dariya gaba daya wajan karfe goma na safe
an kammala da komai manu direba ya jamu zuwa makaranta
cikin lokaci kankane an kammala da komai hatta faki, an bani
da kuma ajin da zan zauna.
Na lura da irin kallan da yaya Auwal ya ringa yi min a
wancen lokacin Juk da cewar a wannan lokacin ban fahimci
manufar kallan ba amma a yanzu a duk lokacinda na tunoshi,
nakan fassara kallan da manufofi da dama kan su tafi ne ya yi ta
yimin fadan karatu gami da hanani wannan shirmen da akasari
makarantu ke yi, wai kawar kunya ko Mommy ko doughter, a
tsaya ana ta faman shirme da jin kunyar juna warsu a dole
soyayya wallahi Humaira na tsani wannan shirmen.
Na sunkuyar dakai idona cike da kwalla nace, "to". yayi
murmushi yace, a'a kuka kuma za ki yi. Da kina ganin Mama
tana hawaye, ke kina murnarki baki kula ba, sai yanzu kuma da
kika ga an kawoki zaki yi kuka, ya sake yin dariya gamida fito
da kudi daga aljihun shi ya ce ga wannan Alhaji yace a baki ni
kuma ga nawa ki kara ko, Dan Allah ki kula da kanki ki san
mutuncin kanki kin ji ko, "To" nace yayin da na janyo dan
mayafina ina goge hawayen da haka muka yi sallama suka tafi.
50
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
Na tabbata har yanzu baka gama fahimtar koni wacece ba
ko ba haka ba yayin da ta dag akai ta kali Yaya Fahad. Taci
gaba da cewa ya kamata duk in turc labarina ins anar da kai dan
akaitaccen tarihina kamar yadda na jiyo a gurins auran
manyanmu. Dan ina ganin kafi gane in da labarin naw aya dosa,
dan na tabbata yanzu jina kawai kake kasan hausawa ma suna
fadin wai waye adan tafiya.
51
Lubabah!
Y
i Humaira Tijjani 'yace a gurin Alhaji Tijjani kuma 'ya N
a gurin hajiya Safiya wacce muke kira da (Mama)
Na ji cewa mahaifina marayane tun da cikinsa
mahaifinsa ya rasu. Kuma ya aksance a garin Kano a cikin gari
a Unguwar Mandawari. Sannan kuma mahaifina, an haifeshi
bakwaini, Allah kuma ya rayashi, cikin koshin lafiya, da
ciakkiyar kulawa. Tun yana dan shekara uku zuwa hudu a
duniya, wan mahaifinsa ya dauke shi mai suna Malam Audu. A
hannunshi ya girma har ya isa shiga makarantar boko aka sashi
a makarantar.
Nan da nan Malamai suka san mahaifina ta hanyar
tsabtarshi da kokarinshi dadin dadawa ga ladabi da biyayya. Ga
girmama na gaba dashi yana kammala Firamare aka sashi a
makarantar Sakandire dake unguwar Gwale. Bayan ya gama bai
ci gaba ba sai wani Aminin mahaifinsa ya dauke shi aiki a
masana'antarsa sunanshi Alhaji Kabir.
Nan da nan ya zama kamar dan gida, a nan ne Allah ya
hada jininshi da mahaifiyata wato hajiya Safiya lokacin da ta
gama karatunta na sakandire sai mahaifina ya fito da maitarshi
fili ya nuna so karara ga mahaifiyata. Amma kuma wani rashin
sa'a da aka yi shine mahaifiyata bata son mahaifin nawa. Yayin
da shi kuma nan duniya bashi da masoyiyar da ta wuce ta.
Nan da nan mahaifinta ya yi kiranta ya shiga lallashinta,
ya nuna mata cewa shifa bashi da surukin da ya wuce shi.
Amma ita sam ta dekyasa kasa ta nuna ba ta yi dashi
mahaifinta Alhaji Kabir shi ya biya musu maka da ita da
mahaifiyarsa da kuma Babarta, wai ya kaita maka ne a wannan
lokacin ba dan komai ba sai don ya lalalsheta ta amince da
mahaifina amma suna dawowa ta nuna ita sam bata yi dashi.
Nan da nan ran mahaifınta ya baci, ya sa aka daura auren
tsakanin mahaifina da mahaifiyata a takaicę dai an yiwa
mahaifiyata auren dole. Wani ikon Allah ko wata biyu bata cika
ba aka sami cikina, akan dole tayi rainan cikin dan babu yadda
za ta yi. Ban tashi fitowa ba sai da na cika wata tara da kwana
52
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
Na tabbata har yanzu baka gama fahimtar koni wacece ba
ko ba haka ba yayin da ta dag akai ta kali Yaya Fahad. Taci
gaba da cewa ya kamata duk in ture labarina ins anar da kai dan
takaitaceen tarihina kamar yadda na jiyo a gurins auran
manyanmu. Dan ina ganin kafi gane in da labarin naw aya dosa,
dan na tabbata yanzu jina kawai kake kasan hausawa ma suna
fadin wai waye adan tafiya.
51
Lubabah!
Y
i Humaira Tijjani 'yace a gurin Alhaji Tijjani kuma 'ya Na gurin hajiya Safiya wacce muke kira da (Mama)
Na ji cewa mahaifina marayane tun da cikinsa
mahaifinsa ya rasu. Kuma ya aksance a garin Kano a cikin gari
a Unguwar Mandawari. Sannan kuma mahaifina, an haifeshi
bakwaini, Allah kuma ya rayashi, cikin koshin lafiya, da
ciakkiyar kulawa. Tun yana dan shekara uku zuwa hudu а
duniya, wan mahaifinsa ya dauke shi mai suna Malam Audu. A
hannunshi ya girma har ya isa shiga makarantar boko aka sashi
a makarantar.
Nan da nan Malamai suka san mahaifina ta hanyar
tsabtarshi da kokarinshi dadin dadawa ga ladabi da biyayya. Ga
girmama na gaba dashi yana kammala Firamare aka sashi a
makarantar Sakandire dake unguwar Gwale. Bayan ya gama bai
ci gaba ba sai wani Aminin mahaifinsa ya dauke shi aiki a
masana'antarsa sunanshi Alhaji Kabir.
Nan da nan ya zama kamar dan gida, a nan ne Allah ya
hada jininshi da mahaifiyata wato hajiya Safiya lokacin da ta
gama karatunta na sakandire sai mahaifina ya fito da maitarshi
fili ya nuna so Karara ga mahaifiyata. Amma kuma wani rashin
sa'a da aka yi shine mahaifiyata bata son mahaifin nawa. Yayin
da shi kuma nan duniya bashi da masoyiyar da ta wuce ta.
Nan da nan mahaifinta ya yi kiranta ya shiga lallashinta,
ya nuna mata cewa shifa bashi da surukin da ya wuce shi.
Amma ita sam ta dekyasa kasa ta nuna ba ta yi dashi
mahaifinta Alhaji Kabir shi ya biya musu maka da ita da
mahaifiyarsa da kuma Babarta, wai ya kaita maka ne a wannan
lokacin ba dan komai ba sai don ya lalalsheta ta amince da
mahaifina amma suna dawowa ta nuna ita sam bata yi dashi.
Nan da nan ran mahaifinta ya baci, ya sa aka daura auren
tsakanin mahaifina da mahaifiyata a takaice dai an yiwa
mahaifiyata auren dole. Wani ikon Allah ko wata biyu bata cika
ba aka sami cikina, akan dole tayi rainan cikin dan babu yadda
za ta yi. Ban tashi fitowa ba sai da na cika wata tara da kwana
52
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
tara, ta haifo 'yarta tubarkalla, dan haka akasararin mutane ke
fada a duk lokacin da suka daukeni, sai suce tubarkallah.
Na kasance banci sunan da ake kirana da shi ba sai da na
cika kwana bakwai a duniya aka radamin suna Humaira.
Mahaifina, mahaifiyata ya bawa zabin sunan. Dan haka ita ta
zabamin sunan. Amma duk da an haihu zaman babu dadı yau
ana shiri gobe an bata, don ita har a wannan lokacin akwai
furbushin kiyayya a zuciyarta ina da shekara daya da wata
shida ne wata rigima ta barke, tsakanin mahaifina da
mahaifiyata, a inda ta kare masa tatas shi kuma zuciya ta
daukeshi ya yi mata saki daya, shi kansa lokacin daya ambata
sakin ya girgiza. Domin ca yayi da ita, "wai ke kina ganin dan
ina son ki shi kenan ba zan iya sakin kiba ko me? Ina nace na
sake ki ya zakiyi kije an sake kin.
Nan da nan ta daun murna da tsalle, yayin da shi kuma
hakan ya girgizashi yakwa dage akan shi ba sakinta ya yi ba,
amma sam taki amincewa ta zauna nanf a ta yi tafiyarta gida, da
maganar takai ga iyaye, shi kuma ya kafe akan ba sakinta ya yi
ba sai kawai aka dangan abin ga Malamai.
Naji an ce tambayar da aka fara yi masa itace, shin lokacin
da suke rigimar ride mata hannu ko zane ya yi ko kuwa yace
"a'a shi babu in da ya rike mata. Malam yace da kamar rike
wani gurin ya yi ko zananta ko hannunta shi kuma ya saketa,
abin nufi ya cika mata hannun ko zanan yace da ita jeki na
sakeki, kuma ya fadi hakanne ba da niyyar saki ba, har a
zuciyarsa. To da sai ace ba saki bane to amma hakan ya nuna
tsananin bakin ciki ne ya kai shida furta hakan, saboda haka sai
dai ya hakura dan kam saki ya saku.
Nan ma ca aka yi dani a nan ya kife yasa kuka. Aka nema
masa biko, babu yadda ba a yi ba da ita tace, ita aure ya kare
kasancewarta bazawara, akan dole aka rabu da ita. Ita kuma taci
gab ada rainona, kanta yayeni, ta auri wanda take so.
Nan dai taci gaba da shayar dani a gidan su masoya da
dama sun kawo mata farmaki,a mma taki Alhaji Safiyanu ya ji
labarin fitowarta nan da nan ya dawo wanda ada tsohon
saurayinta ne da take bala'in so, wato Alhajin da take aure a
yanzu. 53
Lubabah!
Naji ance mahaifiyata tana bala'in sona yadda ba'a zato,
kaji wani ikon Allah, har yau Mamana ba san Abana take sosai
ba, sai don babu yadda za ta yi tun da mun zama daya. Amına
kuma duk cikin 'ya'yanta babu kamata. Haka shima mahaifina
yana sona sosai kamar ya hadiyeni.
Na tashi cikin soyayyar iyaye da kakanni, na kuma yif arin
jini gurin jama'a kowa sona yake, kadan daga cikin 'yan uwa
har kirana suke da Rabo. A wannan lokacin Hajiya Iyace kawai
bata nuna soyayyarta gareni a fili, saboda kunyata da take ji,
kasancewar nice jikarta ta fari. Dan haka sai ya kasance tan ajin
kunyata.
Nan dai Alhaji Safiyanu ya dawo yabi layin zawarawan
mamana nan take tsohuwar soyayyar ta dawo taji nan duniya
babu wanda ta ke so kamarsa. A ka kuwa daura aure, a lokacin
shi dan kasuwane, kuma yana da mace daya da dansu daya,
wato Yaya Auwal. Da mahaifiyar yaya Auwal ta lura da irin
son da Alhaji Safiyanun ya ke wa mahaifiyata, sai taji sam ba
zata iya zama a matsayin bora ba. Dan haka sai ta fice daga
gidan. A lokacin Yaya Auwal yana da shekara shida a duniya.
Nan ma da danta ta tafi, dan a lokacin naji ance kin barwa
mahaifiyata ta yi, wai in ta barshi rabata za ta yi da danta, tun
tana nanma tana nuna mata ta fita san dan, dan tsananin kissa to
ina da bata nan. Amma kasancewar dole da sai gidan Ubanshi
musamman da namiji, ai fa sai sam ya ki zama sai da aka dawo
dashi gurin mahaifiyata. Dan haka mahaifiyata ce ta riki yaya
Auwal wanda ta haifa masa kanne biyar Amma daya ya rasu
wato Kabir shine na fari, sunan Mahaifinta kenan sai kuma
Habib da Khadija, mai sunan matarka. (Yayin da ta kalli Fahad
tayi murmushi) da kuma Mujahid, sai kuma Maryam wacce
muke kiran ta da Mary.
Nan kuma mahaifinmu ya auri Hajiya Rabi, bayan ya yi
shekar abiyu babu aure sai a hankali ya kwantar da hankalinshi
ya fitar da son mamana daga zuciyarshi, ya fanjama harkar
kasuwancinshi kuma yana taba 'yar siyasa cikin ikon Allah,
Allah ya wadatashi, shima ya zama mai dogaro da kansa, har ya
bude wata masa naantar sa ta kanshi. Amma kuma tun daga
kaina Allah bai kara bashi haiwa ba har yanzu.
54
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
Naci gaba da zama a hannun kakana Alhaji Kabir Da
Jakata Hajiya Uwale, cikin jin dadi da kulawa, da nuna tsantsar
fauna gareni in banda shagwaba babu abinda na ke yi a wannan
lokacin ina da shekara biyar a duniya mahaifina ya karbeni, ya
kaiwa Hajiya Rabi ni. Amma sai ta shiga yimin azaba iri-iri.
Sam babu wata kulawa da take bani ta ringa nuna kishi kurufuru da ni, dan ko alawa mahaifina ya sayo min sai t anuna
fushinta a fili, ta shiga mitar ita bai damu da ita ba ko kuwa
alawar ma ba za a bata ba. Tun ba na ganewa har na zo na fara
fahimtarta.
Na ki zama sam, akan dole mahaifina ya daukeni zuwa ga
lya, wato mahaifiyarsa kasancewar ban saba da ita sosai ba
saboda ita bata min waniw asa a lokacin wai ita tana jin kunyata
sai nan ma naki zama akan dole ya maida ni gurin kakannina na
gurin uwa lokacin dana isa shiga makarantar Firamare sai aka
sani dan ban yi wata Nusery ba, kasancewa rukon kakanni ne
ina 'yar shekara goma sha biyu a duniya na gama karatuna na
Firamary. A shekarar kuma na shiga Sacandire.
Na baro hannun kakannina, na dawo hannun mahaifiyata
ina 'yar aji biyu na firamare Sakamakon mitar da Alhaji
Safiyanu ya ke yi wa mahaifina, akan ya rabani da mahaifiyata
ba komai bane ya kawo hakanf ace yawan ambatona da
Mamana take yi. Gashi in ina gida bini-bini ta aiko in zo.
Namijin mutun ne Alhaji Safiyanu a gabanshi mahaifiyata
take nuna irin son da take min, sabanin irin son da takewa
'ya'yansa amma bai taba nuna 6acin ranshi ba kuma ya daukeni
tamkar 'yar cikinshi duk abinda ya yiwa 'ya'yansa haka ya ke
min da yake yana da rufin asirinshida i-dai gwargwado. Haka
kuma Abbana a duk lokacin da zai min wani abu gaba dayanmu
yake hadawa ya yi mana.
Na kasance ban san yaya Auwal sosai ba ko kuma inc e na
mantashi, dan tun ina yarinya rabona da shi, saboda can muna
mahaifinshi ya kaishi karatu, can gurin kaninsa, da ya ke acan
ya sami aikinshi yaya Auwal bai dawo garin nan ba sai yanzu
da ya gama karatun jami'arshi, wani abin sha'awa da yafi
birgeni yaya Fahad shine a yanzu haka Alhaji Safiyanu da
Babana Abokan junane Mama na ce dai na rasa dalilin da yasa
har yanzu batawa Abba na wani kallan mutunci.
55
Lubabah!
Na kasance ina mai sha'awar mahaifina da halayansa. Don
tun da Alhaji kabir kakana ya dan raunana a harkar
aksuwancinshi Abbana bai rage su da komai ba, ako da yaushe
abinda zai yiwa Hajiya lya shi zai musu kuma babu abinda ya
ragu na daga zumuncinsu kai baka ce an yi aure, an bata ba. А
nan ne kuma ake ta samun sabani tsakanin shi da Hajiya Rabi
dan ita a dole duk abinda zai wa iyayen mahaifiyata sai ya yiwa
nata, duk da cewa yana musun, amma ita abin bai gamsar da ita
ba sai taga ya yi musu kai daya wanda kuwa hakan ba zai taba
yiwuwa ba saboda Alhaji Kabir shine asalin tushen
makamashin bunkasarsa a yanzu Hajiya Rabi, tayi asirin tabi
Malamai tabi bokayan gami da yan tsibbun amma duk abanza.
Abin da Allah ya yi Annabi sai ceto.
Na zamanto babbar abokiyar gabar Hajiya Rabi. Dan kuwa
har inda nan ke motsi bama shiri da ita. A duk lokacin da na je
gidan ta shiga hada rai kenan, kamar wacce aka aikowa da
Mala'ikan daukar rai. Tun abin na damuna har na zo na watsar
da yinta gaba daya, tayi zugar har ta gaji. Amma mahaifina bait
aba dauka ba. Ta yi sharri har ba iyaka ta gaji ta bari a yanzu
haka sai dai kallon kallo hararar harara. Daga baya ne ma data
fara koyar kissar sai ta so ta nunamin tana sona, ta shig ajana a
jikinta amma ina wanda ya nuna maka kiyayya tun farko ko ya
dawo yana sanka aikin banzane da taga haka sai suka hada baki
da kananta Nasir akan ya nuna yana sona cikin ikon Allah sai
Allah ya jarrabeshi da son nawa, na gaskiya.W annan shine
tushen labarin da nake kan baka yanzu. Ta dago kai ta dubi
Yaya Fahad tayi murmushit ace ina fata ka fahim ta shima
murmushin ya yi.
ETs в CJS NUuf l ad rez0: IaWIA BVsy nne ndd
MUH дво abndsa ida ab snodet sdA d h
neas a sy நாய்த இ) i ulagatin to
sney tee ed san ning on i
t b wr sda nids win osel
h vaseise ijalla sad inney a oned be i
eesy sb mililsb dest en teh ta sa snsd onsay nsA
56ренe o
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
kowane hutu Yaya Auwal ne yake zuwa daukata, A
amma wannan hutun Manu Direba shi ya zo daukata, a
lokacin ina aji biyar na sakandire kasancewar Yaya
Auwal yana makarantar B.U.K. yana karatun Digiri dinshi na
biyu.
A ko da yaushe yaya Auwal yakan rubuto min wasika
akai, akai dan tambayar lafiyata, da kuma karatu. In kuwa ya zo
gida, lokacin muna makaranta, sai ya kawomin ziyara kafin ya
tafi wannan hutu ne wanda in na koma aji shida zan shiga. A
gaskiya wannan hutun na yi kyau, har na gaji gashi kuma na
fara cikar budurci.
A wannan hutun ya zo dai-dai da hutun su yaya Auwal,
dan haka a ranar da na dawo shi kuma washegari ya dawo ina
kwance a doguwar kujera ta falon Alhaji a lokacin mun hadu da
yara, suna zaune suna yin Video Game ni kuma ina daga
kwance rike da lemon fata a hannuna ina tsotsa. A lokacin na
gama hadewa cikin wasu kaya riga da siket farar riga bakin
siket. Abba ne ya kawo mana su iri daya ni da Khadija da
Maryam. Hakika kayan ba karamin kyau suka yi min ba.
"A'a don Allah Yaya Humaira ba na kada shi ba?” Na ji
Khadija ta katsemin tunanina a lokacin na shiga tunanin ya
kamata da yamma ko gobe in je in gaida Abbana". A'a Habibu
nifa bana san wayo" "Ke fa baki gani ba Yaya, gini fa na hada
kuma tunkan ya fadi na yis auri an daga shi, shine za ta ce wai
an fadi, ni shiyasa bana san yin wasa da Khadija, wallahi ta fiye
runton tsiya". "To in dai fada za ku yi ku hakura haka"
Auwal ya shigo yana murmushi yace ku yaran nan babu
wanda ya iya yiwa mutum sannu da zuwa tun dazu na dawo
amma babu ko sannu da zuwa. Gaba daya muka mide muna
dariya gami da yi masa sannu da zuwa. Na koma na zauna
adoguwar kujerar, Yaya ya zo kusa dani ya zauna wani irin
kallo da ya wurgomin, ban san lokacin da na jefar da lemon
hannuna ba saboda kidima. Domin hakika kallan kallo ne mai
kunshe da fassarori, daban-daban. Hakika nasha jin labarin
irinw anan kallon a bakunan marubuta dan shi suke zaiyanawa 57
Lubabah!
a duk lokacin da masoya suka hadu kaji ance an kashe ido ana
kallan mutumg ami da murmushi.
Amma ni idona bai yi sauring askata hakan ba, saboda ina
ganin bata mana 'yar haka a tsakanina da Auwal domin ni a
ganina mun zama kamar uwa daya uba daya. Ya lankwasa
murya yace, "Humaira 'yan makaranta, tun yaushe aka dawo?
Nayi murmushi nace, "tun jiya" yace "yanzu jiya jiyannan kika
dawo amma tamkar kin yi, kwanaki kin yi fes dake haka"
murmushi kawai nayi yara suka shiga tambayarsa mai ya kawo
musu, yace "Ni babu abinda naaa kawo muku sai kace wanda na
bar garin koda n kung ana kwana biyu ban zo hutun karshen
sati ba. Ai jarabawa ce ta tsaremu bawai garin na bari ba". Ya
kalleni yace gaskiya Humaira kin kara kyau". Habibu ya kaiwa
Khadija duka a baya tace.
"Aaa... wallahi saina rama Yaya Auwal yace kai Habibu
mai yasa ka daketa, yace "yaya tankwabata tayi na fadi".
"Shine kuma ka dake ta, to shi kenan ku ajje ku fita wasanku.
Nan dai suka fice suna gugunai ya dubeni yana murmushi yace
in je muyi aga wanda ya iya. Nace "Yaya ni wallahi ba zan iya
yi da kai ba". Ya yi murmushi yac, "saboda me, Humairan
Yaya?".
A hankali na dago kai ma kalleshi, dan maganar ta
burgeni. To amma abin yana dauren kai yau sai wani iri ya ke
min kamar yana gaban budurwarshi. Ya ce dan Allah ki sauko
mu yi yau sha'awar yin game din na ke yi mama tana can da
baki shi yasa na taho nan.
A kan dole na zo muka fara muna yi muna hira, ya turkeni
akan lallai sai na gaya masa saurayina, wai shi ya gaji da ganina
da zarar na gama karatu aurar dani zai yi. Na tuntsire da dariya
na ce, "Aure Yaya? Aini Aba da Alhaji duk sun ce sai nacig aba
da karatuna, kafin in yi aure dan haka babu wani saurayi da
nake kulawa", yace, "Allah ko? To Babban yaya kuma ya ce
aurar da kanwarsa zai yi. In ma babu saurayin shi ba sai ya aure
ba?" Gaba daya kunya ta kamani.
Amma gaskiya Yaya Auwal ya iya dubara da nasan haka
ya ke so yace, ai da na ce ma da samari da yawa. Na kwashe da
wata mayaudariyar dariya nace, "Yaya ai kana ta dannawa har
ka fadi baka sani ba". Na yi hakan dan a bar maganar.
58
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
Ana haka yara suka shigo da gudu suna murna, suka hada
baki gaba daya suka ce "Yaya Humaira ankul (uncle) sani ya zo
yace, mu shirya zai kaimu gidan Anti (Aunty) Shaima'u a can
zamu yi hutunmu, wai shima zai yi tafiya". Na mike zumbur
nace "La nima dani za'a tafi" Yaya Auwal ya riken hannu,
yayin da ya shishshigar da kwayar idonshi can ciki, yana
murmushi yace "wannan ai kece Yaya godin, kuma sai ki kama
bin su zugum zugum. Haka za a tafi abar Hajiyar, ita kadai
babu in da zakí muje dai mu gaidashi mu dawo.
A nan sai naji duk jikina ya yis an yi muka fita gaba daya
muka gaidashi (Ankul Sanin Kanan Alhaji ne) Nan aka zauna
ana ta hira ana dariya kasancewarsa, mai barkwanci, to a duk
lokacin da yazo in suka hadu da Mamanmu cikin mutum sai ya
yi ciwo sun shiga tuno abubuwan kuruciyar su kenan,
kasancewar tare suka yi makarantar Firamare, tare suke
wasanninsu.
A nan muma muka shantake muna ji muna dariya. A duk
lokacin da na dago idona muka hada ido da Yaya Aulwa, sai ya
fan harareni, alamun mu tashi mu koma falon, amma sai na
shareshi kawai na lura da shi duk abinda na ke yi idonshi na
kaina. Zuwa can yara kowa ya fita da kayanshi, kowa yana ta
murna,s hi kuma ya tashi yace da Mama. To 'yar shagwaba mu
zamu tafi in alhajin ya shigo kyace na zo na ſauke "ya"yana
mun tafi".
"A to zan gaya masa, inc e har wani suna kasa min wai
'yar shagwaba in ya zo ka gaya masa manufarka". Yace, "ato in
kin ga in fada miki manufar tawa ai sai in fada miki. A'a a'a,
kai dai kaje ka gaida matar taka da haka suka yi salama suka
tafı yara na ta murna.
A nan ne Mama ta kalli Yaya Auwal ta ce kai kuma ka zo
cikin yara ka zauna, yau tun da ka dawo ka je ka zauna a gurin
wannan malalaciyar Sarkin kwanciya. Tun da kika dawo kina
falo, ni na yi zaton ma bacci kike yi dazun nan wata kawarki ta
zo nace ba kya nan. Tace ace da ke sunanta Sadiya Haruna.
Amma na ji tana cewa su Maryam yanzu haka kin mantata ko?
Nace "haba Hajiya yaza a yi in mantata. Rabanmu da ita da tun
muna aji daya na sakandire Allah yasa ta dawo.
59
Lubabah!
A to ni je ki ki doramin girki dan Allah Yaya Auwal yace
"Mama tun kan ta gama hutawa har ta fara shiga dakin girki".
Ta yi dariya tace to mcyc amfaninta Auwal. Ni dai nan nayi
gaba na barsu.
A washegari tun da Asuba na tashi nayi sallata. Na koma
bacci, bant ashi ba sai wajan karfe goma na safe, ina tashi na
fada wanka, da na fito ne na daura Alwala na zo na yi sallar
walaha na zauna ina jan carbi Maryam ta shigo da gudu, nace
a'a Malama Maryam ya naga kin dawo tace yaya Humaira kuka
nasa nace sai an dawo dani gida. Na yi dariya nace oh Mary
baby ashe ma kin san kin yi kukan, da wayonki kike yin fitina
ko.
Amma na gayawa Mama in ce kina sane kike yin komai da
komai Mama ta leko tace ke Humaira wannan wane irin
baccine haka, sau biyu ina turo Maryam ta tashe ki, tana cewa
kin ki tashi. Nan Yayankima sau uku yana zuwa nemanki,w ai
meye yake so ki bashi ne? "Wallahi nima ban sani ba Mama".
A hankali na gama shirina tsab, na saka wasu kaya riga da
wando bakin wando da riga mai ruwan goro. Hakika zaka ji ina
yawan sa kananan kaya, gaskiya ni mace ce mai san kananan
kaya kuma har yau haka nake. Na fitina ta ku dai-dai kai ka
rantse wani gurin zani Mama ta kalleni ta yi murmushi tace,
amma kayan sun yi miki kyau sam wanan karan baki rame
sosai ba ko?” Ni dai na yi murmushi, kawai.
A dakin Yaya Auwal naji wayar sadarwa, irin tafi da gidan
ka dinan wato salula tana ta faman kida, Mama tace tun dazu
nake jin wayar nan na kadawa, je ki ga ko ya fita ne, ko ya
shiga wanka. Dan Allah ki gaya musu kada su dami mutane.
Nace to Hajiya.
Amma da na shiga dakin dib na ji babu alamu motsi, zuwa
can na farajin motsi daga bandaki, wayar ta kara kirana dauka
na ga sunan wata wai ita Aisha Isma'il, na yi kamar in kashe
kawai in ajje, sai wata zuciyar tace dani ai kamat ayayi kit
ambeyeta, ko menene. Na kara wayar ke nan a kunnena da
nufin in jida lili sai kawai naji magana daga bayana.
"A'a...a'a, kika san ko waye?" Yaya Auwal ne ya fitodaga
wanka daure da tawul kunya duk tabi ta kamani, kirjinshi ne fal
yake da gashi. Nan take na dabar bare nace dama-damma
60
Duk Wanda Ya ce Namiji Uba Ne......
Mama ce tace in zo in fauka yayi murmushi yace, "lumaira
kenan meyc na rudewa haka mikomin in ga kowaye, ke
bugowa yana duba sunan yayi tsaki ya katshc hanyar ya dago
kai yace dani to sami guri ki zauna ina son yi miki magana, bari
in shiga cikin dakin in shirya ko.
"Amma yaya ai kaji kiran sallar da ake yi dan haka ni dai
zanje in yi salla, in na idar an dawo ya kalleni ya yi murmushi
yace, ai ba wani dadewa zakiyi ba dan haka ki jirani kin gane
ko? wata magana ce