duk na haye na kumbura, zama da ƙyar tashi da ƙyar. Amma sam Inna kamar ba mace ba, kamar bata taɓa haihuwa ba, ko ɗigon tausayi na babu a ranta. Duk wannan abin da yake faruwa ban taɓa yarda na sanar da Hajjo ba. Dake Hassan ya siyo min ƙaramar waya, kusan kullum sai mun gaisa da Hajjo kuma in tabbatar mata komai lafiya.
A irin haka ne watarana naƙuda ta taso mini a bakin rijiya ina janyo ruwan da zan ɗauraye kayan Inna da na wanke...... ✍
_*Wannan littafin na kuɗi ne, da naira N300 kacal zaki more karatunki. Idan kina da buƙata zaki tura N300 ta wannan account ɗin 9061638128, Sumaiya Mohammad Tukur, Opay. Sannan shaidar biya ta wannan lambar. 09061638128. Daga nan sai a antaya ki a paid group.*_
⚡ SHAFUKAN ƘADDARATA ⚡
_*(Pages of my destiny).*_
STORY AND WRITTEN BY:
Sumaiya M Tukur (the Charismatic).
PAGE 11.
Wani irin azaba na ji a gadon bayana da mara, dole ta sanya na saki gugar da nake janyo ruwan ta faɗa cikin rijiyar. Da ke bakin rijiyar tana da ɗan gini na samu na dafa ina murƙususun azaba, ina ƙoƙarin juyawa ƙafata ta zame na wuntsila, ido na na runtse don na sadakar zan faɗa cikin rijiyar ne.A dai dai lokacin Hassan ya iso inda na ke ya riƙo ni, ya janye ni daga bakin rijiyar, tambayata yake ta faman yi, na ce masa ban sani ba cikina da bayana ke ciwo, abinka da sabon shiga. Sai sannu yake ta faman jera min, ina kaɗa masa kai cike da azaba.
ƙƘwalawa Inna ƙira Hassan ya yi ta fito tana tambayar me ya faru aka tada ta tana bacci. Nuna mata wurin da nake Hassan ya yi, ta juyo ta kalli yanda nake cije baki cike da azaba. Don wani irin ciwo nake ji wanda tunda uwata ta haifeni ban taba jin makamancinsa ba.
Cikin nuna halin ko-in-kula Inna ta ce, "To da kake nuna mini ita ciwon zan ɗauke mata ko meye?, haihuwace ta taho mata, sai ka je ka ƙirawo iya ungozoma ta zo ta duba ta."
Ta dube ni ta ce, "Ke kuma dai ba dai raƙin tsiya ba, haihuwarce kike wa wannan katifirin, yau dai zaki ji abin da ko wacce uwa take ji, sai a kama jiki." Daga haka ta bankaɗe labulen ɗakinta ta shige, ta kuma sake leƙowa ta ce, "Sai ka kama ta ka kai ta ɗaki kafin ta haihu min tsakar gida."
Duk da irin raɗaɗin naƙuda da azabar da nake ji, a yau dai sai da na ji ciwon kalaman Inna, yanda ta nuna ko-in-kula a kaina sai da ya min ciwo, ai a tsanmanina ciwo ya kore komai. Ina cikin saƙar zuci na ji Hassan ya tallafo ni ya miƙar muka nufi hanyar ɗakinmu. Marata ta riƙe ko miƙewa bana iya yi, haka a dudduƙe muka ƙarasa yana ta jero min sannu.
Bayan ya kai ni ɗaki ya fita, can ba jimawa sai ga shi tare da iya ungozoma, shimfiɗa ta mini a ƙasan ɗakin bayan da ta fahimci haihuwarce. Ta ce Hassan ya fita, kafin ta tambaye ni ina abubuwan haihuwar da muka tanada. Nan na nuna mata kayayyakin da Hassan ɗin yake siyowa duk lokacin da ya shiga birni, ta duba ta ce min.
"Ai wannan duk kayaki ne, kayan karɓar haihuwa nake nufi."
Cike da azaba na ce mata wanne ne kuma kayan karɓar haihuwa Iya. Nan ta lissafo min, sabuwar reza da zare da zannuwa da kuma babbar ledan shimfiɗa. Na ce mata duk babu. Salati ta saka ta ce
"Yanzu duk me kuke yi, ciki har ya isa haihuwa ba ku tanadi kayan tarbar yaro ba, idan baku sani ba ba za ku tambayi babba ba, ko da yake ba laifinku bane, Inna Zainaba ya kamata ta tanadar muku da komai tunda dai ta san baku sani ba, bari na je na tambayota, ko suna can wurinta."
Kamar zan hanata zuwa sai kuma na fasa, ina ganin ta fita, ban san ya suka yi ba, na dai ga ta dawo kamar ranta a ɓace. Hassan ta ƙira ta lissafa masa abubuwan da zai sayo, ta birkita kayana ta ɗauko zannuwa. Ba jimawa Hassan ya kawo komai, ta karɓa kafin ta sauƙe labulen ɗakin ta shiga aikinta.
Abu kamar wasa, tun shabiyun rana ake abu ɗaya gashi har an doshi magariba haihuwa shiru. Hankula duks un tashi banda na Inna, Hassan da ke waje yana jiyo yanda nake nishi da salati tare da duk wata addu'ar da tazo mini sai sannu yake ta mini daga waje, ina jin muryarsa na san yana cikin damuwa da tashin hankali.
A sannu hankalina ya fara barin jikina, wasu irin hotuna nake gani a ƙwaƙwalwata, dishi dishi nake ganin wata mata tana naƙuda amma a kan wani irin gado, wasu ne zagaye da ita suna gilmawa daga nan zuwa nan, bana iya ganin mutanen sosai, ganin su nake kamar zane a kan ruwa, wani irin sarawa kaina ya min, daga nan ban sake sanin abin dake faruwa ba sai farkawa nayi na ganni kwance a gadon asibiti.
Iya ungozoma ta na ganin halin da Shatu ta shiga hankalinta ya tashi, cike da ruɗewa ta shiga ƙwalawa Inna da Hassan ƙira a gigice, don kuwa hankalinta ya kai mapura wurin tashi, tun da take karbar haihuwa bata taɓa samun irin wannan ba.
A kidime Hassan ya shigo, ganin Shatu kamar bata numfashi, ga shi ta yi kace-kace cikin jini ya sanya shi tambayar Iya ungozoma abin da ke faruwa.
"Nima ba zan ce ga abin da ya faru ba, amma dai na yi iya ƙoƙarina da duk wani dabaran da zanyi abin ya gagara, gashi har numfashinta ya ɗauke, kuma tana zubar da jini." Iya ungozoma ce ta koro ma Hassan wannan bayanin.
Cikin tashin hankali ya ce, "To yanzu me zamu yi Iya?"
"Ban sani ba yanzu kam, sai dai mu zuba wa sarautar Allah ido."
Cikin harzuƙa da tashin hankali ya ce, "Na rantse da mai duka Iya idan Shatu ta mutu sai na ɗaure ki, dama baki san kan aiki ba kika shiga ciki?, Tun farko sai da na ce zan dinga kai ta asibitin birni Inna ta hana, ai gashi nan ina ƙoƙarin rasa Shatu."
Yana gama magana ya ciccɓeta ya fita, abin hawa ya tara suka yi asibiti ba tare da ya sanar da kowa ba. Sai bayan fitarsu ne Iya ungozoma take sanar da Inna abin da ya faru. Ko a jikinta, sai cewa ta yi Allah ya kyauta. Da mamakin Inna Iya ta gyara ɗakin Shatu ta bar gidan.
Suna isa aka karɓeta emergency, katin awonta aka tambaya, nan ya ce ai bata taɓa zuwa awo ba. Masifa suka shiga yi masa harda zagi, kamar baza su dubanta ba, shi dai Hassan shanye komai ya yi ya dinga basu haƙuri. Nan da nan likitoci suka rufu a kanta.
Jininta ya hau dayawa, idan aka ce sai ta farfaɗo ta haihu da kanta komai zai iya faruwa, gashi ta zubar da jini mai yawa, ita da abun cikin nata duk suna cikin haɗari, don zuwa yanzu bugun zuciyar yaron ya yi ƙasa,kuma ma ƙarfinta ya riga ya ƙare, wannan ta sa dole aka mata aiki aka ciro mata ɗanta namiji, sai dai ya galabaita ainun, kamar ma bai da cikakkiyar lafiya, don haka ɗakin kula da jarirai aka kaishi don bashi kulawa na musanman, ita kuma Shatu aka kaita ɗakin hutu, inda ita ma sai da a ka mata ƙarin jini har leda biyu. Kwana da wuni ta yi a kwance sai yanzun da ta farfaɗo, tayi tozali da Hajjo zaune a gefenta. Wanda Hassan ya sanar da ita tun a jiyan.
Hajjo da ta lura da farkawata ne ta shiga jera mini sannu, kafin ta fita ta sanar da likita, tare suka dawo ya duba na ba wata matsala, yace za a iya bani abinci ba mai nauyi ba.
Haka na yi ta jinya har sati biyu a asibiti saboda yaron bai da lafiya, kafin mu koma gida. Ƴan dubiya sunje har asibitin, a wannan karon kam Huse ta fara zubar da makaman yaƙinta don kuwa har asibitin ta je ta duba mu. Kaf gidan Inna idan ka cire Inna da Gambo sai Harisu ƙaninsu, kowa ya je ya duba ni da yarona da ya ci sunan Abubakar Siddik. Wanda haka kawai na ji ina son sunan, kuma na roƙi Hassan a saka ma yaron, shi kuma ya amince, saboda farincikin Shatu shi ne na shi.
Bayan komawarmu gida, sosai Hajjo take kula da mu, da ɗan jikanta, wanda a cikin wata uku ya yi ɓul-ɓul da shi, gashi fari tas kyakyawa kowa sha'awarsa yake yi, farin jini ne da dashi kowa son ɗaukansa yake yi.
Inna kuwa tunda aka haifi yaron ko kamanninsa bata sani ba, duk da ƙaunar da take wa jikokinta amma banda Siddik kamar yanda a ke ƙiransa, sabida kawai ni Shatu ni ce mahaifiyarsa, zuwa yanzu kam na sadaƙar da irin tsanar da Inna ta minu. Tun abin na damun Hassan har ya haƙura ya barwa Allah, tun da ya fahimci abun na Inna da gaske ne.
Ƙawata Haule ma kullum tana gidan, ita ke taya Hajjo hidiman Siddik, mu sha hira da ita, wanda zuwa yanzu na ƙara kyau nayi ƙiba da haske masha Allah, sosai jegon ya karɓeni, da kuma ya haɗu da kula da gyara na musanman da Hajjo ke mini.
Watansu shida suka tattara suka koma gidansu, gidan Inna, gidan da ya bude mata baƙpen SHAFUKAN ƘADKADDARTA.
**************
Ammi ce zaune a falo, cike da damuwar irin yadda maganganu a kan rashin auren Safwan yake yawa, kowa ya tashi sai ya ce, zaman me yake haka, wasu ma cewa suke ba haka kawai yake zaune ba, namijin da ya san daɗin mace shi ne zai iya rayuwa na tsawon shekaru ba mace?, ai ba dutse bane, mutum mai jini a jiki, kuma lafiyayyen namiji. Ga shi kuma kowa ya tashi sai ya kawo mata tallan ƴarta. Yanzu haka ga Suhaima yar Hajiya Saratu, ga Rauda yar abokin Abie ga kuma Hadiza da Umaima yaran ƙawayenta ne, ga kuma Hajara da Maimuna daga dangin Abie. Ita gabaɗaya ma ta rasa yanda zata yi, ga mai gayya mai aikin ya kafe har yanzu ya ce shi fa ya gama aure.
Tana nan zaune tana karanta wasiƙar jaki ta jiyo sallamar anti K, amsa mata ta yi ta shigo, ganin Ammin kamar da alamun damuwa a tattare da ita ya mata daɗi, amma sai ta ɓoye tare da sanya fuskar damuwa ta zauna kusa da ita ta ce.
"Lafiya kuwa Yaya? Na ga kamar akwai abin da ke damunki."
Numfashi Ammi ta sauƙe ta ce "Ai kin san damuwata Khadija bata wuce a kan Safwan, ni na ma rasa me zanyi yanzu, ga maganganu iri iri na ta yawo a kan sa, ni na ma rasa me ya tare wa mutane, kamar shi kaɗai ne wanda ya rasa mace yaki kuma sake aure."
Anti K ta ce, "Yaya abin da nake guje miki ke nan tun tuni, shi yasa na ke ta maganar a masa aure ko ba da amincewarsa ba. Duniyar yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba, mutane da yawa basu kiwon rayuwarsu sai na wasu, mafita daya ita ce ya yi auren, kin ga daga nan an toshe bakin kowa."
Ammi ta dubi anti K cike da damuwa ta ce "Ban ƙi ta taki ba Khadija, na so ai masa auren ko don gujewa bakin mutane, amma kin ga Alhaji ya ƙi sam, ya ce ba mai yiwa ɗansa dole, auren fari ma shi ya kawo kayansa, don haka yanzu ma idan ya ji yana da buƙatar aure zai yi, wai ya girma ya mallaki hankalinsa, ya san dai dai da saɓanin haka. To faɗa mini yanzu a nan me ya zan iya yi don Allah."
"Hmmm, ke kuwa kike da abin da zaki iya yi tun da ɗanki ne."
"Faɗa mini me zan yi?" Ammi ta fada cike da ƙosawa
Anti K ta saki wani murmushi mai ɗauke da ma'anoni ta dubi Ammi ta ce, "Umarni zaki bashi, ai kin san Safwan ba zai taɓa ƙetare umarniki ba, ko baya so zai yi, kawai ki sa shi ya je ya faɗa wa Alhajin yana son auren shi kenan an wuce wurin."
Shiru Ammi ta yi ta na nazari kafin ta ce "Amma kina ganin hakan mafita ce, ba fa na son ya sanƴa damuwa a ran sa har ciwonsa ya tashi, kin ga yanzu ma lallaɓawa a ke yi, idan ya motsa abin ba daɗi, wannan dalilin ya sa Alhaji yake gudun duk wani abin da zai sanya shi cikin damuwa."
Anti K wacce zuciyarta ta fara zafi da kalaman Ammi, amma ta shanye ta ce "Yaya! Ni ina mai tabbatar miki idan ya yi auren ya yi borin na ɗan lokaci komai zai wuce, mace ce fa zai ajiye ya shiga ya fita ya ganta, kuma halalinsa, dole ba zai jure ba tun da shi ba waliyyi ba ne, tuni zai bada kai bori ya hau, kin ga daga nan ai shi ke nan."
Kaɗa kai ammi ta yi alamun gamsuwa kafin ta ce "Shi kenan Khadija, zan jarraba hakan mu gani. Sai dai yanzu babbar matsalata wacce zan aura masa, don kowa ya tashi sai ya ce ya bashi mata."
Anti K ta saki wani murmushi ta ce "Duk wannan ba matsala ba ce, sai ki ture na kowa ki aura masa ƴar'uwarsa Binta, sauran kuma ki faɗa musu da kanshi ya wa kanshi zaɓi, kin ga an gama da wannan."
"Binta kuma Khadija?, da ma dai Jidda ki ka ce, ita ce tasu ta zo ɗaya, kin san Binta da Safwan a matsayin ma'aurata kam gobara kawai za a haɗa."
Anti K ta canza fuska ta ce "To ai Yaya rashin jituwar tasu ya sanya na ce a haɗa su, with time zaki ga fadansu ya koma soyayya, kin ga ko ranarda aka wayi gari babu rayuwarmu, zai zama babu wani matsala ko rarrabuwar kai a zuri'ar da muka bari, tun da dai kin ga iyayenmu mu biyu suka haifa, wallahi wannan rashin jituwar da ke tsakanin Binta da Safwan yana damuna."
Shiru Ammi ta yi bata ce ko ƙala ba. Anti K kuwa ganin kamar Ammi bata yarda da abin ba ya sa ta yi ta zugata da nuna mata anfanin haɗa su auren, har dai daga ƙarshe Ammin ta amince. Ganin haka ya sa anti K ta mata sallama ta tafi tare da jaddada mata kar ta yarda a wannan karon ta nuna wa Safwan ɗin da wasa ta ke yi.
Tana komawa ta dokawa ƙawarta Laura ƙira ta kwashe komai yanda suka yi da Ammi ta faɗa mata, ta ɗora da faɗin. "Ai na faɗa miki, ba boka ba malam haƙata zata cimma ruwa, ai sannu sannu bata hana zuwa, da sannu komai zai tafi yanda nake so, a sannu damo zai kai ga harawa, kuma ki zuba ido ki sha kallo. Daga haka ta kashe wayar. Tunanin yanda suka kwashe da Laura a kan zuwa wurin boka ta yi, daga fari ta amince, amma daga baya sai ta fasa, ba inda Laura bata kaɗa ta raya ba, amma fir ta ƙi, haka dole Laura ta kawo na mujiya ta zuba mata.
Wani shu'umin dariya ta saki ta ce Mubeena ke nan, ai ba za ki taɓa cin bulus ba, dole ke ma ki ɗanɗani baƙinciki kwatankwacin wanda na yi tsawon rayuwata ina ciki ........ ✍
_*Wannan littafin na kuɗi ne, da naira N300 kacal zaki more karatunki. Idan kina da buƙata zaki tura N300 ta wannan account ɗin 9061638128, Sumaiya Mohammad Tukur, Opay. Sannan shaidar biya ta wannan lambar. 09061638128. Daga nan sai a antaya ki a paid group.*_
⚡ SHAFUKAN ƘADDARATA ⚡
_*(Pages of my destiny).*_
STORY AND WRITTEN BY:
Sumaiya M Tukur (the Charismatic).
_*Wannan littafin na kuɗi ne, da naira N300 kacal zaki more karatunki. Idan kina da buƙata zaki tura N300 ta wannan account ɗin 9061638128, Sumaiya Mohammad Tukur, Opay. Sannan shaidar biya ta wannan lambar. 09061638128. Daga nan sai a antaya ki a paid group.*_
*LAST FREE PAGES*
PAGE 12.
Binta na dawowa anti K ta shaida mata an gama da wannan babin. The deal is sealed. Murna, farinciki ne ko me ye Binta za ta yi, ta kasa tantancewa. Burin ta ya kusa cika, ba tun yau ba take tsananin ƙaunar Safwan, shi kuma ta lura idan da akwai wacce ya tsana to a bayanta take.
Washegari Ammi ta tari Safwan da maganar tsaida mata. Abin da ta ke zato shi ya faru, don dama amsar ɗaya ce, "bazan iya auren ko wacce mace ba Ammi".
Dubansa ta yi da kyau ta murtuƙe fuska alamun ba wasa a lamarin kafin ta ce "Safwan" ya amsa da "na'am Ammi". Ta sake tamke fuska ta ce.
"Na gaji da jin wannan amsar daga bakinka tsawon shekara shida, kunnuwana ba za su sake juran jin waɗannan jimillan kalmomi da na haddace su da daɗewa ba."
Sunkuyar da kai Safwan ya yi ya ce, "Insha Allah Ammi ba zan bari ki sake jin su ba, muddin dai daga bakina zai fito, kiyi haƙuri."
Ammi ta ɗan saki fuska ta ce "Shi ke nan Safwan, Allah ya maka albarka. To yanzu ina son sanin ka shirya yin auren ko kuwa?"
Shiru ya yi ya sunkuyar da kai bai iya amsa mata ba. Ganin shirun ya yi yawa Ammi ta katse shi da kiran sunansa. Sai a lokacin ya ɗago da dara-daran fararen idanunsa waɗanda suka fara canza launi ya kalle ta. Yanayin da ya gani a kan fuskarta ne ya sanyaya masa gwiwa. Me ya faru yau, duk a kaina ne Ammi ta shiga wannan yanayin, ni ku.....
"Wace ce ni a wurinka Safwan?"
Tambayar da Ammi ta jefo masa kenan wanda ta yi sanadiyar katsewar zaren tunanin da ya fara saƙawa.
Dubanta ya yi a firgice zuciyarsa cike da kiɗima, muryarsa na rawa ya ce "Amm... Ammi me ki.... Me kike nufi.... da wannan tambayar?, Me yake faruwa ne Ammina?"
"Ba abin da yake faruwa Safwan. Ka amsa min tambayata kawai, ina son sanin matsayina a wurinka."
Sauƙar da kan shi ya yi na ɗan wani lokaci kafin ya dago ya dubi Ammi ya ce.
"Ke ɗin mahaifiyata ce Ammi, majinginata, mai share min kukana, ke ɗin duniyata ce, haƙiƙa Ammi bakina ba zai iya furta iya matsayin da kike da shi a raina da zuciyata ba."
Wani gwauron numfashi Ammi ta sauƙe ta ce, "Idan dai har da gaske kake, kuma abin da ka faɗa har zuciyarka ne, na tabbata ba za ka ƙi abin da zan faɗa ba a yanzu."
Damm! Gabansa ya faɗi, amma sai ya dake ya ce, "Insha Allah Ammi, komai kika ce ya zauna haka za a yi."
"Ma sha Allah, aure nake son ka yi" A razane ya ɗago kai ya ƙurawa Ammi ido, yana fatan wannan maganar ta kasance ba daga bakin Ammi ta fito ba, sai dai su biyu ne kawai a falon wanda ya tabbatar masa da cewa ita ɗin ce dai ta furta wannan maganar.
Gani ya yi Ammi ta kaɗa masa kai alamun yess abin da take nufi ke nan, ta ci gaba da faɗin. "Na san babu wacce kake so a yanzu, saboda haka na maka mata. Abin da nake so da kai shi ne; ka je wurin Abie da bakinka ka faɗa masa kana buƙatar aure a yanzu, shi ke nan.
Da ƙyar ya iya buɗe bakinsa ya ya ce, "Insha Allah Ammi, yadda kika ce haka za a yi." Ya ƙarashe maganar kamar zai yi kuka.
Wani murmushi ne ya bayyana a kan fuskar Ammi, ta ce "Yawwa Safwan, ai na san ba za ka zuba min ƙasa a ido ba, shi yasa bana jin ɗar idan dai a kanka ne. Kayi haƙuri, amma na tabbatar nan gaba zaka fahimci gata nake son maka."
Kaɗa kai kawai ya iya yi, don ya ma kasa furta komai saboda tashin hankalin da yake ciki yanzu. Ammi ce da take ta murmushi ta ce, "Ba ka tambayi wace ce matar ba, ko dai baka son ji ne?"
"ko ma wace ce Ammi na tabbata ba za ki min zabin tumun dare ba, Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi." Ya faɗa muryarsa a sanyaye
"To amin Safwan. Yar'uwarka ce Binta ta wurin Khadija, sai ka samu lokaci ka je ku gana, don bana son abin ya ɗauki lokaci mai tsayi."
Wani gumi ne ya yanko masa ya ce, "Binta kuma Ammi, Binta dai da na sani na anti K, noo, no Ammi please, banda Binta, I will accept any girl but not Binta, please Ammi."
"To ita na zaɓa maka, kuma ita zaka aura, tashi ka ban wuri, kuma ka tabbatar ka je kun gana, don nan da sati biyu ko wata ɗaya nake son a yi a gama ta tare. Kuma a yau ɗin nan ka samu Abie ka faɗa masa aure za ka yi, na faɗa maka ke nan. Don ka ga ina lallaɓa ka ne shi yasa, tashi ka je."
Miƙewa ya yi ya fice ya nufi sashensa. Yana zuwa ya wuce ɗaki ya kwanta a gado rigingine ya yi yana kallon sama, tunani yake na dalilin da ya sa Ammi ta bijiro masa ta wannan sigar, me ya sa Ammi za ta ce dole sai ya yi aure, kuma auren ma of all girls sai Binta, wai ko dai Ammi ta mance wace ce Binta ne, yarinyar da ba ta da kamun kai, wai shin me ma Ammi ta gani a wurin Binta ne.
Jawo wayarsa ya yi ya danna wa wata lamba ƙira, bugu biyu a ka ɗaga daga ɗayan ɓangaren. Muryar mace ce ta rangaɗa cikakkiyar sallama. Ya amsa mata, ko gaisawa bai tsaya yi ba ya ce, "Anti Saima ina cikin damuwa."
Daga ɗaya ɓangaren wacce ya ƙira da anti Saima ta ce "Na ji a cikin muryarka Safwan, me yake faruwa?"
"Ammi ce" ya faɗa
"Me kuma ya faru da Ammin".
"Komai ma anti Saima", nan ya kwashe duk yadda suka yi da Ammi ya sanar da ita.
Numfasawa ta yi bayan jin bayanansa ta ce, "To kai kam Safwan menene a cikin auren, ka yi haƙuri ka yi aurenka, son da Ammi take maka ne ya yi yawa, ta sha ƙirana tana koka mini halin da kake ciki, abin yana damunta, ka daure wannan karon ka yi yanda ta ce, Allah ya sa hakan ne mafi alheri a gareka da ita Bintan, kuma ya sa wannan auren ya kasance silar shiryuwarta. Ka ga ma ai ka yi jihadi, wataƙila abin da Ammi ta hango ke nan ya sanya ta yi wannan haɗin."
Cike da damuwa da karaya ya ce "Yanzu ke ma dai kin bi bayan Ammin taki ke nan, auren dole fa kuke shirin mini."
Daga ɗaya ɓangaren ta yi dariyar ta ce, "Ai kai ɗin ne Safwan sai da auren dolen, Ayrah ta girma ta na buƙatan ƙanne, amma na ga kai ba niyya, ni ai Ammi ta min dai dai, dole na ƙira ta na gode mata." Hira suka yi sosai har sai da ta ga hankalinsa ya ɗan kwanta kafin suka kashe wayar. A zuciyarsa yake raya Ayrah kam ai bata da wasu kannen sai fa idan ana yi a lahira ta samu.
Ammi kuwa bayan ta ga fitarsa ta goge ƙwallar da ta zubo mata, ta yi matuƙar jin tausayinsa, ji ta yi kamar ta ƙira shi ta ce ta janye, amma kuma