Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 8
Hassan ya yi kusa da ni, ya yi ta rarrashi na sai da ya ga na rage damuwa kafin ya shiga ya haɗo min kayan sawata, abun hawa ya je ya samo, shi kaɗai ya tallafe ni ya kai ni har cikin motar, ya dawo ya ɗauki kayan da ya haɗa min. Ina jin yanda su Huse suke ta shewa suna faɗin Allah ya raka taki gona, a je can a cinye iya da Baba, wataƙila suma suna taɓawa. Wani malolon baƙinciki ne ya ke ziyartata duk lokacin da aka aibanta iyayena. Bayan Hassan ya dawo da jakan kayana muka ɗauki hanyar gidanmu. Godiya kawai na ke wa Allah da tasbihi a raina, yau kuma irin shafin da littafin ƙaddararta ta buɗo min ke nan. Aure wata ɗaya na koma gidanmu. Alhamdulillahi. A cikin motar haƙuri Hassan ya ke ta faman bani, yana rarrashi na haɗi da kalaman kwantar da hankali. Jin sa kawai nake yi, don na tabbatar a yanzu ban ga abin da zai kwantar mini da hankali ba. Na yi nadama, nayi danasanin zuwa wannan suna, sai dai abu idan aka ce ƙaddara, to ba yanda ka iya, baka isa ka tsallake ta ba. Ko da muka iso gidanmu, Hassan ya cicciɓo ni a hankali, duk da ina jin yanda ƙafar tawa ke raɗaɗi, amma haka na daure ban nuna masa ba. Ya yi sallama kafin ya shiga da ni. Hajjo ta na kwance tsakar gida tana shan hantsi, kawai sai gani tayi ya shigo da ni a tallafe kamar jaririya, salati ta sanya ta na tambayar abin da ya same ni bayan ta shimfiɗa tabarma ya ajiye ni a kai. Bai amsa ta ba sai ma fita da ya yi ya shigo da jakan kayana. Dafe kirji na ga Hajjo ta yi tana faɗin, "Innalillahi wa inna ilaihi taji'uun, me zan ga ni yau ni Mariya, me yake faruwa ne wai?" Ta kalli wannan ta kalli wancan, dukanmu kowa ya kasa magana, tambayar duniyan nan ta mana ba wanda ya tanka mata. Ni dai ina zaune sai ido, don zuwa yanzu kukan ma na daina sai zuciyata kawai da nake jin tana zafi. Shi kuwa Hassan hawaye kawai ya ke yi ya kasa furta komai. Hajjo shiru ta yi ta na kallonmu, kafin ta jawo lulluɓi ta yafa, ta shuri takalmanta ta yi waje, ashe yaro ta je nemowa ya ƙira mata Baffajo. Ba jimawa kuwa ya iso gidan. Tambayar abin da ya faru shima ya yi, ba wanda ya tanka, sai da ya birkice, ganin ransa ya ɓaci ya sa da ƙyar na buɗe baki da muryata da bai fita sosai na ce masa, "Ba komai fa Baffajo, kawai dai ƙafata ce ta ji ciwo, shi ne ya dawo da ni gida, don can ɗin ba kula sosai zan samu ba, shi yasa ya dawo da ni gida. Baffajo ya dubi Hassan yanda yake ta sharɓan kuka ya kaɗa kai ya ce, "To yanzu kai Hassan matar taka ta ji ciwo shi ne kake ta faman wannan kukan kamar wani abu ne ya faru?, to Allah ya kyauta." Cewar Baffajo. Hajjo kam ji na kawai ta yi ba wai don ta yarda ba, sai dai ganin kamar ba mu cikin natsuwa ya sa ta fadin, "To ai shikenan, Allah ya sauwaƙe." Sai Baffajo ne ya samu zarafin tambayar garin yaya hakan ta faru. Na ce, "Tsautsayi Baffa" Shi ma ɗin Allah ya kyauta kawai ya ce, ya shige turakarsa. Hassan ma sallama ya min ya tafi da alƙwarin zai dawo anjima ya duba ni. GIDAN INNA. Al'ummar gidan Inna kuwa yau kamar sallah don farinciki. Tun bayan da Yaya Salisu ya sanar da su Hassan ya saki Shatu saki ɗaya. Dama ya tarar Inna tana ta masifa dole ne sai Hassan ya saki Shatun, don Huse tas suka faɗa mata abin da Hassan ɗin ya ce, har da ƙarin gishiri. Huse bata koma gidanta ba sai bayan azahar, bayan sun gama bidirinsu, da aibanta Shatu da iyayenta, Gambo kuwa sai goshin magariba ta tafi. Kowaccensu cike da farinciki sun raba mata da dakin mjinta, su kuma suka koma nasu. (Wato duniya ta lalace, a rayuwar da muke yi yanzu kowa kansa ya sani, ba wanda ya damu da me dan'uwansa ke so, idan mutum ya samu kowa ma ya rasa ba damuwarsa bane, an manta da hadisin da annabi yake faɗin "imanin ɗayanku baya cika, har sai ya so wa ɗan'uwansa abin da yake so wa kansa". Kowa aibinsa yake ɓoyewa ya ke hango na wani, kowa take lafinsa ya ke ya hango na wani. Wallahi da a ce kowa zai dinga duba kurakuransa yana gyarawa, bazai ga na wani ba, don da ya gyara wannan zai hango wani, kun ga kenan bai gama da nashi ba ma, bare ya samu lokacin hango na wani. Allah ya sa mu dace, ya kuma bamu ikon gyarawa). SHATU. Zamana da Hajjota sai na fara samun natsuwa da kwanciyar hankali, tana kula da ni sosai, kuma ƙafar ma tana sauƙi, sai dai har yanzu ba na takawa. Kullum Hassan sai ya zo sau biyu ko uku, kuma ko wani zuwa da zaiyi sai ya taho min da abu, kaji kuwa tsallaken kwana ɗaya kawai yake yi. Yaya Salisu ma bayan kwana biyu yake zuwa ya duba gyaran da ya yiwa ƙafar. Yau kwanaki na goma a gida, kuma a yau ne Yaya Salisu ya warware gyaran da ya wa kafar tawa, ta yi kyau kuwa, sai kumburin da bai gama saɓewa ba har yanzu. Sanda ya bani ya ce in dinga dogarawa da shi ina tafiya. Bayan tafiyarsa ne Hajjo take tambayata wai me ya sa ba wanda ya zo duba ni a yan'uwan Hassan sai Yaya Salisu kaɗai? Na dube ta na ce. "Hajjo ai kin san ba wani shiri sosai muke yi da su ba. Huse kan ma jego take, Adda Habiba kuwa wataƙila bata ji ba tunda ta yi nisa." Hajjo ta ce, "Amma dai ai ciwo ya shafe komai, duk wannan ba uzuri ba ne, ita kanta Innar taku bata zo ba, bata kuma turo ba." A nan kam bani da amsa sai shiru, ƙare mini kallo Hajjo ta yi ta ce, "Tun dawowarki na fahimci akwai abin da ke faruwa, na sha kamaki kina zaune kina tunani, wai me ya ke faruwa ne, zamanku da Hassan ɗin ne akwai matsala?" Na girgiza kai na kafin na ce "Ba matsala tsakanina da shi, matsalar dai da 'yan'uwansa ne." Nan na kwashe komai na faɗa mata ina hawaye. Abin da ban taba jin Hajjo ya yi ba yau shi tayi. Wata ƙatuwar ashar ta lailayo ta ce, "Kan bala'i, wallahi idan an isa shegiya nake, 'yar tawa za a laƙaba wa maita, dama abin da ya faru kenan ki ka ja bakinki ki kayi shiru? lallai kuwa Zainaba ta tsokalo tsuliyan dodo, ashe har ta mance wace ce ni, tabbas ta manta baya, idan banda ma Baffajo da ya tsaya tsayin daka a kai na, ai da duk ƙauyen nan ba wanda ya isa ya ɗaga min yatsa ya sauƙe ban karya ba. Zainaba da zuri'arta sun tafka babban kuskure wallahi." Tana gama magana ta zari mayafi ta yafa, ta shuri takalmanta ta yi waje, duk ƙiran da nake mata bata ko juyo ba bare ta ji me nake faɗa. Sandata na dogara na yi hanyar waje ina ƙwalawa Hajjo ƙira, sai dai da fitana ko ƙuranta ban gani ba, wani yaro na ƙira na ce masa ya duba min Baffa a makaranta. Ciki na dawo na zauna jugum ina mai danasanin sanar da Hajjo wannan labari, da a ce na san abin da zai biyo baya kenan da na ci gaba da ajiye shi a raina. Ina nan zaune Baffajo ya shigo, tambayata ya yi abin da ke faruwa, nan na sanar da shi komai da kuma yanda Hajjo ta harzuƙa ta fita. Dafe kansa na ga ya yi kafin ya ce, "Kassh! Ai fa al'amari ya riga ya lalace, tun da kika ga Hajjo ta fita haka to sai abin da Allah ya yi, bari na yi maza na bi bayanta." Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa. Shiru na yi ina addu'ar Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi. HAJJO. Hajjo tana fita hanyar ta ɗaya ta nufi gidan Inna, ko sallama bata yi ba ta afka, nan ta tarar da ita kishingiɗe bisa tabarma tana shan fura. Inna ta dago ta ce, "A'a, lafiya kuwa Mariya, kya shigowa mutane gida ba ko sallama, sai ka ce gidan kafurai?" Hajjo ta dubeta da kyau kafin ta ce, "Zainaba kenan, ai a inda akwai aminci ake nemowa mazauna wurin aminci, ba zuwa nayi don in nema miki aminci ba, zuwa nayi inji ba'asin abin da kuka yiwa ɗiyata." Inna tasowa tayi daga wurin da take ta zo har gaban Hajjo ta nuna mata yatsa ta ce, "Hmmm, ɗiyarki? ɗiyarki fa kika ce, idan kin manta ne sai na tuna miki." Kar ki faɗa min maganar banza Zainaba, ina son ki bani gamsasshiyar hujjar da ya sanya ki laƙabawa ƴata maita, idan kuma ba........" "Idan kuma me? Na ce idan kuma me ye? An ce mata mayyar kiyi abin da zakiyi Mariya, ba mayyar ba ce, ganin idona ta tsallake yarinya ta farfaɗo, wani hujja ki ke nema da ya fi wannan?" Wani dariya Hajjo ta yi kafin ta ce, "iya wannan ne hujjar ta ki, to wallahi tun wuri ki maza ki janye wannan ƙage da kike mata, idan ba haka ba kuma kinsan mai zai biyo baya, ke kinsan wace ce Hajjo, kin sanni farin, kin san me zan iya aikatawa da wanda bazan iya ba, wallahi tun wuri ki fita a gonata. Kuma ki faɗawa ɗanki ya maza ya kawo min takardar sakin Shatu don ta gama zama da dangin marasa mutunci." ." Hmmm, saki kuma?, Yo ai sai dai idan cikashe mata sauran biyun zaiyi, kuma ki zuba ido ki gani, idan dai ni na haifi Hassan a cikina, yau zai aikowa mayyar ƴarki sauran cikon sakinta. " Ina nan ina jiransa, idan kuma bai sakar mini ya ba to tabbas shi ba dan sunnah bane"......✍ Wannan littafin na kudi ne, da N300 kadai zaki more karatunki. Idan kina bukata zaki tura N300 ta wannan account din 9061638128, Sumaiya Mohammad Tukur, Opay. Sannna shaidar biya ta wannan lambar 09061638128. Daga nan sai a antaya ki a paid group. 🙏🏼🙏🏼🙏🏼 ⚡ SHAFUKAN ƘADDARATA ⚡ _*(pages of my destiny).*_ STORY AND WRITTEN BY: Sumaiya M Tukur (the Charismatic). PAGE 07. Hajjo tana fitowa ta yi kiciɓis da Baffajo a ƙofar gidan yana safa da marwa, don bai samu ɗan aika ba, kuma bai kyautu ya shiga gida haka na matan aure haka kai tsaye ba. Kallon Hajjo da take ta tafasa ya yi ya girgiza kai ya ce, "Mariya an tuno baya ke nan, ashe ban haneki ba, ashe baki min alƙwarin har abada kin daina wannan halin na ki ba? To shige mu je gida, kinga nan hanya ne bai kamata mu tsaya muna magana a nan ba" Bata ce masa komai ba saboda yanda take jin zuciyarta na ƙuna, ta san idan ta furta wani abin yanzu bazai musu kyau ba. Gaba Baffajo ya sakata shi kuma yana baya, don gani yake zata iya canza shawara ta koma. Sai da suka isa har cikin gida kafin hankalinsa ya kwanta. Ina zaune cikin taraddadi da tashin hankali suka shigo, ganin yanayin Hajjo yasa na shiga taitayina, don yanayi ne da zance ban taɓa ganinta a ciki ba. Ina kallo Baffa ya ɗibo ruwa a randan sanyi ya zauna ya yi tofi ya miƙa mata. Ba musu ta karɓa ta shanye, ajiyar zuciya ta dinga sauƙewa a-kai-a-kai. Sai da ya fahimci zuciyarta ta yi sanyi tukun ya fara mata magana cikin kwantar da hankali. "Haba Hajjo, har ga Allah banji daɗin abin da kika aikata ba, kin fita gida ba tare da izinin mijinki ba, kinje har gidan mutane kin tada musu hankali, kina magana kina ɗaga murya har mazan waje suna jinki, ina mutunci a cikin wannan? Ai da wannan abin da kika aikata gara da ace haƙuri ki ka yi kika barwa Allah sai yafi miki alkhairi. Kuka Hajjo ta fashe da shi ta ce, "Haba malam, 'yar tawa guda ɗaya tallin tal ake aibatawa ka ce kuma inyi shiru, ka kuwa san yanda na ji a raina, mayya fa malam, mayya fa suke ce mata, ina bazai yiwu ba, wallahi wannan karon sai dai ka yi haƙuri, don sai na nunawa Zainaba bata isa ba, sai na nuna mata iyakarta, sai ta san tayi kuskuren aibata mini 'ya, daga ita har zuri'arta kuwa. Idan har banyi haka ba ka ce ba Mariya ba ce, ɗiyar Kulu jikar Baushe, ai sai ta san cewa ko kura ta faɗi tafi ƙarfin akuya.". Tana gama magana ta miƙe ta shiga ɗakinta. Kallona na mayar inda Baffajo ke zaune dafe da kansa, ga dukkan alamu kalaman Hajjo ne suke karakaina a cikin ƙwaƙwalwarsa. Damuwa ne ta bayyana a fuskata, ban taɓa tunanin faɗa wa Hajjo wannan maganar zai kawo tashin hankali har haka ba, Allah dai ya kawo ƙarshen wannan lamarin. Da dare Baffajo ne ya ƙira Hajjo turakarsa bayan ya tabbatar da Shatu ta yi bacci. Dubanta ya yi sosai yana tunanin ta inda zai fara saƙa maganar da ya ke son yi mata, don ya tabbatar idan abin ya kai gobe komai zai iya lalacewa, musanman ma idan ta kaiwa kakanta Baushe ziyara. Gyara zama ya yi ya ƙira sunanta, ta amsa ta na mai zuba masa ido. Ya sake gyara zama ya ce. "Mariya uwar marayu, mariya ta malan Bashari, bada kanka a sare ka je gida ka ce ya faɗi, Mariya sarauniya kuma tauraruwar Bashari, an buga da ke an barki, kowa nan ya barki inda ya ganki, Mariya ɗiyar Baaba Kulu amanar Baushe, wa yace da ke ba ke ba, Mariya matar rufin asiri, Mariya ƴar aljannah, Mariya sarautar zuciyar Bashari." Tuni wani murmushi ya kaiwa fuskarta ziyara ba tare da tayi shirin tarbansa ba. Ta kalli malam ta ce, "Gaskiya malam ka gama sani na ciki da bai, ka san lagona, yanzu duk yanda na ke jin ɓacin rai, a sannu sai naji duk sun fece." "To ai Mariya, dama fushi da ɓacin rai basu da muhalli a wurinki, murmushi da kwanciyar hankali kaɗai nake son gani a tattare da ke. Yanzu dai ki natsu don Allah muyi magana ta fahimta." Ina jinka malam."Hajjo ta faɗa tana tattara hankalita wuri gudi. Baffajo ya gyara zama ya dubi Hajjo ya ce"Yawwa, so nake don Allah, don son da kike wa annabi ki janye ƙudurinki a kan Zainaba, na san komai kika ce zaki iya, amma wani lokacin haƙuri da fawwalawa Ubangiji lamari shi ya fi komai, kar ki manta kin fa min alƙawari kin daina komai, me yasa yanzu a kan wannan ƙaramin abin zaki sake jefa kanki a halaka, sannan kuma ai faɗa ba naki bane, yanzu fa kin girma, kin wuce yin duk waɗannan abubuwan, don Allah, ina roƙonki a matsayina na mijinki, na san mace ce ke mai biyayya, baki taɓa saɓawa umarnina ba, kuma na tabbatar baza ki fara yanzu ba. Kiyi haƙuri, muyi haƙuri, komai da kika gani yana da ƙarshensa, idan tata ƙaddarar ne tazo a haka mu taya ta da addu'a, Allah ya bata ikon tsallake ta." Wani gwauron numfashi Hajjo ta sauƙe, mai haɗe da wani irin hawaye masu zafi. Bai hana ta ba sai da tayi mai isarta ta ɗan ji sauƙi a zuciyarta kafin ya shiga rarrashinta, da ƙyar da suɗin goshi ta yarda ta bar maganar, amma a can pasan ranta kokawa take da zuciya da ruhinta. Washegari ina jiran jin ta inda Hajjo zata faro sai naji shiru, sai da yamma da Hassan ya zo ta ce ina takardar sakina, a take zuciyata ta tsinke, saki! Na furta. Ban san me ya faɗa mata ba, sai ji nayi ta ce ya tafi kar ya sake taka ƙafarsa a gidan sai dai idan da takardar saki, ba irin magiya da ban haƙurin da bai mata ba amma tayi biris da shi, tun yana zuwa har dai ya ɗauke ƙafarsa ya daina zuwa. Rayuwa ta min ƙunci, na shiga matsanaicin damuwa wanda har ta kaini ga kwanciya ciwo. Wasa wasa fa magana ta fara zagaya gari ana alaƙanta gidanmu da gidan mayu, ɗaliban da suke karatu a makarantar Baffa suka fara raguwa, don iyaye suna cire ƴaƴansu, wasa gaske duk ƙauyen mu ta ɗauki zancen ni mayya ce, wasu har gida suke zuwa su ci min mutunci, idan kuwa aka samu yaro yana ciwon da ba a gane kansa ba, sai a ɗauko a kawo min a ce ni na kama shi, har ma manyan, sai ya zamana duk wanda ya yi ciwo mai tsanani a ƙauyenmu to nice na kama shi, gashi wani iko na Ubangiji kuma a dai dai wannan lokacin ne annobar wata cuta ta shigo ƙauyen namu, wanda idan ka kamu da ita dai da wuya ka tsallake kwanaki uku, mace mace sai ya yi yawa, mutane kuma sai suka alakanta hakan da ni. Nayi kuka mara adadi, baƙinciki da ƙuncin rayuwar da nake fuskanta a ƙauyenmu tayi yawa, ko ƙofar gida ban isa leƙowa ba. Abin ta kai har Mai Gari ya ƙirawo Baffa ya masa kashedi da barazanar korarsa da iyalinsa daga garinsa,rayuwa ta yi mana ƙunci a wannan gabar. Yawan tunani da damuwar da nake ya sanya na rame nayi duhu, gabaɗaya na lalace kamar ba Shatun Hajjo ba, ga wani zazzabi da ciwon kai da ya sanya ni a gaba, bana ko iya cin abinci sai Hajjo ta matsa, tun tana mini faɗa har dai ta sauƙo ta shiga rarrashina da ban baki, shi kanshi Baffajo ba a barshi a baya ba, kullum faɗa da nasiha ya ke min, ga kewar mijina da ya addabi ruhina, ban tabbatar da irin son da nake wa Hassan ba sai a yanzu da ya nisanta kansa da ni. Lokaci lokaci yana zuwa amma sam Hajjo ta hana mu ko da haduwa ne. Haule ƙawata, ƙawar arziƙi ce da bazan taɓa mancewa da ita ba, ita kaiai ce bata ƙyamaceni ba a wannan lokacin, kullum ko da yaushe tana tare da ni tana tausata, iyayenta sunyi yanda zasu yi su raba mu abin ya ci tura, har duka an mata da girmanta amma bata fasa zuwa wurina ba Sannu a hankali nayi wata uku a gida, a wannan lokacin abun ya yi kamari, abunka da mutanen ƙauye da iya zuzuta abu, don har ta kai ga an daina bin Baffajo sallah, haka ya haƙura da limamci ya dawo mamu, sai ya zamana ba mai yarda ya haɗa sahu da shi. Haka nan ma Hajjo, bata isa ta shiga taron mata ba, a take za a dare a watse a barta, kowa tsoron mutanen gidanmu yake, mu kaɗai muka dawo muna rayuwa, sai almajirin Hajjo Musa da bai guje mu ba, sai kuma Haule. Watarana haka na tashi da matsanaicin zazzaɓi, ga jiri, da ciwon kai, ko idanuna bana iya buɗewa, ga tashin zuciya komai na ci haka zan dawo dashi. Hankalin iyayen nawa ba ƙaramin tashi ya yi ba, ba shiri muka nufi asibiti. Gado aka bani bayan an yi mini wasu ƴan gwaje-gwaje, a nan aka gano cikin da nake da shi dan watanni huɗu. Ba kaɗan ba su Hajjo suka yi murna da farinciki da wannan ƙaruwa. Kwanana uku a asibiti kafin aka sallamoni muka dawo gida, kula na musanman Hajjo da Baffana ke ba ni. Bayan dawowar mu da kwana biyu Baffajo ya tara mu yake faɗa mana dole za a sanar da Hassan maganar cikina, Hajjo ta haye ta dire ta ce sam ba za a faɗa ba, da ƙyar da suɗin goshi Baffa ya shawo kanta, tun da dai cikinnan yana da Uba, to kuwa dole a sanar musu, idan ma baida Uba to dole a sanar da waliyan uban. GIDAN INNA. Inna kam tun bayan tafiyar Shatu ta fara ganin anfaninta a gidan, aikin da ya kamata duk ita take yi, don Indo dai bata dawo ba, Huse ta riƙe ta, ita kuwa Mairo ba abun da ta iya sai son jiki da ƙazanta, sai dai duk da haka inna bata ji ko ɗar ba, ranta sawai ta rabu da alaƙaƙai a cewarta. Gefe kuma ga su Huse na ta ƙara zugata. Zaune Inna take tana hutawa da yamma bayan ta kammala musu abincin dare, magana take wa Mairo tun ɗazu ta tashi ta share tsakar gidan ta ɗauraye musu ƴan kwanukansu, amma ko alamum zata tashi babu. Hassan ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, ta amsa masa, ya zo ya zauna a kan tabarmar kafin ya ce, "Barka da gida Inna" "Yawwa sannu Hassan, ya ya kasuwar, ince dai ko lafiya naga duk kayi wani iri" "Ba komai Inna, bari na shiga na ɗan watsa ruwa." "To shi kenan, idan ka watsa sai ka zo ka ci abinci ko" "A'a Inna, bana ci, a ƙoshe nake." Dubansa Inna tayi da kyau ta ce, "Yanzu Hassan ba za ka cire damuwar wannan mai gani har hanjin a ranka ba ko, ka bi ka tsagalgali kanka, abincin kirki ma baka ci, dubi yadda ka dawo fa, ƙashi da rai, duk ka lalace kayi duhu, anya kuwa Hassan?" Hassan ya dubi Inna ya ce, "Inna kenan, damuwa kam ai yanzu na fara, Inna wallahi ina son Shatu." Wani salati Inna ta sanya ta ce, " Ta tabbata dai wallahi yarinyar nan ta gama da kai, bayan maita ma harda yan tsubbace tsubbace?" Hassan ya girgiza kai ya ce, "Wallahi Inna Shatu ba mayya ba ce, kuma ina mai tabbatar miki da koda ƙur'ani aka bani zan rantse a kan Shatu ba mayya ba ce, an dai samu wani akasi ne kawai." Tsaki Inna ta ja ta ce, "Sai kayi kuma, ni dai ganau ce ba jiyau ba, saboda haka ba abin da zaka faɗa mini in yarda, tashi ka bani wuri, kuma ka tabbatar ka zo ka ci abinci, idan ba haka ba sai na ɓata maka rai. Sakarai." Mikewa Hassan ya yi ya wuce ɗakinsu, yana nan yanda yake, kullum kuma sai ya gyara ya share kamar yanda Shatu take yi, haka zai zauna ya yi ta magana shi kaɗai kamar tana nan, wani lokacin kuma ya ci kukanshi ba mai rarrashinsa. Fita yayi daga ɗakin ya shiga bayi yayi wanka, yana fitowa ya je ya ɗauki abinci kamar yadda Inna ta ce, dawowa yayi ya ajiye, ya jima kafin ya fita lokacin ana ta ƙiraye ƙirayen sallar magariba, bashi ya dawo gidan ba sai dare. A cikin watanni ukun da ƴan kai da suka shuɗe masa ba Shatu, rayuwa ta yi masa ƙunci, walwala tayi ƙaura daga kan fuskarsa, Yaya Salisu tare da amininsa Isa sunyi ƙoƙarin ganin ya kwantar da hankalinsa ko yaya ne, amma abin ya ci tura. Yaya Salisu ya je wurin Inna sau ba adadi a kan tayi haƙuri Shatu ta dawo ɗakinta, ko don halin da ɗan'uwansa yake ciki, amma sam Inna ta murje gashin bakinta ta ƙi, tun suna ɗaukan abun wasa har ta kai ga ya daina fita kasuwa, don ko ya je ma babu abin da yake taɓukawa, haka zai wuni ya dawo. Ganin haka ya sa Yaya Salisu ya je ya samu Inna Zulai da maganar, ita ma da fari ta ƙi yarda, tace masa ai ba anfanin zama da maye, duk aminta da shaƙuwarku watarana zai cutar da kai. Kallon Inna Zulai ɗin ya

Chapter 4 of 8