na jiyota shine abin ya dauremin kai nake
son in tabbar da maganar daga gareki.
"Amma jeki kiyi sallar ina jiranki”. "To" nace dashi yayin
dana hanzarta ficewa daga dakin, ka'idar gidan ne a duk
lokacin da aka idar da sallar magariba, akan zauna ayi ta
karatun Alkur'ani kowa yake zuwa ana biya masa war lokacin
sallar isha'i tayi dan haka yau dinma haka aka yi sai bayan mun
yi sallar insha.
Addu'o'i muka fara yi sannan Alhaji ya juyo gareni, yace
Humaira yan makaranta, tun da dai ba'a kawomin sakamakon
ba (result) bari to in tambaya na sunkuyar da kaina don hakika
har ga Allah na manta tunda babu wanda- aka ma maganar
sakamakon na yi dariya nace, la Alhaji mantawa na yi bari in je
in dauko maka Na mike na nufi dakina na dauko jakata na fito
da takardar na kaiwa Alhajin yana gama dubawa ya shimin
albarka ya shiga yabamin. Hajiya ta tambaye shi ko na nawa na
yi?
A'a kaddai in ce tun da tazo baki gani ba haba Safiya, ai
shi dan makaranta kamar wanda ka aika ne da zarar ya dawo ai
aiken da ka masa zaka tambayeshi ni kaina dana yi shirui na zaci
ke zaki kawomin shi yasa, to ta uku ta zo sai kisawa abin
albarka. Alah yasa nan gaba tafi haka dan hakika tayi kokari.
Ai ni nayi zatan ta dainayin karatun ne yanzu saboda
yadda anaga tayi kiba sai naga ai mai akratu baya kiba. To
Allah dai ya taimaka, ya kuma kara bude mata kwakwalwar ya
linke takardar yasa a cikin Aljihunsa ni dai dag anan na tashi an
nufi dakina na barsu Yaya Auwal-ya shigo yana tambayar
Khadija, ina ina tace Yaya ai Yaya Humaira ta yi bacci ina jin
shi ya doka uban tsaki. 61
Lubabah!
Alhaji ya yi kiransa yace tsakin me ka kc yi, Auwal ko
wani abu kake nema ba sai ka hakurcewa safiya ba? in Allah ya
kaimu da randa lafiyar. Nan dai Yaya Auwal ya koma dakinshi,
amma har ga Allah in banda Alhaji ya sa baki ina ganin da sai
ya shigomin dakin. Ina kwance na yi fakarc naji Mama na
tambayar Alhaji ko tana wa nazo yace a'a mantawa kika yiw ai
meye yake damun kine, an tabbata wannan zuciyar akwai
magana, tayi dariya,t ace babu wata magana ji nayi kana ta
yabanta, ina tayi kokari a nan Alhaji wancan hutun fa ta biyu
tazo, mai makon ta tsaya a ta biyunta ko ta tafi ta daya sai ta
cilla har ta uku, kuma ace tayi kokari. Haba Safiya ai yaci a
yaba mata kin san shi yadda karatu yake nan dai suka zauna
suna ta tattaunawa.
A safiyar yau na tashi da matsananciyar ciwan mara,
saboda a duk lokacin da zan yi al'ada nakan fama da hakan
mama ta shigo ta riskeni ina ta juyi a gado, tace "Ke lafiya?" da
kyar na iya buda baki nace da ita "mama marata. Kasancewar ta
sanni da ciwon mara sai nan danan ta rude, tace, "Kai na rasa
yadda zan yi da wannan ciwon mara naki, bari in kirawo
Auwalu ya zo ya kaiki asibiti gashi babu kowa a gidan, kaini
dama ba'a tafi da Khadijaba. Ga Alhaji ya fita tun da dukuduku ni dama maganin hausa aka gwada miki, tunda na yi na
asibitin a banza. Maryam! Maryam!!" Mama ta kwala mata
kira, da gudu Maryam ta shigo tace, "Mama fitsari nake yi" "То
maza ki kirawomin yayanku, kice ya zo ya kai Humaira Asibiti.
A rude Yaya Auwal ya shigoda ga shi sai gajeren wando
da yar T. Sheat yace, "Me ya same ta Mama?" "Cikinta ne yake
mata ciwo dan Allah yi maza ka shiryo kazo ka kaita asibiti,
akwai Allurar da ake mata kawai ka kaita wajen doctor Sa'ida
kwai allurar da yake mata ako da yaushe. Da sauri yaje ya ziro
doguwar riga irin jallabiyyar nan ko T. Sheat din ciki bai
fiddaba. Cak ya daukeni kamar wata 'yar yarinya. Dama tuni
Mama, ta dagani ta shiryani tsab, saboda haka ko da jinin ya
zubo babu matsala, ba zai bata ni ba.
A asibitin ma bamu bata wani lokaci ba muna zuwa muka
ci karo da likita Sa'id yana ganina yace. "Waww Humaira time
is coming ko?" bai jira wata magana ba ya jamu zuwa daya
dakin dake kusa damu duk abin nan ina rungume a jikin Yaya
62
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
Auwal likitan ya fita da sauri zuwa can ya shigo rike da allura a
hannu ya kalli Yaya Auwal yace, to Auwal dan gyarata kafan
zata karbi Allura cikin sauri ya dan bude gefen duwawuna
kadan aka yi min.
Amma hakika da ina cikin hayyaci na ne da ban amince ba
shi kansa likitan ya zaci uwar mu daya Ubanmu (faya dashi, tun
da ba kowa bane ya san dangantakarmu dashi. Daga nan ya
umarci Yaya Auwal da ya kwantar dani nan da minti goma sha
biyar zan ware in sha Allahu. Hakan kuwa aka yi ban kai bama
minti goma sha biyar din ba jinin ya tsinke nan da nan marar
tawa ta lafa saı da na dan dara hutawa sannan muka taho gida.
A hanya ne yake cewa dani, Dama haka kike fama da
ciwon cikin nan, har likita yasan matsalarki amma ni da nake
gidan ban sani ba?" na sinkuyar da kai cike da matsananciyar
kunya dan ni a zatona yasan abinda ya sani ciwon cikin danni in
banda ya gayamin ma shi ya bude gurin da akamin allura da
ban sani ba balle ya yi tunanin ko saboda haka ne na ke jin kunyarshi.
"Amma fa gaskiya na tausaya miki gaskiya ya kamata ace
an yi wani abu, bawai a sami magani na lokacin cuta ba kawai, wallahi Alhaji na zuwa zan gaya masa, gara a nemo maganin da
zan rabaki da ciwon kwata-kwata. Nan dai yaci gaba da surutanshi, amma ni nayi shiru in banda tunani babu abinda na ke yi.
A haka muka karasa gida. Muna zuwa na wuce dakina dan
in yi wanka, in kwanta in huta. Tun da na fito daga wankan na
fada gado na yi kwanciyata ina bacci. Bant ashi tashida ga bacci ba sai da yamma likis misalin karfe hudu. Ina tashi na
kara fadawa ban dakin na dan watsawa kaina ruwa na sake shiri sannan na zauna na shirya kai na tsab, na dauki wasu kayana na fakistan, irin wadanda ake yayinsu a yanzu. Na tsuke kaina, dai dai da sheap din da Allah ya bani Gaskiya kayan sun bala'in yimin kyau na fito tsakar gida na zauna kai bakace nice nasha fama a dazuba. Nace "Mama wai ina Mary ne?" "Ta fita
ina jin ta shiga gidan makota, ba taga yau gidan shiru ba". "Amma Mama bata bin 'yan gidan su bila ko dan wallahi
yaran fitinannu nc. Sam basu da kunya. "Ina ai tun rannan da
wannan yarinyar ta gidan wacce suke kiranta Abulle ta kwada 63
L.ubabah!
mata dutse a kafa har tayi targade, shi ke nan ta daina zuwa gidan.
Alhaji ya fito daga dakinshi, nan da nan na durkusa har
kasa na gaidashi, danni ban san yana gidan ba yace ya jikin na
sukuyar da kai cike da kunya nace da sauki. Dan hakika nasan
ya sani nace kai Allah kai ka doramin wannan ace sam mutum
bashi da sirri, kai Allah ka yayemin yaci gaba da cewa Humaira
ki shirya gobe da safe manu Direba ya kaiki saban gidan
Abanki, dazuma muka gamu dashi yake cewa ya har yanzu baki
zoba? Alhalin kwana biyu dayin hutu? Shine nake masa
bayanin ciwan naki. To amma nace gobe za ki zo ki wuni ko
maman taku bata gaya miki cewa Abban naki ya yi saban gida
bane?"
"Alhaji ni ban sani bama a wacce unguwar ya koma?"
"Yana can Ribado Road Gaskiya gidan ya yi kyau Allah kuma
ya sanya alkhairi. Ai Maman taki ce wani lokacin sai ita. Na yi
juyin duniya taje ta masa Allah ya sanya alkhairi taki. Dan
hakika wanan gidan da ya yi duk wani mai kaunar sa ya masa
murna. Don wallahi ko alondon gidan sai haka.
Amma Mama bata ce da shi komai ba, amma da ganin
yadda bakinta yake motsi kasan akwai magana a zuciyarta, dan
haka tsagar na tashi na bar gurin ina shiga daki tun kan in shige
ciki sosai na ji yo muryar Mama tana cewa, "Haba dan Allah
Alhaji, duk abinda yake tsakanina da mahaifin yarinyar nan ai
bai dace a gaban ta ka ringa nuna ma taba, meye na cewa wai
kayi-kayi in je in masa Allah ya sanya alkhairi naki kana
tunanin cewa, ita yarinyar abin zai mata dadi ne? kuma in ca
aka yi in banje ba nayi Allah sanya alkhairi gidan zai ruguje to
sai dai ya ruguje din. Dan babu in da zani ita dai da ya zame
mata dole taje. Dan haka kada ka karamin haka a gaban
yarinyar nan. Abin da ke tsakanina daita daban, abin da ke
tsakanina da mahaifinta da ban".
A nan ne naji wani makokon bakin ciki, kishi mai tsanani
ya trnokomin, wai har yanzu uwata bata san ubana kishin
Alhaji ya kamani, na ji kamar in tafi in bar masa gidanshi sai na
ji ma kamar da gayya yake gayamin cewa mamana taki zuwa,
gidan mahaifin nawa wato shi ya nuna min cewa yana so in san
har yanzu uwata ba kaunar ubana take ba Nan take nace wai ni
64
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
mc yasd da ta nuna bata san shi ma ya dage, ya aurcta. Rabonki
sjiw ata zuciyar ta bani amsa fakat wanan shine amsa.
A washegari da wuri na kammala da shirina cikin wani
hrdadden dinkin shadda da ake mata hadi da code lace. Hakika
dinkin ya hadu, duk yadda akc tsammani ya wuce nan. Na fito
shirye tsab, yayin da mukaci karo da yaya Auwal a tsakar
ida yacc, "a'a Humaira manya ina kuma za'ad osa yau. Na dan
kaleshi gami da dan kauda kai nace, "Yaya Auwal kenan sai ka
ce wata mai yawan yawo. To gidan Abba zani. Zamu dai, wa
ai kaiki? Alhaji yace Mani ne zai kaini wane Manun bayan
gani, aikin me nake? Bari in karbo mukullin motar ki jirani,
hari in yis auri in yi wanka. Nima jiya nake jin labarin sun tare
a sabon gidanshi kai amma ina tayashi murna Allah ya sanya
Alkhairi amin.
Amin nace adede lokacin da mama ta fito daga dakin
girki, yayin da shi kuma ya shige dakin Babansa ya gaidashi, ya
kuma tambayeshi mukullin motar, yana fitowa ya daga mini
mukullin motar yayi gaba yana dariya.
A lokacin da ya kammala da shirin shi sai ya fito ya
umarceni da in fito mu tafi Maryam ta fito a gujc tace "Yaya
Auwal dani fa za'aje ka tsayani in shirya", Yace, "da kinsan
zaki kika tsaya wasa, yi sauri ki shirya ina jiranki". Mama tace
"Ji yadda ka bata rai kana magana sai kace mai magana da
sa'arsa ke kuma kiyi sauri ki fito ku tafi ke kuma Humaira ai
kun je kya gaida Baban naku ki kuma gaida lya da kyau.
A zahiri wannan abu yakan dauremin kai, sam mama bata
son Abbana, amma tana tsananin san mahaifiyarsa, yayin da ita
kuma lya tana nan tana ciki da bakin cikin yadda Mamana taki
danta fafur, duk da irin wahalhalun da yake sha a kanta. Nan
dai na amsa mata, muka yi mata sallama muka tafi.
A hanya ne Yaya Auwal ya shiga yimin shirarraki, yace,
"Yauwa Humaira wato shine rannan kika shanyani daga kije
kiyi sallah, shi kenan ban kara ganin kiba" "Amma fa yaya
Auwal kasan in muka idar da sallar magariba anan muke zama
muna addu'o'i da karatu har lokacin sallar insha'i. To yanzu
ana zazzaune, sai in tsallako in taho Yaya ai sai sù Alhaji ma su
zargi wani abu. 65
Lubabah!
A'a to in sun zarga meyc? kika sani ko ayi mana zargin
alkhairi a'a Yaya irin haka ai sai kasa a zargeni ko ma soyayya
muke (Hakika ni na san abinda Yaya ya ke nufi kenan, to
amma na yi kodarin in nuna mas aban san inda yasa gab abane,
dan kada yayi saurin gane ni mai wayoce) Ya dan waiwayo ya
kalleni, gami da kashen ido, kasancewar a gidan gaba nake da
zama yace, "Allah ko?" Ashe dai kin san soyayar da har kike
zargin za'a zargeki da ita. Ni na yi zatan ma baki san taba. Nan
da nan na ga ne cewa lallai yaya mai wayo ne,w ato ya dagoni
ke nan. Nan da nan na sunkuyar da kaina.
A hankali muke tafiya sautin kida mai ratsa kwakwalwa
yana tashi, ya sake lumshe ido yana murmushi yace, "Uhm, ina
tambayarki shin ita soyayyar kala nawa ta kasu? A'a ni yaya
wallahi ban sani ba. To shi kenan abar maganar wata rana zan
turaki gonarta, in kinje kya gayamin kala nawa kika noma". Na
tuntsire da wata mayaudariyar dariya nace "Kai yaya ke nan"
ita kanta magana ta wata siga ta daban nayita. Haka muka tafi
muna hira har muka karasa kofar gidan.
A falon Hajiya lya muka fara masauki, bayan mun gaidata
ne take cewa, a'a. Ni wannan shirin ya yi min, ni badan bama
kada ace na yis aurin karaya, daba sai ince na yafe auren naka
ba, in maka can ji da wannan kwakyalarba. Na kwashe da wata
irin dariya mai sanyin sauti, nace. "Amma fa Hajiya Iya kin
gama dani, kuma gaskiya kin sai dani arha, in banda abin ki ina
ni ina auren Yaya. Yaya ai Yaya nane ni kuma kanwarsace, ko
Yaya, ai bama haka da kai ko? wani irin matsiyacin kallo ya
watsomin mai hanzarta ratsa zuciya, baice dani komai ba ya
juyar da kansa, zuwa ga Hajiya Iya yace Hajiya in kinga hakan
ya dace ba sai ayi ba.
A nan dai muka dan taba hira sannan muka karasa cikin
gidan. Zaune a falon Hajiya Rabi Nasir ne kishin gide yana
ganin mu ya hanzarta, tashi zaune tamkar marar gaskiya. Nan
da nan ya shiga kwalawa Hajiya Rabi kira, wai tazo tayi baki,
da ganin idanshi kasan akwai munafunci a cikinshi, dan kuwa
kiran da yake kwala mata wata siginace ya ke mata, t ahanyar
yaudara wato duk abinda take shirin kawo masa ta san dai
akwai baki. 66
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne.....
A nan ne ya shiga wangalc baki, yayin da ni kuma nasha
kunu babu wata alamar fara'a a fuskata na zauna kan kujcra na
gridashi, tunda g anan ban kara cewa komai ba. Shi kuwa yaya
Auwal hannu ya mika masa suka gaisa. Yayin da suna cikin
gaisawa hajiya Rabin ta fito. Na durkusa har kasa na gaida jta
(Dan hausawa suna fadin durkusawa wada ba gajiyawa bane).
Na zauna kadan ina jin su yaya suna hira shi da Nasir. Nasir ya
dago kai yana murmushi, yace Malama Humaira 'yan
makaranta. Ya karatu?" Na doka masa harara nace lafiya lau.
Yayin da na mike gaba daya na nufi waje kai tsaye na lura da
wani dan bangare da ban wanda aka kawatashi, babu tantama
bangaren Abane. Dan haka sai kawai na nufi dakin kai tsaye
rike da Maryam a hannuna ita kanta Hajiya Rabi tasan jiya ba
yau bace shi yasa in taga na nufi dakin mahaifina bata min
katsalandan kamar da. Nasir ya leko yace dani Humair ain kung
ama da Abban, ina son ganinki in na kalleshi hakika zanso
Alade a zuciyata. Na yi banza dashi.
A hankali nayis alama, gami da kwankwasa kofar gaba
daya. Yayin da Abba ya umarceni da in shiga. Na shiga na
durkusa har kasa na gaidashi yace, "Humaira yan makaranta
nayi murmushi, yace "Ya karatu?" Nayi murmushi nace "lafiya
kalau". "Ya jarabawa?" "Alhamdu lillahi" "an yi abin kirki
ko?" E babu laifi Abba nice na zo ta uku Ba laifi kam amma a
kara dagewa Allah ya bada sa'a nace, "Amin".
"Amma gaskiya Abba gidan nan ya hadu kai Allah yasa
rai a ka yiwa. Allah kuma yasa mai amfani ne yayi murmushi
yace Humaira Bahauishiya lallai kin iya addu'a to na gode kin
ga dai yadda Allah ya yi damu kuma? E wallahi, ai da ma shi
Allah babu abinda bai iyaba, Allah dai ya rabaka da mahassada.
Amin Humaira yauwa dama ina son in yi miki wata magana, to
amma na fi son sai mun sami kamilallan guri, tun da na ga ba
ke kadai bace, kuma hakika maganar sirrice, tsakanina da ke to
Abba yaushe zan zo duk sanda kika sami dama, dan yanzu bana
fita sosai koma bana nan ba sai ki jirani ba.
Amma ni dai Humair aina son in ga kin fitar da gwaninki
tun yanzu dan gaskiya ina son in ga da zarar kin kammala
karatunki an yi miki aurenki, dan gaskiya dukw ata mace bata
7
Lubabah!
mutanta sai tana da aure. Kuma nima hankalina yn fi kwanciyа,
tun da ke kadai Allah ya bani.
"Au wai shin ina takardar sakamakon na kine?" "Tana
gurin Yaya Auwal, muna cikin maganar saig ashi ya shigo. Ya
durkusa har kasa ya gaidashi ya dan kalleni ba tarc da sakin
fuskaba sosai yace, ke kije Nasir na kiranki". Abba ya dan
kalleni ya kawar da kai gefe guda, yayin da ya kira Maryam
yace, zo nan maryam tawa. Ni duk naga yau kinyi sanyi sai
kace wacce aka yiwa wani abu yau ko gaisheni ban ji an yiba.
Maryamt aje ta zauna kusa dashi tana murmushi, amma ba ta ce
ko mai ba.
A hankali na kara kallan Abba muka hada ido, yace, "Ke
ba kiranki ake ba? "Na dan bata rai nace Abba to ni in naje mai
zan masa? Ya yi 'yar dariya yace "nasir ya kasa ganewa, nace
dashi ya guji mace da sharrinta, na fada masa ba daya ba ba
biyu ba. Nace in har ya nemi yarinya ta nuna bata sonshi, to ya
rabu da ita. Dan wallah in har ya dage, tofa karshensa shine a
wahale, dan ko ta dawo tace tana sonka aikin banzane
yaudarace kawai.
Amma ai shikenan. Hakika naji dadin wannan magana ta
mahaifina, dan hakan ya nuna bazai min auren dole ba. yayin
da na lura da yadda Yaya Auwal yake fara'a ganin cewa Abana
bai goyi da bayan abin ba. Abba yace da Yaya Auwal ina
takardar Humairar ne? tace tayi na uku ko?" Yaya Auwal ya yi
murmushi yace E Abba amma kuma na manta takardar a gida,
in mun koma na kawo maka yace 'to'.
Abba yaci gaba da cewa Auwalu kai namiji ne in har kuna
shiri da Nasir ka gaya masa gaskiya. Dan gaskiya ni ba zan
yiwa 'yata auren dole ba Yaya Auwal yayi murmushi ya
kalleni.
Abba ya dan doki Maryam a baya yace ke dai Maryamw
ani lokacin kin cika muskilanci. To ku tashi in zaga daku ko ina
a gidan ku gani kai ammafa wallahi gidan ya bala'in tsaruwa
yadda baa tsammani dan ni komai kwancemin ya yi, hakika,
duk wanda yaga gidan yasan mai gidan ya gama hadewa, ta ko
ina. Dan kam babu ce kawai babu agidan, amma komai ya
gama tsaruwa. Nan dai muka kara sawa abin albarka daga nan
muka zarcc dakin Hajiya iya harşhi Abban. Nan ma mun jima
8
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
muna hira ta dubi Abba tace, ni Alhaji, ai da kiran Alhaji
Safiyanu kayi kuka shirya yiwa yaran nan aure, Abba ya yı
dariya yace haba Hajiya, ai ni an daddara da yiwa aure
katsalandan in har suna son junansu har sai mun yi shawara
Hajiya ai su za su je su shirya kansu, tukunna.
Aini Hajiya da hakan zai kasance da nafi kowa so. Don
wallahi yadda Alhaji Safiyanu ya rikemin jinina tamkar nasa, ai
kowani na shine yace yana son 'yata, kuma suka dai-daita ai ba
zan hana shi ba balle kuma 'yar cikinshi. Ni dai auren dole ne kawai ba zan wa 'yata ba.
A zahiri ba karamar kunya bace ta yayyameni, shi kansa
Auwal din na lura da irin tsananin kunyar da ta kamashi, nan
dai muka mike gaba daya muka fice, Hajiya lya tace, "Ja irai
suna so suna kaiwa kasuwa" Aini Alhaji tuni na ganesu". "Tо Hajiya mudai fatanmu Allah ya hada kawunansu.
69
Lubabah!
un daga ranar Yaya Auwal ya shiga nunamin wasu T
alamu amma ya kasa tunkarata gaba da gaba ya gayamin
komai yake tsoro oho? Ana saura kwana shida mu koma
makaranta ne Aba ya aika a gayamin cewa Hajiya lya bata da
lafiya. A rude naje na sami Alhaji na gaya masa, a lokacin
direban Abban ne ya zo ya sanar dani Yaya Auwalu na falon
nan yace wa Alhaji ai sai mu taho tare dashi. Gidan baya na
shiga na yi zaton zai shiga gidan gaban da yake a motar Abban
zamu tafi amma sai naga ya shigo bayan shima, Alhaji ya biyo
mu abaya yana bawa Auwal sakon ya gaida masa da Abban
nawa, ya kuma yiwa Hajiya Iyan sannu suma suna nan tafe shi
da Maman da daddare.
Ta yi dare-dare bisa gado na shiga ina murmushi nace, a'a
duk ciwanne haka? Ya jikin tace da sauki nace ni nayiz atan
zan zo in same ki a kwance sosai, Abba duk yabi ya rude, ashe
ma murace kawai take damunki? Y ajikin tace da sauki yayin
da ta kama tari nace, ke wallahi hajiya lya haka kike, shekara
sittin da hudu kawai duk kin bi kin kwararrabe wannan in kika
kai dari kuma ya ke nan?
Ta dan yi murmushi tace karfin hali tace, kai ya dai 'yar
nan shekara sittin nan take? Yaya Auwal yace, Ai kuwa yanzu
take ganiyar ta, ni dana shirya auren yanzu, ba ita zan
kwasheba. Tace ni na yafe gadai wacce na bakanan dan in
fanshi kaina. Na dan yi dariya nace, ke Hajiya Iya in banda
abinki an taba fansar kai da maganar aure ne?" "E ni na fanshi
kaina ta bani amsa. "Yanzu dai kam jiki da şauki Allah ya kara
lafiya amin summa amin mun jima muna hira da ita, sannan na
koma cikin gidan muka gaisa da Abba sannan muka tafi.
Tun da muka dawo Yaya Auwal ya tsayar dani a kofar
gida yake tambayata a kan lallai sai na gaya masa saurayina. Na
yi dariya nace, "wallahi Yaya bani da saurayi". Yayi murmushi
yace, "Kai Humaira ki gayamin gaskiya. Allah nasan ba zaki
rasa ba koda a boye ne, yanzu shi Nasir a wane matsayin yake?
"Ni wallahi Yaya Auwal ka daina yimin maganar Nasir Nifa ba
saurayina bane makwawącina ne shi kawai. Ni kuwa wallahi
70
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
yayi ya gama ni fa na gaya maka bani da wani saurayi". "To ai
shikenan tun da baki da saurayi zan yi kokari in samo mikı bai
dace ace kyakkyawar mace, kamar ki ba ta zauna bata da
saurayi". Nace "Allah ya kaimu lokacin.
"To Yaya ni zan koma gida" "Au haka ma zaki ce muna
tsaye muna hirarmu shinc zaki gudu gida?" Amma shi ke nan
sai an jima da yamma ma hadu. Ni dai na shige cikin gida yayin
da shi kuma ya shige dakinshi.
Tun da na shiga gidan zaunc muke a tsakar gida ni da
Mama da Maryam muna hira Nace Mama ni na rasa abin da
yasa yanzu Maryam in mun je gidan Abba bata sakewa sosai.
Tayi tsagal tace, "cab bayan hajiya Rabi ce tace wai na cika
shishshigi, sai kace Ubana, wai in ta kara ganin na zo gidan ina
damun mutane da surutu sai ta yankani". "A'a bazata yankan
keba Maryam (Mama ta fada) wannan ankwai mahaukaciya, to
in banda shirme irin nata Maryam dinma abar ayiwa kishi ce.
To ai sai ki dana zuwa, kiyi zamanki gidan Ubanki, bamu
gaji da keba, dadin abin kema da na ki Uban. (Da farko abin ya
dan sosa min rai sai naga kamar da gayya Hajiya ta fadi hakan).
Na yi murmushin, karfin hali nace, "amma Mama bai kamata ki
biyc mata ba tun da dai kin san sam ba wani tunani take da shi
ba ai ni tuni na dawo daga rakiyarta, don hakika nali lajiya
Rabi tunani na rasa abinda yake damunta". A to ai gashi nan
har yanzu jiya wa yau. haka dai muka zauna muna ta hira, a
kalla mun fi awa daya a tsakar gidan saboda ko mun shigama
babu wuta.
Taci gaba da irin rurin kidan da ta saba, wato wayar salula
Yaya Auwal Hajiya tace kai ni na rasa dalilin da yasa Auwalu
yake barin wayar nan a kunne kuma yayi nisa da ita su kuma
masu bugowa ga shegiyar kwawar tsiya, in sun jima ba'a dauka
ba sun ringa yi kenan. Humaira maza ki je ki dauka in kuma
bata kusa shi kenan in sun gaji sa daina. To gida ne babu kowa Maryam ma in tana nan me ye in ba shirme ba. Ai shima
Kawun nasu yayi shirme da yaga an kusa komawa ba sai ya
dawo da suba amma yabar yara ko sai ana gobe za su koma
zaida wo dasu.
Tun da Hajiya tace in je in dau waya naji gabana ya yanke
ya fadi. Ba dan komai ba sai dan ina gudun 'yar gidan jiya wato
71
Lubabah!
kada in ganshi ayanayin da na ganshi ran nan. Na shiga falon
hade da sallama, amma ba'a amsa min ba, shiru na duba ko ina
a falon babu alamun ga daga inda karan yake, dif na ji wayar ta
daina rurin. Na juya zan tafi,s ai da na zo daf da kofar fitar
sannan na kara jiyo sautin kidan ta daga cikin daki, na yi kamar
in share wato in fice kawai sai na yi wani tunani ya zomin ta iya
yiwuwa bama ya fakin yana can waje dan haka kai tsaye na
dama kai cikin fakin.
a
Turkashi, mai zai faru ai Yaya Auwal na gani ya kwanta
bisa gado yayi dai-dai dashi da shigar da n aganshi rannan wato
kwance ya ke daga shi saig ajeren wando. Na yi kamar in koma
sai na tuna cewa in har wayar taci gaba da kida tofa Mama zata
iya tambayata dan me ban dau wayar ba? koma tace dani in
tashi in dawo in dauka. Na dauki wayar a hankali na