Reading DUNIYA TA COMPLETE BOOK 2 COMPLETE by Asma Baffa Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowanne shiri da zai nesantata da auren. duk da

tarin bayanan da kawu yayi mata na ba inda zata shiga a duniya ta iya tserewa me jadda. saidai ta

dauki.maganar tasa a wasan yara ne.

Koshi waye. ko kuma da meye yake taqama tayi imanin saidai idan bata sakashi cikin plan dinta

ba.....

"""Adda baki sha bafa"" Muryar huda da ke zaune gefanta ta fada,wadda kusan kowanne shirye shirye da"

ita ake aiwatar dashi.

"Maida idanunta tayi ta sake lumshewa muryar huda na dawo mata,ta fahimci dari bisa dari ba"

"wani me adawa da auren,kusan kai tsaye ma zata iya cewa dukkaninsu maraba suke da abun,duba da irin walwalar da suke ciki gaba dayansu."

"""Ki nutsu sabreen.......ki nutsu.....karkiyi abinda zargi zai dawo kanki karkiyi abinda su mamma bahijja"

"xasu kasa karbarki da wankeki daga laifi duk sanda kika kammala da wancan game din kika dawo musu"" Wata murya daga can qasan zuciyarta ta soma gaya mata."

Idanunta ta bude ta aza kan huda har sai da hudan tadan sha jinin jikinta. Sunyi mata farin

"sani,daga kallonta kawai suna iya karantar umarni da kuma hani,amma ga sabanin tunaninta sai tayi mata nuni data miqo mata abun. A hanzarce kuwa ta ajiye littafin hannunta ta miqe ta dauko ta miqa"

mata.

"Tsure abun tayi da kallo wanda batasan da meye da meye aka hadasu ba,to amma koda meye"

"aka hada din,ta tabbatar mamma tana asarar kudinta ne kawai,don haka ta kafa kai ta soma kurba a hankali gardin abun yana ratsa kunnenta duk kuwa da bakinta ba taste,haka zuciyarta a quntace take."

"*******Doguwar tafiya,hawa da kuma sauka,kutsawa cikin surquqi dukka ba damuwar maamah bane."

"Fatanta da burinta ta dangana ga mutumin data miqawa al'amarinta gaba daya,ta kuma sanya hope me yawa a kansa."

A yanayin data ganshi a yau ya sake saka mata tabbacin samun cikakkiyar nasara. A hargitse yake

yau din cikin zafin ayyukan mutanen da suka zabi ya zame musu abun dogaro kuma hanyar samun duniyarsu ba tare da damuwa da meye makomarsu ta lahira ba?.

"Bayan shafe shafensa da buge bugensa,ta hautsina dukkanin kayan aikinsa da yayi,ya kalleta da"

jajayen idanunsa qananun ainun dake cike da rashin tauhidi da kuma zallar sabo fajirci da fasiqanci. Dubane daya sake tabbatar mata ba rahama ko tausayi ko misqala zarratin a cikin ransa

"""Akwai tarin sarqaqiya......akwai tarin qalubale. akwai al'amura da yawa da zasu iya wanzuwa ko su"

biyo baya........ita din taurarinta nada tsananin haske da wahalar kutsa kai a cikinsu. tana da wahalar

sha'ani na gaske......tabata kuma abune da zai iya zuwa da nasara da akasin haka. kaman zan iya cewa

KINYI KUSKUREN ZABINTA. to amma kuma ba wani tauraro da zai iya shiga nasa taurarin sai

natan......tamkar itace mahadi masarrafi kuma barin nasa taurarin taurarinta sune abokan tafiyar

nasa.........sunyi matuqar dacewa da juna. wanda hakan shine zai bada damar tafiyar umarninmu da

haninmu a kansa......kusan komai nasu suna matuqar kamanceceniya dana juna. ITACE TA DACE DA

CIKAR BURINKI MUDDIN AKA SAMI GUSHEWAR AKASIN DA NAKE HANGOWA. saidai na gaya

miki.....kamar akwai alamun KUSKURE DA NADAMA.......akwai babban waqeee'a. juyewar komai da

"lullubewar mayanin duhu bisa faifan qaddara""."

Tunda ya fara maganar gabanta ke wani irin faduwa. Hajja da suka gama sauraron bayanan a

tare ta dora hannunta a kafadar maamah da zummar yin magana da ita da neman qarin bayani saidai

da sauri maamah ta zame hannunta daga kafadarta......tayi nisan da batajin zataji kira. zuwa yanzu

"nasara take nema ta kowacce fuska,ta kuma kowanne yanayi bata buqatar tsaiko fashin baqi ko qarin"

bayani a yayin da take dab da cimma nasararta. bayan kuma a baya ya bata tabbacin ta wannan

hanyar ce kawai nasara zatazo mata babu ko kwanto

"""Amma dai akwai hasken nasara ko dan kadanne?"". Kansa dake cike da wasu irin gasussuka ya jinjina ba"

tare daya koda dubi idanunta ba. Cikin samun qwarin gwiwa tace

"""Nasara duk nasara ce komai qanqantarta,baa canza mata suna daga nasarar dai,hakanan daga qaramar"

nasara ake cimma babba......ayimin komai da ake da iko a kansa. a sakamin yarinyar a tafin hannuna

kafin samuwar fu'ad.......itace tsanin ita zan fara mallaka don ta zama hannuna tsani na kuma idona

"zuwa ga wancan babban burin nawa!"". Ta fadi muryarta na raunana tana tsoron jin akasin abinda zuciyarta ke muradi."

"""An gama!"" Ya fada da wata kakkaurar murya maras dadin amo. Saita sauke ajiyar zuciya tana yi relax"

ganin yadda ya soma maida hankali akan aikinta.

"Boyayyar ajiyar zuciya hajja itama ta saki. Ba haka taso lamarin ya kasance ba,taso tana kuma so"

taji cikakken fashin baqi da qarin bayani daga bakinsa.

Wacce irin sarqaqiya ce?

Wanne irin duhu ne?.

Wani irin baqin lullubin mayafi ne haka?.

Wacce nadama ce zata biyo baya?.

Meye kuskure a cikin zabin nata?.

Dukka wadannan amsoshin tana buqatar saninsu ne don tasan daga ina zata dasa nata harsashin?.

"Daga ina tata TAFIYAR zata fara?. Ta wacce fuska zata saita tata DUNIYAR?,ta aza duniyar SHALELENTA?."

"Bata data cewa ko wani motsi,ta sani cikin aikinsa ba shishshigi,ke me rakiya kuma baki data"

cewa......hakanan baki da damar yin komayya kiyi tambaya akan aikin daba naki ba. wannan kadai ya

"kashe mata jiki,ta zurfafa a cikin saqe saqe har ya kammala aikin maamah,ya kuma shaida mata su wuce zasu tadda komai cikin motarsu da qarin bayani."

Bata sake gasgatawa da imani da zancansa ba saida suka samu komai a mota a ajjiye kaman

"yadda yace. Ta sake tsinkewa da lamarin aikinsa,inda da wani suka je wajen ko akwai gilmawar dan"

adam ta wajen sai tace an ajiye musu ne.

"""Kings abun mamaki hajja?,kullum mutumin nan sake dauren kai lamarinsa yakeyi"" Ta fada tana juya"

kayan tsatsubar dake hannunta.

"""Kina zaton gurin qaramin mutum na kawoki amma mariya?,me yasa kikaqi tambayarsa dukka"

"qalubale da matsalolin daya hango miki?"" Hajja tayi tambayar da tafi tsaya mata a rai."

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ

5Ø!Þ5Ø"Þ5Ø'Þ5Ø"Þ5Ø'Þ5Ø"Þ5Ø#Þ5Ø*Þ5Ø:Þ5Ø"Þ5Ø3Þ

6B6O6O6K 2

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 4

A nutse ta daga kai tana kallon hajjan

"""Na tsani matsala ko akasi hajja......musamman a wannan matsayin da nake kai a yanzu me zanyi da"

"ita ballantana na buqaci sharhi a kanta?,bana buqatar dukkan wani jawabi da zai alamta min FADUWA ko MATSALA akan cikar burina a yanzu.......inaji a jikina da raina cewa. zan iya kauda kowacce matsala"

da zata tunkaro muddin na samu nasarar tsallake wannan matakin da muke kai a yanzu da

"qwanjina....da kuma fikirata"". Jinjina kai kawai hajja keyi tanason taji wanne tanadi da tsari tayi akan"

"hakan?,amma kuma bataso ta zafafa tambaya akai har maamah ta zargi wani abun,saita tattarewa ranta komai tana jiran lokaci domin kuwa ta san cewa qwace goruba a hannun kuturu ba abu bane me"

wahala ba.

********Abune sananne a wajen kowa. sharar biki da yawan maganarsa a bakunan mutanen mu ya

ta'allaqa da suna da sharar iyali dangi ko zuri'ar da za'a gudanar da bikin diyoyinsu. Hakan itace ta kasance akan MUHAMMAD FU'AD JADDA mamallakin JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES.

"Daga qishin qishin zuwa samun tabbacin tasowar maganar aurensa,wanda tabbacin ya samu ne"

daga yadda farouq musaddiq saddiq da uban family alhaji hamza kibiya sukewa bikin shiri na gasken gaske.

"Daga abokansu saddiq maganan ya fara yaduwa,kafin kace meye wannan labarin ya fara kewaye"

kowacce kafar sada zumunta.

Duk da a qurataccen lokaci labarin ya fasu. to amma labari ne me dumin gaske daya bawa

mutane da dama mamaki.......ya girgiza zukata da zuciyoyin 'yammata da dama. musamman yaran

masu kudin da suke kwana su tashi da mutuwar sonshi suke kuma da qaqqarfan hope din samun

shiga a wajensa kodon matsayi da mahaifansu ke dashi......walau na dukiya ko na siyasa. ko kuma

kasancewarsu abokan kasuwancin gold da diamond dinsa.

A gefe guda kuma wajen 'yammatan da suka hada duk wata sura kyau da isa. wadanda sukasan

basu da wani tsanin isa zuwa gareshi saidai sunyi mutuwar murus akan mayatacciyar

soyayyarsa......abun ya sake bude musu topic of discussion qarqashin kowanne posting na labarin

"bikin dake dauke da qawataccen IV na bikinsa da aka qawata da zallar ruwan gold,yake kuma wani irin sheqi da daukan idanun da zai gaya maka bikin ba na yaro bane. tarin cincirindon comments ne da"

mabanbantan kalamai masu yawan gaske. Da yawansu suna fatan inama zasu samu hotunan

"amaryar?,ina free wedding pics da sauransu,saidai ko daya basu samu ba face kunji kunji da shaidar zur daga wasu daga cikin commentators na qarya,sai luguden labba da tsabar kyan IV din bikin da aka"

kashesu dashi sai videos na lefen da aka samu wadda ta qwarewa gulma da munafurci ta ba bajesu

dashi abinda ya sake hura wutar tattaunawar.

Sam wadanda ake abin dominsu basusan anayi bama. daga angon har amaryar ba ma'abota

social media bane........idan kaga ta qulla abota da waya to akwai sabon mission a gabanta. data

"gama ta ajiye wayar dama layukan da tayi aikin dasu,wani ta karya ta zubar. wani kuma sai bayan"

wani zamanin yayin da oga fu'ad sam sam ayyukansa basa ma bashi damar tunawa da wani

media. koda WhatsApp dinsa idan ka ganshi akai wani abune ya kama da lallai yake da buqatar hawa

yayi a can din.

Koda yana free ma ko yana annual leave dinsa. yanayin tsaro da dukka rayuwarsa ke buqata

ya sanya ya sake nesa nesa da duk wani harkoki irin wadannan don komai nasa a matakin rayuwar

daya taka yanzu yana buqatar privacy.

A daren da ya rage ayyuka sosai abu daya tak ya rage masa ya kammala yabar qasar. Yana

"zaune saman bean bag chair,daga gefansa ruwan wolfberry ne me dumi yake sipping yana kuma chewing berries din idan sun shigo bakinsa."

Haka kawai yayi shaawar shiga yaga me duniya ke ciki don duka schedule dinsa na yau ya

"kammalasu. Da wani personal account yake amfani,wanda bai taba ba baya kuma wallafa komai a ciki bare ka iya gano waye mamallakinsa. Akwai account na company dinsa kala daban daban dake qarqashin kulawar ma'aikatansu dake kula da wannan fannin,so amma ko su baya bi ta kansu tunda yayi"

imanin zasuyi handling dinsa ya dace da abubuwan da ya kamata ace an sanya din.

"""Ya salam"" Ya fada yana miqewa daga relaxing din da yayi cikin bean bag din yana kallon yadda hotunan"

"katinan daurin auren ke shawagi cikin media. Da farko ma bai fahimta ba,saidai daga bisani da suka yita jeho masa ire iren posting din kamar sunayi da gayya sunsan shike da alhakin abun har sai da"

hankalinsa yakai. Shuru yayi yana sauka gami da furzar da iska daga bakinsa. Yasan aikin mutum uku ne

"wannan farouq saddiq da musaddiq,sai amna ta hudunsu."

"Kamar jira akeyi ya gani kira ya shigo masa,a nutse ya jawo yana dubawa. farouq ne,kusan tun"

"randa yace ya zaba kaya bai sake barin wayarsa yadda za'a sameshi ba sai yau,sai ya katse kiran,ya koma ya laluboshi video call."

"Ta signal ya shiga,amintaccen app din da mafi yawan manyan mutane ke ta'ammali dashi saboda"

samun cikakken tsaro.

"Shigan farko ya daga,fuskarsa ta fito tarwai kaman yana gabansa."

"""Hey "" Ya fada qasa qasa yana duban fu'ad"

"""Don't tell me baka ma taso ba?"" Yayi masa tambayar yana tsuke fuska tare da bata fara'ar fuskarsa"

"""Zuwa ina kuma dude? bakaga abinda kuka jawo ba?,baka ga abinda ke trending ba?"" Ya masa"

tambayar shima hana dan bata fuska kadan.

Kai farouq ya jujjuya hagu da dama yana yarfar da hannu

"""Am asking you seriously fa where are you?"""

"""Ask media users......farouq,you take it very serious fa. wannan fa auren ba wani abu bane da za'a"

damu dashi har haka ba.....ba wani babban abu bane da zai zama ya yada ko ina ba. it's just a

"temporary """

"""Kai kasan wannan......mu bamu sanshi ba......in fact ma idan ka matsa da yawa zan fiddo komai just"

"ka dauko hanya gobe kawai if not,bazan gaya maka abinda zai faru ba"". Datse kiran farouq din"

"yayi,abinda ya sanya fu'ad sakin murmushi ba tare daya motsa daga inda yake ba. Da alama farouq din a qufule yake dashi sosai,shi yasa yayi masa abinda yafi tsana kashe masa kira. Ya kasa fahimtarsa ne,shi sam baiga me yasa zai damu da abinda baida wani muhimmanci ba,baiga abun daurawa kai hidima har haka ba. already sun gama diban kudin komai da komai uban da 'yar,daurin aure kuwa ko aike yayi"

"cikin ma'aikatansa za'a daurashi,gidan da zai ajeta ko ba yanzun ba zai iya bada umarnin tarewarta idan"

"ya gama sabgogin gabanshi,for god sake zai bata lokacinsa ne da ranshi akai?."

Bai sake bi takan farouq ba don yasan fushinsu da juna ba wani abu bane me dorewa ba. Saidai

"yadda farouq din yace idan bai dawo ba washegari baisan me zaya faru ba,yana tsaka da ayyukansa da yake sanya ran sune na qarshe kiran anni ya sameshi."

"Abdul_haleem daya daya cikin guard dinsa ya miqawa folder din hannunsa,ya koma gefan table"

din da yake ajiyar takardun ya zauna yana daga wayar.

Cikin nutsuwar nan tata da ko yaushe take qara mata kima da kwarjini tayi masa sallama cikin

"tsantsar kulawa da qauna irin ta uwa da d'a. Kaman ko yaushe shima,cikin tausasawa da matuqar bada kima ya amsa mata sallamar."

"""Barka da warhaka anni anni ayyuka sun sani gaba,ayimin afuwa"" Yayi riga malam masallaci wajen"

fada. Murmushi ta saki cikin nutsuwa tace

"""Anyi maka Muhammadu ya aikin?,fatan komai yana tafiya daidai?"""

"""Alhamdulillah anni komai alhamdulillah,saidai muna buqatar qarin addu'a"" Ya furta maganar jerin"

"saqonnin daya gani shekaran jiya suna fado masa. Ba'a raina kaidin maqiyi,kuma abokin adawa ko wanda bai sonka ba'a rainashi komai qanqantarsa."

"""Kullum a cikinta muke,ba abinda zai faru in sha Allah sai alkhairi amma nayi zaton samun baquncinka"

a yau......tuntuni mun sauka a sabon gida.....duka duka jibi ne daurin auren nan ga baqi a gidan kowa

"kai yake tambaya"". Hannu ya sanya ya shafi sumarsa,har yanzu ya gaza gano abinda yasa suka daukaki sabgar nan haka. har wani taron gayyar jama'a anni itama tayi kenan bayan ta maamah?."

"""Jibi din zan shigo in sha Allah anni"""

"""Anni jibi yayi kusa.....gobe ko yau ya kamata. private jet ne,baida buqatar samun wani issue ko ya"

"kawo excuse"" Ya jiyo muryar farouq daga gefe tana shigo masa."

"Murmushi ya saki da sautinsa ya gaza boyuwa,wato zuwa yayi ya hadashi da anni kenan?."

"""Bani shi anni please"" Ya fada da sauri,bata ce komai ba ta miqawa farouq wayar tana murmushi. Drama"

"din fu'ad da farouq babu me shiga,idanma kace zaka shiga din kunya zakaji."

"""Definitely idan ka samu dama saika shiga tsakanina da anni ka canza hali wallahi"" Ya fada yana dan"

daure murya.

"""Kome zaka fada ka fada. ina nan ina jiranka"""

"""Kaci gaba da jira.....at last idan bakayi wasa ba kai zan daurawa auren nan da yarinyar. tunda naga ka"

"damu da lamarin ta da yawa"" Daga haka ya katse kiran yana dariya ciki ciki. Yasan ya kunno farouq din,don ba wanda zai rabashi da fannah dinsa sai Allah."

"Haka kawai ya samu kansa dason cika alqawarin daya yiwa anni,ya maida hankalinsa qwarai kan"

qoqarin kammala abubuwan da suke gabansa don ya samu isa nigeria kaman yadda ya alqawarta.

Hannu anni ta miqa tana karbar wayarta daga wajen farouq dake mita. Duk da mitar da yakeyi

din saidai ya kiyaye dukkan wani abu da zai saka anni ta fahimci akwai lauje cikin nadi boyayyen

manufa da qudurin data hana fu'ad damuwa da dukkan wani lamari daya shafi auren.

"""Anni kina sauqaqa masa da yawa........hatta da friends dinmu gobe zasu iso amma ace shi yana can"

"neman kudi?.....har yau ya kasa sanin kalmar hutu a rayuwarsa? ta yaya zai kula da diyar mutane?"""

"Murmushi anni ta sake,yadda farouq din keta mita ke bata dariya"

"""Banda abinka farouq.....na tabbatar ya fika damuwan ya iso fa. sannan tunda kaga haka din ba yadda"

"zai taho dinne,da yau gobe da jibin dukka na Allah ne,kuma kaman yau ne. ina da saqo ma da"

"nakeson ka miqawa d'iyata "" Anni ta fada tana yunqurawa ta miqe."

"""Ina amna ta shiga ne?"" Farouq ya tambayi anni dake qoqarin bude wani side na wata qawatacciyar"

cupboard ta daban dake cikin aljannar duniyar bedroom din nata.

"""Tana bangaren beauty spa"""

5Ø?Þ5ØjÞ5ØcÞ5Ø^Þ5ØnÞ5ØVÞ 5ØiÞ5ØVÞ 5ØcÞ5ØVÞ 5Ø`Þ5ØjÞ5ØYÞ5Ø^Þ 5ØcÞ5ØZÞ.

08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ

5Ø!Þ5Ø"Þ5Ø'Þ5Ø"Þ5Ø'Þ5Ø"Þ5Ø#Þ5Ø*Þ5Ø:Þ5Ø"Þ5Ø3Þ

6B6O6O6K 2

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 5

"""Okay"" Ya fadi kawai a taqaice,don ita kanta yadda yaga alamun ta dauki bikin kamar yafi yadda kowa a"

gidan ya dauka.

"******A duk bugawar daqiqa,wucewar kowacce saa da kuma bugawar agogo sake kusantar da ita kawai"

"yakeyi zuwa ga duniyar mamakin abinda ke shirin faruwa da ita. Sannu sannu taga gidan ya fara cika da baqin fuskokin da da yawansu ta manta da kasancewarsu ahalinta. Wasunsu tun ana taron alhinin rasa mahaifinsu mamallakin gidan gaba daya,yau sai gasu da daya da daya suna bullowa da sunan halarta"

taron bikin da tayi imanin ba wani bane ya gayyacesu.

"Dondai mamma bahijja ba wata mu'amala ke tsakaninsu ba,hasalima ba sanin kaso casa'in da"

"tara a cikinsu tayi ba. Ba sanin jiya ko yau ta yiwa duniya ba,ta sani kusan mafi rinjaye a cikinsu sanin"

"waye yake shirin aurenta shi ya kawosu bikin,bikin da babu wani abu guda daya da take da masaniyar ita ko mamma bahijja ta tsarayi,koda an tsara din ta tabbatar aikin kawu rufa'i ne,wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye,komai yana gaba gaba a kai,hakanan ya saki kudi anata hidima cikin gidan."

Yanayin yadda ya saki bakin aljihunsa ya dasawa sabreen qaqqarfan yaqinin kudade ya samu ko ya

"karba daga wajen mutanen daya sadaukarwa da ita. Bata cewa da kowa komai ba,amma tana karance da kowanne motsi na cikin gidan. Yadda bibo tayi uwa tayi makarbiya,a rana takan hauro saman da zummar dubasu har babu adadi,saman da a baya sai da akasha dambarwa da ita kafin ta daga qafan kasancewarta a can,sai da sukayi baram baram da kawun,ya wanke mata zanin mutuncinta tas tare da buga mata gori nau'i daban daban,yau din sai gata tana zarya tsakanin hidimar da ba tata ba bata kuma"

shafeta ba.

Sanye take da wata simple dubai gown me rangeamen nauyi da sassauqan ado me daukan

"hankali,cotton ce me yankakken hannu da ya tsaya iya damtsenta,sai siririn mayafinta data maidashi tamkar dankwali ta yane sassalkan gashinta dake zube gadon bayanta ba tare data daureshi da komai ba. Cikin jikinta sam babu qwari,tana jin kamar iska zata iya dibanta ta kayas da ita,hakan kuwa ta sani baya rasa nasaba da qauracewa abinci da tayi akan yadda ta saba cin abinci,duk da dama can ita din ba"

ma'abociyar cin abincin bace.

"Ta samu huda ta dafa shinkafa da wake,sai miya da soyayyen kifi daban. Goshinta ta dafe tana"

"zama,kanta tun jiya yake sara mata bayan data jiyo mamma bahijja na magana da qannen mahaifiyarta"

"da kuma kawu Abdul Hakeem,tana shaida masa jibi gobe kenan shine ranar daurin aurenta bayan sallar juma'a."

"""A zuba miki adda?"" Huda ta tambayeta cike da fatan ta amsa cewa zataci din. Hannuwan huda da"

sukasha lalle tabi da kallo. Ko nata hannuwan farare suke sidik da zara zaran yatsunta dake dauke da dan

"baqin lalle dan kadan saman farcenta,ragowar lallen data yiwa adon yatsunta wata biyu baya da suka shude."

"""Zuba......amma kada kisa miya. mai zaki saka da dan maggi kadan"" Ta yiwa huda bayani a taqaice tana"

"zare idanunta daga sashen da suke. Sauka idonta yayi kan wayarta dake ajiye wadda a qalla ta kusa kwana biyu a wajen. Sam bata da sha'awarta ma don batajin zuwa yanzu tana da wani uzuri da ita. Jib,ayshatu,qannenta da sauran mutanen da takejin sun Ta'allaqa a wuyanta kadai zuciyarta ke mata"

amsa kuwwar ta nemesu.......tayi sallama da kowannensu. saidai kuma wani sashen daban yana bata

"qwarin gwiwar bata da buqatar hakan!. Tana ji a rai zuciya dama jikinta tamkar wani gajeran balaguro ne kawai zatayi daga tata duniyar zuwa wata duniyar,balaguron da bai wuce misalin qifatawar idanu daga rufewar zuwa budewar ba. Bataji kwata kwata cewa wai auren zai zama wani dogon aiki da zata kasa yakiceshi cikin qanqanin lokaci. A yanzun zata zubawa komai da kowa idanu kwadin me"

kwadayi......burin me buri......da tsarin me tsari a kanta ya kwanta. sannan ne ita kuma zata aiwatar da

nata shirin hankali kwance( nikam nace uhmmm qaddara dai ta rigayi fata ).

"Da plate huda ta dawo,wanda tsara zuba abincin gwanin sha'awa. Sabreen tasan duka tayi ne don"

"taci,ta jera soyayyen kifin saman shinkafa da waken,sannan ta mata roban yaji da magi daban. Da kallo"

"kawai tabi plate din,don tasan yafi qarfinta koda duniya ma tana kwance bare yanzu da wani abu waishi abinci baya burgeta."

Sallamar kawu rufa'i da sautin muryarsa kadai ya sanya abincin data sanya a bakinta ya tsaya mata

"cak a maqogaronta,sauran na bakinta kuma taste dinsa ya canza mata,har tana jin ba zata iya taunawashi ba,har sai data tattara dukkan juriyarta sannan ta tauna ta turashi zuwa maqogaronta wanda ta samu ya wuce da qyar,sai kawai ta yanke hukuncin ajiye abincin. Idanunta ya sauka kan kawun sanda take ajiye plate din a qasa,wanda yake jaye da wata mini luxury luggage me azabar kyau da kuma daukan idanu. Koda bakasan me duniya ke ciki ba,koda bakasan darajar abinda yake janye dashi ba"

tabbas zata fahimci luggage ne me tsada da madaukakiyar daraja.

Wajen zama mamma bahijja tayi masa tana sanya nadra ta ajiye masa drink da ruwa.

"""Ya hidima ya kuma shirye shirye?"" Kawun ya furta da muryar dake nuni da zallar farincikin da yake ciki"

"""Alhamdulillah ai kune da hidima,tunda mu nan ba abinda zamuyi"" Kai kawu rufa'i ya girgiza yana"

satar kallon sabreen da tunda ta gaidashi bata sake koda kallon sashen da yake ba.

"""Allah ya yiwa yarinyar nan taurin kai bahijja. idan kinga abubuwan da sukaso gabatarwa zakisha"

"mamaki har yanzu quruciya ke dawainiya da ita,inda tasan girman matsayi da darajar mutumin da"

"zata aura,na rantse miki saita qare rayuwarta tana godemin attajirin matashin da babu irinsa a"

"wannan qarnin da muke ciki?"" Dan murmushi kasan momma bahijja tayi,adan zamanta ta fahimci kawun yana sa son abun duniya"

"""Duk bama wannan ba rufa'i,indai har bincikenku ya tabbatar da nagartarsa ai magana ta qare. dukiya"

"wannan wani abune na daban ai"""

"""Habawa. idan ana batun nagarta ma da dattako har ayi magana wadannan dattijan?"""

"""To alhamdulillah.....haka akeson ji """

"""Yanzu haka ma aike ne......saqo ne na musamman daga surukarta. kaya ne tace a kawo mata da zata"

"sanya a gobe kenan"""

"""Tofa. ikon Allah,kuma dai?,basa gajiya?""Momma bahijja ta fada duba da irin kudaden da aka"

"narkar,tun daga dukiyar aure har izuwa batun lefen dasu kansu har yanzu basu gama sanin komai da komai dake cikin akwatunan ba. Tana qara ganin girman qaunar da suke gwadawa sabreen din,a gefe guda har ranta tana jin tamkar sabreen din tayi sa'ar inda zata rayu cikin qauna da kulawa."

"""Wai wai ma sha Allah"" Momma bahijja ta furta tana daga lafiyayyen applique lace da kudi suka koka"

qwarai wajen siyensa. Daga qasanshi kuma wata bazin ce data amsa sunanta sai super Sheraton da iya ado da gayu da kashema kai kudi irin na momma bahijja bata taba katarin ganin irinta ba. Daga qarshe set ne na banguls earrings da sarqa da zobensu duka na danyen gold me matuqar daraja(nikam nace

masu abu da abinsu).

Ko qwaqwqqwaran motsi sabreen batayi ba ballanta ta daga kanta ko zata nuna alamun

Please Login or Register in order to submit comment