gaba da magana tana nuna shi da yatsa "Wani irin bi a hankali, kai ka ta ganin inda aka bi maye a hankali, to ai shi kenan, cigaba da binta a hankali, cigaba ka ji."
"Kiyi hakuri Inna." Ya sake faɗa a karo na biyu ya ja bakinsa ya yi shiru yana jin Inna ta na ta masifa.
Juyowa ta yi inda na ke ta ce, "Ke Shatu wallahi tun muna shaida juna ki sakar min kurwar jika, idan kuwa ki ka ƙi zaki yaba wa aya zaƙinta, don duk maitar ki baki kai Atine mayya ba, kuma ta buga da ni ta kasa, yi maza duk inda kika kai ta ma ki karɓo."
Wani irin matsanaicin kuka na sanya na rashin sanin abun da ya kamata na yi, bani da wasu kalamai a bakina da zan faɗa musu su fahimce ni, ina zaune suka gama mini ɗiban albarka, ba abun da na iya yi, ban tanka musu ba har suka gama suka fita, bayan Inna ta ce dole za'a kawo yarinya in tsallaka ta tunda ni bazan iya zuwa ba.
Bayan fitarsu Hassan yayi ta rarashi na da ban baki, ba abun da na iya faɗa masa shi ɗinma, sai hawaye da na yi ta gogewa. Basu jima ba kuwa suka dawo hannunsu dauke da jaririyar, suka kwantar da ita wai na zo na tsallaka ta. Ba yanda na iya, haka Hassan da Adda Habiba suka tallafe ni dole na tsallaka yarinyar sau uku kafin na dawo na zauna, ƙafata sai zugi ta ke saboda motsawa da na yi.
Ba'a dau lokaci mai tsayi ba kuwa jaririyar ta tsanyara wata irin kuka da muryarsu ta jarirai. Ai kaf wurin suka ɗauki salati da sallallami, ciki kuwa harda Adda Habiba, Gambo ne ta ce, "Ai gashi nan, yanzu gaskiya ta yi halinta, da munyi magana a ce ƙage da ƙazafi, yanzu kuma me za'a ce, an dai ji kunya."
Huse ne ta karɓe da faɗin " Makira mayya, ai na faɗa miki wallahi jinina ya fi ƙarfinki, sai dai ki koma can inda kika saba ki cigaba ba dai a nan ba, oh ni Huse Hassan ka kawo mana bala'i cikin zuri'a."
Inna kuwa ta ce, " Ai kamar yanda ya kawo bala'in haka zai fitar kuwa, don wannan mai gani har hanjin ba za ta ƙara ko awa gidannan ba, dole ta koma gidansu.
Ƙirjina ne ya buga da ƙarfi, wani tashin hankali ya ziyarci ruhi da gangan jikina, jin furucin Inna na yi a kaina kamar sauƙan guduma. Na juya gefen Hassan na kallo shi, a take na karanto tsantsan tashin hankali a fuska da zuciyarsa, wani irin zufa ne ya ke gangarowa daga cikin tarin gashin kansa kwantacce irin na fulani. Magana muke wa juna da ido da zuciya wanda mu kaɗai muke fahimtar yaren nan, muryar Inna ce ta katse mu..
"Kai Hassan wai ba magana na ke maka ba, yanzu nan ka saki wannan baƙar dagan kuma ka tabbatar ka fitar min da ita a gidannan." Ɗago fuska ya yi da niyar baiwa Inna haƙuri ta dakatar da shi da faɗin. "Umarni na ke baka, ba shawara ko ban haƙurinka na ke nema ba, idan har ni Zainaba ni na haife ka, kuma na isa da kai to ka saki Shatu yanzunnan."
************
Safwan ne ya fito a shirye tsaf cikin wani shadda royal blue ɗinkin da mazan yanzu ke yayi, hannunsa rike da Ayrah wacce ita ma ya shirya ta cikin wani baby gown mai kyau blue kalar kayansa, ya gyara mata gashinta ya mata style mai kyau. Duk irin waɗannan abubuwan ya iya su, wasu tun Hasina tana raye, don tare suke shirya Ayrah tun tana jaririya, bayan rasuwar Maa ɗinta kuma shi ya karɓi ragamar kula da ɗiyarsa, tun bai iya wasu abun ba har ya iya, ba yanda Ammi ba ta yi da shi ba a kan ya bata Ayrah amma sam ya ƙi.
Falon suka shigo suna ta tashin ƙamshi abin su, ya samu wuri ya zauna kafin ya dubi Ammi ya ce, "Ammi mu zamo zo mu tafi, yau gidan Baba malam zamu je, na ga mun kwana biyu ba mu je ba, na san yana kewar yar baturiyar amaryarsa." Ya ƙarashe yana kallon Ayrah yana murmushi.
Murmushi Ammi ma ta yi kana ta ce, "A Masha Allah hakan ya yi kyau, idan ka je ka gaida min su." Ta dubi Ayrah ta ce, "To yau kuma Hajiya Binta sai ta shirya taran kishiya ke nan."
Dariya duka suka sanya, har Ayrah da bata gama fahimtar abun da ake nufi ba, tunda Hausar ba isarta ta yi ba. Anti K da ke gefe ne ta yi wani tsakin da ya sanya dukansu suka juya suna Kallonta cike da mamaki da bukatar karin bayani............ ✍
⚡ SHAFUKAN KADDARATA ⚡
_*(Pages of my destiny)*_
Page 05.
Wayancewa ta yi kamar mai duba abu a wayarta ta ce, "Kai amma dai Nadiya akawi iskanci, tsofai tsofai da ita wai zata yi birthday." Ta ɗago ta dubi Ammi ta ce, "Nadiya fa classmate ɗina ce, da yaranta tima tima wai zata yi birthday, Allah ya kyauta."
Da yake Ammi ta san Nadiya sosai wurin son irin waɗannan shagulgulan, don duk cikin yaranta shida ko wani shekarar kowa sai yayi celebrating birthday ɗinshi, shi yasa bata kawo komai a ranta ba, sai ma cewa da ta yi, "Ai kinsan Nadiya sai a barta, akwai son kashe kuɗi a banza da hofi, yanzu kuɗin da zata kashe a wannan bikin, da sadaka ta yi dasu, a mata addu'ar alherin rayuwa da fatan gamawa da duniya lafiya da ya fi mata,ga kuma ɗumbin ladan da zata samu."
"Ai kuwa dai Yaya" anti K ta fadi.
Jin sun fara wani hiran daban ya sanya Safwan kama hannun Ayra suka mike, sallama su ka yi wa Ammi tare da anti K suka fice, don shi har ga Allah hankalinsa bai kama maganar anti K ba. Da harara anti K ta bi bayansu a fakaice ba tare da ta bari wani ya lura ba kafin suka ci gaba da hiransu, ba ita ta bar gidan ba kuwa har bayan magariba.
Safwan kuwa da fitarsa mota ya shiga ya shigar da Ayrah gefen mai zaman banza ya tada motar suka fice daga gidan. Direct suka wuce unguwar Jambutu, wani layi suka shiga wanda da gani mazauna wurin masu rangwamen ƙarfi ne. Dai dai wani gida suka tsaya wanda shi dai kam ya na da ɗan kyaunsa ba kamar sauran ba. Ya kashe motar suka fito, riƙe da hannun Ayrah ya yi sallama a ƙofar gidan, jin ba amsa ba ya sanya shi buɗe dan madaidaicin gate ɗin gidan suka shiga. Tsakar gidan fess kamar ba'a taka shi, broken tiles ne ta ko ina ya sha wanki sai walwali ya ke yi. Tsayawa ya yi ya sake yin wata sallamar, can daga ciki wata murya mai cike da kamala ta amsa mishi kafin ta leko. Babban mata ce amma ba can ba, don baza ta wuce shekaru arba'in biyar ba.
Faɗaɗa fara'ar fuskarta ta yi ta na faɗin, "Wa na ke gani haka kamar kishiyar, ah lale, marabanku da zuwa. Safwan sannu da zuwa, kai dai kullum kamar baƙo, lale maraba ku shigo daga ciki." Ta faɗi tana juyawa ta koma cikin falon.
Da sallama ya shiga, da gudu Ayrah ta je jikin matar ta ce mata, "How are you Hashiya."
Dariya Hajiyan ta yi ta ce "Hajiya a ke cewa bagwariya ba Hashiya ba, kuma na ce ki daina min magana da wannan yare na ku kin ƙi bari, ni no turanci, ke kuma no Hausa to sai yaya ke nan?."
Dariya Ayrah ta sanya ta ce, ina shin Ausa mana Hashiya, Ammina tana yi magana ni da Ausa" ta faɗi da Hausarta na 'yan koyo.
Hajiya ta ce, " Ai gara Ammin ta rinƙa miki magana da Hausa kam, amma a ce jikar Hausa Fulani ba Hausa ba fillanci ai an samu damuwa, yanzu nima fillanci zan rinƙa miki, ato don haka sai ki shirya." Dariya kawai Ayrah ta yi don ba komai ta ke ganewa ba a zantukan Hajiya.
Sai a sannan Hajiya ta ɗago ta kallo Safwan da ke ta faman murmushi suka gaisa, don idan da abun da ya ke saka shi farin ciki to bai wuce ganin Ayrah cikin farinciki ba.
Hira suka shiga yi sosai da Hajiyar, sosai ya saki jiki kamar ba shi ne wanda ya fito yana ta damuwa da haɗe fuska ba. Daga bisani Hajiya ta kawo musu fura mai kyau wanda aka yiwa haɗi da nono da kuma yogurt mai dadi, ya ji gurzajjen kwakwa sai ƙamshi ya ke yi, gashi da sanyin Masha Allah. Ai kuwa suka hau sha shi da Ayrah ba kama hannun yaro. Wannan yana ɗaya daga cikin abun da ya sa ya ke son zuwa wurin Hajiya, don ta iya haɗin fura iri iri, bayan ita kuma sai Hasina wanda ya tabbatar a wurin Hajiyar ta koya, ya sha fura a wurare da dama, bai samu irin wannan ɗanɗanon ba, kai har Ammi ta masa ita ma ya ce bai yi irin na Hasina da Hajiya ba, shi yasa wani lokaci Hajiya ta ke aiko masa ko da bai je ba saboda sanin yanda suke ƙaunar furar shi da tilon jikarta.
Suna sha suna hira da Hajiya, a haka har Baba malam ya dawo ya same su, ya yi farinciki da ganinsu haka, musanman ma Safwan da yana wuya ka ga walwalarsa ko dariya, ga kuma jikarsa da yake matuƙar so, don ita ya ke gani a madadin mahaifiyarta. Yakan yawan yiwa Allah godiya da ya bashi zuri'a ba mai yawa ba, 'ya daya ya haifa, ita ma kuma 'yar ɗaya ta haifa ta tafi ta barsu, a kullum yana addu'ar Allah ya raya masa wannan jikar tasa ya kuma bata zuri'a na gari masu yawa masu albarka.
Shigowa ya yi da sallamarsa, ya samu wuri ya zauna, Hajiya ta masa maraba kafin ta ɗauko masa ruwa masu sanyi ta kawo da kofi, sai da ta tsiyaya ta miƙa masa kafin ta koma mazauninta.
Murmushi kawai Safwan ya yi tunowa da matarsa da ya yi, tabbas duk wani kyaun hali da ɗabi'u da take dashi da kuma girmama miji a wurin hajiya ta ɗauko, uwa uba kuma ga tarbiyya da iyayenta biyu suka haɗu suka gina ta a kai, wanda ya yi wa 'ya'yansa kwaɗayin samu, sai dai Allah bai yi ba, ta tafi ta bar su a lokacin da ba wanda ya yi tsanmani.
Ƙiran sunansa malam ya yi a karo na biyu. Firgigit ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka ya dubi Baba malam. Sai kuma a lokacin ya ankara da guntun hawayen da suka sirnano daga kurmin idonsa, ya sanya hannu ya ɗauke su.
Girgiza kai kawai Baba malam ya yi kafin ya ce, "Wato har yanzu Safwan baka daina wannan doguwar tunanin da damuwar ba ko, na yi ta maka faɗa, na yi nasihar, Hajiya a nan tana ƙopƙari ita ma, ga Ammi da Alhajinka, amma a ce har yanzu, anya kuwa Safwan, ko dai kana fushi ne da hukuncin Ubangiji?"
Da sauri ya girgiza kai ya ce, "A'a Baba, wane ni na ja da hukuncin Ubangiji, kawai dai na kasa mancewa da Hasina ne a raina, Hasina mace ce ta gari, irinsu ba su da yawa a duniyar nan."
"To idan kuwa haka ne, ka cire damuwa a ranka, addu'a Hasina ta fi buƙata a yanzu, wannan shi ne kaɗai soyayyar da zaka nuna mata, Allah da ya bamu ita ya fi mu son ta, kuma shi ya karɓi abin sa."
"Haka ne Baba, addu'a kam muna yi, sai dai zamu kara in sha Allah."
"To ai haka ake so, sai dai yanzu ina so ka min alƙwarin zaka cire damuwa a ranka, zaka dawo asalin Safwan ɗin da na sani, mai yawan murmushi, mai dariya da raha, Safwan da na sani mai cike da natsuwa da kwanciyar hankali." Faɗin Baba malam ke nan.
Girgiza kai Safwan ya yi ya ce, " Baba alpawari abu ne mai girma, wanda idan ka yi to sai ka cika, ka yi haƙuri Baba, bazan iya maka alƙawari ba, amma in sha Allah zan yi iya ƙoƙarina wurin ganin na sauya, na dawo kamar yadda ake so, zan yi ƙoƙari matuka in canza ko da iya zahiri na ne."
Baba malam ya yi murmushi irin nasu na manya kana ya ce, "Safwan ke nan, ka yi ƙoƙarin canza baɗininka kafin zahirinka ya canza, ba yanda za'a yi ka canza zahirinka kaɗai, saboda baɗininka zai dawo yana farautar zahirinka, kayi ƙoƙarin sauya duka biyun kaji, kuma don Allah ka samu wata matar ka aura, wataƙila sanadin hakan zai iya gusar maka da damuwar da ka ke ciki."
Wani murmushi Safwan ya yi mai ɗauke da ma'anoni da dama kafin ya ce, "Aure kuma Baba, ba na jin zan iya auren wata mace har in mata adalci a gidana. Wallahi ban san me yasa ba Baba, har yanzu ina jin Hasina a jinin jikina, sai ina jin kamar tana raye bata mutu ba, ina jin numfashi da ruhinta suna kawo mini ziyara a mabanbantan lokuta, ko yaushe ji na ke kamar muna rayuwa a doron duniya ɗaya, ina jin kamar Hasina ba ta mutu ba."
Baba malam ya ce, "Subhanallahi, haba mana Safwan, kada soyayya ta sa ka zauce mana, kada so ya sa ka runtse idanunka daga kallon gaskiya, kada ka bari so ya kaika ga saɓon mahalicinka. Safwan." Malam ya ƙira sunansa.
Ɗago kai ya yi ya Kalli Baba, idanunsa tab da kwalla. Baba ne ya ci gaba da magana, "Safwan kai da kanka ka suturta gawan Hasina, ni din nan ni na jagoranci jana'izarta, na mata sallah, da waɗannan hannaye nawa, da naka muka sanya ta a kabarinta, kaga ke nan tabbas Hasina ta bar mana wannan duniyar, kuma ka san ba'a mutuwa a dawo, bare ka ce ko dawowa ta yi, don Allah ka sanya haƙuri da tawakkali a ranka, wanda ya mutu ya mutu baya taba dawowa. Ka samu mata ka yi aure."
Share hawayensa ya yi ya ce, "Ba wacce za ta so ni Baba."
"Akwai da yawa Safwan, kai yaron kirki ne, kuma kana da tarbiya da kyawawan halaye, ba macen da zata shigo rayuwarka bata so ka ba, ko wasu iyaye zasu so baka auren ƴarsu Safwan, yau da Hasina ta na da ƙanwa, da tabbas zan aura maka ita, don bazan so na yi asaran suruki na gari ba."
"Ina Baba, bazan taɓa iya auren wata ba ma, bare kuma ƙanwar Hasina wacce suke jini ɗaya, ba wacce zata maye gurbin Hasina, zan adana mata kai na har Allah ya sake haɗa mu a aljannah."
Kaɗa kai kawai Baba ya yi, don ya lura Safwan ya yi nisa baya jin kira. Nashia ya shiga yi masa mai ratsa jiki kasancewarsa babban malami kuma limami, a cikin hikima irin ta su yake nusar da shi anfanin haƙurin da ɗaukar ƙaddara a wurin bawa. Sun kwashe lokaci mai tsayi suna tare har Hajiya da ta fice da Ayrah tun sanda suka fara magana ta dawo riƙe da hannunta, daga nan aka ɗaura hiran da ita, ta kawo musu alkaki da takan ajiye saboda malam na so. Ba su suka tashi ba har sai da ladani ya doka ƙiran sallar magariba, nan malam da Safwan suka wuce masallaci, a yayin da Hajiya da Ayrah suka yi na su a ɗaki.
Bayan sun dawo Hajiya ta kawo musu abinci suka ci, Ayrah kam ba abin da ta ci sai fura da ta sake ɗurawa cikinta da alkaki kayan zaƙi. Basu bar gidan ba har sai takwas na dare suka koma gida.
A falo suka tarar da Ammi, Abie ma ya dawo. Gaida su Safwan ya yi ya zauna suka ɗan tattauna da Abie a kan harkan business nasu kafin ya musu sai da safe ya tafi, suna dagawa juna hannu shi da Ayrah, wacce da ƙyar ta yadda ta ke kwana a wurin Ammi. Tun bayan dawowarasu ta ɗauke ta, don a ganinta ba dacewa su rinƙa kwana da ga shi sai Ayrah a ɗaki ɗaya, duk kuwa da kasancewarta 'yarsa, kuma bata tantama a kan tarbiyar Safwan, amma akwai sheɗan, wai maganin bari kar a fara.
************
A bangaren anti K kuwa, tun da ta koma gida ta ke saƙawa da warwarewa, ta rasa ta wani hanya za ta bi don cinma ƙudurinta, Ammi ta na da masifar taurin kai, duk ta yanda ta biyo mata sai ta kauce, amma tabbas ba za ta sare ba, zata ɗan bata wani lokaci kaɗan tukunna.
Jin sallamar Alhaji Munnir mijinta ne ya dawo da ita daga duniyar tunani da ta afka. Amsa sallamar ta yi tana mai gyara zamanta, har ya zo ya zauna a kan kujerar da ta ke bata motsa ba.
Cire hularsa ya yi ya ce mata, "Sannu sa gida".
Ta ce masa "Yawwa sannu kai ma".
Ya kaɗa kai ya ce, "Khadija ke nan, ba za ki taɓa canzawa ba, yau kuma wa ya taɓo ki?"
A harzuƙe ta juyo ta ce, "Don Allah malam ka rabu da ni, ba na son damuwa da takura yanzu, haba daga dawowarka za ka wani cika min kunne da surutu, ina ruwanka da damuwata tunda ba ka da maganinsa."
"Hmmmmm" kawai ya ce ya ɗauki hularsa ya nufi hanyar falonsa. Yana shiga ya cire babbar rigarsa ya ajiye a gefe haɗe da hulan, ya zauna a kujera yana tunanin halin matar tasa, tsawon shekara ashirin da biyar haka suke rayuwa, ya yi mata uzuri sau da dama amma ta ƙi sauyawa, bai san daɗin zama da mata ayi hira ko shawara ba, bai taɓa jin yanda maza suke ji idan a na girmama su a gidansu ba, ba wata magana mai daɗi wanda zai ce ya taɓa haɗa su da matarsa, zuwa yanzu kam ya fara tunanin ɗaukan shawaran yan'uwansa da suke cewa ya ƙara aure.
Yana nan zaune yana karanta wasiƙar jaki, Jidda yarsa ta shigo. Ganinsa a haka sai ya bata tausayi, a shekarunta na ashirin da ɗaya, ta fahimci mahaifinta ba shi da kwanciyar hankali a gidansa, irin kulawa da tarairaya da ake wa miji duk ba ya samu, idan ka ga wannan kam sai a gidan Ammi.
Sallama ta yi don ya san da shigowarta, bayan ya amsa ta shiga ta gaishe shi, kafin ta nufi ƙaramin firijin da ke falon ta ɗauko masa ruwa da drinks masu sanyi ta zo ta tsiyaya a cup ta miƙa masa. Ya karɓa ya sha yana sanya mata albarka. Fita ta yi sai ga ta ta dawo da abinci jere cikin basket ta kawo masa har inda ya ke, tun da ta san ba ya son cin abinci a dinning. Godiya ya mata kafin ya sauƙo ya fara cin abincin.
Jidda ta ce, "Don Allah Abba ka ƙara hapuri da halin Mami, kar ka yi fushi da ita, in sha Allah watarana sai labari."
Yana yabawa da hankali irin na Jidda, sam ba ta ɗauko halin mahaifiyarta ba. Kallonta ya yi cike da so irin na ɗa da mahaifi ya ce.
"Ba komai Uwata, Allah ya miki albarka ke da sauran ƴan'uwanki, don Allah ina miki wasiya da cewa, kar ki kuskura ki gwada abin da ki ka gani a gidanku idan ki ka je na ki gidan."
"In Sha Allah Abba", hira sosai su ka yi har ya kammala cin abincin ta tattare wurin kafin ya tashi ya shiga ciki don kintsawa.
Tana fita da kwanukan Mami ta bita da harara, haɗe da tsaki, ta furta, "Masu Uba, daɗin dai baki isa ki ce ba uwarki ba ce ni."
Suhaima da ta shigo yanzu ba ko sallama ta ce, "A to faɗa mata dai Mami, wallahi yarinyar nan akwai kwainane da neman suna." Ita dai ta wuce bata tanka musu ba, ta ajiye kwanukan a kitchen ta zo ta wuce su suna kus_kus.
************
Inna ta na gama maganarta ta juya ta tafi, wani zufa Hassan ya share ya dube ni na kaɗa masa kai alamun ya aikata abun da Inna ta ce. Maida dubansa ya yi kan Yaya Salisu, kaɗa masa kai shi ɗinma ya yi alamun ba ka da wata mafita. Dubansa ya mayar kai na bakin sa na rawa ya kamo hannuna, muka haɗa idanu muna yiwa junanmu kallon bankwana, sunkuyar da kansa ya yi ya ce,
"Kiyi hakuri Aishatu, ni Hassan mijinki na........ ✍
⚡ SHAFUKAN ƘADDARATA ⚡
_*(pages of my destiny)*_
STORY AND WRITTEN BY:
Sumaiya M Tukur (the Charismatic).
Page 06.
Kiyi haƙuri Aishatu, ni Hassan mijinki na amince zan zauna da ke ko da na wani irin hali, ko da ke mayyar ce da gaske bare kuma na san ba haka ba ne, kai wallahi ko da kuwa aljana ce ke zan zauna da ke, ba zan taɓa iya sakinki ba.
Salati su Gambo da ke tsaye a wurin suka sanya, Huse ta ce, "Wai ka san me ka ce kuwa Hassan, ka na cikin hayyacinka kuwa, ka san abin da ka ke fada, ko dai ta yi maka wani siddabarun ne irin na su na mayu, tab! Dankari."
Gambo ta amshe da faɗin, "Au, to ke dama kin tsanman zata bar shi haka ne, sai yanzu na fahimci dalilin da ya sanya ya kafe kai da fata sai da aka yi wannan ƙaddararren auren."
Ɗago rinannun idanunsa ya yi ya dubi Gambo kafin ya daka mata wata tsawar da ta razana mazauna wurin, "Ke Gambo!! Akwai sa'anki ne a nan, kar in ƙara jin bakinki munafuka, tashi ma ki bamu wuri."
Sum sum ta miƙe ta fita, don ba ƙarya ta firgita da yanayinsa. Ƙwafa Huse ta yi ta bi bayanta tana yaɗa habaici da zagi. Yaya Salisu ne kaɗai ya rage. Bayan ya bi kannen nasa da kallo ya mai da dubansa garemu. Faɗa ya shiga yi mana da nasiha kafin daga ƙarshe ya dubi Hassan ya ƙira sunansa. Bayan Hassan ɗin ya amsa Yaya Salisu yaɗaura da faɗin, "Ka daure zuciyarka ka yi abin da Inna ta ce, bin umarnin iyaye wajibi ne, kar ka bari ta yi fushi da kai, saboda fushin iyaye yana tare da fushin Ubangiji, ka yi mata saki irin wanda zaku dawo da zamanku idan komai ya lafa."
Tuni gudun hawayena suka ƙaru bayan jin maganar da ta fito daga bakin Yaya Salisu. Dubansa Hassan ya yi da wani irin yanayi da na kasa fassarawa ya ce.
"Hakan ya na nufin ke nan Yaya kai ma ka yarda da abin da suke faɗi a kan Shatu?, kuma ka bada goyon baya wurin sakinta?" Girgiza kansa ya ke kafin ya ce, " Bazan iya ba, wallahi bazan taɓa iyawa ba, har abada ni Hassan bazan taɓa iya furtawa ko rubutawa Shatu takardar saki ba, ai ko Ubangiji ya ce kar a yi wa wani biyayya wurin saɓa masa, sakin Shatu zunubi ne, bata da haƙƙin kowa, bazan saki matata ba."
"To ya ka ke son muyi Hassan, ka san dai halin Inna, tun da ta faɗa sai an yi. "
"Taimako ɗaya za ka min Yaya, kawai ka ce wa Inna anyi sakin, ni kuma zan maida Shatu gidansu ta yi jinya, zuwa lokacin da zata ji sauƙi, komai ya lafa sai ta dawo, ka yi min wannan alfarmar don Allah Yaya." Ya haɗe hannunsa alamun roƙo.
Ɗan jimm Yaya Salisu ya yi kafin daga bisani ya ce, "Shi kenan Hassan, zan maka wannan afarma, Allah ya sa hakan shi ya fi alheri." Yana gama magana ya tashi ya fice shi ma aka bar mu mu biyu.
Matsowa