Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 8
ta daure zuciyarta ta danne duk wani tausayinsa, saboda a ganinta wannan shi ne soyayyar da zata nuna masa a yanzu, matuƙar dai tana son farincikin sa. Da dare bayan sun kammala cin abinci dukkansu suka bar dinning ɗin, bayan sun natsu a falo Safwan ya bijirowa Abie da maganar aurensa, ya ce ya samu mata, Binta ƴar anti Khadija. Da fari Abie ya so ya gane cewa ba da son ransa ba ne, sai dai ya yi duk yadda zai yi ya nuna masa ra'ayinsa ne. Sosai Abie ya yi farinciki da wannan batu, inda ya ce ba ɓata lokaci, a washegari zai samu Alhaji Jafar mahaifin Binta su tsai da magana. Ba tare da wani ɓata lokaci ba kuwa a ka tsayar da biki sati uku. Anti Khadija kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, gani take burinta na tarwatsa farincikin Ammi ya kusa cika. **************** Bayan komawarmu gidan Inna, zama muke hankali kwance, ban fasa yi wa Inna hidimar da na saba mata ba, duk da a yanzu aiyukana sun ƙaru saboda ɗawainiyar Siddik. Haka zan goya shi a bayana in yi ta aikina, sai idan Indo tana nan ne take tayani aikin da rainon Siddik wani lokacin, ita kuma yanzu ba ta cika zama sosai a wurin Inna ba, mafi yawan zamanta a gidan Huse ne. Assiddik yaro ne mara fitina, idan an ji kukansa dai to ƴunwa ne, idan ya ƙoshi kuma bai da wata damuwar, gashi bashi da ƙyuya ko kaɗan, shi yasa mutane suke ƙaunar yaron sosai, uwa uba kuma ga tsafta. Ba yabon kai na ba, duk yawan aikin da nake yi ba na taɓa barin shi da datti ko kaɗan, ko yaushe ka ɗauke shi yana ƙamshi mai daɗi, saboda Hassana ya na ƙoƙarin sayo masa turare irin na yara duk lokacin da ya shiga birni. Sa'i da lokaci Hajjo ta kan turo a ɗaukar mata shi ya wunar mata, da yake ya na shan kunu sosai, ga kazar kazar da ƙiriniya. Shekarsa ɗaya ya fara takawa, ranar saboda murna sai da na yi sadaka, washegari kuma na tashi da azumi. Zaku yi mamaki idan na faɗa muku cewa, a tsawon wannan lokacin ko da kuskure Inna ba ta taɓa ɗaukan Siddik ba, bana tunanin ko inda yake ta taɓa kallo, wataƙila idan a ka ce ta faɗi kamanninsa ma ba za ta iya ba. Hakan bai dame ni ba, saboda na saka a raina watarana zata so shi, za ta ɗauke shi, kuma ko ma mene ne dai ba za ta taɓa goge shi daga cikin jerin jikokinta ba, kuma dai dole ne a kira shi jinin Hassan, don ba a canzawa tuwo suna. Yanzu ni abin da ke damuna ɗaya ne, yanayin da nake shiga lokaci zuwa lokaci, yanayin da nake ganin wasu da suke rayuwa mai kamanceceniya da irin tawa, banbancin kawai su basu cikin matsi da ƙuncin rayuwa irin tawa. Musanman idan Siddik ya yi wani abin, sai na fara ganin ƙaramin yaro kamar shi yana irin haka, a take kuma wani irin ciwon kai yake bijiro mini wanda wani lokacin har sai ta kai ga na fita hayyaci na. Mun nemi magani iri iri ba sauƙi, kaka Baushe ya tabbatar da babu wani iska ko sammu a lamarina, amma har zuwa yanzu an kasa samun maganin abun. Shekarar Siddik ɗaya da watanni huɗu na yaye shi, sabida ba abin da baya ci, nonon ma bai dame shi ba, ganin haka ya sa kawai na yaye shi. Wata ɗaya da yayensa kuwa sai ga wani cikin, mai masifar laulayi har ya fi na Siddik, ba na ci ba na sha, kullum kwance nake kamar ruwa. Ganin haka ya sa Hajjo ta zo ta ɗauki Siddik ya koma wurin ta. Haka nake ta faman wannan jarababben laulayin, Haule ce kaɗai mai zuwa kullum ta duba ni har ta ɗan min gyare-gyare da shara, gashi kuma aurenta nan da wata ɗaya ne ita ma. Bayan auren Haule dole ta sa na koma gida wurin Hajjo, ba ni na dawo ba sai da ciki na ya shiga watanni bakwai, ba a son raina na dawo ba, sai dai kawai ba yadda na iya ne. Sai dai wannan karon ba abin da Inna take min, aikin da nake iyawa ina yi, Indo ta na nan ta na taya ni. Cikina na cika wata tara na haifi yarinyata santaleliya jazir da ita. Lafiya ƙalau na haihu wannan karon. Sai dai kuma abin mamakin shi ne ƴar bata yi kama da ni ko mahaifinta ba, kai kaf cikin zuri'a ba wanda ta ɗauko, daga asibiti Hajjo ta wuce da ni gidanmu. Tsananin kyawun da ake zuzutawa na yarinyar ya sa Inna ta tako har gidanmu ta zo ta ga yarinyar. Bata furta komai ba sai jinjina kai da ta yi ta, ta yi tafiyarta. Ba wanda ya damu da abin da ta aikata, kawai dai kowa ya yi mamakin da a ka ce Inna ta zo ganin yarinya. Sati na zagayowa a ka yi raɗin suna, inda yarinyar ta ci sunan Mubeena. Na yi matuƙar mamakin jin sunan yarinyar, bayan Hassan ya faɗa mini Inna zai yiwa mai suna. Sai daga baya Hajjo ta ke faɗa min ai Hassan ɗin ya same ta da maganar sunan da za a sanyawa yarinyar don Inna ta dire ta ce ba zai saka wa yarinyar sunanta ba, shi ne ta ce a sanya mata Mubeena, saboda ina son sunan, kuma na sha faɗa mata a cikin hira idan Allah ya bani ƴa mace zan sanya mata sunan Mubeena. Ɓata fuska na yi na ce "Amma Hajjo ai ban ce ƴa ta ta fari ba, maimakon ki ce a sanya mata sunanki, shi ke nan na samu Hajjo ƙarama sai kuma ki ce a sanya mata Mubeena." Dariya ta yi ta ce "Ai yanzu kam bakin alƙalami ya bushe, idan da tsawon rai ai haihuwa yanzu kika fara, na tabbatar zaki min mai suna nan ba da daɗewa ba." Sunne kai na na yi saboda wani irin kunyar Hajjo da na ji. Wani lokacin idan ina magana mantawa nake da Hajjo mahaifiyata nake hira sai na saki baki na yi ta sakin duk maganar da ta zo bakina. An yi taron suna lafiya a ka watse, Hassan ya yi bajinta matuƙa, saboda shi dai ƙaunar ɗiyarsa yake har cikin zuciyarsa, duk da an fara soki burutsun zance game da kamannin yarinyar. A wannan karon muna gama wankan arba'in Hajjo ta tattaro ni a ka mayar da ni ɗakina, sai dai ta riƙe Siddik ta ce ya zama na ta, ko zai koma kuma ba yanzu ba, sai na gane kai na sosai.......... ✍ Hmmmm, wasan yanzu fa a ka fara. Wani irin zama Safwan zai yi da amaryarsa sa? Wai shin menene pudurin anti Khadija a kan Ammi?, Wai ma me Ammin ta mata take son ɗaukar fansa? Wace ce Hasina, kuma mene a tare da ita na musanman da ya sa Safwan ke mata makahon so? Ina makomar ɗiyar Shatu, shin da wa ta yi kama? Me shirun Inna yake nufi? Menene tarihin Shatu, wani irin cuta take fama da shi? Wani abu ne tsakanin Inna da kuma Hajjo? Menene sanadin ƙiyayyar da Inna take yi wa Shatu? Waɗannan da ma wasu tarin tambayoyi sai kun biyo alƙalmin the Charismatic a cikin labarin SHAFUKAN ƘADDARATA, nan za ku samu amsoshinku. SARƘAƘIYA. SOYAYYA. ƘIYAYYA. NISHAƊANTARWA. FAƊAKARWA. ILMANTARWA. D. S ........ ✍ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 8 of 8