min da cewa muddin nayi amfani da jininka na hadashi da jinin wadannan kabilun mutanen da na tattara, to a cikin dakika hamsin kacal burina zai cika.
Saboda haka Ina Yi maka bankwana da wannan kalami, saboda ka kawo kanka Tsibirin mutuwa inda ba a zuwa a fita, duk abinda ya shigo Nan ya shigo kenan har abada.
Kafin RA'UFUL KALLUS yace wani abu, tuni wannan Bokan Aljanin ya bayyana Tsulum a gabanshi, sannan ya runbabeshi sun bace.
Basu bayyana a ko'ina ba sai a cikin dakin dodanni na farko.
Bayyanarsu keda wuya sai bakon Bokan Aljanin ya bace bat Yana Mai cigaba da kyalkyala dariyar mugunta.
Cikin tsananin zafin nama dodannin nan sukayo caa akan RA'UFUL KALLUS suna suka daddaure shi.
Nan fa suka rinka gana Masa azabobi kala-kala har guda dari bakwai da saba'in.
A wannan lokacin gaba dayan siffar RA'UFUL KALLUS ta canza saboda tsabar azabar da ya Sha, domin dakyar yake iya daga hannunsa ma saboda tsabar galabaita.
Nan fa wadannan dodanni suka dauko wani irin murtukeken karfe Mai matukar tsini Kuma jajur a sama da nufin su tsire RA'UFUL KALLUS.
Koda RA'UFUL KALLUS yaga mutuwa muraran sai ya takarkare ya kwarara uban ihu, ba zato ba tsammani sai yaji sihirin tsafinsa ya dawo.
Nan take yayi Amfani da karfin sihirin tsafi ya tsittsinka Sarkar da dodannin suka daddaureshi.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga wasu muggan makaman yaki na wuta sun bayyana a hannunsa, Nan fa ya hau dodannin nan da Sara da suka tamkar wutar da aka bulbulawa fetur.
Nan fa RA'UFUL KALLUS ya rinka gutsirewa dodannin nan Kai, jini ya rinka fantsama da Malala a cikin dakin tamkar ruwan teku ya balle.
Nan fa ihu da gurnanin dodannin nan ya yawaita a cikin wannan daki, kafin cikar dakika dari da arba'in RA'UFUL KALLUS ya kashe gaba dayan DODANNIN.
A wannan lokacin jinin dodannin ya kusa cika dakin gaba daya.
Saboda haka gaba dayan jikin RA'UFUL KALLUS a cikin jini yake, Koda jinin dodannin nan ya ratsa jikin RA'UFUL KALLUS sai gaba dayan raunikan da sukayi Masa suka cicciko Kuma fatarsa ta zama Mai tsananin tauri tamkar Dutse.
Nan fa ya rasa hanyar da zai wuce izuwa daki na gaba, kawai sai ya debo jinin wadannan dodannin yasha.
Faruwar hakan keda wuya sai kawai yaji anyi sama da shi, sannan an jefa shi izuwa daki na biyu.
Har a sannan akwai jinin wadannan dodannin a jikinsa sai diga yake, sa'annan Kuma yana rike da muggan makamansa.
Koda ganinsa izuwa wannan dakin, sai ya tsinci Kansa a tsakiyar wasu lafta-laftan dodannin da suka ninka na baya girma sai goma.
Kafin wani yace wani abu tuni dodo Daya daga cikinsu ya suri RA'UFUL KALLUS sannan ya shako shi da hannu guda, ya daga sama yana Lilo.
Faruwar hakan keda wuya sai wannan dodon ya wangame tafkeken bakinsa Mai dauke da wadansu zabtara-zabtaran hakora ya Kafa Masa a wuya da nufin zukewa RA'UFUL KALLUS ya jini.
Nan fa wannan dodo yaji fatar RA'UFUL KALLUS tauri tamkar Dutse ko kadan hakoransa bazasu iya hudata ba.
Domin har sai da hakoransa guda goma manya-manya suka kakkarye.
Ba shiri ya Sako RA'UFUL KALLUS ya fado, sannan suka rufar Masa da duka da mangari da nufin su kallashi.
Nan fa suka wanzu suna harba RA'UFUL KALLUS tamkar kwallo Yana gwaruwa da bangon dakin Yana faduwa.
Cikin kankanin lokaci RA'UFUL KALLUS yasha bakar wahala har jikinsa ya kukkumbura.
Ba shiri ya jawo makamansa sannan ya tunkari dodannin Yan karkashesu suna mutuwa tamkar ruwan sama.
Kafin cikar sa'a guda ya kashe dukkansu, sannan yasha jinin dodannin Kuma ya wuce izuwa daki na uku.
Nan ma wasu nau'in dodannin ne suka azabtar dashi sau dubu sannan sukayi yunkuri kasheshi daga bisani ya yake su ya karkashe su, Kuma yasha jinin su.
Haka ya rinka yi har sai da ya tsallake dakuna dari Tara da casa'in da tara. Kuma a cikin kowane daki sai da ya hadu da dodanni na musamman Kuma sunyi Masa azaba Mai yawa har guda dubu daga bisani ne yake yakarsu sannan yasha jinin su ya wuce gaba.
Lokacin da RA'UFUL KALLUS ya tsinci Kansa izuwa cikon daki na dubu, sai yaga gaba dayan siffarsa ta canza daga ainihin wadda ya sani.
Domin gani yayi rabin jikinsa daga hannun dama ta rikide izuwa siffar dodanni, sannan Kuma rabin jikinsa daga hannun Hagu Yana Nan a siffar aljaninsa.
Da shigowarsa wannan dakin na cikon Dubu, sai yayi arba da wasu gabza-gabzan dodannin da sukafi dukkan dodannin da ya wuto baya.
Sudai wadannan dodanni babu komai a hannunsu, duk lokacin da suka kama wata halitta sai suyi Amfani da karfin damtsen su, su rinka gutsire sassan jikinta suna ci a hankali-a hankali har ta kare.
Ba tare da Bata lokaci ba wadannan dodannin suka rirrike RA'UFUL KALLUS sannan Daya daga cikinsu ya bangaren hannunsa na dama ya Bude tafkeken bakinsa, sannan ya kaftara hakoransa a jikin RA'UFUL KALLUS.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga wannan dodon ya kama da wuta ya kone kurmus.
Koda sauran dodannin suka ga haka, sai suka lura da kyau, cewa Ashe bangaren jikinsa na dama duk siffar dodanni gareshi.
Nan take suka juyo izuwa bangaren jikinsa na hagu, Nan ma wani daga cikin ya Bude lafcecen bakinsa ya lafta Masa cizo, sai gashi dodon nan ya cika bakinsa da Naman RA'UFUL KALLUS sannan cizgo wata lafceciyar tsokar nama daga jikinsa.
Nan take RA'UFUL KALLUS ya kwarara wani uban ihu har da kwallun wuya suka zuba Masa.
Bayan wannan dodon ya kammala cinye wannan tsokar Naman da ya cizgo ne, sai ya kauce wani dodon ma yazo ya Bude wangamemen bakinsa da nufin cika bakinsa da fatar RA'UFUL KALLUS, ba shiri RA'UFUL KALLUS ya fizgo wadannan makaman nasa da dayan hannun sannan ya fillewa wannan dodon Kai, Nan take RA'UFUL KALLUS ya takarkare wajen kisan dodannin nan Jini ya rinka malala da fantsama a sama.
Kafin a jima gaba dayan dakin ya cika makil da jinin dodannin nan.
A wannan lokacin ya kashe sama da dodanni dari biyar da hamsin.
Saboda tsabar yawan jinin dodannin da ya cika dakin ya zamana cewa shi kanshi RA'UFUL KALLUS jinin ya kusa shanye shi, dole sai da ya rinka iyo yana Kai hari da kisan dodannin.
Koda sauran dodannin suka ga haka, sai kawai suka rikide suka zama wani Katon dodo guda Daya.
A dai-dai wannan lokaci ne hannun RA'UFUL KALLUS yakai kan Kasar tsakiyar da aka daure a cikin wani Dan karamin kuttu.
Cikin zafin nama ya sure Kasar ya jefa a cikin battarsa, faruwar hakan keda wuya sai akaga wannan jibgegen dodon ya dauko Aljani RA'UFUL KALLUS da hannu guda, Yana wutsil-wutsil da kafafu sannan ya wangame Katon bakinsa ya jefa shi ciki.
Nan take dodon ya rufe bakinsa, sannan ya hadiye RA'UFUL KALLUS.
Ba zato ba tsammani sai kawai akaga RA'UFUL KALLUS ya fado birni na bakwai.....
Mu hadu a HATSABIBIN ALJANI na hudu part B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️♥️🥰
Najibullah Muhammad legends ✍️♥️♥️**HATSABIBIN ALJANI**
LITTAFI NA HUDU 4 ✅
PART B ✍️♥️
AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING: Najibullah Muhammad 🥷🥷🥷
Whatsapp Num... 08112778656.
Lokacin da RA'UFUL KALLUS ya tsinci Kansa a cikin birni na uku, sai yaga gaba dayan birnin zallan dabbobi ne.
Kuma dabbobin nau'i-nau'i ne gasu nan birjik babu kalar da babu.
Duk irin dabbar da mutum ya sani ko ya taba Jin labarin ta to akwai nau'inta a cikin wannan birni.
Saboda tsabar yawansu sun cika birnin gaba daya babu ta inda mutum zai bi ya wuce dole sai yabi ta cikinsu.
Su dai wadannan dabbobi gaba dayansu an rene su ne da Naman mutane da Aljanu saboda haka Basu da wani abincin da suke ci su rayu face Naman mutane da Aljanu.
Haka zalikha Kuma tsananin yawan dodannin yafi karfin a yake su, domin adadinsu ya haura milyan goma Kuma sun kasance jibga-jibga tamkar giwaye.
Bugu da Kari suna da tsananin gudu tamkar a Saman iska suke gudun.
Lokacin da RA'UFUL KALLUS ya tsinci Kansa a cikin wannan birni, sai yaga gaba dayan dabbobin nan sun rugu iyakar karfinsu da nufin yagalgala shi su cinye.
Cikin tsananin zafin nama ya hau Saman Gangar jikinsu ya rinka taka su Yana gudu iyakar karfinsa.
Nan fa wasu daga cikin dabbobin suka rinka tasowa sama suna kawo Maza bangaza da nufin kado shi daga Saman dabbobin da yake gudu, amma yana gocewa.
Wasu kuwa suka rinka amfani da jelarsu suna cilla Masa da nufin sargafo shi.
Cikin tsananin juriya da zafin nama RA'UFUL KALLUS yaci gaba gudu tare da tsalle-tsalle a Saman dabbobin nan tamkar Dan biri akan bishiyoyi.
Ana cikin hakane wata Mafi naci daga cikin 6aunaye ta daka tsalle sama ta cakawa RA'UFUL KALLUS kahonta guda a cinya, Nan take kahon ya Huda cinyar ya lume a jikinsa.
Nan fa jini ya rinka bulbula tamkar magudanar ruwa ta balle, ba shiri RA'UFUL KALLUS ya kurma wani wawan ihu.
Karfin ihun nasa ya cika birnin gaba Daya.
Nan take wannan 6aunar ta sargafo RA'UFUL KALLUS da kahonninta sannan ta mako Kasa a tsakiyar milyoyin dabbobin nan.
Fadowar sa keda wuya sai wata Katuwar giwa ta daga kafarta ta gaba ta take hakarkarinsa na dama inda siffar dodanni take.
Nan take kafar ta burma har sai da Kashin hakarkarinsa ya karye guda Daya.
Cikin tsananin radadin zafi da dimaucewa ya Kara kwarara uban ihu kawai sai ya langabe Kasa sumamme.
Ana cikin hakane wata Katuwar kura ta daka mugun tsalle ta duro ta cika bakinta da kafarsa da nufin cinyewa.
Nan fa sama da dabbobi dari uku da arba'in suka Afkawa RA'UFUL KALLUS da nufin kowa ta yagi rabonta.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai akaga Jikin RA'UFUL KALLUS ya rikide ya zama wani NARKEKEN DODO Mai tsananin girma da mummunar siffa.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga wannan jibgegen dodon ya Bude tangama-tangaman hannuwansa masu kama da manyan Tsaunika, ya tattaro sama da dabbobi dubu uku a tafin hannunsa sai gashi yana mutsittsike su tamkar yadda ake mutsittsike danyen tuwo a hannu.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga wannan jibgegen dodon ya watsa gaba dayan dambun Naman dabbobin a cikin bakinsa ya taune, sannan ya kwarara wani uban ruri Mai tsananin razanarwa Wanda ya haddasa girgizar birnin gaba Daya, Nan take wasu daga cikin dabbobin suka rinka faduwa Kasa matattu saboda tsananin Karar rurin dodon.
Sai da dodon nan ya shafe dakika dari da arba'in yana ruri sannan ya tsuke bakinsa.
Nan fa dodon nan ya dage iyakar karfinsa yana talitse dabbobin da kafafunsa, a duk lokacin da ya daga kafarsa guda Yana iya talitse dabbobi dubu.
Cikin abinda bai wuce sa'a guda ba RA'UFUL KALLUS ya kashe da dabbobi Milyan Daya da dubu dari biyu.
Ashe duk wannan Gumurzu da akeyi, akwai kimanin dabbobin ZAKUNA guda dubu Dari bakwai a can gefe guda sun tsaitsaya suna ta kallon yadda ake ta bakin GUMURZU.
Koda wannan dodon ya gama kashe gaba dayan dabbobin Dake gabansa,
Sai ya tunkari wannan rundunar zakunan take.
Koda isowarsa sai ya daga kafarsa guda da nufin talitse su, cikin tsananin zafin nama sama da zakuna dubu Dari suka cunkushe wuri guda sukayi wani ruri.
Koda kafar dodon ta dira akansu sai ta haifar da wata Kara wadda ta cika birnin gaba Daya.
Shi kuwa dodon sai yaji tamkar ya taka kafarsa akan karfe ne saboda tsananin taurin zakunan.
Faruwar hakan keda wuya sai ya janye kafarsa, Nan take wadannan ZAKUNAN sukayi wani gurnani Mai matukar razanarwa.
Faruwar hakan keda wuya sai aka ga gaba dayansu sun rikide sun zama wani JIBGEGEN ZAKI guda daya, wannan girmansa ya ninka na giwaye Arba'in.
Nan fa aka kacame da azababben yaki mai tsanani a tsakanin dodon nan da Kuma Zakin, ya zamana cewa suna bugun juna hannu da kafa.
A duk lokacin da dodon nan ya naushi Zaki sau Daya, sai da aga ya fadi Kasa sannan ya sake tashi cikin tsananin zafin nama yaci gaba da GUMURZU.
Shi kuwa Zakin idan ya naushi dodon sai yaga dodon ya shanye dukan sannan ya mayar da martani.
Nan Zakin ya fusata ainun ya rinka makalkale dodon Yana yakushinsa da manyan farata masu matukar girma da kaifi tamkar takubba aka lillika a jikin kafafun.
Kuma ya hada cizo da yakushi.
A duk lokacin da Zakin ya soka faratansa akan fatar dodon nan, sai yaji fatar tauri sosai tamkar karfe da karfe ne suka hadu har wani tartsatsin wuta ne ke tashi.
Amma saboda tsabar nacin Kai harin wannan Zakin har ya fara samun nasarar fara huda fatar dodon nan.
Kafin cikar dakika hamsin Zakin Nan ya samu nasarar yiwa dodon nan raunika arba'in a sassan jikinsa.
Koda ganin wannan Ala'mari sai ran dodon ya Baci, cikin tsananin Kunan rai, sai akaga wannan jibgegen dodon ya takarkare iyakar karfinsa ya matse wannan Zakin da dukkan hannayensa.
Nan fa Zakin Nan ya rinka wani irin ruri da gurnani saboda tsabar zafi da radadin da yake ji.
Koda dodon nan ya Kara matse shi sai ya fara kakkarya Kasusuwan jikin Zakin.
Nan fa dodon nan ya rinka Amfani da dukkan karfinsa yana gutsittsira sassan jikin Zakin Nan tamkar yadda ake gutsittsira Albasa akan fai-fai.
Kafin a jima yayi filla-filla da sassan jikin Zakin, sannan ya wangame tafkeken bakinsa ya juye shi a ciki, Nan take ya taune shi ya hadiye.
Faruwar hakan keda wuya sai yaga girmansa ya koma kamar yadda yake da, Amma har yanzu a bangaren hannunsa na dama siffar dodanni gareshi.
Kafin yayi wani yunkuri sai yaga bangaren jikinsa na hagu ya rikide daga siffar Aljani izuwa siffar zannan Zakin.
Nan take ya wuce Kai tsaye cikin birnin, sai da ya yawace gaba dayan kusurwowin birnin ya cizgo ganyayen bishiyoyin nan sannan ya zo tsakiyar birnin ya debo Kasar birnin ya zuba a cikin battarsa sannan ya juya hanyar ficewa daga cikin birnin gaba Daya.
Sai da yayi tafiyar sa'a biyu Sannan ya iso birni na takwas.
Da shigarsa wannan birni sai yayi arba da wadansu irin jibga-jibgan TSUNTSAYE masu matukar girma da tsinin baki.
Saboda tsananin girmansu duk tsuntsu Daya na iya daukar rakuma goma da kafafunsa yayi tafiyar wuni guda batare da ya gaji ba.
Haka Kuma bakinsu yana da tsananin tsini tamkar mashi ne aka lika a jikin bakin.
Duk abinda suka soka da wannan bakin sai dai aga abun ya huje ya rarake tamkar ansa wuta an Kona abun.
Tsuntsayen na da manyan fuka-fukai guda biyu masu girman gaske, wadanda ko bishiya suka makawa wannan fuka-fukan sai dai aga bishiyar ta tuge saboda tsabar kwarin fuffuken.
Tsuntsayen dukkansu kama sukeyi da MIKIYA.
Koda RA'UFUL KALLUS ya shigo wannan birni sai ya cika da tsananin mamakin ganin yadda tsuntsayen Nan suka cika ko'ina a cikin birnin.
Kafin yayi wani yunkuri tuni wani NARKEKEN TSUNTSU daga cikinsu ya fyauceshi ya tashi dashi sama sai ga RA'UFUL KALLUS yana ta wutsil-wutsil da kafafu tamkar an rataye shi.
Yana cikin wutsil-wutsil din ne ya waigo kawai sai yaga gaba dayan tsuntsayen nan sun biyo bayansu cikin matsanancin gudu tamkar na tauraruwa Mai wutsiya...
MEZAI FARU A TSAKANIN ALJANI RA'UFUL KALLUS DA WADANNAN TSUNTSAYEN?
SHIN RA'UFUL KALLUS ZAI SAMU NASARAR TSALLAKE HADARIN WANNAN BIRNIN?
SHIN BURIN ALJANI RA'UFUL KALLUS ZAI CIKA AKAN ZAMA GAGARABADAU KUMA SADAUKIN SADAUKAI?
INA LABARIN YAKIN DA AKE TSAKANIN DODDANIN DA RA'UFUL KALLUS YA AJIYE A KOGONSA DA KUMA SAURAN SARAKUNAN DUNIYA A KOGON DURGAFUL KALLUS?
Don Jin Amsar wadannan tambayoyin sai mu hadu a littafin HATSABIBIN ALJANI na biyar 5.
Daga mai debe maku kewa wato NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️🙏🙏
Nake cewa ku huta lafiya ✍️♥️
**HATSABIBIN ALJANI**
LITTAFI NA BIYAR 5 ✍️🙋
PART A &B complete book ✍️✍️🤝
AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷🥷
Lokacin da wannan NARKEKEN TSUNTSU ya Suri ALJANI RA'UFUL KALLUS da kafufuwansa yayi sama da shi, sai gashi yana ta wutsil-wutsil da kafafu tamkar an sargafe Dan tsako a jikin Katuwar kuka.
A wannan lokacin gaba dayan ragowar tsuntsayen sunbi bayan Katon tsuntsun da nufin kwato RA'UFUL KALLUS daga hannunsa su cinye shi.
A bisa wannan dalili ne yasa suke gudu iyakar karfinsu da nufin cimmasa Amma sun Kasa.
Shi kuwa wannan Katon tsuntsun Koda ya Suri RA'UFUL KALLUS burinsa shi ne, ya Kai shi can wata Katuwar sheqarsa dake cikin kogon wani Dutse a tsakiyar birnin ya cinyeshi shi kadai.
Dalilin da yasa sauran tsuntsayen suke iyakar kokarinsu wajen riskar Katon tsuntsun su kwato RA'UFUL KALLUS shi ne, lokuta dayawa idan wata halitta mai tsautsayi ta fado cikin wannan birni to wannan babban tsuntsun ne yake wuf ya dauketa sannan ya ruga dashi cikin kogon dutsensa ya cinye shi kadai.
Sai da wannan Katon tsuntsun yayi shekara arba'in yana cinye mutane da Aljanu da suka shigo wannan birni, Kai hatta dabbobin daji bai bari ba.
Komai hatsabibancin halitta muddin ta shigo wannan birni sunanta gawa.
Domin cikin kankanin lokaci yake kurewa halittar gudu ya kama ta, sannan ya caka mata mugun bakin nasa Mai kama da kibiya saboda tsananin tsini, take Halittar take ragargaje ta zama gawa, sai ya kwashe ta izuwa cikin kogonsa ya cinye ya zubar da Kasusuwan Nan.
Masana sun tabbatar da cewa wannan tsuntsun ya cinye mutane da Aljanu a Kalla guda dubu goma, domin da zarar ka kunna Kai a cikin kogonsa to tun daga farko zaka fara yin arba da Kasusuwan mutane da Aljanu wadanda tuni sun zama kwarangwal harma sun fara bushewa suna ratattakewa a Kasa.
Yau kimanin shekaru goma kenan wadannan tsuntsayen Basu ci Naman mutane da Aljanu ba, dole sai dai su rinka cin 'yayan itatuwa don su rayu.
Duk da cewar suna matukar son Naman mutane da Aljanu, Kuma suna iyakar kokarinsu wajen ganin sun kashe yunwar dake addabarsu, Amma abun haushi wannan jibgegen tsuntsun ya hana su sakat, har yau sun Kasa samun ko guda Daya su ci.
Wannan yasa gaba dayan ragowar tsuntsayen suka rarrame ainun saboda tsabar yunwar Naman mutane da Aljanu, a sakamakon haka ne yasa suka sallama rayuwarsu akan cewa lallai kota wane hali, a yanzu duk halittar da ta shigo cikin wannan birni to su ne zasu cinyeta, idan kuwa har haka Bai faru ba to dole zasu hada karfi da karfe akan su yaki wannan babban tsuntsun Koda zai kashe gaba dayan su.
Alla-bashi idan sun kashe shi, sai su cinyeshi, Kuma daga Nan sunyi maganin Mai cinye rabonsu.
A bisa wannan dalili ne yasa har suka raya a ransu cewa Koda zasu rasa rayuwarsu sai sun kwato RA'UFUL KALLUS daga hannun wannan tsuntsun.
Nan fa aka Kasa mugun tsere a tsakanin wannan Katon tsuntsun da Kuma sauran 'yan uwansa.
Ya zamana cewa tsuntsun sai shawagi yake yi a sama tare da jujjuyawa domin kaucewa harin da sauran tsuntsayen ke kawowa RA'UFUL KALLUS.
Har a sannan dai RA'UFUL KALLUS na maƙale a jikin kafafun wannan Katon tsuntsun yana wutsil-wutsil, tsuntsun yayi Amfani ne da yatsun kafarsa ya rike Aljani RA'UFUL KALLUS da su, ta yadda duk juyin juya hali bazai taba kuccewa ba.
Domin yatsun kafar tsuntsun sun rintse gaba dayan jikin RA'UFUL KALLUS, ya zamana cewa tamkar ansa igiyoyi an daddaure shi.
Sai da aka shafe sa'a guda ana wannan tsere batare da kowa ya samu nasarar komai ba.
A wannan lokaci ne babban tsuntsun ya iso inda sheqarsa take, da zuwansa bayyi wata-wata ba ya kutsa Kai cikin kogon.
Koda sauran tsuntsayen Nan suka ga haka sai suka yanyame Saman kogon dutsen nan suna masu wangame manyan bakunansu suna cakar Saman dutsen kogon ba kaukautawa tamkar yadda kaza ke caccakar hatsi.
A duk lokacin da tsuntsayen nan suka caka bakinsu akan Dutsen, sai dai aga sun 6antaro wani wawaken dutse daga Saman kogon.
Nan fa zage dantse sosai wacen caccaka bakinsu akan kogon shi kuwa dutsen ya rinka tarwatsewa Yana ragargajewa tamkar ana fasa Marmara da gudumar karfe.
A cikin dakika hamsin sai da sukayi raga-raga da gaba dayan dutsen kogon ya zamana cewa, sun ragargaje dutsen gaba daya tamkar yadda ake ragargaje soshiya domin fidda tsabarta, sai gashi Katon tsuntsun da RA'UFUL KALLUS sun bayyana a sarari, tamkar wani Dutse Bai taba wanzuwa ba a wajen.
Cikin tsananin mamaki RA'UFUL KALLUS ya bude Baki Yana kallon irin Kaifi da Kuma kwarin bakunan wadannan tsuntsayen, sannan Kuma ya lura da irin tsananin karfi da zafin naman tsuntsayen.
Kuma babban abinda yafi bashi mamaki shi ne, har suka kammala ragargaje dutsen kogon ko alamar kwarzane daya a bakunansu babu ballantana tsinin bakinsu ya lalace.
Kafin wani daga cikinsu yayi yunkuri tuni wadannan tsuntsayen sunyiwa Katon tsuntsun Nan Kawanya sannan sun afka Masa gaba dayan su.
Cikin tsananin zafin nama Katon tsuntsun nan ya suri RA'UFUL KALLUS da dan yatsa guda ya jefa shi a kui6in fuffuken sa na hagu, Nan take yayi Amfani da wannan fuffuken ya rufe shi ruf.
Nan fa RA'UFUL KALLUS yaji tamkar an wurgashi a cikin RIJIYA GABA DUBU saboda tsananin zurfin fuffuken tsuntsun, domin ji yayi tamkar ansa Katuwar kwarya an kife dan tsako saboda tsananin girman tsuntsun.
Faruwar hakan keda wuya sai aka kacame da masifaffen yaki a tsakanin tsuntsayen, ya zamana cewa suna tsalle da cakar junansu da wadannan bakunan nasu matukar Kaifi da tsini.
Koda aka fara wannan Gumurzu sai Katon tsuntsun nan ya rinka cakawa kananun tsuntsayen nan tafkeken bakinsa iyakar karfinsa, kawai sai dai aga bakinsa ya lume a jikin tsuntsun yayi fata-fata da gangar jikinsa tamkar an markade jikin tsuntsun.
Tsananin zafin naman tsuntsun ya wuce misali, a cikin dakika dari da arba'in sai da ya kashe sama da tsuntsaye dubu uku da dari biyar.
Duk Inda mutum ya duba sai dai yaga gawarwakin tsuntsayen nan birjik himili guda tamkar Tsauni.
Koda ragowar tsuntsayen suka ga haka, sai suka rinka rarrabuwa izuwa rukuni-rukuni, ya zamana cewa wasu a sama, wasu a gefensa hagu da dama, wasu gabansa da bayansa, wasu Kuma a kasansa.
Koda sukayi wannan dabarar sai suka sake afka Masa a lokaci guda.
Nan take suka yanyameshi tamkar yadda kudan Zuma ke yanyame gidansa idan yayi Saqa.
Nan fa tsuntsayen nan sukayi wa Katon tsuntsun nan rubdugu, ya zamana cewa ta ko'ina kawo masa Sara suke da wannan mugun bakin nasu Mai kama da sabuwar Reza.
Ana fara wannan Gumurzu ne wannan Katon tsuntsun ya rena Kansa, domin harin da sauran tsuntsayen ke kawo masa ya wuce misali.
A duk cikin dakika daya jal suna iya kawo masa caka da wannan bakunan nasu sau dari da tamanin, ya zamana cewa ko kadan baya iya kare hare-haren su gaba daya.
A Sakamakon hakane yasa suka rinka samun nasarar caccaka masa wannan zungureren bakin nasu a sassan jikansa.
Nan fa wannan Katon tsuntsun ya rinka wani irin kuka Mai ban tausayi, ya rinka tumuwa Kasa yana tashi, ya rinka karo da bishiyoyin birnin da sauran gidaje suna zubewa Kasa, Amma duk da haka sauran tsuntsayen Basu fasa caccaka masa wannan lafcecen bakin nasu ba.
Ba su gushe ba suna yakar wannan Katon tsuntsun sai da sukayi fata-fata da sassan jikinsa ya zamana cewa sun samu nasarar huhhuda jikinsa, ko'ina Yana ta kwararar da jini tamkar wani sashe daga cikin tekun jini.
Ana cikin hakane wasu daga cikin tsuntsayen mafiya karfi da naci suka samu nasarar cizge gaba dayan fuka-fukan Katon tsuntsun, sai gashi kowane fuffuke ya fadi Kasa, a wannan lokaci dakyar Katon tsuntsun Nan ke iya tsayuwa akan Kafafunsa.
Koda RA'UFUL KALLUS yaga ya fado Kasa Kafafunsa sun taba turba yayi tsuru-tsuru shi kadai.
Nan take ya runtuma a na kare domin gujewa wadannan tsuntsayen.
Shi kuwa wannan Katon tsuntsun sai ya rinka wani irin kuka mara dadin ji, tamkar ana goga dutse da dutse akan karfe.
Kawai sai akaga yayi wani irin girgiza da nufin kado sauran tsuntsayen Dake samansa.
Nan take ya rinka jeho su suna fadowa Kasa tamkar ana girgiza bishiyar mangoro, ana cikin hakane wani tsuntsu Mai tsananin naci ya Bude lafcecen bakinsa ya caka akan tsakiyar Kan Katon tsuntsun nan iyakar karfinsa.
Nan take bakinsa ya lume a jikin Kan, sai gashi kokon kan ya burma tamkar an 6urma kabewa.
Nan take jini da kwanya suka rinka Malala a Kasa suna tsiri da fantsama a sama tamkar magudanar ruwa ta balle.
Kafin cikar dakika biyar ya fadi Kasa matacce ko shurawa Bai Kara Yi ba.
Faruwar hakan keda wuya sai sauran tsuntsayen gaba dayansu suka bi bayan RA'UFUL KALLUS, a wannan lokacin tuni ya kusa fita birnin gaba daya saboda tsananin karfin gudunsa.
Amma a cikinsa abinda bai wuce dakika arba'in ba tsuntsayen nan suka cimmasa, da zuwansu sai tsuntsun da ke kan gaba ya bude Katon bakinsa ya cafko RA'UFUL KALLUS da nufin hadiyeshi, kafin ya Ida nufin abinda yayi niyya tuni wani tsuntsun dake biye da shi ya lafta mashi cizo a wuya, Nan take wuyan ya gutsire sai ga tsuntsun ya rabu gida biyu kowane bari ya fadi can gefe guda, shi kuwa RA'UFUL KALLUS sai ya fado Kasa.
Cikin tsananin zafin nama wani tsuntsun ya sake cafko RA'UFUL KALLUS da nufin cinyeshi, Nan ma wani daga cikin tsuntsayen ya ragargaje wannan tsuntsun da bakinsa ya fado Kasa matacce.
A haka wadannan tsuntsayen suka rinka kashe 'yan uwansu batare da sun ankara ba, ya zamana cewa duk tsuntsun da ya dauki RA'UFUL KALLUS da nufin cinyewa take wani