sonta yana fara maganar kamar dama iyayenta jira
suke yi suka matsa masa akan lallai ya fito.
Da da farko yace shi bais hirya ba in kuwa haka ne sai dai
ya hakura da ita a inda mahaifinsu yace atabau sai ya yi auren
jiran me ya ke yi kuma ba zai maidasu mutanan banza ba ta sha
jin yana cewa shi yarinyar har ta fice masa a rai dan dai kawai,
baya san ya sabawa Babansu maganarsa ne kuma hakika kowa
da ya ganta ya furta cewar sam basu dace da juna ba.
12
3
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
B
ahad, dane na farko a gurin mahaifiayrsu yayin da yake F
na biyar a gurin mahaifnsa. Duk cikin su babu wanda ya
tsaya yayi ilimin boko sosai kamar shi, domin kuwa a
yanzu haka shi likita ne guda a bangaran fata, da kuma ido, to
amma ya fi bada karfi a gurin fata, a yanzu haka aiki ya ke a
asibitin Abuja, a matsayin likitan fata yanzun ma hutu ya dauka
na wata daya ya dawo nan Zamfarar amma da zarar ya
kammala hutunshi zai koma.
Fahad ya kasance mutum ne mai kunya da kuma kawaici,
ko lokacin kuruciyarsa manya na yaba hankalinsa, kawo ya
zuwa yanzu, dan duk 'ya'yan gidan babu kamarsa yayunsa
daya ne namiji, amma sauran duk matane wanda tuni su
mahaifiyarsu ta rasu, amma a. yanzu sun dauki mahaifiyar
Fahad kamar ita ta haifesu. Dan komai nasu ya koma hannunta,
sauran matan ma duk an musu aure.
Fahad sun kasance susu uku ne a gurin mahaifiyarsu,
dayar ta rasu a yanzu haka saura su biyu, daga shi sai Shafa'atu
wacce ta gama makarantar. Sakandire dinta shekara biyu da
suka wuce, miji ne dai har yau Allah bai bata ba. Bawai bata da
samarin bane a'a tana da su auren ne dai Allah bai kawo lokаci
ba.
Fahad ya auri matarsa Khadija, kusan ace akan dole, to har
yanzu dai zamang ashi nan ne, dan iyayen yaran mutane ne
masu san nuna tsabar iko yayin da shi kuma yake nuni da cewa
basu isa ba su juyashi, mahaifiyar ta kullum tana hanyar gidan
dauke da jarkar rubutu ko kullin magani, dana zuba masa, har
shi da kansa ya fara fuskantar hakan yayin da ya taba kora
musu ita akan shi ba zai dauka ba, asalima daga yin auren har
ya mata saki daya saboda sam Khadija bata cikin tsarin matan
da yake muradin aura a rayuwarsa.
Fahada ra'ayinsa baya sha'awar mata biyu, dan shi
likitancin ya ratsashi, kuma shi mutum ne mai sha'awar matar
da ta kware wajan kula da mijinta, gami da bashi hakkinshi, sai
gashi Allah bai cika masa burinshi ba, dan kuwa gaba daya
13
Lubabah!
tsarin Khadija kni ka ranise bate yi makaranta ba tamkar ir matan nan ne da ake musu lakanin babu arabi babu boko.
Fahad ya tsani dabi'unta, shi yasa ako da yaushe yana cikin hantararta, ta kasancewa sam bata iya abinciba, dan haka yake kunyar zuwa da at stansa gidan, ga kuma kazanta, tukwananta duk, sun dafe da b. i tamkar wacce ta yi shekara
da shekaru a gidan. Ga rashin ku wa da al'amuranta, sau biyu Coker gas tana kamawa a gidana shiri ya daina kawo mata
gas a dole ta koma aikin risho amma duk da haka in ka shiga
gidan ka kuma shiga dakin girkinta zaka rantse da itace take
girki. Ga wani abin haushin daki guda aka ware dan kayan wanki, amma wani lokacin ma da zarar ta cire kayan kawai
jefasu zata yi dakin babu tunanin ta adanasu gu guda, wani
lokacin ma in ta rasa kayan da zata sa a cikin kayan dattin take
zuwa ta zabo, koda kuwa unguwa za su tafi, bata damu da
yamutsarsu ba kamar yadda bata damu ta sa turareba. Hakika
wannan dabi'un nata su suka hana Fahad tafiya da matarshi
Khadija, Gashi sam bata iya wata kissa ba, balle ta janyo
hankalinshi burinta kawais hine, in zai tafi Abuja ya bata
isassun kudi, to ko wata zai yi ya je ya yi, wannan bai dame ta
ba matsalarsa ce ba tata ba.
Fahad ya kasance mutum ne mai kare mutuncinshi Allah
kuma ya taimakeshi bai kasance mai sha'awa ba sosai shi yasa
babu ruwansa da naiman mata, abin da kawai yasa a gaba shine
aikinshi, wani abin sha'awa kuma gaba daya 'yan gidansu
kansu a hade yake babu wani banbanci. Gaba daya yan gidan
nan sun tsani Khadija ko kuma in ce sun tsani halayanta, kowa
kuma mamaki yake, da ya aureta, saboda Fahad mutum ne, shi
fan kwalisa. To amma duk da haka in aka ce kaddara to fa an
gama komai, hakika kaddara da matsanancin rabo ne suka
haddasa wannan kadartaccen aure.
14
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
A
lokacin da suka isa Asibitin, har sun tarar da wasu sun A
fara zuwa, wanda harsun fara korafın anbar yarinya
sama da awa daya ko wando ba a sa mataba, suna cikin
tattauna maganar nc saig ashi sun shigo nan da nan kuma sai
suka yi tsiru-tsiru, wannan ya kalli wannan wannan ya kalli
wannan, Fahad ya dan hada rai kadan alamar babu wasa ya durkusa har dasa ya gaida su ya ja wata kujcra ya zauna yayin da Shafa'atu da Humaira suke a tsatstsaye Fahad ya karbi jakar ledar dakė hannunsu ya mikawa bakin yace a duba kayan da ya dace a sawa yarinyar a sa mata.
A zahiri hakan ba karamin kunya suka kara jiba dan haka
suna gama sawa jaririya kaya suka fice, suka ce da Khadijan za
su jira a waje. Fahad ya tashi daga kujerar ya koma gefen gadan ya zauna, yayin da ya umarci Humaira da ta zauna. A hankali ta dubi Khadija ta gaida ita gami da yi mata barka. Fahad ya karbi jaririyar ya mikawa Humaira ita yace, kin gantanan dawa kuka ga tayi kama a cikinmu? lumaira ba tace komai ba baya ga murmushi da tayi Shafa'atu ta shiga mamakin yadda yaya Fahad ya ke sakarwa Humaira fuska haka sabanin yadda ya ke wa mutane.
Amma fa ba karamin faduwar gaba Khadija, ta ci karo da shi ba ta dubi Shafa'atu tace, "Shafa wacece wannan kuma, tsagal Fahad ya yi yace bakuwace, kin santa ne kike tambayar wacece?" "a gani na yi ban san ta ba shi yasa nake tambayarta "Uhm to bakuwace" wai shin da likita ya zo mai yace ne?
ko da
"A'a ni tun tafiyarka likita bai zo ba-sai dai in kai za ka je wani abu" "To bari in je in same shi shin me yake
tafı
damunki ne a yanzu, in kuma ba bu in nema mana sallama mu gida ko kuwa ba yanzu kike son komawa ba?" "Wa zai so zaman Asibiti, amma Inna ta aiko kan cewa su gwaggo su sanar da
ta
kai a kaini gida in yi wankan jegon a can tun da haihuwatace fari.
"Allah ko?" to a zahiri ni bani da irin wannan ra'ayin a
tsarin rayuwata wai shin ma in tambayeki wani abu ne zai kamaki a gidanki har in kuka yi wanka a can na lura da ke tun 15
Lubabah!
kan ki haihu kike cewa dani zaki gida wanka, kuma na gaya
miki ni ban aso to kuma mai ya dada tado da maganar yanzu?"
"Aı wallahi babu ruwana, ni dai bani nace musu zan koma
ba, sų suka ga ya dace in koma". "Uhm I sec, kina nufin kice
min su suke iko da ke ko, ba ni ba? "To ba iyayena bane zan
kuskure maganar su ne?" Shiru ya yi saboda takaici ganin haka
Humaira ta mika masa jaririyar suka yi waje abinsu.
Amma wannan akwai sakarai, yanzu mijin nata take
gayawa magana haka a tsatstsaye? (In ji Humaira) yayin da taci
gaba da cewa shin tayi makaranta kuwa?" Ta yi mana hadda
Sakandire.
A gaskiya in har haka ne to kuwa ta yi asara a rayuwarta,
ta ringa magana kamar ba da mijinta take magana ba ko irin
'yar kwaikwasar nan babu sai tayi wani sangargar tana magana
a tsatstsaye kai amma yayan nan naku ya more da mata".
"A zahiri ba ke kadai kike jin ciwon abin nan ba wallahi
duk 'yan uwanmu suna jin haushin wanan abu ai sam ba sa'ar
gurbinsa bace shi kansa na tabbata ba a son ransa yake zaune da
ita ba, dan babu yadda zai yi ne saboda Babanmu yace, ba zai
mai da shi mutumin banza ba ya so a nemo masa auren daga
zuwan yarinyar ya sake ta, to wallahi saboda haka ne kawai ya
ke zaune da ita".
"A to kinsan rabo kuma in rabo ya rantse babu makawa,
amma fa gaskiya ba sa'ar yinsa bace. Ta yaya za a yi mutum
mai ilimi kamar wannan wanda ya ke da matsayi har na likita,
amma ya zauna da irinw annan matar. Ai kinsan yawanci
matansu daban suke tamkar dan su Allah ya ke halittarsu. To
amma duk da haka ke ma da ke tun da dai ke wayayyiya ce
kuma kince in yayan naku baya nan ke kike zuwa tayata kwana
ai kamata ya yi ku ringa nuna mata irin kissosin da kika sani.
Amma wallahi yayannan naku macece kawai ta rage shi".
"Amma duk da haka za ki sha mamaki in har nace miki
bashi da sha'awar kara aure, shi ako da yaushe maganarsa daya
a rayuwa mace daya yake muradi, shi baya san mata biyu. To
"ai naga yadda zai yi tunda Baba ya hanashi sakin matarshi, ita
kuma bata gabanshi, na gani, shin sakinta zai yi ya karow ata
ko kuwa haka zai daure ya ci gaba da rayiwa da ita. In kuwa
16
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
haka no to kuwa lallai zamu iya kiran унун da irin muzип ри
Ruke rako maza duniyn",
H
"Alfn feren, rabu da maganar yayan nan naki, ai namiji
bashi da tabbas, su bi su kalallame ki da magana yayin da uke
shaukin soyayya sai gaba Nonon ya dade ya fara tsami sai
manta da alkawarin da aka yi ni nawa mijin meye bai ce dani
ba, amma daga karshe da zan sanar dake abinda ya yi min da
kinsha mamaki".
"Au don Allah dama kina da aurc? Wallahi ko kadan baki
yi kama da mai aure ba. Ke kuwa dan Allah mai ya yi miki?"
Ke dąi kawai share za ki ji komai a lokacin da na tashi baki
labari na. Asalima a yanzu haka babu aure a kaina aini ba jahila
bace da zan gudo da igiyoyin wani a kaina hatta iddata sai da ta
cika, amma a ranar da iddar tawa ta cika na tsallako kafa na
gudo. Ai har ina da 'ya'yana biyu mace da namiji.
"Ai kuwa wallahi babu kama, wallahi ni abinda nake zato
da ke shine, ko za a miki auren dole ne kika gudo, ko kuma
kishiyar uwace ta takura miki kika gudo". Ta yi murmushi
tace," ke dai share wannan maganar bana san tuna ta a yanzn
amma in na tashi baki labari za ki sha mamaki, hatta yadda
Babana ya yi soyayya da uwata zan sanar dake, domin kuwa
labari ya iskeni". "To Allah ya kaimu lokacin".
A hankali Fahad ya kc tafiya yayin da ya fito daga dakin
dan su tafi kallo daya za ka masa kasan cewa ba a hayyacinshi
ya ke ba, wanda hakan ya tabatarwa da su Humaira cewa sun
haura da Khadija, kuma hakika bata gaya masa, mai dadiba.
Idan sa kyar akan Humaira wanda hakan ya masifar bata
mamaki, ta tuna tsananin kishi irin na mata, kar dai ace akanta
suka haura yayin da duk jikinta ya yi san yi hakan kuma ya
yiwa Fahad dadi a rai dan yana ganin a duk lokacin da ya fadi
tayin sa za'a hanzarta sai da masa, dan tabbas alamomin kunya
ma suna daya daga cikin alamomin soyayya. Duk da 6acin ran
da ke addabarshi, hakan bai hana shi murmusawa ba yace, "Sai
ku zo mu tafi ko.
"Amma yaya ai ya dace muje muyi sallama da Anti
Khadija ko?" cewar Shafa'atu "E ke kya iya zuwa, amma ita ta
zo mu karasa mota ki je ki dawo" Ta yi shiru kamar tace wani
abu amna sai ta kasa sakamakon kallan da ya wurgo mata
17
Lubabah!
alamun ba wasa ita kanta Humaira sai taji duk jikinta ya yi
sanyi tabbas abinda take zargi ya zama gaskiya.
A motane da suke zaune kafin Shafa'atun ta dawo, yacc da
ita, "lumaira wai mai ya baroki daga gaban iyaycn ki kika zo
nan? Kuma hakika daga ganin ki ke 'yar manyan mutane cе.
Sannan kuma hakika akwai dattako a gidanku tunda ki ka yi
tunanin tahowa nan wannan ya nuna tabbas akwai tarbiyya a
gidanku, kuma kema da g ninki an ga kamilalliyar yarinya ko
da ya ke Hajiya ta sanar dani, duk abinda ki ka gaya masu.
Amma in da gizon ya ke saka a nan shine ya kamata ace
kin sanar damu labarin ki da ainishin dalilin baro warki gaban
iyayenki ko da yake Hajiya ta gargadeni da cewa kada in
tambayeki a bari sai kin saki jikinki damu sosai to amma a
kwana dayan da kika yi naga kin saki jikinki, don duk wanda
ya ganku ke da Shafa'atu zai yi wahala yace jiya-jiyanan kuka
san juna.
A hankali ta dago kai ta kalleshi, idanta cike da hawaye,
yayin da shi kuma ya zuba mata ido, kamar ya cinyeta danye. А
hankali ta saukar da kwayar idonta kasa hakan ya dimauta
Fahad. Dan kam ta bala'in kayatar da shi.
A gaskiya Humaira bai dace ki maida kanki kabewaba.
Hajiya ma tace dani da suka tambayeki kuka kika fara shin wai
duk mai ya kawo haka Humaira ya zama dole ki sanar damu
dalilin da yasa kika baro gidan iya yenki, dan sanar damudin
shi zai karamana, kwarin gwaiwar amincewa da zamanki damu,
bawai dan bamu yadda da ke bane no ba haka bane, don da ba'a
yadda da keba tun farko da ba a kyaleki kin kwana a gidan ba.
Amma yaya Fahad zan so ace kun min hakuri nan da 'yan
kwanaki in sha Allahu zan sanar da ku komai. To na ji ama
kimin alkawarin ni kadai zakif ara sanarwa labarinki, in Allah
yaso sai ki sanar da su Hajiya daga baya. "To shi ke nan na
amince, amma dan Allah ya ya Fahad mai yasa kaki amincemin
da in je in yiwa matarka sallama kaddai ace zuwana ya haddasa
fitina a tsakaninku kasan mu mata da gajen hakuri tun da ba
sanina tayi ba. Ta kasa gajen hakurin da za ta ji labarina kada ta
kawo zargin komai.
Amma kin ban mamaki da kika kasance mai saurin
fahimta, wallahi ina san mace mai saurin fahimta, ki ga dai ke
18
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
ba sanina kika yi ba. Asali ma yau yau din nan kika fara ganina
amma lokaci daya har kin fahimceni. To amma kada ki damu,
wanan 'tsakanin munc ni da ita kin gane, kuma yanzu har na
gama yi mata bayani ta kuma gamsu kai ku dai mata da wuyar
sha'ani kuke. Shafa ta karaso a hankali, Fahad ya dubeta yace
shin ke mai ya zaunar dake haka wallahi da mun yi lafiyarmu.
A raunane tace da shi a'a sako ta bani gurin hajiya yayin da ta shiga suka tafi.
F
ahad zaune gaban Hajiya, ransa a bala'in bace, yace "To
yanzu dan Allah Hajiya naka zanci gaba da zuba musu ido,
sai abinda suka ga damar yi dani wannan ma ai na zubar da
mutuncina kuma kimata da martabata zata zube a idon mutane
da abokaina, yau kwana hudfu da haihuwarnan, amma kullum a
tashin hankali muke, wai ta dage ita ana yin suna tafiya za ta yi
dan ma nace da ita in har tace gida zata tafi to kuwa bazan mata
komai da taron suna ba, shi yasa ta hakura ta zauna. Amma
wallahi Hajiya ni na riga na rantse, in har suka ce sai ta koma
gida to kuwa sai dai in auren babu shi. Dan na lura kullum da
masu zuwa su zugata. Allah ki sanar da Malam, tabas suka zo
suka dauketa to kuwa su hada da kayanta su kwashe ni dama
Hajiya tuni yarinyar nan ta fita kaina Hajiya kinfi kowa sanin halin da na ke ciki, to ni dai na yanke hukuci na karshe
tsakanina da ita".
"Fahada ko da yaushe ina nusar da kai da cewa komai na duniya hakuri ake yi a rayuwa, ka yi hakuri ta tafi din, kwana
nawane, in kasawa zuciyarka hakuri sai kaga kamar yau ne, in banda rigima irin taka, kai da ba mazaunin gari ba ji nake kai da ba kinka kake sanar dani cew abayan suna da kwana uku zaka tafi kuma in ka tafin nan ka kan yi wata baka dawo ba. To mai
19
Lubabah!
nena na kalcwa haka a zauna ana ta faman ciccira magana, ni
wallahi bana son tashin hankali ko kankane".
Fahad kansa a sinkuyc ya dago da kansa a raunane, yace, "Hajiya duk nasan da haka. To amma abinda za'a duba a nan
shine, hajiya tun kan yarinyar nan ta haihu muka yi maganar
nan da'ita,c ewa ni bana son zuwa gida wanka, tun da ba addini
bane ya shimfida nace in ma tana ga tafi son a kawo mata mai
dora garwa ta Gangaren tane, ta sa a kawo mata ammá komawa
gida babu shi. To kuma Hajiya sai yanzu iyayenta su zugeta,
yarinya ta tubure min tace sai ta koma Hajiya in har na kyaleta
ai kuma shi kenan sun sami abin yi gaba kuma ban san abinda
za su tsiro min da shi ba su kansu, ai sun nuna rashin dattako a
al'amuransu. Dan haka gara tun yanzu in nuna musu nifa
namijine, kuma da kafata na tsaya, ban dafa kowa ba a
bangarensu balle su shimfida min mulkin da za su takurani, da
sharadin in ban bisu ba a goce in fadi".
Fahad na san da haka kuma hakika nasan kaima kana da
taka- gaskiyar dan shi kansa Malam yace bai amince ba. To
amma ina ganin da ka amince tun farko Malam ba zai hana ba,
zai ce ai matarkace, kana da iko da ita amma Fahad tun da na
fara hafuwa sai hakuri habu yadda za a yi an riga an zama
daya".
Fahad yace, "Dan Allah Hajiya kiyi hakuri, kin san
wannan bashi ne karo na farko ba, da suke son ta kuramin yin
abinda ban yi niyya ba, dan Allah wannan karon kiyi hakuri ki
barni dasu, tunda Malam ma ba so yake ba to fa na kara samun
mafaka gami da kwarin gwiwa. Hajiya dan Allah wannan karan
ki barni dasu ina ji Allah ne ya karbi addu'ata dan ako da
yaushe addu'ata daya in zamanmu da ita babu alkhairi a ciki to
kuwa Allah ka gaggauta misanyamin da mace ta gari, wace zata
zaman komai tarbiyartan min da 'ya'yana.
"Fahad ohoho, to Allah dai ya zaba mana abinda ya fi
alkhairi wane sunan kuke son sawa yarinyar? "Hajiya ai bata dà
sunan da ya wuce naki sunanta Zuwaira amma zamu ringa ce da
ita Nuraiya". To Allah ya rayata, Allah kuma yasa mai
albarkace, Allah yasa cikon musulunci ce, kuma mahaddaciyar
Alkur'ani mai son shimfida komai bisa Kaunar addininta.
20
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
Fahad da kansa ke sinkuye tare da jin dadin addu'ar dи
mahaitiyarsa take yiwa 'yarsa yn dan dnga kai yana soNиWи
cike da murmushi yace "lajiya wai ina su Shafa'atu da
Humaira ne? "Ta dago kai ta kalelshi, abinka da manya nan da
nan ta gano inda yasa gaba. Itama ta murmusa cike da jin dadin
dan hakika al'adun yarinyar na birgeta ta yadda take da hankali
da biyaya gata da kunya da kawaicі.
"Fahad ke nan yau kuma neman Shafar ake me za ta yi
maka" "A'a dama ina so in ce da su da ita da Humairan su
koma can gidan saboda wasu 'yan aikace-aikacen kuma in suna
kusa ma wasu 'yan gulmace-gulmacen za su kaи".
"Fahad kenan, to in sunda wo an sanar dasu" Hajiya Allah
ki yiwa Shafa'atu magana karfa ta koyawa 'yar mutane yawo".
Uhm 'yar mutane bazata koyi yawo ba Fahad sai dai in dama
tana da yawanta. Ita shafar yawo take zuwa da zakace haka to
nice na aiketa nan gidan su Abdulkadir na akesu gurin
mamansa.
Fahad yaji gaban shi ya yanke ya fadi dan kuwa yasan
Abdulkadir kamai yinwar cikinsa dan kuwa Abdul kadir abokin
sa ne tare sukayi firamare zuwa karatunsu na sakandire ta
jami'ace dai ta kowa daban har yanzu su abokan junane amma
yawanci sai dai in an hadu a gaisa har a zauna ayi hira, ko ina
an hadu a majalisa amma habu mai zuwa neman wani.
Fahad yasan Abdulkadir kwallon shege ne, a duk lokacin
da ya kyalla ido yaga kyakkkkyawar mace, tofa babu sarki sai
Allah sai yasan yadda yayi ya yi mata magan kuma gashi da iya
magana da tsari, duk matar da ya tsara, duk abinta sai ta tsaru,
nan take yaji gabanshi na faduwa don haka sai yaga yabi
bayansu ko yaje ya zauna a majalisar su Abdul kadir din shi
yafi.
Fahad nayin sallama da hajiya sai ya nifu can yace kwa
sami Abdul kadir zaune da wani abokinsa da suke ce dashi
Ustaz saboda tsatstsauran ra'ayinshi Abdulkadir din na bawa
Ustaz din labarin garin Humaira.
Fahad na zauwa suka shiga gaisawa Abdul kadir yace kai
Fahad, kazo a dai-dai wallahi yanzu shafa ta gidan ku ta shiga
gidan mu ita da wata hadaddiyar cika wallahi yarinyar nan ta
ginu yadda baka zato kasan mu munsa sirrin mata sosai dan
21
Lubabah!
haka da zarar munga mace munsan sirrinta, mun kuma san a
sahun da take. Bawai kyan fuska kawai bane yakc rudar mu
Yanzu nake ba Ustaza labari yake cewa wai inbi a hankali. N,
kwa naga ai da zafi-zali ake dukan karfe. Ko ya kace mutumina
yayin da ya kawo hannu don su tafa.
Fahad ya gotar da hannunshi yace inani ina fawa da
mutumin da zai min fashin mata. Kace gara da Allah ya kawoni
to bari in gaya maka gaskiya sa ranace kawai tarage mana. Don
haka ka shiga taitayinka, ai gaskiyar Ustaz dai da yake cewa
kabi a hankali, dan a irin haka sai wata ran ka jawowa kanka, tsare mutuncinka ai wani abune bai dace ace duk matar da
kagani sai ka mata magana ba. dan haka zaka saidawa kanaka
mutunci wataran, tunda kasan akwai kannan abokanmu da
bamu san suba.
Fahad ya dubi idon Abdulkadir da tuni yayi zuru-zuru
kunya duk ta rufeshi. Abdul kadir yace dan Allah kayi hakuri
wallahi duk kunya ta rufeni".
Fatima wato kanwa gun Abdul kadir ita ta yowa su
Humaira da Shafa rakiya, suna tafe suna hira ne Humaira takece
da Shafa gaskiya garin nan yana burgeni wani lokacin ma
Karamin gari yafi amma da kanone cikin garinnan da zarar
yamma tayi kamar haka zakiga duk garin ya kauraye da samari
da yammata. Don dama su samarin sai su wuni babu wanka
wasuma sun tafi kodago a dai samu a taro kudi kan yamma
yamma nayi za'asha wanka mai gogaggun kaya ya saka mai aro
kuma ya aro a saka azo duk a cika tituna kungiya kungiya ana
kallan mata in kaga wacce tayi maka ka kira.
Fatima tayi dariya tace, to su kuma 'yammatan yawo
suke, dan a gansu a taya?" "To ai sana'a kenan”, in ji Humaira
"wato suma 'yammatan sai kiga yarinya taci uban aiki ta koshi,
mai wanki ta nadi wankinta, ta dau na sawa ta goge, in kuna da
dutsin guga (Iron) falillahi hamdu, in kuma babu kije ki aro ki
goge sai yamma tayi asha wanka a kece raini wata nata, wata na
aro. A fito ana taku daidai, da dai daya kaika rantse batasan
wani abu wahalaba ayi ta zaga gari daga gidan wannan kawa
sai gidan wannan kawa a haka, har ki sami mai tayawa, a tsaya
tsarashi tas ayi gaba in ma babu gurin zuwan haka za a yi la a
22
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
zaga gari in an gaji a taho gida in an samu shi ke nan in ba a
samu ba ba damuwa gobe ma rana ce.
Fatima da Shafa'atu suka kece da dariya suka ce kai
amma haka babu kyau ai kimar 'ya mace a nemet a gidansu,
bawai gamuwar titi ba shi yasa wasu matan suke sai dawa
kansu mutunci, kuma akasarin irin haka za kiga duk yaudara cc,
shi saurayi burinshi ya zama yana irga 'yan matan da ya nema,
ko kuma wance hadaddiyace, duk yadda za'ayi sai ya nemeta.
To a zahiri haka bashi da kyau kuma har gara namiji ya yi da
ace mace na yin haka". Kuma ai ko ina ma haka ake yi Humaira
tace, "ai na sani na fadi na garin mu ne dan kar ace nayi san kai.
Fatima tace gaskiya kam don wallahi Shafa'atu mace
rayuwarta da kuruciyarta takaitacciya ce wata tana ganin
birgewa ce, ace tana da samari da yawa wanda ita bata san
kuncewa kanta mutunci ta yi ba. Dan ba mutuncin mace bane,
ace kowa na zuwa ya kulaka, ına amfanin haka kuma Humaira
kada kice a Kano ne kadai ake haka wallahi ko ina haka ce take
faruwa ke dai Allah ya kyauta, wallahi in na sanar dake wasu
abubuwan da ke faruwa a wasu garuruwan za ki sha mamaki. In 'yan garinma suka ji har sa zagen suce na tona musu asiri.
Fahad kawai suka gani a gabansu da mota yace, "Ku daga
ina kuke"? Ya yi tamkar bai san in da suka jeba, Shafa'atu ce ta
sanar dashi cewa Hajiya ce ta aikesu cike da tsoron kada ya yi
musu fada. Ya daga kai ya kalli Humaira shigar da tayi ta birgeshi, hakika dole Abdul Kadir ya rude lokacin daya ganta, hankali ya lumshe idansa, lokaci guda yace, "bisimilla ko? sai
ku shige in kaiku gida.
a
Fatima ta gaidashi su kuma suka shiga motar ya jasu ya kaisu gida, suna tsayawa yace da su, "Su shirya kafin ya dawo
za shi wani guri ne zai zo ya kaisu gidanshi. Nan take gaban Shafa'atu ya