Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 8
yaki Kuma har sun fara jaa da baya sai ransa ya Baci, sannan ya dakawa Sauran rundunonin tsawa akan su dena guduwa, sannan ya fito waje shi kadai. Kuma yayi masu nuni akan su zuba Masa idanu Kar Wanda ya biyo shi. Nan take ya fito filin yakin ya tsaya shi kadai Yana Mai fuskantar wannan Katon dodo. Lokacin da wannan jibgegen dodon yaga SARKI ZURUKUL TARGUL ya fito shi kadai da nufin tunkararsu sai ya takarkare ya wangame wawakeken bakinsa ya kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya wadda ta haddasa kogon ya rinka girgiza kamar zai ruguje, har sai da Duwatsun cikin kogon suka rinka bantarowa suna fadowa saboda tsabar karfin dariyar. Nan take komai ya hautsine har sai da dodon ya rufe bakinsa sannan kogon ya dena girgiza. Nan take SARKI ZURUKUL TARGUL ya zare wani sihirtaccen zungureren mashinsa Mai tsananin Kaifi da tsini Yana Mai fuskantar wannan dodo. Koda dodon yaga haka, sai ya zuro Dan yatsansa guda da nufin ya talitse SARKI ZURUKUL TARGUL. Cikin tsananin zafin nama SARKI ZURUKUL TARGUL ya daka tsalle sama ya haye kan tafin hannun wannan dodon sannan ya daga mashin iyakar karfinsa ya caka akan babban Dan yatsan dodon. Faruwar hakan keda wuya sai akaga mashin ya lume a jikin Dan yatsan, nan take Dan yatsan ya fara zagwanyewa Yana zabtarewa Yana faduwa Kasa, tamkar Katuwar gaba na fadowa cikin teku. Koda ganin wannan Ala'mari sai dodon nan ya kwarara wani uban ihu, sannan ya cilla SARKI ZURUKUL TARGUL a cikin bakinsa da nufin ya taune shi ya hadiye. Faruwar hakan keda wuya sai akaga SARKI ZURUKUL TARGUL ya rikide ya zama wuta, sannan ya fada cikin Katon bakin dodon. Nan fa aka ga wannan Katon dodo ya haukace Yana ta dukan ko'ina da Ina a cikin kogon saboda zafin Wutar. Kafin a jima duk ya kusa ruguje gaba dayan kogon Dutsen saboda tsananin dimaucewa. Nan take akaga sashin wannan dodon na bangaren dama ya kama da wuta Kurmus sannan ya tarwatse yayi filla-filla. Kafin wani daga cikinsu yayi wani yunkuri tuni wannan dodon ya rikide ya dawo ainihin siffarsu ta da, Wanda a wannan lokacin adadinsu Bai wuce Milyan Talatin ba, gaba dayan dodanni sama da Milyan Dari da sittin sun mutu Kuma sun kone kurmus. Koda ganin wannan nasara, sai sama da rundunar Aljanu Milyan hamsin suka rugo ga SARKI ZURUKUL TARGUL suna masu tsananin farin cikin wannan nasara da ya samu. Koda zuwansu sai suka yayyanme Sarki ZURUKUL TARGUL suna masu jin-jina Masa. A lokacin da aljanun Nan suka shagala wajen yiwa SARKI ZURUKUL TARGUL jin-jina akan wannan gagarumar nasara ne, su Kuma wadannan DODANNI suka fakaici idanunsu suka daka wani wawan tsalle sama suka fesa masu wata irin muguwar hodar banju. Nan take gaba dayan wadannan Aljanun sama da Milyan hamsin suka bingire Kasa suna ta sharbar barci abinsu. Faruwar hakan keda wuya sai akaga wadannan dodannin sun tattaresu gaba dayansu sun jefa su a cikin waccan ragar karfen da suka jefa Aljanun farko ciki, sannan sun Kara daure bakin ragar ram sun Kara fitowa waje rike da muggan makamai... Wannan shi ne abinda ya faru a Kogon BAHAR DURGAFUL KALLUS bayan an fafata kazamin yaki a tsakanin DODANNIN Aljani RA'UFUL KALLUS da Kuma wadannan mayakan Aljanu da mutane.. A bangaren ALJANI RA'UFUL KALLUS kuwa. Lokacin da ya shiga birni na hudu, sai ya iske gaba dayan birnin babu gida ko bishiya ko Daya. Sannan babu dabbar gida ko daji ko Daya. Gaba dayan birnin SAHARA ce Mai tsananin laushi, sannan Kuma saharar a shimfide take babu tudu da kwari. Idan ya tsaya daga inda yake Yana hango abinda ke can gaba, Wanda sai anyi kusan tafiyar kwana bakwai kafin a riske shi. Lokacin da ALJANI RA'UFUL KALLUS ya tsinci Kansa a cikin wannan birnin sahara sai ya shiga tunanin tayaya zai gane ainihin tsakiyar birnin, Kuma tayaya zai gano inda wadannan bishiyoyi suke alhalin gaba dayan birnin babu bishiya ko guda. Haka dai RA'UFUL KALLUS yaci gaba da tafiya yana ta tunani a cikin zuciyarsa. Yana cikin wannan hali ne hango wata iska Mai tsananin karfi ta yo kanshi, Nan take aka Kasa tsere tsakaninsa da wannan iskar. Cikin dakika hamsin wannan iskar ta kurewa Aljani RA'UFUL KALLUS gudu sannan ta lullube shi sai gashi rairayin Sahara ya rufe gaba dayan Gangar jikin RA'UFUL KALLUS ya zamana cewa iyakar Kansa kawai ake gani. Nan fa yayi iyakar kokarinsa don ganin ya fito daga cikin saharar Nan Amma Abu ya gagara. Bisa dole ya dangana a haka har tsawon sa'a arba'in ba ci ba Sha. A cikin kwana na biyu ne, RA'UFUL KALLUS ya hango wata shirgegen macijiya ta keto cikin wannan Sahara tayo kanshi tana Neman abinci. Koda ya fuskanci cewa wannan macijiyar ta ganshi, Kuma muddin ta riskeshi a wannan wuri to sai tayi Loma guda dashi. Sai ya takarkare iyakar karfinsa yayita jijjiga jikinsa har ya samu Kasar da ta rikeshi tayi sakwa-sakwa sannan ya fito fit daga cikinta. Koda fitowarsa sai wannan macijiyar tayi arba tashi, Nan take tayo kanshi da nufin Loma guda da shi. Faruwar hakan keda wuya sai aka Kasa mugun tsere a tsakaninsa da wannan macijiyar. ALJANI RA'UFUL KALLUS gudu yake iyakar karfinsa don gujewa wannan murtukekiyar macijiyar, Amma da zarar ya waigo sai yaga wannan mummunar macijiyar dab dashi tana fito da zabgegen harshensa tare da furzar da mugun bakin dafi a kusa da shi. A wani lokacin ma idan ta Mika harshenta gaba sosai, har laso bayan RA'UFUL KALLUS takeyi. Nan fa RA'UFUL KALLUS ya kamu da tsananin razana domin gashi dai Yana gudu iyakar karfinsa kamar ya tashi sama, Amma har yanzu tazararsa da wannan macijiyar Bata wuce taku biyar ba, domin saboda tsabar yawan laso bayanshi da take yi duk jikinsa ya jike sharkaf da mugun yawun macijiyar. Yana cikin gudu ne Yana tunanin hanyar da zai gujewa wannan macijiyar ne, ya hango bishiyar farko ta karshen birnin bangaren yamma. Koda ganin haka sai farin ciki ya kama shi, Nan take ya ruga ya daka tsalle sama ya maƙale can Karshen bishiyar. Da zuwan wannan macijiyar gindin bishiyar nan sai ta nannade wannan bishiyar da wutsiyarta sannan ta tugo gaba dayan bishiyar. Koda Aljani RA'UFUL KALLUS yaga haka sai ya cizgo wasu ganyaye daga jikin bishiyar sannan ya daka tsalle sama ya duro Kasa yaci gaba da falfala azababben gudu, ita kuwa macijiyar sai tayi wurgi da wannan bishiyar sannan ta Kara bin RA'UFUL KALLUS. Haka dai aka ci gaba da gudu tsakanin wannan macijiyar da Kuma RA'UFUL KALLUS, har sai da suka zagaye birnin nan gaba daya batare da sun tsaya ko ba dakika Daya ba. Kuma duk Inda suka ci karo da wannan bishiyar sai RA'UFUL KALLUS ya maƙale samanta ya cizgo ganyenta sannan abunda ya faru da bishiyar farko ga wannan macijiyar haka yake faruwa da sauran bishiyoyin har suka zagaye birnin gaba Daya. Sai da ALJANI RA'UFUL KALLUS sukayi kwana arba'in suna gudu tsakaninshi da wannan macijiyar batare da sun tsaya ko sau Daya ba. A hakane ya samu nasarar debo gaba dayan ganyayyakin birnin tare da Kasar tsakiyar birnin, a sannan ne ya tunkari hanyar barin birnin. Nan fa RA'UFUL KALLUS yaci gaba da gudu iyakar karfinsa har Yana faduwa Kasa Yana tashi saboda tsananin Gajiya. A haka sai da suka Kara kwanaki goma ya zamana cewa sunyi gudun kwana hamsin ba Hutu, a wannan lokacin numfashin RA'UFUL KALLUS Yana sarkewa har Kafafunsa na hardewa Yana faduwa. Dakyar da sidin goshi ya fito daga birnin sahara, ai kuwa yana fita sai ya fadi Kasa sumamme saboda tsananin Gajiya da yunwa da kishirwa. Bai farfado ba sai bayan kwanaki biyu, lokacin da aka yi ruwan sama ya Dake shi. Bayan farfadowar sa ne ya nemi 'yayan itatuwa Yana ci tare da Shan ruwa har ya samu kwarin jikinsa sannan ya kunna Kai izuwa birni na biyar.... Mu hadu a HATSABIBIN ALJANI na uku part B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️♥️🥰🥰**HATSABIBIN ALJANI** LITTAFI NA UKU ✍️✍️ PART B ✍️💯 AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷 Whatsapp Num... 08112778656. Lokacin da ALJANI RA'UFUL KALLUS ya tunkari birni na biyar, da zuwansa bakin birnin sai ya iske wata Katuwar Katanga mai tsananin tsawo da kauri ta kewaye birnin gaba daya. Nan fa ya fara kewaya Katangar domin ya samo hanyar shiga birnin Amma bai alamar wata kofa ba, sai da yayi tafiyar sa'a biyu Sannan yaga wata irin murtukekiyar kofar karfe, wadda akayi ta da zallan lu'u-lu'u mai kwarin tsiya. Koda RA'UFUL KALLUS ya dafa kofar da hannunsa guda sai yaji ta bude. Yana kunna Kai cikin birnin sai ya ci karo da wadansu dakuna da aka jejjera kimanin guda goma. Koda ya lura da kyau sai yaga ashe babu hanyar da za'a bi a shiga cikin birnin dole sai anbi ta cikin kowane daki. Bugu da Kari gaba dayan dakunan dundum suke, Kuma duk dakin daka shiga take kofofin dakin suke rufe kansu. Koda shigar Aljani RA'UFUL KALLUS wannan daki na farko sai yayi nufin ya juyo da baya domin Bai ga hanyar wucewa ta cikin dakin ba, Nan ma sai ya ga kofar ta shafe tamkar bata taba wanzuwa ba. Ba zato ba tsammani sai kawai yaga wadansu zabga-zabgan Aljanu masu matukar yawa sun bayyana a gabansa rike da manya-manyan bulalu na wuta. Da zuwansu basuyi wata-wata ba suka fara Zane ALJANI RA'UFUL KALLUS da wadannan bulalu na wuta sannan suna bacewa. Duk Aljanin zurawa RA'UFUL KALLUS bulala sai kaga Aljanin ya bace tare da bulalarshi, sannan wani Aljanin ya bayyana ya sake dukanshi. Su dai wadannan Aljanu adadinsu ya Kai dubu, Kuma kowannensu na rike da zabga-zabgan bulalun wuta wadanda duk Wanda aka buga dasu take wurin yake darewa sannan ya kone . Nan fa Aljanun Nan sukayi ta Zane ALJANI RA'UFUL KALLUS shi kuwa Yana ta kwallara ihu, har sai da gaba dayan Aljanun suka gama Zane shi sannan yayi shiru. Lokacin da wadannan Aljanun suka gama Zane shi gaba dayan jikinsa yayi kaca-kaca da raunika Amma babu digon jini ko guda saboda wutar da tayi ta Kona shi. Da kyar da sidin goshi RA'UFUL KALLUS yaje karshen wannan daki sannan ya dafa bangon dakin, faruwar hakan keda wuya sai yaga kofar daki ta biyu ta bayyana. Nan take ya kunna Kai cikin dakin, wannan kofar ta Kara rufe kanta tamkar bata taba wanzuwa ba. Faruwar hakan keda wuya sai yaga gaba dayan raunikan da ke jikinsa sun bace bat, jikinsa ya koma tamkar babu abinda ya taba samunsa Kuma yaji kwarin jikinsa. Nan fa ya tsaya yana kalle-kallen abinda zai faru da shi a wannan dakin. Kafin yayi wani yunkuri sai yaga wani tafasasshen ruwa mai tsananin gudu yana ta bulbulowa ta Kasan dakin, cikin abinda bai wuce dakika goma ba dakin ya cika tab, da wannan tafasasshen ruwa. Nan fa RA'UFUL KALLUS yayi ta tsandara ihu saboda jinshi a cikin wannan tafasasshen ruwa. Kafin cikar dakika hamsin gaba dayan fatan jikin RA'UFUL KALLUS ya sulbe sannan jikinsa duk ya kukkumbura tamkar Gawar da tayi kwana da kwanaki ba a binne ba. Kafin cikar wata dakika hamsin din, sai wannan ruwan ya janye kanshi ya tsotse a cikin Kasa. Faruwar hakan keda wuya sai yaga gaba dayan jikinsa ya fara ciccikowa wata sabuwar fata tana lullube jikinsa har sai da ya koma tamkar babu abinda ya taba samunshi. Kafin RA'UFUL KALLUS yayi wani tunani kawai sai yaga wani ruwa Mai tsananin sanyi Yana ta bulbulowa ta Kasan dakin tamkar yadda wancan na farkon yayi. Cikin abinda Bai wuce dakika goma ba, ruwan ya cika dakin gaba daya. Koda Gangar jikin RA'UFUL KALLUS ta nutse a cikin ruwan nan, sai gaba dayan ruwan ya daskare ya zama kankara, tun RA'UFUL KALLUS na kwallara ihu har gaba dayan jikinshi ya daskare ya zama kankara ya zamana cewa ko dan yatsansa baya iya dagawa. Nan take wannan daskararriyar kankarar ta rinka matse shi, har sai da ta kakkara Masa gaba dayan Kasusuwan Dake jikinsa sannan RA'UFUL KALLUS ya dige ya zama ruwa saboda bala'i. Faruwar hakan keda wuya sai wannan daskararriyar kankarar ta zuke kanta komai ya bace, sannan Kuma sai jikin RA'UFUL KALLUS ya dawo dai-dai tamkar babu abinda ya faru da shi. Nan take ya ruga da nufin zuwa karshen wannan dakin ya taba bangon dakin domin fita daga wannan masifa, Amma kafin ya Kara daga kafarsa ta biyu tuni wannan tafasasshen ruwa ya sake dawowa ya cika dakin sannan ya maimaita irin yadda yayi Masa da farko. Haka dai RA'UFUL KALLUS ya kasance cikin bala'i da masifa a wannan dakin, ya zamana cewa sai da akayi sa'a biyu tafasasshen ruwa da daskararriyar kankarar Nan suna azabtar da shi, idan wannan ruwan ya fito ya azabtar da shi sai ya zuke dayan ya sake fitowa. Haka ya wanzu har tsawon sa'a biyu Sannan suka dena, har yaje karshen wannan daki ya dafa bangon dakin. Dafawarsa keda wuya sai dakin ya Bude sannan ya kunna Kai cikinsa. Da shigarsa cikin dakin sai kofar dakin ta bace bat, sannan wani duhu Mai tsanani ya mamaye dakin. Kafin RA'UFUL KALLUS ya Ankara tuni wata shirgegiyar macijiya ta bayyana a cikin dakin. Da ganin wannan maciyar sai ya razana ainun sannan ya ruga da nufin zuwa karshen dakin, kafin ya Isa karshen dakin tuni wannan Katuwar MACIJIYAR ta wangame lafkeken bakinta ta cafko RA'UFUL KALLUS sannan ta yi Loma guda dashi. Sai da zafin cikin macijiyar nan ya dafa RA'UFUL KALLUS jikinsa yayi luguf-luguf tamkar tamkar mangwaron da aka daddakuna. Bayan kamar shudewar dakika hamsin sai ga wannan macijiyar ta amayo dashi, nan fa jikin RA'UFUL KALLUS ya dinga karkarwa tamkar Mai Jin sanyi. Nan take wannan jibgegiyar macijiyar ta sake rankwafo da kanta sannan ta cafko RA'UFUL KALLUS ta sake yin loma guda da shi, bayan wasu dakiku ta sake amayo shi. Haka dai wannan macijiyar ta rinka hadiyar RA'UFUL KALLUS tana amayo shi, har sai da ta hadiye shi sau dubu sannan ta amayo shi ta bace bat. A wannan lokacin tuni ALJANI RA'UFUL KALLUS ya Suma, Kuma numfashinsa ya dena harbawa. Sai da ya shafe sa'a guda sannan ya farfado, ya taho da Jan kafafu ya dafa bangon dakin na hudu. Dafawarsa keda wuya sai kofar dakin ta bayyana sannan ya kutsa Kai cikin dakin, da shigarsa sai kofar ta rufe kanta sannan ta bace. Koda RA'UFUL KALLUS ya tsinci kanshi a cikin wannan daki na hudu, sai yaga jikinsa ya koma kamar daa, duk wani zafin jiki da ciwo da yake ji ya bace. Faruwar hakan keda wuya sai yaga wadansu jibga-jibgan KUNAMU masu matukar girma tamkar giwaye. Su dai wadannan KUNAMU adadinsu ya kai dubu. Koda wadannan KUNAMU suka kyallara Ido suka ga RA'UFUL KALLUS a tsakiyarsu, sai sukayi Masa Kawanya sannan gaba dayan su suka afka Masa, a lokaci guda suka kafta Masa mugun Sara da wannan mugun qarin nasu mai tsananin zafi. Faruwar hakan keda wuya sai akaga RA'UFUL KALLUS ya fadi Kasa sumamme jikinsa ya fitar da wasu kofofi manya-manya inda wadannan KUNAMU suka harbe shi. Ba zato ba tsammani sai kawai akaga wannan fatar ta jikin RA'UFUL KALLUS ta sabule kanta sannan wata sabuwar fatar ta fito Masa, Nan take ya sake mikewa tsaye tamkar babu abinda ya same shi. Koda kunamun Nan suka ga haka, sai suka Kara dankara Masa Harbin da yafi na wancan, Nan take fatar jikinsa ta sake ratattakewa ta lalace Kuma ta sabule kanta, wata sabuwar fatar ta fito. Haka dai wadannan KUNAMU suka rinka azabtar da RA'UFUL KALLUS da harbi da cizo, har sai da sukayi Masa azaba kala dubu sannan suka bace. Lokacin da suka kammala Masa azaba kala ta dubu din ce, suka bace wata sabuwar fatar ta fito Masa. Amma duk da haka sai da ya shafe dakika hamsin Yana bulbula aman jini bakikkirin Mai yauki da kauri tamkar an kada lalle, sannan ya samu lafiyar iya mikewa tsaye. Nan take ya yaje karshen dakin sannan ya dafa bangon dakin, Nan take kofa ta bayyana sannan ya kunna Kai ciki, kofar ta bace bat. Faruwar hakan keda wuya sai yaganshi cikin wani daki Mai matukar fadi, Wanda aka daddaure wasu sharba-sharban takubba da sarkoki masu matukar girma da kaifi a Saman dakin. Da shigarsa cikin wannan dakin, Yana daga kafar farko sai yaga wata sharbebiyar takobi ta cillo da gudu sannan ta lafta Masa wani mummunan Sara a kafada, take takobin tayi Masa wani lafcecen rauni Mai zurfi jini ya kama shatata. Cikin tsananin dimaucewa sai ya ruga da nufin riskar karshen dakin, Amma sai yaga sama da takubba Dari biyu sun cillo da gudu sannan lafta Masa Sara a wurare daban-daban. Nan take kofofin gashin jikinsa ya zama wurin zubar da jini tamkar teku. Nan fa cikin layi da tangadi ya rinka daga kafarsa dakyar Yana yin gaba, Amma duk taku Daya sai wata takobin ta rugo ta lafta Masa Sara da haka da haka har sai da gaba dayan takubban nan guda duba kowace ta lafta Masa a inda take so. Koda yakai karshen dakin sai ya kife a Kasa jini na ta Malala a cikin dakin, kafin cikar dakika hamsin jinin RA'UFUL KALLUS yayi faca-faca da ko'ina a cikin dakin. Nan take RA'UFUL KALLUS ya shiga doguwar Suma. Bayan kamar Dakika sittin da bakwai, sai kawai akaga duk jinin RA'UFUL KALLUS da ya zuba Kasa ya tattaro Kansa da Kansa ya zo ya shiga a jikinsa. Faruwar hakan keda wuya sai akaga ALJANI RA'UFUL KALLUS ya Mike tsaye sannan ya tunkari daki na shida. Haka dai RA'UFUL KALLUS ya rinka shiga dakunan Nan Daya bayan Daya har yazo karshen daki na goma. Yana zuwa wannan dakin sai yaci karo da wani Katon Dutse sagale a can saman dakin. Kafin RA'UFUL KALLUS ya Ankara tuni wannan murgujejen dutsen ya fado Masa aka, nan take RA'UFUL KALLUS ya ragargaje ya zama tamkar an Nika hatsi. Nan take Dutsen ya dauke kanshi da kanshi ya koma ainihin inda yake. Bayan kamar Dakika arba'in Kasusuwa da fatar jikin RA'UFUL KALLUS suka hade, jikinsa ya koma kamar babu abinda ya same shi. Kafin yayi wani yunkuri tuni wannan Katon Dutsen ya sake fado Masa, ya sake rugurgujewa. Haka dai wannan dutsen ya rinka fado Masa Yana dagargajewa Kuma Yana sake tashi har sai da akayi haka sau dubu sannan ya dena. Koda faruwar wannan Ala'mari sai RA'UFUL KALLUS yaje can Karshen dakin sannan yayi arba da wata takobin Zinari Mai tsananin haske a sakale a jikin bangon dakin. Da zuwansa sai ya Mika hannu ya dauko takobin, Nan take kofar daki ta wanzu, Sannan ya kunna Kai a cikin kofar. Da shigarsa sai ya tsinci Kansa a tsakiyar birnin Kuma, yaci karo da wadannan bishiyoyin guda hudu a wuri daya. Nan take yaji wani Gagarumin Karfi ya shige shi ninka na daa sau goma. Nan take batare da Bata wani lokaci na, yazo wajen bishiyoyin nan sannan ya cizgo ganyayen su ya Saka a cikin battarsa sannan ya debo Kasar birnin yayi gaba. Sai da yayi tafiyar kwana biyu Sannan ya iso birni na shida..... ME ZAI FARU A BIRNI NA SHIDA? SHIN RA'UFUL KALLUS YANA SAMUN NASARAR TSALLAKE DUK HADARURRUKAN DAKE SAURAN BIRANEN? INA LABARIN WADANNAN DODANNI DA KUMA SARAKUNAN DUNIYA? SU WAYE ZASU SAMU NASARA A TSAKANINSU A WANNAN YAKIN? SHIN BURIN RA'UFUL KALLUS ZAI CIKA KUWA? MU HADU A HATSABIBIN ALJANI NA HUDU don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi ✍️♥️ Ni Najibullah Muhammad nake cewa ku huta lafiya fatan kunji dadin wannan littafin✍️✍️🙏🙏❤️**HATSABIBIN ALJANI** LITTAFI NA HUDU 4 ♥️🥰 PART A ✍️✍️ AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️🙋🥷 Whatsapp Num....08112778656 Lokacin da ALJANI RA'UFUL KALLUS ya kutsa Kai izuwa birni na shida. Da shigarsa sai ya tsinci Kansa a cikin wadansu irin mutane mabambanta wadanda gaba dayansu sun bambanta. Su dai wadannan mutanen birnin adadinsu yakai dubu, Kuma kowa yarensa daban. Ma'ana wannan bayajin yaren wancan, haka Kuma wannan baya jin yaren wancan. Kuma asali kowa garinsa daban, wani hatsabibin Bokan Aljani ne ya rinka sato su Yana kawowa wannan birni yana ajiyewa don ya cika wani burinsa na sihiri.. Asalin wannan birni wadansu Kananan halittu ne masu matukar kankanta wadanda duk abinda suka kama sai sun cinye shi, hatta Dutse idan suka yanyameshi suna saranshi da mugayen hakoransu sai dai aga dutsen yana gutsirewa yana fashewa har su Karar da shi. Haka Kuma idan bishiya suka samu suka tarar mawa sai sun cinyeta tass har jijiyoyin ta sannan suke Kara gaba. Wannan yasa a iya rayuwar da sukayi cikin birnin suka Karar da gaba dayan bishiyoyi da Duwatsun birnin, ya zamana cewa babu komai a birnin face Fili fetal Wanda babu gine-gine ko wani abu a Kansa. Amma Kuma daga 6angarorin wannan birni akwai wadannan bishiyoyin guda hudu a Raye wadannan halittun sun Kasa cinyesu, domin da zarar sunzo garesu da nufin tararwa bishiyar su cinyeta sai dai su rinka kamawa da wuta suna konewa kurmus. Wannan yasa suka hakura da cinye bishiyoyin suka Cigiba da rayuwarsu a cikin birnin suna tunanin yanda zasu rinka samun abincin da zasu rinka ci suna rayuwa. Dare daya suka ga wannan bakon Bokan Aljani yazo masu, da zuwansa sai ya rinka hura masu wata irin hodar sihiri Mai warin gaske, suka rinka kamawa da wuta suna konewa kurmus. Kafin cikar sa'a biyu dukkansu sun gama cinyewa da wuta ya zamana cewa sai dai tokar su. Koda ganin haka sai Bokan Aljanin ya kyalkyale da wata irin mahaukaciyar dariya. Nan take yayi tsafi sai ga wata gagarumar iska ta bayyana, sannan ta rinka kwashe tokar wadannan halittun tana watsawa a sama har sai da birnin ya zama babu wani abun kazanta a cikinsa. Sannan Bokan Aljanin ya cigaba da Gina gidajen sihiri a birnin har sai da ya Gina gidaje guda dubu, Kuma duk gida daya iyakar rayuwar mutum Daya ne saboda kankantar shi. Daga tsakiyar wannan birni kuwa, sai Bokan Aljanin nan ya karkashin Kasar birnin, sannan ya Gina wani tafkeken gidan Kasa Mai matattakala guda dubu, sa'annan Kuma a karshen Kasar ya rinka Gina manyan dakuna har guda dubu. Bayan kammala dakunan Kuma sai ya zubawa kowane daki zallan dodanni kala-kala har guda dubu. Ma'ana dodannin daki na farko basa cin Naman mutane ko aljanu, su kawai amfaninsu yiwa duk halittar da aka jefo cikin wannan dakin azabobi guda dubu, sannan su jefata daki na biyu, haka Suma dodannin daki na biyu basa yiwa mutum komai sai dai su zukewa mutum jini, sannan suyi Masa sihiri Shima ya zama dodo Dan uwansu, bayan sun gama sai su jefa mutum izuwa daki na uku, da haka da haka dai har su kammala jefa mutum izuwa daki na cikon Dubu. Bayan wannan bakon Bokan Aljanin ya kammala wannan aikin, sai ya rinka zuwa Kasa ya rinka mutane mabambanta masu yaruka daban-daban har sai da ya Ziyarci kasashe guda dubu, sannan ya dauko kabilu iri-iri guda dubu ya kawo wannan birni ya ajiye. A halin yanzu wannan Bokan Aljanin na can gidansa na karkashin Kasa inda ya ajiye dodannin nan ya shiga halwar tsafinsa domin kammala aikinsa akan wadannan kabilun mutanen da ya tattara. Lokacin da ALJANI RA'UFUL KALLUS ya shigo cikin wannan birni, sai ya cika da tsananin mamakin ganin mutane iri-iri musamman yanda yaga wasu farare, wasu bakake, wasu dogaye, wasu Kuma gajeru gasu Nan dai birjik iri-iri. Yana cikin tafiya sai yaga wadannan mutanen sun rugo gareshi sun rikeshi sun daddaureshi a wani wuri Mai rumfa, sannan sun taru gaba dayansu suna koya Masa yarukansu. Tun RA'UFUL KALLUS baya gane komai daga harsunansu har ya rinka fahimta, sai da yayi kwana arba'in a cikin wannan birni tare da wadannan kabilun mutanen. A wannan lokacin ne ya kammala koyon gaba dayan harsunan mutanen guda dubu, har ya iya magana da kowannensu. Inda ya fada masu dalilin zuwansa wannan birni sannan Kuma ya rokesu akan su kwanceshi, Nan take suka kwanceshi bisa yarjejeniyar lallai zai ceci rayuwarsu daga hannun wannan mugun Aljani, Kuma zai mayar dasu kasashensu cikin aminci. Batare da dogon tunani ba, RA'UFUL KALLUS yayi masu alkawarin taimakonsu, tare da mayar dasu kasashensu dukkansu. Nan take suka kwance igiyoyin da suka daureshi, sannana sukayi Masa kwatancen inda wadannan bishiyoyi suke. Batare da Bata wani lokaci ba, RA'UFUL KALLUS ya zagaye kusurwowin birnin gaba daya tare da tsinko ganyayen bishiyoyin, sannan ya dawo ainihin tsakiyar birnin Nan. Da zuwansa sai ya iske wannan wawakeken rami Mai matattakala Wanda Bokan Aljanin nan yayi. Nan fa RA'UFUL KALLUS ya tsaya Yana mamakin yanda aka wawaken wannan wuri, da Kuma irin yanda aka tsara gini a karkashin Kasa haka. Ba zato ba tsammani sai kawai RA'UFUL KALLUS yaji an bushe da wata mahaukaciyar dariya mara dadin ji, a cikin sautin dariyar yaji ana cewa... Lale marhabun da Gwarzo Kuma jarumin Aljani wato RA'UFUL KALLUS Wanda ya gagari duk mutane da Aljanun duniya. Kayi sani cewa irin burin da kake dashi, Nima shi ne nake dashi a cikin Raina. Kuma nayi bincike na gano cewa Nan da wani lokaci zaka zo har wannan birni domin dibar Kasar birnin da kuma tattaro ganyayen bishiyoyin karshen birnin guda hudu. To kayi sani cewa bincikena ya tabbatar

Chapter 3 of 8