamaki, in ka na canja wasu
guraren in anzo bawa su hajiya labarin saboda kunyarsu da
nake ji. Amma in sha Allahu kai babu abinda zan boye maka
sabdoa na lura da wasu abubuwa da dama da suka ringa wakana
ya yi murmushi yace, "Na kwa gode da aka yi saurinf ahimtata
yayin da ya sami guri ya zauna taf ar abashi labari kamar haka. a
le
a fito da gudu daga dakin soron kofar gida, in da N
akasari a nan muke haduwa, mu da sauran yara 'yan
unguwa muna yin wasa. Yau dinma wasan muke dan a
lokacin babu wata makaranta da nake zuwa saboda na gama
karatuna na F'iramare. To a yau mahaifina ya zo ya kawomint
akarda ta shaidar na ci makarantar gaba da Firamarc. A nan
dakin ya sameni ya bani shine na shiga cikin gida da gudu ina
murna, dan in nunawa mahaifiyata.
Na shiga kwala mata kira ina cewa Mama-Mama. Ban
daina kiran sunanta ba har sai da na ganni tsaye a kusa da gadan
da take kwance tana bacci. Nan ma ban hakura ba na shiga
fadin Mama! Mama!! Mama!!!. Ta tashi ranta a bace tace,
"waike wacce irin yarinyar banza ce ba na hanaki tashina daga
bacci ba? Na gaya miki muddin kika sameni ina bacci, ki
hakura da duk wani abu da kike san gayamin, ki bari sai na
tashi.
Na yi tsagal nace Mama dama yanzunnan Abba ya zo ya
kawo min takardata shaidar naci makaranta ta gaba da
Firamare, yace garin Babura naci.
Nan take ta bata ranta, na rasa dalilin da yasa ako da
yaushe na yiwa mahaifiyata maganar mahaifina sai in ga ta
bala'in bata ranta, sam bata kaunar taga ina kula mahaifina.
Alhalin ni kuma ina son Ubana, kamar yadda yake nunamin so
44
n
n
a
e
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
A
kowane hutu Yaya Auwal ne yakc zuwa daukata, A
amma wannan hutun Manu Direba shi ya zo daukata, a
lokacin ina aji biyar na sakandire kasancewar Yaya
Auwal yana makarantar B.U.K. yana karatun Digiri dinshi na
biyu.
A ko da yaushe yaya Auwal yakan rubuto min wasika
akai, akai dan tambayar lafiyata, da kuma karatu. In kuwa ya zo
gida, lokacin muna makaranta, sai ya kawomin ziyara kafin ya
tafi wannan hutu ne wanda in na koma aji shida zan shiga. A
gaskiya wannan hutun na yi kyau, har na gaji gashi kuma na
fara cikar budurci.
A wannan hutun ya zo dai-dai da hutun su yaya Auwal,
dan haka a ranar da na dawo shi kuma washegari ya dawo ina
kwance a doguwar kujera ta falon Alhaji a lokacin mun hadu da
yara, suna zaune suna yin Video Game ni kuma ina daga
kwance rike da lemon fata a hannuna ina tsotsa. A lokacin na
gama hadewa cikin wasu kaya riga da siket farar riga bakin
siket. Abba ne ya kawo mana su iri daya ni da Khadija da
Maryam. Hakika kayan ba karamin kyau suka yi min ba.
"A'a don Allah Yaya Humaira ba na kada shi ba?" Na ji
Khadija ta katsemin tunanina a lokacin na shiga tunanin ya
kamata da yamma ko gobe in je in gaida Abbana". A'a Habibu
nifa bana san wayo" "Ke fa baki gani ba Yaya, gini fa na hada
kuma tunkan ya fadi na yis auri an daga shi, shine za ta ce wai
an fadi, ni shiyasa bana san yin wasa da Khadija, wallahi ta fiye
runton tsiya". "To in dai fafa za ku yi ku hakura haka"
Auwal ya shigo yana murmushi yace ku yaran nan babu
wanda ya iya yiwa mutum sannu da zuwa tun dazu na dawo
amma babu ko sannu da zuwa. Gaba daya muka mide muna
dariya gami da yi masa sannu da zuwa. Na koma na zauna
adoguwar kujerar, Yaya ya zo kusa dani ya zauna wani irin
kallo da ya wurgomin, ban san lokacin da na jefar da lemon
hannuna ba saboda kidima. Domin hakika kallan kallo ne mai
kunshe da fassarori, daban-daban. Hakika nasha jin labarin
irinw anan kallon a bakunan marubuta dan shi suke zaiyanawa
57
Lubabah!
a duk lokacin da masoya suka hadu kaji ance an kashe ido ana
kallan mutumg ami da murmushi.
Amma ni idona bai yi sauring askata hakan ba, saboda ina
ganin bata mana 'yar haka a tsakanina da Auwal domin ni a
ganina mun zama kamar uwa daya uba daya. Ya lankwasa
murya yace, "Humaira 'yan makaranta, tun yaushc aka dawo?
Nayi murmushi nace, "tun jiya" yace "yanzu jiya jiyannan kika
dawo amma tamkar kin yi,kwanaki kin yi fes dake haka"
murmushi kawai nayi yara suka shiga tambayarsa mai ya kawo
musu, yace "Ni babu abinda na kawo muku sai kace wanda na
bar garin koda n kung ana kwana biyu ban zo hutun karshen
sati ba. Ai jarabawa ce ta tsaremu bawai garin na bari ba". Ya
kalleni yace gaskiya Humaira kin kara kyau". Habibu ya kaiwa
Khadija duka a baya tace.
"Aaa... wallahi saina rama Yaya Auwal yace kai Habibu
mai yasa ka daketa, yace "yaya tankwabata tayi na fadi".
"Shine kuma ka dake ta, to shi kenan ku ajje ku fita wasanku.
Nan dai suka fice suna gugunai ya dubeni yana murmushi yace
in je muyi aga wanda ya iya. Nace "Yaya ni wallahi ba zan iya
yi da kai ba". Ya yi murmushi yac, "saboda me, Humairan
Yaya?".
A hankali na dago kai ma kalleshi, dan maganar ta
burgeni. To amma abin yana dauren kai yau sai wani iri ya ke
min kamar yana gaban budurwarshi. Ya ce dan Allah ki sauko
mu yi yau sha'awar yin game din na ke yi mama tana can da
baki shi yasa na taho nan.
A kan dole na zo muka fara muna yi muna hira, ya turkeni
akan lallai sai na gaya masa saurayina, wai shi ya gaji da ganina
da zarar na gama karatu aurar dani zai yi. Na tuntsire da dariya
na ce, "Aure Yaya? Aini Aba da Alhaji duk sun ce sai nacig aba
da karatuna, kafin in yi aure dan haka babu wani saurayi da
nake kulawa", yace, "Allah ko? To Babban yaya kuma ya ce
aurar da kanwarsa zai yi. In ma babu saurayin shi ba sai ya aure
ba?" Gaba daya kunya ta kamani.
Amma gaskiya Yaya Auwal ya iya dubara da nasan haka
ya ke so yace, ai da na ce ma da samari da yawa. Na kwashe da
wata mayaudariyar dariya nace, "Yaya ai kana ta dannawa har
ka fadi baka sani ba". Na yi hakan dan a bar maganar.
58
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
haka kuma itama ina sonta a matsayin uwata, kamar yadda take
nuna min so amatsayina na 'yarta.
Nan dai naci gaba da murnata ta naci makaranta ban damu
da laifin da nayi ba na tashin mamanmu dag abacci. Ta
dakamin tsawa, tace sakarar banza sakarar wofi. Ai bacin
makarantar ba karatun shine. Ba wai kawai a je aci kwaki da
kanzo ba a dawo, ba a san komai ba, sai dai a yi ta faman yanga
a titi yayin da ta warci takardar a hannuna ta doka uban tsakit
ace, "Wai shi Abbań naki har kofar gidan nan ya zo?" nace E
mama shi ya kawomin da kansa, ina fada ina murna cike da
fara'a a fuskata. Ta kuran ido na dan lokaci sannan tayi kwafa
ta shige daki, tana mai gargadina da kada in kara tayar da ita
daga bacci". Gikin sanyin jiki nace da ita "to"yayin da na koma
can soron kofar gidan na tarar da abokan wasana mukaci gaba
da wasanmu. Amma duk da haka ina ciki da tunanin abinda
yasa mahaifiyata bata kaunar mahaifina. Ni ba wani bambanci
nake nunawaba tsakanin Abbana da kuma mijin da take aure ba.
Domin kuwa ya rikeni sosai kamar yadda ya rike 'ya'yansa,
babu wani ban banci da yake nunamin.
Na fito da saurina, na yi kofar gida sakamakon tsayiwar
motar Alhaji da naji muka tare shi ni da yara kannena, muna
masa sannu da zuwa. Na karbi jakar dake hannunshi, kai tsaye
falon shi muka wuce, Maryam ta fita da saurinta ta sanar da
mama dawowar Alhajin, zuwa can sai gata ta fito rike da robar
ruwa a hannunta, gami da kofi tayi masa sannu da zuwa ta
zauna ta zuba masa ruwan yasha sannan ta sami guri ta zauna
sosai. Alhaji da ke zaune a kasa kan kafet ya jingina da
doguwar kujera kansa babu hula, wanda sanko yayi masa
katutu. Ya dan shafa sankon yana murmushi yace
"Naga yau. Humaira sai fara'a take mene ne ya faru ne?"
Mama tayi dan murmushit ace," Ai tun tuni in banda ina
harararta da tuni ta baka labari, to amma tunda ka tambaya bari
a gaya maka dama na bari ne sai ka huta sosai. Daga nan ta
bashi labarin samin takardata, ta shaidar cin jarabawata zuwa
makarantar kwana".
"Ni fa in ce wannan farin ciki yayi yawa". Yana fada yana
dariya". To ai shike nan Allah ya bada sa'a Allah kuma yasa
hakan shine mafi alkhairi amma dani ina nan ina nema mata
45
Lubabah!
makarantar gaba da Firamaren, wacce take cikin garin nan. To
amma hakan ma na yi farin ciki sosai, to amma yanzun ma na
gamu da Abban nata in yi masa bayani.
Ni da na fi son makarantar Shekara, to tsarin makarantar
ne baya burgeni wato yadda tsarin ginin su yake amma hakika
akwai karatu to amma yanzu in ya bari sai a nema mata Dala ko
ba haka ba Mama ta yi murmushit ace duk abinda ka yi ai
daidai ne. Allah dai ya zaba mana abinda ya fi alkhairi.
Na yi dariyar jin dadı, murna fal cikina yace "Humaira sai
ki shirya gobe kije ki gayawa Abban naki, abinda ake shirin yi
in sha Allahu nan da litinin ta sama, sai a kaiki makarantar dan
bai dace a bari lokaci ya kure ba".
Nace "To" yayin da na tashi na fice daga dakin ina ta
murna. Gari na wayewa na shiga shirin tafiya can gidan
Abbana, Mama tana kalona, amma ko ta tafasa bata ce min ba.
Ta dago kai ta kalli Fahad, ta dan yi murmushi tace, ko da ya
ke nasan an dan rikita ka. To auren mahaifiyata tuni ya mutu,
amma bari dai zan gaya maka komai taci gaba da cewa.
Na gama shirina tas da 'yar Atamfata ta Nicam, na dubeta
nace, "to Mama zan tafi ta kalleni tace, ke tunda sassafe haka,
sai kace wacce za ta je ta tarar da su yabar garin". "Mama ai
dan kar in je in tarar ya fita". To in kin je kice ina gaida Hajiya
Rabin da kuma Iya. Wato Mahaifiyar mahaifina nace "To".
Naje na tarar Abban bayanan duk da tsananin saurin da na
ke yi. Da naga baya nan sai kawai na gaida Hajiya Rabin na fito
na nufi bangaren Iya. Saboda kwata-kwata matar Abban nawa
bata sakarmin fuska shi yasa bana zama a gurinta muyi hira sai
dai in tafi gurin Iya in yi zamana in jirashi.
Na jiyo tsayiwar motarsa a farfajiyar gidan, dan haka yana
shiga cikin gidan sai na biyoshi abaya ba tare da na mása
amgana ba mai makon in bishi falon nashi, a'a sai na nufi falon
Hajiya Rabin na sanar daita zani gurin Abban, saboda ta yimin
gargadi mai tsanani akan kada in sake in je gurin Abban ba tare
da na sanar da ita ba, ka jifa yaya Fahad ni da'mahaifina. Sai da
ta dan basar dani sannan ta amsamin, ta kuma ce in jirata sai da
ta gama abinda take yi tukunna ta tashi tace in biyo ta.
Na bita sokai-sokai har falon Abban duk da cewar ya saba
ganin rawar kaina da nuna farin cikina a fili a duk lokacin da
46
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
muka gamu amma saboda tsanan tsoron Hajiya Rabi da na ke
yiwannan karan a sanyaye na shiga fakin na durkusa har kasa
na gaidashi, ya bukaci in koma kusa dashi na koma na zauna ya
tambayeni lafiyar Alhajin. Nace "yana nan lafiya, ya ce ma
agaida kai". Yace. "Maman na ki fa da sauran kannan naki suna
nan lafiya?"
Na ce, "Duk suna nan lafiya. To fa a nan ne Hajiya Rabi ta
mugun bata ranta. Na lura da cewa Hajiya Rabi tana tsananin
kishin mahaifiyata wanda na rasa dalilin hakan yaya Fahad bafa
su taba zama tare ba. Amma bata kaunar taga mahaifina ya
nuna kulawarsa ga mahaifiyata.
Na sanar dashi sakon da Alhaji ya yomin hakika ba
Karaminf arin ciki ya yi ba yace, "wallah ki gaya masa duk
abinda ya yi dai-dai ne, ai ya tashi ce ko. nan dai muka zauna
muka dan taba hira yace wannan yace wanan ya kuma
tambayan wancan ya tambayen wannan. Amma duk da haka
Hajiya Rabi bata s amana baki ba. Asalima in ya yi mata
maganar kawai sai tace, uhm ko uh-uhm, da ya lura da ita
kawai sai ya watsar da ita. Nace dashi ni zan tafi, yà yi
murmushi yace, "to Hurnaira Baban naki ya hana in yi miki
komai. To amma ga wasu Atanfofi da ha saya mu ke da su
Maryam. Ga kuma dubu uku ki ba Maman naku, kice in jini ta
biya muku kudin dinkin.
Na karba na yi godiya. Amma kallo daya za ka wa Hajiya
Rabi ka fuskanci tsananin bakin cikin dake can kasan zuciyarta.
Ta hade girar sama da ta Rasa tayi murtuk. Ni dai nan nayiwa
Abbana godiya na tashi na tafiyata na abrau ko sallama ban
mata ba kamar yadda itama bata yi min ba, amma nasan tsabar
bakin ciki ne, sai dai kuya ya kasheta. Tun da tsakanin da da
mahaifi sai Allah.
Na koma gida cike da farin eiki da murnata na nunawa
Mama kayan da na zoda su gami da mika mata kudin nace,
"Mama yace yana gaidake, kuma yace in baki wadannan kudin
kya bayar da kudın dinkinmu ta ee uhmm, sai kije ki Ajjesu in
an bada dinkin an bayar da kudin. Ga yadda ta amsamin aai duk
jikina yayi san yi sati daya aka yi ana neman makarantar aka
samu, batare da ansha wahala ba. Nan take Alhaji yaee, "А
Lubabah!
ranar litinin mai zuwa za'a kaini makaranta. Nan na shiga
murna ina addu'ar Allah ya kawo ranar.
Na tashi tunda asubar fari sabosa tsabar doki, saboda a
yaune ranar da za'a kaini makarantar: Tun da duku-duku na
shiga wanka na shirya, kafin karfe bakwai na safe na kammala
da komai, ni dai kawai ina jiran azo a kai ni makaranta.
Na nufi dakin Alhaji don in gaidashi da misalin. karfe
takwas na safe ya dubeni ya yi murmushi yace Malama
Humaira 'yar makaranta, har an gama shiryawa". Na sinkuyar
da kai ina murmushi cike da dokin in ji yace in fito mu tafi, kan
ya kara cewa komai sauran yara suka shigo ya dubesu ya yi
murmushi yace, "Kun ga har Humaira ta rigaku zuwa nan ya
yiwa Maryam wasa, sannan ya juyo gareni yace. "Humaira sai
dai kiyi hakuri, don da kyar ne in tafiyar zata samu a yau wato
wata tafiyace ta gaggawa ta riskeni. Yanzum nan zan tafi
Abuja. Amma a yau zan dawo in sha Allah dan ko siyayyar ban
miki ba. Da Auwalma yana nan da ya yo miki, amma ai yau zai
dawo dan tun shekaran jiya suka kammala karatunsu. Don haka
sai kiyi hakuri sai na dawo koni ko Auwal din sai wani ya kaiki
makarantar.
Na ji gabana ya yanke ya fadi domin har ga Allah gani
nake kamar ba kaini za'ayi ba. Alhaji ya kara dubata yace karki
damu kin ji, da zarar Allah ya dawo dani lafiya zan kaiki
makarantar. Khadija da Mujahid suka tashi suka nufi dakinmu
na yara Nima a hankali nace, "To Alhaji Allah ya dawo dakai
lafiya ya ce amin Humaira.
Na fito na nufi dakinmu na yara, ina shiga Kadija da
Mujahid suka kama yimin dariyar an fasa basu kyaleni ba har
sai da suka kular dani. Raina ya yi bala'in baci, Nan da nan na
fito fuuu na nufi dakin Mama na sanar da ita abin da Alhajin ya
fada, tace to Allah yasa hakan shine mafi alkhairi. Na kara bata
rai ya yin da idanuwana suka cicciko nace, "Mama kin ga su Khadija suna min dariya ko?" Tace yi hakuri. To kuma meye
na kukan, hako za ki je makarantar kina yiwa yara kuka sa
maidake sakarai sam ace baki da hakuri sai saurin fushi ga
zuciyar banza.
Na góge hawayen da yake a idona. Na ce "Mama dariya fa
suke min, ni wallahi bana sonda riya, yayin da na sake ficewa
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
daga dakin, raina a bace, dan ba haka na so ba, naso ta
kirawosu ta mammaresu ko tayi musu fada.
Na yi wankana tsab da yamma kai ba kace nice na sha
kuka dazun nan ba. Na dauki wata doguwar rigata da Abbana
ya sayo mana, ni da sauran kannena, na saka, hakika rigar ina
matukar santa. Dan in na sata ji nake kamar ba a kasar nake ba.
Na dauki jambaki ruwan bula kamar yadda naga manyan 'yan
mata na yi na wannan zamanin. Mama ta shigo tace, "Kai 'yar
nan da kwainanen tsiya kike, tun yanzu an fara iyayi, irin kune
sai shegiyar yanga babu kokari wai ku 'yan sakandire.
Na yi dariya na ce, haba dai Mama ai ni ina da kokari, nan
dai na gama iya yina a gaban madubi na yi gaba. Na fito tsakar
gida na zauna ina shegen kaudi in ce wannan in ce wannan.
Na ji gaba daya yara suka shigo gidan suna fadin ga yaya
Auwal ga yaya Auwal Nan da nan Hajiya ta dau murna duk da
'cewa ba sosai ba. Amma ta nuna farin cikinta kada ran kada
han. Suna shigowa Mama ta tambaye su yana ina?" Suka ce
yanzu Saminun bayan gida yace, wai tare suke da Auwalun shi
saboda kaya yana can tashar motar yace a turo masa mani ya
daukoshi" Tas yi tsaki tace "Shine kuke fadin ga yaya Auwal,
ku da ko ganinshi baku yi ba.
Ni yanzu bana san in da ya ke ba, amma ku duba can
shagon Ema ko yana can gaba daya suka fita da gudu, sai gashi
sun dawo tare da Manin, ya karbi mukullin mota a gurin
Hajiya. Ya kwashi yara suka tafi,da ga ni sai Habibu kawai aka
bari agidan ban damu in jeba saboda na manta dashi hakika na sanshi, to amma tun kan in yi wayo sosai.
Nan da nan suka dawo da uban shirgin kayansa, tamkar
wanda ya yo cirani. Ni dai na je na durkusa na gaidashi daga
nan na kama gabana yace Hajiya kaddai in ce wannan Humaira
ce kai amma fa ta girma hutu ta zo muku Hajiya?" "A'a ai ta
dawo nan. Habibu ne ya yi karab ya fada ya ce, yauwa Mama ai kinga hakan ya fi. Ni dai nan na barsu.
Na ji yara na murnar dawowar Alhaji sama-sama domin ni
a lokacin bacci ya fara daukata. Firgigit na tashi, ya lai kuwa
ina zuwa yi masa sannu da zuwa ya turo min katan kwali da
leda yace, ga kayan tafiya ne, kinga gobe sai ki shirya a kai ki
49
Lubabah!
makaranta, amma ina jin mani direba zan bada, da Auwal su
kaiki shi kenan ko.
Na fito riki-riki da jakar leda a hannu na nufi dakin mama
ina murna. Tayi farin ciki gami da murna, tace kin yi godiya
ko?" Nace "E Mama, yace ma gobe da safe za'a dauko akwatin
da katifar, da kuma bokiti.
Na tashi da wuri, a washegari ni na tashi mamanmu, nace
ta tashi ta shiryamin kayana, da farko ta dau fada, amma daga
karshe sai ma na bata dariya. Bata kulani ba sai da safe misalin
Karfe takwas, sannan aka dauko akwatin aka shirya min kayana,
aka kuma shiryamin kayan sawar a cikin jaka Mama ta hada
mukullan guri daya ta mikomin tace saura ki yadda. Gama naga
rawar kanki ta yi yawa Yaya Auwalyace ni na rasa irin wannan
murna, karfa kije kwana biyu kisa kwaki a gaba ki cinye ki zo
kina kuka ba fa ci muka turaki ba, a'a karatu a ke so ki tsaida
hankalinki guri guda kiyi karatu kin ji ko? kada ki zama irin
wasu 'yan matan sai shegen ci kamar gara, amma babu karatu.
Nan ne aka sa