Reading DUNIYA TA COMPLETE BOOK 2 COMPLETE by Asma Baffa Chapter 21 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata yaro yana wasa da kan maciji koda kuwa ya rasa abun wasa?."

"Yanayinta ta daidaita don yayi dai dai da yadda maamah zataso taji,tana mamakin zallar rainin"

"hankali irin nata. Bayan mummunar sakayyar da tayi mata,kuma wai ta nemeta da tata matsalar tamkar ma batasan me ya faru ba?."

"""Me yake faruwa?"""

"""Garkuwata ta subucemin daga yanzu zuwa kowanne lokaci zan iya fuskantar barazana daga wajen"

"abun hari na,kowanne hope nawa kuma ya subuce hajja. meye abunyi?"" Ta qarasa maganar da sigar"

"tambaya cike da damuwa. Iska hajja ta furzar tana dan bubbuga tafin qafarta kadan kadan,a nutse tace da ita."

"""Bani lokaci mariya nayi tunani mintuna kadan nake buqata"". Jikinta a sanyaye ta amsa mata suna"

katse wayar su dukka biyun.

"Wayarta take dan bugawa cikin tafin hannunta cikin salo na tunani. Mariya shegen kai ce,tana"

da nata matsanancin wayon da kai da kake rayuwa da ita kayi kadan ka fahimci komai idan ba ita taso ba. saidai kuma a wannan yanayin da ake ciki mariya tana tafin hannunta ne. Bata isa tayi wani motsi

"cikakke ba ba tare da ita ba,itace ginshiqin itace kuma madogarar. To shin batasan abinda tayi mata"

"bane?,batasan me ya faru ba?,ko tsananin iya bariki ce kawai?."

"""Inaso na samu tabbaci"" Ta furta tana daukar wayarta data aje tun daxun ta sake lalubar number"

maamah din.

"Bugu daya tak ta daga,ta sanya wayar a kunnenta tana kiran sunan hajja."

"""Duk abinda zaka daukoshi ko ka matso dashi don biyan buqatarka. kuma ya gaza yin wannan aikin sai"

"nakega bashi da wani amfani,kau dashi kawai zaifi me zai hana ta gusa daga rayuwar fuad tun kafin"

"matsalolin da boka ya baki a dunqule su fara bayyana har sufi qarfin shawowarki? ga laila nan?,umarni"

"na da naki sune zasu zama abun binta,a azata a bigiren da wannan ke kai,nayi Imani da laila. tabbas ba"

"zata sabawa tsarinmu ba. sirrinmu kuma a lullube""."

"Nauyi maamah taji maganar tayi mata,sannan sam bataji maganar ta kama hankalinta ba. Har"

"cikin jininta da zuciyarta takejin laila bata mata ba,kwata kwata bata dace da wannan aikin ba,bata dace ma ta zama matarsa ba koda na minti guda ne kuwa. Tasan wacce hajja farin sani,tana tunanin ita ko yaronta zasu kubuta daga ayyukanta ne?,sai ta girgiza kai a fili tana jin abun bai kama hankalinta ba. To amma dole sai tabi ta takatsantsan kafin ta fahimtar da hajja din,tafi kowa sanin hajjan akan laila bata"

dagawa kowa da komai qafa.

"""Aah fa hajja harira,laila ni dake duka 'yarmu ce. ba zamj jefata cikin wannan risk din da wahalar"

"ba......qyale bare dai,wanda idan ya sabawa tsarinmu kowanne mataki zai iya fadawa kansa. kamar"

yadda itama wannan din MUMMUNAN SAKAMAKO na rantse miki da Allah zai yita bibiyarta. ba zan

"qyaleta ba,sai na banbance mata tsakanin aya da tsakuwa!"" ."

"Turqashi!. hajja ta fada qasan ranta,kai tsaye a bayyana ko a kaikaice maamah bata qaunar laila"

ta kafa tarihin zama matar muhammad me jadda. wannan shine amsar tambayarta kai tsaye idan aka

cire kauce kauce.

"""Ke yanzun wanne shiri ne na gaba kike ganin ya kamata muyi?"" Ta mata tambayar tana relaxing kanta"

don samun bakin zaren daga inda zata dasa nata aikin.

"""Ki bari tukunna na samu nutsuwa daga wannan,abubuwa su hau kan saiti,zaki ganewa idanuwanki ba"

"tare da nace dake komai ba"". Ta fadi mata kaman yadda ta saba. Tana da boye duk wani shiri nata,zai"

"wahala tana kan shiri ka sani,ko a baya wannan ne ya zama SILA da sanadin da LAILA ta shiga DUNIYAR lissafinta,qila data tsaya neman fashin baqi wajen boka kamar yadda hajja taso suji ba shakka da qila"

yanzun haka laila bata fada wannan BAQAR MASIFAR ba. dukka hajja ke wannan tunanin cikin ranta

tana jin wani bacin rai yana taso mata.

Hajjan ta bude baki zatace wani abu sautin kukan laila ya mamayi kunnuwanta daga cikin wayar.

"Wani abu ya daketa,tayi shuru tana sauraren tambayar da maamah keyi mata kafin kiran ya yanke."

"""Tashin hankali!"" Ta fada a sarari tana miqewa tsaye,ji take kamar ta wuce kai tsaye gidan maamah"

amma wata zuciyar na jan kunnenta

"""Sai kinyi kamar baki sani ba. sai kinyi kamar baki fahimci komai ba,saikin maida komai ba komai ba""."

Wadannan maganganun suka sanyata rusuna ta koma ta zauna wuta naci gaba da balbala a zuciyarta. Daidai sannan nafessa ta shigo da mopper da broomstick tare da sallama a sanyaye cikin girmamawa.

"""Ubanme kika shigo kiyimin?"". Kai ta sunkunyar"

"""Kiyi haquri,haidar ne ya tashi da zazzabin haqori yau shi yasa ban shigo sharar da wuri ba"". Duk da"

"jikanta ne bata tsaya ta nuna kulawa ko alhinin komai ba,hasalima bata fahimci gaya mata take baida lafiya ba yaron,sai ta daka mata tsawa tana fadin"

""" Sharar da bakiyita dazu ba sai yanzu ko?,baqar munafuka,fita ki bani waje"". Tashi sosai hankalim"

"nafeesa yayi,take idanunta suka tara ruwan hawaye,tana tsoron me zata gayawa d'anta a kanta idan ya dawo,tanason aurenta batason ta kashe mata shi,wannan ya sanya ta sulale tana tsugunnawa ta soma"

mata magiya tana bata haquri

"""Ki tashi bani waje kafin na rufeki da duka,sharar ce nace banaso ko ana dole?"" A nan ta fahimci bawai"

"iya rashin sharar bane kawai da ba'ayi ba ya sanyata haka,akwai wani abu na daban da ya bata mata rai,wannan ya bata sassauci sai ta miqe tana sake bata haquri ta bude qofar ta fita gami da rufe mata. A"

qasan ranta tana tafe tana addu'ar

"""Ubangiji ka qara mata damuwa fiye da damuwoyin data sanyawa zukatanmu ya rabbi ka shagaltar"

"da ita da damuwarta ta yadda zata zame mana mu kuma hutun da bamu taba samunsa cikin gidajen mazajenmu ba""."

49

"_Daga abi sa'eed RA yace:manzan Allah S A W yace; ""idan dayanku yazo masallaci,ya duba"

"takalminsa,idan akwai qazanta ya shareta ya kawar da ita daga jiki,yayi sallah da takalminsa_"

"*_halal ne sallah da takalmi a qafa,na haramci a ciki muddin ba najasa ko dauda a jiki_*"

49

"Ta furta har tsakiyar ranta tana jin ciwon bautar da suke ciki,wadda basusan ranar fitarsu a ciki din"

"ba,sunfi kyautata zaton wataqila sai ranar da surukar tasu ta kwanta dama."

Ajiye wayar maamah tayi a gefanta tana duban laila da hawaye ya yiwa fuskarta shabe shabe

"""Lafiya laila?,me yake faruwa?"" Ta maimaita tambayar tana riqe hannunta"

"""Hamma fu'ad ne maamah ya koreni"". Fuska ta ya mutse tana duban lailan,tashin hankalin da take"

"ciki a yanzun bata jin yakai korar laila daga gidan fu'ad,duk kuwa da cewa hakan da yayi taji ya tabata ya kuma qara bacin ran da takeji a ranta. Ya nuna bata isa ba kenan kamar yadda ta saba. amma yanzun"

"ba shine abinda ya kamata ta damu dashi ba.....tanason tasan ina yaran? ina suka shige?,meye"

"manufar yarinyar?,meye takunta na gaba?."

"""Kina da buqatar ki koma gidan?"" Maamah tayi mata tambayar kai tsaye,don son tabbatar da maganar"

"da sukayi da hajja a yanzun. Shuru lailan tayi,tana jin tamkar kowanne tsari na zuciyarta da kuma tunani na qwaqwalwarta ya birkice,tsare tsarenta. burikanta dama duk wani abu dake gabanta sai takejin"

yana sauya muhalli. Tanason fu'ad sosai......tana kuma jin soyayyarsa. amma sai takejin zama da

"maamah yafi mata zama da fu'ad dadi hakanan ko me maamah ta furta shine umarninta,to tabbas"

zata iya aikatashi komai tsanani da tsaurinsa.

"""Inason hamma fu'ad sosai,inaso na aureshi.......kuma hajja tayimin alqawarin sai na aureshi """

"Maganar sai ta zowa maamah banbarakwai,tayi mata saukar ba zata,ta xubawa laila idanu tana mamakin furucinta tare da tantamar lafiyar qwaqwalwar laila din."

"""Tayi miki alqawari?,yaushe kenan laila?"" Maamah data tattara dukka hankalinta akan lailan ta fada cikin"

tsananin mutuwa da kuma sanyin jiki.

"""Tun sanda ake shirin auren hamma fu'ad ta kaini gidan na zauna don na karanceshi tsaf,sannan ta"

bani ayyukan da zan bashi yaci saboda jawo da hankalinsa kaina da kuma siyan soyayyata. wanda

"daga qarshe takeson ya dawo hannunta gaba daya""."

""" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"" Maamah ta fada tana jin saman kujerar yayi mata tudu da yawa,ba zata"

"iya zama a kai ba duk da laushinta,sai ta sulale ta zauna sosai a qasa. Ta sake zubawa laila idanu sosai maganar na ratsata,amma kuma tana cike da tantama da tunanin cikakkiyar lafiyar kwanyar laila."

"""Tabbas laila ta fara shaye shaye"" Shine abinda maamah ke ayyanawa a ranta. Ba yadda za'ayi hankalin"

laila daidai lafiyarta kuma qalau ta dauki babban sirri da labarin cikakkiyar cin amana irin wannan ta

gaya mata.

"""Don Allah kada kiyi fushi dani kome kike buqata zan miki maamah"" Laila ta fada alamu na bayyana"

kuka nason qwace mata. Al'amarin ya sake jefa maamah a madaukakin mamaki

"""Me kikeso in sake baki labari?"" Laila da gabanta keta faduwa cikin matsanancin tsoron kada ta batawa"

maamah ta fada tana durqusawa a gabanta.

"Mamaki ya sake kashe maamah,ta sake saka idanu ko zataga wani abu na tabin hankali ko hauka"

"tattare da laila,saidai ko kadan bataga wannan ba illa tsantsar biyayya da faranta rai da takeso ta yiwa maamah din."

"""Ki nutsu mariya.....ki nutsu,makashinka tabarmarka. makashinka yana tare da kai"" Wata zuciyar ta"

"ankarar da ita,wannan ya sanya ta aje mamakinta da tunaninta meke faruwa?,ta maida hankalinta ga laila"

"""Tashi ki zauna sosai muyi magana"" Cikin hanzari ta miqe ta koma inda saitin inda maamah ke nuna"

mata ta zauna.

"""Me yasa kika yanke hukuncin gayamin sirrinku ke da mamarki?"" Ta tambayeta da matsanancin mamaki."

"""Saboda ya zamemin dole na inyi miki biyayya.....inajin cewa ke din kamar uwargijiyata ce. ni kuma"

"baiwarki,inajin kamar dama can an halicceni ne don na miki biyayya,inajin komai zai iya samu na muddin ban miki biyayya ba......burina na mutu ina miki biyayya. burina na mutu ina bauta miki"". Ta qarashe"

"maganar da zallar gaskiya da kuma yanayin da yake nuna cewa da gaske take furta maganar dake cikin ranta din. Kowacce tsiga ta jikin maamah sai data zuba,wannan shine kwatankwacin abinda take buri,take fata take kuma mafarkin taji ta kuma gani daga wajen fu'ad ya akayi haka ta kasance akan"

laila.

"""Laila. akwai abinda aka dafawa fu'ad a gidansa baici ba ke kika ci?"" Ta jefa mata tambayar da zallar"

kokwanto a ranta.

Kai tsaye ta gyada mata kai tana dubanta

"""Eh. kwana hudu da suka wuce,naci abincin dare a dining dinsu"""

"""Shikenan!"" Maamah ta furta tana runtse idonta,tayi tsam da ranta bata iya cewa komai ba. Tsahon"

"wasu sakanni tana nazari a zuciyarta,kafin kuma a hankali taji kowanne tashin hankali yana sulalewa daga zuciyartata. Idanunta ta ware akan lailan"

"""Meye shirinku a kaina. meye shirinku akan fu'ad?"" Tambayar data yiwa laila kenan tana da yaqinin da"

tabbacin zata gaya mata komai tiryan tiryan.

Shuru maamah tayi tana biye da laila din har ta gama kwashe mata bayanin komai. Ba bayanin

"yadda lailan ta zayyane mata komai bane yafi daga mata hankali ba,qulli da tuggun da hajja ta shirya qarqashin nata shirin shine abu mafi tsoratarwa da razanarwa a wajenta."

Don baje sirrinsu tasan zata samu information akan dukkanin abinda ya shafi hajja sama da abinda

laila ta gaya mata ma a yanzu muddin wannan hadadden tanadin data yiwa fu'ad ne ya isa cikin

laila.....to ko kashi lailan zatayi kuma take da buqatar ta shaida mata kafin ta yishi lallai ko bayan gida

zai kashe laila ba zatayi ba sai da yarjewar maamah.

Take dukkanin wani alhini da fargabar cin abincin da laila tayi ya fice daga zuciyar maamah.

"Baqincikinta daya asarar data jawo mata,gagarumin shirinta daya baci,wanda ta kashewa maquden kudade masu yawan gaske don ta samu fu'ad a hannunta,yanxu samun laila me zai tsinana mata?,banda kaya da zata zame mata?."

Idan akwai riba guda da zata samu itace. ribar nunawa hajja kuskurenta na ha'intar qauna da

aminci da tayi

"""Lallai zan mulki laila ko don na nunawa hajja itadin qanqanuwar maciyar amana ce. zan mulki laila a"

"gaban idanunta. zan kuma bautar da ita yadda take bautar da d'iyoyin mutane cikin gidanta""."

Duk da takaici tashin hankali da baqinciki daya cika mata zuciya amma saita dubi laila da dan

murmushi

"""Zaki zauna dani?"" Da sauri ta daga kanta tana jin kamar an mata rahama ne"

"""Zan zauna.....zan zauna dake maamah hakan yafimin komai dadi a duniya"""

"""Da kyau"" Ta fada a hankali,dan daga murya tayi sannan ta kira daya daga cikin masu aikinta na gidan"

tace

"""A bata daki"" Ta bisu da kallo sai data tabbatar sun fice a falon sannan ta maida hankalinta cikin jikinta,"

Iska me zafi ta furzar tana lula kanta cikin duniyar tufka da warwara. babu babban target dinta

a yanzu haka idan ba sabreen ba. Bata gidan ta fita. shine abinda ta yita nanatawa tana shafa lips dinta

"da yatsantsa. Da sauri kaman wadda aka tsikara ta jawo wayarta,ta tafi kai tsaye izuwa ma'ajiyar lambobi ta zarce can qasa."

"A jere numbers din nasu suke,saidai kuma tayita kai kawo akan waye zata kira a cikinsu?,waye yafi"

zafin aiki?. Cak idanunta ya tsaya akan wata number da aka rubuta sunan HANZARI bata tsaya jinkiri ba ta danna kan number ta tura gaba izuwa kira.

"Bugu daya tak aka daga,da wata iriyar birktacciyar murya ake fadin"

"""Allah yabar mana ke uwar dakina maganin kuka na"". Wannan kirarin nasa yana fasa mata kai"

"ainun,kuma ko a yanzun shi kadai ya bata tarin qwarin gwiwa"

"""Nayi missing target hanzari.......ka shirya ko da kowanne lokaci zaka iya jin kirana idan kiran kuma ya"

"tabbata. babban aiki nake da buqatar ayimin wanda daga shi bani da sauran haufi ko matsala"""

"""An gama uwar dakina"" Ya fada da qatuwar muryarsa,bata jira komai ba ta kashe kiran,ta kuma maida"

akalar kiran nata zuwa ga number huda.

"Abu daya dai ake sake gaya mata,layin a kashe yake,saita saita lokutan da zataci gaba da kira daga"

"nan har zuwa awa ashirin da hudu,ta aje wayar ta kuma shiga tunanin meye abunyi na gaba?."

*MASHKUR*

"A hankali ya sake gilmawa da motar ta gaban gidan,ba kuma wai don yana da wani abunyi ba ko"

"kuma lalura ke sanyashi wannan zirga zirgar da yakeyi ba. aah,yana yine saboda nazartar gidan da"

kuma dukka wani kai kawo na jama'ar gidan dama ma'aikatan dake aiki cikin gidan daga dare har rana. Wadanda suke shifting da kuma wadanda zamansu kenan.

"Yayi gaba,amma sai yaci gaba da kallon gidan ta rearview mirror yana kada kansa a hankali. Babba"

"duk inda yake babba ne,gidan na daya daga cikin dream house dinsa daya jima yana tunanin idan har ya samu yadda yakeso a shekaru goma masu zuwa zaya mallaki irinsa. Hannunsa ya sanya ya daki steering din motar yana jin wani zafi cikin ransa. Yarinyar tasha dashi da yawa a rayuwa,banda wani abu daya rinjayi zuciyarsa tabbas plan A dinsa a yanzu shine zai zama plan B,plan B kuma shine a plan A,to amma duka wannan bazaiyi aiki ba. yana ganin gwara ya fara diban ganimar tukunna,idan yaso ko meye zai"

faru daga baya me sauqi ne.

"""Ina fata ka gama kallon komai?"" Yayi magana da mutumin dake zaune a back seat wanda zai wahala ka"

iya fahimtar da mutum a gurin.

Kai ya jinjina yana motsa system din dake saman cinyarsa

"""Na gani......aiki ne me bala'in hatsari da dukkaninmu zamu jefa rayuwarmu cikin hatsari amma"

"kuma,ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba.......let's try it......idan mukayi winning "" Sai ya"

saki murmushi yana rufe system din

"""Zamu kasance mutane mafi sa'ar zuwa duniya"" Ya qarasa maganar yana dukan bayan kujerar dake a"

gabansa. Iya nasarar da yayi musu hasashe ta saka mashkur qyaqyacewa da dariya

"""Inaso naji dandanonta.....inaso naji ya take bansan adadin mafarkin da nayi a kanta,ban taba sanya"

kwadayina akan wata 'ya mace ba tunda na fara sanin 'ya'ya mata. wannan macen ta zullemin bansan

"ya take ba sai a kanta,dole ta fahimci wannan kuskuren data aikata!"" Ya fada da qwarin gwiwa qwarai da gaske,yana jin ya zaqu da komai ya tabbata."

"""Bazan iya dogon jira ba Mike ka shirya komai tsakanin kwanakin nan biyu"" Daga hakan sai kawai ya"

qarawa motar wuta sosai suna gaggawar ficewa daga layin.

"*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*"

08187255862

50

"_Daga ibn juhaim bin haris RA(wannan sunan sahabin annabi ne ),yace:Manzan Allah S A W yace ""da"

"me wucewa ta gaban me sallah yasan abinda yake kansa na sabo,tabbas da ya tsaya(ya jira me sallahn ya gama)tsahon gwargwadon shekara arba'in shine yafi masa alkhairi akan ya wuce ta gabansa_"

_Bukhari da muslim ne suka rawaito_

50

"&Daure da babban towel ta fito daga wanka,qaramin tana tsane doguwar sassalka sumarta dake a jiqe sharkaf da ruwa,alamu dake bada tabbacin wankesa tayi. Idanunta a lullumshe tana jin kalan nauyin da yayi mata saboda kukan da tasha a jiya. Duk da nauyin da zuciyarta tayi mata amma ta wani fannin sai take jinta sawai kamar wani nannauyan dutse dake danne da ita ne ya sauka. Tun daga jiyan"

data tabbatar ta miqasu hannun da bata haufi akan zasu cutu ko wani abu maras kyau zai samu riskarsu.

"Tana daga gaban madubin,kadan kadan tana hangen yadda iska take kada labulayen dakin,wata"

"sassanyar iska me dadi kadan kadan tana ratsowa cikin dakin. Lumshe ido ta sakeyi sanda ta gama gyara gashinta ta matseshi cikin ponytail holder bayan ta lanqwasa jelarsa me tsaho sosai,fuskarta ta fito sosai,sai ta sake lumshe manyan idanunta da suka rusuna sosai. Zuciyarta ciwo takeyi idan ta tuna da"

"tuhumar da yayi mata jiyan,tana jin wani zafi cikin qirjinta duk sanda kalmar"

"""Wajen wa kika je?"" Ta dawo mata a kunnenta"

"""Me kikayi?"" Tana sake sakata jin zuciyarta na matsew a qirjinta."

Vibration din da taji daga gefanta shi ya ware zaren tunanin dake qulluwa cikin kanta. Maida

"dubanta tayi wajen,wayar huda data karba ce wadda ta sakawa charge tun da asuba,bayan wayar ta cika kuma sai ta kunna kanta da kanta kamar yadda tsarin wayar yake."

"Sunan MAAMAH data gani ya isheta bayanin wacece,wani matsiyacin tsaki taja tana janye"

"idanunta daga kan wayar,sannan ta juya tana wucewa closet dinta don neman kayan da zata saka."

"Idan ta tuna abinda d'anta da ita sukayi mata,sai taji kanta ya cika da shawarwarin hanyoyin da"

"zata dauki mummunar fansa a kansu kafin ta tattare tabar rayuwarsu. Duk da cewa nashi me sauqi ne,don baiyi yunqurin taba mata kowa nata ba,saidai ya taba mata zuciyarta da munanan kalmomin da"

koda tayi nesa da rayuwarsa bata jin zata iya mancesu.

Har zuwa yanzu da take wannan tunanin ta rasa wanne kalar abu ya kamata ta yiwa maamah?.

Abu daya tayi ittifaqi akai shine......tabbas zata banbance mata tsakanin aya da tsakuwa. zata kuma

shayar da ita mafi girman mamaki.

"Tabbas inda tana da ra'ayin d'anta. lallai da zata mallakeshi a gaban idanunta ne,mallakar da"

babu boka babu malam mallaka ta ruwan sanyin da sai ta gwammace bata sanyata a shirmen

shirinta ba.

Har ta ciro kayan ta dawo ta shirya cikin Palazzo da blouse data kasance cif cif jikinta don bata

"buqatar kaya masu nauyi kiran bai daina shigowa ba,ta kammala ta feshe jikinta da turare . Scarf ta sanyawa kanta sannan ta taka a hankali tana isa inda wayar take sanda take dab da tsinkewa."

Stool taja ta zauna bayan ta daga kiran ta sakashi a handfree ta kuma ajiye saman mirror table din

tana tattara hankalinta akai.

"""Dawa nake magana?"" Abinda ya fara fita kenan daga bakin maamah da wani yanayi na zaquwa da son"

jin wayar a hannun wa take?. Idonta ta lumshe sannan ta bude

"""Gaggawar ta meye?,kina tunanin wayar huda zata kasance a hannun wani qato ne?,ko a hannun wata"

"sabanin halastacciyar 'yar uwarta data shirya sadaukar da tata rayuwar saboda tasu?"". Maganar ta kama"

"zuciyar maamah sosai,ta kuma saukar mata da matsananciyar fargabar data bata tabbacin KOMAI YA QARE saidai a sake sabon zubi da lale."

"""Naga alamar hakan......kin kuma yi qoqarin sadaukar da rayuwarki ma 'yan uwanki ni shaida ce,amma"

inaso kisan wani abu guda. kina wasa da baqin kumurcin maciji ne daya shirya dukka dafinsa da

"xummar harbi ga duk wanda yabi ta hanyarsa"" Wani dan murmushi ta sakarwa maamah din tana murza hannuwanta,har yanzu tana jin bata gama dawowa ainihin sabreen dinta ta asali ba. amma kuma da"

alama komai yana bisa hanyar saituwa

"""Shi wannan macijin idan har yayi sake halittar data fishi sanin kogon da yake kwana yake kuma"

tunqaho dashi.......tabbas akwai yiwuwar a cimmasa har inda yake. a kuma sanyashi ya yanke wannan

"kan dake dauke da dafin da kansa da kansa ba tare da yasan hakan ta faru ba. """

"""Ke dakata qaramar alhaki!"" Maamah ta furta bayan dukkan haqurinta ya gaza da yadda yarinyar dake"

qarqashin igiyar auren d'anta ke iya maida mata magana me zafi haka kanta tsaye. ba shayi ba

"fargaba,yarinyar da a haife dukka cikin 'ya'yanta ba sa'anta."

"""Shshshsh. "" Sabreen ta fada tana dora yatsanta akan lips tamkar maamah na zaune a gabanta."

"""Meye na saurin fusata haka? ina cewa abun baiyi zafi har haka ba?"" Ta furta da alamun murmushi"

cikin muryarta.

"""Yaro man kaza......yaro baisan wuta ba sai ya taka..."""

"""Your royal highness. har yanzu bansan meye dalilin wadannan zafafan kiraye kirayen ba da safennan""."

"Iya maqura a rainin hankali maamah tana jin sabreen tayi mata shi,ta dinga qoqarin tausa kanta da daidaita kanta kada yarinyar ta tunzurata furta abinda batayi niyya ba."

"""Yaro yaro ne.......sabreena kina da masaniyar cewa nice na tsugunna na haifi fuad?"" Dan"

murmusawa tayi kadan sannan tace

"""Haka naji labari!"""

"""Amma kina da yaqinin ni na daukoki ko kawoki cikin gidan na maidaki sunan matarsa?. idan naso"

"qasa da awa biyu rak! Zaki rasa wannan damar?"" . Qaramar dariya ta saki ma maamah din,ta gyara zamanta sosai tana kallon kanta a madubi. A yau hirar nishadi take bata a maimakon razani da take"

samu a kwanakin baya da suka shude.

"""Kina zaton kina da wani makami da zaki iya fiddani daga gidan yaron naki? kiyi haquri da abinda"

zance......amma ko shaidan a yanzu bai isa ya fiddani daga gidan yaron naki da kike tutiya ba. bana

son danki ko kadan bazan kuma taba sonshi ba......amma yadda kika sakoni cikin rayuwarku. kika

maidani matarsa da qarfin qwanji dana kudi to haka fitata daga gidansa da rayuwarku zata kasande

"bisa zabin kaina a kuma duk sanda nayi niyya......so kibi a hankali,bawai sonshi nake ba. infact ma"

"baiyimin ba. amma bazan fita daga rayuwarku ba har sai sanda nayi niyya"""

"""Qarya kike. baki isa ba!"""

"""Dama bance na isa ba......amma zan gwada saiki tayani tabbatarwa. """

"""Kina kirawa kanki ruwa!,zaki iya rasa rayuwarki ta dalilin haka fa!"""

"""Bari na fara raba naki d'an da rayuwarsa tukunna ki fara ganin kalar wannan baqin cikin kafin ki aiwatar"

a kaina. zan shayar dashi ruwan guba a ruwan shayinsa na yanzu a maimakon tsubbace

"tsubbacenki....."" Tana kaiwa nan ta kashe kiran tana ma kashe wayar gaba daya."

"Murmushi ta dinga yiwa kanta a madubi,hirar ta sanya mata nishadi sosai,ko ba komai ta dasa"

mata tsoro da fargici tabbas na mintunan data ambata.

Da gasken haka shine ya faru. Wani irin gumi ya fara tsatstsafowa maamah da wani irin kalar

tashin hankali. Zuwa yanzu bata da tabbas akan yarinyar. tana ji a jikinta zata iya aikata komai da tace

"din. Kasa zama tayi,jikinta yana rawa ta soma lalubar layin fu'ad tanason gargadarsa akan ya kaucewa komai da zai fito a yanzu daga hannun yarinyar."

"Kira kusan goma tayi masa a jere saidai ba wanda ya daga,abinda ya sake tsananta tashin"

"hankalinta kenan,ta dinga duban agogo tana qirga mitunan da yarinyar ta kwasa mata."

Daidai lokacin ma shi ya jima a office. Ayyukane da yawa a gabansa da suka hade masa saboda

jiya bai samu yin komai ba a office din yayi baqi da suka tsaidashi har zuwa dare.

Daga jiyan

Please Login or Register in order to submit comment