Reading DUNIYA TA COMPLETE BOOK 2 COMPLETE by Asma Baffa Chapter 26 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko ya ambaci daga inda ainihin

"kwangilar aikin ta fito,wanda fadin daidai yake da fadawar mutanen da suka jibanceshi da yawa cikin masifa da bala'in da baisan ranar fitarsu ba......gwara ya danganta kanshi da mashkur. kusan yasan"

waye.....kuma koda yafi haka hatsari yazan bazai zartashi a hatsari da hatsabibanci ba. koda ya

zartashi yasan bazaikai mutanen da suka qirqirar da aikin ba.

"""Kana da masaniyar cewa maqabarta ka kawo kanka? nan da kake zaune Motuare ce?!"" Ya furta da"

sautin da hatta da mashkur sai da yaji kaman an buga masa guduma still saman ka bayan masifar azabar da yake ciki.

Firfito da idanu hanzari yayi.......yayi gwagwarmayar rayuwa da yawa. ayyukan rashin imani

bila'adadin......ya shiga komar Jami'an tsaro masu yawan gaske da wannan kadai yana iya gane

"mutum da muhallin da ake magana ta gaske kai. Salati ya debo wanda ya manta rabon da ya ambaceshi a bakinsa,sallah kanta ba'a maganarta sam bars aje ga gurbin xama ayi wani xakiri ko tasbihi."

"""Zip your mouth!"" Fu'ad ya furta da fushi"

"""Ko burbushinku ba zaa samu ba. daga yau ba zaku sake gigin tsallaka gonar wani ba"""

"""Innalillahi wa inna alaihi "" Ya jiyo muryar daga can gefe tana fada cikin maqyarqyata saboda tsananin"

tsoron data shiga. Duk tsawarsa guda daya sai taji kamar ana finco mata hantarta tare da qoqarin bintiko zuciyarta daga muhallin da take a dashe.

Waiwayawa yayi yana mamakin wanda ya rage a falon bayan ya bada umarnin kowa ya fice.

Zuwaira ce tsaye yana rawar dari kamar wadda ruwan da yayi saura har yanzu yake sauka kadan kadan a kanta ya qare.

"Sulalewa tayi a wajen tana jin wata razana tana saukar mata,idanunsa sun mata wani kaifi da bata"

"da juriyar daukarsu. Yadda yake magana ga duk wanda yake falon zai tabbatar abinda yake fadin zai aikata ne. Ba wasa ko digo cikin kalamansa. Itakam a yanzun ina ta shirya mutuwa?,a irin wannan qadamin da take lissafin sake inganta rayuwarta da jin dadin da yake hange daga wasu?,itama ta samu ta dandala ta baza nata ikon da isar kafin zuwan randa zata bar numfashi?,shine tun a yanzu a gabanta"

wannan manya manyan alkaba'in yake faruwa?.

"Idanu ya zuba mata da kyau yana qoqarin karantarta,saidai kuma kafin yayi nisa an murza pivot"

door din daga can wajen falon an shigo.

"Farouq ne a gaba,Dr rubayya a tsakiya sai saddiq daga bayanta ."

Shigowarsun kawai cikin falon hada idanunsa da farouq sai yaji kaman an janye wani kaso na

bala'i da masifar da yakeji tana kunnuwa cikin zuciyarsa. Wani irin tashin hankalin da baisan dame zai fasaltashi ba.

Dr rubayya na qoqarin gaidashi saidai shi hanyar hallway din kawai yake nuna mata da yatsa ba

"tare da yace komai ba,sai itama bata sake magana ba kasancewar halinsa ba baqonta bane,ta wuce da kayan aikinta kai tsaye zuwa hanyar."

"""Ka leqa ka kiramin saddam suzo.su biyu"" Yace da saddiq da rinannun idanunsa da suka sanya saddiq"

shan jinin jikinsa bayan mutane biyun da ya gani zube a wajen. Shima baice komai ba ya juya yana fita daga falon.

"A nutse farouq ya isa gabanshi,ba tare da yace komai ba duk da idanunsa na nuna kaduwa da"

abinda yake gani ya kama hannunsa yadan juya sannan ya saki

"""Dude. wai meke faruwa?"" Ya qarasa maganar yana saka idanunsa cikin na fu'ad din."

Janye nasa idon faud din yayi daga na Farooq yana hadiye wani abu me tauri daga qasan

"zuciyarsa. To shi ta yaya ma zai fara bada wannan mummunan labarin?,yace meye?,yace masa wiwi ya kamasu suna sha har ya bugu asthma dinta ya tashi?,ko yace masa ta gayyato maza cikin gidan sun bugu sukaso gwada mata qarfi?,ko kuma yace sharri akayi mata?,barayi zai kirasu ko 'yan fashi?,zaice sun hauro masa gida ne?,gida ma irin nasa?,gidan da ba wani abu daya isa ya shiga ko ya fita cikinsa saida"

"cikakken tsaro da kulawar security waye hankalinsa zai dauka?,waye zai yadda da wannan labarin?."

"""Ka kwashesu ka sakaminsu a cage din dogs dincan "" Ya fada yana miqewa sanda hanzari ke qoqarin"

riqo rigarsa a gigice

"""Kayi mana rai oga.....ka hukuntamu duk yadda kaso,amma kada ka hadamu da karnukan can wallahi"

"ko kafin safiya sun gama cinye namanmu oga. "" Yayi magana fitsarin da yaketa son riqeshi yana kubce"

"masa. Tun shigowarsu gidan yanayin karnukan ya tabbatar masa sunsha banban da dukka karnuka daya sani. Basu bi ta gefensu ba. amma wani abun mamaki yadda suketa haushi ya ninku,yana ganin sanda"

"me kula dasu ya dubasu,ya kuma yiwa security na gidan magana suna sake bincike sassannin gidan"

"amma basu ga komai ba saboda sun shigo ne ta hanya mafi sirri da samun tabbaci,kuma sun samu"

mafakar da binciken me bincike bazai taba kaiwa nan ba.

"""What are you waiting for?!!!"" Fu'ad da dama dukkaninsu suma a cike yake dasu ya fada a tsawace,ba"

"shiri suka durfafesu,hanzari yayi wuf ya kama qafarsa yana sake roqonsa."

"Wani wawan duka yakai masa da qafar daya sanya hanzari zubewa warwas,basu saurara masa"

"ba suka sungumeshi suka hada da mashkur da tsabar razana ya kasa magana,sai yakejin kamar qiyama"

"ce zata tashi. Yasan illar karnukan,don sanda yake sharafinsa ya ajesu a gidansa sun kusa guda biyar,hakanan baisan adadin mutanen da ya sanya suka yagalgala ba."

"""Karku sakasu a cikin cage din ku ajiyesu dakin kusa dashi"" Ya basu umarni sanda suke kicin kicin fita"

dashi.

"""Okay sir"" Suka amsa masa sanin wayeye farouq wajen boss din nasu. Shi daya ne duk duniya yake tada"

"hukuncin da fu'ad yayi kuma ta zauna ba tare da haufi ko kankare ba,shi yasa suka karba umarnin nasa kaman yadda ya basu."

Yadda yaga komai yasan ba lafiya ba. yadda kuma yaga yanayin hannunsa da gidan ya tabbatar

akwai gagarumin wani abu daya faru uwa uba wani kwantaccen fushi d yake gani a fuskar Fu'ad ya

sanar masa akwai matsala ko a yadda ya fita a fusace.

"*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*"

08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ

_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 2

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 60

60

Tun bai qarasa inda yake hangen security na gidan daya tara ba yakejin muryarsa dauke da fushi

"me nauyi. Fada yake da duka zuciyarsa da jikinsa ma,sam kaman ya manta dare ne a yanzun daren"

ma kuma irin daren da akayi ruwan sama ya dauke wanda ke ninka kowanne dare a shuru da daukewar sawu.

"""Your services are no longer required you were fired!"""

"""Ya salam"" Farouq ya fadi,abinda yaketa sauri ya dakatar dashi kenan. Fushinsa na yau yanata bashi"

"mamaki,sau tari shike daukan abu da sauqi yawancin lokuta shike jan qafa da jan lokaci akan"

"abubuwa irin wadannan yana bin komai da lura a kuma tsare,har sai ya tabbatar dashi a inda ya dace."

"Kasa cewa komai yayi,don su kansu ma'aikatan da security din dake on duty a daren kowa cikin"

matuqar tashin hankali yake. Yadda suke roqonsa da mabanbantan harsunansu dukka sai suka bawa farouq din tausayi. Kowanne a cikinsu idan ka dubi fuskarsa ya kadu da hukuncin ba zata na me gidan nasu.

"""Calm down. ya isa"" Farouq ya isa gabansu yana fadi bayan komawar fu'ad din ciki. Hankulansu kuwa"

suka bashi cikin mutuwar jiki hankali a tashe.

"""Ku kwantar da hankalinku.....kowa ya koma bakin aikinsa kafin wayewar gari but,ku sake tsaurara"

kula kafin muga abinda hali zaiyi.

Duk da bawai tabbaci ya basu na cewa ya dawo dasu bakin aiki ba amma hakan ya faranta musu.

Sun sani babu wani guri da zasu samu walwalar rayuwa da 'yanci da albashi me tsananin azabar tsoka kaman gidan jadda.....salary yake musu na kece raini irin salary din da sunyi imani ko a villa suke aiki

"babu me biyansu irinsa. Uwa uba ga ihsani da alkhairi da suke samu kowanne lokaci,wanda ya kusan"

"kamo abinda ake biyansu albashin aikinsu. Da yawansu suna jin idan ba gidan Muhammad jadda ba babu a inda zasu iya aiki,shi yasa suke riqe da aikinsu fiye da yadda ma yake tsammanin zasuyi."

A parlor ya sameshi a tsaye kaman wanda zama ya gagareshi. Baice masa komai ba ya taka inda

"yake tsayen ya riqe hannunsa sannan ya wuce dashi,suka ratsa hallway din suka saura samansa."

"Saman monotti sofa ya zaunar dashi,ya taka da kansa zuwa shiyyar da aka tanada don ajjiye first"

"aid box,don kusan yasan komai na gidan tunda shine ma tsara yadda zai kasance din."

"A gabansa ya zauna,ya bude box din ya ciro cotton wool da spirit ya tsiyaya ya fara goge masa"

"ciwon. Sai a yanzu yake danjin radadin da hannun ke masa amma kadan kadan,saidai har yanzu abinda yakeji a zuciyarsa ya dara wanda ke a hannunsa."

"""Ko meye da sauqi ake daukarsa. da irin wannan temper din da kake ji a ranka komai fa bazai warware"

"ba"" Farouq ya fada yana qarasa goge masan,har yanzu kuma yana mamakin abinda ya birkita nutsatsen mutum irin fu'ad din. Duk da ya sani,ba abu bane me sauqi a keta alfarmar gidanka a shigo maka ba. to amma kuma yadda yasan fu'ad zai iya cewa tun wani zamani can daya shude rabon da yaga"

wannan attitude din a tattare dashi.

"Wayar tafi da gidanka din dake falon,wadda ke ajiye kusa da console mirror din parlor din ce ta"

dauki tsuwwa. Saddiq dake zaune daga gefe dukka jikinsa a mace ne ya dauka

"""Daga hallway bedroom ne"""

"""Ka daga ko Dr rubayya ce"" Farouq ya fadi sanda yake tattare ragowa ragowan audugan da yayi amfani"

"dashi. Maganan second goma sukayi kwata kwata,ya sauke wayar yana duban farouq"

"""Dr ce ke magana.....tace ta kammala amma wai tanason ganin hamma""."

"""Ka gaya mata tayi abinda ya dace kawai basai nazo ba"" Ya fada yana jin ciwon kan daya tashi da jin"

"dadin ya sauka yana son dawowa. Kai farouq ya girgiza yana dubansa,muryarsa a qasa qasa yadda saddiq bazaijishi ba yace"

"""Dole kaje tunda tace kaje din dole saika gwadawa duniya halinka?"" Idanunsa da har yanzu basu koma"

"fararensu ba ya watsawa farouq,kaman zai magana sai kuma ya fasa ya tsuke bakinsa. Kamar bazai tashi ba kafin ya miqe yana kiran sunan Allah,wanda motsawar bakinsa ne kadai zaisa gane hakan."

"A hankali yake sauka zuwa qasan,saidai duk sanda ya kusanci dakin sai abun daya faru mintunan"

"baya yayita dawo masa. Bama irin idan ya tuna ba komai a jikinta. daga ita sai towel sai hijab,sai yaji"

tamkar iskar da yake shaqa tayi masa kadan. Su biyu a daki tana daga ita sai shi su biyu a dakin da

babu cikakkiyar sutura a jikinta......gaban hijabinta yasha cukuikuiya? duk sanda ya kawo nan sai ya

lumshe idonsa saboda ji yake kaman an dauka adda an kafta masa sara a tsakiyar kansa.

Handle din ya murza ya tura ya shiga da sallama saman labbansa. Ma'u dake gyara dakin ta dago

"daga kwashe sharar data gama,ta rusuna tana gaidashi duk da dare ne,sannan ta kwashe dustpan da vacuum cleaner din tayi waje dasu."

"Haka kawai ya samu kansa da bayason kallon fuskarta,don ba abinda yake tuna masa sai a yanayin"

data fado jikinsa.

"""Numfashinta ya koma normal,kuma yanzun haka bacci take me kyau ko da wanne lokaci ma zata"

farka abinta........amma please sir. koda asthma dinta baiyi tsanani ba at least ya kamata ace an ajjiye

"mata in healer. and ya kamata ta dinga kula da gujewa ta'ammali da abubuwa masu hayaqi da yawa""."

Kai kawai ya jinjina ma Dr rubayya

"""Allah ya qara afuwa yasa kaffara.......idan kuma ana buqatar wani abun am ready in sha Allah,koda"

"yaushe kuka kirani am available for your needs""."

"""Thank you"" Ya fada can qasa da kalar miskilancin nan nasa da ba wani baqon abu bane a wajenta."

"Already kafin ta fita ya kira saddiq ya gaya masa gata nan su maidata gida,yana kuma sauke wayar"

kiran farouq ya shigo masa

"""Mu duka mun wuce gida,but.....na kira wasu daga cikin guards dinka an qara akan na cikin gidan in"

"sha Allah kome zaiyi daidai......but please please. karka dauki doka a hannunka akan mutanen nan""."

"Farouq ya fada cikin narke murya. Ya dade da sanin halinsa,muddin ranshi yakai qololuwar baci irin wannan bai iya hukunci ba."

"""Kaji?"" Farouq ya sake maimaitawa jin yayi shuru baice komai ba."

"""Alright"" Ya fadi a hankali kamar wanda maqoronsa ke masa ciwo yana gintse kiran."

"Iska ya sake furzarwa daga bakinsa,daga jikinsa har zuciyarsa babu wani abu dake masa dadi,sai"

ciwo kawai wani irin ciwo me radadi a gangar jiki da zuciyar.

"Karon farko ya maida dubansa saman fuskarta,wanda daidai nan idanunsa suka hangar masa"

"wayar dake gefan pillow dinta. Wani abu ya tsarga masa har yatsun qafarsa,sai ya miqa hannu ya dauko wayar."

Tabbas itace wayar daya gani a hannunta shekaran jiya. wayar da baisan yadda akayi taxo gidan

ba ta kuma zama mallakinta har take amfani da ita.

"Jujjuya wayar yayi sosai yana qare mata kallo,sai ya latsa malatsin gefe haske ya kawo,ya sanya"

dan yatsa ya shafi fuskarta take ta bude.

"Bangaren kira ya shiga ya soma dubawa,kirane da numbers barkatai wanda kusan dukansu babu"

suna. Ci gaba yayi da dubawa har zuwa kan date din shekaran jiya wanda wata number data qare da 01 itace number qarshe da aka amsa kira da ita.

Kai ya jinjina a hankali yana komawa bangaren saqonnin karta kwana wato sms. Dunqule

"hannunsa yayi da kyau yana ci gaba da duba saqonnin da suka shigo da mabanbantan numbers suma,wanda dukkaninsu suna dauke ne da nau'ikan kalaman soyayya iri iri,saidai kowanne saqo ba wata"

amsa guda daya da ta maida masa.

"Kasa ci gaba yayi da dubawa saboda yadda dukka jikinsa ya dauki tsuma,sai ya kashe wayar ya"

"jefata aljihunsa sannan ya miqe yana dubanta da wani zafin zuciya. Takawa ya soma yi a hankali,har cikin jiki da zuciyarsa yana jin bazai iya zama da ita na daren gaba daya ba a daki daya,sai daya hau saman sannan ya kira sashen ma'u yace taje ta kula da ita,baima aje wayar daidai ba ya dora kansa a hankali"

saman sofa din yana fidda numfashi kansa kaman zai fado.

"Tunani ne iri daban daban suke barazanar tarwatsa masa kai,ya rasa da wanne zaiji?,da wanne zai"

"fara?,meye daidai cikin hasashensa meye ba daidai ba?,ganin yana neman rasa nutsuwarsa cikin qasa da minti talatin,sai ya miqe a gaggauce ya jawo earpiece ya toshe kunnuwansa da karatun qur'ani,abinda ya sanya duk abinda yakeji ya soma sauka a hankali,nutsuwarsa ta soma daidaita,nauyin da yakeji a qirjinsa da zuciyarsa suka soma raguwa,sannu a hankali ya maida idanunsa ya lumshe wani bacci yana yin awon"

gaba dashi a cikin falon.

*_TO ASUBA TA GARI. SAIDAI KUMA KO DAME SAFIYAR RANAR ZATA WAYE MUSU DASHI?_*

"*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*"

08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ

_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 2

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 61

61

Tun daga sanda ta farka bata samu wata nutsuwa ko kwanciyar hankali ba sai bayan data tabbatar

ba wani abu a jikinta da mshkur din ya samu kaiwa gareshi

"""Allah na gode maka. Allah na gode maka"" Ta dinga maimaitawa cikin bandaki hawaye na layi bisa"

kuncinta.

"Wanka ta sakeyi dab da asuba da ruwa me dumi sosai,koda ta fito ma'u ta ajiye mata wasu kayan"

"da zata saka. Har zata fita ta bata waje ta canza kayan tace ta zauna,tana jin ma'u kamar jininta,tana jin gamsuwa da dabi'un ma'un. Mutum ce me kamun kai sosai,kawaici gami da kauda kai daga kan komai da bai shafeta ba ko kuma ba'a sanya da ita ba,wannan yana daya daga cikin dabi'un da suka sake sanyawa"

hankalinta ya kwanta da ma'un.

"Ko data shirya hijabi da abun sallah ta buqata,ma'un ta bata ta koma ta zauna. Ta shimfida ta"

"tada sallar. Isha'in da bata samu yi ba a dazu ta bayar,sannan ta dora da shafa'i ta kuma zarce da nafilfilun da ita kanta batasan adadin guda nawa tayi ba. Sam sam bata jin koda digon bacci a idanunta,samun kanta tayi da tsananta addu'o'i masu yawan gaske cikin sallarta. Idanunta sun zubda hawaye masu yawan da adazu bata zubda su ba,jikinta yayi wani mugun sanyi zuwa bayan wani lokaci,qafafunta sunsha tsaiwar da zama kawai take da buqata,saita zauna din tana irga tashihi da yatsun"

hannunta.

"Tuna abinda ya faru da ita dazun kawai razani yake haifar mata,yayin da kwanyarta tayi nisan"

zango wajen tunanin waye yake da alhakin zamewa mashkur jagoran daya risketa har cikin dakinta.

Tayita qoqarin tuna abinda ya faru bayan zubewarta amma ta kasa tuna komi abinda kawai

take iya tunawa sanda ya shigo dakin da fadawa jikinsa da tayi tana neman tallafi cikin kubcewar numfashi.

"Kiran farko dana biyu duka akan kunnenta akayi shi,bayan sauran masallatai sun tada tasu sallar"

sai itama ta miqe ta bada nata faralin.

Ci gaba tayi da zama still a wajen. tana tsammanin wai ko zataji bacci amma babu shi ba

alamarsa. Wani firgici takeji har tsakiyar zuciyarta wanda bada taimakon hailala da takeyi zuwa yazu batajin zata iya zaman dakin ma gaba daya.

"Sanda gari yayi haske ta kalli ma'u dake gefe a zaune,qaunar ma'un da darajarta yana qaruwa"

cikin idanunta. Sam tana lura da ita batayi bacci ma itama

"""Kije ki huta ma'u baki samu bacci ba kema"" Sabreen ta fada muryarta a karye da wani irin sanyi da"

bata taba yi ba. Dan murmushi ta saka tana gyara zamanta

"""Ba wani damuwa.....bai kamata ai na barki ke kadai ba. saidai ko idan kina buqatar cin wani abu?"" Kai"

sabreen ta girgiza mata

"""Bana buqatar komai.....kije kidan rage baccin ma'u ki kintsa. kya dawo daga baya,bana buqatar"

"komai"". Kai ta jinjina sannan ta miqe tana mata sallama ta fice."

Qarasa shafa addu'o'inta tayi ta miqe tana son jin qara watsa wani ruwan dumin ko jikinta zai

"qara yi mata dadi. Wannan karon saita taka zuwa bakin qofa ta murza lock dake jikin qofar kamar me tsoron maimaituwar abinda ya faru daren jiya ya sake faruwa,sannan ta juya a hankali tana wucewa toilet din."

"Tare dasu Jordan da farouq ya kawo suka wuce sallar asuba,wadda duk da qarancin baccinsa"

hakan bai hanashi samun sallar asuba ba. Tun daga fitarsu zuwa dawowarsu su kansu sun fahimci sam yau ba'a mode dinsa yake ba. Idan kai baqo ne a rayuwarsa ba lallai ka fahimci lokutan walwalarsa dana bacin ransa ba......kawai zai zame maka kaman daya ne saboda rashin fara'a da bai da ita. amma gasu

"da suke tare dashi tsahon shekaru,suna iya fahimtar walwalarsa da akasinta dukka qarqashin dabi'arsa"

me kamanceceniya da juna.

"""Mu qarasa ciki jordan"" Yace da jordan din bayan sun shigo ainihin farfajiyar gidan. Ba musu ya takewa"

uban gidan nasa baya suna takawa zuwa dakin da ya bada umarni a ajjiye masa su.

"Duk da kusan dabi'ar gidan shuru ce,amma a yau tana jin gidan ya sake zama shuru gaba daya."

"Hakan yake don tun daga gate din farko na gidan zakaji gidan yayi wani mugun shurun da ko tarin wani babu. Zaka rantse da Allah mutuwa akayi cikin gidan saboda yadda kowa ya sake shiga nutsuwarsa. A mugun kasalance da wani irin rashin kuzari ta shirya cikin atamfa dinkin plain zani da riga,wanda babu"

wani ado da akayi mata ko guda daya face qwarewa da gwanancewar dinki daga telan nasu.

"Dare daya amma gaba daya ta fada,tayi wani rama da ta bayyana har a qasusuwan"

"wuyanta,fuskarta tayi fayau,inda ya fashe a jiya sai yanxu ya fito sosai ta ganshi. Tsaga ce 'yar siririya bame yawa ba,fuskarta tayi wani fayau kaman wadda tayi zazzabin dare. Koda ta kalli fuskarta gaba daya sai taji zuciyarta ta karye,ta koma da baya a hankali tana sake tuna yadda mashkur ya fado mata daki."

Duk wanda wani bala'i ya sameshi kalleshi kawai ashe fiye da haka matan da ibtila'in fyade ya

"fadawa suke ji?. Raurau idanunta sukayi,can qasan ranta sai ta samu kanta da godewa Allah da ya bata"

ikon tsame mata da yawa da suka fuskanci ibtila'i irin wannan zuwa sauyin rayuwa daya kawo musu

sassauci da rangwame.

"Qasa tayi da kanta,daidai lokacin da taji ana mata knocking. A nata zaton ma'u ce. wannan ya"

"sanyata kanta tsaye ta nufi qofar ta kuma bude tana bada hanya,saidai a maimakon ma'u anni ta gani,gefanta kuma amna ce tsaye tana riqe da purse din annin."

"Wani irin nauyi da bata taba jin irinsa ba ya saukar mata,tayi qasa da kanta tana basu hanya."

"""Ai jikinma yayi kyau basai mun shigo har uwar daki ba,mu koma falo mu gaisa a can"" Anni ta fada"

cikin dattakon nata tana juyawa da nuna alamu na surukuta

"""Da kun qaraso din dai anni"" Sabreen ta fada adan kunyace da nufin tsaida annin"

"""A'ah qaraso nan din sabreen. ki fito a hankali karki gaggawa"" Anni ta fadi tana qara yin gaba,amna da"

abun yaketa burgeta takeson tayi tsokana nata binsu da dariya.

Dukka hannayensa ya zube a aljihun wandonsa yana qare musu kallo cikin quntataccen qaramin

"store din ajiyar kayan aikin sola dana engine din gidan idan ya samu matsala. Daga daren jiya zuwa yau idan ka kalli fuskokinsu sai kace basu bane,kada ma mashkur daya kwana a daure yaji labari."

A duk sanda ya kalli mashkur din shi kadai yasan abinda yakeji har yanzu maganganunsa sunqi

daina amsa kuwwa a kuwwa a kunnensa. har yanzu ya gaza daina tuna sunyi gamayya a daki guda

qarqashin abun shaye shaye guda.

Taku biyu yayi y is gaban qofar yana duban mashkur din

"""Waye ya aikoka?,ko kaine ka aiko kanka da kanka makasarka?"" Kai ya mirgina alamun eh koda meye"

zai faru bayajin zai iya buda baki ya fallasa wannan sirrin sirrin da idan har ya bari ya fita to tabbas

shima ya gama jin dadin rayuwarsa har gaba da abada koda yayi escape. Abu ne bisa sharadi da

yarjejeniyar da aka qullata bisa masaniya da kuma abinda zai faru a qarshe.

"Sosai fu'ad ya zuba masa idanu yana karantarsa,yanayinsa ya tabbatar masa bai shirya fadin"

"gaskiya ba duk da baqar wahalar da ta nuna kanta a tattare dashi. Bayajin zai iya wahalar da kansa tsaiwa yana batawa kansa lokacin tambayarsu,yana da wadanda zasu tafi masa dasu har su gane kuskuren da suka tafka na shiga gonar da ba nasu ba. Hannu kawai ya daga ya yiwa Jordan alama,Jordan din ya jinjina kai sannan ya juya yana fita hanyar waje da sassarfa irin ta majiyin qarfi,cikin qasa da minti"

biyar sai gashi sun shigo da wani.

"Kakkauran mutum ne,me qiba da madaidaicin tsaho,yana da baqar fata data haska sosai cikin"

"color din uniform din 'yan sandan dake jikinsa. Maqale da jikin rigar rubutun sunansa ne S.nuhu,wanda iya rank dinsa zai nuna maka cewa shine commissioner of police na jahar gaba daya."

"Salute na juna sukayi shi da fu'ad din,sannan yace"

"""Yallabai yace idan da damuwa ayi gaba dasu"" Kai fu'ad ya jinjina yana baro jikin qofar yana takowa a"

hankali gami da dubansa

"""A wuce dasu a ajjiyemin su,har sai zuwa sanda na buqacesu"". Kai s nuhu ya gyada cikin"

"girmamawa,daga yanda fu'ad yayi maganar ya gama fahimtar komai. Suna girmamashi kaman yadda yake girmamasu,tun daga can copral har zuwa matakin qarshe na samansu,wannan ya sanya basuyi qasa a gwiwa ba suka bashi kyautar jami'an tsaro cikin mutanensu,mutum ne me qoqarin kiyayewa da mutunta doka. Yana da qarfin mulki dana dukiyar da zai iya komai da yaga dama musamman a yanayi irin na qasarnan da zaka iya komai ba komai bane,amma baya yin hakan,komai din yana qoqarin ganin"

ya azashi akan mizanin daya dace.

"""Don girman Allah ka taimakeni.....kayimin sutura. yallabai ni na fadi gaskiya,na fadi"

"gaskiyata. iyakar gaskiyata kenan"". Hanzari ya fada yana hade Hannayensa waje guda yana kallon"

fu'ad da tuni ya soma wucewa xuwa cikin gida.

"Ko muryarsu bayason ji bare yakai ga kallon fuskokinsu,don haka baiko waiwayo ba bare ya"

saurareshi. CP s.nuhu ya daka masa tsawa

"""Miqe muje......ku daukeshi ku samin a mota,mutanen banza kawai banda ma me jadda din kuka"

"samu waye kamanshi da zaku keta masa haddin gida ku shiga ku wayi

Please Login or Register in order to submit comment