Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
yi ya ce, "Wallahi Inna kar ki so ganin yadda Hassan ya dawo, ya rame ya lalace, ko aski baya yi, duk yayi wani iri, kuma ma ni Inna har yanzu ban ma yarda wai Shatu na maita ba, don da ta na yi da ta cinye kurwar waɗanda suka wulaƙantata." "Hmmm kai dai kawai ka bar mutum a inda ka ganshi" cewar Inna Zulai. Da ƙyar da suɗin goshi Yaya Salisu ya shawo kan Inna Zulai ta amince zata je tayi wa Inna magana. A lokacin da ta je ne ta samu Inna tana ta sababi tana bala'in baza su yarda da wani ciki ba, su je can su nemi uban cikin, ko kuma su riƙe kayansu don ita dai ba za ta haɗa zuri'a da mayu ba. Sai da Inna Zulai ta mata jan ido kafin aka samu tayi shiru ta shiga ɗaki. Sai dai duk faɗa da nasihar da Inna Zulai ta mata ba wanda ta ɗauka, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, waɗanda suka kawo labarin ma ba ƙaramar tijara ta zuba musu ba. Shi kuwa Hassan yana can ɗakinsu daɗi da farinciki sun ziyarci rayuwarsa bayan lokaci mai tsayi, rabonsa da dariya tun ranarda Hajjo ta masa koran kare ta hana masa ganin Shatu, sai yau da wannan daddaɗan labari ya zo masa. Duk masifar da Inna take yi yana ciki yana ji, fitowa yaƙi yi. Suna cikin haka, Inna bata daina ɗaga muryar tana bala'i daga can ɗakin ba suka jiyo sallama a tsakar gida, amsawa suka yi, tun kafin su fito suka tsinkayi muryar tsohon yana faɗin, "Waye ne ya lakabawa jikata maita, wallahi maza ku fito da shi, zan nuna masa uban kuturu ma yayi kaɗan bare na makaho, wihuhuuuuuu dawa dai mazaje........ ✍ _*Wannan littafin na kuɗi ne, da naira N300 kacal zaki more karatunki. Idan kina da buƙata zaki tura N300 ta wannan account ɗin 9061638128, Sumaiya Mohammad Tukur, Opay. Sannan shaidar biya ta wannan lambar. 09061638128. Daga nan sai a antaya ki a paid group.* ⚡ SHAFUKAN ƘADDARATA ⚡ _*(Pages of my destiny)*_ STORY AND WRITTEN BY: Sumaiya M Tukur (the Charismatic). Page 08. Hantar cikin Inna ne suka kaɗa, don tass ta shaida muryar mai maganar, bata manta karonsu na ƙarshe ba, shekaru kusan takwas baya. ************* Zaune suke a dinning suna lunch, Ammi, Safwan da Ayrah, hira suke yi cikin nishaɗi, a yayin da Ammi ta tasa Ayrah gaba sai ta ci tuwo da miyan kuka, ita kuwa ta ce baza ta ci wannan green soup ɗin ba, dariya duka suke mata, don kuwa duk ranar da aka yi kuka haka take ƙin ci. Sallama suka jiyo daga bakin ƙofar shigowa falon. Ammi ce ta amsa tare da mikewa don dubo mai sallamar. Tana isa falon kuwa ta washe baki tare da faɗin. "Ah ah, Hajiya Saratu ke ce tafe, lale maraba sannu da zuwa." Wacce aka ƙira da Hajiya Saratu ta amsa tana faɗin, "Wallahi kuwa Hajiya Munnira, na ce dai yau kam bari na kawo miki ziyara." "Faɗaɗa murmushinta Ammi ta yi, ta ce, "Ai kuwa kin kyauta." Ta dubi budurwa da ke biye da ita ta ce, "Au ashe da mutuniyar kike tafe, sannu Suhaima." Murmushi ta yi ta ɗan duʼa ta ce, "An wuni lafiya Ammi?" "Lafiya ƙalau Suhaima, ku zo mu karasa dinning, muna ta zance a nan tsaye." Ranƙayawa suka yi gabaɗayansu suka nufi dinning room ɗin, suna tafe suna gaisawa da Hajiya Saratu har suka ƙaraso, kujera suka ja suka zauna, a yayin da Ammi ta yi serving nasu. Safwan tun da ya ga shigowarsu dinning room din yayi kici-kicin da fuska kamar ba shi yake dariya ɗazu ba, sama sama ya gaishe da Hajiyar wacce ta kasance ƙawa ko ma aminiyar Ammin tasa, sai dai bai san dalili ba, sam zuciyarsa taƙi aminta da ita sam, tun a shekarun baya, kuma har yanzu. Amsa masa ta yi da fara'a, har tana yiwa Ayrah wasa, ita ma ko kulata bata yi ba tun bayan gaisuwar da ta musu, don ita ma ba laifi, miskila ce ta bugawa a jarida. Suhaima wacce tayi ƙoƙarin ganin ta jawo hankalin yarinyar ma haka ta gwasaleta, daga karshe ma duban Papinta ta yi ta ce, "let's go Papi, I'm okay." "Ok dear." Ya ɗauki 'yarsa suka bar wurin. Ba haka Hajiya Saratu da Suhaima suka so ba , domin zuwan dama musanman saboda Safwan suka yi shi. Duk da dai cewa Suhaima a da bata ra'ayin wannan abu da mommynta ta ke so, amma gani ɗaya tayiwa Safwan ya tafi da imaninta, shi ya sa yanzu duk wani hanya da take ganin zata shawo hankalinsa shi take bi, watarana har office ɗinsa take zuwa, haka zai disga ta, amma ko a mayafinta, don ita a wurinta komai ya yi burgeta yake yi. Bayan tafiyarsa ba jimawa suma suka tashi suka fita a dinning room ɗin inda mai aiki ta shiga gyarawa. A falo suka yada zango, inda aka buɗe babin hira, ita dai Suhaima tana daga gefe tana fama da wayarta, gabaɗaya hankalinta yana kan hirar da take da ƙawayenta a group. Yayin da su Ammi ke hirarsu ta yaushe gamo. Can Hajiya Saratu ta dubi Ammi ta ce. "Wai ni kuwa Hajiya Munnira, ya batun da mukai kwanaki dake a waya?". Ɗan jimm Ammi ta yi kafin ta ce, "Wani magana kuwa Hajiya Saratu?" Duk da Hajiya Saratu ta ji wani iri, bata nuna ba sai murmushi da tayi ta ce, "Kai Hajiya da mantuwa kike, batun haɗa Safwan da Suhaima aure, shi ne har kika manta, ni ina can tausayin bawan Allah ya cika mini rai." Fuskan Ammi ce ta canza daga farinciki zuwa damuwa, ta dubi Hajiyar ta ce, "Ke dai bari Hajiya, ba wai mantawa na yi ba, Safwan ɗin ne sai a hankali, duk ranar da aka masa maganar aure sai ya birkice, ni na ma rasa yanda zan yi wallahi." "Haba Hajiya, ai maganin hakan ba magana zaki masa ba, auren kawai zaki masa sai dai kice masa ga matar. Ina mai tabbatar miki duk wani abin da zai yi da halin da zai shiga na lokaci kaɗan ne, musanman idan kika aura masa macen da ta san kanta, ta kuma iya kula da miji, shi yasa ma na yi masa sha'awar auren Suhaima. Don kin ganta nan ni kaina idan abu ya carke min tsakanina da Babansu ita nake nema." "lallai kuwa, an gaishe ki Hajiya, yanzu yaran kike sakawa a sha'aninku. Ni ba ma wannan ba, Abie ɗinsa nake ji, ko da na amince ba lallai ne shi ya amince ba." Muskutawa Hajiya Saratu ta yi ta ce, "Hajiya ke nan, sai ka ce ba mace ba, ai kin san yanda zaki bi da shi har ya amince, rayuwar Safwan ɗin shi ne abin dubawa ai." Wani gwauron numfashi Ammi ta yi kafin ta ce, "Hmmm ke dai bari Hajjajo, shi kan shi Safwan ɗin case ne, da bakinsa ya ce bazai iya zama da wata mace kuma ya mata adalci ba, duk matar da ya aura zaman haƙuri zata yi." "Kuma ki ka biye masa, ai wuyanta ya ga mace a gefensa ne, tun yana sharewa har zaki ga ya sauƙo yana kula ta, a hankali kuma sai ki ga komai ya wuce ya zama labari." Cike da sarewa da gajiyawa da zancen Ammi ta ce, "Shi kenan zan jarraba, Allah ya zaɓa mana abin da yafi zama alheri." "Ameen" Hajiya Saratu ta faɗi, daga nan suka shiga wani hiran na daban kuma. Sun ɗan daɗe kaɗan kafin suka yiwa Ammi sallama suka tafi, leda fal ta cikawa Suhaima da kayan kwalliya da turaruka, don Ammi kam ba dai son ƙamshi ba. Bayan tafiyarsu kuma sai maganar da suka yi ta tsaye mata a rai, tunani ta fara ko dai auren zata masa ba tare fa amincewarsa ba, don kuwa halin da Safwan yake ciki sosai yake damunta. Haka ta ƙarashe wunin ranar sukuku da ita. Safwan bai shigo gidan ba sai dare, ko da ya shigo ma Ayrah ya kawo mata da tayi bacci, don a ƙoshe suke, fitarsu dazu gidan Baba malam suka yi, can suka ƙarashe nasu wunin, suka sha furan Hajiya, suka ci dambu abin su suka cika cikinsu kafin su dawo, shiyasa ko abinci basu nema ba. Ko da dare ya yi, bayan Abie ya dawo ya ci abinci ya gama duk wani abin da ya kamata, Ammi ta tare shi da maganar da ke cin ranta tun da rana. Kallonta Abie ya yi sosai bayan ya gama jin abin da take faɗa, kafin ya sauƙe numfashi ya ce, "Yanzu Amminsu kina ganin wannan shawara ce, kar ki manta fa Safwan ba yaro ba ne yanzu, ya mallaki hankalin kansa. Ta ya ya ki ke ganin zaki masa aure ba tare da amincewarsa ba, auren dole fa kenan, mata ma yanzu an daina musu auren dole bare kuma namiji." Kallon Abie ɗin ta yi da wani irin yanayi ɗauke a fuskarta kafin ta sauƙe wani nannauyan numfashi ta ce, "Haka ne Alhaji, halin da nake ganin Safwan a ciki ne yake damuna, shiyasa nake tunanin masa auren zai iya canza shi, ka san idan aka ce da mace a kusa da shi, maybe abubuwan su ɗan ragu." "Munnira!" Abie ya ƙira sunanta. Maido da hankalinta ta yi kacokam a kansa, don tunda ya ƙira ta da sunanta ta san yana buƙatan hankalinta ne. "Ki dawo da hankali da natsuwarki jikinki, wannan shawara ba mai yiwuwa ba ce, idan kuwa kika aura masa mata a wannan halin da ake ciki, zamu zalunci yarinya ne, don na tabbatar baza ta ji daɗin mijin ba, wataƙila sai dai ta yi zaman haƙuri, kinga an cutar da ita, abin da nake so ki lura da shi shi ne, a wannan zamanin namiji da kansa zai zaɓo mata ya aura, idan zama tayi zama sai kiga an dawo sai zaman haƙuri, to ina kuma ga wanda auren ne ma gabaki ɗaya baya so, ba wai iya matar ba?" Jijjiga kai Ammi ta yi alamun ta gamsu da maganar tashi, sai dai kuma damuwar kan fuskarta bai gushe ba, duban ta ta mayar kan Abie ta ce, "To Abie, Allah ya kyauta, lamarin Safwan ne sai a hankali." "Addu'a kawai zamu yi ta masa, insha Allah watarana komai zai wuce." Abie ya faɗa tare da jawo matar tasa zuwa jikinsa. Ƙara lafewa Ammi ta yi a jikin Abie tana faɗin Allah ya nuna mana lokacin Abie, sai na fi kowa farinciki." ************ Wallahi Murja taurin kan Yaya Munnira yana da yawa, duk hanyar da na san zan bi don in jawo hankalinta abun ya ci tura, son da take yiwa wannan Safwan ɗin ya yi yawa, a ce wai sai abin da yake so ne za a yi, inda kika san fa shi ya haifesu daga ita har Alhajin." Aunty Khadija ke nan tare da kawarta Murja suke tattaunawa. Murja ta dubi aunty Khadija da kyau ta ce, baki dai bi ta kowanne hanya ba, ai idan dama ta ƙi sai ki koma hagu, ko kin manta ance ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, ai tunda biyan buƙata kike nema ko ta wani hanya sai ki bi." "Wacce hanya ke nan kike nufi Murja?" "Bokaye da malaman tsubbu" Murja ta bata amsa kai tsaye. "Murja ke nan, wani irin bokaye da malamai ne ban je a kan al'amarin Yaya Munnira ba, ke shaida ce tunda wani lokacin ma ke ce ke raka ni. Banda asaran kuɗi da lokaci mai nake yi, kin santa kamar waliyiya, duk wani addu'a ta san shi kuma tana yi, daga ita har waɗannan ƴaƴan nata." Murja ta ce, "Daɗi na dake saurin karaya, kin manta ance a rashin sani akan bar arha, ai da rashin gwaji sai ki bar sa'arki ta wuce." "Hmmm, to yanzu ya kike ganin za ayi Murja, akwai wani wanda kika sani ne?" "Ai kin san ba a rasa nono a ruga, akwai wani mashahurin boka da na ji labarinsa, ainkinsa kamar yankan wuƙa. Yanzu kawai duk ranar da kika shirya sai mu je." "To shikenan zan miki magana idan na shirya, amma ni a nawa ganin da an bar maganar malaman nan, zan ci gaba da ƙoƙartawa, sannu sannu sai ki ga watarana an kai ga cimna abin da ake nema." "Haka dai kike gani Khadija, yanzu fa duk wanda ki ka gani ya cinma burukansa sai da ya nemi taimako, ba wanda ya samu a ɓagas." "Ai shi kenan nan Murja, zan sa rana sai mu je." Nan suka ci gaba da maganarsu daga baya suka shiga wata hirar daban. Kafin Murja ta mata sallama ta tafi. Tafiyan Murja ba daɗewa Binta ta shigo gidan, ba ko sallama, shigar jikinta ma abun Allah wadai, kamar ba ɗiyar musulma ba, ga kan nan ya sha ƙarin gashi, abin ma ko fasali babu kyan gani. Tana shigowa wurin Mamin tasu ta nufa tana faɗin, "Wash Mami, wallahi na gaji ainun." "Sannu ɗiyar albarka, kin dai kusan hutawa, ina mai tabbatar miki dagabzarar kin auri Safwan kuma ai shi kenan." Miƙewa zaune Binta ta yi fuskarta fal fara'a ta ce, "Na ji kin ce na kusa Mami, Ammin ta yi wa Yaya Safwan magana ya amince ne?" Ta faɗa tana dariya. Aunty Khadija ta dube ta ta ce, "Ke dalla shashasha rufe min baki, da kika ji na ce kin kusa ai mafita na samu." Dariyar da Binta take ne ya ɗauke kamar an ɗauke ruwan sama ta ce ce, "Mamie wani irin mafita kika samu haka?" Nan da nan kuwa aunty Khadija ta kwashe komai yanda suka yi da Murja kawarta ta faɗa wa Binta. Taɓe baki kawai ta yi ta ce, "Yanzu Mamie wannan ce mafitar? Allah dai ya kyauta." Da Ameen Mamin ta amsa mata. Binta ta ce, "Wallahi ko Mami, ina bala'in son Yah Safwan, na tabbata idan na rasa shi bazan yi aure ba, zan shiga wani yanayi. Ya Allah ka mallaka min Yah Safwan ɗina." Wani kallo aunty Khadija ta mata kafin ta ce, "Idan har ina numfashi a doron ƙasa zaki auri Safwan, amma ina mai gargaɗinki da kar ki zurfafa a soyayyarsa, don komai zai iya faruwa, saboda nima ina da nawa ƙudurin a kan wannan auren. Idan kunne ya ji, to gangan jiki ya tsira." A lokuta da dama irin waɗannan kalaman Mamin take yawan mata a duk lokacin da ta bayyana mata sirrin zuciyarta, wanda ita kam dai ta rasa ina ne suka dosa, idan ta tambaye ta kuma sai ta ce mata, idan lokaci ya yi zata sani. Duk wannan bidirin da ake yi, Jiddah na ɗaki ta na jiyo su, addu'ar shiriya kawai take ma Mamin tata da 'yar'uwarta. Ita kam ta rasa me suke nema a duniyar nan. Allah dai ya kyauta. *********** Sake ɗaga murya kaka Baushe ya yi ya ce, "Ba mutane a gidan ne wai?" Inna Zulai ta fito ta ce, "Ah kaka Baushe kai ne tafe, sannu da zuwa, ai muna daga ciki ne, sannu bari na kawo maka tabarma." "Bar tabarmarki Zulaika, ina ita Zainaban, wurinta na zo, wato dai har yanzu tana nan da halinta ko?, ke Zainaba zaki fito ne ko kuwa?" Ya ƙarashe yana ɗaga murya. Simi simi Inna Zainaba ta fito, har ƙasa ta durƙusa ta gaida kaka Baushe kamar yanda suke ƙiransa. A zuciyarta take tunanin ya aka yi yazo, bayan an tabbatar yana daji. Abin da bata sani ba shi ne, tun bayan da Baffajo ya ce zai sanar da Hassan da iyayensa maganar cikin Shatu, Hajjo ta tashi Musa almajirinta ta tura shi can gidan iyayenta da yake maƙwabtaka da ƙauyen da take aure. Ko da ya isa kuwa aka tabbatar masa ya shiga daji, kuma zai kwana biyu bai dawo ba. Haka Musa ya bishi har cikin dajin duk da yiwuwar zai iya haɗuwa da haɗari a dajin, haka ya runtse ido ya dumfari dajin ya sanar da shi komai, don halin da yake ganin Shatu yana damunsa, bata taɓa ɗaukansa kamar almajiri ba, kullum ganin ƙani take masa, wannan dalilin ne ya sanya shi sayar da rai ya bi kaka Baushe har cikin dajin. To fa shi ne daga nan suka yiwa ƙauyen su Inna tsinke, ko wurin Hajjo kaka Baushe bai isa ba ya yiwo nan gidan Inna. bayan ya kaiwa mai gari gaisuwa. Duban Inna dake durƙushe kaka Baushe ya yi ya ce, "Yanzu Zainaba yaushe zaki san annabi ya faku, ashe dai kina nan da halinki ko, me baiwar Allah ta miki kika kafa mata ƙahon zuƙa, na ji ance kin hanata kwanciyar hankali a gidanta, ƙarshe kuma kika bita da sharrin maita?" Ɗago fuskarta ta yi ta ce, "Wallahi kaka Baushe ba sharri na mata ba, ganin ido na fa tana tsallake yarinyar ta tsanyara ihu, to idan ba maita ba menene wannan?" "To ai shi kenan, tun da na zo ai yau komai zai zo ƙarshe da izinin Allah, yau gaskiya zata yi halinta, ina son ki gayyato mini duk iyalan gidannan, gabaɗayanku kuma mu haɗu a can fadar mai gari, ita ma Mariya da Bashari zasu zo tare da Shatu. Yana gama magana ya juya yana tafiya a hankali irin na jaruman tsofaffi......... ✍ _*Wannan littafin na kuɗi ne, da naira N300 kacal zaki more karatunki. Idan kina da buƙata zaki tura N300 ta wannan account ɗin 9061638128, Sumaiya Mohammad Tukur, Opay. Sannan shaidar biya ta wannan lambar. 09061638128. Daga nan sai a antaya ki a paid group.*__ ⚡ SHAFUKAN KADDARATA ⚡ _*(Pages of my destiny).*_ STORY AND WRITTEN BY: Sumaiya M Tukur (the Charismatic). PAGE 09. Kai tsaye kaka Baushe gidan Baffajo ya nufa. Da sallamarsa ya shiga ya samu Hajjo zaune ta zabga tagumi, tun bayan da labarin abin da ya faru a gidan Inna ya zo mata. Tun farko abin da take gudu ke nan shi yasa ta ce kada a faɗa musu. Halin da Shatu ta shiga shi yafi komai ɗaga mata hankali, tun da abin nan ya faru bata taɓa ganin damuwar Shatu irin ta yau ba. Amsa sallamar kaka Baushe ta yi, ta shimfiɗa masa tabarma ya zauna, ta ɗibo masa ruwa a randan sanyi ta kawo masa kafin ta zauna don su gaisa Ruwan ya ɗauka ya sha kafin ya amsa gaisuwar da Hajjo take masa, ya dubi Hajjo da kyau ya ce "Mariya" ta amsa da "Na'am kaka Baushe" Ya muskuta ya ce, "Faɗa min dalla-dalla abin da yake faruwa. Tas Hajjo ta kwashe komai da ya faru tun daga fari ta shaida masa, har da irin zaman da Shatu take yi a gidan na bauta ba abin da ta rage. Nisawa kaka Baushe ya yi kafin ya ce "Amma shi ne baki sanar da ni ba sai da abin ya yi tsamari, ai da yanzu ba a kai ga haka ba, da an yiwa tufkar hanci tun tuni, amma yanzu ma bata ɓaci ba, kira min Shatun." SHATU. Muna tsakar gida labarin abin da ya faru a can gidan surukai na ya zo mana. Ban taɓa shiga tashin hankali ba irin na yau, jin ana ƙoƙarin sheganta min ciki tun bai zo duniya ba, ni kam na rasa me nayi wa Inna har haka, na tabbatar Inna ta na sane ta yi hakan don ta san cikin nan dai na Hassan ne. Da fari nayi farinciki da aka ce za a sanar da su maganar cikina, don a yadda na san Inna take son ganin jikokinta na ɗauka hakan zai sa ta sauƙo daga dokin na ƙin da ta hau komai ya wuce, ashe abin ba haka bane, ƙiyayyar da take mini har ɗan cikina ta shafa. Hawaye ne kawai na ji suna rigegeniya da juna a kan fuskata, Hajjo ta riƙo ni tana rarrashi, buɗe baki nayi na ce "Hajjo wallahi ciki na ba shege bane da ubansa, me ya sa tun bai shaƙi iskar duniya ba suke son su shafa masa baƙin fenti? Me nayi wa Inna wanda ya sa har ɗan cikina bai tsira daga ƙiyayyarta ba?" Share min hawayen Hajjo ta yi ta ce "Baki mata komai ba Shatu, wannan faɗan tsakanina da Zainaba ne, shi ne yanzu ya shafe ki, kiyi haƙuri kinji Shatu, ba wanda ya isa ya sheganta min jika, jika na ɗan sunnah ne ba shege ba, ki kwantar da hankalinki kinji ko." Kaɗa mata kai kawai na yi na tafi ɗakina na kwanta, kuka nake bilhaƙƙi, har banji sanda Inna ta shigo tana ƙira na ba, sai da ta ɗaga murya ta sake ƙiran sunana kafin na jiyo, faɗa min ta yi kaka Baushe ne ya zo yake ƙirana. Da to na amsa na miƙe na biyo bayan Hajjo. Zaune na hango sa kan tabarma, na je har inda yake na durƙusa na gaida shi. Bayan ya amsa na dawo gefensa na zauna. Allah ya sani ina kaunar tsohon nan. Nasiha ya min sosai mai shiga jiki ganin yanda duk na sanya damuwa a raina. Hajjo ya ƙirawo ya ce ta kawo masa garwashi idan da akwai. Ba ɓata lokaci ta ɗebo masa a murhu, har gabansa ta kawo ta ajiye, wani ƙullin magani ya kunto daga jakarsa na fatar ɓauna ya barbaɗa a cikin wutan, sannan ya matso da shi kusa da inda nake zaune. Ni dai zaune nake ban ko motsa ba, har zuwa wani lokaci kafin ya sake saka wani garin maganin, shi ma ya ɗan daɗe kafin ya kira Hajjo ta ɗauke rushin. Bayan ta ajiye ta dawo ta zauna a inda muke, don ta san dole da bayani. Mai da kallonsa kaka Baushe ya yi kanmu ya ce "Wato babu wani alamu na maita ko aljanu a tattare da ita, ku kwantar da hankalinku komai zai zo ƙarshe da yardar Allah. Yanzu dai ku shirya ku je can fadar mai gari, nima ina nan tafe, yau za a yi ta ta ƙare. Kaɗa kai kawai Hajjo ta yi ba ta ce komai ba, ta kamo hannuna ta miƙar da ni ta kaini har ɗakina ta ce na shirya, bari ta shirya ita ma sai ta fito mu tafi. Ban iya ce mata komai ba don duk jikina a mace, tunanin abin da zai faru a can fadar mai gari ita ta tsaya min a rai, ko me yasa ma kaka Baushe zai ce sai munje fadar mai gari oho. Haka na kammala shirina ina kananan tunane tunane. Muryar Hajjo na ji tana tambayata ko na gama, nace mata eh tare da fitowa. Ina fitowa Baffajo ya shigo gidan shi ma ya shirya tsaf, da alamun ya san da maganar zuwa fada, nan muka ranƙaya muka tafi. Muna isa can fadar mai gari muka gano taron mutane kamar wani abu ake na musanman. Wuri muka samu muka zauna muna fuskantar Inna da ahalinta, har da Huse da tagwayenta. Sunkui da kaina na yi na kasa ɗagowa in kalli kowa, duk a tsarge nake. Zuwa can mai gari ya fito aka mika masa gaisuwa, ba jimawa kuwa kaka Baushe ya iso shi ma. Bayan kowa ya natsu mai gari ya buɗe taro da addu'a kafin ya ɗaura da jawabi. "To jama'a kowa dai ya san abin da yake faruwa a karkarar nan game da yar gidan malam Bashari, abin da ya haɗa mu ke nan a yau, domin muna son gano gaskiya game da wannan al'amari, ba zai yiwu mu zuba ido haka kawai ana ɓarna a ƙasarmu ba, saboda haka

Chapter 5 of 8