karfen Nan ta samu Daya daga cikin Aljanun sai dai kaga ta tsinka shi biyu, idan kuwa bil'adama ta samu to Nan take yake ratattakewa tamkar an daka shi a turmi...
Koda ganin wannan Ala'mari sai rundunar mutane ta rikide ta zama wani NARKEKEN MUTUN guda dubu, kowane mutum daya girmansa ya ninka na dodo sau uku.
Cikin tsananin zafin nama suka rinka fizge majaujawar karfen daga hannun dodannin sannan suna maka masu ita akai, sai dai aga kan dodon ya fashe jini da kwanya sunyi tsiri a sama sannan sun sulale Kasa matattu.
A bangaren Aljanu kuwa, Koda suka ga dabarar da bil'adama sukayi akan dodannin, sai Suma suka rikide suka zama wadansu jibga-jibgan SAMUDAWAN MARIDAI masu tsananin girma da kauri tamkar bishiyar kuka, wadanda adadinsu yakai dubu Dari.
Nan take maridan nan suka Afkawa dodannin nan suna masu naushinsu hannu da kafa.
A duk lokacin da maridi daya ya gabzawa dodo naushi, sai dai aga hannunshi ya Burma a jikin dodon sannan ya jefar da Gawarsa Kasa.
Wani lokacin Kuma sai dai aka maridan suna cafko dodannin da hannu daya suna zura kawunansu a cikin bakinsu, sun gutsure su sun taune sun hadiye.
Nan fa kisan dodannin nan ya yawaita, ya zamana cewa tako'ina mutuwa ke daukarsu ba ji ba gani.
A cikin abinda Bai wuce rabin sa'a ba, sai da aka kashe masu dodanni dubu dari biyar.
A wannan lokacin tuni dodannin nan sun karaya, domin sunyi iyakar kokarinsu wajen yakar samuwadan mutanen da Kuma maridan nan Amma Abu ya faskara har yanxu ko kwarzane sun Kasa yiwa kowannensu.
Ana cikin haka ne.
Ba zato ba tsammani sai kawai aka hango wani bakin hayaki ya fito daga cikin Kogon tamkar igiya, ya kanannade gaba dayan DODANNIN.
Faruwar hakan keda sai kowanne dodo ya sandare a wuri guda, kafin cikar dakika hamsin gaba dayan DODANNIN sun zama gumaka.
Faruwar hakan keda wuya sai aka wannan hayakin ya rikide ya zama wata murtukekiyar macijiyar Kasa Mai tsananin girma da tsawo.
Saboda tsabar tsawonta har ba iya hango karshenta.
Cikin tsananin zafin nama Mai kamar walkiya wannan macijiyar ta rinka kanannade wadannan MARIDAN da samuwadan mutanen Nan, suna ji suna gani ta kanannade gaba dayan su, ya zamana cewa ta matse su tamau ta yadda ko motsi Basu iya yi.
Faruwar hakan keda wuya sai ta rinka matse su suna kakkaryewa, nan fa suka rinka kwallara ihu saboda azabar da suke Sha.
A cikin abinda Bai wuce dakika arba'in ba, ta gama kakkarya gaba dayan Kasusuwansu, Koda kammala wannan aikin sai ta Bude bakinta ta rinka Loma guda da su.
Nan fa macijiyar nan ta rinka hadiyar maridan nan da samuwadan mutanen Nan tamkar ana jefa tsakuwa a cikin RIJIYA GABA DUBU, sai dai Kaji Karar hadiyarsu wani mukut-mukut.
Kafin cikar dakika dari biyu da tamanin ta kammala cinye gaba dayan maridan nan da samuwadan mutanen.
Faruwar hakan keda wuya sai tayi wata irin kururuwa mai tsananin razanarwa Wanda har sai da ragowar Dakarun Aljanu da mutanen dake wajen kogon sukaji kamar su ruga a guje, Amma sai suka kanne dai suka tsaya.
Bayan kamar Dakika arba'in macijiyar ta rufe bakinta, sai ta rinka furzo da wani mugun bakin dafi Mai kauri da yauki kamar an kada lalle, faruwar hakan keda wuya sai wannan macijiyar ta juya ga dodannin nan ta hura masu wata iska Mai tsananin karfi sannan ta bace.
Nan take dodannin nan suka dawo ainihin siffarsu ta da, dawowarsu keda wuya sai suka Riga wurin da macijiyar Nan ta zubar da mugun dafinta suka Kafa kawunansu suna ta Shan wannan dafin.
Sama da dodanni Milyan Daya ne suka Sha wannan dafin, saboda haka suna kammala Shan shi sai aka sun rikide sun koma kamannin wannan macijiyar sak, ragowar dodannin Kuma sun Kara girma da kauri akan siffarsu.
Duk wannan Abu da ke faruwa rundunar Aljanu ta hudu ta shigo cikin kogon dauke da Dakaru Milyan Dari biyu, kowannensu na rike da makamai dauke da wuta na ci a jikinsu.
Gaba dayan wadannan Dakaru zuciyarsu ta kekashe ga barin tsoro, saboda ganin irin mummunan Kisan gillar da akayi wa 'yan uwansu .
Kuma sun raya a ransu cewa Koda wane Hali sai sun Dauki fansar ran 'yan uwansu.
Kafin wani daga cikinsu yayi yunkuri sai gaba dayan Aljanun nan suka rugo da gudu wajen dodannin nan rike da muggan makamai suna ihu da Karaji tamkar duniyar ce gaba daya ta tattaro kanta...
MEZAI FARU A WANNAN YAKI TSAKANIN DODANNI DA WADANNAN ALJANU?
SU WAYE ZASU SAMU NASARA A TSAKANINSU?
SHIN WADANNAN SARAKUNAN DUNIYA SUNA SAMUN NASARAR SHIGA WANNAN KOGO HAR SU CIKA BURINSU?
INA LABARIN ALJANI RA'UFUL KALLUS?
YANA SAMUN NASARAR KUBUTA DAGA WANNAN KURKUKUN KUWA?
Mu hadu a HATSABIBIN ALJANI na bakwai 7 domin Jin Amsar wadannan tambayoyin..
Daga Mai debe maku kewa wato NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️🙏🙏
**HATSABIBIN ALJANI**
LITTAFI NA BAKWAI 7
PART A..
AUTHOR: NAJIBULLAHI MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷
Whatsapp Num.. 08112778656.
GORON JUMA'A 🤝❤️❤️♥️
Idan baku manta ba, a wancan littafin mun tsaya ne a inda, rundunar Aljanu ta hudu ta shigo cikin kogon da dodannin nan suke.
Kowannensu na dauke da muggan makamai masu matukar hadari, bugu da Kari wuta ce ke ci a jikin makaman.
Gaba dayan wannan Dakaru zuciyarsu tafarfasa takeyi kamar zata kone, saboda tsananin fushin kisan gillar da dodannin nan suka yiwa 'yan uwansu.
Haka zalikha Kuma dukkansu sun raya a ransu cewa Koda zasu mutu a wannan kogo, to babu gudu babu jaa da baya har sai sun Dauki fansar 'yan uwansu Kuma sun shiga cikin kogon domin lalata dukkan sihirin tsafin RA'UFUL KALLUS.
Lokacin da wannan runduna ta Aljanu ta gama shigowa cikin kogon dauke da muggan makamai, sai gaba dayansu suka takarkare duka kwarara wani uban ihu Mai tsananin razanarwa Wanda kararsa da Amsa kuwwarsa ya cika kogon gaba Daya, har sai da kogon ya fara girgiza kamar zai ruguje sannan suka tsuke bakinsu.
A lokaci guda, suka ruga da guda izuwa kan dodannin nan suna ihu da Karaji.
Wohoho! Tashin hankali ba a sa Masa Rana!
Hakika yaki abun tsoro ne.
Inda ace mutum na wurin, yaga lokacin da rundunar Aljanun nan suka ruga izuwa kan dodannin nan gaba dayan su a lokaci guda, da sai yayi tunanin kamar tsuntsayen duniya da dabbobin duniya ne kaf! Suka hade wuri guda suna Kai farmaki.
Koda haduwar wadannan Aljanun da dodannin nan, sai aka runguntsume da bala'e'en yaki Mai tsananin ban tsoro.
Ya zamana cewa Aljanun suna yaki ne da dukkan karfinsu, suna wurwura makamansu tamkar yadda ake jujjuya tsintsiya a hannu.
A duk lokacin da suka samu nasarar sarar wadannan dodannin sai dai aga jikinsu na gutsirewa Yana faduwa Kasa.
Aljanun suka zage dantse wajen kaucewa da zillewa harin dodannin.
Koda dodannin nan suka ga haka sai suka haukace, Kuma suka dimauce, Nan fa suka rinka kawo mugun mangari da lafta-laftan hannuwansu tare da kawo mugun taku da Kafafunsu da nufin talitse Aljanun.
Idan tsautsayi yasa dodo ya kawo mangari ya samu Daya daga cikin Aljanun, sai dai aga Aljanin yayi sama tamkar an janye shi da Kugiya, yaje ya gwaru da Saman dutsen kogon, sannan ya ratattake tamkar an markade shi.
Idan kuwa ya samu nasarar take Aljanun da wannan muguwar lafceciyar kafar tasa, saboda karfin takun sai dai aga Aljanin ya nutse a cikin karkashin Kasa tamkar bai taba wanzuwa ba.
Nan fa ihu da kururwar mazaje ta yawaita, lokacin yakin nan yayi tsamari sosai, sai Kasar kogon ta fara girgiza kamar zai ruguje, saboda mugun takun sawun da dodannin suke kawowa ya wuce misali.
Bugu da Kari duk lokacin da suka Kai mangari Basu samu kowa ba, sai dai aga hannunsu ya mako dutsen kogon ya fado Kasa.
A bisa wannan dalili ne yasa kogon yayi kamar zai ruguje, kura ta turnuke wajen, Hayaki da bala'in yaki suka yanyame wajen, ya zamana cewa wurin yayi duhu dundum ba a iya komai a ciki.
Koda ganin wannan Ala'mari sai wadannan zabga-zabgan macizan Dake gefe guda, suka kutso Kai cikin filin yakin.
Nan fa suka rinka daukar mutane suna wurgi dasu tamkar yadda iska ke daukar karmami tana yawo dashi sama.
Faruwar hakan keda wuya, sai sauran dodannin nan suka koma gefe guda suna kallon yadda macizan Nan ke karkashe Aljanun.
Karfin macizan da Kuma zafin namansu ya wuce misali.
Haka zaka ga sun rugo da gudu suna kawalwainiya suna fasa Kai, sannan sun Kaftawa Aljani Sara.
Duk Aljanin da suka Sara da wannan lafcecen bakin nasu, sai dai aga Aljanin ya rabe gida biyu tamkar ansa takobi an rabashi.
A bangaren Aljanu kuwa, Koda macizan Nan suka shigo filin yakin, sai suka rasa yanda zasuyi da su, domin macizan sun zame masu alakakai.
A duk lokacin da aljanun suka daga makamansu da nufin saran macizan, sai dai suga macizan sun make su da jelarsu, Nan take suke faduwa Kasa matattu saboda ita kanta wutsiyar tasu tamkar zabira take saboda kaifinta.
A cikin sa'a guda sai da macizan Nan suka kashe Aljanu sama da Milyan hamsin.
Ya zamana cewa duk Inda mutum ya duba a cikin kogon sai da yaga gawarwakin su himili guda tamkar Tsauni.
Kai komai kididdigar mutum bazai iya lissafa gawarwakin Dake wurin ba.
Domin gawar ce wata kan wata, haka suka cika ko'ina a cikin kogon.
Su kansu macizan tun suna hadiyar Aljanu da sauran gawarwakin Dake kwance a Kasa, har suka gaji suka dena, domin cikinsu ya cika makil, da kyar ma suke iya tafiya saboda tsabar koshi.
A wannan lokacin gaba dayan macizan Basu da wani kuzarin kashe Aljanun saboda yadda suka cika cikkunansu da Aljanu.
Koda rundunar Aljanun Nan suka ga haka, sai suka rinka daka tsalle sama suna cakawa macizan makamansa a kaa, take kan yake fashewa jini da kwanya su malalo Kasa suna tsiri a sama tamkar teku ta balle.
Koda suka ga sun fara samun nasarar kashe macizan sai sama da Aljanu Milyan hamsin suka rugo gaba dayansu suka yanyame macizan nan.
Nan fa suka wanzu suna doka masu dogon mashinsu a tsakiyar Kai, Yana fashewa suna sulalewa Kasa matattu.
A cikin abinda bai wuce sa'a guda da rabi ba, Aljanun Nan suka samu nasarar Karar da gaba dayan macizan Nan.
A wannan lokaci adadin Aljanun Bai wuce Milyan tamanin ba.
Wato dai an kashe sama da Aljanu Milyan Dari da Ashirin a wannan Yakin.
Lokacin da sauran dodannin nan suka ga an kashe masu 'yan uwa sai suka razana ainun, Kuma ransu ya Baci.
Cikin tsananin fusata suka ruga izuwa cikin kogon gaba dayansu suka dauko wadannan Manya-manyan SANGWAMIN nasu suka rugo izuwa kan Aljanun Nan suna ihu da Karaji.
Duk da cewa yawan dodannin nan Bai wuce Milyan biyu ba, Amma Kuma ihun da suke da gurnaninsu ya disashe na Aljanun.
Koda aka hadu sai aka Kara runguntsumawa da masifaffen yaki ya zamana cewa dodannin suna makawa wadannan Aljanun Katon Sangwamin da ke hannunsu.
A wannan lokaci ne aljanun suka fara Gane kurensu.
Domin girman kowane Sangwami Daya ya ninka Aljani sau uku, saboda haka a duk lokacin da dodannin nan suka kawo duka da Sangwamin Nan sai dai aga sama da Aljanu arba'in sun maku a jikin dutsen kogon sannan sun fado Kasa matattu.
Nan fa matattun Aljanun Nan suka rinka shawagi a sama tamkar karmami suna makuwa a jikin kogon tamkar ana watsa tsakuwowi a sama.
Duk da kasancewar Aljanun sun ninka waɗannan DODANNIN yawa sau dari, Amma sai aka Sara Aljanin da zai iya ko kwarzanarsu.
A zahiri dai gashi ana kashe Aljanun ba kaukautawa Amma Kuma sai Kara tuttudowa suke, tamkar yadda tururuwa ke fitowa daga cikin raminta.
Haka aka cigaba da wannan Yakin har sai da aka sake kashe Aljanu sama da Milyan hamsin, ya zamana cewa ragowarsu Bai wuce Milyan Dari ba.
Su kuwa a bangaren dodannin an kashe sama da Milyan Daya.
Koda ganin haka sai zuciyar Aljanun Nan ta Kara tafarfasa Nan fa suka yiwa dodannin nan rubdugu.
Ya zamana cewa sun yanyamesu ta ko'ina kawo Sara sukeyi, sama da Kasa hagu da dama.
Nan fa Suma dodannin suka dage iyakar karfinsu suna jeho dodannin daga samansu, Amma duk da haka sai da Aljanun Nan suka rinka karkarshe su, saboda ance Sarkin yawa yafi Sarkin karfi.
Lokacin aka kashe sama da rabin dodannin nan, ya zamana cewa an kusa Karar da gaba dayansu har sun sakankace da mutuwa.
Ba zato ba tsammani sai kawai akaga wani Jan haske ya yi fitar burtu daga cikin Kogon ya zo ya Doki kirjin Daya daga cikin dodannin nan.
Kawai sai gani akayi dodon yayi sama sannan ya tsaya cak, a cikin iska yana Lilo.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga wannan Jan hasken ya shige a jikin wannan dodo.
Nan fa dodon ya rinka kumbura tamkar ana hura shi da iska, Kasusuwansa suka zama manya-manya jikinsa ya murde tamkar jijiyoyi ne aka sassargafa Masa.
A haka ya rinka cigaba da kumbura Yana Kara girma, har sai da ya ninka girman da yake da shi sau arba'in sannan ya tsaya haka.
Koda ganin wannan Ala'mari sai kowane bangare suka tsaya cak, ga barin yakin.
Gaba dayansu suka kurawa dodon idanu suga abinda zai faru.
Kafin Daya daga cikin su yayi wani yunkuri tuni wannan NARKEKEN DODON ya wangame wannan lafcecen hannun nasa, ya tattaro gaba dayan ragowar dodannin nan wadanda adadinsu yakai dubu dari biyar.
Kawai sai gani akayi ya tattaresu a tafin hannunsa guda, sannan ya wangame tafkeken bakinsa ya watsa su ciki ya hadiye, tamkar digon ruwa Daya tal ya fado Kasa.
Gama hadiye su keda wuya, sai akaga wannan jibgegen dodon ya takarkare ya kwarara wani uban ihu Mai tsananin razanarwa Wanda ya haifar da wata irin iska Mai tsananin karfi, hade da wata tsawa Mai karfin tsiya tamkar sama ke Shirin ruftowa.
Ana cikin hakane akaga wannan Jan hayakin ya fito daga bakin wannan dodon sannan durfafi sauran Aljanun Nan.
Kaico! Idan masifa tazo wadda ba ta da magani to dole ne a saduda.
Koda Jan hayakin Nan ya ratsa ta cikin Aljanun Nan, sai akaga kawunansu ya gutsirewa suna faduwa Kasa matattu.
Koda Aljanun Nan suka ga haka sai suka ruga da baya, da nufin Neman matsera Amma Jan hasken Nan ya tasa su gaba, ya rinka gutsire masu kawuna.
Kafin cikar dakika hamsin ya gama Karar da gaba dayan Milyan Darin da suka rage.
Faruwar hakan keda sai akaga wannan Jan hayakin ya sake dawowa Yana shiga cikin gawarwakin dodannin da aka kashe.
Kafin cikar dakika dari da arba'in ya gama zagaye gaba dayan matattun DODANNIN.
Koda gama wannan Ala'mari sai dukkan dodannin da aka kashe suka sake tashi cikin tsananin Jin karfi tamkar wani abu bai taba samunsu ba.
Sai da dodanni sama da guda Milyan Dari suka tashi rayayyu, sannan wannan Jan hasken ya Kara shigewa a cikin jikin ainihin Katon dodo na farko...
A dai-dai Nan, na gaji da rubutu nake cewa...
Mu hadu a HATSABIBIN ALJANI part B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️♥️🥰 Najibullah Muhammad ✍️✍️🙏**HATSABIBIN ALJANI**
LITTAFI NA BAKWAI 7 ✍️✍️
PART B ✍️♥️❤️
AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING: Najibullah Muhammad 🥷🥷
BARKANMU DA JUMA'A 🤝❤️
A baya idan baku manta ba, mun tsaya ne a inda wannan Jan hayakin ya shige a cikin gangar jikin dodannin da aka kashe.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga dukkansu sun tashi a matsayin rayayyu cikin Jin izza da karfi tamkar wani abu bai taba samunsu ba.
A halin yanxu adadin dodannin nan ya kai kimanin Milyan dari da arba'in, Kuma dukkansu sun jejjera sahu-sahu a gaban wannan Katon dodo.
Kowane daga cikin dodannin na rike da mugun makamin da ko a tarihi ba a taba ganin irinsu ba.
Kamar hadin Baki, sai suka fara wani irin mugun gurnani a lokaci guda Mai tsananin Kara marar dadin ji, Wanda inda bil'adama na wurin kunnuwansa na iya dodewa saboda rashin dadin gurnanin.
Sai da dodannin nan suka shafe dakika dari da tamanin suna wannan gurnani tare da yiwa kansu kirari a bisa ganin irin gagarumar nasarar da suka samu.
Domin su a zatonsu sun gama da gaba dayan makiya..
A bangaren dakarun mutane da Aljanu kuwa dake can wajen Kogon da ake fafatawa, Koda suka ga dodannin nan sun hallaka gaba dayan rundunar Aljanu Milyan Dari, Kuma har ma sun samu nasarar tayar da matattun dodanninsu.
Sai suka razana ainun.
Nan fa zuciyarsu ta fara karaya akan wannan yaki.
Domin lokuta dayawa sai sunzo kamar zasu samu nasarar kashe dodannin gaba Daya, Amma sai a samu akasi su a kashe su.
A bisa wannan dalili ne wasu daga cikinsu suka Yanke shawarar janyewa ga barin wannan yaki su juya da baya.
Batare da Bata lokaci ba, wasu daga cikinsu suka fara juya linzamin dawakansu da nufin komawa gida.
Kwatsam sai suka ga an daka masu wata irin tsawa kamar kwarankwatsa ce ta fado.
Cikin tsananin rudewa da firgicewa kowannensu ya tsaya cak! Suna ta faman duben-duben ta inda wannan Karar ta fito.
Ba zato ba tsammani sai kawai akaga wani Sarki daga cikin jinsin bil'adama ya tako da kafafunsa a hankali yazo a gaban gaba dayan rundunar mutane da Aljanu yana Mai fuskantar su cikin mummunar shigar yaki.
Sarkin ya rufe jikinsa gaba Daya da sulken yaki, sannan a Saman Kansa akwai hular karfen zinare mai tsananin kwari da kauri irin wadda babu makamin da zai iya huda ta.
In Banda idanuwansa babu abinda ake iya gani.
Sarkin na rike ne da wata zabgegiyar takobi wadda aka yiwa wadansu rubuce-rubuce a samanta.
Yanayin rubutun yayi shigen Irin na masu wani irin bakon addinin, da basu yawaita a duniya ba.
Koda Sarkin Nan ya fuskance su cikin natsuwa, sai ya gyara murya Yana Mai cewa.
Yaku 'yan uwana abokan wannan yaki, kuyi sani cewa Kuna Shirin tafka wani babban abun kunyar da har abada bazai taba disashewa ba.
Domin muddin muka juya da baya ga barin wannan yaki, to za'a rubutamu a cikin kundin tarihin duniya cewa mun hada karfi da karfe tsakanin mutane da Aljanu domin yakar halitta guda daya jal! Amma mun kasa nasara, Wanda a sanadiyyar haka muka gudu a filin yaki.
Ai kuwa da hakan ta faru gwara mu mutu gaba dayanmu a wannan wuri, koba komai dai za'a rinka tuna mu a matsayin jarumai.
Saboda haka a yanxu Ina so ku bani wata dama Wanda zanje na yaki wadannan dodanni ni kadai na hallaka su, batare da taimakon Daya daga cikin ku ba, Amma bisa sharadi guda Daya idan Kun yarda.
Koda gama wannan Batu, sai gaba dayan mutane da Aljanun wurin suka bushe da dariya tamkar sun ga mahaukaci sabon kamu.
Bayan sunyi dariyar Mai yawa, sai wasu daga cikin SARAKUNAN mutane da Aljanu suka dube shi suka ce, tayaya kake tunanin cewa zaka iya ganin bayan bala'in da ya gagari milyoyin mutane da Aljanu Kai kadai?
Kuma wannan wane irin sharadi ne?
Sannan Kuma Muna so mu San Sunanka da Kasar da kake Mulki a yankin bil'adama da Kuma irin abunda ka taka, Wanda yasa kace Kai kadai zaka yaki wadannan dodanni?
Koda Jin wannan batu sai Sarkin Nan yayi gyaran murya a karo na biyu sannan ya ce," da farko dai ni sunana SULTAN IBN JABIR.
Sannan Kuma ni ne Sarkin da ke mulkin birnin DAHALASH da ke makwabtaka da birnin SIN.
Haka Kuma ni da dakaruna guda Milyan arba'in mun kasancewa ma'abota Addinin musulunci.
Dangane da tambayarku ta karshe kuwa, shi ne babu abinda sai Allah Ubangijin musulunci Wanda shi ya halicci kowacce halitta dake doron Kasa, da Kuma duk abinda ke cikin sammai da halittun da ke cikin karkashin Kasa.
Shi ne kadai buwayayyen Sarkin da ba ya mutuwa, Kuma baya gajiya akan komai.
Shi ne Sarki Mafi daukaka da Iko akan komai, saboda haka shi kadai ya kamata a kowa ya Bauta mawa.
Haka zalikha ya kasance Mai tsananin rahma ne ga duk bawan da yake Bauta Masa yake Masa biyayya, Amma Kuma ya tanadi azaba Mai radadi ga Wanda ya bijire Masa.
Koda Sarki SULTAN yazo Nan a zancensa, sai wani daga cikin SARAKUNAN Aljanu ya dube shi ya ce to munji batunka, Amma har yanxu baka fada mana sharadin dakace zaka Sanya mana ba, idan har ka yaki dodannin nan Kai kadai Kuma kayi nasara ba.
Cikin murmushi SARKI SULTAN ya Kara dubansu a karo na uku ya ce, ba sharadi bane face inasu muddin nayi nasara akan wannan yaki to gaba dayanku zaku bayar da Gaskiya ga Ubangijin musulunci.
Koda Jin wannan sharadi sai dukkansu sukayi zuru-zuru suna duban junansu an rasa Wanda zai ce wani abu.
Daga can sai wani daga cikinsu ya ce Muna bukatar muyi shawara da 'yan uwanmu sarakuna.
Nan take SARKI SULTAN a yarda da bukatarsu.
Batare da Bata lokaci ba, sarakunan bil'adama suka ware gefe guda suna kus-kus.
Su ma sarakunan Aljanun suka ware can gefe suna tattaunawa akan wannan Ala'marin.
Bayan kamar Dakika sittin suka kammala shawarar sannan suka dawo suka ce sun amince da sharadinsa, Kuma zasu ci gaba da sauraron dawowarsa.
Batare da Bata wani lokaci ba, sukayi sallama da shi ya juya ya shige cikin Kogon Yana mai zare takobinsa.
Koda ganin haka sai sauran sarakunan suka bushe da dariyar mugunta.
Ba wani abu bane suka tattauna akai, face ba zasu taba karbar Addinin musulunci ba, domin Tsafi shi ne abinda suka gada tun zamanjn iyaye da kakanninsu Kuma a kan haka suka ginu.
Tayaya za'a ce rana daya wani ya saukar da su ga barin tsafi, ai abunda ba zai taba yiwuwa ba kenan.
A bisa wannan dalili ne yasa suka Yanke shawarar cewa, da zarar Sarki SULTAN ya samu nasarar kashe dodannin nan gaba dayansu, to su Kuma zasu tare shi su kashe shi da karfin tsiya don kada ma yaje ya yada addininsa a wasu kasashen cikin duniya.
Ala'marin SARKI SULTAN kuwa, lokacin da ya kunna Kai cikin wannan kogo sai yayi arba da rundunar dodanni kimanin guda Milyan dari da arba'in kowannensu na rike da zabga-zabgan sarkoki da makamai kala-kala a hannuwansu.
Sannan Kuma daga can baya, wannan SHIRGEGEN DODON ne ya tare kofar shiga ainihin inda RA'UFUL KALLUS yayi ajiye-ajiyen kayan Tsatsubarsa da dukiyarsa ta yadda babu halittar da zata iya ratsawa ta shiga wannan wuri dole sai ta hanyar wannan Katon dodo.
Lokacin da wadannan DODANNI suka hango SARKI SULTAN ya tunkaro inda suke shi kadai Kuma ya zare takobinsa, sai Suma suka yiwa Daya daga cikin dodannin nan inkiya da nufin yaje ya gama da shi.
Kafin kiftawar Ido dodon ya falfala da azababben gudu yana tunkarar Sarki sultan, tun gabanin ya riskeshi ya jefa Masa wata murtukekiyar Sarkar tsafi da nufin ta kanannade wuyansa.
Amma abun mamaki, sai akaga SARKI SULTAN ya kwallah wata kabbara da karfi sannan ya Kaftawa Sarkar Sara da takobinsa.
Sai gani akayi Sarkar ta tsinke tamkar zare ne aka tsinka.
Cikin tsananin zafin nama SARKI SULTAN ya cillowa wannan dodon takobinsa.
Nan fa takobin ta shillo izuwa kan dodon nan, tana tafe cikin mugun gudu hade da wata Kara tamkar hucin kububuwa.
Koda zuwan takobin sai ta soka kanta a kirjin wannan dodon ta lume a ciki, sannan ta fice fit daga jikinsa ta dawo hannun Sarki SULTAN.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga wannan dodon ya kama da wuta ya kone kurmus Gawarsa ta zama toka.
Koda sauran dodannin suka ga wannan Ala'mari sai gaba dayansu suka ruga izuwa kan SARKI SULTAN suna ihu da Karaji..
Nan fa aka runguntsume da masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro tashin hankali.
Ya zamana cewa dodannin sun yiwa SARKI SULTAN rubdugu sun yayyanme shi ta ko'ina, ko hangoshi ba'a iya yi.
Amma abun mamaki duk wannan Kawanya da suka yi masa sai ta zama ta banza, domin ko kwarzane an rasa Wanda zai iya yimasa saboda tsananin zafin namansa ya wuce misali tamkar walkiya.
Nan ya wanzu Yana Mai kwallah kabbara Yana saran dodannin suna zubewa Kasa jini na tsartuwa a sama Yana Malala a Kasa tamkar teku ce ta balle.
Duk inda mutum ya duba sai dai yaga jini na ta Malala daga jikin sassan jikin dodannin.
Nan fa Kasar kogon ta sauya launi izuwa jaa.
Sai da aka shafe sama da sa'a guda ana wannan gumurzu Amma ko kwarzane an rasa Wanda zai yiwa SADAUKI SULTAN.
A wannan lokaci Sarki Sultan ya Kashe dodanni Milyan Daya.
Irin kisan gillar da Sarki sultan ke yiwa dodannin yayi Muni matuka, domin gunduwa-gunduwa yake yi masu.
Sai dai kaga ya fillewa dodo Kai da hannuwa da kafafu.
Babban abinda yafi daurewa mutane Kai shi ne, ganin yadda takobin Sarki sultan take lumewa a jikin dodannin tamkar ana caka wuka a cikin kabewa.
Alhali kuwa babu makamin da yake tasiri a jikinsu.
Bugu da Kari irin zafin naman da yake Amfani dashi yafi gaban tunani, domin tamkar bacewa yakeyi.
A duk cikin dakika goma yana iya kashe dodanni hamsin.
Lokacin da sa'a uku ta shude, ya kashe dodanni Milyan biyar daga cikinsu.
Nan fa jinin dodannin ya cika kogon gaba Daya, ya zamana cewa yayi yawan da har ya kawowa Sarki sultan iya wuya, dama a wannan lokacin ya fara gajiya ainun.
A lokacin da Sarki sultan yake ta faman iyo a cikin jinin dodannin nan ne, yake cigaba da yakar dodannin ne aka samu akasin wani daga cikin dodannin ya shammace shi ya gabza Masa naushi a