An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
**HATSABIBIN ALJANI**
LITTAFI NA DAYA 1 ✍️
PART A ✍️♥️
MARUBUCI: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️♥️
MARUBUCIN GASAR JARUMTAKA......
Kimanin shekaru dubu uku baya da suka wuce a Kasar HARKUMU. Anyi wani takadarin Aljani Wanda ya fitini gaba dayan jinsin mutane da Aljanu.
Shi dai wannan Aljani sunansa RA'UFUL KALLUS.
Kuma shekarunsa dubu arba'in da bakwai a duniya.
Aljani RA'UFUL KALLUS ya kasance tsawon zamunna a cikin duniya.
Masana tarihi sun tabbatar da cewa wannan Aljanin tun kafin zuwan Annabi Sulaimanu dan Dawuda ( A.s ) yake.
Haka Kuma a gaba dayan rayuwar Aljanin RA'UFUL KALLUS ba a taba samun aljanin da ya iya nasara akan sa ba.
RA'UFUL KALLUS ya kasance Kasurgumin matsafi Kuma Azzalumi Wanda ya mayar da zalunci a matsayin Sana'a.
Dalilin dayasa Aljani RA'UFUL KALLUS ya zama Gawurtaccen Azzalumi shi ne, tun Aljani RA'UFUL KALLUS Bai wuce shekara Dari biyar ba a duniya yake Bauta a hannun manyan BOKAYEN DUNIYA na jinsin mutane da Aljanu.
Kuma ya Sha matukar wahala a hannun wadannan BOKAYEN domin duk lokacin da wani aiki Mai matukar hatsari ya tashi, to shi ake nemowa ace dole sai yayi shi.
A haka ya rinka daurewa Yana yin Bauta a hannun BOKAYEN mutane da Aljanu har tsawon shekaru dubu Ashirin da biyar.
RA'UFUL KALLUS yayi iyakar kokarinsa wajen ganin ya samu 'yancin Kansa ga barin yiwa BOKAYEN DUNIYA Bauta Amma Abu ya faskara, domin duk lokacin da yayi yunkurin yin Tawaye daga hannun bokayen da yake yiwa Bauta sai Bokan yayi Amfani da karfin tsafinsa ya ladaftar da shi, ta yadda sai yayi jinya ta Kwanaki casa'in sannan yake warkewa.
A kullum ALJANI RA'UFUL KALLUS ba shi da wani buri face ya samu 'yancin kanshi, ya zamana cewa yafi karfin duk Jaruman duniya da Kuma bokayen DUNIYA da Kuma sarakunan duniya.
A haka ALJANI RA'UFUL KALLUS ya ci gaba da Bauta a wurin bokaye daban-daban har guda Milyan arba'in.
A dalilin Bauta da yake karkashin bokaye iri-iri ne yasa ya mallaki sirrikan tsafin da duk duniya babu kamarsa.
A hankali a hankali ya fara shahara.
Koda Aljani RA'UFUL KALLUS yaga ya tumbatsa Kuma ya samu duk abinda yake son samu, sai ya Yanke shawarar bibiyar duk iyalan bokayen da suka azabtar dashi lokacin da yake Bauta a wurinsu domin ya dauki fansar wahalar da shi da sukayi.
A cikin shekara biyar sai da Aljani RA'UFUL KALLUS ya kashe 'yayan Bokayen mutane da Aljanu Dubu saba'in da bakwai.
Duk da haka sai ALJANI RA'UFUL KALLUS ya rinka bin kasashen duniyar mutane da Aljanu Yana Amfani da karfin sihirin tsafin da yake dashi da Kuma tsagwaron karfin damtsen shi, Yana kwashe gaba dayan duk dukiyar birnin Yana kwashewa ya Kai ta can wani Katon kogon dutsen da ya ajiye sirrakan tsafinsa acan.
ALJANI RA'UFUL KALLUS Bai gushe ba, Yana yakar sarakunan duniya Yana kwace dukiyarsu har sai da kogon Dutsen da yake Tara dukiyarsa ya cika makil da zinare da Azurfa da jauhari, zubar-daji Azurfa, lu'u-lu'u da sauran duwatsu masu daraja.
ALJANI RA'UFUL KALLUS ya kasance gabjejen Kato Mai tsananin karfin damtse na gaban kwatance.
Lokuta dayawa sarakuna sun Sha yin Shirin yaki domin hallaka Aljani RA'UFUL KALLUS Amma Abu ya gagara domin cikin abinda Bai wuce rabin sa'a ba yake hallakar da gaba dayansu.
Sau dayawa idan ALJANI RA'UFUL KALLUS ya Rena runduna a filin yaki ma, sai dai kawai ya daka masu wata irin tsawa Mai hade da lantarki wadda take shiga mutane.
Sai dai aga kawai cikin dakika hamsin rundunar ta sulale Kasa matattu komai yawansu.
ALJANI RA'UFUL KALLUS na iya rikide kowace irin halitta yake so, walau cikin mutane da dabbobi.
Kai hatta bishiyoyi da sauran kwaruka masu yawo a Kasa Yana iya rikidewa izuwa siffarsu.
A bisa wannan dalili ne yasa gaba dayan BOKAYEN DUNIYA da SARAKUNAN duniya na jinsin mutane da Aljanu suka hada KARFI DA KARFE domin ganin bayan Aljani RA'UFUL KALLUS.
LOKACIN da Aljani RA'UFUL KALLUS yaga bokayen duniya da sarakunan duniya sun hada Kai domin su yake shi, sai ya shiga halwar tsafinsa na kwana biyu domin ya gano hanyar da zai gagari duk mutanen duniya da aljanun duniya.
Bayan ya kammala bincikensa a halwar tsafinsa sai ya cika da tsananin farin ciki mara misaltuwa.
Ba komai bincikensa ya nuna Masa ba face, muddin Yana so yayi nasara akan duk makiyansa shi ne dole ne ya shiga duniya domin ya tattaro Hatsabiban bil'adama masu taurin zuciya guda dubu, sannan ya shiga kasashen Aljanu su ma ya tattaro manyan sadaukan Aljanu masu tsananin taurin zuciya guda dubu.
Bayan ya gama tattara gaba dayansu ne, zayyi Amfani da wani ruwan tsafi ya wankesu da shi, sannan sai ya Saka su a cikin wani Katon turmin tsafi ya Dake su, ya tsiyaye jininsu a cikin wata Katuwar kwatanniya ya rinka Sha har tsawon kwana bakwai, shi Kuma dakakken Gangar jikin Aljanu da mutanen sai ya rinka shafawa a jikinsa sau uku a Rana tsawon kwana biyar.
Muddin yayi haka to duk halittar da ta tunkaro shi da nufin cutarwa, da zarar sunyi arba da shi za a ga halittar ta kone kurmus ta zama toka.
Yayinda Aljani RA'UFUL KALLUS ya kammala wannan bincike nasa, sai ya cika da tsananin farin ciki nan take ya rinka kyalkyalewa da dariyar mugunta kamar bazai dena ba..
Daga karshe ya Yanke shawarar fara aiki Nan take.
Daga wannan rana Aljani RA'UFUL KALLUS ya rinka ni kasa-kasa Yana dauko manyan jarumai masu dakakkiyar zuciya da taurin zuciya har sai da ya samu nasarar dauko guda dari bakwai da tamanin da Tara.
Dama tuni Aljani RA'UFUL KALLUS ya Gina wani wawakeken gida Mai daukar mutum dubu goma, Kuma ya tsafe gidan da sirrikan tsafi guda dubu Daya, ta yadda Komai hatsabibancin mutum bazai iya fitowa daga gidan ba.
A lokacin da Aljani RA'UFUL KALLUS ya tafi domin dauko jarumi na cikon takwas cif-cif.
Koda yazo kofar birnin sai yayi niyyar shiga Amma ya Kasa, sai da Aljani RA'UFUL KALLUS ya zagaye birnin Nan sau dari da arba'in Yana Neman hanyar shiga Amma ya Kasa.
Nan fa Aljani RA'UFUL KALLUS yayi nufin ya fasa Katangar birnin domin ya shiga da karfin tsiya, Amma sai ya Kasa domin duk lokacin da ya tunkari birnin sai yaji tamkar an daddaure da sarkokin tsafi bisa dole yake yin baya.
Nan fa abun yayi matukar bashi mamaki Kuma ya daure Masa Kai.....
Tom mu hadu a HATSABIBIN ALJANI part B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️♥️🥰**HATSABIBIN ALJANI**
LITTAFI NA DAYA 1 ✍️
PART B ✍️♥️
MARUBUCI: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️🥷🥷
MAWALLAFIN GASAR JARUMTAKA ✍️✍️🤝
Lokacin da ALJANI RA'UFUL KALLUS yayi iyakar kokarinsa wajen shiga birnin Nan Amma ya Kasa, sai abun yayi matukar bashi mamaki ya Kuma daure masa Kai.
Nan take ya yanke shawarar komawa kogonsa domin ya sake bincike akan dalilin da yasa ya Kasa shiga wannan birni.
Ba tare da Bata lokaci ba ya juya ya tunkari kogon tsafinsa, da isowar sa ya shiga halwar tsafi ta sa'a biyu.
Koda kammala binciken sai hankalinsa yayi mummunan tashi, idanuwansa sukayi jawur saboda tsananin fusata har sai da gashin Kansa ya mimmike.
Ba komai Aljani RA'UFUL KALLUS ya binciko ba, face ganin cewa wannan birnin da ya gagare shi shiga gaba dayan mutanen birnin ma'abota Addinin musulunci ne, Kuma suna da kariya ta musamman daga wajen ubangijinsu ta yadda duk duniya babu wata halitta da ta Isa ta shiga har cikin birnin ta cutar da su.
Nan take ALJANI RA'UFUL KALLUS ya sake shiga halwar tsafi domin gano wata hanyar.
Sai da ya sake shafe sa'a Ashirin cif Yana bincike sannan ya gano mafita.
Mafitar kuwa ita ce, muddin Yana so ya cika burinsa na zama GAGARABADAU Kuma SADAUKIN SADAUKAI Wanda har abada ba za'a iya nasara akansa ba, to dole ne yayi shiri ya shiga karkashin Kasa domin ziyartar wasu birane masu matukar ban a'aljabi guda dubu Daya, sannan duk birnin da ya shiga sai ya debo Kasar birnin, tare da tsinko ganyayen wasu bishiyoyi guda hudu na bangaren gabas da yamma Kudu da Arewa.
A haka zai rinka shiga wadannan birane Daya bayan Daya Yana debo Kasar tsakiyar birnin kowane tare da wadannan gayayye har ya kammala ziyartar duka guda dubun.
Bincike ya tabbatar Masa da cewa muddin ya harhado nau'ikan Kasar biranen Nan guda dubu Daya da Kuma ganyayyakin su.
Sa'annan Kuma ya hada su a tukunyar tsafinsa gaba dayansu ya Sha, ya shafe jikinsa da su.
To sai ya Mulki duka duniya, domin Hatta tsuntsaye da dabbobin daji da kowace halitta zasu rinka karbar Umarni ne daga wajensa kafin su aiwatar da komai.
Haka Kuma zai taka matsayin da duk duniya babu Wanda ya taka shi tun farkon kafuwar duniya, Kuma har duniya ta nade babu Wanda zai maye gurbinsa.
Yayinda ALJANI RA'UFUL KALLUS ya gama wannan bincike sai kawai ya kyalkyale da mahaukaciyar dariya kamar Wanda ya samun tabun kwakwalwa, sai da ya shafe sa'a guda Yana kyalkyala dariyar mugunta sannan ya tsuke bakinsa.
Bayan ya gama dariyar ne sai tunanin yakin da ke gabanshi tsakaninshi da bokaye da sarakunan duniya ya fado Masa a Rai, Wanda a yanxu haka sun kusa karasowa gareshi, domin Nan da cikar sa'a arba'in zasu iso gareshi.
Nan fa ALJANI RA'UFUL KALLUS ya shiga tunanin Neman mafita, domin yasan cewa muddin ya shiga karkashin Kasa domin fara aiwatar da wannan aikin nasa, Kuma wadannan mayakan suka zo Basu iske shi ba, to sai sun lalata gaba dayan sirrikan tsafinsa sannan su kwashe gaba dayan dukiyar da yayi shekara da shekaru Yana Tarawa.
Idan kuwa hakane duk burinsa ya Yanke.
Yana cikin wannan tunani ne wata dabara ta fado Masa, kawai sai ya sake bushewa da dariya a karo na biyu.
Ba wata dabara bace, face ya tuna cewa a can Karshen duniya daga bangaren kudu akwai wasu jibga-jibgan SAMUDAWAN DODANNI masu cin Naman mutane da Aljanu da suke rayuwa a wajen.
Kuma wadannan DODANNI suna da tsananin yawa na gaban kwatance, domin sun Haura Milyan arba'in.
Bugu da Kari a halin yanzu wadannan DODANNI cike suke da kishirwar Naman mutane da Aljanu, saboda a yanzu shekara arba'in kenan rabon da wani Aljani ko bil'adama yaje yankisu, ballantana har su cinyesu.
Tabbas kwadayin Naman mutane da Aljanu ya addabesu ta yadda a halin yanzu sun kusa Karar da gaba dayan bishiyoyi da Duwatsun Dajin saboda yunwa.
Koda Aljani RA'UFUL KALLUS ya gama wannan tunani sai Bude fuka-fukansa guda dubu goma ya luluka sama ya tunkari bangaren da wadannan DODANNI suke.
Cikin abinda Bai wuce sa'a guda da rabi ba, ya iso wurin da suke.
Da zuwansa sai sama da DODANNI dubu Dari suka Miko hannu da niyyar cafko shi su cinye.
Koda ganin haka sai ya rikide ya zama iska, ta yadda kamshinsa kawai suke iya ji Amma basa iya ganinsa.
Nan fa sukayi iyakar kokarinsu domin ganin inda wannan Aljani ya boye Amma Abu ya faskara.
Zuwa can sai sukaji an bushe da dariya, sannan Kuma ance sunana ALJANI RA'UFUL KALLUS, ni ne Aljanin da ya gagari duk mutanen duniya da duk Aljanun duniya.
Saboda haka ba zaku iya cutar Dani ba, Koda zaku shekara Milyan Kuna kokarin hakan.
Kuyi sani cewa na San abinda ya addabeku na rashin samun Naman mutane da Aljanu tsawon shekaru.
To kuyi sani cewa a yau nazo maku da cikar burin ku, ta yadda indai kukayi abinda nake so, to sai Kun Gaji da cin Naman mutane da Aljanu iya tsawon rayuwarku.
Cikin tsananin farin ciki waɗannan DODANNI suka ce sun amince da kowane irin aiki ne.
Nan take ALJANI RA'UFUL KALLUS yayi tsafi sai wata iska Mai tsananin karfin tsiya ta tattare gaba dayan DODANNIN Nan suka bace.
Ba su bayyana a ko'ina ba sai a kofar Kogon Nan da ya ajiye sirrakan tsafinsa da Kuma dukiyarsa.
Da zuwansa sai yayi masu nuni da cewa inaso kuyi Mani gadin wannan kogon, Kuma Kar su bari ko sauro ya shiga cikinsa.
Haka Kuma yayi masu bayanin cewa Nan da kwanaki biyu masu xuwa akwai rundunar mutane da Aljanu da zasu zo domin shiga wannan Kogon, Kuma adadinsu yakai Milyan Dari.
Saboda haka suyi iyakar kokarinsu wajen hanasu shiga Kogon.
Koda gama wannan jawabi sai Aljanun suka cika da tsananin murna, Kuma suka raya a ransu cewa muddin wadannan rundunoni suka karaso, to ba zasu kashesu duka ba, sai dai su boye su a wani wuri su rinka tsakurowa da guda-guda suna ci kullum har su kare.
Nan fa tsananin maitar su da kwadayinsu ya tashi suka kama lashe-lashen Baki, sukaji cewa sun kagara ko sun fara yin Loma guda da mutane da Aljanu.
Nan take ALJANI RA'UFUL KALLUS yayi sallama da wadannan DODANNI tare da sanar dasu cewa sai ya dawo.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga ALJANI RA'UFUL KALLUS ya rufe idanunsa sannan ya fara karanto wadansu dalasiman tsafi Yana tofawa a Kasa, kafin cikar dakika hamsin sai akaga Kasar wurin ta Samar da wata wawakekiyar tsaga, Nan take ALJANI RA'UFUL KALLUS ya rikide ya zama haske ya ratsa ta cikin tsagar.
Wucewar sa keda wuya sai Kasar wurin ta koma ta hade tamkar babu abinda ya faru...
Ala'marin ALJANI RA'UFUL KALLUS kuwa, lokacin da ya shige cikin karkashin Kasa bayan yayi tafiyar sa'a biyar kawai sai ya tsinci Kansa a wani tafkeken birni Mai matukar kyau da kawatuwa.
Gaba dayan gidajen wannan birni a ginasu ne da zallan jauhari Mai siffar ruwan kwai.
Sannan Kuma babu komai a cikin wannan birni face wadansu irin halittu masu siffar karnuka da birai.
Daga wuyansu abinda yayi gaba dayan kansu duk na Karnuka ne, sannan Kuma daga kirjinsu zuwa Kafafunsu na birai ne.
Su dai wadannan halittu adadinsu yakai Milyan Dari, Kuma kowannensu harkar gabansa yake domin babu Wanda ya Kalli inda ALJANI RA'UFUL KALLUS yake ma ballantana yayi yunkurin cutar da shi.
Koda ALJANI RA'UFUL KALLUS ya lura da cewa wadannan halittun ba ma ta shi suke ba, kowa harkar gabansa yake.
Kawai sai ya tafi izuwa tsakiyar birnin, da isarsa yasa hannu da nufin dibar Kasar.
Ba zato ba tsammani sai kawai yaga wani Mafi kankanta daga cikin wadannan halittu ya rugo gareshi ya gabza Masa naushi a Fuska, saboda tsananin karfin naushin sai da ya sulale Kasa sumamme.
Nan take sauran halittun suka jawo murtuka-murtukan igiyoyi suka daddaure Aljani RA'UFUL KALLUS da su, Sannan suka kinkime shi suka rinka tafiya dashi, suna ratsa lungu da Sako na cikin birnin har suka zo da shi wani tafkeken gida Wanda yafi kowane girma a birnin.
Da zuwansu sai sukayi turus, bayan kamar Dakika sittin sai ga wani jibgegen halitta kamar ya fito cikin gidan, a Kansa akwai hular karfen zinare Mai nuna sarautar birnin.
Mu hadu a HATSABIBIN ALJANI na Daya part C domin Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️✍️🙏**HATSABIBIN ALJANI**
LITTAFI NA DAYA ✍️✍️
PART C ✍️♥️
MARUBUCI: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷
GORON JUMA'A 🤝
Lokacin da wadannan halittu suka kawo ALJANI RA'UFUL KALLUS a gaban Sarkinsu, sai gaba dayansu suka koma gefe guda suka risina cikin girmamawa.
Basu dago daga sujjadar su ba, har sai da sukaji Sarkinsu yayi wani irin gurnani sannan suka dago Kai.
Nan take Sarkin garin ya nuni da nufin me ALJANI RA'UFUL KALLUS yayi aka kawo shi Nan a daure, cikin biyayya wani daga cikin halittun ya fito Yana Yi Masa bayani akan laifin da ya aikata a cikin wani yare Mai Kara da gurnani Wanda babu Mai fahimtar shi sai su kadai.
Koda fara Jin wannan jawabi, sai Nan take ran halittun ya Baci ainun Kuma suka fusata, har sunyi nufin Afkawa ALJANI RA'UFUL KALLUS domin su yagalgala shi saboda wannan gagarumin laifi da yayi Amma sai Sarkinsu ya dakatar da su ta hanyar daga masu hannu.
Ba komai yasa sauran halittun suka fusata ainun saboda Jin bayanin laifin da Aljanin ya aikata ba, face saboda wannan Kasar da yake kokarin diba, ita ce gaba dayan halittun suke Bauta mawa, saboda su kansu Basu yarda dayansu yayi Amfani da Kasa ba bisa kowace irin bukata.
Wannan yasa hatta gidajensu da zallan jauhari suka ginasu babu sirkin Kasa ko kadan.
Bugu da Kari Kuma a duk bayan wata guda suna zuwa bangarorin garin, su debo ganyayyakin bishiyoyin da ALJANI RA'UFUL KALLUS yazo Nema, sannan su zubawa wannan Kasar da sunan hadaya.
Nan take Sarkin yayi nuni akan a kwance a Aljani RA'UFUL KALLUS, cikin hanzari wadansu manyan Sadaukai daga cikin jinsin halittun suka zo suka tsittsinke Sarkar da ta daureshi.
Sannan Sarkin ya dubi Aljani RA'UFUL KALLUS yayi Masa bushara da cewa daga yau ya zama bawansa Kuma shine zai rinka kwashe Kasa da fitsari da duk wani abun kazanta Yana Wanka dasu a jikinsa tsawon kwana saba'in a matsayin hukuncin laifin da ya aikata.
Koda Jin hukuncin da aka yankewa Aljani RA'UFUL KALLUS sai sauran halittun suka bushe da dariya, saboda sun San irin warin da Kashin Sarkinsu ke da shi.
Domin duk lokacin da Sarkinsu zayyi bahaya to sai gaba dayan birnin ya gauraye da wari da doyi, Kuma sai garin yayi kwana bakwai warin Bai dena ba.
Shi kuwa ALJANI RA'UFUL KALLUS sai ya cika da tsananin bakin ciki har sai da kwallah ta zubo Masa.
Yayi tunani a cikin ransa cewa, shi ne Aljanin da ya gagari duk mutanen duniya da aljanun duniya, Amma yau gashi a cikin wadansu irin Hatsabiban halittu wadanda suka Fi shi hatsabibanci domin har sun mayar da shi bawansu.
Nan fa ALJANI RA'UFUL KALLUS yayi iyakar kokarinsa domin yayi Amfani da karfin sihirin tsafi Amma a banza tsafin yaki yin tasiri.
Bisa dole ya hakura ya cigaba da Bauta ga wannan Sarkin.
Kuma kullum sai Sarkin Nan yasa anyiwa ALJANI RA'UFUL KALLUS bulala Dari.
Daga wannan Rana kullum sai Sarkin Nan yayi Kashi Mai yawa, Kuma ya tilastawa ALJANI RA'UFUL KALLUS akan dole ya shafe jikinsa dashi ko kuma ya hallaka shi.
Bisa dole Aljani RA'UFUL KALLUS ya cigaba da biyayya ga wannan Sarki Kuma Yana ta tunanin mafita.
A haka ya wanzu har tsawon kwanaki goma, a duk cikin wadannan kwanakin Aljani RA'UFUL KALLUS ya lura da wadannan halittu cewa iyakar ganinsu da rana ne, da zarar dare yayi dundum suke gani sai kowannensu ya tsaya a inda yake har gari ya waye sannan suci gaba da harkokinsu.
Koda ALJANI RA'UFUL KALLUS ya lura da haka sai farin ciki ya kama shi, domin ya San cewa lokacin guduwarsa yayi.
Amma dole zai Jira izuwa lokacin da wadannan halittun zasu je su debo wadannan ganyayyakin su zuba a kasarsa inyaso daga baya shi sai ya kwashe su cikin dare ya sulale yabar garin.
Haka kuwa Ala'marin ya kasance, wato washe garin kwana na goma ne Sarkin garin ya tara manyan Dakarunsa sannan ya umarce su akan su kasu Kashi hudu, na kowace kusurwa a garin domin tsinko ganyayen bishiyoyin nan a kawowa uwargijiyarsu Kasa.
Nan da suka fantsama, bayan 'yan sa'o'i da tafiyar su suka dawo.
Sannan Sarki ya Bada Umarni gaba Daya aka dunguma aka tafi tsakiyar birnin aka zuba wadannan ganyayen bishiyoyin Kuma suka yanka wadansu manyan dabbobi da nufin Kara Neman kusanci ga Abar bautarsu.
A Wannan lokacin Aljani RA'UFUL KALLUS Yana lura da duk Inda aka ajiye kowane ganye.
Saboda bayan sun gama bautarsu sun koma gida dare ya raba, sai Aljani RA'UFUL KALLUS ya sadado batare da kowa ya ganshi ba, ya rinka tafiya cikin Sanda don Kar aji motsinsa.
Haka ya rinka wuce wadannan halittun a tsaye tamkar gumaka Amma Basu iya ganinshi har yazo dai-dai inda aka ajiye wadannan ganyayen bishiyoyin, Nan take Yasa hannu ya diba Kuma ya debo Kasar birnin ya zuba su a cikin wata Katuwar battar fata wadda ya rataya.
Faruwar hakan keda wuya sai ya tunkari hanyar barin garin, Yana tafiya cikin sauri da Kuma gudu don Kar safiya tayi Masa.
Bai gushe ba Yana tafiya har tsawon sa'a biyar, a wannan lokacin ya kusa fita birnin gaba Daya, Amma Kuma hasken rana ya fara fitowa har halittun birnin sun fara gani Kuma sun fara cigaba da harkokinsu.
Koda suka hango ALJANI RA'UFUL KALLUS na Shirin guduwa sai sama da halittu dubu suka bishi da nufin su kamo shi.
Nan fa aka Kasa tsere, ya zamana cewa Aljani RA'UFUL KALLUS gudu yake iya karfinsa har tashi sama yake saboda karfin gudun, Amma da zarar ya waigo sai yayi arba da wadannan halittu dab da shi.
Nan fa hankalinsa ya dunguzuma ya Kara kaimin gudun, domin ya tabbatar da cewa indai ya sake ya Kara fadawa hannunsu to sai sun hallaka shi.
Haka dai akaci gaba da tsere har ya fara hango birni na biyu, Koda ganin haka sai dukkansu suka Kara kaimi.
Ya zamana cewa su halittun suna so su kama shi ne kafin ya shiga wannan birni na biyu, shi Kuma Aljani RA'UFUL KALLUS Yana so ya shiga wannan birnin kafin su cimmasa.
Haka wadannan halittun suka zage dantse wajen Kai Masa wafta da cizo da tunkuyi, shikuma Yana zillewa a haka har ya fada birni na biyu.
Da shigarsa cikin birnin, sai ya hango halittun sun tsaya cak sun dena binshi sun Kasa shiga birnin, sannan sai suka rinka zubar da hawayen bakin ciki bisa rashin nasarar kama shi.
Shikuwa Aljani RA'UFUL KALLUS sai yayi ta murnar kubuta daga hannun wadannan halittu, domin jikinsa gaba Daya wari yake sannan Kuma yayi tsami sosai saboda azabar da ya Sha, na yi Masa bulala Dari kullum har tsawon kwanaki goma Sha biyu.
Haka dai ALJANI RA'UFUL KALLUS yaci gaba da tafiya a cikin wannan birni batare da ya ga kowa ba.
Birni ne Katon gaske, Wanda akayi Masa manyan gine-gine da zallar danyar Azurfa, Kuma an kawata Katangar birnin da karfen yakutu Mai kyalkyali.
Sai da Aljani RA'UFUL KALLUS ya shafe sa'a biyar Yana yawo a cikin birnin Amma ko kaza Bai gani ba ballantana wasu halittu.
Amma duk Inda ya gifta sai dai yaga kayan alatu iri-iri, da kayan abinci da abin Sha.
Sannan Kuma gaba dayan birnin a haskake yake da matukar haske ta yadda ko allura ta fadi sai an ganta.
Hakika wannan birni ya cika Aljannar duniya, domin gaba Daya birnin an shafe kasansa da wasu duwatsu masu daraja da daukar idanu.
Abinda ya tayarwa ALJANI RA'UFUL KALLUS hankali shi ne, tunda ya shigo wannan birni Bai ga Kasa ba balle ya diba, Nan fa rinka