Reading DUNIYA TA COMPLETE BOOK 2 COMPLETE by Asma Baffa Chapter 25 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na daya daga cikin damar da zai samu cikakkiya kan ya aikata komai"

hankalinsa kwance.

"Wata wawiyar zuqa ya yiwa wiwi din ya sake fesa mata kan fuska,sannan ta birkitota gaba daya"

yana kici kicin fincike hijabin daga jikin ta.

"Dole ta daga fuskarta,duk da yamutsewar hazon dakin dole ta bude kafofin shan iskarta ta fara"

masa magana a rarrabe

"""Kada ka ketamin haddi na,kada ka lalatamin mutuncina"" Tayi.maganar sanda ya samu nasarar salube"

"kan hijabin daga kanta. Bayyanar sassalkar sumarta ya sanyashi sake gigicewa,bai taba tunanin ta mallaki suma har haka ba."

"""Wow"" Ya fada yana qoqarin samun wuyan hijabin don itace hanya mafi sauqi da zata bashi damar"

"tsarge hijabin cikin sauqi daga jikinta. Ta fahimci abinda yake shirin yi,saita tattara dukka dan qarfinta ta cukuikuyeshi da kyau tana kiran sunansa cikin qaraji gami da fadin"

"""Kada ka aikata!. ka qyaleni mashkurrrr!!!!""."

A hankali ya bude idanunsa wadanda basu sauka akan komai ba sai agogon dake gefan gadon nashi.

Idanu ya zuba mishi kafin ya miqa hannu a hankali yana jawoshi yana duba time da weather na gari. A

"nan yaga alamun saukar ruwan sama,sai ya maidashi sannan a hankali ya furta addu'a yayin saukar ruwan sama"

'ALLAHUMMA SAYYIBAN NAFI'AN'.

"A nutse ya tashi daga kwanciyar,ya motsa kadan yana sauke qafafunsa daga qasan gadon wanda"

suka sauka daidai bedroom slippers dinsa yana jin yadda gaba daya ciwon kan da yakeji din ya sauka. A

yanzun tsabar ta'ammali da home remedies ya sanya ba kasafai ya fiya afawa kansa qwayoyin bature ba

yayin zazzabi da ciwon kai ba.

"Miqewa yayi ya fara takawa zuwa qofa yana mamakin yawan baccin da yayi,yadan shafi cikinsa"

"yana jin yadda yunwa ta fara yamutsa hanjinsa,don haka ya yanke shawarar ya sauka qasa kawai yaci abinci,yadan duba ayyukansa koda na awa biyu ne kafin ya sake kwanciya."

"A parlor ya tsaya ya duba wayarsa,ya samu tarin miscal amma ciki na farouq yafi yawa,ya samu"

"saqonsa da yake masa mita akan bai bada komai na tafiyarsu ba bayan saura sati guda. Qasan zuciyarsa kawai yayi murmushi yana sauka daga duba saqonnin. Har ya aje wayar wani tunani ya fado masa,sai ya"

tsaya ya zubawa qofa idanu.

Yana tuna tahowarta ne jiya daga bedroom dinta zuwa qofan falo. Tabbas idan idanunsa ba

qarya sukayi masa ba kallo yaga tanayi.

"""A ina ta samu waya?,waye ya bata waya?"" Ya yiwa kansa tambayar a bayyane yana zurfafa nazarin ta"

inda zata samu waya tana cikin gida.

"Kaman yadda ya sanya doka ya sani ba wanda ke shiga gidan,sai amna da tazo baifi sau biyu ba."

"Amna kuwa yayi imanin ba zata taba bata waya ba musamman idan ta gaya mata shi ya karbe. Duk abinda yayi ko ya aikata amna tasan yana da dalili,ta fita saninsa,so ba zata karya dokarsa ba."

"Kai ya jinjina yana tuna fitar da tayi ba tare da sani ko izininsa ba rannan,tabbas wayar tana da"

alaqa da wannan fitar duk da ya bincika babu wani abu da yayi kama da gurin wani taje amma how

and when ta samu waya?.

Tambayar data masa susa kenan a qirji. Yanaji kaman ya kamata ya maida hankali a saka CCTV

"din. Company din yazo har sau biyu shi yace su bari ya zama free ya kirasu,yana jin kamar gamsuwa daya fara bawa kansa don tana karatun addini sosai a yanzu ta hannun jikar malam kaman bai kamata ya"

bata amanna har haka ba.

"Da wannan tunanin ya bude smart door dinsa,ya kuma fara sauka zuwa qasa."

Abinda ya soma bashi mamaki shine jin gaurayar wani qamshi qamshi me kama da wari wari da

"gauraye stairs din. Koda ya kawo qarshenta sai yaji warin yana dada qarfi,ya tsaya cak yana buda hancinsa sosai,a nan yaji daga inda warin yafi qarfi."

"Mamaki ya kamashi sosai,yana da wani irin experience na iya hasashen abu da gano sauyawar"

motsi ko yanayi kaman wanda ya karanci aikin binciken tsaro na sirri. Fara takawa yayi zuwa cikin

"hallway din a hankali,yana sake shiga ciki xarginsa kuma na sake qarfafa saboda daduwar warin da sai a sannan ya fahimci warin wiwi ne."

"""Wiwi?"" Ta maimaita sunanta can qasan maqoshinsa sanda ya iso bakin qofar dakin."

"Tsaiwar da yayi duka baifi ta minti guda ba,amma sai yaji jikinsa bai aminta da dakin ba,baya"

"buqatar yayi knocking don ba qa'idar bincike bace akan abinda kakeson ganin gaskiyarsa quru quru,juyawa yayi da sassarfa yana tuna inda yaga an tanada a dakin nasa saboda ajiye kowanne key na kowacce qofa ta gidan a matsayinsa na mamallakin Master bedroom."

"Dubawa daya ya hango master key,sai ya daukoshi yana juyawa gami da saukowa kai tsaye yana"

nufar hallway din.

"Ta riqe ya riqr,yaja taja,har daga baya ya fahimci kamar hayaqin wiwin din kawai ke iya bugar da"

"ita. Hakan ya sakashi tsugunnawa ya dauki guntuwar data rage,ya jata da kyau ya fesa mata a fuska. Numfashin ta ne ya soma yankewa,ta jawoshi da wani irin hanzari tana tuna komai zai iya faruwa idan ta sake ta rasa numfashinta. Ci gaba yayi da bulbula mata tana ci gaba da riqe numfashin nata da taimakon"

hasbunallahu wa ni'imal wakil da take ambata cikin maqogoronta.

"Dariyar mugunta ya saki,sai kuma yace"

"""Are you asthmatic?"" Bai jira komai ba ya danna mata wiwi din a baki,abinda ya birkitata kenan ya"

"sanyata hautsinewar da batasan sanda ta daki al'aurarsa da gwiwar qafarta ba,tsananin zafi ya sakashi"

"sakinta gami da hankadata. dukka jikinta ya gama saki,numfashinta kuma yayi qaura daga gangar"

"jikinta,wannan ya sanyata tafiya luuuuu bakin qofar dakin,wanda haka dama ya saita da nufin fuskarta ta daki qofa ta kuma suma kafin ya gama daidaita radadin daya ziyarceshi."

"Saidai kuma tana isa bakin qofar sai yayi daidai da sanda ya murza handle ya bude,abubuwa biyu"

"duka dakeshi,warin wiwi da fadowarta qirjinsa da guntun wiwin a bakinta,sulalewarta a jikinsa ya sanyata ta gangara ta fadi ta gefen bakinta,ta qarasa zubewa a jikinsa unconscious."

"*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*"

08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ

_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 2

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 58

58

"_Daga ibn abbas RA,manzan Allah S A W yace""duk wanda yaji kiran sallah baije yayi sallar ba(ya zauna ya"

"yita a gida).to bashi da sallah,saidai idan wani uzuri ya hanashi fita(kamar yanayin firgici na rashin tsaro ko tsoro)_"

Dukkanin hannayensa ya sanya tallabota jikinsa yana bin guntun wiwin din daya fadi da kallo. Maido

"dubansa ya sakeyi fuskarta cikin wani irin yanayi dashi kansa baisan yadda zai fassarashi ba,sannan ya sake daga kansa yana bin mashkur dake tsaye da wani birkitaccen kallo. Na wucin gadi tsaf tunaninsa ya tsaya kafin qwaqwalwarsa ta dawo da aiki,yayi hanzarin maida dubansa fuskarta da take bayyanar da"

gushewar numfashi a tattare da ita.

Tattarota yayi sosai sannan ya dagata cak yana jin wani abu yana zagayaw a gangar jikinsa. Waye

"wannan cikin dakinta?,waye wannan da yanayin da ya tabbatar masa ba mutumin kirki ko aziqi ne ba. me ya kawo qaton gardi cikin tsakiyar dakinta daya kaure da mummunan warin wiwi. Duka yana da"

"buqatar wadannan amsoshin,to amma kuma hankalinsa ya rabu gida biyu yana jin kamar ya fara cetar"

numfashinta da ya dauke shine abu mafi muhimmanci na farko a tare dashi.

"""Ina zakaje da ita?"" Muryar mashkur dake a shaqe ta sauka a kunnuwansa sanda ya fara dosar qofar"

"dakin da ita. Wani mahaukacin mamaki ya kasheshi daya sanyashi waiwayowa ya zubewa mashkur idanunsa. A karon farko kaifin birkitattun idanun fu'ad din suka ratsa nasa jijiyoyin idanun suka kuma aike saqo ga sassan jikinsa,saidai kuma a yadda yakejin zuciyar tasa a tsike. ba muhammad jadda"

ba. koma waye zai iya fito na fito dashi indai akan cikar muradinsa ne.

"""Shawara zan baka ka ajiyeta ka rufe mana qofa......don ba suma ba. ko mutuwa tayi tabbas sai na"

"biya buqatata a kanta.......ita ta kira wannan ruwan ita ta kira fitina a sanda fitinar take bacci"". Wani"

"dummmm fu'ad yaji kunnuwansa sun masa na wani lokaci,take wani irin gumi ke dumi ya soma fesowa ta kowacce kafar gashi ta jikinsa. Idanunsa suka soma sauya launi tamkar an diga jan zabibi a cikinsu."

Murna da mamaki suka cakude suka saukarwa mashkur sanda yaga ya sake turo qofar dakin yana

dawowa. Saidai shakku sun cikashi a sanda yake tuna waye muhammad fu'ad? wanne risk ya tsallake

"kafin ya zama abinda ya zama yanzu?,kafin ma ya mallaki asalin abinda ya zama shine silar arxiqinsa a yanxu?."

"Kyakkyawar ajiya yayi mata saman sofa din,da wani irin zafi ya miqe yana nufar inda mashkur"

yake tsaye yana danne da inda ta doka masa bedside lamp da har yanzu wajen yake masa matuqar zugi.

Tun daga yadda idanunsa suka jirkice da kuma yadda jikinsa yake wani irin shaking hankalin

mashkur ya fara dawowa jikinsa.

"""Dakata!. kada ka qaraso nan wajen!"" Mashkur ya fara da qarfi shima yana qoqarin ciro bindigar dake"

maqale a qugunsa.

"""Waye kai?!"" Fu'ad ya watsawa mashkur tambaya da sautin tsawar data sanya dukka dakin ya dauki"

amsa kuwa ba tare daya damu da bindigar dake riqe a hannun mashkur din ba.

"""Sanin koni wanene bazai maka amfani ba abu daya zan baka shawara kaman dai dazu,ka juya ka fita"

"salin alin ka barni da ita"". Kalmar tasa ta qarshe ta sake zamantowa tamkar digar ruwan dalma saman"

"sabuwar fatar jariri. Ya daga qafarsa ya soma takawa da wani irin fushi zuwa inda mashkur ke tsaye idanunsa na sake ninka rinewarsu,kai kace bai fahimci da gaske bindiga bace a hannun mashkur ba."

"""Waye kai!!!"" Ya sake maimaitawa kaman zai tsaga dakin da muryarsa yana jin wani bala'i daga saman"

zuciyarsa. Takowar tasa da yadda yake durfafarsa ba wani sauran tsoro yana tunkararsa ne kai tsaye

kaman bindigar wasan yara ce riqe a hannunsa bata gaske ba shine yake saka dulmiya mashkur a matsanancin mamaki mamakin da yake qarasa dauke ragowar duk wata nutsuwa dake jikinsa yana

kuma dagula masa lissafi da Kalar jarumtar da yake hange tattare dashi.

"""Ina sake gaya maka,kaman yadda ta jawoni rayuwarta. yau ko zaka mutu sai na kwanta da"

"matark. "" Bai samu daman qarasawa ba saboda saukr kwalbar turare saman daidai bakinsa,ta kuma"

"fashe a take,abinda ya bata daman yankan wani sashe na fuskarsa. ya kuma sanya jini soma diga."

Saukar kwalbar a fuskarsa ya sanya bindigar subucewa daga hannunsa. Jinin daya soma diga a

fuskarsa baija hankalinsa ba fiye da faduwar bindigar daga hannunsa. Yayi imani bashi da garkuwar data

"wuce masa bindigar,kuma muddin ta subuce masa to tabbas dukkan wata dama ta subuce masa,tuna wannan ya sanyashi durqusawa ya saka hannu yana laluben inda ta tsalle ta fadi."

"Daga can gefan gadon ya hangota,da azama da kuma sassarfa ya zura hannunsa da zummar"

"daukota,saidai kuma ya makara,don yana dora hannunsa akai qafar fu'ad na sauka saman hannun nasa."

"Da dukkan qarfinsa ya take masa hannun,wani irin zafi da radadi suka ziyarceshi yana jin kamar"

"dukka yatsunsa biyar sun karye. Daya hannun nasa mashkur ya sanya da nufin ture qafar fu'ad din,amma ta nan ma ya rigashi ta hanyar sanya daga qafar tasa ya daki tsintsiyar hannun fu'ad din,bai kuma bari radadin ya gama ratsashi ba ya sake take daya hannun da dole ta sakashi ya zare hannun daga saman bindigar. Da qafa fu'ad ya daki bindigar ta qarasa shigewa can qarqashin gadon,abinda ya daga hankalin"

mashkur kenan

"""Komai zai iya kwabemin......dole na samu abinda nazo nema koda guda daya ne cikin biyu. "" Bai qarasa"

qulla mafitar data dace dashi ba wani kyakkyawan naushi ya saukar masa a tsakiyar kansa.

"Azaba ce ta ratsashi tun daga tsakiyar qwaqwalwarsa har zuwa tafin qafarsa,bai murmure ba"

"wani lafiyayyen naushin ya sauka a kumatunsa. Qarfin naushin ya sakashi yin baya,yayu taga taga zai fadi ya dire da qafarsa. Cikin abinda bai gaza second daya ba yaji wani abu me yauqi da gishiri ya cika masa baki,dole ya hadiye ko ya zubar wanda zubarwar yakejin zaifi masa,sai ya furzar din yana jin yadda kansa ya sake qullewa da azabar data zarce har cikin bakinsa. Furzar da jinin saman marbles din ya bada"

"sauti,saiga haqoransa nan jere reras guda hudu da haskensu ya bayyana cikin jajur din jinin."

"Idanu warwaje yake duban fu'ad,ya tabbatar ya masa illa ta farko kenan da har ya mutu da ita xai"

"tafi lahira?,zuciya ta ciyosa,ta yaya yana namiji shima haka ya tsaya ya masa irin wannan barnar,wannan tunanin ya sanya koda yakai masa naushi na uku ya kauce ya naushi iska,sannan kuma hannunsa ya zarce zuwa ga glass din madubi dake daura da wajen,take ya tarwatse zuwa piece's,ya kuma samu lallausar fatar hannunsa ya yanki inda yakeso. Cikin qasa da second daya shima jini ya soma diga da mugun gudu a a tafin hannunsa da bayan hannun nasa,wannan shine abinda ya baiwa.mashkur qwarin gwiwa,ya kuma Tunxura fu'ad ya sake kai masa wani naushin ba tare daya damu da jinin da yake zubarwa ba. Ya sake samunsa still a wuyansa,zuwa sannan qaramin fitsari ya qwace ma mashkur saboda azabar da yaji ta sauka akan kowacce jijiya tashi. Yanke hukuncin maida martani yayi,cikin nasa fushin"

yakai masa nasa naushin yans cewa

"""Bari na nuna maka iya tawa bajintar"" Saidai baiko qaraso inda yake ba ya yiwa hannun nasa wani"

mummunan bugun da sai da yaji qarar qaramin qashin dake riqe da tsintsiyar hannun nasa.

"Wani ihu ya kwarara don azaba,ihun da lallai inda qaramin gida ne wala'alla har jama'ar dake"

"farkon layinsu sai sunji sautin ihun nasa ya samu ratsawa tsawa ta kowacce kafa dake dakin,ta kuma"

"isa ga kunnen daya daga cikin securities na gidan dake on duty a daren,yaketa kuma kai kawo domin tabbatar da tsaron gidan da amincin masu gidan."

"Tsayawa yayi sosai yana son tantance daga inda qarar ya fito,a lokacin fu'ad ya sake isa inda"

"yake ya kuma daki gwiwarsa da qafa,abinda ya sanyashi zubewa saman gwiwoyin nasa shima yana sakin ihu karo na biyu saboda yadda yaji qoqon gwiwarsa kaman ya fice fit daga jikinsa."

"""Zan saka kayi nadama,zakayi dana sanin abinda kakemin wallahi sai na d'an d'ani xumarta kamar"

"yadda kuma kuka d'an d'ana......saina huce fushina a kanta,sai nayi mata fata fata "" Wani mulmulallen"

"abu me kama da wuta yazo ya daki zuciyarsa,har baisan sanda ya sake saka hannu yakai masa dukan daya sanya haqoransa na gaba wannan karon suka baqunci waje ba yana wani irin huci kamar tsohon"

kumurci.

"A gigice ya sake fidda idanunsa yana kallon haqoransa guda biyar zube a gabansa cikin jini,a"

"qiyasi ya rasa haqora aqalla goma sha biyar,sha biyar suka rage masa a baki sai ya saki wata"

kururuwar data tabbatarwa security din daga cikin gidanne.

"Wayarsa ya zaro ya fara kiran number gaggawa ta cikin gidan,saidai kiran daga parlor hallway"

"xuwa sassansa ya tsaya,bai kawo dakin sabreen ba saboda datse layin da mashkur yayi. Cikin gunji duk da yadda jini yake ambaliya a bakinsa amma bai fasa duban fu'ad dake jawo wata cable me kauri ba yace"

"""Saina lalata rayuwarka......sain......"" Maganan ta katse saboda wani naushin daya sake xuba masa a"

"tsakiyar kai,take wuta ta dauke masa,sashen maganarsa kuma ya dakata na wucin gadi,sannan ya tafi yifff ya fada akan jininsa jikinsa yana saki,komai baya aiki illa numfashinsa dake fita a wahalce."

"Da qafa ya dakeshi ya juyashi,ya tsugunna yana sanya cable din daga hannunsa zuwa"

"qafafunsa,sai daya tabbatar ya daureshi sosai sannan ya fara jansa kaman mushe ko kayan wanki yana bude dakin ya fiddoshi."

Sai daya kawo parlor na biyu sannan ya zubeshi a tsakiya. Jijiyar kansa na wani mugun gudu da

harbawa ya qarasa gaban telephone ya fara kiran sashen tsaro na gidan.

"""Yes sir. "" Security din dake tsaye yana jiran kota kwana ya fada sanda kiran fu'ad ya riskeshi."

"""Ku bincika min cikin gidan nan da kewayensa.......ina kyautata zaton akwai wani mutumin daban na"

"baku minti goma kacal"" Yadda yaji muryar boss din nasu a yau sai yaji wani tsoro da razani ya kamashi,bai taba magana dasu da irin wannan sautin dake cike da fushi da tsawa ba. Maida wayar yayi"

sannan ya matsa cikin hikima ya qyasawa abokin aikinsa.

"A zuciye ya wurgar da kan wayar,sannan ya juyo yana takowa zuwa inda ya ajiye mashkur."

"Zagayashi yayi har kusan sau uku,zuciyarsa na masa wani irin tsalle a qirji,ba abinda zuciyarsa ke"

"gaya masa illa ya dauko bindigar ya fasa tsakiyar kansa da ita. Numfashi yaja sosai,sai ya juya yana komawa ciki bayan tunawa da yayi da ita,sa'annan muddin yaci gaba da zama a gaban mashkur zai"

harbeshi dinne abinda yaketa qoqarin hana kansa aiwatarwa.

"A bude qofar dakin yake,wannan ya bashi damar shiga kansa tsaye. Dakin da zuwa sannan gaba"

"daya komai na cikinsa ya hargitse,banda fasasssun glass da kwalaben fitilar data kwatsawa mashkur ba komai a qasan,sai wargatsatstsun kayan dake saman dressing table dinta da suka tarwatse a qasa."

"Inda take kwace ya maida idanunsa,har yanzu tana kwance inda ya barta din,idanunsa kafe a"

"kanta ya qarasa gabanta. Sauka idanunsa yayi a saitin bakinta,pink lips dinta da suka sauya launi kadan suka kuma bushe qamas,hoton yadda wiwin ta zauna akan lips dinta ya dawo masa,wani mulmulallen abu ya tokare masa wuya,da sauri ya ture hoton daga kwanyarsa,ya tsugunna a gabanta yana tunanin"

"me zaiyi mata?,me ya kamata ya fara yi?."

"Sake maida dubansa yayi ga fuskarta wadda har dogon dokin wuyanta ya bayyana,hakanan wani"

"sashe na kafadunta saboda saukar hijabin da ya fara samun nasarar yagawa. Sauka dubansa ya qarayi xuwa saitin qirjinta,inda a daidai nan hijabin ya nuna muguwat cukuikuyewar da zata gaya maka an riqe wajen ne da mugun riqo. Qirjinsa yaji ya wani doka,yawun bakinsa kuma yaji ya dauke qaf kaman ba'a taba halittar yawu cikin bakinsa ba. Abinda bai taba ji ba tsahon rayuwarsa yau karon farko ya jishi wata mummunar faduwa gaba,sannan take yaji hannuwansa da qafafunsa sun fara rawa"

"sakamakon tunanin daya bijiro masa. Sake xubawa wajen ido yayi,yayin da zuciya ta fara masa imagination na hannuwan mashkur a wajen,wani abu me qarfi ya daki zuciyarsa har sai da ya fusgo numfashinsa da kyau,dai dai sanda yaji itama ta ja numfashin da matsanancin qarfi har sai da qirjinta ya"

daga.

"*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*"

08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ

_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 2

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 59

59

"Da wani irin yanayi numfashin nata ya soma fita,abinda ya sanyashi karon farko tunaninsa yazo masa"

cewa asthmatic ce. Miqewa yayi yana ranqwafawa saman kanta da nufin dagota ya canza mata

"makwanci duk da abinda yakeji,yana dagata din towel din jikinta yana zamewa ya kuma fadi saman qafafunsa."

"""La haula wala quwwata illa billah"" Ya furta a sarari da wani irin bugawa da zuciyarsa tayi yana jin sautin"

har cikin kunnuwansa. Wani jiri da dan qaramin duhu yaji yana mamayarsa har sai daya lumshe idanunsa

"yana jan numfashi da kyau,ya tattaro dukka ragowar qarfinsa ya hada waje daya sannan ya soma takawa da ita ya ajiyeta saman gadon."

"Zamewa hijabinta ya qarayi,santala santalan fararen cinyoyinta suka fito,ya dauke idonsa da sauri"

"yana jin yadda bugun zuciyarsa ya dake qaruwa,sai ya sanya hannu yana jan hijab din yana jin zuciyarsa na qara quntata waje daya kaman an daureta a tsakanin qirjinsa"

"""Why?"" Ya fada da mabayyanin sauti yana jin idanunsa na masa wani yaji yaji. Ta yaya wani zai samu"

"hanyan shigo masa gida?,garin yaya hakan zata faru?. Kai ya girgiza,hankalinsa bazai dauki wannan ba. kanshi da tunaninsa ba zasu iya karba ba. Taimakon gaggawa ya soma bata kaman yadda sukewa"

anni idan irin haka ta taso. Sam ya kasa hada bakinsa da nata saboda warin wiwin da yake tashi daga

"ciki,wanda yana daya daga cikin abubuwan mayen da ya yiwa muguwar tsana."

"Laluba aljihunsa yayi,sai a sannan ya tuna da wayarsa,ya cirota a nutse yana budewa gami da"

"nemo number saddiq. Saddiq dinne kadai yasan bai fiya bacci da wuri ba,shima kaman shi yake,yanayin"

"aikinsu ya sanya sukan iya raba dare a gida suna rage ayyuka. Bugu daya tak kuwa ya daga,muryarsa can qasa yace"

"""Barka da dare hamma..."" Bai amsa gaisuwar tasa ba yace masa."

"""Ka nemomin Dr rubayya. please ku kawota gida yanzu if possible"""

"""Subhanallah...waye baida lafiya hamma?"". Rasa amsar ma da zai bawa saddiq din yayi,sai kawai yace"

masa

"""Ba wani abu bane can just kayi sauri ku qaraso""."

"Sauke wayar saddiq yayi yana duban farouq dake zaune a gefansa,wanda tunda ya daga wayar"

"yaji da waye suke waya ya maida hankalinsa wajen duk da idanunsa suna kan system dinsa yau din yana sashen su saddiq dinne,don shima aiki gareshi sosai,sun samu sabon iri da sukeson su fara gwadawa manoma da manyan manoma da 'yan kasuwa,yanaso yayi settling na komai kafin ya kwanta,charger dinsa na system dinsa tayi masa tutsu,dole ya shigo ya karbi ta saddiq din ya jona gudun kada tayi"

shutting down.

"""Lafiya yace maka ba?"" Farouq ya fada kansa tsaye yana duban saddiq. Daga masa kai saddiq din"

"yayi,sai farouq din ya soma tattare ayyukan nasa waje daya ya killace yana cewa"

"""Ka kirata kace zamu biyo mu dauketa. fu'ad bazai taba gaya maka worsening na komai ba indai"

"shine"". Ya furta yana saving ayyukan da sauri cikin aikin nasa,wannan ya sanya saddiq shima ya soma qoqarin kiran nata."

Sai daya ajiye wayar saman bedsheets dinnan sannan ya lura da hannunsa da har yanzu yake

"tsatsafar jini. Radadin dake cikin zuciyarsa ya danne wanda yake ji a hannunsa,shi yasa sam bayajin komai a hannun nasa. Idanunsa ya sake mayarwa kanta,sai kawai ya samu kansa da miqewa yana daukan wayarsa,ya daidaita iskar dakin saboda gumi daya gani saman goshinta ya qara hasken qwan dakin sannan ya fara takawa cikin takatsatsan gudun kada ya taka wani abu ya soma fita a dakin yana"

komawa parlor.

Tun bai qarasa ba ya hangesu sun cika hannunsu da wani baqin kakkauran matashi wanda ke

"sanye da baqaqen kaya full dress,tun daga hula riga zuwa wandon jikinsa. Iya riqon da sukayi masa kadai zai gaya maka yadda ya matsu a hannunsu."

"Ci gaba yayi da takowa yana karantarsa,duk wani alamu dake nuna tashin hankali da rudani sun"

tabbata a fuska da jikinsa.

"""Sakeshi"" Fu'ad ya fadi yana jin hatta da security din gidan suma a yau bazasu tsira a hannunsa ba."

Gaban mashkur ya qarasa ya zauna saman kujerar falon

"""Ku zaunarmin dashi a nan"" Ya fada yana musu nuni da gefan mashkur din. Wani mugun duka sukayi"

masa wanda ya sanyashi zubewa ba shiri yana fasa qara.

"""Ku jirani a waje"" Fu'ad din ya fadi yana qoqarin hana jinin dake diga a hannunsa bata sofa din da yake"

kai.

"Kallon fu'ad kawai matashin yakeyi,yana jin yadda kashi da fitsari gaba daya suke neman kufce"

"masa,saidai kuma yasan babban kuskure na gaba da zaiyi shine ya saki fitsari ko kashi a wannan kyakkyawan falon. Zai iya cewa a tarihin rayuwarsa kaf. a tarihin manya manyan laifukan daya aikata a"

"rayuwarsa bai taba cin karo da mutumin da yayi masa kwarjini irin muhammad jadda ba. Yana zube a gabansa yana jira yaji koda wata kalma daya daga bakinsa amma ko qwayar idanunsa bai daga ya kalleshi ba bare ya sanya ran wata tambaya zata biyo baya,ta goge jinin hannunsa kawai yake da"

lallausar tissue din daya ciro a tissue box din dake gefansa.

Bawai yayi hakan bane saboda ciwon yana da muhimmanci a rayuwarsa ba.....a'ah yayi shuru

"ne saboda a yanzu babban muradinsa shine yayi mummunan lahani a garesu da babu me iya gane fuskokinsu,duk kuwa da cewa ko a yanzun fuskar mashkur ta haye tayi kumburin da dukka wata halittar"

"fuskar ta sauya daga asalin yadda take,abinda yake sake sanya tsoro me yawa kenan ga zuciyar hanzari."

"""Don Allah me gida.... Kayimin rai,ka tausayamin me gida. don girman Allah"". Kalaman hanzari kenan"

"wanda ya gaza jiran yaji abinda fu'ad din zai fada. Cillar da tissue din yayi,sannan ya daga idanunsa da har yau launinsu bai koma daidai ba ya aza akan hanzari"

"""Waye ya gayyato ka?,duka ku biyun kuma waye ya aiko ku?' Tambayoyi guda biyun da a wajen hanzari"

suke masa kamanceceniya da tambayar kabari ga kafiri a ranar daren farko

"""Shine!. shine wallahi"" Hanzari ya fada yana nuna mashkur dake yashe a qasa har yanzu bakinsa na"

fidda jini.

A yadda mashkur din yake yayita qoqarin murgina kai ya kalli koda idanun hanzari ne amma ya

kasa ballantana ya fadi wata kalma da zata zama kariyar kai a gareshi. Kiran sunan mashkur da hanzari yayi shine abu mafi sauqi mafita mafi sauqi a gareshi akan ya ayyana

Please Login or Register in order to submit comment