An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
⚡ SHAFUKAN KADDARATA ⚡.
STORY AND WRITTEN BY:
Sumaiya M TUKUR (the Charismatic).
GARGADI: Ban yarda ba, ban amince ba a sauya min labari, saboda hakin mallakata ce, a kiyaye.
Wannan labarin kirkirarre ne, idan ya yi kama da rayuwar ki/ka, to arashi ne.
01.
Dandazon taron jama'a ne ke fitowa daga wani ƙaramin masallaci, sai raba goro da alawa ake yi, ga dukkan alamu ɗaurin aure aka yi a ciki.
Daga can gefe kuwa wani kyakkyawan matashi ne cikin wasu sutura masu kyau na dai dai ƙarfinsa wanda suka ƙara fito masa da kyawunsa, fuskar sa ɗauke da kyakkyawan murmushi, sai faman gaisawa ya ke da mutane cike da murna da farincikin da ya kasa ɓoyuwa a fuskarsa.
Suna nan tsaye wani dattijo ya zo inda suke, fuskarsa a haɗe kamar hadarin tsakiyar Augusta, yana isowa ya kamo hannun saurayin ya damƙa masa goro da alawa kana ya ce, "Gashi nan Hassan, ga goron ɗaurin aurenka, yau na sauƙe nauyin da kuka ce nawa ne, a yau dai na karɓa maka auren wacce kake so kake muradin kasancewa da it. Sai dai ina son ka sani, duk abunda zai biyo baya kada ka neme ni, tun da dai nayi iya bakin ƙoƙarina, amma kai da Salisu kun nuna min ba ni na haife ku ba, to kuje, ga ka ga matar, Allah ya sanya alheri, don bazan maka mugun baki ba. Daga haka ya kaɗa malum malum nashi ya yi gaba ba tare da ya jira jin abun da zai ce ba.
Jikin Hassan ne ya mace, walwalar fuskarsa ta ragu, abokinsa Isah dake kusa da shi ne ya shiga kwantar masa da hankali da cewa; "Haba Hassan, ka kwantar da hankalinka, kada ka bari maganganu Kawu Sanusi su gusar da wannan annurin da ke kwance kan fuskarka, yau fa ranar ka ce ranar farinciki, ka mallaki abar ƙaunarka, to mai zai dame ka kuma bayan burinka ya cika? ka yi haƙuri kar ka bari mutane su fahimci halin da ake ciki "
Kallonsa Hassan ya yi fuska ɗauke da damuwa kana ya ce; " Dole na shiga damuwa Isah, ko ka san kaf gidanmu ba mai son aurennan, hatta fa Inna, daga ni sai Yaya Salisu da Adda Habiba, wallahi tausayin kaina da na Shatu nake ji, da kuma yaran da zamu haifa gaba."
Dafa shi Isah ya yi ya ce, "Ba abun da zai faru sai alheri, ku yi ta addu'a, komai yayi farko yana da ƙarshensa, a hankali sai kaga watarana komai ya wuce kamar ba'ayi ba, na tabbatar watarana kowa zai so Shatu, ko don kyawawan halayenta." Haka ya yi ta lallabashi da kwantar masa da hankali har ya dan saki fuska.
************
Da gudu Harisu kanin Hassan ya shigo gidan yana haki, ɗakin Inna ya wuce inda suke zaune da yan'uwanta da suka zo biki, yana zuwa ko sallama bai yi ba ya ce, "Shikenan Inna, wallahi an ɗaura auren Yaya Hassan, yanzu aka watse."
Wani tsaki Inna ta ja mai sauti ta ce, "To meye ne na zuwa faɗa mini, har wani labarin farinciki ne wannan da zaka wani zuro a guje kana gaya mini, ni wallahi har ka ƙara ɓata mini rai, tashi je ka."
Inna Zulai yayarta ce ta dube ta ta ce, "Haba mana Zainaba, ai kya ce ko Allah sanya alheri ne ina laifi, amma sai ki hau sababi?"
Inna ta dube ta ta ce, "Wallahi Yaya idan na tuna da wai Hassan ɗina ne ya auri waccan mai kama da sadakayallar ko, raina suya yake min, ace duk matan garinnan Hassan bai gani ba sai waccan baƙar dagan? tsintacciyar mage?"
Inna Zulai? ta ce, "To yanzu tunda an riga ana ɗaura, ai sai ki sanya musu albarka, ba mu san me Allah yake nufi da haɗa wannan al'amarin ba, ko fa me zakiyi baza ki hana abun da Allah ya riga ya ƙaddara ba, don haka kiyi haƙuri ki saka musu albarka."
Hmmm kawai Inna ta ce ta ja bakinta tayi shiru, aka ci gaba da hidiman biki. Ko da la'asar tayi kuwa aka fara shirin zuwa ɗauko amarya, amma firr kowa ta ce bazata ba, har waye amaryar, ta dawwama a gidansu mana, idan shi mijin ya ga zai iya sai ya je ɗauko ta, ko danginta su kawo ta idan suka ji shiru, sai da Inna Zulai ta tsawatar tukun aka samu mata uku da zasu je, ciki kuwa harda Habiba Yayar Hassan.
**********
Zaune nake a ɗakin Hajjo,ina tunanin sabon shafin da ƙaddararta ta buɗo mini a yau wanda ban san me zan tarar a ciki ba. Tun bayan da aka sanar da ɗaurin aurena da Hassan, yau ita ce ranar da ya kamata na kasance cikin farin ciki mara misaltuwa, sai dai kash damuwa da tunani su suka maye wannan gurbi, damuwar wace iriyar zama zanyi a gidan su Hassan tare da Innarsa, da kuma tunanin rabuwa da Hajjota, su suka haɗu suka hautsina min kwanya ta, duk wani bidirin bikin da ake yi ina daga ciki ina jiyowa, dake fashin sallah nake, shiyasa ko leƙe ban leƙo ba.
Inna Hari ce ta shigo, wacce ƙanwa ta ke a wurin Hajjo wato mahaifiyata, ta iske ni cikin wannan halin, da yake ta riga ta san komai ke faruwa, rarrashi da ban baki ta shiga yi min haɗe da nasiha cikin hikima da kwantar da hankali, kafin ta umarce ni na fito za'a min wankan tafiya ɗakin miji.
Haka na fito jiki ba ƙwari, na isa inda aka tanadar mini don zama yin wankan. Wani al'ada ne da ake yiwa ko wacce amarya a ranar aurenta. Lalle aka fara shafe min jiki da shi, bayan ƴan mintuna kuma aka ɗauraye shi da ruwa, daga nan sai wankan ruwan madara wanda aka tatsa daga jikin saniya, sai a biyo baya da wankan ruwan ƙamshi, daga nan kuma sai na je nayi wanka a bayi na fito. Wasu sabbin kaya Inna Hari ta bani na saka, sannan ta lulluɓe ni da mayafi har fuskata, kafin ta rike hannu na muka nufi wurin Baffajo, Ya min nasiha sosai game da haƙƙin miji da mata, da kuma muhimmancin iyayen miji, ya jima yana mini nasiha kafin aka kaini wurin Hajjo, ita ma nata ta ɗaura a kai, kafin a mayar da ni ɗakinta.
Ina zaune daga ni sai, Haule kawata, wacce ta kasnace ita kaɗai ce ƙawata ta sosai, muna jiran zuwan ƴan ɗaukan amarya, tana daɗa kwantar min da hankali. Zuwa can kuwa muka ji sallamar ƴan ɗaukan amarya, Inna Zulai ce da Yaya Habiba, sai wata panwar Babansu Hassan Karime, inda cikin mutunci aka gaisa, sai dai ita karime sai yaɗa habaici take a fakaice, wannan ma Inna Zulai ta ja mata kunne sosai kafin zuwansu, daga nan suka tasa ni a gaba muka tafi tare da masu min rakiyar, banda kuka babu abun da nake yi, duk iya yanda na so in rarrashi kaina abun ya ci tura.
Koda isarmu ɗakin Inna aka fara kaini, haka ta karɓe mu kadaran kadahan, ba yabo ba fallasa, daga nan aka ɗauko ni zuwa ɗakina, wanda aka ɗan kewaye da zana, yana ɗan nesa kaɗan da na Inna, muna zuwa, Inna Hari ta sanya nayi bismillah tare da jerin addu'o'i kafin suka shigar da ni. Ba laifi ɗakin mai ɗan girma ne, wanda aka sanya masa madaidaicin gado, sai sauran kayan jere na da yake gefe, tare da tarkacen kayan girki na, baya ƴan gyare-gyare da aka yi, kowa ya watse ya barni daga ni sai Haule, wacce ita ma ba jimawa zata yi ba zata tafi, tunda ba jiran zuwan ango zata yi ba. Ana magariba kuwa ta min sallama, kamar kar mu rabu, hawaye shabe shabe haka ta tafi ta barni ni kaɗai, a gidan da zan riski sabuwar rayuwa.
Ina zaune ba wanda ya leƙo ni, tun ina jiyo hayaniyan mutanen gidan har na ji shiru daga baya, alamun an watse kenan, duk zaman kaɗaici ya ishe ni, tunowa nayi da ina gida yanzu muna hira da Hajjota, cikin farin ciki muna nishadi. Ango na bai shigo gidan ba sai da tara ta gota, ya shigo da yar ledarsa da aka gaso masa yan shila.
Dakin Innarsa ya fara zuwa, can kuwa sai gashi ya shigo da sallama, da alamun damuwa akan fuskarsa, amsa masa nayi ina sunne kaina, zama ya yi ya dafe kansa da hannu bibbiyu, kafin ya cire ya dube ni yana saka wa fuskarsa murmushin ƙarfin hali, haɗe da faɗin, "Barka dai Shatu tauraruwar Hassan, amarya bakya laifi, to a ɗan buɗe min fuskan mana na gani."
Ƙara sunkuyar da kaina nayi nima ina sakin murmushi ta ƙasan mayafi na, banyi aune ba sai gani nayi ya ɗage lulluɓin da yake fuskata yana leƙowa. Cike da kunyarsa na daɗa sunne kaina ƙasa. Gyara zama ya yi kafin ya kira sunana yana mai ɗago fuskata, jin yadda ya kirani ya sanya na ɗago na kalle sa kafin na sake sadda kaina. Magana ya fara min ya ce.
"Aishatu, ina mai baki haƙurin abun da za ki ji ya fito daga bakina" Rass na ji gaba na ya fadi, sai dai ban ko motsa ba, ya ci gaba da cewa. "Kinsan komai Shatu ba sai na sake faɗa ba, ina mai roƙon ki da kiyi haƙuri, tabbas ina tsananin ƙaunarki, kuma wallahi bazan taɓa tozarta ki ba, amma Shatu sai kinyi haƙuri da yan'uwa na, musanman ma Inna, kinga ita Uwa ce, ban so muka zauna a gidannan ba, amma wannan umarnin Inna ne, kuma bazan taɓa iya ƙetare shi ba, na san ki da haƙuri da kawaici, don Allah ki ƙara akan wanda na sanki da shi, sannan hakurin zai fara tun daga yau, saboda Inna ta karɓi yan shilan da na sayo miki na amare, amma ki bini bashi zan biya." Ya ƙarashe yana sake min murmushinsa mai tafiya da guntun imanina.
Sai a lokacin na ji hanaklina ya kwanta, nima murmushin na saki na sadda kai na ƙasa na ce masa, "Haba kar ka damu don wannan, ai komai Inna ta yi ta isa ne, da ni da kai duka dole mu mata biyayya, kuma in Allah ya yarda zaka same ni fiye da yanda ka ke tsanmani , fata na kaima kayi haƙuri kuma ka kasance mai yi min uzuri a rayuwa, saboda dan Adam ajiizi ne."
Ga dukkan alamu ya ji daɗin kalamai na, don na gani a fuskarsa, daga nan ya umarce ni in yo alwala mu gabatar da nafila, nan kuwa gizo ke saƙar, don ban san ta yanda zan sanar masa bani da tsarki ba, har ga Allah kunyarsa nake ji, da kanshi ya fahimci halin da nake ciki, girgiza kai kawai ya yi haɗe da murmusawa ya ce, "Shatu sarkin kunya" daga haka ya fice ya yo alwala ya dawo, shafa'i da witiri na ga yayi, kafin ya yi addu'a ya miƙe, sauya kayan jikinsa ya yi ya haye gadon, inda nake ƙudundune ya kwanta,ya umarce ni da in rage kayan jikina don inji daɗin bacci, ina jinsa ya yi addu'a ya tofa mana, tun ina karanta wasiƙar jaki har bacci ɓarawo ya sace ni ba tare da na sani ba.
************
Kwance ya ke a cikin ƙayataccen falon gidan wanda ya ji dukiya da kayan alatu, kai da gani ka san kuɗi sun samu mazauni a wannan wuri. Matashi ne da bai wuce shekaru talatin da biyar zuwa da bakwai ba, rungume yake da wata kyakkyawar yarinya da apalla baza ta haura shekaru shida ba, idanunsa a lumshe suke amma ba bacci ya ke yi ba, a yayinda yarinyar take bacci kwance a kirjinsa yana shafa kanta mai ɗauke da yalwataccen gashi wanda ya sha gyara irin na yara ya yi kyau. Ya yi nisa a cikin tunani har bai san sanda ta iso inda ya ke ba, duk maganar da ta yi bai ji ba har sai da ta ɗan bugi kafaɗarsa tukun ya buɗe dara-daran fararen idanunsa da suka rine suka koma ja ya dube ta, sauƙe yarinyar ya yi a hankali ya kwantar da ita a gefensa kafin ya zauna da kyau ya fuskanceta.
Dattijuwa ce da aƙalla zata yi shekaru hamsin ko da biyar, wuri ta samu ta zauna kafin ta dube shi ta ce "Yanzu kai Safwan ba za ka cire wannan tunani da damuwa a ranka ba ko, so ka ke kaima na rasa ka kamar yadda na rasa Hasina ko, so kake ka zamar da Ayrah cikakkiyar marainiya ko, haba mana Safwan, ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi, na tabbata da Hasina zata dawo taga halin da kake ciki baza ta yi farinciki da hakan ba, ko baka yi imani da ƙaddara ba ne, Allahn da ya bamu Hasina shi ya karɓi abunsa, kuma ya fi mu sonta, addu'a kawai yanzu ta ke buƙata daga wurinka ba damuwa da kuka ba."
Girgiza kai ya yi tare da share hawayen da suka samu matsuguni a dandamalin fuskarsa kana ya ce, "Ki taya ni da addu'a Ammi, ina ƙoƙarin ganin na cire damuwa daga zuciyata, amma abun ya ci tura, Reina ta yi wani irin gini a zuciyata mai wahalar rushewa, kuma sai ta tafi a dai dai lokacin da nafi buƙatarta, Allah ya jiƙanki Reina, Allah ya kai haske kabarinki, halinki na gari ya biki."
"Ameen ya Allah." Ammi ta amsa tana mayar da dubanta kan Ayra wacce ta ke ta juyi alamun baccin baya mata daɗi, dubanta ta mayar kan Safwan ta ce, "Ya ya zazzaɓin nata ince dai ko ya sauƙa?"
Taɓa jikin nata ya yi kafin ya ce " Ai tunda aka mata allura zazzaɓin ya saupa, idan ta tashi sai ta sha magani."
Ammi ta ce "To alhmdlhi, sai ka kaita ɗaki ka kwantar da ita don na ga nan ɗin kamar kwanciyar bai mata daɗi ba."
Da to ya amsa ya miƙe tare da ɗaukan Ayrah ya saɓa ta a kafaɗarsa suka fara tafiya, har ya fara hawa step ya jiyo muryar Ammi tana faɗin, "Saura idan ka je ka saka ta gaba kana kallo kana kuka, don na san halinka sarai."
Murmushi kawai ya yi ya na girgiza kai ya ci gaba da tafiya ba tare da ya furta komai ba har ya ƙaraso ɗakin da ya kasance mallakar Ayrah ɗin kafin ya kwantar da ita a ƙayataccen gadonta na yara, ya ja blanket ya rufe mata rabin jikinta. Zaman kuwa ya yi a gefenta yana ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo, ba inda ta baro mahaifiyarta, hatta da farcen hannu da ƙafafunta irin na maa ɗin ta ne. Shafa kanta ya yi ya tofe ta addu'a kafin ya fito daga ɗakin.
Ammi na ganin ɓacewarsa ita ma share hawayen da suka makale mata tun ɗazu ta yi, tana matuƙar tausayin ɗan nata, tun bayan rasuwar matarsa Hasina yanzu shekaru biyar ake nema, bai sake wawala ba, idan kaga dariyarsa to da tilon ɗiyarsa ce Ayrah, sannan idan kana son ganin fushinsa to ka masa maganar aure. Ta rasa wacce iriyar soyayya ce yake wa Hasina, duk da kowa ya ji mutuwarta, saboda Hasina mutum ce, yarinya ce mai hankali da hangen nesa, ga kuma girmama manya, tun zamnasu baza tace ga abun da Hasina ta taɓa mata ba sai zallar kyautatawa, tabbas tayi rashin suruka, "Allah ya miki rahama Hasina, Allah ya raya miki ɗiyarki ya sa ta gaji kyawawan halayenki" bata san a fili ta yi addu'ar ba sai da ta ji Safwan ya amsa da "Ameen."
Murmushi ta yi ta ce"Har ka sauko kenan." Ya amsa mata da "Eh Ammi zan ɗan fita ne, bazan jima ba zan dawo."
"To Allah ya dawo da kai lafiya."
Ya amsa da"Ameen" ya fice........,✍️✍️✍️
⚡ SHAFUKAN KADDARATA ⚡
_*(Pages of my destiny)*_
STORY AND WRITTEN BY:
Sumaiya M Tukur (the Charismatic).
PAGE 02.
Bugun da ake yiwa ƙofar ɗakinmu da ƙarfi shi ne ya farkar da mu daga daddaɗan baccin da muke yi tun bayan dawowar Hassan daga masallacin sallar asuba. A firgice duk muka farka, Hassan ne ya yi ƙarfin halin tambayar waye ne.
"Ubanka ne! Nace Ubanka ne Hassan, nuna mini kayi mata, shi ne ka ƙunshe ta a ɗaki kuna bacci, tunda ga bayi kun ajiye nan cikin gida su maku aikin gida."
Hassan wanda ya fito tun lokacin da ya ji muryar Inna ne ya shiga girgiza kai kafin ya ce "A'a Inna ki yi haƙuri, baccin ne ya ɗan ɗauke mu, ina kwana, an tashi lafiya." Ya fada bayan ya durƙusa.
"Rike gaisuwarka ba shi na zo karɓa ba, ai idan ka so gaida ni ka san inda nake, ina ce dama daga ka dawo masallaci kake zuwa gaishe ni, amma daga kawo wannan makirar har ta fara biya maka nata salon karatun ko, munafuka."
Hassan da ke tsugunne ya sake sadda kansa ƙasa ya ce, "Wallahi Inna ba laifin Shatu ba ne, ha........"
"Shiru! Inna ta katse shi cikin tsawa kafin ta ci gaba da faɗin, "Ai dama ina zaka ga laifinta, bayan ta wanke ta baka ka shanye tun kafin ta shigo."
"Kiyi hapuri Inna" Hassan ya furta daga tsugunne da yake.
Inna ta sake haɗa rai ta ce, "Duk ba wannan ba, shiga ka taso ta maza ta je ta kama abun da ya kamata. Ina ta ke ma munafuka ai tana ji na, da ke ba uwarki ba ce ko albarkan gaisuwa ban samu ba, makira ai sai ki fito."
Gaba na ne ya faɗi da jin furucin Inna, tun lokacin da naji muryarta na so fitowa, amma jin ta fara yiwa Hassan masifa ya sa na kasa fita, saboda wani irin tsoro da tashin hankali da suka dabaibaye ni, don idan da abun da yake ɗaga min hankali bai wuce faɗa ba. A hankali na tako zuwa bakin ƙofar na sunkuya har ƙasa na ce, "An tashi lafiya Inna?"
"A'a! Ban tashi ba, algunguma, ai kina jina tunda na ke magana, kika yi muƙus a ciki, to shige mu je."
Haka Inna ta tasa ni a gaba muka wuce can cikin gidan. Wani tarin wanke-wanke ta nuna mini wanda da alama tun na bikin jiya ne ta ce, "To fara da wannan, kwanonin da akayi taron bikinki ne, saboda tsaban baƙinjininki aka rasa mai wankewa, idan kin gama ki same ni a ɗakina."
Da to na amsa, bayan ta shige na dubi tarin kwanonin wai kuma duka ni ɗaya zan wanke, ko da yake ma ai ya wuce wai, tunda dole dai sai na wanke, haka na ɗauko bokiti na nufi rijiyar da ke tsakar gidan na shiga ɗiban ruwan a tsorace, don kuwa tsoron rijiya ne da ni, shi yasa ko da wasa Hajjo bata aika na ɗiban ruwa. Bayan na gama jawo iya wanda nake ganin zai isheni ne naje na zauna na fara wanke kwanukan.
HASSAN.
Hassan kuwa tun bayan da ya ga ficewarsu da Inna ya koma ɗaki cike da damuwa, ya ja tagumi ya zauna, ya ma rasa me ya kamata ya yi, Shatu bata cancanci haka ba sam, tun shigowarta gidan daga jiya zuwa yau Inna ke son ganin ta baƙanta mata, sai dai ba yanda ya iya da Inna tunda mahaifiyarsa ce.
Yana nan zaune yana karanta wasiƙar jaki, tsam kuma ya tashi ya leƙa tsakar gidan, hango ta ya yi gaban tarin kwanuka ta na ta faman goge zufa tana wanke su ita ɗaya, daga can gefe kuma ɗakin ƙannensa ya ke jiyo hirarsu harda shewa, Inna kuwa tana daga nata ɗakin ita ma, wani takaici ne ya turnuke sa, to wai ne suke yi su a ɗaki da za'a bata duka wannan aikin ita ɗaya, sanin idan ya yi magana zai iya zama wani tashin hankali ya sa shi yin shiru ya lallaɓa ya je ya fara taya ta, duk da ta hana shi amma ya ƙi, nan suka ci gaba da aikin tare suna ɗan taɓa hira, sai kuwa ta ji damuwar da take ji ya ragu.
Can mun kusa gamawa kuwa sai ga Inna kamar an ƙira ta, wani sallallami ta saka tana tafa hannu wanda shi ya ankarar da mu wanzuwarta a wurin, tuni hankalina ya tashi, shi kuwa na lura ko ɗar bai yi ba, sai murmushi da ya sakar wa Inna. Tsinkayo muryarta na yi tana faɗin, "Mai zan gani haka ni Zainaba?, me zan gani haka Hassan?"
Kallonta ya yi ya ce, "Wai dama Inna gani nayi kamar aikin ya ɗan mata yawa shi ne nake taya ta don ta kammala da wuri, kar a ɓata miki lokaci."
Tafa hannu ta yi tana salati kafin na ji ta ce, "Anya kuwa Hassan, ah lallai dole na miƙe, zama bai ganni ba, to tashi ka bar wurinnan tun ban ɓata maka rai ba, ni na ce maka na damu da ɓata lokaci ne, ita kaɗai na ke son ta yi aikin, idan sauri nake ai akwai waɗanda zan saka, ɓace min da gani."
Ina kallo ya tsame hannunsa daga ruwan ya tashi, maimakon ya koma ɗaki sai gani nayi ya yi hanyar waje, damuwa fa bacin rai shinfiɗe a fuskarsa, haka na bishi da kallo har ya fice kafin na ji Inna tana faɗin, "Idan kin gama kallon sai ki ci gaba da aikin, ko kuwa bin sa zakiyi mara kunya, amaryar rana ɗaya har kinsan ƙure miji da kallo, wa ma ya sani ko akwai wani baƙin tabon da