Reading DUNIYA TA COMPLETE BOOK 2 COMPLETE by Asma Baffa Chapter 11 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shigar fari kowannensu yayi,da wani irin tsarin shiga da sutura da zata bayyana alfarmar wanda suke aiki a qarqashinsa. Abdulgafar shugaban tawagar tsaronsa shi ya fara nufoshi a gaggauce cike da kuzari yana tarbarsa cikin girmamawa kaman yadda suka saba shi"

da mataimakinsa jordan

"""Good morning sir"" Ya fara gaidashi kafin muryoyinsu ya karade wajen suna gaidashi suma"

"""Morning hope you are fine?"""

"""Fine sir"" Suka hada baki wajen amsawa"

"""Good"" Ya maida musu yana gyada kanshi."

"""Jordan"" Fuad yayi kiransa"

"""Sir"" Ya amsa yana matsowa."

"""Where's abdulbasit?"""

"""Am here sir"" Wanda aka kira da abdulbasit ya furta yana matsowa cikin shigar wani uniform da yasha"

banban da nasu jordan

"""Have you finished?"" Kai ya gyada a girmame"

"""Yes sir. """

"""Okay,kada ka manta.....zan bar muku jordan jordan,ba shiga ba fita har sai na dawo ko na bada"

"umarnin hakan. Ko waye bazai shiga ba,ko waye kuma bazai fita ba hope i made it clear?"""

"""Yes sir"" Jordan din ya gyada kai,don shi ya fahimci inda aikin yasa gaba,zasu maimaita salon aikin da"

sukayi satittikan da suka wuce kenan.

"""Yi mana addu'a"" Ya fada a taqaice yana duban abdulra'uf wanda kusan duk sanda qaramin meeting irin"

haka ya kamasu shike da alhakin hakan.

"Cikin mintuna uku aka kammala kowa ya wuce motarsu,motocin suka jeru kamar kullum,security"

din dake kula da qofa ya wangale musu ita suka fice daya bayan daya.

"""Am on the way banason jira"" Abinda ya gayawa saddiq kenan da yayi kiransa sanda suke a cikin"

"motar,sai ya kashe wayar kawai ya maida aljihu. Titi ya zubawa ido yana fesar da iska daga bakinsa. Baya tunanin maamah zata saka a kasheshi saidai wani abu na daban,amma ita kuma fa?,may be ta tsallake gona da iri,wala'alla ta wice limit da iyakokinta,amma duka ita maamah bata gani ba?,why zata zabi mace me irin wadannan dabi'u da halayen ta kasance a tare dashi?. Tambayar da yaji ta sake quntata zuciyarsa,abinda kuma bayaso ya faru kenan don yau din yana buqatar freshness don gobe rana ce me"

muhimmanci a wajensa.

"*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*"

08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ

_ZAFAFABIYAR_

6B6O6O6K 2

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 25

25

"""Nayi zaton tare zaku tafi?"" Shine abinda anni tace dashi sanda yake zaune sosai gaban abba suna"

breakfast dashi. Kai ya girgiza

"""Ba daman hakan anni,idan munje ma zata dinga wuni ita daya ne saboda ba zama zanyi ba akwai"

"baqi da sauran shirin da zamuyi daga yau zuwa goben in sha Allah"" Kai ya jinjina"

"""To Allah yayi jagora. yasa a bude a sa'a"""

"""Allahumma ameen"" Suka kusa hada baki wajen amsawa shi da abban."

"""Amma ba za'a kai mata abokin zama ba?"" . Anni ta fada cikin salon nuna kulawa. Basarwa yayi don"

baison anni ta gane komai game da lamarin

"""Ba ita daya bace anni,banajin zata damu,akwai mutane a gidan"". Kai ta gyada"

"""To Allah ya tsare"""

"""Ameen ya rahman"" Ya sake amsa mata."

Duka duka mintuna arba'in suka qara suka fice a gidan shi da musaddiq zuwa airport inda private

jet dinsa ke jiran isowarsu.

A hankali hasken ranar dake ratsowa ta tsakanin labule ya soma qarawa dakin haske yana kuma

"tabbatar da bayyanar rana sosai ya wuce kai tsaye ya taddata har inda take kwance,wanda wannan shine abinda ya sanya idanunta budewa a hankali suka kuma sauka kai tsaye kan agogon dake manne a"

dakin.

"Sha biyu na rana saura minti biyar kacal shine abinda idanunta suka gani,abinda ya sanyata ware"

idanunta gaba daya tana kuma miqewa da dan sauri. Bayan Hannunta ta saka ta mutstsike idonta tana

"sake duban lokaci,sam batasan tayi bacci me nauyi haka ba,don ko wanka bata samu tayi ba ta koma ta"

kwanta bayan ta tabbatar ta gama duk abinda ya dace.

"Miqewa tayi tana miqa,tana jin yadda gajiya kebin duka sassan jikinta,can cikin zuciyarta kuma"

"tana raya lallai zuwa yanzu ya debi abincin yaci,tana sake jin wani tabbaci da qwarin gwiwar komawarta zuwa ga rayuwarsu ita da 'yan uwanta."

"Toilet ta wuce tayi wanka,ta fito ta shirya cikin doguwar rigar atamfarJulius gold data zauna mata"

daidai jikinta da wani irin dinki da bazai takuraka ba. Sai a sannan taji cikinta yana wani yamutsawa. a

"lokacin ta tuna lokacin data dauka rabonta da wani abu me suna abinci cikakke. Plate tummy dinta ta shafa,sai ta miqe a nutse tana nufar hanyar fita daga dakin."

Tun daga nesa idanunta nakan stairs din har tazo ta gotata tana fita falon farkon. Tadan shaqi iskar

"dake kadawa tsakanin hallway stairs din da parlor din,wani qamshi ne ke kai kawo na daban wanda bata"

"taba jin sassanyan qamshi irinsa ba,wani sashe daban na zuciyarta kuma tana jin kamar ta taba ji ko sanin irin qamshin."

"Xarcewa falo na biyu tayi,tunda kuma ta fito idanunta suna kan dining din. Gudun zuciyarta ya"

"qaru kadan,yayin da ta cika da fatan taras da komai ya tafi daidai."

"Bude komai tayi,daga kallon farko ta fahimci ba'a taba komai ba. daga nan din kuma dukka"

"gwiwoyinta na qafa da hannu sukayi wani irin sanyi,sai taji ta kasa tsaiwa,taja kujera daya ta zauna tana girgiza dispensers din taji ko yawan adadin tea din ya ragu?. Nan ma ba abinda ya sauya,yadda ta zubashi haka nauyin yake,sai ta saka hannuwanta guda biyu tana dafe kanta,daidai sanda idanunta suka"

sauka kan sticky notes din dake maqale a wajen iska tana dan kadata.

"Hannu daya ta saka ta ballota daga inda take liqen,ta sanya idanunta akan kwantaccen rubutun"

dake a tsare kamar wanda aka tafa a inji bawai hannune yayishi ba

_mission accomplished_ iya abinda takardar ta qunsa kenan. Jujjuyata ta shiga yi tanason fahimtar

"saqon dake rubuce a jiki amma ta gaza kaiwa ga nan,abu daya ne kawai ya tsaye mata a rai da baici din ba. A niyyarta ta koma daki ta zauna ta jira wai koda zai sauko yaci bisa rashin sanin ya dade dayin nisa cikin gajimare. Amma qaguwa dason taga yaci din ya hanata komawar,sai tayi zaune a parlor parlor din"

"tana saka kunne akan kowanne motsi na gidan,amma sam motsin da take iya ji din ba wani motsi bane"

"na azo a gani,don hatta da securities na gidan bawai suna kusa da ita bane bare ta jiyo motsin nasu da kyau."

Sha biyu daya daya da rabi biyu biyu da rabi ba wani batun motsin kowa da komai cikin

"gidan,zuwa lokacin ta fara sarewa da lallai bazaya sauko ba,don koda wasa bata kawo cewa wai baya cikin gidan ba. Koda zai sauko a yadda suka lissafa mata halinsa tayi imanin bazaici komai na daga breakfast din ba,wannan ya sanyata cikin mutuwar jiki ta tattare kwanukan tayi kitchen dasu ta ajjiye"

tana tunanin yadda zatayi da kayan abincin.

A makare ranar tayi sallar azahar. har ta idar da sallar tunaninta ya karkata ga me ya kamata

"tayi?,ta shaidawa maamah din ko ta barta?,kada sanar mata ya sanyata ta dauka cewa gazawa ce har ta nemi yin wani motsi akan qannenta."

"Wannan tunanin ya sanyata ta share,duk kuwa da cewa wani sashe na zuciyarta a matse yake"

"data gaya matan,amma ta danne da wani irin qarfin hali tana saka ran zai fito yaci na dare."

"Tana idar da sallar la'asar ta fada kitchen,ko a sannan ma tsaiwa tayi tana tunanin wanne irin"

"kalar abinci zatayi da zaija ra'ayinsa har haqarta ya cimma ruwa?. Sai data kusa qure tunaninta kaf sannan ta zabi abu daya,ya wuce zuwa store tana duba dukkanin abinda take da buqata."

Dab da magariba ta baro gaban dining din data cika da warmers masu dauke da abinci. Tana

"takawa zuwa hallway din tana satar kallon stairs din. Zuciyarta cike da mamakin wanne irin mutum ne shi haka?,wanne irin mugun baqin hali ne dashi da har zai debi wadannan wannin a qunshe a sama ba tare daya sauko ko anji motsinsa ba?"

"""Ko yana zuwa masallacin ma oho"" Ta furta a ranta a sarari tana jan tsaki gami da tabe baki,ta tura qofar"

"dakinta ta shiga tana addu'a yadda a daren nan data saka hope me yawa,ta zuba komai da yawan adadi Allah yasa a wannan daren komai ya ratsahi har fiye da yadda maamah din keso don ta samu"

tickets din matsawa daga rayuwarsu ita da 'yan uwanta.

"Cikin toilet dinta tayi wanka,takuma shirya cikin sassaqan cotton lite material me sauqi. Sallar"

"magariba tayi,sai taci gaba da zama a nan. A hankali yaran suka fado mata,sai taji tana kewarsu,tana so"

taji!muryarsu koda kuwa maamah din zata kafa mata wani sharadi na daban kafin ta barta ta

"gansu,wannan tunanin ya sanyata miqewa a nutse tana mamakin duka yau bata dauki wayarta bata kuma yi amfani da ita ba."

"Kai tsaye tasan inda ta aje wayar tata,can ta nufa,ta daga wajen da zummar dauka,saidai kuma"

"wayar tace daukeni inda kika ajiyeni. Mamaki kadan ya kamata,amma sai ta share tana tunanin qila ta"

"canza mata waje ne ta kuma manta inda ta ajjiyeta,don haka ta fara bincikawa guraren dake daura da nan ko a nan ta ajiye din."

"Guri hudu duka bataga wayar ba ba alamarta,ganin zata gajiyar da kanta saita ajiye wannan ta"

"koma laluben wayarta ta asali data barta a handbag din da suka dawo da ita jiya dake ajiye saman mudubin nata tunda ta ajiye jakar. Kaf ta lalube jakar sannan ta zazzageta,saidai babu wayarta babu alamarta a ciki. Mamaki yadan sanyata ja da baya,nan ma zuciyarta ta soma ayyana mata wataqila itama ya canza mata waje ne,don haka sai ta fara jaye jayen lockers tana bincike dakin. Wasa wasa har closet dinta ta duba babu wasu alama na akwai wayoyin. A hankali ta dawo tana zamewa ta zauna daga qasan"

carpet din da aka qawata gaban sofa bed din tana maida numfashi.

"""Ya akayi haka?,me yake faruwa?,dukka wayoyinta babu ko guda daya?"" Ji tayi sam ta kasa aminta ko ta"

"samu nutsuwa,sai kawai ta fadada bincikenta har zuwa kitchen dining area waiko ta barsu a can,saidai babu komai kamar dai yadda ta gani a dakin."

"A parlor din ta zame ta zauna,tana jin wani shakka da kokwanto na shigarta. Kota wacce fuska"

bataga waje ko wani sarari da wani zai samu daman shigowa gida irin wannan ba. me wasu irin

madaukakan katangu da kuma gwabza gwabzan security irin wadannan ballantana tayi tunanin wani ya hauro ya shigo musu. Da sauri ta zauna sosai tana qanqance idanunta sanda wani tunani ya fado

mata.

"""Idan har haka ne shine kenan ya dauke wayoyin?,yaushe?,garin yaya?,a ina kuma ya samu damar"

"aiwatar da hakan?"" Tambayoyin dake danqare a kanta kenan data dinga juyasu."

"Idanunta ta maida tana duban sashen da stairs dinsa suke,zuciyarta na bugawa kadan kadan,tana"

"jin kamar ta tashi ta haura ta sameshi a can,taji meye hujjarsa na daukar mata wayoyi,bayan hakan ba huruminta bane?."

Bata fahimci cewa gidan ba kowa ba. ita daya ke rayuwa a cikinsa duk girmansa ba sai da sha

"daya na dare ta gota a idanunta. Sai a sannan taji wani irin tsoro ya soma mamayarta sanda zuciyarta ke bata hasashen ita daya ce qwallin qwal a gidan. Wani irin karyewa zuciyarta tayi,tsoro yana sake shigarta sanda take qudundune cikin duvet dinta. Bata taba kwana ita daya ba koda cikin dakinsu ballantana a gidansu gaba daya ba. wanne irin azzalumi ne shi da zaya fita yabarta a gidan da yafi qarfin zaman"

mutum hudu ma yace ta kwana ta rayu ita kadai? ba wayar da zata kira wani ballanta taji

sassauci koda ta duba wayar girke dake parlor din da zummar ta sadata da security din da suke waje

"taji ko zata samu aron waya daga hannunsu cikin rashin sa'a ta samu an yanke sadarwarta,ba zata iya yin magana da kowa ba banda dakunan dake cikin gidan."

Kanta ta cusa cikin pillow din tana jin yadda bugun zuciyarta ya qara tsananta sanda karen dake

wani sashe daban na gidan ya tsananta haushinsa. Bata taba tunanin akwai halittar tsoro a qirjinta har haka ba sai yau.....ashe dukka jarumtar da take zaton tana da ita ba jarumta bace. ko tace ta tsaya ne

kadai ta bangaren saita maza daukan darasin rayuwa da sanin ciwon rasa wani abu da xukata suke

tsananin so da qauna.

Batasan ya akayi ba ta samu da qyar wani takurarren bacci yayi awon gaba da ita.

"*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*"

08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ

_ZAFAFABIYAR_

6B6O6O6K 2

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 26

26

"Kwana daya kwana biyu haka awanni suka dinga juyawa da ita cikin gidan,cikin wani irin"

"matsanancin shuru kewa da kuma kadaici. A hankali ta dinga jin wani matsanancin takura,ta yaya zata zauna irin haka ba waya ba gilmawar kowanne dan adam?,tv kuwa sam taqi ta kalleta bare ta gwada kunnata. Da farko ta dauka zata iya jurewa,amma sannu a hankali saita fahimci ashe mutum rahama ne a kusa da kai,koda kuwa ba wata mu'amala da zata hadaka dashi. Tayi dukka juriyar da zata iyayi sai taji haqurinta ya soma gazawa. Wani danqararren bacin rai ne yake cinta game dashi wanda qilan inda yabar mata wayar ma a wannan karon batajin akwai abinda zai mata shamaki daga kiransa ta zazzage masa abinda yake cikinta. Ta yaya ita din da ta kwashi shekara aqalla biyar zuwa shida,ba wata ranar banza da zata fito ta fadi bata fita ba yanzu kawai rana tsaka ta wayi gari da mummunan kulle irin wannan?. Ko"

"a baya batata ji a ranta akwai wani lokaci da zayazo a sanyawa qafafunta irin wannan sasarin ba,ba"

lissafin aure kwata kwata cikin kanta shi ya sanya bata kawo yiwuwar afkuwar hakan a kanta ba koda sau daya.

"Ranar data cika kwana na hudu,tun qarfe goma na safe taji takai maqurar da ba zata iya jurewa"

"ba. Sha daya da rabi daidai ta kammala shirinta cikin atamfa. Ta taka a hankali zuwa inda take da tabbacin ta ajiye kudinta data shigo dasu cikin gidan,ta bude locker din ta zura hannunta don debosu,don ta gama tsarawa kanta zata taka ta fita ta samu napep duk kuwa da cewa tasan area din kwata kwata yana da wahala kaga abun hawa na haya to amma ta gwammace tayi tattaki zuwa"

babban titinsu tayita jira cikin rana har ta samu abun hawan da zai kaita gida. Zuciyarta da tunaninta gaba daya yana kan taje ta binciki lafiyarsu huda. kowanne dare dasu take kwana dasu kuma take

"tashi,suna cikin aminci ko kuwa aah? da qyar ta iya jure wadannan kwanakin suka shude ba tare da"

tasan komai game dasu ba.

Ta dauka yadda ta dokanta ta fita ne idanunta suke mata gizo sanda ta hangi babu ko burbushin

"kudi a wajen,amma data bude sosai sai taga gaskiya take gani ba komai a ciki kamar yadda ta gani da"

farko.

Mamakinta ya ninku akan mamakinta na kwanaki hudun da suka shude. ta sulale tana sake

zama a saman stool din dake kusa da ita.

"""Wai wa yake da alhakin aikata haka?"" Ta sake tambayar kanta tana jin tantama akan tabbacin zargin"

farko da zuciyarta ta bata.

"Duk wani karsashi na fitar saita rasashi yaushe ya samu damar shigar mata daki?,dame dame"

"ya bincika mata?,me zaiyi da wayarta?,dame dame zai bibiya cikin wayar?. Wadannan tunanin su suka"

"sakata a gaba,ta kasa tuna komai ko abinda ya dace tayi,har sai da agogo ya alamta mata sha biyu dai dai na rana."

"Cikin qarfafawa kai gwiwa ta koma toilet ta sake wanke fuskarta,ta dawo ta wuce closet ta"

dauki handbag da shoe da zai dace da shigarta sannan ta soma barin dakin tana jefa atm dinta a jaka da zummar idan ta fita ta samu wani guri ta cire kudi daga account dinta.

Wannan ce ranar farko kuma karan farko data fito daga cikin gidan a yanayi irin wannan. Faffadar

haraba yalwatacciya me wani irin tsari me jan hankali. Kusan gurare da yawa an qawatashi da koriyar ciyawa a maimakon tiles marbles ko concrete da akafi yawan amfani dashi. Sai wasu irin fararen stone da aka zuba a wasu daga cikin hanyoyin da zaka taka ka wuce zuwa haraba ta biyu. Idanunta suna iya gane nata wasu qofofi da babu qofa a jikinsu face wani irin design da aka musu wanda batasan ainihin inda zasu sadaka dashi ba. Sosai harabar ta qawatar da wani irin yanayi da zakayi tsammanin ba cikin qasata nigeria kake ba. saidai wutar dake can qasan zuciyarta ta danne burgewar da wajen yayi

"mata,taci gaba da tafiya cikin confidence zuwa qofar gate din da take da tabbacin zata sadata da waje."

"Tsaye kawai tayi don bata fahimci ta inda zata ratsa ta wuce ba,sam qofar ba irin qofofin data"

"saba gani bane. Gajiya tayi da tsaiwar ta kuma gaji da kallonta da tunanin ta inda zata fita din,don haka ta saka hannu ta soma knocking da tunanin zasu iya jinta."

"Tun tana knocking din a hankali har ta fahimci ba kowa ke jinta ba,ta qara dada qarfinsa saidai a"

"banza don ba wani motsi da taji da zai bara hope din wani na kusa zaiji ya kuma budeta,wannan ya qara hasala mata zuciya,ko a kurkuku take bangaren muggan laifin kisa ko fashi da makami iya horon da za'ayi mata kenan,don haka ta sake maida kai wajen buga qofar da kyau ba tare da tunanin cewa babu me"

jinta ba.

A hankali wani sashe kadan daga saman qofar ya zuge kanshi da kanshi. Fuskar jordan ta bayyana

wannan karon sanye cikin uniform din daya zama kayan sawa ga duk wani ne aikin tsaro dake cikin gidan.

"""Good afternoon maa"". Ya furta da wannan matsananciyar girmamawar da yake mata wadda ba abinda"

take sawa zuciyarta sai wani irin qarin takaicinsa. Fuskar jordan fuskace da ba zata manta da ita ba ko kadan

"""Open the door"" Ta fada adan fusace tana kallonsa,tana jin kamar ta miqa hannu ta zabga masa mari."

Cikin rusunawa da girmamawa kaman yadda ya saba ya fara mata magana da hausa

"""Am sorry maa. boss bai bada umarni ba,idan ba damuwa ko zaki kirashi kuyi magana tukunna?""."

"Idanunta ta janye kawai daga kan jordan din bacin ranta yana ninkuwa,abinda yayi mata a wancan lokacin shi ya maimaita mata kenan?,waishin me yake daukan kansa ne shi?,don yana da kudi?,yana da dukiya shi yasa yake tunanin zaiyi duk abinda yaga dama?,zai taka wanda takeso a duk sanda yaso?,zai wulaqanta mutane sannan kuma ya kwana lafiya?. Ta ina zata nemeshi bayan babu ko waya guda daya a tare da ita?,ta ina zasuyi magana bayan ya yanke sadarwar gidan gaba daya?,koda ma komai yana nan a"

muhallinsa ta rantse ba zata kirashi ba.

"""Kawu ne ya jawo miki"" Amsar data dawo cikin kanta kenan. Idan ma kira ne shine mutumin daya"

"kamata ace ta kira,har yanzu tana ji a jikinta kan ta inda ake hawa ta nan ake sauka,kawun shine ya bada ita ya kuma saida mutuncinta. don ta nata bangaren ba'a kan muhammad fu'ad bane farau"

shallakewa maza masu kudi da kuma hadari don haka don shi kadai bazai zame mata matsala ba inda

"anbi karatun yadda ta saba. Har taji kamar ta sare,sai taga idan ta bari hakan ta kasance yasha da ita,don haka ta matsa bakin gate din"

"""Can you barrow me your phone?"". Ta tambayeshi tana kallonsa. Jinin jikinsa yasha,yadan kalleta yana"

kokwanto. Yaya zata rasa waya tana a gida irin wannan?.

"""Afwan madam amma me zakiyi da waya?"" Idanunta da suke mata zafi ta lumshe"

"""Zan kira uncle dina ne. i lost my phone"". Dan jim yayi kadan,sai kuma ya amsa mata yana sanya hannu"

a aljihu ya fiddo wayar ya miqa mata bayan ya sake bude glass din ya qara girma.

Yadda yake bata wayar kamar tana a kurkuku ya sake matsa zuciyarta ya qara yawan adadin

bacin ran da take ciki.

Wani sashe daban na gidan ta koma ta zauna saman wasu rukunin kujeru da aka qawata cikin

wata rumfar bamboo dake bada iska me kyau da sanyi. Da qyar ta iya hada lambobin kawun don ba haddacewa ta taba zama tayi ba saidai kawai kira na yau da gobe daya bata daman kallonsu daya

bayan daya suka kuma zauna a kanta.

Bugu biyu kawun ya daga da cikakkiyar sallamar data kusa sanyata jan tsaki

"""Kamar gaske"" Ta fadi a ranta tana amsa sallamar tasa a daqile."

"""Wa nake ji kamar sabreena?"" Ya fadi da annashuwa cikin muryarsa,zuciyars na bashi tabbacin lallai"

"zama ya soma miqawa,wataqila wani alkhairinma ta bugo tayi masa"

"""Nice"" Ta amsashi a hankali"

"""Kai madalla Allah ma sha Allah,amma fa naji dadin kiranki kin kyauta diyar albarka,dama inata zube"

"kunne naji kiran naki """

"""Eh gashi na kira......na kiraka ne kuma na gaya maka. wannan mutumin daka saida masa dukka 'yan"

"cina da mutuncina ya kamata ka kirashi ka bashi labarin haihuwata akayi bawai a baiwa aka ribatoni ba. ka fada masa abinda ke tsakaninka dashi daban da abinda ke tsakanina dashi,bazan iya daukan"

dukka wannan izzar tasa da izgilancinsa ba. ina da 'yance kafin zuwansa zan kuma ci gaba da

kasancewa me 'yanci a rayuwata. don har yanzu babu d'a namijin da zai dinga ruling dina yadda yaga

"dama ba tare da naso haka ta kasance ba""."

"""Kai jama'a. waike wacce irin yarinya ce ne me butulci?,Allah yayi miki wannan babban gamo da katar"

"din da miliyoyin mata ke fatan samu amma ki zauna kina shashanci?,yo Allah na tuba idan ranka ya dade baiyi mulki da izza ba meye zaiyi?,kudi ne dashi fa?,arziqi garai irin arziqin da gwamnati ma wani lokaci biyayya takeyi maka.......ina gani malam rufa'i?,to wallahi bada ni ba. hasalima ni bamu taba waya"

"dashi ba,dan uwansa kuwa farouqu bazan dauki sirrin gidan ma'aurata nakai masa ba Allah bazai la'anceni ba,in zaki nutsu kiyi biyayya ki tara abinda kika tara karki mana buqulu to,amma wannan jan kunnen bada ni ba. wane mutum inji mutuwa,Allah baki da hankali sabreena"" Har ya qare"

"maganganun idanunta suna kulle saboda yadda yake mata magan da qarfi da hayaniya,uwa uba ita"

bataga dalilin dogon jawabinsa ba.

"""Kawu"" Ta kirashi a nutse."

"""Yaushe su huda suka zama cikin kayan gado da har za'ayi rabonsu zuwa ga wata mace da basu hada"

"alaqar komai dasu ba?""."

"""Wata mace?,Allah na yarda dai da gaske akwai sauran qarancin nunar hankali a tare dake. kina"

"magana akan hajiya mariyah surukarki?,mutuniyar kirki me yawan alkhairi da son zumunci?,yo wannan kika fadi mummunar kalma a kanta aisai Allah ya tsine miki albarka. ni baza'a zageta dani ba,sai"

"anjima sabreena"" Kafin ta ankara ya yanke wayar,abinda ya sanyata a razani ta maida dubanta kan"

fuskar wayar tana kallonta cikin mamaki.

A wannan karon duk yadda taso tare kukan sai da hawaye ya sauko mata bayan ta maida wayar

wa Jordan. Sai kawai ta soma tattaki da sassarfa tana komawa ciki cikin yankewar kowanne tsammani.

A falo na biyu ta zube don ta gaza isa bedroom din. Wasu irin hawaye masu zafi suka fara gangaro

"mata. Me yasa rayuwa zata juye mata da zazzafan yanayi irin wannan dare daya?,yanayin da ko s mafarki bata taba tunanin zaya risketa ba?. Ya cika mugu na gaske,ya rufe mata kowacce qofa ko hanya da zata samu sassauci me ya rage ita kuwa tsakaninta dashi banda itama tayi duk yadda zatayi tayi"

"nesa dashi?,me ya rage banda ta aiwatar da nufin maamah a kansa don ya gwada shiga halin mulkin"

mallakawa d'an adam yaji idan hakan da dadi?.

"*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*"

08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ

_ZAFAFABIYAR_

6B6O6O6K 2

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 27

27

"&&Madaidaiciyar haraba ce wadda yanayinta yayi kama da gine ginen turawa ainun,irin gine ginen qasashen qetare,saidai kuma ba harabar kadai ba. gidan dama sauran gidajen dake wajen dama"

unguwar gaba daya ba zaka dauka kana cikin abujar nigeria bane ba.

"Tamkar shi daya ne cikin gidan saboda rashin hayaniyar jama'a da kuma motsi,saidai a yawancin"

"lokuta yakan zabi yanayi irin wannan don bawa zuciyarsa hutu da kwanyarsa. Bayan doguwar gwagwarmayar tabbatuwar buduwar kamfaninsa ap lagos kwanaki uku da suka wuce,sai ya zabi tsaiwa a abujan don ya sanya ido game da gudanarwar kamfanin koda na sati guda ne kafin ya koma bakin nasa"

ayyukan da suma a yanzu suke buqatar hankalinsa.

Farin boxer ne a jikinsa da wata cotton shirt me gajeran hannu wanda ta bayyana ginuwar

"muscles na jikinsa,zubi da qirar qarfin da yake da ita."

Tataccen natural ruwan

Please Login or Register in order to submit comment