ga nan Baba Baushe, kowa ya san shi, sanannen mai bada magani ne a ƙauyen nan har ma da maƙwabta da ya danganci ko wane ɓangare, yanzu ma kuma shi zai warware mana wannan sarƙaƙiyar."
Shiru wurin ya ɗauka kafin kaka Baushe ya miƙe ya yi ɗan jawabinsa kana daga ƙarshe ya ce"Idan ka san kana tare da maita kuma baka son tonuwar asiri a bainar jama'a tun wuri ka bar nan. Ganin ba wanda ya motsa ya sanya shi fara gudanar da ayyukansa. Ba jimawa kuwa wata mata ta zube a wurin, wani matashin saurayi ya bi bayanta, sannan sai wani ɗan karamin yaro ɗan shekara bakwai. Duk da ganin sun faɗi kaka Baushe bai fasa aikinsa ba har sai da ya ida kafin ya nemi wuri ya zauna, ya ce a ɗibo waɗanda suka faɗi a kawo masa gabansa, wani garin magani ya zuba a cikin rushin wuta da ya bukaci a kawo masa daga cikin gidan mai gari, nan take suka fara tari suna birgima.
Kaka Baushe ya dubi tarin mutanen sannan ya mai da kallonsa kan Inna wacce ta yi tsumu tsumu, ya dubi mai gari ya ce "To ka ga duk taron mutanen wurin nan babu wani me maita ko kanbun baka, sai wadannan mutanen guda uku da ke gabana a yanzu, sannan wannan saurayin ba maita gareshi ba kanbun baka ne, wannan tsohuwar dai ita ke da maita. Ko zan iya sanin a ina suke da zama?".
Mai gari da tunda ya ga bakin gidansa guda biyu sun faɗi ya sha jinin jikinsa, jin bayanin da Baba Baushe ya yi da kuma son sanin ahalin waɗanda suka faɗi ya daɗa dugunzuma hankalinsa. Da ƙyar ya buɗe baki ya ce "Waɗannan biyun dai baƙin gidana ne, ita kuwa wannan matar ban ma san ta a karkarar nan ba."
Wata ce daga can cikin taron mutanen ta ce, a ƙauyen gangare take dake maƙwabtaka da wannan kauyen, wucewa ta zo yi ta ga ana taro shi ne ta tsaya kallo."
Kaka Baushe ya shiga bankawa tsohuwa turare da magunguna, da ƙyar aka samu ta dawo hayyacinta, sai dai ta ce sam baza ta bar maita ba, gadon gidansu ne tun iyaye da kakanni, amma su basu cin mutum. Ba shiri mai gari ya sallameta ya kuma jaddada mata ko mai kama da ita kar ya gani a yankinsa, ta karkaɗe jiki ta ɗauki ƴar bakkonta ta wuce abin ta. Kan sauran ya dawo, ashe shi yaron a makarantarsu aka bashi ya ci, ko iyayensa ma basu sani ba. Magunguna kaka Baushe ya basu, da yake baƙi ne kwanansu biyu a gari, shi yasa zargi bai biyo ta kansu ba.
Bayan komai ya lafa, mai gari ya yi jawabi ya sallami mutane, bayan an wanke ni daga zargin maita da ake min wata da watanni, mutane dayawa sai da suka miƙa ban haƙurinsu ga Baffajo da ahalinsa kafin su tafi. Wurin ya rage daga mu sai su Inna. Kaka Baushe ya dubi Inna ya ce.
"To yanzu kin gani da idonki ko Zainaba, ba a yankewa mutum hukunci ba tare da tabbatarwa ba, yanzu wa gari ya waya, ina zaki da tarin alhakin wannan baiwar Allah. Ki gode wa Allah kuma ki gode wa Shatu, don yanda na shigo karkar nan a harzuƙe, ba domin ta dakatar da ni ba, yanzu da wani magana ake daban ba wannan ba."
Sunkuyar da kai Inna ta yi ta ce, "A yi hakuri Baba Baushe, mai faruwa dai ya riga ya faru, amma abin tambayar a nan shi ne, menene dalilin da ya sanya da Shatu ta tsallake jaririyar ta hau kuka, bayan ko tari bata yi ba kwana da yini. Wannan lamarin shi ne dalili na na faɗin Shatu ce ta kama ta, don kowa ma haka zai dauka."
Kaka Baushe ya ce, "Eh kowa zai iya ɗaukan lamarin a haka, amma kuma na ki sai ya haɗu da baƙin hali da ƙiyayyar da kika ɗaurawa ƴar mutane, kuma lallai hakan yana faruwa, amma dai tabbas babu maita a tattare da Shatu."
Kuka muka jiyo daga gefe, juyawar da zamu yi kuwa muka kalli Huse ce ke kuka harda shessheƙa. Tamabayarta mai gari ya yi ko mai ya faru. Ƴar ta ta nuna masa ta ce, "Ai to gata nan, tun ranar da abin ya faru bata sake lafiya ba, har yanzu da suke da watanni uku ita wuyanta ko tsayuwa baya yi, saɓanin ƴar'uwarta da har ta fara koyon zama, kuma ko ina muka je sai a ce mana shafar mayu ne."
Salati Hajjo ta sanya ta ce "Ai wai dama ƴar har yanzu mayun basu sake ta ba, ikon Allah, sai kuma gashi ana zaton wuta a maƙera, wa ya sani ma ko wani baƙin abin aka aikata ya waiwayo kan baiwar Allah."
Nan kuwa Inna ma ta hayyaƙo suka fara musayar baki, dama Hajjo a cike take da Inna da ahalinta.
Abu fa kamar wasa Hajjo ta ce wallahi sai ta ɗaure Inna, ba abin da zai hana ba ta yi shari'a da ita ba, kotun birni zata kaita. Tuni cikin Inna ya ɗuri ruwa, idan da abin da take tsoro to a bayan hukuma ne. A ka taru a na ba wa Hajjo haƙuri ta ce sam ba za ta haƙura ba, Inna kam zawo kaɗai ne ya rage bata yi ba a wurin, tuni ta jiƙe jagaf da zufa, duk kuwa da yanayin sanyi da a ke ciki. Da kyar da suɗin goshi a ka samu Hajjo ta haƙuram, hakan ma da sharaɗin sai Inna da ahalinta sun durƙusa sun ba wa Shatu haƙuri, shi ma kuma sai idan Shatun ta haƙura ta yafe musu to shi ke nan.
Duk izza da girman kan Inna sai ga ta gurfane gaban Shatu ta na ta faman bata haƙuri ita da tawagarta. Da hanzari Shatu ta ɗago ta ta ce "Har abada Inna ni kam na yafe miki, dama can ban riƙe ki ba." godiya Inna ta shiga zabgawa, Mairo kuwa baƙincikin wannan haƙurin da suka ba Shatu kamar zai yi ajalinta.
Bayan an kashe wannan wutar ne kaka Baushe ya karɓi yarinyar ya duba ta, sai ji muka yi ya ce, "Assha, to ai wannan bugun aljanu ne, ba wani maita a nan, ga abu nan a cikin idanunta, da a ce ma an magance da wuri ai da duk abin bai kai nan ba." Ya miƙa ma Huse yarinyar ya ce gobe ta kai ta can wurinsa akwai maganin da zai basu, suka masa godiya.
Faɗa mai kamar nasiha mai gari ya mana kafin ya sallami kowa, tun a wurin ya so ya sulhunta in koma ɗakina amma sam Hajjo ta ce bata san wannan zancen ba, ai na gama zama da dangin marasa mutunci. Haka Inna ma ta ce ai dama Hassan ya gama aurena, kar wai a ga an wanke ni daga zargi a tsanmani ta canza, tana nan a Zainaba da aka sani.
Ganin zasu sake tada wani bala'in ya sa Baffajo samu a gaba muka tafi gida. Zuciyata cunkushe da abubuwa guda biyu, farinciki da kuma damuwa.
A zahiri farinciki ya kamata na yi saboda rufuwar baƙar shafi daga shafukan ƙaddararta, sai dai kuma rufuwarsa dai dai take da buɗewar sabon shafi wanda ban san menene rubuce a ciki ba.
Haka muka isa gida, zuciyar Hajjo wasai, tun bayan faruwar wannan al'amari sai yau na ga cikakkiyar farinciki a fuskar iyayena, sai hakan ya danne nawa damuwar, muka haɗu muka yi ta murna. Ba jimawa kaka Baushe ya shigo ya mana sallama zai koma, magunguna ya bani irin waɗanda masu juna biyu ya kamata su rinƙa anfani da shi. Baffajo ya rakasa har marrabar ƙauyen namu da nasu, don kaka Baushe da kafa zai koma, idan dai ba wai nisan wuri ya yi nisa ba, baya taɓa hawa abin hawa.
Kwana biyu gidan namu baya rabo da baƙi, ƴan taya murna, da kuma masu zuwa bada haƙuri, muatne dayawa sun ji kunyar abin da suka aikata mana, musanman ma Baffajo, har limanci aka mayar masa amma ya ƙi karɓa ya ce ba damuwa, a bar malam muttaƙa ya ci gaba da jan sallah. Hakan kuwa aka yi.
Ranar kuwa sai ga Inna Zulai; Adda Habiba da kuma Indo sun zo wai dubani da bani haƙuri, har da matan Yaya Salisu. Hajjo bata nuna musu komai ba, ta musu tarba mai kyau. Bayan an gaisa ne naji Inna Zulai ta na baiwa Hajjo baki a kan tayi haƙuri ta janye maganar ƙin komawata, yanzu haka Hassan ɗin ma yana kwance ba lafiya ko kasuwa ya daina fita.
Ina ji Hajjo ta ce.
"Au wai shi Hassan ɗin ne ba lafiya, to Allah ya bashi lafiya, amma dai kam sai dai ya ɗau na annabawa, don kuwa Shatu baza ta koma gidansa ba. Duk haƙuri da ban bakin da Inna Zulai ta yi Hajjo ta kafe ta ƙi canza ra'ayi, har sai daga ƙarshe ta ce wa Inna Zulai, "Nikam Yaya Zulai, dubiya ku ka zo ne, ko kuwa dai dama maganar da ta kawo ku ke nan kuka fake da dubiya."
Inna Zulai ta ce "Haba Mariya wani irin zance ne haka, har ga Allah dubiya muka zo da ban haƙuri, wannan maganar ma da kika ji ina yi ni na sanya kai na ba wanda ya san da shi.
Ina daga ɗaki ina jin duk tattaunawar da suke yi, a gefe kuma Indo na bani labarin halin da Hassan ya shiga, duk sai na ji damuwa ta lulluɓe mini zuciya, ina son Hassan har cikin raina, don shi mutum ne mai daɗin zama. Da ina da iko da na roƙi Hajjo ta barni na koma gidan mijina, sai dai kuma bazan iya hakan ba. Ina ji ina gani suka tafi.
Zuciyata ta gama yanke min hukuncin na samu Hajjo kawai da maganar ko za ta sauƙo ta amince........ ✍
_*Wannan littafin na kuɗi ne, da naira N300 kacal zaki more karatunki. Idan kina da buƙata zaki tura N300 ta wannan account ɗin 9061638128, Sumaiya Mohammad Tukur, Opay. Sannan shaidar biya ta wannan lambar. 09061638128. Daga nan sai a antaya ki a paid group.*_
⚡ SHAFUKAN ƘADDARATA ⚡
_*(Pages of my destiny).*_
STORY AND WRITTEN BY:
Sumaiya M Tukur (the Charismatic).
PAGE 10.
Da dare bayan mun kammala komai na je ni har ɗaki na samu Hajjo. Har ta yi shirin kwanciya, Baffajo bai dawo ba yana can masallaci yana bada karatu wa maza magidanta, sai zuwa ƙarfe goma zai dawo.
Wuri na samu na zauna na yi shiru, ina ta ƙoƙarin tattaro ƙwarin gwiwa na yafawa kaina, na rasa ma ta ina zan fara yiwa Hajjo maganar da ta kawo ni.
Ganin shirun nawa ya yi yawa ya sanya Hajjo tashi daga kishingiɗar da ta yi ta dube ni ta ce.
"Lafiya kuwa Shatu, ko dai akwai abin da ke damunki ne?"
Na rasa me zan faɗa mata, kawai sai na samu kaina da furta, "Ba komai Hajjo"
Tashi ta yi ta dawo kan tabarma inda nake zaune,ta ƙare mini kallo ta cikin hasken fitilar ƙwai da ta kunna, kafin ta ce.
"Shatu ke nan, tabbas da magana a bakinki, kin san sarai na san ki ciki da bai, menene yake damunki da har zaki kasa faɗa mini, akwai wacce zaki iya faɗawa matsalarki ne bayan ni?"
Girgiza kai na yi na ce, " Da gaske Hajjo ba komai"
"ƙarya ki ke Shatu, tabbas akwai wani abin, maza sanar da ni."
Saddakarwa na yi kawai na ga gara na yi shahada na faɗa mata ko za'a wuce wurin. Na buɗe baki da ƙyar na ce, "Uhmm dama.... Dama Hajjo Uhmm... Maganar ne da naji... Naji dazu......" Sai kuma na yi shiru na kasa ƙarasa maganar tawa.
Wani murmushi na gani a kan fuskar Hajjo wanda na kasa fassara ma'anarsa. "Aishatu" naji ta ƙira sunana, na amsa da na'am. Kafin na ji ta fara faɗin.
"Tun ɗazu da su Yaya Zulai suka tafi na fahimci akwai canji a tare da ke, ban san me suka faɗa miki ba. Haka tun shigowaki ɗakin nan na fahimci dalilin, don dama na yi tunanin haka zata iya faruwa."
Numfashi ta ja ta sauƙe kafin ta ci gaba da magana. "Kiyi haƙuri Shatu, ba wai haka nan kawai na hana ki komawa ɗakinki ba, ai ba wata Uwa da zata so goga kafaɗa da ƴarta a gida, musanman ma da sunan zawarci. Sai dai ki sani halin Zainaba nake jiye miki, don ni na san har abada ba za ta taɓa canza halinta ba. To kin ga ina anfanin zaman auren da babu kwanciyar hankali a ciki? Da zan baki shawara ki ɗauka da na ce kiyi haƙuri ki cire Hassan a ranki kamar yadda na faɗa miki tun kafin aurenku."
Hawaye na share na ce, "Shikenan Hajjo, Allah ya sa haka shi yafi alheri."
" Ameen Shatu, Allah ya sauƙeki lafiya."
Ban iya amsa ta ba na miƙe na mata sallama na wuce ɗakina, kuka na sanya ina shafa cikina ɗan wata huɗu da ya fara tasawa, tunani da kewar mahaifinsa sun cika zuciyata. Haka kawai sai na samu kaina da sakin murmushi na shiga hira da ɗan cikina. Wani iri na ji kaina ya na yi, a take na rufe idanuwana, nan kuwa na fara hango wasu al'amura da suke yawo a kaina, gani nake kamar hoton mace mai ciki kwance tana shafa cikinta kamar yadda nake yi a yanzu, sai dai saɓanin ni ita da wani ko wata a gefenta da yake mata hira da bana ji.haka nake hango abin kamar wasu gwaiguna. Ganin zan ƙarawa kaina ciwo ne a kan wanda yake yi, ya sa nayi saurin bude ido na. Ilai kuwa wani irin sarawa kaina yake kamar ana shirin saukeshi daga kan wuyana. Haka na yi ta fama da shi har na samu wani wahalallen bacci ya ɗaukeni mai cike da mafarkin rabin raina.
HAJJO.
Hajjo kuwa maganar da suka yi da Shatu ya tsaye mata a rai gani take kamar ba ta mata adalci ba idan ta dage sai an raba auren nan, don kuwa ta hango soyayyar Hassan ɗin a idanun Shatu, kuma ta shaida yanda shi ma Hassan ɗin yake ƙaunar Shatun. Tunanin da take kenan har Baffajo ya dawo. Bayan ya gama komai ya yi shirin kwanciya ne Hajjo ta ke faɗa masa maganar da tayi mata tsaye a rai.
Numfasawa Baffajo ya yi ya ce, "Maganar gaskiya Mariya ita ce, a bar Shatu ta koma ɗakinta, tun da dai shi mijin tsakaninsu ba matsala, ta je ta ci gaba da haƙuri da mahaifiyarsa, ita kuma kalar shafin da ƙaddarar aure ta buɗo mata ke nan, dama kowa da jarabawar da Allah yake jarabtansa da shi a gidan aure. Addu'a kawai zamu taya ta da shi. Komai zai wuce da izinin Allah."
Wani gwauron numfashi Hajjo ta sauƙe ta ce, "Shi kenan malam, Allah ya zaɓa mana abun da yafi alheri."
"Ameen" Baffajo ya amsa mata. Daga nan suka kwanta tare da addu'a suka yi bacci.
HASSAN.
A ɓangaren Hassan kuwa tashin hankali ya ƙara shiga, shi duk a tunaninsa komai ya wuce, tunda dai gaskiya ta fito, ashe bai san cewa akwai sauran rina a kaba ba. Ya samu da ƙyar da suɗin goshi Inna ta amince ya maido matarsa, bayan roƙo da magiya da Yaya Salisu da Adda Habiba suka yi mata, da kuma Inna Zulai, sai ga kuma wani batu daga gidan su Shatun.
Tun ranar da Inna Zulai suka je dubiya, suka koma suna faɗawa Inna abin da ya faru ya mayar da gidan Baffajo wajen zuwansa. Don kaff hiran da suka yi a kunnen Hassan ya faɗa. Magiya da ban baki da roƙo ba wanda bai yiwa Hajjo ba. Duk da ta sauƙo ta haƙura zata koma, amma sam ta ki nunawa Hassan ɗin haka, ta fi son sai manya sun zo biko don ta kafa musu nata sharuɗan.
Kamar ya sani kuwa ya shiga gayyato Yaya Salisu suna zuwa ban haƙuri, ganin abin ya ƙi aiki kawai Yaya Salisu ya kawo shawaran zuwa wurin kawu Sanusi, tun da dai shi ne walikin shi Hassan ɗin, sai a samu waliyyin Shatu a zauna. Don har ga Allah ya gaji da ganin ƙanin nasa cikin wannan yanayin, tun da aka yi auren nan Inna ta hanasu kwanciyar hankali, gabaɗaya Hassan ɗin ya fita hayyacinsa.
Da wani yammaci Yaya Salisu ya je har gidan kawun nasu, ya kora masa jawabin duk abin da ke faruwa.
Kawu ya muskuta ya ce, "Salisu ke nan, ai na ɗauka mun gama rufe babin nan da ni da ku, ko ban faɗa muku bayan karɓo masa aure ba abin da zan sake shiga na sha'anin abin da zai biyo baya ba?"
Ƙasa Yaya Salisu ya ƙara yi da kansa cike da girmamawa ya ce, "Haka ne kawu, tabbas anyi haka, amma dai daurewa zaka yi, a matsayinka na babba kada ka biye wa shiririta da rashin hankalinmu. A daure dai kawu a saka baki, wallahi Hassan yana cikin wani yanayi, kar ka so ka ga yanda ya lalace."
"wannan kuma shi ya jawo wa kansa, lokacin da aka hanashi aurenta ba gani yake kamar ƙaunarsa ne bamu yi ba, tun da aka yi auren wani kwanciyar hankali ya samu. A nan na ce masa ga Saude ƴar'uwarsa ya zo ya aura, na bashi halak malak ya bijire, ai dama duk mai jayayya da maganar iyayensa ba zai ga dai dai ba."
"Ayi hapuri Kawu, mai afkuwa dai ta riga ta afku, amma insha Allah gaba za'a gyara. Don Allah a duba wannan lamarin."
Bayan doguwar muhawara, daga ƙarshe dai Yaya Salisu ya samu da kyar ya shawo kan Kawu ya amince zai je ya yi magana da malam ɗin. Godiya ya masa da alheri ya tafi.
Washegari kuwa Kawu ya samu Baffajo bayan sun fito sallah ya tare shi da maganar. Baffajo ya nuna masa ba komai ai magana ta wuce, in Allah ya yarda Shatu zata koma ɗakinta, suka yi musabaha suka rabu kowa ya kama hanyar gidansa.
Kawu na komawa ya nemo Yaya Salisu ya shaida masa yanda suka yi da Baffa ya kuma faɗa masa ya gama aikinsa. Farinciki fal ransa ya koma ya samu Hassan ya sanar masa. Shi ɗin ma baki har kunne, godiya yake ta zubawa Yaya Salisu ba iyaka har sai da ya dakatar da shi.
Yamma ta na yi kuwa ya ɗau wanka iya wanka ya ƙure adaka, ya bulbula turare, ya yiwa gidan malam Bashari tsinke. Da sallama ya shiga gidan, Hajjo ce kaɗai zaune a kan tabarma tana tsintan wake. Ita kuma haka take, bata iya zama ba abun yi.
Ganin Hassan ya sa ta ƙara haɗe fuska, a take gwiwowinsa suka yi sanyi, haka dai ya daure ya nemi wuri ya zauna kafin ya gaisheta. Kadaran kadahan haka ta amsa shi. Sai ya samu kansa da kasa tambayar Shatu.
SHATU.
Ina daga cikin ɗaki kamshin turaren Hassan ya kai wa hancina ziyara, a yau dai kam na kasa haƙura, na sako kallabi na fito. Karaf idanunmu suka sarƙe a na juna, wani irin saƙo muke aikawa junanmu ta cikin ido. Ni na fara kawar da nawa idon na mayar kan Hajjo wacce ta saki baki da hanci ta na kallonmu. Ba ta ce komai ba sai gani na yi ta ɗauki tiren wakenta ta yi shigewarta ɗaki. Hakan ne ya bani damar zuwa kusa da Hassan na zauna. Ƙare masa kallo nake, ganin yanda duk ya rame ya zama wani iri, sai dai kuma wannan kyaun nasa tana nan. Murmushi muka sakarwa juna kafin ya ce.
"Na yi kewarki Shatu"
Murmushi kawai na masa, duk hiran da yake min ban iya furta masa komai ba, ni kaina a lokacin na rasa dalili, farinciki kawai nake ji a zuciyata irin wacce na daɗe ban ji ba. Haka ya ƙaraci zancensa ya tafi gab magariba. Sai bayan tafiyarsa ne na fara mamakin ya aka yi Hajjo ta sauƙo, to ko dai fushi ta yi don na fito ta shiga ciki ta barmu. Murmushi na yi na ce.
"Allah ya huci ranki Hajjota, amma dai idan fushi ne ma ni ya min rana" na tattare wurin na yi alwala na shige ɗaki.
Bayan kwana biyu sai gani na yi Hajjo tana ta faman yi mini shiri, da gyaran jiki irin na gargajiya. Abin ya ɗaure min kai, ban tamabayeta ba na barwa raina. A kwanakin kuwa kullum sai Hassan ya zo kuma Hajjo bata korinsa, sai na ga ma kamar ta ɗan fara sakar masa fuska. Sati biyu Hajjo ta yi tana min wankan lalle da wasu gayran jikin, irin wanda ba zai cutar da mai juna biyu ba.
Wata ranar Alhamis da dare ta pira ni, nan take shaida min gobe zan koma ɗakina. Ban san lokacin da wani murmushi mai bayyana farinciki ya ziyarci fuskata ba. Ban san lokacin da na ce wa Hajjo "Da gaske."
Make ni ta yi ta ce "Ja'ira, da wasa."
Tashi na yi na fice da ɗan sauri na nufi ɗakina, wani irin nishaɗi nake ji, ji nake ina ma yanzu Hassan na kusa da ni. Ranar dai bacci ɓarawo ne ya sace ni, asubar fari kuwa na farka, shafo cikina na yi na ce, "Yau dai kaima kwanan gidan mahaifinka zakayi." Fita na yi na ɗauro alwala na zo nayi ta jera nafilfili ina godewa Allah kafin lokacin sallar asuba ta yi.
Washegari kuwa da yamma sakaliya Hajjo ta sa ni a gaba ta maida ni ɗakina da kanta. Abin ba ƙaramin mamaki ya bani na, a iya sani na al'adarmu ta Hausa/Fulani ba a haka. A wannan karon ma wurin Inna ta fara kaini, daga baya ta kaini ɗakina ta min nasiha sosai kafin ta tafi. Sai naji kamar kar ta tafi.
A wannan dare mun nunawa junanmu ni da Hassan irin kewar da muka yi, dare ne da ya shiga kundin tarihin rayuwata ya zauna daram, munyi salloli muka miƙa godiyarmu ga mai duka. Ko yanzu kuma wani kalar shafi ƙaddarata zata buɗo mini a wannan karon, ko ma wacce iri ce Allah ya sauƙaƙa min ya sanya ya kasance mai daɗi ba irin na baya ba.
Washegari da safe na yi wankana na fesa kwalliya da wata sabuwar atanfa da Hajjo ta ɗinka mini. Na yi kyau kuwa da cikina dan wata biyar da ya taso sai ya ƙara mini kyau. Ina lura da Hassan yanda ya kasa ɗauke idanunsa a kaina, sai yaba kyawun da na yi yake. Mayafi na ɗauka na ce masa bari na je na gaida Inna. Tare muka je gwanin sha'awa.
Ba laifi Inna ta amsa gaisuwata da ƴar sakin fuska, har da tambayata ya ya ƙarfin jikin. A kunyace na amsa mata.
Zamanmu da Inna wannan karon ba wata damuwa, ina kama mata aiyukan gida waɗanda ya kamata.
A lokacin da cikina ya shiga watanni bakwai, watarana Inna ta yi wata baƙuwa, a yanda na ji suna faɗa aminiyar Inna ce ta zo daga can wani gari. Ban san me ya faru ba tun bayan da baƙuwar ta tafi na fara fuskantar matsala da Inna, zagi da hantara ba wanda bata mini, gabaɗaya na kasa gane kan Inna, aikin gida kuwa sai ta ninka mini su, bata duba halin da nake ciki ba.
Tun Hassan bai fahimci halin da ake ciki ba har ya gane, ko da ya samu Inna da maganar sai ta fatattake shi, duk iya yinsa ya kasa gano abin da ke faruwa. Dole ta sa ya haƙura, kullum cikin bani haƙuri da tausata yake.
A lokacin da cikina ya shiga wata tara kuwa aikin sai yake bani wahala sosai, gashi