Reading DUNIYA TA COMPLETE BOOK 2 COMPLETE by Asma Baffa Chapter 19 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komawa motar,ranshi yana tsananin baci da kalar wannan kiran nata da dukkanin numbers dinsa,kamar wadda batasan abinda ya dace ba,baisan ma ya akayi take da dukka numbers din nasa ba."

"""Soulmate"" Sunan da tayi kiransa dashi kenan da wani irin salo na kashe murya da jan ra'ayi."

"""Why?.....ke bakya gajiya da kira ne?,it's so annoying.....please don't do it again stop it"" Ya fada da"

sautin bacin rai a muryarsa.

"""Haba ka fahimceni mana"" Ta sake fada da hanzari cikin tsoron kada ya katse mata wayar. Kada ya"

ajiye wayar bayan ta samu dama ya daga wayar bayan dukka wahalar da tasha

"""Na fahimci me?....ke bakya ganewa cewa macace ke?,ke ya kamata abi bawai kibi ba? kina mantawa"

"mace da kamun kai aka Santa? "". Da sauri take girgiza kai"

"""Indai a kanka ne bani da wadannan qualities din """

"""Okay....then karki sake kirana. "" Yaja qaramin tsaki yana yanke kiran hadi da jan dogon tsaki yana"

wurga wayar gefe.

Gaba daya soyayya tana sake tona masa kanta a matsayin wani abu da yafi komai zama matsala

"da takura a rayuwa,shi yasa bazai bari ta kunno rayuwarshi yanzu ba har sai sanda ya shirya ya kuma kebe mata lokaci nayin nata."

"Idanunshi akan motar BMW din da aka sanyasu a ciki,sai da yaga fitarsu a gidan sannan yayi"

musu umarni suka tashi motocin suna fita suma daga layin.

Sauke labulen window din da yake bata daman ganin farfajiyar gidan tayi cikin wata irin

"matsananciyar fargaba da kuma tashin hankali. Gaba daya kowacce idea tata ta kunce,ta rasa wanne zaren tunani zata kamo?."

"Wacce irin baqar rana ce yau?,wanne tsautsayi ne qaddara ya sanyata lokacin shigowarsa ya"

"kubce mata har ta saki yaran haka?. Idanunta ta mayar saman agogo sai a sannan ta lura,yau ya"

"sabawa lokacin shigowar tasa ne,ya shigo da wuri ba kaman yadda ya saba ba,sai tasa hannu tana sharbe gumin fuskarta da tafin hannunta."

"Da dan hanzari ta taka da kanta tana fita farfajiyar gidan tana qwalawa mansir kira,kiran daya"

sanyashi sakin duk abinda yakeyi ya qaraso babu shiri.

"""Ka fito da mota,kabi bayan motar jadda diamond zuwa gidan muhammadu akwai yara da sukaje"

"gaida matar gidan,suna shiga minti goma kacal ka aika su taso ka dawomin dasu mansir?,idan ka"

kuskura aka samu akasi baka maidominsu akan kari ba to ka kuka da kanka. ban yarda ku biya ko ina

"ba. ban kuma yarda ka ajesu ako ina ba"" Ta fada tana zare idanu tanaji a jikinta tamkar wani abu zai"

faru.

"""In sha Allahu ba zaa samu ko daya daga ciki ba"" Daga haka saita juya tana komawa ciki."

"Kasa zama tayi ko a cikinma,a jikinta takejin kamar akwai wani abu da ba daidai ba"

"""Ki kira zuwaira kisa ta kula miki da motsinsu"" Wani sashe na zuciyarta ya bata shawara."

"Bibbiyu ta dinga hada stairs din tana haurawa samanta,cikin lokaci qanqani ta isa dakinta,ta"

zauna gefan gado tana daukan wayarta dake saman drawer ta fara kiran zuwairan.

"Saidai kash!,kiran farko aka shaida mata kwata kwata wayar a kashe take,ta sake gwadawa cikin"

"rashin gamsuwa da bayanin farko na na'urar still sukace mata yana a kashe,ta sake dai gwadawa a"

"karo na uku,nan dinma amsar dukka daya ce,saita ajiye wayar a gefanta tana jan wani matsiyacin tsaki"

44

"_Daga hassan dan sumra R A yace,daga manzan Allah S A W yace:Duk macen da waliyyai biyu suka aurar"

"da ita ga maza mabanbanta a lokaci guda,to ita din mallakin na farkon ce(wanda aka fara daura mata aure dashi)_"

"""Tur da halinki zuwaira,Allah wadai da halinki"" Ta fada tana cika tana batsewa,har cikin ranta tana"

"jin kamar tayi tsuntsuwa ta tafi gidan da kanta. To amma kuma idan tayi duba ga wasu abubuwa,hakan bame yiwuwa bane,dole taci gaba da zama tana gwada kiran akai akai,yayi da idanunta ya ta'allaqa akan"

agogo tana qidanye da mintunan fitarsu daga gidan.

"Daga qarshe ta sare kan samun xuwaira,to amma dole tana da buqatar kiran wani da zame zame"

mata garkuwa a can gidan

"""Laila"" Zuciyarta ta tunasar da ita."

"""Yauwa"" Ta fada da madaukakin zumudi,ta soma lalubar number wayar lailan."

Duk da safiya ce amma ta kusan awa guda da rabi a gidan nasu. Cikin asalin dakin da yake shine

"mallakinta,saman gadon sun qule ita da mahaifiyarta hajja harira wadda ta tsareta da idanu bayan ta gama zayyane mata karonsu da fu'ad na qarshe."

Sai da tayi kaman ba zata daina kallon nata ba kafin taja wani tsaki tana dauke dubanta daga

kanta.

"""To wai meye ma amfanin zamanki a gidan laila?,kada ki zama albasa mana wadda batayi halin ruwa"

"ba?,na kaiki gidan badon kin rasa wajen zama ci sha ko sutura ko kuma gata cikin naku gidan ba. na"

kaiki ne saboda ki karanci komai ki haddace komai ki kuma bi kowanne taku da motsi na kowa a gidan

kafin mu fara gabatar da namu shirin koda kuwa.mariya batayi nasara ba. nasarar mariya ko

"faduwarta ba damuwata bane.....hasalima inda zata fadi hakan shine daidai a tare dani kinsan me?"""

Kai laila ta girgiza tana jin faduwar gaba da kiran sunan maamah da akayi.

"""Nasarata itace ya kamata ta fara samuwa. nasarata ita ya kamata ta fara wanzuwa kafin ta"

mariya........ni ya kamata na fara samun fu'ad na mallaka miki shi muddin mariya ta rigamu samun

fu'ad to ba shakka dukkan wata nasara da muka sanya rai a kanta zata iya zuwa mana da tsauraran hanyoyi da matakai......shan kai nake da buqata mu yiwa mariya laila. donme kikaje kika kwanta kina

"bacci?,waye ya gaya miki nasara na zuwa ta sameka har inda kaka?,bakisan fita ake a nemota ba?!"" Tayi maganar da alamun qunan rai a cikin muryarta,hatta kuma da lailan ta karanci haka,saidai batasan me yasa a kwanakin nan takejin sam bata da damuwa akan wannan lissafin na hajja ba. tamkar wannan"

lissafin an zare mata shi kwata kwata daga zuciyarta.

"""Ban sauka ba hajja. kawai dai saina dinga jin kamar idan mukayi hakan bamu kyautawa maamah"

"ba,kamar idan mukabi komai a sannu zaifi "" . Baki kawai hajja harira ta sake tana kallon laila da wani"

"mamaki daya taru a fuskarta,kuma koda ta zubawa lailan idanu saita karanci da gaske take maganar. Tana shirin yin magana aka turo qofar aka shigo."

Madeena ce dauke da serving tray data jero dukka kayan dadin da aka dafawa hajjan a matsayin

"abincin safe. Tun asuba take tsaye don kawai ta faranta mata,kuma bata da tabbacin zata yaba ko kuma tayi accepting abincin gaba daya."

"""Gasu hajja an gama. "" Ta fada tana rusunawa ba tare data iya hada ido da ita ba. Wani abu me nauyi"

"da girma ya riga ya sauka a zuciyarta game da zancan laila,don haka bacin ran daya taso mata maimakon ta huceshi akan laila sai ta fara ragewa akan madeena"

"""Wannan wanne irin iskancin banza ne?,ina ciki muna sirri da yarinya saiki wani bankowa mutane daki?""."

Murya a karye cike da ladabi tace

"""Kiyi haquri,kin manta ke kikace idan na gama na kawo miki a daki zakici"""

"""Naji da Allah.....koma dashi ki aje saman table. tsnnnnn"" Ta qarasa da tsaki."

"""Awnnn Me dame kika dafa mata ne?"" Laila tayi tambayar tana maida dubanta ga madeena wadda je"

"tiri tirin fita da tray din. Ido kawai hajja ta zubawa laila tana mamakin yadda take nuna halin ko in kula da magana me muhimmanci irin wannan. Dawowa madeena tayi ta durqusa ta bude mata dukka bowls da warmers din,sai lailan ta karyar da wuya."

"""Wallahi meat pie nake mugun kwadayin ci da safen nan don Allah hadamin yaji naman rago cikin"

"sosai"" Ta fada kanta tsaye da sigar umarni."

"""Tom"" Madeena ta amsawa lailan wadda a qalla tayi qanwa ta hudu da ita,ta miqe ta kwanukan tana"

sauka.

"""Idan da a rayuwa tsaiwa ake duba abinda ya kamata. inda a rayuwa jira ake sannan ayi abinda ya"

"dace. tabbas ke kanki da baki juya matan yayunki kamar haka ba"" Hajja tayi zancan tana tsare laila"

da ido tare da qoqarin maida mata girman zancan cikin zuciyarta.

"Dan muskutawa laila tayi tadan kashingida,har yanzu a ranta ita batajin damuwar komai,duk da"

"kuwa bayan kowacce daqiqa sai hoton kyakkyawar fuskar nan tasa ta gilma ta gaban idonta,abinda ke sakata sakin ajiyar zuciya lokaci lokaci gami da sakin qaramin murmushi."

"""Inaso komai sauya.....inason ki canza akalarki daga yau dole gobe ki dawo ki karbi naki kayan"

"aikin......ki kula da zuwaira......banason tasan komai bana son kuma ta fuskanci komai"" Ta fada tana"

"tsareta da ido. Saidai bata kai ga amsawa ba wayarta dake saman kanta ta dauki tsuwwa. Tana daga kwancen ta daga kanta tana duban me kiran,saidai ganin sunanta kadai ya sanyata wani irin zabura hadi"

da tashi zaune.

Hakan kuma baiyi mata ba sai data zamo daga saman gadon ta durqusa a qasa sanda take daga

kiran hade da sallama. Dukka wadannan abubuwan da tayi su suka ja hankalin hajjan sosai taji tanaso taji da wanne mutum me matuqar girma da daraja haka a rayuwarta take waya?.

"""Ina kwana maamah kin tashi lafiya?,kiyi haquri inata zuci zucin na kiraki na gaidaki da safen"

"nan amma na kasa tuna waye zan kira"". Maganar ta yiwa maamah banbarakwai,to amma bata wani"

"kawo komai a ranta ba,duk da laila bata taba mata magana da ladabi rusunawa da kuma kirki irin haka ba"

"""Ba komai,kina gida ne zan baki wani aiki?"". Rawa jikinta ya hauyi saita miqe tana daukan mayafinta"

"""Bana gida maamah amma bani minti goma sha biyar yanzu zan isa gidan,saiki gayamin abinda kikeso"

"ayi miki ko mene"". Mamaki kadan ya sake kamata,to amma a yanzu garkuwa kawai take nema don haka ta amsa mata da"

"""Okay. idan kika isa ki kirani"""

"""Ko kibar wayarma kawai on hold karki kashe yanzu yanzu zan isa,zanyi sauri ma saboda agama komai"

"da wuri"". Wani mamakin dai still ya kamata,amma sai tace"

""" Zan sake kiranki"""

"""To"" Ta amsa mata tana sauke wayar. Jakarta ta kaiwa sura,kamar ma ta manta da hajja dake"

"wajen,kowanne sashe na jikinta rawa yakeyi,ta jefa wayar a jaka ta rataya tana yafa mayafinta. Sai a sannan hajja da mamaki ya kasheta ta kira sunanta da qarfi"

"""Waike da waye kike waya haka lokaci guda hankalinki ya tashi?"". Murmushi ta sakarwa hajjan sanda"

take saka takalminta

"""Maamah ce fa?,ta tambayeni ne ina gida?,wani aiki zata sakani kinga ya kamata na koma ai bai"

"kamata ma ace na fita ban tambayeta ba,amma zan bata haquri daga baya. hajja na tafi,idan na gama"

"mata da wuri zan tambayeta,idan ta barni gobe na dawo zan dawo""."

"Mamaki da ganin almarar abun ya hanata cewa komai,ta sanqame a wajen kawai baki bude tana"

bin laila da kallo wadda keta sambada sauri kamar zataci da baka.

"*_turqashi?,wai meke faruwa?,nace meke faruwa ne jama'a?,shin qaiqayi ne koma kan masheqiya ko"

"kuwa yaya?,wanda lamarin nan ya yiwa dadi ya danna 1 ,wanda baiji dadi ba ya danna 2_*"

"*_gasu huda a hanyar zuwa gidan addansu,yaya zata kasance kenan?_*"

*_yanzu wasan zai fara tafiya daidai _*

*_muje zuwa _*

45

_Daga nana Aisha R.A tace:manzon Allah S A W yace:Duk matar da tayi aure ba tare da izinin waliyyinta

"ba,to aurenta batacce ne,idan mijin ya tare da ita taci sadakinta saboda halastar farjinta a gareshi_"

"Ware idanunta tayi sanda ta isa dining area,sai ta tsaya cak tana sake ware idanunta da kyau"

"tamkar wadda bata gani sosai,kwanyarta na gayawa zuciyarta kawai yaudarar kanta takeyi,basu huda dinta bane.....ba nadra a wajen. auta haneefa tana hannun waccar azzalumar"

"""Adda.."" Muryoyinsu suka zame mata kamar tsani a gareta na tashi daga wani dogon mafarki,kamar"

"wadda aka daki bayanta,sai ta fara nufarsu tanason ta tabasu don ta tabbatar shin su dinne?."

"Allah ne kadai ya sauko da ita daga steps din,don qafafunta hardewa kawai sukeyi har zuwa sanda"

"ta isa garesu. Haneefa da tafi kusa da ita ta jawo,ta miqa hannu tana shafar fuskarta,sai kuma taja hannun huda ta riqe d kyau,sannan ta dafa kafadar nadra."

"Murmushi suka fara yi mata,da alama sun gane abinda take nufi,kuma dariya sukeso suyi"

"mata,saidai yanzun ba Lokacin dariya bane."

"""Ku tsaya a nan ina zuwa"" Shine abinda ta fada kenan tana juyawa ciki cikin gudu gudu sauri sauri. Ko ina"

"a jikinta rawa yakeyi,batasan ya akayi suka kubuto ba,tana ji a jikinta addu'ar data tsananta a wannan Lokacin Allah ya karba mata."

"Birkice closet dinta tayi wajen neman hijab daya tamkar idanunta basa gani,da qyar idanunta"

"suka nuna mata wani ruwan sararin samaniya,ta sanya hannu ta fuzgoshi ta saka,sannan ta dawo falon."

"""Ku taso ku taso mj tafi"" Ta fada da wani irin hanzarin daya sanyasu tsaiwa kawai suka zuba mata"

"idanu,har sai data fusgi hannun nadra da haneefa sannan huda ta biyo bayanta a mamakance."

"Tana riqe da hannuwansun take ratsa farfajiyar gidan,girmanta yasa take ganin kamar ba zasu"

"fita daga ciki ba maamah zata riskesu,kamar tayi nisa da yawa. Security da sauran ma'aikata nata zubewa suna gaidata,amma ita ba wannan bane a gabanta,don ko gane gaisuwar nata basa yi."

Kai tsaye kuma a karon farko security suka bude mata gate ta fice. Taci gaba da jan hannunsu da

wani irin sauri da kaf rayuwarta bata tana yin tafiya da irinsa ba

"""Ina zamuje adda?,ko zama baki barmu munyi ba?"" Haneefa ta tambaya adan shagwabe saboda saurin"

da suke zubawa din ya fara isarta

"""Zaki gani auta. karki damu"" Ta ambata tana duban hanya,daidai sanda ta hangi tahowar motar da tafi"

mata kama da motar da akan kawo maamah a ciki.

"Hagu da damanta ta duba,ba wani gurin labewa. Unguwa ce da dukka gine ginenta ke bisa"

"tsari,layukansu shimfide da wadatacciyar kwalta,manyan gidaje da kowanne gate yake a kulle dame gadi ko kuma kare."

"Cikin ikon Allah ta hangi gida daya da qaramar qofar dame gadi kan fito a bude,saita jasu zuwa"

can ta kuma turasu ciki itama tana me shigewa.

"A gabanta motar tazo ta wuce da gudu,saita sake kamo hannun haneefa tana cewa"

"""Kuzo mu tafi"" Zuciyarta na tsananta bugu qwarai."

"Sai da sukayi tafiya me nisa kafin su samu adaidaita sahu,kasancewar unguwar unguwace ta"

"masu kwalli masu hannu da shuni,zai wahala kaga abun hawa na haya a cikinta. Koda zai shigo ma sai ainihin security da suke gadin unguwar sunyi checking sun tabbatar da amincinsa da ingancinsa. Basa wasa ta wannan fannin saboda dukka unguwar manyan mutane ne a cikinta."

"Sai data tabbatar me abun hawan yayi nisa da unguwar sannan ta sauke ajiyar zuciya,ta juya a"

"hankali tana kallonsu sai taga dukkaninsu ita suka zubawa ido,da alama qarin bayani suke nema. Murmushi kawai ta saki,ta dora hannunta saman kansu ta shafa tana cewa"

"""Zakuji komai bari mu isa""."

Kamar yadda zama ya gagareta haka tsaiwar ma sai taji kamar tana neman gagararta. Wani tashin

"hankali takeji mara misaltuwa,yaran su kadai ne hope dinta,idan har tayi loosing yaran tabbas bata da wani sauran hope."

Yadda take juya yarinyar tayi imanin bawai girman asiri bane. don dama ya bata tabbacin abun

"bame qarfi bane,idanma me yawan addu'a ce kwana uku zai saketa. In kuma me qarfin kurwa ce da tsananin hasken taurari sati biyu zuwa wata daya zai iya sakinta."

"A yadda take maida mata magana da tsananin izza da rashin tsoro,ta tabbatar komai ya"

"saketa,kawai tana biyeta ne saboda yaran da suke hannunta. idan babu su ya zata kaya mata kenan?."

Wani tashin hankalin ya sake rufto mata data tuna da waya fa a Hannun huda. Ita ta siya mata

ita sati guda daya wuce kenan data sake jawota jikinta. Yau idan sukayi amfani da wayar suka kira wani fa?. Abinda ya sakata rarumar tata wayar don sake kiran zuwaira ta karbo mata wayar ko da qarfi

"ne,tana me manta ma wayar zuwaira din a kashe take."

"Cikin sa'a bugu biyu ta dauka,muryarta na nuna alamun bacci. Ashar ta lailayo mata wanda ya"

sanya zuwaira miqe ta zauna da duwawunta

"""Dama bacci na aikeki kiyi?Kinsan aikinki kuwa?,kinsan muhimmancin abinda na aikeki kiyi zuwaira?!"""

"Maamah ta tambaya a tsawace tana jin kamar ta jawo zuwaira daga cikin wayar ta zabga mata mari. Rawa jikin zuwaira ya dauka,batason tayi asarar maamah tun yanzu alhalin bata samu tudun dafawa ba."

"""Kiyimin aikin gafara hajiya tuba nake"""

"""Ki rufemin baki,ki tashi ki dubamin cikin gidanku,daga parlor din matar gidan har bedroom dinta,akwai"

"qannenta da sukazo,ki fara karbamin wayar hannun babbar,minti goma kuma nace ki qara musu su taso ki biyosu har sai kin kawominsu gidannan""."

"""Angama ranki ya dade"" Ta fada tana miqewa da hanzari har dankwalinta yana faduwa,duk da ranta a"

bace yake ainun da irin tsawar data daka matan.

Parlor ta duba na farko dana biyu duka ba kowa. A kitchen ta samu ma'u tana juye mata kunun a

flask gudun kada yayi sanyi jin shuru bata dawo ba.

"Ido suka hada mau ta dauke dubanta a wajen. Haka kawai jininsu baizo daya da zuwairan ba,duk"

"da ma'u bata nuna mata komai,saidai ita zuwairan cike take da haushin ma'un ganin yadda sabreen din ke mu'amalantarta sama da yadda take sakar mata."

"Ko ina na gidan ta duba,tana shirin fita farfajiyar gidan ta duba can sai ga laila ta shigo afujajan"

"""Ina matar gidan?"" Lailan ta tambayi xuwaira."

"""Ban sani ba nima"" Ta bata amsa cikin jin haushi zuciyarta tana raya mata itama aikin dubata ta bata."

"Dole data gama dube dubenta ta dawo parlor din,daidai sanda ma'u ta kammala komai tazo ta"

rabesu tana ficewa abinta ba tare da tace da kowa komai ba.

Dukkansu qoqarin kiran maamah suke don kowa ya fara shaida mata yadda ake ciki. Laila ce ta

"fara samunta,cikin tsananin biyayyar data sanya zuwaira sakin baki tare da tunanin ko wani sabon makircin shiga jikinta suka qullo ta tsaya tana dubanta"

"""Maamah kaman bata gidan nan fa?"". Wata zazzafar zufa ce ta karyo mata,taji kamar gudawa zata tsinke"

mata. To amma yaushe suka shigo da har za'ace basa cikin gidan?.

"""Kun duba ko ina da ina?"" Kai laila ta girgiza tana duban hallway din"

"""Banda bedrooms dinta"""

"""Me kuke jira?,ku dubamin har can"" Ta bata umarni a tsawace har sai da wayar hannun lailan ta kusa"

faduwa.

"""Zan shiga na duba"" Lailan ta fada tana duban zuwaira. Wani kallo ta watsa mata tana samun daya daga"

cikin kujerun ta zauna tana tabe baki.

"Da karsashinta ta soma nufar dakunan,har cikin ranta tana jin dokin shiga taga dakunan ya"

"suke?,tunda koda hallway din bata taba takawa ba bare akai ga shiga ciki."

"""Alhamdulillah"" Ta samu kanta da furtawa lokacin dame napep ya ajiyesu a qofar gidan. Sai a sannan"

"hankalinta ya dawo jikinta,ta tuna bata riqo komai a hannunta ba."

"""Don Allah dan yi haquri,bari a karbo maka kudinka,fitar ce ba'a tsanake ba"" Ta fada tana dubansa. Bai"

"wani damu ba sam,saboda yanayinta kadai ya tabbatar masa idan bai samu qarin abinda ya kamata a bashi ba to tabbas ba za'a rageshi da komai ba. Waiwayawa tayi ta kalli su huda"

"""Ku shiga ciki ku karbomin dubu biyar wajen titi"". Huda ce tayi gaba suka bita a baya. Basu jima ba nadra"

"ta fito da kudin ta miqawa sabreen din,ta karba ta bashi sannan suka wuce cikin gidan a tare."

"Tana sallama aishatu ta fara gani,tana duqe tana wankin uniform dinta daga can bakin famfon"

"da akayi musu saboda hidima irin wannan. Tadan zubawa yarinyar idanu farinciki yana ratsata. Ko a iya aishatu kawai idan ta kalla tana jin wani farinciki da sassauci yana ratsata,kamar ba aishatun da aka debe"

"tsammani da rayuwa da ita ba,kamar ba aishatun da idan ka fita ba zakayi tsammanin zaka dawo ka"

"sameta a raye ba. Sai data dago don yin shanya suka hada idanu,ta watsar da uniform din,ta rugo da"

gudu tana kiran sunanta

"""Adda sabreeennn"" Ta maqaleta da kyau,sai itama ta tsugunna tana rungumeta cikin jikinta qwallar"

farinciki na sauka a idanunta.

"""Aishatu......haka kika koma? alhamdulillah"" Ta fada tana shafa sumarta me santsi."

"""Adda na warke. na samu sauqi adda"" Ta fada itama tana kwantar da kanta a kafadarta."

"""Ki barta ta qaraso ciki mana aishatu"" Muryar titi ta ratso kunnuwansu tana dubansu cikin"

"murmushi,daga nesa kuma tana kallon yadda sabreen din tayi wani irin kyau,fatarta ta qara tsananin haske da wani irin murjewa,sai glowing takeyi duk da tadan fada kadan qibarta ta ragu."

Tana riqe da hannun aishatun suka shiga parlor din titi. Duka sauran yaran falon suka miqe don

basu fahimci ita ake magana ba.

"Dukkaninsu suka baibayeta suna qoqarin kiran sunanta,sai ta zame kawai ta zauna tana"

rungumesu cikin jikinta gaba daya tana kiran sunansu daya bayan daya.

Ruwa da lemon zobo da titi din ke saidawa ta dire musu tana zama gefanta. Sai a sannan yaran

duka suka tashi suna ficewa don basu sarari.

"""Banyi zaton sake ganinki nan kusa ba"" Titi ta fada bayan sun gama gaisawa da gaske farinciki yana"

"nunawa saman fuskarta,duba da sanin babban mutumin data aura. Murmushi sabreen din tayi wanda yakai mata har zuci,musamman data tuna daga rana irin ta yau ta nesanta maamah din da rayuwar"

"qannenta kenan,nesantawa ta har abada"

"""Me zai hana titi?,ban fara fita bane kawai"" Ta amsata tana gyara zamanta"

"""To ma sha Allah,ubangiji ya sanya alkhairi,ya bada zaman lafiya ya kade fitina"". Bata amsa duka"

"wadannan addu'o'i na titi din ba,sai tace da ita"

"""Alfarma nazo nema titi don girman Allah"" Kallonta titi takeyi wani yanayi yana bin fuskarta"

"""Haba sabreen.....haba don Allah,aike din kifi qarfin alfarma. saidai bada umarni kawai"" Murmushi ta"

"saki tana girgiza kai,har yanzu suna mata wani madaukakin kallo."

"""Su huda na kawo miki,inaso kuma ki riqemin su zuwa wani lokaci,don Allah titi ko nan da qofar gida"

bana so su leqa idan zai yiwu bare sukai ga fita waje. akwai gagarumar matsala da take tunkararmu

"gaba daya,akwai masu bibiyar rayuwarsu,ki kulamin dasu don Allah"". Sosai maganar ta shigi titi,saita girgiza kai tana fadin"

"""Aiko su din ba jininki bane sabreena sai inda qarfina ya qare. ba abinda bakiyi mana ba,banda ke da"

Allah ya jefo mana da yanzu bansan a wanne bigire rayuwarmu take kai ba. zan kula miki dasu fiye da

"yadda kike muradi"""

"""Na gode titi kina da tsohuwar waya da bakya amfani da ita?"""

"""Banga abun godiya a nan ba,hasalima kamar wajibi na na aikata. akwai wayata da kika canzamin"

"sanda zamuyi tafiyar nan bari na dauko miki ita"""

"""Idan zan samu da wata wayar daban zanyi kira"" Ta fadi tana qoqarin hada numbers din momma a kanta."

Banda tana da kaifin basira da saurin riqe abu ba yadda zata iya hada number wayar momma

"din,saidai cikin ikon Allah ta hadasu tsaf ta kuma kira zuciyarta na bugawa da fatan ta kira daidai."

"Bugu uku aka daga,muryar momma ta mamaye speaker din tana amsawa da sautin da yake kama"

"sak dana ummensu,sautin da har tata mutuwar ta risketa ba zata manta dashi ba."

"""Mom momma"" Sabreen din ta kirata bakinta yana rawa idanunta suna cika fal da hawaye."

"""Sabreena? kun dawo?,yaushe kika dawo?"""

"""Daga ina?"" Ta tambayi momma din a mamakance qwallar idonta suna tsagaitawa."

"""Tafiyar da kukayi mana ke da me gidan ko sanda zan koma ai naso haduwa dake dole sai hannun"

surukarki nabar qannenki.......saboda dole sai passport dinsu ya zama ready duk dama dai munyi

"magana tana ta iya bakin qoqarin ta,kuma kusan kullum sai munyi waya da yaran"". Mamaki ya sandarar da sabreen,sai ta bude bakinta a hankali"

"""Momma me ya faru?,ban fahimta ba,ita ta nema ki bata su?"""

46

"""Eh kusan hakanne,don naso ganinki ban samu ganin naki ba......tafiyar tawa bata shiri bace. abbansu"

"ne rashin lafiya ta taso masa,dole kuma ana buqatata a kusa,a yadda na tsara zan jira passport din nasu da komai ya kammala,amna dole na tafi saboda jinyarsa,saidai ba inda zan barsu don ban aminta da hannun kowa ba. Randa nake wannan tunanin saiga surukarki Allah ya jeho ta. Ita ta roqeni na bata yaran zata sanya mai gidanki yayi magana don a kammala basu komai da wuri,tace kuma zata turosu ko ta kawominsu da kanta,to amma lokacin da nayi tsammani ma sai gashi har ya gota. Kawai abinda yake kwantarmin da hankali duk sanda mukayi waya da yaran alamu suna nunamin basu da matsala ko damuwar komai"". Kai kawai sabreen ke jinjinawa tana sake girmama kaidin

Please Login or Register in order to submit comment