Yana dauke da kayan tarkacen tsafi kala-kala.
Sannan duk Inda mutum ya duba sai dai ya rinka ganin kokunan kawunan mutane da Aljanu a sagale a jikin bangwayen gidan.
Hatta Kan hanyar da suke ratsawa suna wucewa yayin shigarsu cikin gidan, ta kan rubabbun kwarangwal din mutane da Aljanu suke bi, har ma Kasusuwan sun bushe rakau ta yadda da zarar an taka su za aga suna rumurmushewa suna zama gari.
Haka Kuma a wani bangare daban na wannan gidan, wasu gorunan jini ne nau'i-nau'i gasu Nan birjik.
Bugu da Kari a gaba kadan, sai RA'UFUL KALLUS yaga sun shigo wani daki Wanda wasu korai suke yawo a cikin iska dauke da ruwa na zabalbala a cikinsu..
A dakin gaba Kuma sai ya rinka ganin wasu kwala-kwalan layu da guraye rututu a cikin dakin suna ta kumbura suna sacewa.
Haka dai RA'UFUL KALLUS yabi wannan mummunar Aljana suka rinka ratsawa ta cikin dakuna kala-kala har guda dari tara da casa'in da tara, sannan suka iso wata babbar farfajiyar fada Mai tsananin kyau da kawatuwa.
Shi dai wannan daki ya Sha bamban da sauran duk dakunan da suka wuto, domin dakin a haskake yake da matukar haske Mai dadin gani.
Sannan Kuma an kawata dakin da abubuwan burgewa.
Duk inda mutum ya duba a cikin dakin sai dai ya rinka ganin manyan katifu na Alfarma da kujeru masu daukar Ido.
Hatta bangwayen ginin dakin da zallan lu'u-lu'u akayi sui, wannan yasa dakin yake ta haske Yana dallare idanu.
Ga gayan alatu Nan birjik tamkar su sukayi kansu don kyau.
Bugu da Kari ga tambulan na ruwan inibi a cikin manyan kufunan zinare.
Nan fa RA'UFUL KALLUS ya saki Baki Yana ta kallon abubuwan mamakin Dake cikin wannan daki.
Bayan sun gama shigowa cikin dakin, sai kawai yaga wannan mummunar Aljana ta rufe idanunta tana Karanta wadansu dalasiman tsafi tana tofawa akan tafin hannunta na hagu.
Fara hakan keda wuya sai akaga jikinta Yana tsattsagewa tamkar daskararriyar kankara.
Kafin cikar dakika dari da arba'in sai kawai yaga wannan mummunar Aljanar ta rikide izuwa wata tsaleliyar budurwa Mai tsananin kyau da cikar zati.
RA'UFUL KALLUS Bai San lokacin da ya Bude Baki har yawu na zuba ba, wajen kallon wannan kyakkyawar halitta.
Budurwa ta kasance fara tas tamkar ruwan korama yayinda yake gangarowa daga Saman duwatsu.
Tana da manya-manyan idanu masu matukar daukar hankali, hancinta siriri ne tamkar bakin alkalami.
Tana da dogon gashi Wanda ya sauko har bayan kwankwansonta.
Murmushin wannan kyakkyawar budurwa yafi ayiwa mutum kyautar duniya da duk abinda ke cikinta dadi.
Babu wani da namiji a duniya walau a cikin mutane ko aljanu da zayyi tozali da wannan kyakkyawar budurwa batare da ya iya sallama rayuwarsa domin kawai ganin farin cikin ta ba..
Uhmm hatta ku Kanku masu karatu kuwaπππ
Koda RA'UFUL KALLUS ya gama kallon yadda zubin wannan kyakkyawar budurwa ta kasance, sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi.
Nan take yaji a ransa cewa inda zai mallaki wannan kyakkyawar budurwa a matsayin mata, to ko kallonta kadai yakeyi bazai Kara bakin ciki a rayuwarsa ba.
Kuma yace a cikin ransa, " tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya kirkirar wannan zankadediyar kyakkyawar halitta, tabbas inda wannan budurwa zata fito duniya Kuma ace duka mutanen duniya da Aljanu zasuyi arba da ita, to Nan take zasu yarda ta zama sarauniyar duniya ba don komai ba sai don tsananin kyawunta.
Haka dai RA'UFUL KALLUS ya shagala da kallon wannan kyakkyawar budurwa har ma ya manta da burin da ke gabanshi.
Domin tuni kibiyar so da kauna sukayi fitar burtu daga zuciyarsa suka afka a kanta.
Kuma yaji a ransa cewa shi Kam, yanzu bashi da sauran buri a duniya face ya zauna tare da wannan kyakkyawar budurwa iyakar rayurwasa Yana kallon kyakkyawar fuskarta Mai Saka natsuwa da sanyaya Rai.
Yana cikin wannan Hali ne, ya ga wannan kyakkyawar budurwa ta nuna shi da hannunta guda, take wadansu igiyoyin tsafi suka daure shi suka jawo shi suka zaunar da shi akan Daya daga cikin kujerun nan masu laushi, Yana Mai fuskantar inda ta zauna sannan suka kwance kansu daga jikinsa suka bace.
Kyakkyawar budurwa ta kalle shi tayi Masa wani lallausan murmushi, Sannan ta ce, " ya Kai wannan hatsabibin Aljani kayi sani cewa ni sunana BOKANYA AGADAMU.
Kuma na kasance daya daga cikin jinsin maridan Aljanu na duniya.
A halin yanzu duk duniya ni kadai ce wadda na rage daga cikin irin kabilarmu, sakamkon wani mummunar Annoba da ta afko mana a Garinmu.
Annobar wata irin muguwar iska ce Mai dauke da bakar guba, wadda da zarar mun shake ta take jikin yake bushewa ya ratattake ya zama gawa.
Haka wannan Annobar ta rinka ketawa ta cikin lungu da sako na cikin birninmu har sai da Karar da gaba dayan kabilar mu ni kadai na kubuta daga bala'in wannan Annoba, nima din inba don nayi amfani da karfin sihirin tsafi ba da tuni wannan Annobar ta gama Dani.
Haka Kuma duk da cewa Annobar ta Karar da dukkanin kabilarmu sai tayi zaune a birninmu ta yadda koda wani daga cikin kabilar ya samu nasarar tsira da rayuwarsa to zarar ya koma wannan birni Annobar nan zata gama da shi.
Aljanar ta ci gaba da cewa, lokacin da na tsira da rayuwata sai na Yanke shawarar barin yankin Aljanu gaba daya domin nayi bincike na musamman akan dalilin afkuwar wannan Annoba a garemu.
Nan take nayi bincike na ga cewa babu inda yayi dai-dai da rayuwata sai wannan wuri da ka ganni ni da kuyangina da bayi na.
Bayan nazo wannan birni ne, sai na shiga binciken dalilin da yasa wannan Annobar ta Karar da kabilarmu gaba Daya.
Sai da nayi kwana dubu Ina bincike sannan na samu nasarar binciko dalilin faruwar wannan Ala'mari.
Bincikena ya tabbatar min da cewa akwai wani takadarin BOKAN ALJANI Wanda yake rayuwa a duniyar karkashin Kasa, Kuma wanda yake da burin mallakar duniya da abunda ke cikinta ta hanyar sihirin tsafi.
To amma yayi bincike ya gano cewa burinsa ba zai taba cika ba, har sai ya kashe gaba dayan maridan duniya domin su kadai ne zasu bashi matsala akan aikinsa.
Kuma ya tabbatar da cewa indai yaki zayyi dasu to tabbas sai sun samu nasara a kanshi.
Saboda sanin kowa ne cewa kabilarmu ita ce Mafi tsananin karfin damtse akan dukkan kabilun Aljanun duniya.
Komai tsananin karfin Aljani indai ya shigo hannunmu to Autan cikinmu muke sa wa ya kama shi da karfin tsiya sannan ya dinga Yi Masa azabobi kala-kala har iyakar rayuwarsa.
BOKANYA AGADAMU ta ci gaba da cewa, Koda BOKAN ALJANIN nan ya fahimci cewa ba zai iya yakarmu gaba da gaba ba, sai ya hada wani sihirin tsafi Mai hade da wannan bakar gubar wadda duk duniya Bata da wani magani sai mutuwa.
Ita dai wannan guba an kirkireta ne da ruhin nau'ikan halittun duniya guda dubu.
Ma'ana sai da ya gutsiro ruhin duk halittun da ke cikin duniya iri-iri guda dubu sannan ya hada wannan gubar sihirin.
Ya fara ne tun daga Kan dodannin duniya, da dabbobi da kananun kwari, da bishiyoyi, da duwatsu har izuwa kan mutane da Aljanu kowane daga cikinsu sai da ya gutsiro ruhinsu guda dubu sannan yayi wannan aiki.
Haka Kuma ita wannan bakar guba, muddin mutum ya kirkireta sannan ya aikata izuwa inda yake so.
To Koda mutane da Aljanun duniya zasu taru ba zasu taba iya karya ko Bada maganinta ba, face kawai a Nemo Wanda ya kirkiri gubar a kashe shi.
Bincike ya tabbatar da cewa da zarar an kashe shi, duk halittun da gubar ta kashe take zasu tashi rayayyu tamkar basu taba mutuwa ba.
A bisa wannan dalili ne BOKANYA AGADAMU ta Kara zurfafa bincike domin gano hanyar da zata bi, ta kashe BOKAN ALJANIN nan don ta dauki fansar cutar da su, da Kuma dawo da 'yan uwanta da danginta a matsayin rayayyu.
Sai da sake shafe kwanaki guda dubu tana bincike sannan ta gano mafita.
Mafitar dai ita ce, muddin tana so ta samu nasarar kashe BOKAN ALJANIN nan to dole ta yake shi gaba da gaba da makami, Kuma hakan ba zai taba yiwuwa ita kadai ba, domin ta San cewa yafi karfinta nesa ba kusa.
Hanya Daya ce kawai zata bi wadda zata bi wadda zata cika burinta.
Hanyar ita ce dole ne ta rinka zuwa tana farauto manyan sarakunan Aljanu, bokayen Aljanu, da manyan zakakuran jaruman Aljanu tana kwanciya da su sannan.
Duk Wanda ta kwanta da shi, take zata dauki cikin maridan Aljanu guda dari, Kuma a cikin kwanaki arba'in kacal zata haifesu sannan ta Kara farauto wani Aljanin.
A sakamakon haka ne yasa BOKANYA AGADAMU ta rinka bazama cikin duniya tana sato manyan sarakunan Aljanu da karfin sihirin tsafi tana kwanciya da su sannan tana haihuwar maridan Aljanu.
A halin yanzu ta haifi MARIDAI MILYAN TARA da dubu dari biyar, saura cikon Dubu Dari biyar kacal burinta ya cika, wato adadin yakai yanda zasu iya yakar wannan Bokan Aljanin.
Babbar matsalar shi ne, duk Aljanin da wannan budurwar ta kwanta dashi to da zarar sun gama abinda zasuyi sai ta kashe shi, saboda tana bakin cikin wani da namiji yayi mu'amala da ita sannan yaje yayi da wata mace bayanta.
A bisa wannan dalili ne duk Aljanin da ta farauto sai ta kashe shi.
Wannan yasa kwarangwal din Aljanu yayi yawa turmus a ko'ina a cikin wannan gida nata.
Haka Kuma ta sihirce gaba dayan gidan ta yadda Komai sihirin tsafin mutum ko Aljan indai ya shigo wannan gidan to ba zai taba aiki ba.
Koda BOKANYA AGADAMU tazo Nan a zancenta sai ta dubi Aljani RA'UFUL KALLUS Sannan ta ce Kai ne Aljani na karshe da zan kwanta dashi domin cikar burina.
Kuma kayi sani cewa da zarar mun gama abinda zamuyi yanzu a take zan halaka ka domin Ka'idar wannan gida kenan duk Aljanin da ya shigo ya shigo kenan har abada ba zai Kara fita ba.
Koda Jin wannan batu daga bakin BOKANYA AGADAMU sai na kamu da tsananin razana sannan hannuwana suka kama karkarwa Wanda yasa tsoro ya mamaye min zuciyata har na Kasa cigaba da rubutunπ₯Ίπ₯Ί
Anan nake cewa sai mun hadu a part B don Jin yadda zata kaya a tsakanin BOKANYA AGADAMU da ALJANI RA'UFUL KALLUS..
Ina maku fatan Alkhairi, tare da fatan Allah ya sadamu da duk alkhairan da ke cikin wannan Rana Mai albarka π
Haka Kuma Allah ya kare mu daga dukkan sharri na kowace irin halitta ta Fili da ta boyeβ₯οΈβ₯οΈβ₯οΈβ₯οΈ**HATSABIBIN ALJANI**
LITTAFI NA TARA 9 βοΈ
PART B βοΈπ―
AUTHOR:- NAJIBULLAH MUHAMMAD βοΈβοΈ
POSTING:- Najibullah Muhammad π₯·π₯·
Note:- kuyi hakuri a bisa jinkirin posting da nake yi kwana biyu. Hakan ya faru ne sakamakon rashin lafiya da nake fama da ita kwana biyun nan.
Saboda haka Ina fatan zaku tayani da addu'ar samun lafiya domin cigaba da nishadantar da ku.
Ina maku fatan Alkhairi β₯οΈβ€οΈπ₯°
βββββββββββββββββββββββββββββββ
Cigaban littafin.....
Idan baku manta ba a baya mun tsaya ne a inda BOKANYA AGADAMU take sanar da ALJANI RA'UFUL KALLUS cewa Kai ne Aljani na karshe da zan kwanta da Kai, Kuma da zarar mun gama abinda zamuyi zan halaka ka.
Bugu da Kari Kuma Daman Ka'idar wannan gida ne cewa, duk Aljanin da ya shigo wannan gidan to ya shigo kenan har abada, ko Gawarshi ba zata fita ba dole sai dai ya mutu anan Kuma har Kasusuwanshi su rube su zama Kasa.
Saboda haka Ina Mai shawartarka akan kayi abinda nake so kayi cikin saukin rai ko hakan zai sa kayi mutuwar farin ciki kamar yadda dayawa sauran Aljanu sukayi.
Ko Kuma ka bijire min sannan ni Kuma nayi amfani da karfin damtse da na sihirin tsafi domin na biya bukatata dakai, sannan daga bisani nayi maka mummunan kisan gillar da ba a taba yiwa kowace irin halitta irinsa ba.
Koda Jin wannan batu sai RA'UFUL KALLUS ya kamu da tsananin razana, sannan ya dube ta a tsorace yace ya Shugabata, Ina Mai rokonki akan ki gafarceni sannan ki kyale ni na tafi ki Nemo wani yayi maki wannan aikin.
Kiyi sani cewa Ina da babban burina a gabana, Wanda a sanadiyyar wannan burin ne nake rayuwa domin na sallamar da gaba dayan numfashina don cika wannan buri.
Kafin RA'UFUL KALLUS ya gama maganar da ya fara, tuni BOKANYA AGADAMU ta tari numfashinsa ta hanyar daka Masa tsawa Mai tsananin Kara wadda tasa ya Kara razana ainun.
Sannan ta turbune fuska ta dube shi a karo na biyu ta ce," dole Kai ne zakayi wannan aiki, domin bincike ya tabbatar min da cewa Aljanun da zan Haifa ne tare dakai kadai zasu iya jagorantar wannan yaki da zamu tafi har a samu nasara.
Nayi iyakar bincikena na gano cewa idan har banyi Amfani da kwayoyin halittar dake jikinka ba, to ba zan taba haihuwar maridan Aljanun da zasu iya yakar bakon Bokan Aljanin da ya addabemu ba.
Saboda haka a yau ta kowane Hali sai kayi wannan aikin.
BOKANYA AGADAMU na gama fadin hakan, sai akaga ta rikide daga kyakkyawar budurwa izuwa wannan mummunar Aljana yankwananniyar tsohuwa mara kyan gani.
Tana gama rikida ne ta dakawa RA'UFUL KALLUS tsawa akan cewa Maza kazo muyi abinda ke gabanmu.
Nan take RA'UFUL KALLUS ya tuna irin matsayinshi da irin yadda ya gagari duniya gaba Daya.
Sannan Kuma ya tuna irin wahalhalu da gwagwarmayar da ya Sha a duniya tun gabanin ya iso birnin wannan Aljana.
Kuma ya tuna a ransa cewa, yanzu fa da zarar na yarda da bukatar wannan Aljana shikenan burina ya yanke Kuma daga Nan an manta Dani har abada.
Ya ci gaba da cewa ai kuwa da hakan ta faru gwara a fafata, duk Wanda yayi nasara a tsakaninsu shikenan.
Koda BOKANYA AGADAMU taga Aljani RA'UFUL KALLUS yayi shiru Kuma ya fiddo makamansa da nufin yakarta a Maimaikon bin umarninta, sai ta Kara turbune fuska Wanda ya Kara fito mata da munin fuskarta Wanda duk Wanda ya kalle ta a wannan lokaci zai iya shekara bayyi barci ba saboda munin fuskarta.
Nan take ta dubi RA'UFUL KALLUS ta ce," Kaiconka!! Ya Kai wannan Aljani Mai taurin Kai.
Kayi sani cewa ka tafka babban kuskure a rayuwarka da har ka bijirewa Umarni na.
To kayi sani cewa na rantse da darajar tarkacen kayan tsafina sai na gana maka azabobi kala-kala har guda dubu sannan daga bisani nayi maka mummunan kisan gillar da ba za'a taba mantawa da irinshi ba.
Kafin RA'UFUL KALLUS ya ce wani abu tuni BOKANYA AGADAMU ta bace bat daga inda take, cikin kiftawar Ido sai ta bayyana a gaban RA'UFUL KALLUS da zuwanta ta kawo masa wawan cafka a makoshi da hannunta.
Cikin tsananin zafin nama ya kare harin nata da takobinsa, Nan take Takobin ta kama da wuta ta kone kurmus.
Kafin yayi wani yunkuri tuni ta tasa kafarta guda ta doki kirjinsa.
Saboda karfin dukan sai da RA'UFUL KALLUS yayi baya luu tamkar an janye shi da Kugiya yaje ya gwaru da jikin bangon dakin ya fado Kasa a matukar galaibace.
Cikin matukar karfin hali ya daddafa bango ya Mike da kafafunsa sannan ya rike dayan makamin nasa dakyau Yana Mai fuskantar wannan yankwananniyar tsohuwar Aljana.
Koda BOKANYA AGADAMU taga haka sai ta saki murmushin mugunta. Nan take ta Bude hannuwanta ta runtse idanuwanta Yana Karanto wadansu dalasiman tsafi na musamman.
Fara hakan keda wuya sai RA'UFUL KALLUS ya rinka ganin faratan hannunta suna ta fitowa zarkala-zarkala tamkar wani karfe aka sa ana jawo su.
Sai da gaba dayan faratan suka fito sukayi tsayi tamkar takubba goma ta rike a hannuwanta, kowane makami daga jikinsa sai wani turari ke fita da jikinsa.
Koda RA'UFUL KALLUS yaga haka sai ya dake zuciyarsa sannan ya tattara karfinsa gaba Daya ya falfalo da azababben gudu izuwa kan BOKANYA AGADAMU.
Nan take ita ma ta tare shi suka runguntsume da masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro da tashin hankali.
Ya zamana cewa suna kaiwa junansu Sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta tamkar jikinsu ba na jini da tsoka bane.
A duk lokacin da takobin RA'UFUL KALLUS ta hadu da makaman hannun BOKANYA AGADAMU sai dai aga tartsatsin wuta mai yawa yana zubowa a kasan dakin.
Koda yawan Kai saran su ya yawaita, sai wutar ta rinka kama bangarorin dakin tana ci.
Lokuta dayawa BOKANYA AGADAMU na Amfani da karfin sihirin tsafinta wajen kashe wutar da ke tashi dakin, Amma duk da haka kafin cikar dakika hamsin sai da rabin dakin ya kama da wuta ya kone kurmus.
Koda BOKANYA AGADAMU taga cewa wannan aljanin Yana Neman zame mata matsala sai ranta baci Kuma ta cika da matukar mamaki a cikin ranta.
Cikin tsananin shammace ta finciko ALJANI RA'UFUL KALLUS da hannu daya sannan ta jujjuyashi a sama tamkar yadda ake jujjuya bulala a hannu, ta maka shi a jikin bangon dakin.
Saboda dokuwar da yayi sai da bangon dakin ya Burma burum, ya fito ta wani dakin.
Nan take BOKANYA AGADAMU ta bace bat, ta bayyana Tsulum a gaban RA'UFUL KALLUS tana Mai kyakyata dariyar mugunta.
A wannan lokacin idanun RA'UFUL KALLUS na lumshewa da budewa da kyar saboda tsananin jigatar da yayi.
Ita kuwa BOKANYA AGADAMU sai ce cikin izza, Ashe Daman iyakar Jarumtakar ka kenan har kake min taurin Kai akan bukatata.
Na rantse da matsayina, yanzu take zan biya bukatata dakai sannan na cika alkawarin da nayi a kanka wato na gana maka azabobi kala-kala har guda dubu sannan nayi maka mummunan kisan gilla.
Tana gama fadin hakan sai ta juya da baya ta nufi wani wuri daban, inda ta ajiye wata kwalbar sihiri.
A cikin kwalbar akwai wani ruwa na zabalbala Yana yamutsawa kamar Yana Shirin fasa kwalbar ya tarwatse, Amma da zarar ruwan ya juya sama ya tabo wani bakin gashi Dake jikin murfin, sai ya lafa.
Koda tazo dai-dai kan kwalbar Nan, ta Mika hannu da nufin dauka.
Ba zato ba tsammani sai kawai hannunta guda a Kasa ya fice fit.
Cikin tsananin dimaucewa da razana ta juyo da baya.
Ba wani bane yayi wannan gagarumin aiki na guntule mata hannu ba face RA'UFUL KALLUS.
Yayi tsaye a bayanta rike da takobi tana digar da jinin dungulmin hannunta.
Cikin tsananin Kunan rai BOKANYA AGADAMU ta kwarara wata kururuwa mai tsananin ban tsoro wadda amsa-kuwwarta ta cika birnin gaba daya.
Nan take RA'UFUL KALLUS ya rinka dudufniyar takun sawaye bila'adadin dun durfafo inda suke.
Ana cikin hakane idanun RA'UFUL KALLUS suka Kai kan wannan kwalbar sihirin da BOKANYA AGADAMU take kokarin dauka.
Cikin tsananin shammace ya banke BOKANYA AGADAMU ta fadi Kasa can gefe guda, sannan ya Suri kwalbar nan ya maka ta jikin bango.
Take kwalbar ta tarwatse ruwan cikin kwalbar ya fantsama a ko'ina.
Faruwar hakan keda wuya sai hayakin da ke cikin wannan ruwan ya turnuke ko'ina.
Ya zamana cewa ya mamaye ko'ina cikin birnin, tamkar an cinnawa gaba dayan bishiyoyin birnin wuta.
Kash! Rashin sani yafi dare duhu.
Ashe da wannan kwalbar sihirin ce BOKANYA AGADAMU tayi Amfani ta sihirce gaba dayan 'yayanta.
Wanda ta samu nasarar tattara gaba dayan ruhinsu a cikin kwalbar domin kawai su rinka bin umarninta tamkar yadda bawa ke biyayya ga Ubangijinsa.
Ai kuwa kafin cikar dakika dubu uku gaba dayan Aljanun birnin sun kone kurmus, sun zama gawa.
Hatta ita kanta BOKANYA AGADAMU rayuwarta na cikin mummunan yanayi tsakanin Rai da mutuwa.
Domin gaba dayan idanunta sunyi kwala-kwala saboda wahalar.
Kafin cikar dakika hamsin ta karasa mutuwa.
Mutuwarta keda wuya sai gaba dayan birnin yayi girgiza ya bace bat, sannan nan take duk gidaje da sauran halittun da suke yawo a cikin iska su ma suka bace bat.
Kafin wani lokaci tuni komai ya dawo dai-dai da na kowane birni.
Dama BOKANYA AGADAMU ce tayi Amfani da karfin sihirin tsafi domin juyar da birnin domin cikar burinta.
Koda RA'UFUL KALLUS ya ganshi bisa turba, Kuma yaga Yana iya gane kowane bangare na birnin.
Sai ya durfafi bangarori hudu na garin ya debo ganyayen bishiyoyin birnin sannan ya dawo ya Debi Kasar tsakiyar birnin ya cigaba da tafiyarsa..
Sai da RA'UFUL KALLUS ya shafe kwanaki uku cur Yana tafiya ba tare da yada zango ko Daya ba, sannan ya iso birnin na Sha biyu.
Da shigarsa wannan birnin sai ya cika da tsananin mamaki abinda ya gani.
Ba wani Abu bane RA'UFUL KALLUS yayi arba da shi a wannan birni ba, face iya hangensa ruwa ne gabas da yamma kudu da Arewa TEKU CE wadda girmanta ya mamaye birnin gaba daya.
Babu ta yadda za'ayi a wuce ta wannan birni dole sai anbi ta cikin wannan teku.
Nan take RA'UFUL KALLUS ya tambayi Kansa a cikin ruwa cewa tayaya zan iya tsallake wannan ruwa Mai yawa haka?
Kuma tayaya zan mallaki ganyaye da Kasar Dake cikin wannan birni?
Bayan ya Kasa ba Kasa Amsar tambayoyin Sai ya tunkari wannan TEKU gadan-gadan.
Da zuwansa sai ya tsaya Yana nazarin wannan TEKU.
Ba zato ba tsammani sai kawai RA'UFUL KALLUS yaji an finciko shi daga cikin karkarshin Tekun.
Ai kuwa Nan take yaji shi tamkar an jeho igiya ta fizgo shi, kawai sai jinsa yayi cikin ruwa.
Da shigarsa cikin wannan teku sai yaji Ashe Yana iya Bude idanuwansa kamar yadda yake iya Bude su a Saman doron Kasa.
Kawai sai yayi arba da manyan gine-ginen birnin tare da mutane da dabbobi da sauran Kananan halittu suna ta harkokinsu a karkashin TEKU.
Ashe gaba dayan birnin ne ya nutse karkashin Kasa, Kuma babban abin mamaki shi ne duk da kasancewarsu cikin ruwa hakan Bai Hana su numfashi, tare da sauran harkokin gudanar da rayuwa kamar yadda sukeyi a doron Kasa ba.
Yana cikin kalle-kalle ne Yana mamakin irin yadda akayi har wannan birni ya kasance haka, sai kwatsam....
ME ZAI FARU DA RA'UFUL KALLUS A CIKIN WANNAN BIRNI?
SHIN ZAI SAMU NASARAR TSALLAKE DUKA MASIFUN BIRANEN DA KE GABANSHI?
INA LABARIN YAKIN DA AKE FAFATAWA ACAN KOGON BAHAR DURGAFUL KALLUS?
Domin Jin duka wadannan Amsoshi sai mu hadu a HATSABIBIN ALJANI na goma 10.
Ina maku fatan Alkhairi tare da cewa sai mun hadu wani lokaci βοΈβοΈβοΈβ₯οΈβ€οΈπππ
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels