Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 8
yawo cikin birnin Yana Neman inda Kasar tsakiyar birnin take Amma Bai gani ba, a haka yaci gaba da yawo har yazo kusa da wani Katon Tsauni Mai tsananin girma a tsakiyar garin Wanda ya cika hanyar babu ta inda za a bi a wuce. Nan take ya yanke shawarar bin kowace kusurwa ta garin domin neman wadannan ganyayyakin alla-bashi daga baya sai yaci gaba da Neman Kasar birnin. Nan take ALJANI RA'UFUL KALLUS yayi Amfani da wannan shawarar, ya rinka bin kowace kusurwa Yana tsinko ganyayen bishiyoyin Nan, har sai da ya zagaye birnin Kuma ya samu nasarar samo duka ganyayyakin sannan ya dawo cikin tsakiyar birnin Yana ta dubawa har yazo wurin da aka killace Kasar wurin batare da an shafeta ba. Cikin tsananin farin ciki Aljani RA'UFUL KALLUS ya Debo Kasar sannan ya zuba ta a cikin battarsa. Faruwar hakan keda wuya sai ya falfala da matsanancin gudu ya tunkari hanyar barin garin. Sai da Aljani RA'UFUL KALLUS yayi gudun sa'a goma batare da Jin motsin komai a bayansa ba. Ba zato ba tsammani sai kawai ALJANI RA'UFUL KALLUS yaji an dauko shi sama da 'yan yatsu biyu Sannan anyi sama dashi an dawo dashi ainihin inda ya fara gudun an ajiye shi. Koda ya daga Kansa sama sai ya hango wani shirgegen mutum, Wanda girmansa ya wuce misali. Ashe daman wannan Katon tsaunin da Aljani RA'UFUL KALLUS ya gani a tsakiyar birnin, ba Tsauni bane wannan shirgegen mutumen ne.. Nan fa wannan shirgegen mutumen ya sunkuyo da Kansa Kasa, ta yadda Aljani RA'UFUL KALLUS zai iya ganin fuskar mutumen. Koda suka hada idanu sai Aljani RA'UFUL KALLUS ya kamu da tsananin razana, saboda tsananin munin fuskar mutumen. Shidai Wannan shirgegen mutumen tsawonsa zira'i dubu biyu ne, sannan fadinsa zira'i dubu ne. Yana da kahonni guda biyu a tsakiyar Kansa, Kuma tsawonsa ya kere gaba dayan gidajen birnin. Idan ya Mika hannunsa guda daga inda yake zai iya kaiwa can Karshen birnin, duk da cewa sai anyi kusan tafiyar wata guda ana gudu kafin a fita birnin. Shirgegen mutumen ya takarkare ya kwarara wata mahaukaciyar dariya wadda ta rinka haifar da wata irin mummunar Kara tamkar ana ruwan kwarankwatsa, har wani irin farin Hayaki ne ya rinka fita daga bakinsa, Koda wannan Karar da wannan hayakin suka Doki Aljani RA'UFUL KALLUS sai ya fadi Kasa sumamme... ME ZAI FARU TSAKANIN ALJANI RA'UFUL KALLUS DA WANNAN SHIRGEGEN MUTUMEN? SHIN ALJANI RA'UFUL KALLUS ZAI SAMU NASARAR ZIYARTAR DUKA BIRANEN GUDA DUBU DOMIN CIKAR BURINSA? WANE IRIN YAKI ZA'AYI A TSAKANIN DODDANIN DA ALJANI RA'UFUL KALLUS YA KAWO A MATSAYIN MASU GADIN KOGONSA DA KUMA SAURAN BOKAYE DA SARAKUNAN DUNIYA? SU WAYE ZASU SAMU NASARA A WANNAN YAKI? SHIN BURIN ALJANI RA'UFUL KALLUS NA CIKA? Domin Amsar wadannan tambayoyin sai mu hadu a HATSABIBIN ALJANI na biyu don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️♥️🥰🥰 **HATSABIBIN ALJANI** LITTAFI NA BIYU 2 PART A ✅♥️ AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷 Lokacin da wannan shirgegen mutumen ya takarkare ya kwarara wata mahaukaciyar dariya wadda ta rinka haifar da Kara tamkar ana ruwan kwarankwatsa, har wani irin farin hayaki ya rinka fita daga bakinsa. Koda wannan Karar da hayakin suka doki Aljani RA'UFUL KALLUS sai ya fadi Kasa sumamme. Koda Shirgegen mutumen nan yaga ALJANI RA'UFUL KALLUS ya Suma, sai ya tsuke bakinsa sannan yasa 'yan yatsu biyu kacal ya dauko Aljani RA'UFUL KALLUS sannan ya bude wangamemen bakinsa Mai kama da Katuwar kofar gari, ya jefa shi ciki tamkar an jefa tsakuwa a cikin RIJIYA GABA DUBU. Kash! Hakika masu iya magana sunyi Gaskiya da suka ce, rashin sani yafi dare duhu. Inda wannan shirgegen mutumen yasan abinda zai biyo baya da Bai jefa ALJANI RA'UFUL KALLUS cikin cikinsa ba. Ashe kashin wannan Sarkin da ALJANI RA'UFUL KALLUS yayi ta yin Wanka da shi tsawon kwana goma, yana mammanne a jikinsa har yanzu, Kuma har yanzu bayyi Wanka ba. Saboda haka har a lokacin jikinsa wari kawai yakeyi. Kuma duk duniya babu wani makami ko sihirin da zai iya hallaka wannan shirgegen mutumen. Haka Kuma duk duniya babu Mai karfin damtsen da zai iya tunkarar wannan shirgegen mutumen yayi nasara akansa. Abu Daya ne kawai za'a iya Amfani da shi a hallaka wannan shirgegen mutumen, shi ne a bashi kashin Sarkin wancan garin na farko yaci. Muddin ya shiga cikinsa take yake zama Masa muguwar guba Mai tsananin zafin da zai mutu a cikin dakika hamsin kacal. Koda fadawar Aljani RA'UFUL KALLUS a cikin cikin wannan shirgegen mutumen sai ya rinka karo da 'yan hanjin cikinsa. A duk lokacin da Aljani RA'UFUL KALLUS yaci karo da hanjin wannan shirgegen mutumen sai dai aga suna tsittsinkewa tamkar tsumman da aka babbaka a wuta. Nan fa wannan shirgegen mutumen ya rinka kururuwa Yana magowa hade da ihu Mai tsananin razanarwa. Nan da nan ya rinka kokarin amayo ALJANI RA'UFUL KALLUS Amma Abu ya gagara, cikin kankanin lokaci ya fita hayyacinsa ya rinka dukan gine-ginen birnin suna rugujewa. A cikin dakika arba'in sai da ya ruguje gidaje Dari biyu da arba'in da bakwai. Bayan kamar sa'a guda ne da fara hargowar wannan shirgegen mutumen sai aka ga ya kame Kam a tsaye, ya dena motsi gaba dayan jikinsa ya dena motsi ko'ina ya sandare. Nan take shirgegen mutumen yayi baya luu tamkar Tsauni zai ruguje, kawai sai ya fada Saman wasu manyan gidaje guda dubu suka rugurguje.. Ala'marin ALJANI RA'UFUL KALLUS kuwa sai da ya shafe dakika dubu Yana karo da hanjin wannan shirgegen mutumen Amma Bai farfado ba har sai da ya Kai karshen cikin nasa inda ya fada cikin wani Katon ruwan tumbinsa, Mai kamar teku. Da fadawarsa cikin wannan tumbin sai ya farfado daga dogon suman da yayi, a wannan lokacin tuni ya nutse a cikin ruwan cikin shirgegen mutumen. Ai kuwa yana farfadowa sai ya kama iyo, yana Jan ruwa har kawo Baki wata gaba. Koda zuwansa sai ya rinka Amfani da wani karfe Mai tsananin Kaifi ya rinka yanka cikin mutumin. Bai gushe ba Yana yin haka har tsawon kwanaki uku sannan ya samu nasarar huda tumbin mutumin ya fito waje. Koda ya duba sai yaga Ashe ma wannan shirgegen mutumen ya kusa ruguje gaba dayan gidajen birnin. Nan take ALJANI RA'UFUL KALLUS ya Bude gaba dayan fuka-fukansa guda dubu sannan ya falfala da gudu yana Mai tunkarar daji na uku. Bayan kamar fara tafiyarsa ne da kwana biyu ya iso birni na uku. Da shigarsa cikin birnin sai yaga babu komai a cikin birnin face bishiyoyi kala-kala. A wannan birni babu bishiyar da babu, domin babu wata halitta Mai Rai a cikin birnin face bishiyoyi. Kuma hatta gine-gine da da wuraren shakatawa da wuraren Wasanni duk da zallan bishiyoyi aka yi su. Kai hatta sauran ababen rayuwa irinsu mutane, dabbobi, kwaruka, da komai na cikin birnin siffar bishiyoyi garesu. Ma'ana dai duk abinda ka gani a birnin to bishiya ce Kuma tana da rassu da jijiyoyi. Nan fa ALJANI RA'UFUL KALLUS ya cika da tsananin mamakin wannan birni, yana cikin tafiya sai ya ga wani wuri inda wasu bishiyoyi suka harde da junansu sannan sukayi siffa irinta kogon dutse, sannan wani ruwa garai-garai Yana gangarowa ta tsakaninsu. Nan take ya duka ya kwankwadi ruwan nan har da yaji cikinsa ya cika taf. Sai da ALJANI RA'UFUL KALLUS ya shafe kwana bakwai Yana yawo cikin wannan birnin sannan yazo dai-dai inda tsakiyar birnin yake. Da zuwansa sai ya duka a tsakanin wasu bishiyoyi da sukayi gwafa, da nufin ya debi Kasar wurin. Ba zato ba tsammani sai kawai yaga wadannan bishiyoyin sun fito da wasu murtuka-murtukan jijiyoyi masu tsananin kwari da kauri sannan sun daddaure ALJANI RA'UFUL KALLUS sun daga shi sama Yana Lilo a tsakiyarsu. Faruwar hakan keda wuya sai wasu zabga-zabgan bulalu suka sauko kasa-kasa saitin inda aka daure ALJANI RA'UFUL KALLUS. Nan fa bulalun nan suka rinka Zane ALJANI RA'UFUL KALLUS Yana ihu da kururuwa, Kuma Yana ta kokarin ganin Wanda ke dukansa Amma ya Kasa. Bugu da Kari yayi iyakar kokarinsa wajen kubuta daga rikon wadannan jijiyoyin Amma ya Kasa. Bisa dole ya hakura. Yana ji Yana gani wadannan bishiyoyin suka rinka Zane shi, har sai da sukayi Masa bulala dari biyu da tamanin sannan bulalun suka bace... Washe gari ma haka Ala'marin ya kasance, wato wadannan bulalun suka rinka saukowa suna Zane shi adadin bulalun jiya. A haka har tsawon kwanaki bakwai sannan, a wannan lokacin ne fatar jikin ALJANI RA'UFUL KALLUS ta fara tulbewa saboda tsabar duka. Nan fa labari yasha bamban domin duk bulalar da ta taba jinin jikin ALJANI RA'UFUL KALLUS sai dai aga ta kama da wuta ta kone kurmus, a cikin dakika goma sai da gaba dayan bishiyoyin da suka daddaure Aljani RA'UFUL KALLUS suka kama da wuta suka kone kurmus. A wannan lokacin ALJANI RA'UFUL KALLUS yasha bakar wahala na bulalun da yasha tsawon kwana bakwai, Kuma gaba dayan jikinsa zubar da jini yake. Bayan kamar Dakika sittin ya fara dawowa hayyacinsa, sai yasa hannu a wurin ya debo Kasar birnin ya zuba a cikin battarsa, sannan ya zagaya kusurwowin birnin ya ciro ganyayen bishiyoyin nan guda hudu sannan ya Kara komawa wurin da bishiyoyin nan suka harde suka Samar da siffa kamar kogon dutse, Kuma suna fitar da wani garai-garai a cikinsa. Da zuwansa ya tsittsinko 'yayan itatuwa kala-kala guda dubu sannan ya kama ci, sai da ya koshi sosai, sannan ya duka ya Kafa Kansa a cikin wannan kogon da ruwan ke gudana Shima yasha ya koshi. Faruwar hakan keda sai yaga gaba dayan raunikan jikinsa sun bace bat, sannan duk wata gajiya Dake addabarsa babu haka Kuma sai ya rinka Jin wani irin gagarumin karfi na shigarsa tamkar Yana iya daukar gaba dayan duniya da hannu Daya. A hakali- a hankali Kuma sai ya rinka yin girma tamkar ana hurashi da iska, sai da ALJANI RA'UFUL KALLUS ya ninka girman da yake dashi daa sau arba'in sannan ya tsaya haka. Koda ganin wannan Ala'mari sai ya cika da tsananin farin ciki, Kuma yaji a ransa cewa babu wani bala'i da zai Hana shi cikar burinsa, tunda ko yanzu Yana Jin idan ya koma Duniyar mutane da Aljanu to zai iya tunkarar gaba dayan halittun duniya ya yake su batare da ko mutum Daya yayi Masa kwarzane ba. Batare da Bata wani lokaci ba, ALJANI RA'UFUL KALLUS ya tunkari birni na hudu Yana tafiya Yana kasaita tamkar Wanda aka mallakawa sarautar duniyar Baki Daya. Wannan shi ne abinda ya faru a birni na uku birnin bishiyoyi, bayan ALJANI RA'UFUL KALLUS ya samu abinda yake a birnin Kuma ya tunkari birni na hudu... Ala'marin wadannan DODANNIN da ALJANI RA'UFUL KALLUS ya dauko domin suyi gadin KOGONSA kuwa. Sai suka kasance kullum cikin Shirin tarar wadannan Abokan gaba da aka ce masu zasu so, sannan suka yi ta wasa wadansu falka-falkan makamai masu siffar majaujawar karfe wadanda idan aka jefa guda izuwa kan Abokan gaba sai ta sargafo wuyan mutane saba'in sannan da an finciko ta, sai dai aga kan mutanen na gutserewa tamkar ana cizge masara daga jikin goyonta. Wasu Kuma suka rinka tugo manyan bishiyoyi suna feke su, suna mayar dasu tamkar mashi Mai tsananin nauyi da tsini, ta yadda duk lokacin da aka jefa shi izuwa ga abokan gaba to sai ya kashe guda dari da arba'in sannan yake dakatawa. Haka dai wadannan DODANNI suka wanzu suna ta kera manyan makamai domin tunkarar abokan gaba. A bangaren mutane da Aljanu kuwa, sai da sarakunan Aljanun duniya suka kammala ziyartar duka sarakunan bil'adama dauke da rundunoninsu, sannan suka tattara gaba dayansu kaf! Suka tunkaro Kogon BAHAR DURGAFUL KALLUS wato inda ALJANI RA'UFUL KALLUS ya ajiye wadannan DODANNIN. A wannan lokacin duk Wanda ya hango wannan rundunar guda biyu, to Nan take yake haukacewa ko ma zuciyarshi ta buga ya fadi Kasa matacce saboda tsananin kwarjinin wannan rundunar. Daga nesa idan Mutum ya hango wannan rundunar gani zayyi tamkar sama da Kasa ne zasu hade saboda tsananin yawansu. A bangaren Aljanu sama da runduna Milyan dari ne, suka tashi sama suka yiwa rundunar mutane inuwa. Gaba dayan Aljanun sun jera sahu-sahu a sararin samaniya. Saboda tsananin yawansu daga sararin sama har cikin giza-gizai suke shiga. Kowanensu na rike muggan makamai masu matukar hadari, wadanda Ko a tarihi ba'a taba Jin labarin irinsu ba. A bangaren rundunar mutane kuwa, sama da sarakuna DUBU ne, suka hada kansu a wannan Yakin. Kuma kowannensu ya debo zakakuran dakaru guda Milyan goma. Sannan Kuma gaba dayan Dakarun sunyi shigar sulken bakin karfe ne, Kuma kowannensu yana bisa Doki Yana ihu da Karaji. Haka Kuma sarakunan sune jagororin yakin, ma'ana kowane Sarki shi ne ke jagorantar rundunar sa. Bugu da Kari wadannan Dakarun kowacce runduna na rike da muggan makamai daban-daban masu matukar hadari. Domin wasu sun rike zallan Takubba da garkuwowi, wasu kuwa masu suka rike masu matukar Kaifi da jini Wanda ko karfe aka cakawa mawa sai ya huje. Haka Kuma wata rundunar kuwa ta rike zallar kwari baka masu matukar yawa, wadanda duk abinda aka harba take abun yake bushewa ya lalace tamkar bishiyar da aka kwakulo sauyunta. Wata rundunar kuwa gaba dayansu majaujawar karfe ce wadda suke wurwurawa su cillata izuwa kan abokan gaba ta rinka cakewa a kawunansu sai da aga kwanya da jini na Malala. Bayan haka Kuma wasu rundunar gaba dayansu sun rinke zabga-zabgan sarkoki ne masu matukar kauri da kwari wadanda zasu rinka Amfani wajen nannade duk jarumin da ya fisu karfi. Da zarar sun daddaure shi da wannan Sarkar sai suyi Masa rubdugu su kashe shi. Haka wadannan rundunoni suka wanzu tafiya, suna keta koramai da manyan Dazuzzuka har suka iso Kogon BAHAR DURGAFUL KALLUS... TOM mu hadu a HATSABIBIN ALJANI na Daya part B don Jin yadda ta kaya... Daga mai debe maku kewa a kullum da Koda yaushe wato NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ Ina maku fatan Alkhairi 👆🙏🙏🙏🙏🙏**HATSABIBIN ALJANI** LITTAFI NA BIYU 2 PART B ✍️♥️ AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷 Whatsapp Num.. 08112778656 ------------------------------------------- Lokacin da wadannan rundunonin suka karaso Kogon BAHAR DURGAFUL KALLUS, sai suka iske wadansu jibga-jibgan SAMUDAWAN DODANNI masu mummunar siffa, sannan kowannensu Yana rike da mugun makami Mai tsananin hadari ga rayuwar mutum da Aljan. Su dai wadannan DODANNI adadinsu yakai Milyan Arba'in, Kuma dukkaninsu garza-garzan katti ne wadanda duk guda daya ya ninka girman Aljani sau goma. Suna da wawakeken Baki Mai tsananin fadin gaske, Wanda zasu iya hada bil'adama biyar suyi Loma guda dasu a lokaci guda batare da bakin ya cika ba. Bugu da Kari suna da zako-zakon hakora masu Matukar Kaifi da tsini wadanda duk abinda suka tauna sai ya ragargaje Koda kuwa Dutse ne. Suna da kwala-kwalan jajayen idanuwa masu matukar girma tamkar na kwan jimina. Sa'annan Kuma jikinsu a murde yake tamkar zana su akayi a takarda. Kai, komai dakewar zuciyar mutum ko Aljan idan yaga irin zubin siffofin wadannan DODANNI dole ne ya razana ya juya da baya. Wadannan DODANNI a halin yanzu suna matukar bukatar jinin mutum da Aljan, domin sun Haura shekaru tamanin rabon da su dandana su, wannan yasa gaba dayan jikinsu yayi fari fat! Tamkar babu jinin Dake gudana a tsakaninsu. A bangaren dakarun mutane da Aljanu kuwa, Koda sukayi arba da wadannan DODANNI sai suka kamu da tsananin firgata, Amma da suka duba yawansu sai suka samu kwarin gwiwar tunkararsu saboda sun San cewa Sarkin yawa yafi Sarkin karfi, koba komai dai ai sun ninka waɗannan DODANNIN yawa sau dubu, saboda haka ta kowane hali yau sai sun samu nasara a wannan yaki. Ala'marin rundunar mutane kuwa, da zuwansu sai suka ja linzamin dawakansu suka tsaya cak, sannan SARAKUNAN da ke jagorantar rundunar su, suka cewa Aljanun da suke tare dasu, yaku abokan tafiya tabbas wannan Aljanin ya bar mana babbar masifa a wannan kogo, Amma duk da haka sai mun yaki wadannan dodanni Kuma mun kashe dukkaninsu sannan mu lalata gaba dayan sihirin tsafin da Aljani RA'UFUL KALLUS yake da shi. Amma a shawararmu ku yakamata ku fara afka masu kafin Mu kammala Shirin tunkararsu saboda Kunfi mu girma da karfi. Koda Aljanun suka ji wannan Batu sai suka ce, tabbas gaskiyar ku. Kuyi sani cewa a yau kota wane hali sai mun Karar da gaba dayan wadannan dodanni sannan mun cimma burinmu. Kuma Muna so ku zuba idanu kusha kallon yadda zamu hallakasu a cikin kankanin lokaci. A lokacin da rundunar mutane da Aljanu suke wannan tattaunawar, su Kuma a wannan lokacin wadannan Dodannin tuni yawun bakinsu ya tsinke da kwadayinsu. Saboda sai wani irin mugun yawu ke dalala a bakinsu, Nan da nan basu San lokacin da suka ruga gaba dayansu ba, suka afkawa rundunar Aljanu. Koda Aljanu suka ga haka, sai SARKI GUHUMUL Mai Shugabantar rundar farko wadanda suke rike da muggan takubba, ya dakawa Dakarunsa tsawa akan su Afkawa waɗannan DODANNIN. Wohoho!! Nan fa sama da Aljanu Milyan hamsin suka cillo da matsanancin gudu izuwa kan dodannin nan tamkar an cillosu daga cikin baka. Aljanu Milyan daya daga cikinsu suka wurwura Takubbansu sannan suka cillasu izuwa kan dodannin, nan da nan takubban nan sukayi fitar burtu daga hannuwansu suka rinka cakewa a jikin dodannin nan. Nan fa sama da DODANNI dubu arba'in suka zube a Kasa cikin mummunan yanayi, sakamakon muguwar illar da takubban da ake jeho masu sukayi. Yayinda rundunar Aljanun Nan suka hade da dodannin nan, sai labari yasha bamban, domin dodannin sun ninka waɗannan Aljanun karfi nesa ba kusa ba. Sai dai kaga dodo Daya ya mako Aljani hamsin da majaujawar karfe a lokaci guda sun fado Kasa matattu, sannan yasa hannuwansa ya tattarosu gaba dayansu, ya zuke dukkan jininsu su zama kamar kwarangwal, sai ya wangame tangamemen bakinsa Mai kama da Katon tire ya watsa su ciki ya tauna ya hadiye. Karar tauna Kasusuwan Aljanun a bakin wadannan dodanni ta cika Dajin gaba daya, domin wata irin Kara ce mara dadin ji tamkar ana yiwa mutum susar kunne, ji kake suna gurus-gurus ba dadin ji. A cikin dakika Dari uku da arba'in sai da dodannin nan suka kashe sama da Aljanu Milyan daya, Amma babu Gawar Aljani ko Daya a Kasa, dukkansu suna cikkunan dodannin. Yayinda ragowar Aljanun suka ga irin wadannan mummunar barna da ake masu, sai suka fusata ainun ransu ya harzuka. Nan take shugaban wannan rundunar SARKI GUHUMUL ya bayar da Umarnin a dena tunkarar dodannin gaba da gaba, a rinka shawagi a Saman kawunansu ana saran dodannin a kawunansu. Nan da nan wadannan Aljanun suka bi Umarni, Nan take suka rinka kada fuka-fukansu suna tashi saman dodannin sannan suna ta Luma masu takubba akai, wasu Kuma sai dai kaga sun shammaci dodannin sun soka masu zureriyar takobinsu a idanu da a Kunnuwa. Koda fara wannan dabarar sai aka fara kashe wadannan dodanni, nan fa kwanyar kawunan dodannin ta rinka bulbula da Malala daga jikin kawunansu. Kafin cikar dakika dari biyu an kashe dodanni dubu Dari, ya zamana cewa gawarwakin dodannin sun taru himili guda tamkar Tsauni. Koda wadannan dodanni suka ga haka akaga sama da DODANNI Milyan biyu sunyi wani irin ruri Mai tsananin razanarwa, Nan take gaba dayansu duka daka wani wawan tsalle sama sannan suka Bude wata Katuwar ragar karfe Mai tsananin girma da fadi, suka rinka mangare Aljanun Nan suna fadawa cikin ragar. Idan dodo guda yakai mangari da lafcecen hannunsa Mai kama da Katuwar bishiyar kuka, sai dai kaga ya mako sama da Aljanu Dari biyar cikin ragar Nan. Kafin cikar sa'a guda dodannin nan sun zuba gaba dayan rundar farkon Nan ta Aljanu sama da guda Milyan arba'in cikin ragar karfen Nan. Sa'annan suka dauren bakin ragar da wani irin murtukeken mulmulallen bakin karfe, ta yadda koda gaba dayan Aljanun zasu taru ba zasu iya tsinka ragar ko balla wannan karfen ba. Faruwar hakan keda wuya sai akaga sama da DODANNI Milyan biyu sun Suri wannan ragar sunyi sama da ita, sun shigar da ita can cikin kuryar kogon Dutsen, sannan sun zubawa Aljanun cikin ragar wani mugun banju Mai tsananin sa barci, Wanda ba zasu iya farkawa daga nannauyan barcinsu ba sai bayan wata guda. Faruwar hakan keda wuya sai suka jawo wasu murtuka-murtukan bishiyoyi masu siffar masu, wadanda suka feke sukayi Kaifi da tsini sannan suka Kara fitowa filin yakin. Koda ganin wannan Al'amarin sai rundunar mutane ta ce itama bari ta jaraba, kawai sai rundunar da Sarki DURSAL yake jagoranta suka ware, sannan gaba dayansu suka daga zabga-zabgan masunsu sukayo Kan dodannin nan suna ihu da Karaji. Adadin wadannan runduna sun Kai Milyan goma. Idan Mutum yaga lokacin da wadannan rundunonin suke rugawa izuwa kan dodannin nan rike da muggan makamai, sai yayi zaton gaba Daya mutanen duniya ne suka taru domin yakar dodannin saboda tsananin yawansu. Koda wadannan Dodannin suka hango rundunar bil'adama ta tunkaro su bisa dawakai, sai suka cika da tsananin farin ciki domin sun San cewa a duniya Kaf babu abincin da ya Kai Naman bil'adama dadi. Nan da nan sama da Dakaru dubu Dari suka cilla masunsu izuwa saitin idanuwan dodannin nan da cikkunansu. Nan fa wadannan masun suka cilla da matsanancin gudu suka rinka lumewa a jikin kawunan dodannin suna faduwa Kasa matattu, wasu kuwa suka rinka lumewa a jikin tumbin dodannin suna Farka cikkunan, sai kaga tumbinsu ya fado Kasa tare da kwarangwal din Aljanun da ya hadiya. Koda ganin haka, sai Suma dodannin suka wurwura wadannan bishiyoyin da suka feke suka rinka cillasu kan bil'adama. Nan fa wadannan bishiyoyin suka rinka cakewa a jikin dokunan Dakarun. Idan aka cillo bishiya Daya, to sai ta lume a jikin dokuna dari da arba'in sannan take faduwa Kasa, sai dai kaga dokuna na bultsewa suna tunkuyar Kasa a matsayin matattu suna jefar da mahayansu. Idan kuwa Dakarun bil'adama bishiyar ta samu, sai dai kaga tana tarwatsa Gangar jikinsu tana yin gaba tamkar macijiyar da ke yin Loma guda da kwayar gero. Sai ta tarwatsa mutum Dari biyar sannan take dakatawa. Ana haduwa a tsakanin rundunar mutane da DODANNIN aka kacame da masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro da tashin hankali na gaban kwatance. Nan fa wasu daga cikin dodannin nan suka rinka Amfani da wani Katon Sangwami suna fyade mutane duk da dawakansu suna sulalewa Kasa matattu, su kuwa suna tattarasu su zuke masu jini sannan su watsa kwarangwal din gangar jikinsu a cikin Baki. Kafin cikar dakika hamsin jikin dodannin yayi bulbul ya zama jajur saboda tsabar zukar bil'adama da suke yi. A duk dodo daya Yana iya zuke jinin bil'adama dubu sannan ya watsa kwarangwal din gangar jikinsu a cikin Baki ya taune. A bisa wannan dalili ne zafin namansu ya yawaita, suka rinka kashe mutanen tamkar GOBARA DAGA KOGI. Kuma Koda Dakarun mutanen sunyi nasarar datse ma wani dodon hannu ko Kai ko Kafa, Kai ko ma wane sashe ne. To zarar digon jinin dodon ya taba Kasa, sai aga sama da dodanni hamsin sun tashi irinshi sak. A bisa wannan dalili ne yasa a cikin dakika Dari bakwai da hamsin, sai da yawan dodannin ya ninku sau goma yazamana cewa yanxu yawansu yakai kimanin Milyan dari da tamanin. Faruwar hakan keda wuya sai akaga gaba dayan wadannan dodannin sun rikide sun zama wani NARKEKEN DODO Wanda tsayinsa yafi karfin kogon gaba Daya, dole sai dai ya durkusa kamar yadda gwaggwan biri ke yi. Kafin wani daga cikinsu yayi wani yunkuri tuni wannan jibgegen dodon ya Mike lafcecen hannunsa ya cafko gaba dayan ragowar Dakarun rundunar mutanen Nan duk da dawakansu wadanda adadinsu yakai Milyan bakwai da dubu dari biyar. Faruwar hakan keda wuya sai akaga ya wangame kanfacecen bakinsa ya watsa dukkanninsu cikin bakinsa ya taune... SU WAYE ZASU SAMU NASARA A WANNAN YAKI TSAKANIN DODANNI DA KUMA RUNDUNAR MUTANE DA ALJANU? INA LABARIN ALJANI RA'UFUL KALLUS? WANE IRIN KALUBALE ZAI FUSKANTA A SHIGARSA BIRNI NA HUDU? SHIN BUKATARSA ZATA BIYA KUWA,? SHIN DAGASKE ZAI SAMU NASARAR ZAMA GAGARABADAU KUMA SADAUKIN DA BABU KAMARSA A FADIN DUNIYA? Domin Jin amsoshin wadannan tambayoyi sai mu hadu a HATSABIBIN ALJANI na uku. Na ku har kullum a Koda yaushe wato NAJIBULLAH MUHAMMAD ke cewa ku huta lafiya, sai mun hadu a na uku in-sha Allah✍️✍️🙏🙏🙏 **HATSABIBIN ALJANI** LITTAFI NA UKU ✍️✍️ PART A 💯♥️ AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷🥷 Whatsapp Num.....08112778656 Lokacin da wannan Shirgegen dodon ya tattara gaba dayan rundunar SARKI DURSAL yayi loma da su. Sai gaba dayan ragowar rundunar mutane da Aljanun suka razana ainun. Nan take suka fara jaa da baya, domin sun tabbatar da cewa babu nasara a cikin wannan yaki. Yayinda SARKI ZURUKUL TARGUL Mai jagorantar rundunar Aljanu ta biyu yaga wannan Ala'mari sai ransa ya Baci matuka. Nan take gashin jikinsa ya mimmike tamkar an taje gashin. SARKI ZURUKUL TARGUL gawurtaccen Sarki ne a kasashen Aljanu kuma ba karamin sadaukin jarumi bane Kuma matsafi. Domin masana sun tabbatar da cewa a gaba dayan nahiyar Aljanu babu Kasaitacciyar Kasar da ta Tara manyan sadaukai da matsafa da Kuma attajirai na gaban kwatance tamkar Kasar ZURUKUL TARGUL. Shi kanshi SARKI ZURUKUL TARGUL masana sun tabbatar da cewa duk duniya in Banda ALJANI RA'UFUL KALLUS babu Wanda ya kaishi tsananin karfin damtse da Kuma karfin sihirin tsafi. Lokacin da SARKI ZURUKUL TARGUL yaga cewa duk da yawansu, Amma rundunar mutane da Aljanu sun karaya da wannan

Chapter 2 of 8