da fadar
manzon Allah(S. A. W) inda yake cewa baya tare da duk wani
mai raba zumunci,"saboda haka, Yallabai don girman Allah
kasaki zuciyar ka akan safiyanu, nayi maka alkawarin koma ace
zaka mutu, wallahi bazan taba auran duk wani tsatson
safiyanuba, to balleshi.
Kai kuma kanka kasan dai ba sakina zakayiba, balle kace
kozan koma wajansa, kai koma kasakeni ni fa bazan auri
safiyanuba, da ina son auranshi, wallahi tuni da nadade da
aurannshi, saboda munyi shekara shidda da shi a baya, haba
Yallabai,"
"Hamida kinfi fa matarsa kyau," nayi murmushi, "to sai
me? Kasan dai ba'a canjan mata balle kace zai iya rokonka
arzikin ku canja a nan gaba,"Hamida,"nasa hannu na shafa
83
gashinshi dayake kwance a cinyata,(You shoulda always
remember lam your wifc and I would continue to be uptil th end
of our life) ka tuna irin yanda mukayi a baya ni da kai wanda har
ranar da aka kawoni gidanka ban taba yardarwa zuciyataba kaine
angon da aka daura mani aure dashi ba.
Amma ka duba yanzu gamu da danmu wanda muka haifeshi
bana aroba,Yallabai me ya kawo mana haka? hakuri da kawar da
abubuwan da suka faru a baya daga zukatanmu, please my love
bana son inga kana sawa zuciyarka shakku a kaina.
Ka tuna nice matarka ta farko, kayi tunani nimafa gaba
zaka iya cewa zaka auro mani wata mu zauna tare, mudinga
rabaka biyu ni daita, (sharing) muraba komai na mallakinka
biyu, amma duk na hakura na danne kishin hakan nazo na zauna
da kai ba tare da na dinga tunano hakan ba har na daukeshi na sa
a zuciyata, saboda kawai ina son mu samu zaman lafiya a
junanmu.
To kana tunanin ko ni bani da kishine,wallahi Mustapha
nafi kowa sonka a dun'yarnan, amma acire Maama kada kayi
tunanin zuciyata na tunanin wani da namiji inba kaiba,("you are
the oniy one in my mind)
A hankali na saki dan kukan da yake tafiya da kissa da kara
raunana zuciyar duk wani mai jinshi, shin ko baka yarda daniba
ne Yallabai? kokana tunanin in ka sakarwa sufiyanu fiska zanci
35 amanar
"Ya isa Hamida na amince da ke dari bisa dari, dama ina
kin sakin jiki da shine gudun kada yazo yalike a gidana, "inka
sakarmasa fuskar yin hakako?" to naji kiyi hakuri in sha Allah za
kiga canji, amma duk da haka sai ki danyi mani hakurin yin
canji a hankali," ya tallabo fiskata an hakura,?".
Na daga kaina, ayi mani murmushinnan mai sanyaya mani
zuciya, nayi murmushi tare da dukawa na sumbaci kumatunsa.
Taronsuna kam yayi kyau, yaro kuma ya samu sunan
Abdulyasir, Yallabai na kuwwa ya dan canja akan yarda ya dauki yi a baya, duk da nasan dai shi ke kaini gidan zulaiha,
kuma shike zuwa ya daukoni karfe shida na yamma.
84
Duk da haka dai ban Kara cemasa kornai ba, tunda ance
dama sai a hankali za'a rage.
*** *** ***
Maama ta yaye jiniyo, wanda mu kuma muka shirya
kayanmu mukatafi aikin haji, daga can muka wuce indiya bayan
mun gama aikin haji lafiya.
A indiya kwananmu goma sha hudu, inda suka dinga yi
mana mitar me yasa muka baro masu yaransu, shi kuma kakan
jiniyo cewa yayi damunzo dashi, da shikenan shi ya samu aboki,
amma duk da haka shima sai da yayi korafin inda ma muka dan
fita, da muka cemusu Maama tace zatazo dashi kwanannan da
mun koma.
Maimakon mu nufi gida Nigeria sai Yallabai ya dinga yawo
dani duk wata kasar da yasan yana hulda da su da inda yake da
gidaje, a karshe muka wuce faris(paris) inda Yallabai yake da
kamfani turare wanda sai da muka je kamfanin sai naga sunsa
"Hamida perfume company).
Mamaki yasa sai danace masa me ya sa yasa sunana haka,
ga sunan iyayensa da 'yan'uwansa sai yake gaya mani cewa
wannan kusan shine kamfani na karshe a cikin kamfanoni su shi
da mahaifinsa, saboda duka kamfanin shekararsa bakwai kenan
da budewa.
Cikin watanan biyu da 'yan kwanaki da nayi a kasashen
duniya, tAbbas ni kaina nassan nayi yawon bude ido wanda ya
kara sani na waye na kara dauko darrissa kala-kala daban-daban,
banda kyau da kiba mai mulmul da jikina da yayi.
Ranar da muka sauka gida Nigeria,ranar nayi murnar da ban
taba yi ba, saboda ganin iyayena da nayi, jiniyo kuwa ko kadan
kin yarda yayi damu, har babansa sai awayence tukuna ya dan
rika yarda da babansa.
*** *** ***
(Honey moon) yawan bude ido yayi dadi tunda gani a
kwance ina jinyar laulayin dan yaran cikina, wanda yanzu ya
85
shiga cikin wata na uku kenan, amma kafin ya kai mani wannan
lokaci nasan na dan ji jiki sosai.
*** ***
Allah mai nashi iko yauni Hamida ni ce mai 'ya'ya biyu wai
duk ni na haifesu, haka na saka yarana biyu a gaba suna barci, ni
kuma ina kallansu, Immal-Khari sunan da yarinyata ta ci kenan, wanda damani tun da na haife ta nasan sunan da za ta samu
kenan wanda yanzun ta samu wata goma kenan da haihuwa.
Karfe takwas na daran talata nike kwance ina yin wannan
tunanin, wanda hakan ya faru sakamakon bakin da Babansu yayi
a falan kofar gida.
Gajiya ce tasa daga ni har yaran muka nemi makwanci da
wuri kamar hąka, duk da nasan ni ban isa in runtse idanuwana
ba, tun da mai gidana baya kusa dani.
Gajiyar zuwa yini da naje gidansu Halimatu na bikin
kannanta da akayi, wanda aka hadashi da bikin 'yar kanwar
Mamata da take zaune a hannunta, ga ta biyawa gidan Zulaihat
jiya, shine yake tambayata, wanda yau kuma tunda safe muka
kara ziyartar gidan Momin su Halimatu, sannan muka wuce
gidanmu wajan mamana domin karasa tattauna harkokin, duk da
nasan bani kwana goma banje gidanmu ba, ko gidan Maama sai
dai in bani da lafiya ne, ko bani kasar.
Karfe tara da kwata na dare Yallabai na ya shigo ya sameni
a kwancan da, nike, a natsa ya zo ya zauna ya sunkuya ya
sumbaci goshina, yaya dai my love?" nayi murmushi, "me ka
gani", gani nayi kin yi shiru ke kadai kina ta tunani, shine nake
son a gaya mani ko tunanin me ake yi".
Na dan yi juya kadan na kama hannunsa ina wasa da yan
yatsunsa tare da mayar da hankalina a garesu, sannan na fara
magana ahankali, "dama tunani nake da gashi har na fara tara
yara, amma har yau baka yi mani wani zancan makaranta ba,
wanda dama ka sameni ina cikinta".
"Ban fahimceki ba", "wai manufata in koma makaranta in
cigaba da karatuna" "Saboda me kika yi wannan maganar
86
Hamida? Yau kinyi bakin ne? "Sai nayi baki zan yi maka
maganar makaranta", "E, gaskiya, saboda rabon da kayi mani
maganar karatu tun kina amarya, kuma in baki mantaba tun
alokacin na gayamaki ra'yina na ni nafison matata ta zauna gida
tana kulawa dani da kuma yarana.
Hamida nasan zakiyi tunanin abubuwa biyar din da mata ke
yawan tunanisu, wanda sune ke sa a kassarin matanmu yin
karatu, sune kamar.
Mutuwar miji
Rashi da taimakon Jama'a
Koyar da yara insun dawo daga makaranta
Ma'amula da jama'a
BAbban taro in mijinku ya zama wani abu.
Alhamdulillahi, Hamida duk matar da tace zatayi karatu, har
tayi aiki saboda wadannan abubuwan da na lissafa, bai can canci
'a hanatashiba, sai dai ni anawa tsarin, gaskiya ba zan iya
barinkiba saboda ni nasan dukkan abubuwan da na lissafa ni na
riga nasan kowanne daga ciki kina da shi 'a kwakwalwarki.
Misali mutuwa, Hamida nayi imani da Allah in na mutu, ina
da dukiyar da zaki kwanta ki dinga cin abinci ke da yarana ko
dakuwa su ashirin na barmiki nasan kuma har ki mutu ba zata
kareba, koda kuwa bakwa juyata ta karu, tunda akwai shiyas ta
ko ina zasu dinga shigo maku.
Na biyu taimakon jama'a nasan zaki iya taimakawa jama a
ta ilimin da Allah ya baki ko kiyi aikin asibiti ko koyarwa, ko
wani abu da zai taimakawa jama'a.
Anawa tsarin ni kuma, a ganina in har kina son haka, to zan
bude maki kamfani da sunan nakine a dinga kawo maki ribar, sai
ki dinga taimakawa jama'a dasu.
Kinga a bangaren koyarwa, ki bude makaranta ki zuba
malamai su dinga koyar da 'ya'yan jama'a har da iyayensu,
bangaran boko ko islamiyya, sai ki dauke masu nauyin biyan
kudin makaranta, da duk wani abinda za'a nema a cikin
makarantar, kinga nan ma taimakone.
87
A 6angaran asibiti kuma, ki dinga kai ziyara asibitoci duk
sati kamar juma'a kenan, kina taimakawa bayin Allah gasu nan
da yawa a cikin duniya, ba wai nan asibitin Abuja ba, duk
asibotocin arewa ko baki je ba, kina iya dora Abdulrashid, nayi
imanin zai yi maki abinda ya fi haka, tunda yaro ne mai amanar
gaske.
Rashi, Allah ya zaremu dashi, ban wuce shiba amma rasan
ko ya samemu, ko baki da karatu na san ina da hanyoyin da za'a
koya maki sana'o'in hannu ki yi su, ki kuma samu da su, har ki
samma na kusă da ke, Allah ma ya kiyaye mu, wadanda suke
kai shi kuma Allah ya yaye masu da gaggawa. Amin.
a
Kin san dai kina da ilimin da zaki koyar da yaranki ko da
kuwa za su wuce jami'a, saboda kin samu darin karatu mai kyau
tun kina yar yarinya karama "Foundation", saboda haka nan
fangaran ma nasan bani da shakkun komai a kanki, sai dai Allah
ya tayaki ki kular mani da yarana.
Bani da wata faduwar gaba akanki ta fangaran ma'amalla
da duk wani wanda zai shigo gidan nan, ko ki kai mashi ziyara,
saboda nasan karatun da kika yi baya ya wadatar da ke akan
komai na ma'amalla da jama'ar duniya, saboda hak aki godewa
Allah tanan 6angaran. Sannan sanin kowane matata yar
masarice, kinga kuwa duk Nageria tasan da cewa masari garine
na hazikan masu kwakwalwa, sannan gata a Jahar Katsina, kinga
ba wani shakku kenan akan nan bangaren.
Taro kuma nasan ko da buturan Ingila zaki zauna hirar
kwana talatin ba tare da kin yi fargabar zai kureki ta wajan
Turanci ba", "Kai Yallabai, "karya nayi?" "ni dai bance ba,
amma ni ban iya turanci ba fa" "zan kawo Malama ta dinga
koyar da ke, mu gani Malamar zata koyar da falibar ko kuwa
dalibar zata koyar da Malama?".
"Ni dai Yallabai," "ke dai dame Hamida my beby? Hamida
wallahi duk matar da kika ga tana yawan yin aiki, wallahi in kika
zauna hira da ita, za ki ji ta ce maki bata son aikin nan, sai dan
ya zame mata dole.
88
Misali, Imma mai kishin al'umma a samu, ma'ana tana
aiki ne ba dan kudi ba, dan kishin mutanan mu, ko yaranmu su
tashi cikin ilimi, ko kuma matanmu a asibitoci, wallahi Hamida
da karatun likita ki ka yi, tAbbas ko baki je asibiti aiki ba, da sai
in ce na dauki nauyin bude maki asibitin kanki domin
taimakawa jama'a kawai.
Ko kuma karatun koyarwa, shima da na bude maki
makaranta, amma kiyi tunani, karatun girka mani-abinki fa kika
je kika koya, na kuma yaba na gode, tunda yanzu na san kullum
tumbina a cike ya ke ba yunwa a tattare da cikina, ko na
'ya'yana, kai har yaran dake tattare damu ma suna koshi kullum".
"Ni wallahi" "ke kiyi shiru Allah ko in sa kwado in kulle
maki bakin nan muga ta surutu" wallahi Hamida, masu aiki
mata, da kika gani, da daya daga cikinsu ne kawai suke yi dan
ra'ayi, amma ragowar duk saboda wasu abubuwan da na lissafa
maki baya suke karatun, har suka kai ga aiki.
Saboda wasu mazajan wallahi suna kwarar matansu sai dai
a ce sakayyarsu naga Allah, tunda wani yana da halin da zai
tallafawa matarsa da wata sana'ar a gida tayi ta dinga samu,
amma sai kiga ya kiya, har sai ta kaiga matsuwa ta nemi aiki da
kanta tana yi domin ta dan cin abinci mai kyau mai ko sitira mai
kyau. Ke dai wannan hirar tana da yawa, zaki iya bani wani
lokaci in yi maki ita a wadace, (a saurara cikin littafai masu
fitowa za'a samu cikakken bayani akan ilimi).
Ban manta da wanda na yi maku aikawali ba, watau na
maza masu yawon dare, ko mabukata sosai, ina son duk ku
saurareni, komai nawane ya na tafiya da tsari.
"Cikin tarairaya da nuna mani ni kadaice a gareshi, ya samu
ya lallasheni, tare da yi mani alkawalin bude mani kamfani na
kaina.
*** *** ***
Muna falo ni da yarana da yan yaran da suke zaune a
hannuna, na bangaran yan uwana, da dai sauran jama'a da ba
za'a raba su da gidan masu hannu da maiko ba, ko dan su kula da
rayuwarsu ta gyaru.
'Yan yarana, an baje anata 'Home work, aikin gida, wanda
nima ina cikin a zaune, ina kulawa da yanda suke yinshi,
sallamar da muka ji, ita ta dan dauke mani hankali, da na yan
yarana ma dake gabana.
Asana ne da akwatin giwa bAbbar jeje ya shigo dashi,
yallabaina ke nan yara, sai rugawa taryar yan tafiya. Indiya ni
kuwa ina zaune na hakince ko kallan kofar banyi ba, sai da naji
takun takalmansa ya shigo falo, sannan na daga kaina tare da yin
murmushin da nasan yana kara mani kyan fiskata, kallona da ya
tsaya, cak yana yi shi yasa na dan nuna masa da ido yara fa.
Sai a lokaçin yadan nuna, ai Fahat yake kallo wanda yake
zaune a gefena, yana ta daga hannuwa wai shima oyoyo Papa
dinshi ya dawo, yaran da ko rarrafe bai fara ba.
Ya taho har in da muke zaune, ya sunkuya ya dauki 'Fahat'
tare da ce mani (Come on my love) a hankali, na harareshi kadan
irin hararar da nasan ya kan biyani in nayi ta.
Ya mike ya dinga yiwa 'Fahat' wasa su kuwa ragowar yara
ana rike da shi ta ko ina, ina kallansu ya shige ciki dasu gaba
daya yana ta tambayarsu ya karatu, da sauran tambaya irin ta
yara, suma kuwa suna ta yi mashi surutunsu na yara.
Minti biyar tsakani sai gasu sun rugo da gudu, kowa da
kayan wasansa a hannu, wani jirgi, wani yar mota da dai sauran
kayan wasan yara, wanda suke ta ce mani Papan su ne ya basu
yace sai ya kwance kaya akwai wasu.
Na nuna masu na taya su murna tukunna na mike nima na
tafi tawa sannu da dawowar, sai dana biya dakina na kara gyara
fuskata tare da kara feshe jina da turaran(words for women)
sannan na dubi gashina na kara kwantar da shi yabi bayana.
Ina yin sallama yana tsaye ya jingina da tebirin cin abinci ya
harde hanneynsa a kirjinsa, ina shigowa sai aka kawar da kai
gefe daya, nayi murmushi, na isa gefan da ya mayar da fiskarsa
na jingina nima, "you are highly welcome, bai kalleni ba "I am
sorry please", haba my heart na dan jinkir tane ka gama da yan 90
yaranmu tukuna in zo in nuna maka cewa nayi bAbban Missing
dinka na tsawon lokaci, wanda har yasa sai da jikina ya dade
yana rashin lafiya, rashinka, zuciyata kuwa tun daga ranar da ka
tafi bata kara samun jin dadi ba, sai yau da kayi mata zuwan ba
zata.
Na mika hannuna ahankali na kama nasa, "har yanzu ban
samu karbuwa ba, ko an samu wacce ta fini ne a can?" sai na
saki hannunshi na dan juya," hannuna naji ya janyo, na juyo na
kalleshi tare da harar nan da nake masa,, "zan biya hararrar nan
yanzu, amma sai an yarda da zuciyar Mustapha ba kowa a
cikinta sai Hamida," ya janyoni ya kanga ajikinsa, "kin amince",
na daga kaina.
"To saura biyan kallo biyu da aka yi mani, na falo da na
nan, "ya tallabo kumatuna, ya kai bakinsa ga nawa nayi alamar
zan goce, "Hamida sati biyu fa, ya isa a tarye ni da duk ma
abinda na zo da shi", "Yallabai ka tsufafa ka saurarawa yara,
jiniyo fa ya girma," "don Allah ki daina yaran dan shekara goma
zaki ce wai ya girma, kannansa uku fa, "haba sai yayi kannai
takwas zan san ya dan fara girma, "Kai Yallabai nayi zantan
mun gama kenan hudu fa, "yanzun dan Allah baki ji kunya ba da
kika ambaci hudu, ni na yiz atan goma ma zaki ce.
Yallabai hudu fa da yawa," "gaskiya da yawa na amince
dake, amma a daure a karo mani biyu shidda, ko ya kika gani"
"ni dai gaskiya?" yayi mani mintsili a fiska wanda ya sakani yar
kara, wanda hakan yayi daidai da shigowar Ummal-khairi da
Amma mai sunan Maama kenan dauke da fahat suna surutai,
"Mam danki yana ta kuka wai sai na bashi jirgina, shine nace
bari in kawoshi wajan mamanshi ta siyo mashi nima Papana ne
ya siyo mani, ko Papa, yace kwarai Ummal-Khairi bata danta ki
tafi kiyi wasanki".
"Haba Ummata, yanzu ba zaki rika mani autan nawa ba, to
shekenan na gode "Amma" ruga ki kirayo mani Jiniyo ya rike
mani shi, an jima dashi zani makarantar yara".
"Ina zuwa Mam kinji," a'a bani zuwa da ke sai Ammata ko,
"E Mam da yaya ko "Mam", "Sai fa shi" "zan rike maki shi 91
Mam kinji, kinga naba danki jirgi, karbe girjinka, na ma bashi
duka kingani "Mam to shikenan ku tafi ki koya mashi kunnawa
shima
Suka fita a nata murna wai zani da dasu Unguwa, unguwar
kuwa makarantar yara ce na bude daga yan shekara hudu, zuwa
sha takwas, in sun gama aji shiddan bAbbar makaranta kenan.
Sannan in dauki nauyin wadanda iyayensu suka barsu
wucewa zuwa jami'a" yanzun haka wadanda na dauki nauyinsu
har jami'a kar sun kai shekarar fita kenan su kusa kammala digiri
dinsu, duk da nasan sune set na farko da na fara daukar nauyinsu
amma ina saran ba iyaka a bayansu.
Suna fita ya lokaci hancina, "wallahi Hamida har yau
kinanan da wayan nan naki da hikima, jiba yanzun cikin hikima
kin janyo hankalin yaranki gareki, sannu na gode Allah yayi
maki albarka.
Wannan shi ya nuna mani matar sarkin nace da rashin
zuciya tana kula mashi da iyalanshi ko bayanan na gode, "na dan
zame, "Allah ka daina tsokanata, za kasa yanzun in yiwa
sufiyanu waya in ce, ya zo tsohuwar matar da ya kusan samu,
abaya gata yanzu a samu".
"Ya yi saurin zan gashin kaina, "ni ni zakiyıwa haka na
kubuce na ruga, ya juya baya wai shi fushi, na dawo na juyo
dashi.
"Haba Papa, mantawa kayi ne, Hamida fa taka ce har abada
ka zuba ruwa a kasa kasha, ni da kai mutu ka raba takalmin
kaza", a", ya juyo ya yace "Allah Hamida?" "Da gaske "Papa" "sai
dai kuma da abu daya da kika manta," "to meye shi?" ya nuna
bakina, nace, "nakane shima to shi kenan yanzun kuwa zan karbi
abina" "Allah ya baka sa'a, ni yar kalloce, "yayi saurin tallabar
kumatuna ya nufi
Alhamdulillah
92
Na gode Allah da ya bani ikon gama wannan littafi, Allah yasa
zai yiwa masu karatu dadi, duk da an rubuta shine saboda
mahimmancin alkawali, amana da rike gaskiyarka, ragowar
kuwa rahace, ko ince domin mai karatu ya ji dadin fahimtar
abinda ake nufin koyarwa, ya kara mashi raha da annashuwa a
kiyaye da amana alkawali, gaskiya
Mu hadu a littafi na gaba mai suna (SAUYI)
ALLAH YA BANI IKON RUBUTASHІ
Mai kaunarku Anty Maryam
93
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels