Reading DUNIYA TA COMPLETE BOOK 2 COMPLETE by Asma Baffa Chapter 27 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gari haka da sauran lafiyarku?,ba a nan zamu gane gaskiyar taka ba. muje don ubanka"" Cp ya fada shi kansa abun yana masa takaici."

"Sam baisan da zuwan annin gidan da safen ba,don haka kanshi tsaye ya shiga falon hankalinsa"

yana ga samanshi. So yake ya isa ya kulle kansa don baya buqatar ganin kowa kaman yadda bai buqatar

hayaniya ko dogon magana sam sam. Saidai yana sanya qafarsa a falon yaji muryar annin sanda take fadin.

"""Allah ya qara lafiya. yasa kaffara,saiki dinga kula da jikinki da kyau,Allah ya inganta"". Murna ta kama"

"amna,duk yadda taso cinye maganar amma sai data fito"

""" Anni......wai wai hamma shima ya kusa zama daddy?""."

"""Ungo nan"" Anni ta fada tana watsa mata yatsunta biyar,saita saka hannu ta qunshe bakinta tana dariya."

Shikam daga shi har sabreen dake zaune daga gefe maganar tazo musu a wani irin ba zata.

"""Allah ya inganta? zama daddy?,wata qaryar ta gilla musu kenan?"" Ya fada qasan ranshi yana yamutsa"

"fuska gami da watsa mata wani irin kallo duk kuwa da cewa yana nesa kadan dasu,sannan dukkansu ba wanda yasan ma ya shigo parlor din. Kai ya jinjina wani abu yana tsaye masa a wuya"

"""To yaushe tayi cikin?"" Yaji tambayar ta taso daga ransa,take yaji kansa ya qara masa wani nauyi saboda"

wani tunani da yazo ransa.

"Dukka juriyarsa da yakejin kamar tana sulalewa ya tattaro yana sake maimaita sallamarsa,suka"

daga kai dukansu suna amsawa banda sabreen da tayi qasa da nata idanun tana jin sam sam bata sha'awar dubanshi.

"Gefan anni ya zauna kaman yadda ya saba a gida,duk sanda zai iso gabanta gefan ta nan ne wurin"

"zamanshi. Tuni amna ta kama kanta tana gaidashi cikin tsoro,don tasan zai wahala baiji abinda ta fada ba."

"""Ina kwana?"" Sabreen ta samu kanta da fadi duk da bata dubeshi ba,haka kawai takejin wani irin nauyin"

anni.

"""Lafiya qalau ya jikin?"" Ya furta a dake yana dan duban fuskarta kadan wajen daya lura a jiya ya"

"fashe,baiga komai ba don ta rufe wajen da dan kwali,sai ya dauke dubansa daga kanta zuciyarsa tana masa zafi."

"Ba abinda ya hanga saman fuskartata sai guntuwar wiwin daya gani jiya a bakinta,zuciyarsa ta sake"

"matsewa,baya jin zai samu wani nutsuwa a zuciyarsa muddin bai samu cikakken bayani abinda yake faruwa ba ko kuma ya farun."

Hankalinsa ya maida kan annin ya soma gaidata cikin nutsuwa da girmamawa. Yaji dadin yadda

"farouq bai daga mata hankali ba ya gaya mata abinda ya faru a gidan ba jiya da daddare,yadai gaya mata kawai sabreen dinne bata da lafiya"

"""Allah ya qara lafiya.....sai ka kula da ita sosai inajin idan zai yiwu ma nabar amna a gidan,don a"

"yanayin mace irin haka zaman kadaici qara miki ciwo kawai yakeyi"". Dan satan kallon anni yayi,ya fuskanci tunda ta zauna a wajen kawai kallon me ciki take yiwa sabreen din,inda anni tasan cakwakiyar da yake ciki zama zatayi tayita masa kuka."

"Kwata kwata a birkice yake kan lamarin,kusan komai nema yake ya dagule masa,yana jin kamar"

kwanyarsa ta daina aiki yadda ya kamata. Ya lumshe idanunsa yana jin ciwon yadda mahaifiyarsa ta

xama silar qulluwar alaqa tsakaninsa da yarinyar da kullum munanan boyayyun halayenta sake bayyana sukeyi.

"""Ashsha da kinyi zamanki ai,ina ke ina hidima damu ke da ba cikakkiyar lafiya gareki ba?"" Anni ta fadi"

"sanda Sabreen din ta fito daga kitchen ta ajiye mata tray dake dauke da spicy black tea soyayyen qwai da kuma farfesun kan rago wanda ta yi tun shekaran jiya waccan amma ta kasa ci,kasancewar ita din cin abinci ba damunta yayi ba. Zataci din amma gutsul gutsul kamar na dan qaramin yaro,shi yasa ko yaya ita ko ma'u suka girka abu sai yayi musu yawa."

Sallamar da akayi daga bakin qofa ya maida hankalinsu can.

"""Sannunku dai gafaranku"" Zuwairan ke fadi tana rarraba idanu. Zuciyarta cike fal da fargaban kada"

shigowarta ya zama silar barinta aiki amma kuma tana jin relief na wani fannin idan ta tuna tana da

assurance na bazaice komai ba muddin annin tazo gaidawa.

"Zubewa ta gaidashi,amsawa daya yayi mata,ganin hakan sai ta tattara hankalinta ta maida kan"

annin tana zuba gaisuwa.

"""Ya mukaji da wannan abu?"" Zuwairan ta fada duk da a tsorace take."

"""Ke!"" Fuad ya fadi da kakkaurar muryarsan nan dake saurin isar da saqo gun wanda aka kira saboda"

zurfin muryar da wani irin kaifi

"*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*"

08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ

_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 2

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 62

62

"""Eh. na'am"" Ta fadi adan zabure"

"""Kin taba samun matsalan qwaqwalwa?"" Ya tambayeta kai tsaye da wani kallo da yaso rikita duk"

lissafinta. Kai ta fara girgizawa

"""Ranka ya dade. aah"""

"""Good"" Ya jinjina kai"

"""Bacen a gun"" Ya fada a taqaice wanda yana kaiwa qarshe tana miqewa da hanzari gami da cewa"

"""Tuba nake. tuba nake"". Daga shi anni har amna binta sukayi da kallo,a mamakance anni ta maido"

dubanta kansa bayan ta fice

"""Allah me mutane. ina ka samo wannan Muhammadu?"""

"""Maamah ce. "" Ya fadi a taqaice yana jin wani abu game da matar tare da bin hanyar da ta wuce da"

"kallo kaman tana wajen har a lokacin. Tun bai qarasa ba ta fahimci inda zancan ya dosa,kai kawai ta gyada tana fadin"

"""Allah ya rufa asiri......mu zamu wuce. diyata"" Anni ta fadi tana murmushi. Qasa sabreen ta sakeyi da"

"kanta tana dan qaramin murmushi. Karon farko idanunsa suka soma kaiwa kanta,karon farko kuma yaga wani abu me.kama da murmushi akan fuskarta. hakanan lokaci na farko da yaga wani alamu na wata"

"aba wai ita KUNYA a tare da ita. Tsaki yaja qasan ranshi,bayajin wannan abun da takeyi har qasan ranta"

"take yinsa,yadda ta wani sunkuyar da kanta,abinda bai taba gani ba a tare da ita sai yau."

"""Allah ya qara sauqi kinji ki kula da jikinki da kyau"" Anni ta fadi tana jin yaqinin kamar abinda dai take"

"hasashen ne yake tare da sabreen. Har cikin zuciyarta takejin yarinyar,tana kuma jin kamar ta taba ganinta a wani wajen kafin yanxu,amma kuma ta gaza tunawa."

"""Ameen anni na gode"" Siririyar muryarta da yau kadai tayi wani irin laushi ta fito tana furta hakan har"

yanzu kanta a qasa.

Dukkaninsu suka takawa anni xuwa inda lafiyayyar BMW dinta take jiranta da masu tsaro

lafiyarta mutum biyu

"""Zamu tafi tare da amna din amma anjima da dare in sha Allah zata dawo,sai kinfi jin dadin"

xaman......nasan halin Muhammadu indai kin ganshi gida zaune to saidai annual leave dinshi yazo ko

"kuma baida lafiya da gasken gaske"". Haka kawai ta samu kanta da kallonshi ta gefen idonta. Duk da ba dogon zama sukayi ba,gajeran zama ne maras dadi da ma'ana,zaman da baida wani alqibla ko kadan,amma ta karanci dabi'u masu yawa tattare dashi. Aiki kaman baisan ciwon kansa ba,kamar kuma yafi kowa sanin muhimmancin lokaci,bata taba ganinsa ba system ko takardu ba. sannan zaman"

kadaici baya damunsa sam sam.

Suna a tsaye motar ta soma motsawa tana fita ta tafkeken gate din gidan. Idanunta akan bayan

"motar,tana jin kaman ta hanasu tafiya ita da amna din,dan wanzuwarsu na qananun mintuna kadai sai taji kaman an rage mata wani nauyi da takeji a zuciyarta. Lallai maraici babbar masifa ce,ciwo ne wanda bashi da magani har xuwa randa naka ajalin xai ruskeka,wanda ya rasa uwa shi daya yasan irin asarar"

daya tafka da ba zata fadu ba.

"Sai da motar ta gama ficewa tas sannan ta tuna a inda take a tsaye,da kuma wajen waye take?."

Ba tare data juya ta kalli inda yake a tsayen ba ta juya a hankali tana komawa ciki.

Da kallo ya bita ranshi yana sake masa susa idanunsa suka sauka kan hips dinta da suka

"bayyana sosai saboda mayafin dake saman kanta bame girma bane,take zuciyarsa ta wullo masa hoton hijabinta na jiya da yasha cukuikuiya,wani zazzafan abu me tauri ya taso masa da ya sanya ya gaza riqe"

"kansa,sai kawai yabi bayanta yana jin ya zama dole lallai lallai yasan kome."

Tana dab da isa qofar da zata sadata da parlor dinsu na farko ya cimmata. Bata zaceshi ba ta

"tsinceshi a gabanta. Kallon kallo suka yiwa junansu,wani irin kallo na tsakiyar idanu,tsakanin shi da ita kowa zuciyarsa na dauke da wani irin nauyi da baisan yadda zai rageshi ba."

Ta dauka zata iya jurewa ci gaba da kallon tsakiyar idanun nasa amma sai taji ta sare nan da

"nan,ta janyesu bugun zuciyarta na daduwa wanda batasan meye sila ba. Qasa tayi da kanta,so samu ta rabeshi ta wuce saboda fushi take gani cikin idanunsa,ita kuma yanzu qirjinta bazai iya daukan fada masifa ko tashin hankali ba hakanan. Kai kawo kawai adams apple dinsa keyi alamun akwai abinda yaketa qoqarin hadiyewa,jiyan ce kawai ke dawo masa,yana tuna sanda ya dagata towel din jikinta daya xame warwas a qasa,daga ita sai hijabi. Sai daya tabbatar yayi babban aikin rage fushinsa da abinda yakeji sannan ya soma magana,cikin bacin rai amma kuma yanata kokawar kalmasa harshensa,don bayani yake buqatar ji,duk da cewa ta kowacce fuska.....duk kuma inda ya juya. kowacce hujja idan ya"

"daga,ya tattaro ta nan data can ba abinda take sake nuna masa sai ainihin WACECE ITA."

"""Wancan lokacin na taba ganinsa cikin hotel a abuja yana cigiyar karuwarshi da suka kama daki,ta"

"kwashe masa kudade masu yawa kwatankwacin yadda ya faru da kamfanin JADDA DIAMOND CHORES RESOURCES,sanda naga fuskan wayar ba kowa bace a ciki sai KE!. Wanene shi?,ya akayi ya shigomin"

"cikin gidana?,cikin dakin da aka gina da tsaftatacciyar dukiya ta halak?""."

"Wani irin duka tambayar tasa tayi mata,wadda tazo mata hade da labarin da batasan ya faru"

ba......eh ta taba binsa abuja. kuma aikin mashkur kusan shine aiki na qarshe da tayi har yau kuma bata

sake sha'awar maimaita wani abu makamancinsa ba. amma yaushe ya fiddo hotonta ya nunata a

matsayin karuwa yana cigiyarta?. KARUWA kalma mafi muni da tafi tsana taji ta gilma a kunnuwanta. duk yadda takai tsakaninka da ita muddin xaka kira wannan sunan a gaban

fuskarta. to takan iya manta ya kuke da ita?.

"""Am asking you "" Ya fada yana jin ya soma hasala ganin shurun da tayi kamar ba da ita yake magana"

ba.

"""Ban sani ba. "" Ta bashi amsa muryarta tana so ta fara rawa. Me zata gaya masa wanda zai sanya ya"

fahimceta?.

"""Baki sani ba kaman yaya?,ya shigo har dakin ba tare an fasa kowanne gini na gidan nan ba. ya shigo"

dakinki ba tare da kinyi yunqurin kiran koda security daya na gidan nan ba. ya shigo dakinki daidai

"lokacin kwanciyar baccinki?,a sanda kike daure da towel kadai da hijabi?"" Ya qarasa maganar yana"

"qarasawa dab da ita,yana kuma kaiwa qarshe a tsawace har sai data lumshe idanunta ta kuma gaza budesu."

"Tsawa......tsawa,bata son tsawa,bata qaunarta,tsawar ma daga wajen d'a namiji wanda tuni ta"

"karanci sun jima da raina ajawalin mata. Wani abu data jima da shawa kanta alwashi,raini.....wulaqanci izgili da toxarci na da namiji,ita ko 'yan uwanta ba wanda zata lamunta ya"

daukesu.

"""Ban sani ba nima"" Ta sake maimaita masa don da gasken batasan yadda akayi mashkur ya shigo ba."

"""Harda wayar daya baki kenan itama ita ta kawo kanta?!. nace ita ta kawo kanta?!!!"" Ya fadi da qarfi"

kaman yana shirin fasa mata kunnuwa.

"""Stop it!. wanne kakeso na amsa maka?,wacce tuhuma kakeso na baka amsarta?!"" Itama ta maida"

"masa muryarta na rawa,oily eyes dinta suna qara walainiya cikin hasken ranar daya fara dagawa."

"""Ni kikewa shouting?"" Ya tambayeta da tsananin mamaki,saidai kuma qarar wayarsa ta janye magana ta"

gaba da yaso fadi. Bai fiya daga waya a cikin irin wannan yanayin da yake cikin tsananin fushi ba. amma yana expecting kira me muhimmanci daga gurin wani dan kasuwa mazaunin qasar ivory

"Coast,dole ya ciro wayar."

"Shi da ita dukansu akan sunan FAREEDA KHALEED MUSTAPHA ya sauka,ita ta fara janye idanunta"

tana jin wata wani fushinta yana ninkuwa.

Ya sanyata a gaba da tarin tambayoyinsa amma shi a daidai lokacin karuwarshi ko

yarinyarsa. batasan da wanne suna zata kirata ba ita ke kiransa?.

Ta nashi bangaren banda muhimmancin da wayar ke dashi a wajensa tabbas ba abinda zai hanashi

tarwatsata ita kanta wayar a wajen bama fareeda kawai ba.

"""Sorry sir"" Yaji an fada da sauri,abinda yakai hankalinsu kenan wajen. Me sunan malam ne,da sassarfa"

"yake barin wajen saboda kunyar yadda ya samesu a tsaye dab da juna,baisan kuma zai samesu a hakan ba da bai biyo ta wajen ba."

"""Zo nan"" Ya kirashi a nutse yana duban hannunsa dake dauke da newspaper daya saba ajiye masa duk"

safiya daga kamfanin jaridu daban daban.

"Sunkuyawa tayi ta zame ta gefansa tana takawa don barin wajen,haka kawai taji bama zata iya"

"zama ta fuskanceshi ba sam. Kwata kwata bata yarda dashi ba Shima. wacece faridan?,meye alaqarsu"

da koda yaushe layinsa cikin karbar kiranta yake?. Yana jin wucewarta amma bai waiwaya ba don hankalinsa yana kan me sunan malam.

"""Good morning sir"" Ya sake gaidashi cikin girmamawa yana rusunawa ba tare daya miqa masa"

"newspaper din ba kaman yadda ya saba,duk da yawancin lokuta ma yana samunsu ne a daura da dining suna jiran fitowarsa,idan ga kammala dubawa kuma zai kwashesu sai kuma fitowar gobe."

"""Morning how you doing?"""

"""Fine sir"" Still ya kuma amsa masa amma ba alamun zai miqa masa su. Abun yadan bawa fuad"

"mamaki,yana shirin miqa masa hannunsa don ya bashi kira ya kuma shigo masa."

Kai tsaye aka gaya masa farouq ne don haka ya daga ba wani bata lokaci

"""Good morning dude"" Farouq ya furta kaman yadda ya saba masa,saidai kuma daga can qasan muryarsa"

kaman yana iya tsinto wani abun

"""Morning mun tashi lafiya?"""

"""Fine. ya jikin naka?,ka fita ne ko ka sauko daga stairs?"" Duka farouq din ya cure tambayoyin ya"

"masa,abinda yaja hankalin fu'ad kenan."

"""Ban fita ba. na sauko qasa na rako anni yanxun xan koma ciki""."

"""Good but do me a favor mana"" Ya fada yana fatan idanunsa basuga abinda ya gani ba."

"""Ehnnnnn"" Fu'ad ya fada yana jin zaquwa na jin abinda zai fito a bakinsa."

"""Kayi skipping duba newspapers na yau mana. instead of that ka bani aron time din muyi magana"""

"Yadda farouq yayi maganan kawai ya sanyashi yasha jinin jikinsa,sai kawai ya miqawa me sunan malam hannunsa yana masa nuni da newspapers din da yake rqe dasu yana kafeshi da idanun nan nasa da kwarjini ke cike dasu kullum ba tare da ya sauke wayar a kunnensa ba."

"""Kowanne lokaci na yini na zan iya baka farouq,not the only news time"" Ya bashi amsa sanda me sunan"

"malam ya miqo masa newspapers din da hannu biyu cikin mutuwar jiki,ya kuma janye daga wajen da sassarfa don bazai iya tsaiwa yana dubansa a sanda yake kallon labarin dake buge a jaridar ba."

"*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*"

08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ

_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 2

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 63

63

"""Wannan abun kawai nake buqata please"" Farouq ya maimaita sanda ya shiga motarsa dake"

farfajiyar gidan. So yake yaja maganan da tsaho sannan ya cimmasa kafin ya duba abinda ke faruwan

saidai sanda yake bashi amsa na qarshe yana bashi amsar ne sanda idanunsa suka sauka akan tittle na labarin da yaci shafin farko gaba dayansa na jaridun guda biyu.

*_TSINTAR DAMI A KALA_*

_BABBAR JARABAWA. SHIN KUSAN WACECE ASALIN MATAR MATASHIN MILLIONAIRE DINNAN

MAMALLAKIN KAMFANINNIKAN DAKE SARRAFA GWALA GWALAI?_

"""Farouq.....you have my time,amma kafin sannan "" Maganar ta yanke masa sanda makeken hotonta"

ya biyo bayan title din ita da mashkur.

Hoto ne da aka daukeshi gaban wani hotel da sunan kawai ya iya kalla ba tare daya tantance

wanne bane. sanda ya bude mata murfin motar ita kuma tana qoqarin fitowa a motar yana riqe da

handbag dinta.

"""Hasbunallahu wa ni'imal wakil"" Ya fada yana jin dukka gabbansa suna daukan dumi kafin daga baya"

kuma suyi wani irin sanyi kaman ba'a jikinsa suke ba.

_mrs muhammad fu'ad jadda sabreen ahmad_.

"Baya jin idanunsa zasu iya ci gaba da kallon abinda ke gabansa,sai kawai ya hade newspapers din"

"waje daya ya curesu a hannunsa yana takawa zuwa cikin gidan ba tare daya tsaya tuna cewa magana suke da farouq ba,kuma yabar farouq din akan line na waya."

"Shuuuu din da farouq yakeji ya sanyashi qarfafa zarginsa akwai abinda ya faru,sai kawai ya aje"

"wayar ba tare daya kasheta ba,ya tada motar da wani irin hanzari wanda yanayin gaggawar da security na gidan suka ga yanayi ya sakasu dage masa qofa ya fice tun bai qaraso ba."

Bazaice ga wani abu da ya faru daga sanda yakai kansa samansa ba banda azababben ciwon kai

da yake masa kutufo kota ina. Ba abinda bakinsa ke furtawa sai Astgafirullah yana me kyautata zaton akwai wani abu daya aikatawa ubangiji wanda ba daidai ba shi yasa ya jarabceshi da wadannan abubuwan. Dukka komai akan yarinya daya? yarinyar da koda ta zame masa zabi a nasa qashin kan

hakan ba lallai ya tabbataba banda miqewa da kafewar maamah akan lamarin?.

Da qyar ya iya amsa sallamar farouq sanda ya bude smart door din ya qaraso cikin parlor din

idanunsa akan fu'ad. A yadda yaga idanunsa sun jirkita ya tabbatar labarin ya gama ruskarsa.

"Da idanu yabi farouq din,har zuwa sanda ya qaraso,ya tsugunna ya debi duqunqunannun jaridun"

ya bude ya kuma rufesu a take.

"""Da gayya aka buga wannan news din """

"""To menene qaryar da sukayi a ciki?.....ban karanta sauran labarinta a qasa da suka saka ba. amma"

"wanne ne qarya farouq?"" Maida dubansa yayi kan fu'ad da yake dubansa kai tsaye. A zahiri jijiyoyin kansa ke tashi sosai har sun nuna ta farar fatarsa,wanda abadini yake nuna ciwon kai yakeyi sosai,irin ciwon kan da ya dinga addaba masa sanda yake fama da matsalar depression dinsa,wanda ya tabbatar"

ya jima rabonsa dashi.....

Sakin baki yayi yana kallon fu'ad din daya fara magana cikin sanyi saidai akwai zafi me yawa a

kalamansa.

"""Stop dude.....ina gaya maka.....don't judge book by his cover. ka daina judging mutane haka"""

"""Judging nasu nake ma?,bayan ina da full details na evidence akan duk maganan da nakeyi farouq akan"

"yarinyar?"" Yayi maganan da sanyin dai,amma lafuzzansa na nuna zallar zafin da yakeji."

"""Evidence kadai bazasu tabbatar da hakan ba. kayi managing personal boundaries tsakaninku kaman"

"na kowanne miji da mata,akwai buqatar wani sensitive. """

"""Haba mana!"" Fu'ad da yakeji zuciyarsa na matsewa kaman zata fashe ya tsaida farouq yana zama sosai"

yana jin jiri daga inda yake zaunen.

"""Kada bakinka yakai nan wajen. bakasan wacece ita bane farouq?,bakasan sunan da kowa yake"

"kiranta dashi ba?,baka gani jikin newspapers ba?"""

"""Na gani.....na kuma sani......kuma ka rigani sanin haka kace zaka daukota ka gyarata. ya akayi ka kasa"

"fu'ad?"" Ya jefa masa tambayar yana riqe habarsa. Kansa ya jijjiga sosai yana duban farouq"

"""Ban kasa ba......bazan kuma kasa ba......abu daya kemin burki duk sanda na kalleta sai naji tayi"

qanqanta da yawa nayi mata kalar azabobin dana tanadar mata. tayi mitsitsiya na sanyata a prison din

dana shirya mata......amma duk sanda ta aikata wani abu kota bullo da wani abun sai naga nine

naketa kuskuren kallon tayi qanqanta......a abinda zuciyata ke rayamin wannan karon duk hukuncin

"da yazo na dauka a kanta a tunanina na qarshe dashi zanyi amfani """

"""Banda divorcee. """

"""Harda shi idan ta kama"" Ya fada confidently."

"Ido Farooq ya zuba masa kawai,ga mamakin fu'ad sai yaga ya saki wani irin murmushi yana girgiza"

"kai. Shima duban farouq din yake kafin yaji murmushinsa ya bata masa rai. Bayajin a yanayin da yake ciki ya kamata wani abu me kama da murmushi ya fita a fuskan farouq,don haka ya miqe tsam yana dosar"

bedroom dinsa. Da hanzari farouq ya miqe yana kiransa

"""Wait dude. wait"" Don ya tabbatar wannan bedroom din nasa me smart door idan ya shiga ya rufe"

"baka isa ka bude ba muddin bai sakaka cikin wadanda zasu iya budeta ba. Bai saurareshi ba ya shige dakin abinsa,da qarfi ya rufe qofar yabar farouq a nan a tsaye. A yanzun da baya ganinsa sai murmushinsa ya ninka na dazu,bayan minti uku yayi qoqarin daidaita kansa,ya matsa yana daukan"

telephone na falo din ya kira cikin dakin nasa.

"Yayita kira yana jiyota tana ringing,kaman bazai daga ba kafin ya daga daga baya,ya sakata a"

kunne ba tare da yace komai ba.

"""Am really sorry dude. na hango wani abu ne daban da yake durfafoka da matuqar qarfi fiye da qarfin"

guguwa......amma it seems like baka ganshi ba baka kuma fahimceshi ba. anyways kayi aiki da

"hankalinka da intelligent dinnan dana sanka dashi am always free,and then it's time to act for koma"

waye behind all these issues......na tabbatar akwai wani abu boyayye......think wisely am always by

"your side. take a rest,but please kasha magani""."

"Sanyaya ranshi sosai maganganun farouq sukayi,yayi shuru kawai yana saurarenshi bai iya ce masa"

komai ba. shi kansa baisan me yasa a bangaren nan kaman qwalqwalwarsa bata iya aiki daidai ba?.

Yana jin kamar ya gaji yana buqatar hutu da gaske na jiki dana kwanya

"""Am tired farouq......I'm feeling burnt,i need some time to unwind and focus on my well-being kayi"

"magana da saddiq i want him to schedule my annual leave cikin kwana uku""."

"""Kowa ma lokacin hutunsa yazo International gateway to Maldives"" Ya furta yana motsa labbansa"

gami da jefa hannunsa sama yana kwatanta yadda jirgi yake cillawa sama yayin daya cirata daga qasa.

"""Zan kawo nesa zuwa kusa......zan dawo da mafarki zuwa gaskiya......komai zai warware. zan kuma"

"baka mamakin yadda zan juya maka rayuwarka dare daya"" Farouq ya fada yana dariya kaman mummunan abu irin wannan bai faru ba."

"Kawai wani nishadi yakeji qasan ransa idan yayi imagination na yadda komai zai kasance,sai yaji"

"kawai ya qagu shi Kansa lokacin yayi,sai ya juya ya tattare key da wayarsa yana maidawa aljihu ya soma sauka yana barin gidan,ko saddiq dinma bazai nema ba shi zai shirya komai,sai komai din ya kammala"

sannan kowa yaji ya gani.

"*_tom me karatu?,wanne plan kake tunanin farouq yana dashi akan fu'ad?,muje zuwa_*"

Yana driving a mota amma tunani fal kanshi. Tunda yake bai taba hangen wani abu daya jigata fu'ad

komai tsananinsa ba kaman wannan anya ba burbushin wannan halittar daya tsirowa zuciyarsa

"kuwa?, wadda kusan itace jigo na kowanne tsanani da wahala da zuciya kan iya shiga akan wani dan adam?."

"*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*"

08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ

_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 2

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 64

64

Bayason irin fushin da yakeji cikin ruhinsa da jikinsa gaba daya. yana buqatar yayi cooling down

"ko yaya ne,a lokacin ayar nan da taxo cikin alqur'ani me girma ta fado masa"

"""Ku saurara. da ambaton Allah kadai zukata ke samun nutsuwa"""

"""Sadaqallahul azeem"" Ya fadi yana miqewa hadi da fara jin sassauci daga tuna ayar kawai."

"Toilet dinsa ya shiga,ya daura alwala me kyau,sannan ya dawo cikin dakin yana kunna chandelier"

"din dake kafe tsakiyar dakin,wadda ke hade da Bluetooth da kuma fanka me bada sassanyan iskar data banbanta data sauran fankoki. Remote ya dauka ya kashe hasken don baya buqatarsa,ya kuma kunna speaker din dake jiki yana daidaitata da wayarss,take muryar fasihin malamin nan limamin ka'aba wato"

sheik abdurrahman assudais ta karade dakin cikin sauti mafi tsarki na karatun alqur'ani.

"Relaxing yayi sosai soman sofa din dake dakin yana jin wani sukuni ya soma ratsahi,kaf a cikin"

"malamai idan akwai wani sauti da yafi so yafi qauna bazai wuce sautin sheik abdurrahman assudais ba,wannan dalilin yaja

Please Login or Register in order to submit comment