yake gamawa da shi, ta hanyar shammatar sa ya caka Masa mugun bakinsu.
A dai-dai lokacin da wadannan tsuntsayen ne suke ta cafko RA'UFUL KALLUS suna kokarin cinyeshi, wasu daga cikinsu na caka masu bakunansu suna mutuwa, a dalilin yawan fadowa Kasan da yake yi ne yasa ya samu munanan raunika sakamakon yawan fadowa Saman duwatsu da Kuma Saman busassun bishiyoyi masu tsinin resuna.
A sakamakon haka ne yasa gaba dayan jikinsa ya zama wurin zubar da jini, domin da kyar ma yake iya gani saboda tsananin galabaita.
A cikin sa'a guda sai da tsuntsaye dubu arba'in suka daukeshi da nufin hadiyeshi Amma suna jeho shi Kasa a dalilin hallakar dasu da 'yan uwansu ke yi.
A wannan lokacin tsuntsayen da suka rage Basu wuce guda uku ba.
Koda suka Ankara da cewa gaba dayan 'yan uwansu sun hallaka, sai suka fusata ainun.
Nan take suka yunkura su duka ukun da nufin su cafko RA'UFUL KALLUS su datsa shi gida uku su cinye.
Koda RA'UFUL KALLUS ya ga abinda ke Shirin faruwa sai ya takarkare ya falfala da matsanancin gudu tamkar na tauraruwa Mai wutsiya don gujewa wadannan tsuntsayen har tashi sama yake saboda karfin gudun nasa.
Amma duk da haka da zarar ya waigo sai yaga wadannan tsuntsayen suna ta shawagi a Saman Kansa suna kawo masa wafta da kafufuwansu, Kuma suna kawo masa cizo da bakunansu.
Da zarar yaga haka sai ya Kara kaimin gudun.
Nan fa aka Kasa mugun tsere a tsakaninsa da wadannan tsuntsayen, sai da suka kewaye birnin nan gaba dayansu suna gudu batare da sun samu nasarar kama shi ba, Kuma duk Inda suka ci karo da daya daga cikin bishiyoyin nan sai RA'UFUL KALLUS yayi tsalle ya cizgo ganyenta ya jefa a cikin battarsa.
A haka ya samu nasarar tattara gaba dayan ganyayyakin bishiyoyin gaba daya, yana gama wannan aikin ne sai ya debo Kasar birnin ya zuba a cikin battarsa.
A wannan lokacin RA'UFUL KALLUS ya gaji ainun domin har a sannan jini na zuba a jikinsa, bugu da Kari ga Kuma mugun gudun da suka Sha na tsawon sa'a biyar, Nan take jiri ya debe shi ya fadi Kasa sumamme.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga wadannan manyan tsuntsayen guda uku sun Bude tafka-tafkan bakunansu sun cafko sassan jikin RA'UFUL KALLUS a tare a lokaci guda.
Ya zamana cewa Daya ya cafko Kansa, dayan kuwa ya cafko kirjinsa zuwa cikinsa, dayan kuwa ya cafko daga cibiyarsa zuwa karshen Kafafunsa.
Cikin tsananin zafin nama suka yi nufin datsa shi gida uku da nufin kowanne ya cinye abinda ya samu.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai akaga wannan NARKEKEN DODON ya bayyana Wanda ALJANI RA'UFUL KALLUS ya fafata dashi acan birnin kabilun mutanen nan guda dubu, inda bakon Bokan Aljanin nan ya dana wa RA'UFUL KALLUS tarko da nufin hallakar dashi, ta hanyar jefa shi a cikin dakunan Azaba guda dubu.
Kafin wani daga cikin tsuntsayen nan yayi wani yunkuri tuni wannan SHIRGEGEN DODON yasa 'yan yatsunsa guda biyu ya cafko gaba dayan wadannan tsuntsayen guda uku.
Sai gashi ya matse su a cikin tafin hannunsa, take Kasusuwan su suka kakkarye tamkar ana mutsittsike karmami.
Ba shiri suka saki RA'UFUL KALLUS ya fado Kasa a matukar galaibace, cikin tsananin zafin nama wannan GABJEJEN DODON yasa dayan hannun nasa ya cizgo kawunan tsuntsayen duka, sannan ya wangame tafkeken bakinsa ya watsa su a ciki ya taune.
Karar taune kawunan tsuntsayen ya cika birnin gaba Daya, domin ji kake wani gurus-gurus tamkar an zuba tsakuwowi a cikin injin Nika.
Kafin cikar dakika goma ya gama taune su ya hadiye, sannan ya watsa uban jikinsu ya hadiye.
Gama taune su ke da wuya sai dodon nan ya takarkare ya kwarara wani uban ruri Mai tsananin ban tsoro, Wanda yayi sanadiyyar farfadowar Aljani RA'UFUL KALLUS daga dogon suman da ya shiga.
Kafin RA'UFUL KALLUS yace wani abu, tuni wannan murgujejen DODON ya sure shi da Dan yatsa guda, sannan ya wangame tafkeken bakinsa ya jefa shi a ciki ya hadiye.
Nan take RA'UFUL KALLUS ya ganshi ya fado tsakiyar birni na Tara.
Fadowarsa keda wuya yaci karo da wata shirgegiyar macijiya Mai kawuna goma Sha biyu.
Kowane Kai daga cikinsu girmansa ya kai na Katon Dutse, idanunta kwala-kwala ne tamkar na Katuwar bukka.
Tsawon maciyar zira'i Milyan arba'in ne, saboda tsananin tsawonta yasa ta shimfida gaba dayan Gangar jikinta a gaba dayan birnin, ya zamana cewa duk ta inda mutum yabi sai yayi karo da gangar jikin macijiyar nan.
Bugu da Kari duk da haka sai da ta nannade sauran Gangar jikinta cikin birnin. Gaba dayan birnin babu komai sai wannan macijiyar.
Haka zalikha Kuma babu wata halitta sai wannan macijiyar, adaa akwai wasu halittu masu kawunan gwaggwan biri a cikin wannan birni kafin zuwan wannan macijiya.
Su dai wadannan halittu adadinsu ya Kai Milyan saba'in Kuma dukkaninsu sun kasance jibga-jibga tamkar giwaye.
Tun ranar da wannan macijiyar tayo dirar MIKIYA a wannan birnin ya zamana cewa a cikin abinda Bai wuce dakika arba'in ba ta wangame sharba-sharban kawunanta guda goma Sha biyu ta rinka Loma guda da wadannan halittun, sai gashi kafin cikar dakika arba'in ta Karar da gaba dayansu.
Tana kammala hadiyesu ne ta hau gidajen birnin da ci, sai da ta cinyesu gaba Daya Suma, sannan ta hau bishiyoyi da gonaki da gidajen birnin da ci, su ma ta cinye su kaf ta hadiye, a cikin abinda Bai wuce sa'a biyu ba ta cinye komai da kowa dake cikin birnin ya zamana hatta Katangar birnin Bata bari ba, gaba dayan birnin ya zama Fili fetal babu komai samansa, a sannan ne ta nannade gaba dayan jikinta a cikin birnin.
Saboda tsabar tsawonta sai da jikinta ya kewaye gaba dayan birnin, ya zamana cewa duk kusurwar da ka je a birnin sai anga Gangar jikinta..
Koda wannan Katuwar MACIJIYAR tayi arba da RA'UFUL KALLUS a gabanta, sai ta wangame tafkeken bakinta guda ta cafko shi ta hadiye.
Faruwar hakan keda wuya sai RA'UFUL KALLUS yayi arba da bishiyar bangaren gabas a cikin cikin wannan macijiyar, Nan take bayyi wata-wata ba ya cizgo ganyen wannan bishiyar.
Nan take wannan jibgegiyar macijiyar ta kwarara wani uban ihu sakamakon cizgo ganyen bishiyar da yayi.
Nan take ta amayo shi a lokacin da jikinsa yayi luguf-luguf tamkar an dafa shi a cikin tukunya saboda tsabar zafin da ke cikin-cikin macijiyar.
Bayan kamar Dakika sittin ta sake wangame tafkeken bakinta na biyu ta hadiyeshi, Nan ma ya sake ganin bishiyar dake bangaren bangon yamma na Birnin, bayyi wata-wata ba ya sake cizgo ganyenta.
A wannan lokacin saboda tsananin wahalar da macijiyar ta sha har sai da ta fadi Kasa sumamma.
Bayan kamar Dakika arba'in ta farfado Sannan ta sake amayo dashi.
Batare da Bata lokaci ba ta sake hadiye shi da Kai na uku, Nan ma ya ga ganyen bishiyar bangaren kudu Kuma ya cizgo shi.
A wannan lokaci ne saboda tsananin bala'i yasa macijiyar ta wangame gaba dayan bakunanta ta rinka feso wata wuta Mai tsananin zafi da radadi, faruwar hakan keda wuya sai gashi RA'UFUL KALLUS ya biyo wutar Nan ya fado Kasa a matukar galaibace.
A wannan lokacin duk fatar jikinsa ta sassale saboda zafin Wutar da macijiyar ta feso masu.
Bayan kamar cikar dakika Ashirin da biyar macijiyar ta sake jefa shi izuwa Kai na hudu, Nan ma bayyi wata-wata ba ya cizgo ganyen bishiyar bangaren Arewa.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga Jikin macijiyar ya sandare ta zama matacciya.
Ashe daman wadannan ganyayyakin bishiyoyin sune ruhin wannan macijiyar, Kuma daman iyakar ruhin da take dashi kenan guda hudu, a duk lokacin da aka cizgo daya daga cikin ganyayen bishiyoyin take wannan ruhin yake mutuwa, idan kuwa aka samu nasarar cizgo duka ganyayyakin to hakan na nufin mutuwarta.
Koda RA'UFUL KALLUS ya tsinci Kansa a cikin-cikin wannan Katuwar MACIJIYAR, sai ya fito da zabga-zabgan makamansa ya rinka sarar wannan macijiyar.
Bai gushe ba Yana yin haka har tsawon kwanaki bakwai sannan ya samu nasarar huda tumbin macijiyar ya fito waje.
Da fitowarsa sai ya debo Kasar tsakiyar birnin, sannan ya kama hanyar fita birnin gaba Daya.
Sai da yayi tafiyar sa'a goma Sha biyar Yana gudu akan Gangar jikin macijiyar Nan Sannan ya kawo karshenta, ya sauka samanta sai ya tsinci Kansa a cikin birni na goma..
ME ZAI FARU A CIKIN BIRNI NA GOMA?
SHIN ALJANI RA'UFUL NA KAMMALA ZIYARTAR DUKA BIRANEN GUDA DUBU?
WANE IRIN YAKI AKE YI A CAN KOGON BAHAR DURGAFUL KALLUS?
SUWAYE ZASU SAMU NASARA A WANNAN YAKI?
Domin Jin Amsar wadannan tambayoyin sai mu hadu a HATSABIBIN ALJANI na shida don Jin yadda ta kaya..
Daga mai debe maku kewa wato NAJIBULLAH MUHAMMAD ♥️🥰 ke cewa ku huta lafiya Ina maku fatan Alkhairi ♥️❤️✍️✍️🙋
**HATSABIBIN ALJANI**
LITTAFI NA SHIDA 6
PART A 💯♥️
AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷
Whatsapp Num.. 08112778656.
Email add.. najibullahmuhammad405@gmail.com
!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!
Lokacin da Aljani RA'UFUL KALLUS ya shigo cikin birni na goma sai ya cika da tsananin mamaki da Al'ajabi, Kuma zuciyarsa ta kamu da tsananin tsoro tamkar ace kyat ya fita da gudu saboda bala'in da yayi arba da shi a wannan birni.
Ba komai ne ya gani a wannan birni ba, face wadansu jibga-jibgan halittu masu tsananin yawa, Kuma dukkaninsu sun lullube jikinsu da bakaken kaya ba'a iya ganin komai akan siffarsu.
Ba zato ba tsammani sai kawai RA'UFUL KALLUS yayi arba da wannan BAKON BOKAN ALJANIN yana yawo a Saman iska yana mai kyakyata dariyar mugunta.
Bayan kamar dakika arba'in sai Aljanin ya tsuke bakinsa, sannan ya dubi RA'UFUL KALLUS yace, barkanmu da sake saduwa a karo na biyu.
Ya kai RA'UFUL KALLUS kayi sani cewa kayi matukar sa'a da har ka iya tsallake birnin dodannin nan a raye.
Hakika ka cika namijin gaske Kuma jarumi Wanda kayi abun bajintar da ba'a taba samun wani mahalukin da yayi tamkar ka ba.
Bokan Aljanin yaci gaba da cewa, ya kai RA'UFUL KALLUS kayi sani cewa duk burin da kake da shi, nima irinshi gareni.
Kuma a halin yanzu na tsallake manyan matakai sama da guda dari tara da hamsin domin cikar burina.
A halin yanxu matakai hamsin ne kacal suka rage domin na cikar burina.
Wadannan matakai ba wasu bane face ziyartar manyan biranen karkashin Kasa guda dubu kamar yadda kakeyi, Kuma a halin yanxu na wuce birane dari Tara da hamsin, ragowar ne suka gagareni.
Sai da nayi shekara Arba'in ina jarabawa Amma na Kasa iya haura Koda birni Daya daga cikin na cikon hamsin din nan.
Haka Kuma duk wasu masifofi da bala'o'in da kake gani a cikin duk biranen da kake shigowa, to Koda ka kashe masifar da ka riska a cikin birnin kana fita daga cikinshi, wannan masifar zata sake tashi tamkar bata taba mutuwa ba, domin taci gaba da tsaron birninta iyakar ranta saboda Koda wani hatsabibin mutum ko Aljan zai zo daga baya.
Duk wannan bayanin da BOKAN ALJANIN nan yake yiwa RA'UFUL KALLUS, har yanxu wadannan jibga-jibgan halittun suna nan tsaitsaye ko waigo su basuyi ba ballantana suyi Shirin afka masu.
Koda Bakon Bokan Aljanin yazo nan a zancensa, sai RA'UFUL KALLUS ya dube shi ya ce.
Ya Kai wannan hatsabibin Aljani Ina rokon ka da ka sanar dani sunanka da Kuma yadda akayi sihirin tsafinka yake aiki a ko'ina, sannan Ina so ka sanar dani matsayinka a cikin Al'ummar Aljanu, da Kuma irin masifun da zan riska a Nan gaba da Kuma yadda zan kubuta.
Koda Jin wannan tambaya, sai Bakon Bokan Aljanin nan ya sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan ya ce, " ya kai RA'UFUL KALLUS kayi sani cewa da farko dai sunana JUMZAHUL DAUSUS.
Kuma na kasance a karkashin Kasa tsawon shekaru dubu saba'in.
Haka Kuma dalilin dayasa sirrikan tsafina suke aiki anan shi ne, a Ka'idar wadannan birane, duk mahalukin da ya samu nasarar kashe halittun birnin da ya shiga, Kuma ya bar birnin a raye, to da zarar ya Kara dawowa wannan birnin shikenan zai ci gaba da Amfani da sihirin tsafinsa kamar da, haka Kuma bala'in da ke cikin wannan birnin bazasu iya cutar da shi ba.
Dangane da tambayarka ta uku akan son sanin matsayina da Kuma inda na fito da Kuma yadda akayi burinmu ya zamo iri daya da Kuma yadda akayi har na tsallake manyan birane guda tari Tara da hamsin, kayi hakuri ba yanzu zan Amsa maka wannan tambayar ba sai lokaci yayi zaka San komai idan kana da tsawoncin kwana.
Amsar tambayarka ta hudu kuwa akan sanin irin bala'o'in dake gabanka kuwa shi ne, ya Kai wannan Aljani kayi sani cewa na rantse da Karfin sihirin tsafina, bala'in dake gabanka tamkar a rinka debo ruwa ne da cokali a cikin teku, da haka da haka har a kwashe gaban dayan ruwan.
Domin a halin yanzu ko kaso daya daga cikin dubu baka dauka ba.
Wadannan su ne Amsar tambayoyin da kayi min, Kuma daga yanzu ba zamu sake saduwa ba sai ranar da ka samu nasarar wuce birane dari sannan.
Koda gama fadin hakan sai Aljani JUMZAHUL DAUSUS ya bace yana mai kyakyata dariyar mugunta.
Cikin tsananin mamakin abinda Aljani JUMZAHUL DAUSUS ya fadawa RA'UFUL KALLUS yasa yayi shiru Kuma jikinsa yayi sanyi tamkar bashi da laka a jikinsa.
A hankali dai ya rinka tafiya jikinsa ba kwari yana ta sake-sake iri-iri har yazo dab da inda wadannan jibga-jibgan halittun suke batare da ya Ankara ba.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai kawai yaga wadannan halittun sun yaye mayafin dake lullube dasu, cikin tsananin mamaki RA'UFUL KALLUS yayi arba da wadansu Aljanu masu kamanninsa sak tamkar an tsaga gara.
Hatta yanayin girmansa da kirar jikinsa da komai iri daya ne da nasu.
Adadin Aljanun sun kai dubu arba'in.
Kowannensu na rike da muggan makamai irin na RA'UFUL KALLUS.
Koda ganin wadannan Aljanun sai RA'UFUL KALLUS ya juya da baya da nufin ficewa daga cikin birnin, cikin tsananin zafin nama wadannan Aljanun suka rugo da gudu suka Sha gabansa, nan take sukayi Masa Kawanya.
Koda ganin wannan Ala'mari sai RA'UFUL KALLUS ya tsaya yana mai fuskantar wadannan Aljanun, sannan ya Kara rike makamansa dakyau.
Koda ganin haka sai wadannan Aljanun suka kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya, nan take guda dubu daga cikinsu suka rugo gareshi suna ihu da Karaji.
Ana haduwa aka kacame da masifaffen azababben yaki mai tsananin ban tsoro tashin hankali gumurzu, ya zamana cewa RA'UFUL KALLUS ya takarkare iyakar karfinsa wajen yakar Aljanun amma kamar a banza, domin Koda ya sari jikin daya daga cikinsu sai yaji tamkar dutse ya Sara domin ko Kwarzanewa bayayi.
Amma saboda tsananin zafin namansa ya wuce misali yasa Aljanun suka Kasa Koda lakutar jikinsa, domin yana iya kare gaba dayan hare-haren Aljanun guda dubu a lokaci guda.
Haka Kuma idan yaga sun yanyameshi suna neman kamashi, sai yayi Amfani da karfin damtsensa ya rinka bangaje su, suna zubewa Kasa.
Su kuwa da zarar sun fadi Kasa sai kaga tamkar Saman sifirin suke fadawa, domin kamar walkiya haka suke tashi suci gaba da GUMURZU.
Sai da aka shafe sa'a guda da rabi ana wannan gumurzu batare da dayansu ya samu nasarar komai ba.
Koda ganin haka sai ran Shugaban Aljanun ya baci Kuma zuciyarsa ta harzuka bisa ganin cewa a matsayinsu na manyan sadaukan Aljanun da babu kamarsu a duk fadin duniyar karkashin Kasa Amma ace wani bakon Aljani mai kama da su, Yana Neman gagarar yaransa.
Kawai sai akaga wannan jibgegen shugaban Aljanun ya daka tsalle sama daga can gefe guda tamkar an cillo shi daga cikin baka ya diro a gaban RA'UFUL KALLUS, kafin RA'UFUL KALLUS yayi wani yunkuri tuni wannan murgujejen Aljanin ya cafko wuyansa da hannu daya ya daga shi sama sannan ya fyadashi da Kasa, saboda karfin kayen sai da RA'UFUL KALLUS ya Suma.
Nan take Aljanin yayiwa sauran yaransa Umarnin a daure RA'UFUL KALLUS a cikin Sarka, sannan a dauko shi a kaiwa Sarkinsu.
Nan take suka cika Umarni sannan suka dauke shi suka dunguma gaba dayansu izuwa cikin birnin.
Sai da sukayi tafiyar dakika dari da arba'in sannan suka iso tsakiyar birnin inda suka tsaya a wani katafaren gidan sarauta Wanda aka Kawatashi da zallan danyen yakutu Mai kyalkyali aka suranta ginin fadar da siffar dawisu.
Komai wayewar mutum ko Aljan idan ya zo wannan fada sai ya zamo cikakken dan kauye saboda yanda aka shirya fadar, sannan akayi mata ado iri-iri, tare da zuba mata kayan alatu kala-kala.
Bugu da Kari a gaba dayan gidan sarautar a haskake yake koyaushe, saboda tsananin hasken da yake da shi ko allura ce ta fadi Kasa sai an ganta, Kuma hasken a kowane lokaci Yana nan, wannan yasa Aljanun da ke rayuwa a gidan sarautar basu iya gane lokacin dare da lokacin Rana.
Lokacin da wadannan Aljanu suka karaso fadar birnin, sai suka tsaitsaya sannan suka watsawa RA'UFUL KALLUS ruwa ya farfado daga dogon suman da yayi, kwatsam sai yaganshi a daddaure a cikin Sarka, Kuma a cikin wata Kasaitacciyar fada Mai matukar kyau da kawatuwa.
Ana cikin hakane aka hango SARKI tafe Dakaru na take Masa baya.
Wani shirgegen Aljani ne Wanda yafi kowa girma a birnin.
Sannan Yana sanye ne da zallan lu'u-lu'u, Zinari, da jauhari mai launin Kore a jikinsa.
A Saman Kansa akwai hular karfen zinare wadda aka yiwa kira da siffar Zaki.
Nan take Sarkin yazo cikin fadarsa sannan ya zauna Kan KARAGARSA.
Koda RA'UFUL KALLUS yayi arba da wannan SARKI sai ya Kara cika da tsananin mamaki, domin gani yayi shi kanshi Sarkin kamanninsu iri daya ne sak ba wani bambanci, sai dai kawai ace Sarkin ya fishi girman jiki da Kuma IZZAR MULKI.
Nan take Sarkin nan ya dubi shugaban Aljanun da suka kawo RA'UFUL KALLUS Sannan ya ce, " An gaishe ka ya kai Sarkin yaki FARZILUL KUWAIS, tabbas yau kayi aiki mai girma Kuma mai matukar muhimmanci na kamo mana babban makiyinmu wato RA'UFUL KALLUS wanda yazo domin ya debe mana ganyayen bishiyoyi hudu da suke bawa birninmu kariya daga kowane irin bala'i.
A sakamakon haka ne yasa zan sakanka maka da kyauta Mai tsananin yawa, sannan Kuma zanyiwa wannan hatsabibin Aljani azabobi kala-kala har guda dubu sannan daga bisani nayi Masa mummunan kisan gillar da ba'a taba yiwa wani irinsa ba.
Yana gama wannan jawabin ne, ya dubi Sarkin yaki FARZILUL KUWAIS a karo na biyu, sannan ya ce na umarceka akan ka je ka Kai RA'UFUL KALLUS kurkukunmu mai dakunan azabobi guda dubu ka jefa shi ciki, Kuma ka umarci masu tsaron gidan kurkukun dakyau akan su Saka idanu akansa da kyau, Kuma kada suyi wasa wajen gana Masa azaba a koyaushe.
Nan take Sarkin yaki FARZILUL KUWAIS ya cukuikuyi RA'UFUL KALLUS da hannu daya sannan ya tafi da RA'UFUL KALLUS izuwa wannan kurkuku.
Da zuwansu sai aka Bude masu Kofa, suka kunna Kai ciki.
Da shigarsu kurkukun RA'UFUL KALLUS yayi arba da yanayin kurkukun da Kuma matsaran da aka zuba a cikin gidan.
Kurkukun Yana dauke da dakuna guda dubu, kowane daki akwai Aljanu guda masu ganawa duk fursunan da aka jeho azaba Mai radadi.
Koda RA'UFUL KALLUS ya lura dakyau sai yaga Ashe gaba dayan halittun da ke cikin birnin irin siffarsa garesu mazan su da matansu.
Yana cikin wannan tunani ne yaji an cafke shi an jefa shi izuwa daki na farko...
Sai mu hadu a part B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi da debe kewa ✍️✍️🙏🙏**HATSABIBIN ALJANI**
LITTAFI NA SHIDA 6 ♥️
PART B ✍️💯
AUTHOR : NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷
Whatsapp Num...08112778656.
Zai rinka zuwa maku duk bayan juma'a insha Allah ✍️✍️🙏🙏
-------------------------------------------------
Lokacin da wadannan DAKARUN ALJANU suka jefa RA'UFUL KALLUS daki na daya daga cikin Kurkukun azaba da aka kawo shi.
Koda shigarsa cikin dakin sai yayi arba da wasu murtuka-murtukan Aljanu wadanda duk sun ninka shi girma da karfi da komai.
Kowannensu na rike da zabgegiyar takobi Mai kyalli tamkar wasu fitilu ne aka Sanya mata, domin takubban sun haskeken dakin da matukar haske.
Adadin wadannan Aljanun ya Kai dubu.
Koda ganin RA'UFUL KALLUS a cikin wannan dakin sai suka gareshi gaba dayansu kowannensu ya daga falleliyar takobinsa da nufin daddatsa jikin RA'UFUL KALLUS, Koda ya fahimci nufinsu sai Shima ya takarkare ya kwarara uban ihu Mai tsananin razanarwa sannan ya zare muggan makamansa ya tunkare su.
Duk da cewar RA'UFUL KALLUS yayi matukar razana da yin arba da wannan ALJANU, domin ya tabbatar da cewa sun fishi karfi nesa ba kusa.
Amma Kuma sai yaga gwara ya tunkaresu a fafata wakila yayi masu barna kafin a kasheshi, saboda masu iya magana sun ce Dan hakin da ka Raina shi ke tsone maka Ido..
Lokacin da aka hadu sai aka runguntsume da sabon masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro da tashin hankali Wanda a kowane lokaci rayuwar su na iya salwanta.
Nan fa suka wanzu suna masu kaiwa junansu Sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta tamkar jikinsu ba na jini da tsoka bane.
Babban abinda yafi bawa RA'UFUL KALLUS mamaki shi ne, ganin yadda karfinsa da zafin namansa ya ninku ninkin ba ninkin.
Domin saboda tsananin zafin namansa har yanzu ko sau Daya an rasa Aljanin da ya iya saransa, Yana iya kaucewa harin Aljanu Dari a lokaci guda.
Haka Kuma a duk cikin dakika guda Yana iya Kai Sara sau tamanin, Amma babban abinda yafi daure Masa Kai shi ne, ganin yadda makamansa basa yin tasiri a jikin Aljanun.
Domin duk lokacin da ya sari jikin daya daga cikinsu sai dai yaji wata Kara tamkar an buga gudumar karfe akan dutse, har wani farin Hayaki ne ke tashi sama.
A bisa wannan dalili ne Karar saran Aljanun ya yawaita sannan Hayaki ya cika dakin gaba daya ya zamana cewa har bama su iya ganin RA'UFUL KALLUS.
A sakamakon haka ne yasa suka rinka kai hari a cikin duhu batare da suna ganin RA'UFUL KALLUS ba, Nan take suka fara kakkashe junansu.
Domin Koda RA'UFUL KALLUS yaga haka sai ya koma can kuryar dakin ya kura masu idanu, yaga yanda suke yakar junansu da muggan Takubbansu.
Kafin cikar dakika Dari da arba'in wadannan Aljanun sun kashe sama da guda dari Tara daga cikinsu, ya zamana cewa ragowarsu bata wuce hamsin ba.
A wannan lokacin ne suka Ankara cewa ai RA'UFUL KALLUS baya cikinsu duk junansu suke kashewa, Nan take suka Dakata da yakin sannan suka duba da kyau, sai suka hango shi can ya sake a jikin wata kusurwa mai duhuwa, Koda ganin haka sai suka ruga da guda izuwa kanshi da nufin yi masa kisan gilla.
Cikin tsananin jarumtaka RA'UFUL KALLUS ya daka wani wawan tsalle sama daga inda yake tamkar an cilla shi sama, sai gashi ya diro akan wuyan wadannan Aljanun.
Nan fa ya rinka tattara gaba dayan karfinsa Yana kama wuyansu ya murde, sannan ya jefar da Gawarsa.
A duk lokacin da RA'UFUL KALLUS ya dira akan wuyan daya daga cikinsu da nufin murdewa, sai dai kaga sama da Aljanu goma sun kawo masa Sara a Saman da nufin tsargeshi gida goma, Amma sai dai ya goce cikin tsananin zafin nama tamkar walkiya sun fillewa Dan uwansu Kai.
A bisa wannan dalili ne yasa cikin dakika hamsin kacal suka Karar da gaba dayansu ya zamana cewa babu sauran aljani a tsaye, face wani Aljani Wanda tsawonsu Daya da RA'UFUL KALLUS.
Nan take RA'UFUL KALLUS yayi wata katantanwa a sama ya Doki kirjin Aljanin, sai gashi yayi baya luu tamkar an janye shi da Kugiya yaje ya gwaru da bangon dakin ya dawo, cikin tsananin zafin nama kamar kiftawar Ido RA'UFUL KALLUS yasa hannuwansa ya murde Masa Kai ya fadi Kasa matacce.
Cikin tsananin zafin nama ya zare gaba dayan kayan jikin wannan aljanin Sannan ya Saka a jikin sa.
Faruwar hakan keda wuya sai ya fito wajen gidan kurkukun a matsayin badakre Yana ta kalle-kallen gidan tare da nazarin abinda ya kamata yayi....
Wannan shi ne abinda ya faru a birni na goma bayan an jefa RA'UFUL KALLUS a gidan kurkuku Kuma har ya samu kubuta daga cikin daki na farko...
Ala'marin wadannan DODANNIN kuwa.
Lokacin da suka jefa su SARKI ZURUKUL TARGUL a cikin wannan ragar karfen, sai suka sake fitowa cikin filin daga dauke wasu irin majaujawar karfe Mai tsinaku-tsinaku Wanda duk abinda aka maka mawa, sai abun ya dagargaje.
Nan fa ALJANI Mai jagorantar rundunar Aljanu ta uku ya dubi jinsin bil'adama ya ce, a wannan karon dole sai mun hada karfi da karfe domin yakar wadannan dodannin, saboda haka ku ma ku turo runduna Daya sai mu hadu mu tunkari wadannan dodannin, ta yadda zamuyi yawan da bazasu iya nasara akan mu ba.
Nan take wani Sarki daga jinsin bil'adama ya yarda da wannan shawara Kuma ya fito waje tare da dakarunsa guda Milyan arba'in, Koda ganin haka sai Shima SARKI DANKAZU ya fito waje tare da Dakaru Milyan Dari.
Koda suka hadu sai suka zaburi dawakansu gaba dayansu suna ihu da Karaji suka tunkari wadannan dodannin rike da muggan makamai.
Koda ganin haka sai Suma dodannin suka rinka wurwura majaujawar karfen nan suna jeho masu ita tana cakewa a jikinsu.
A duk lokacin da majaujawar