kika baro a rayuwarki, irin wannan rashin ta idon." Tana gama maganarta ta saɓi buta ta shige bayi.
Ba kaɗan ba maganganun Inna suka doki zuciyata ba, har ban san lokacin da hawaye ya surnano bisa dakalin fuskata ba, na sanya bayan hannu na na share kafin na ci gaba da aikin dake gabana, ina gani Inna ta zo ta wuce tana zagi da yada min magana, ta shige ɗakinta. Na kwashi lokuta masu yawa kafin na gama wanke kwanukan na adana su sannan na share wurin, na gaji ainun ga kuma ƴunwa da ke addabar ciki na. Na je na yi sallama ɗakin Inna na sanar da ita na gama, wani kwano ta nuna min ta ce in ɗauka abun karin mu ne, idan kuma na karya maza nazo na aza sanwan rana tun da mun samu na safe. Haka na ɗauka na tafi ɗaki na da shi, duk yunwar da nake ji sai da nayi wanka na canza kaya, na tattare ɗakin kafin na share harda da madaidaicin tsakar gidan da aka zagaye min.
Bayan na gama na zo na zauna zan karya, sai a lokacin na tuna shi ma Hassan bai karya ba ya fita, to yanzu ya zanyi gashi bai dawo ba, kuma bana son na ci na rage masa. Bude kwanon na yi na ci karo da wani kalan ɗumame baƙiƙƙirin, kuma yanka biyu ne kaɗai, wanda idan na zage ko ni ɗaya zan cinye, kuma ba lallai ma na ƙoshi ba, mayarwa na yi na rufe da nufin zan jira shi ya shigo, nan kuwa na tuna Inna ta ce zan ɗaura sanwan rana, nayi maza na tashi na ja ƙofar na rufe na nufi wurin inna tun kan ta fara min abun da naƙi jini wato fada.
Ina zuwa kuwa ta nuna min komai na girki na fara yi, yunwa nake ji da gajiya, don ba sabawa na yi da aiki haka ba, can gidanmu daga ni sai Hajjo sai Baffajo ne kaɗai, sai kuma almajirin da ke ɗibo mana ruwa, aikin gidan ba wani mai yawa ba ne. Ina nan har azahar kafin na gama, duk lokacin kuma Hassan bai shigo ba, duk na damu, ina gani Inna ta zo ta raba abincin ta miƙo mini na mu, yanzu kam da ɗan dama ta zuba mana, na mata godiya bayan fitarta na tattare madafin na share na kimtsa ko ina, kafin na ɗauki abubuwan da na ɓata na wanke su tass, na ɗauki abincinmu na wuce ɗakinmu da shi jikina kamar wacce aka min duka.
Ko da na shiga ɗakin gado kawai na hau na kwanta, sai da na huta kafin na tashi na yi wanka, ina cikin saka kaya na jiyo sallamar Hassan a bakin ƙofar, da sauri na ida saka rigar kafin ya ƙarasa shigowa. Fuskarsa da alamun damuwa har yanzu, amma haka ya yi ƙoƙarin sakar mini murmushi, nima murmushin na masa ina sunkuyar da kai na na ce masa, "sannu da dawowa."
"Yawwa sannu Shatuwata tauraruwar zuciyar Hassan, ai ke ce da sannu."
Murmushi kawai na yi na fita, ruwa na kawo masa a kofi mai murfi, sannan na sake fita na kamfaci ruwa a bokiti na kai masa bayi, sannan na ɗauki kayan wanka na kai masa kafin na dawo ɗaki na ce masa "na kai maka ruwan wanka"
"To sarauniyar mata, na gode Allah miki albarka."
A zuciyata na amsa da ameen don kuwa na ji daɗin addu'ar, shi kuwa fita ya yi ya je ya yo wankan ya dawo, baya na bashi sai da ya gama shiryawa kafin na ɗauko mana abincin, buɗe masa na yi na saka cokali da ke shinkafa ce dafa duka, sannan na ɗauko na safen na kawo shi ma. Buɗewa ya yi ya ce wannan kuma fa?".
"Na karyawarmu ne, nayi ta jiranka baka dawo ba."
Kallo na ya yi alamun bai ji daɗi ba kafin ya ce, "Haba Shatu, kina nufin baki karya ba har yanzu, don Allah kar ki sake haka, kar ki sake zama da yunwa kinji, ko bana nan ki ci abincinki ba sai kin jira ni ba, ban ji daɗin zaman da kikayi da yunwa ba sam, don Allah kar ki sake."
Kaɗa masa kai kawai na yi alamun na ji, don ni na matsu mu fara cin abincin, rufe na safen yayi muka fara cin shinkafar, kaɗan ya ci ya ce ya ƙoshi, ni kuwa zagewa na yi sai da na fatattaki yunwar da nake ji tukun na sarara, sai lokacin kuma na ji kunya ganin yawan abincin da na ci. Na tattare kwanukan na fitar kafin na dawo ɗaki.
Hira muke yi tsakaninmu, yana ta daɗa bani hakuri, na kuwa nuna masa ai ba komai, idan banyi wa Inna hidima ba wa zanyi wa, ai ita uwa ce, kuma duk ɗa na gari baya gajiya da hidimtawa iyayensa.
Ranar da na yi kwana uku a gidan, a ranar na samu tsarki, Hassan kuwa bai ɗaga min ƙafa ba ko kaɗan, sai da ya ɓarji angoncinsa yanda ya kamata, na sha wahala ainun, wanda ko da safiya ta yi da kyar na tashi, cinyoyina duk ciwo suke min, haka na lallaba na fita don ɗaura mana abun kari, don na san idan ma na zauna Inna zata zo ta fara faɗa, abun da ke ɗaga min hankali ke nan, shi ma angon bai san na fice ba, ina cikin aikin na jiyo muryarsa yana faɗin, "Haba Shatu ke da baki jin daɗi ai da kin kwanta sai na sanar da Inna."
Murmushi na masa ina sadda kai na ƙasa na ce masa ai zan iya, ina ganin sa ya shige ɗakin Inna, ban san me ya faɗa mata ba sai jiyo muryarta nayi tana faɗin, "Lallai ma Hassan, wato nan aiko ka ta yi ka faɗa min bata da lafiya, to ka koma ka sanar da ita ko cutan mutuwa ta ke yi sai ta mana abincin a gidan nan, don ba mai dafawa ya bata tana daga kwance." Ban ji me ya kuma faɗa mata ba sai jiyowa na yi ta ce, "Ba za su yi ba, Mairo tun jiya ta ke ciwon ciki, don baƙon watanta ya zo, Indo kuma tana gama kari zata gidan Huse ta ɗan kama mata wani abun tunda ta shiga watan haihuwarta, ina ga ma can zata koma har ta haihu tukun."
Gani na yi ya fito ya wuce bai ko dubi inda nake ba, na sani sarai ba ya son mu hada ido ne, don ya san na ji duk abun da Inna ta ke faɗa, ban damu ba haka na gama abun da zanyi, na haɗa kwanukan na fara wankewa, Indo ce ta fito daga ɗakinsu ta zo ta zauna muka fara yi tare, naso hana ta.amma ta nuna zata yi, muna yi tana ɗan min hira, cikin hikima ta ke bani haƙurin abun da Inna ta ke min, ban kuwa nuna mata hakan ya dame ni ba, don kuwa cikin kwanaki uku da nayi na fara sabawa da aikin, don dama can ni ba mace ce mai son jiki ba. Haka muka gama muka tattare ko ina, ita ta share tsakar gida ni kuma na share madafin, zuwa yanzu ni ke raba abincin idan na gama.
Lokacin da na koma ɗaki na samu Hassan ya zuba tagumi alamun damuwa kwance a kan fuskarsa, da sauri ya taso ya karɓi kwanon hannuna, ya zaunar da ni bakin gado, taɓa jikina ya yi yaji ya ɗau zafi alamun zazzabi, cike da kulawa ya ke jero min sannu tare da bani hakuri. Na masa murmushi kawai na zame na kwanta, ganin haka ya haɗa min ruwan wanka kamar yanda nake masa kafin ya ce naje na yi wanka, ina shiga ya fita, ashe magani ya siyo min, ko da ya dawo sai da ya tilasta ni kafin na iya cin abincin kaɗan na sha kunu, ya miƙo min magani, da ƙyar na haɗiye na kwanta, ban jima ba kuwa bacci ya kwashe ni a wurin.
Hassan zama ya yi yana kare mata kallo, tausayi take bashi, tun lokacin da bai aure ta ba, wanda wannan tausayin shi ya rikiɗe ya koma tsantsan soyayya ba tare da ya farga ba, yana mata wani irin so da bai san yanda zai misalta shi ba, ya musu tanadin rayuwar jin dadi da farin ciki, sai gashi Inna ta ruguza shi a lokaci daya. Bai so suka zauna a cikin gidan ba, amma Inna ta kafa masa sharaɗin muddin yana son auren sai dai ya gyara ɗaki a cikin gidan su zauna, haka ya haƙura ya amince, daga baya kuma ta ce sam baza'a raba girki ba, dole girki gabaɗaya gida za'a rika yi,ba yanda ya iya, yana ganin abar ƙaunarsa ta na wahala bazai iya komai ba.
Ya ɗauki lokaci mai tsayi zaune a wurin kafin ya mike ta fita, kai tsaye ɗakin Inna ya wuce, wuri ya samu ya zauna kafin ya dubi Inna da fuskar neman agaji ya ce, " Don Allah Inna ki yi haƙuri ko na iya yau ne, wallahi Shatu bata da lafiya, yanzu haka zazzabi ne a jikinta, magani na anso mata nan wurin Musa mai kemis ta sha, shi ne ta ɗan samu bacci."
Kollon sa Inna ta yi kana ta ce, "To yanzu wannan dogon sharhi da ka ajiye ni kana min me ka ke da buƙata, don na san banza dai bata kai zomo kasuwa."
Sadda kai ya yi ya ce, "Dama.. dama wai aikin yau ɗinne na ke son a ɗan ɗaga mata ƙafa har zuwa gobe ta dan ji sauƙi, a yi hakuri Inna."
Sai da ta mula kamar baza ta ce komai ba kafin ta furta, "Ai shi kenan tabbatacce, tashi ka fice min da gani, idan ka fita ka ƙirawo min Mairo tana ɗakinsu."
Godiya ya yi kafin ya fice, yana mai farin ciki, ko ba komai yau Shatunsa zata huta. Ya leƙa dakin kannensa don ƙiran Mairo, ita daya ce a ciki don Indo ta tafi can gidan yayar tasu tun ɗazu, ya sanar da ita Inna ke kiranta kafin ya koma ɗaki, ya tasa matar tasa gaba yana kallo.
*********
Baffajo ne zaune a tabarma riƙe da ƴar rediyonsa yana jin labarun safe na BBC, Hajjo ta iso wurin hannunta ɗauke da kofin kunu, da kwanon da ta zubo musu dumamen karin su a ciki, ta ajiye kafin ta zauna gefen Baffajo ta ce, "Wash Allah am, wallahi na gaji ƙafafun nan duk sun riƙe."
Dariya Baffajo ya yi ya ce, "Ke dai Mariya ba dai raki ba, wato kin saba da hutu ko, yanzu kuma mai kama miki aikin bata nan, Shatu ta sakalta ki da yawa, shi yasa da nake magana idan na ga komai ita ke yi, irin wannan lokaci na ke tuna miki."
"Ai kuwa dai kam mallam, gashi yanzu ina ji a jikina ai. Allah sarki shatu baiwar Allah, ko me take yi yanzu sai Allah, ni ka san abun da nake ji mata kuwa?" Ta karashe maganar da sigar tambaya.
Baffajo da ya gama sauraran labarun ne ya kashe rediyonsa ya ce, "To Maririta, me ki ke jiye mata?".
Dara wa kaɗan Hajjo ta yi ta ce, "Kai kam mallam baka rabo da zolaya. Wato halin Zainaba nake jiye mata, ka san bata da daɗi, musanman ma da ya kasance bata ƙaunar wannan auren, Allah kaɗai ya san irin zaman da Shatu zata yi a gidan tare da ita."
Gyara zamansa Baffajo ya yi ya ce, "Haba Mariya, ki kyautata mata zato, insha Allah ba abun da zai faru da Shatu sai alheri, tana tare da Allah, kuma muma muna biye da ita da addu'o'i ba dare ba rana, Allah zai kare ta, khairan insha Allah."
"To Allah ya sa haka mallam." Daga nan suka fara karyawa suna ɗan taɓa hira sama sama tare da yabon kokari da kyauwun halin Shatu.
**************
Ammi ce zaune tare da Ayrah tana faman lallaɓa ta ta ci abinci, ita kuwa sai shagwaɓa ta ke da kananun kuka irin na taɓara, don sam bata son cin abinci, ita dai barta da kayan ƙwalam da maƙulashe, abun da suka saba kenan da Papinta, don bayan rasuwar Maa ɗinta yayi jinya, da ya samu lafiya kuwa ya ɗauki yarsa suka tafi London, a can suke rayuwa su biyu, sai da ya yi shekaru uku kafin Ammi ta matsa ya dawo, shima sai da ta nuna masa bacin ranta sosai, a cewarsa ba zai sake rayuwa a ƙasar da ya rasa Hasina ba. Tun bayan dawowarasu ta lura da rashin cin Ayrah, ta kuwa yi mita ba kaɗan ba, kuma ta ce bata san wannan zancen ba, haka ta ke saka ta gaba da abinci, duk da bata wani cin mai yawa, amma dai ya fi babu.
Suna haka kuwa Safwan ya shigo, ba kunya ya ɗauke Ayrah daga ƙafan Ammi yana murmushi ya ce, "Ai mun koshi Ammi, a yi haƙuri kuma sai gobe ko." Ya faɗa ya na ɗagawa Ayrah gira daya. Ai kuwa ta saki dariya ta ce, "Yess Papi" haɗi da ɗaga masa hannu alamun su tafa, ya kuwa kawo nasa suka kashe abunsu suna dariya.
Sakato Ammi ta yi da lomar tuwo a hannunta tana kallonsu, bata yi aune ba kawai ta ji saukar hawaye a fuskarta, saurin gogewa ta yi kafin Safwan ya gani. " Ko yaushe ne zan sake ganin ainihin Safwan ɗina mai yawan fara'a da barkwanci, mai walwala da nishaɗi, mai cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali."
Bata san a fili ta yi maganar ba, sai da taji daga gefenta an furta, "Sai ranar da ya kawo wata mace cikin rayuwarsa."
Shi da ita a tare suka ɗaga ido suka sauƙe a kan mai maganar, fuskar Safwan har ta canza, kamar ba shi ya ke dariya da yarsa yanzu ba..........✍✍✍
⚡ SHAFUKAN ƘADDARATA ⚡
_*(pages of my destiny)*_
STORY AND WRITTEN BY:
Sumaiya M Tukur (the Charismatic).
PAGE 04.
Duka na suke ta ko ina suna jifana da muggan sunaye, tsananin firgici da tashin hankali da na tsinci kaina a ciki ya hana ni ko motsawa, wanda hakan ya basu damar dukana yanda suke so. Ina daga durƙushe a ƙasa na jiyo muryar Inna Zulai tana faɗin.
"Kai kuna hauka ne, kashe yar mutane zaku yi, ku rabu da ita shashashu kawai. Ke kuma Zainaba kina zaune kina kallo baza ki tsawatar musu ba, to wallahi idan suka kashe yarinya har da ke za'a kulle, haba wani irin rayuwa ne haka."
Ina nan dai ban ɗago kai na ba na ji ta kamo ni ta miƙar da ni, wani azababben zafi na ji a yayin da na tsaya kan kafata ta hagu, wanda ya sanya ni yin kuka a hankali. Haka na lallaba ina ɗingisa kafata guda daya, Inna Zulai na rike da ni ta kaini har ɗakina tana ta faman min sannu kafin ta fito ta barni.
Ban kuma sanin abun da ya ke faruwa a can cikin gidan ba, ina nan zaune azaba ta isheni, tuni ƙafar ta kumbura kamar doya, a daddafe na samu na yi sallar magariba da Isha, tun ina jiyo hayaniyarsu har dai na ji gidan ya yi shiru, tashi na yi na ƙoƙarta na rufo ƙofata, ko kayan jikina ban sauya ba na haye gado na kwanta. sai dai fa bacci ya gagari idanuna, jikina ko ina ciwo ya ke, ga ƙafata da take mini zugi, ji na ke kamar na ɓalle ta na yar.
Wani irin kuka ne ya ƙwace mini mai cike da damuwa da kaɗaici, yinsa na ke babu ƙaƙƙautawa, ina kuma godewa Allah da sabon shafi da ƙaddararta ta buɗo min, a yau ina ji na kamar wata marainiya wacce ba ta da kowa, a yau na ga gurbin mijina, don na san tabbas da yana nan bazai taba bari na haka ba.
Ganin kukan ba inda zai kai ni yasa ni jawo ƙur'ani na da ke gefen gado na na soma karantawa ko zan samu sauƙi a zuciyata, karatu na ke rerawa mai haɗe da kuka, tun ina hawaye har na fara jin wani irin natsuwa yana shiga zuciyata, wani sanyi da salama suka ziyarci ruhina, duk wani damuwa sai na ji kamar an wanke min shi, lallai alƙur'ani waraka ce ga dukkan damuwar bawa, ƙafata ce kawai da ke min zugi ya hana ni runtsawa. Ina nan zaune na ji an kira sallar asuba, zuwa yanzu ko motsa ƙafar bana iya yi, a inda na ke na yi niyyar taimama na yi na tada sallah, ina sallamewa na ci gaba da azkar ɗina har zuwa gari ya yi fara haske.
Hayaniya na fara jiyowa daga cikin gidan kamar muryar Huse, da na kasa kunne da kyau kuwa ita ɗin ce, abun da naji tana faɗi ne ya sake dulmiya ni cikin tashin hankali. Faɗi ta ke; "ina ta ke, wallahi Inna sai ta sakar min kurwar yarinya, muna zaman zamanmu lafiya Hassan ya je ya ɗebo mana masifa, ina dalili ta rasa inda maitar ta zai sauƙa sai a kan ƴata, wallahi ba zai yiwu ba."
Wannan kalma ta maita da na ke jin ake jifata da ita tun a jiya shi ya fi komai ɗaga min hankali, to ma wai shin me ya faru da jaririyar ne bayan tafiyata, kodai mutuwa ta yi. Da sauri na furta Astagfirullah ina rufe bakina.
Na yi nisa a duniyar tunani na ji wani irin bugun ƙofa da ya dawo da ni duniyata, bugawa a ke yi ba ƙaƙƙautawa, sai dai kuma duk yanda na so tashi na buɗe abin ya ci tura, ina ji Gambo kanwarsu ta na faɗin, "Ai makirar ta san abin da ta aikata ina zata yarda ta buɗe ƙofar, to wallahi ko ki buɗe ko mu ɓalle ƙofar, kuma idan kika yarda muka same ki a ɗakin nan sai mun miki abin da bakiyi tsanmani ba."
Na jiyo muryar Huse na faɗin, "Don ubanta ai dole ta buɗe ta sakar min kurwar ɗa, kinyi kuskuran taɓa jinina, wallahi na fi ƙarfinki, na fi ƙarfin maitarki, ki buɗe ƙofar nan na ce don iyayenki." Ta ƙarashe zancen kamar mai shirin ɓalla ƙofar.
Kuka kawai na ke yi ina jin yanda a ke zagar min iyaye, da da yanda na iya da na buɗe musu ƙofar ko da kuwa kasheni zasuyi idan dai har zasu bar zagar min iyaye, sai dai bazan iya ɗaga ƙafata ba, a yanda nake zaunen nima fitsari na ke ji bansan yadda zanyi ba. Ina cikin wannan halin na jiyo muryar Hassan yana tambayar abun da ke faruwa. Wani irin farinciki ne na ji ya lulluɓeni, ban san lokacin da murmushi ya ziyarci laɓɓana ba, ji na ke kamar manzon ceto ne ya sauƙo mini, na yi hamdala ba adadi. Ban gama jin abun da suka faɗa masa ba na ji yana ta ƙiran sunana. So nake na amsa amma ita kanta muryar tawa ta dashe,jin ban amsa ba ne ya sanya shi fara bugun ƙofar, daga baya na ji shiru, zuwa can kuma na jiyo muryar Yaya Salisu da Hassan, balla ƙofar suka yi.
A kiɗime ya shigo ɗakin ya hauro kan gadon, juyo da fuskata ya yi, ido na duk sun kumbura sunyi luhuluhu gashi sunyi jazir, alamun na ci kuka ga kuma rashin bacci, ita kanta fuskar ta yi jazir abin ka da farar fata. Cikin wani yanayi na dube shi ina girgiza masa kai alamun ban san komai ba. Shi ɗinma kaɗa min kai ya yi alamun ya sani, ko da ya yi ƙoƙarin zaunar da ni na saka ihu, duk da muryata bata fita amma ya jiyo, ganin ina nuna ƙafata ya sa shi kai dubansa wurin. Cike da tashin hankali ya ke tambayar me ya samu ƙafar. Ba bakin magana sai kai na da na ke girgiza masa kawai.
Gani na yi ya fita ya shigo da Yaya Salisu yana nuna masa ƙafar tawa, da yake yana ɗori da jan targaɗe, yana dubawa kuwa ya ce gocewar ƙashi ne, a take ya gyara min ƙafar, ba aaramar azaba na sha ba, don fitsarin da na ke ta matsewa ma ban san lokacin da ya zubo ba, sai bayan an gama ne, Hassan ya taimaka min na gyara jikina, kafin Yaya Salisu ya tara duka ƙannen nasa a pofata, tunda ni bazan iya fita ba, gyaran murya ya yi kafin ya fara magana.
"Ina son duk ku bani hankalinku a nan, ke Huse me ya ke faruwa kika baro gidanki da asubar fari ga ɗanyen jego da jarirai, duk da dai, Larai (amaryarsa) ta fara faɗa mini wani magana jiya da ban fahimta ba."
Yana shiru kuwa Huse ta sanya kuka ta ce, "Wallahi Yaya ka ganta nan, jiya daga Adda Habiba ta ce ta dawo gida shi ne kawai ta ɗauke min kurwar yarinya ta tafi da shi, gashi can tana kwance har yanzu ko ruwa baya iya wuce maƙoshinsa."
Yaya Salisu ya ce, " To kuma shi ne aka ce miki kurwarsa a ka kama, kuma a ka faɗa miki matar ɗan'uwanki ita ce mayyar.?
"To Yaya idan ba ita ba ce wacece, duk danginmu dai ba maye, sannan duk waɗanda muke gidan ba bare, ita kaɗai ce, kuma ma tana tafiya bai daɗe ba fa yariyar ta fara shiɗa kamar zata mutu, kuma da aka biyo bayanta ba ta zo gida ba, ina ta tafi idan ba zuwa tayi cinye kurwar ƴata ba? Huse ta faɗa tana harata.
Girgiza kai kawai Yaya Salisu ya yi, a yayin da Hassan ke gefe haushi da baƙincikin ƙazafin da ake min ya ke cin zuciyarsa. Ina kallon yanda ya ke jifata da kallon rarrashi da ban haƙuri, ni kuwa hawaye kawai ne ke sintiri a dandamalin fuskata.
Yaya Salisu ne ya sake kallon Huse a karo na ba adadi ya ce, "Iya wannan ne hujjarki na cewa ita ta kama miki yaro?
Ta kaɗa kai ta ce, " Ƙwarai kuwa Yaya, idan ba ita ba ce, me ya sa da ake buga mata ƙofa yau ta ƙi buɗewa, don munafurci wai ƙafarta ce da ciwo, ai sai ta yi magana a ji muryarta idan da gaskiyarta."
Ba hujja ba ce wannan, sannan babu tabbacin ma mayu ne suka kama miki yarinya tunda ke ba mai magani ba kuma ba mai duba ba ce, maimakon kuyi tunanin miƙa yarinyar asibiti tun wuri kun zauna kuna ta abun da ba shi ne ba."
Ya dube ni ya ce, "To Aishatu kinji abun da suka ce, shin kina da masaniyar yanda abun ya faru ko kuwa, kuma ina ki ka je jiya bayan kin baro gidan sunan?"
Hawaye masu zafi na share kafin cikin dasasshiyar muryata na ce, "Wallahi Yaya ban san komai ba, ni ko ɗaukan yaran ma ban yi ba......... "
" Ai baƙincikin haka ya sa kika yi ƙokarin salwantar da rayuwarsu" Gambo ce ta katse ni tun ban kai aya ba.
"Ke Gambo ki rufe mana baki tun da ba ke aka tambaya ba." Yaya Salisu ya fada cikin tsawa. Shiru kuwa ta yi tana ta ƙwafa. Ni kuwa na ci gaba da maganata na faɗa musu inda na je jiya, kuma na ce zasu iya tambayar Hajjo ma idan ba su yarda ba.
"Wallahi Salisu ka fita ido na in rufe, wai a kan meye ne ga abu a fili kana ta ƙoƙarin sauya akalar zancen, to maza a sakar mini kurwan jika idan ba haka ba rayuka su baci na faɗa muku." Inna ta faɗi ta na ƙarasowa inda muke zaune.
Yaya Salisu ya dube ta ya ce, "Kiyi hakuri Inna, komai ina binsa a hankali ne, don a warware matsalar cikin sauƙi."
Salisu! Inna ta kira sunansa a fusace kafin ta ci